CANJIN YANAYI SADY JEGAL 1-6

[4/14, 11:18 AM] Sady Jegal: CANJIN YANAYI

®NWA

DAGA ALK’ALAMIN Y’AR MUTAN JEGA

©SADY JEGAL

GODIYA
Godiya ga Allah mad’aukakin sarki mai kashewa mai rayawa, maji6incin bawanshi, mai juyarda al’amurra yanda yaso a kuma lokacinda yaso, daya bani ikon koma d’ora Alk’alamina domin sake kawo maku wannan gajeren littafin, kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min, yasa kuma sak’on ya isar muku cikin fahimta da hange.
YABO
Gareku d’aukacin masoyana dake nunamin so a gabana ko a bayana, nagode sosai Allah yabar k’auna a tsakaninku, da fatar zaku fahimci cewa nima ina sonku.

JINJINA
Gareku 
Sanah Ismail Suleiman Matazu (Ummu Beena)

                &

Anty na Jidda Musa (Mmn Twins).

UWA MABADA MAMA
Nagarta writers Association Allah yabar zumunci a tsakaninmu, ILVSM.
TUKUICI
Tukuici ne gare Ku Y’an uwana na jini, Allah yakara mana dank’on zumunci da taimakon junanmu har zuwa kan Y’ay’anmu.
KE TA DABAN CE
Zulaihat (Mmn Jafar) A duniya inason mutum mai karamci daya san karamci kuma yake bawa karamci muhimmanci, wanda baya raina kad’an yake godiya ga abu komai k’ank’antarshi, bakina bazai iya furta gurbinki a zuciyata ba, nagode nagode nagode, Allah ya d’orar da zumuncinmu ya sadamu da juna ra’ayul Ayn.

        “Abban Farha yau a ina za’ayi ma shimfid’a, bedroom ko filin gida?, saboda naga yau garin da d’an alamar sanyi ba kamar jiya ba”.
Ruwan da ke cikin cup ya d’an kur6a kad’an sannan ya kallota da gefen ido ya furta’ “kiyi shimfid’ar filin gida”. Har ta kai k’ofar fita waje d’in komai ya tuna ya bud’a baki yace’ “Zainab yi shimfid’ar a bedroom”.
Hakan ta koma bedroom d’inshi ta yi shimfid’ar ta fito gefenshi ta zauna, “ina fatar kin kunna A.c d’in?”.
“Aah”, ta bashi amsa a tak’aice.
Nan ya tashi ya shige bedroom d’in ya kunna A.c kana ya fito gurin suka cigaba da tad’i.
Hawaye take yi har ta kai ga shiga d’akinta, kwance ta yi rub da ciki tana kuka har da ajiyar zuciyarta, saboda tana jin zafin yanda Abban Farha ke nuna banbanci a tsakaninta da Zainab, ta rasa gano cewa me yasa duk ranar girkinta zai ce a fitar da shimfid’a daga waje, amma ranar girkin Zainab sai dai su shige bedroom d’inshi su kunna A.c suyi kwanciyarsu, bama wannan ba in ma ba Nepa koda yana cewa baida kud’i a hannunshi hakan bazai hanashi siyen mai da zai tada gen ba.
Sannan ga wani babban abinda ke ci mata tuwo a k’warya duk ranar girkinta ba zai ta6a lamunta cewa tayi wanka d’akinshi ba, sai dai yace taje nata d’akin tayi wanka sannan taje d’akinshi, amma tun ranar da ya auro Zainab sama da shekara biyu idonta basu ta6a hasko mata ita tayi wanka daga nata d’akin taje nashi ba. Dama a duniya yawanci ba kishiya suke gudu ba, bak’in halinta ko kuma sauyi daga Maigidan, ma’ana ya nuna banbancin a tsakaninku na zamantakewa, amma in ba wannan ba kishiya y’ar uwa ce.
(Anan zan so naja hankalin mata y’an uwana kan cewa Ku rage d’orawa kanku mugun zafin kishi akan kishiya, wallahi muddin Allah ya k’addarto ba zaki rayu da Mijinki ke kad’ai ba to duk dad’ewar da kika yi dashi wallahi sai ya yi auren, wani lokaci ma sai kin fara tsufa yara sun sakaki gaba sannan yaje yayi aure, kuma a lokacin ke yara zasu tauye a wasu abubuwan shi ba ruwanshi wallahi don jin kanshi yake tamkar wani sabon Ango, kinga ko hakan bai yi tasiri ba na hanashi auren da kika yi da wuri ba.
Magana ta gaba itace, cewa ni kishiya bata da rana gareni, ko hanyar da kishiya tabi bana so nabi wallahi lolx, masu irin way’annan maganganun na bani dariya sosai wallahi, shin kin manta cewa akwai ciwo akwai mutuwa ne Y’ar uwa?.
Ku k’iyasta da kanku kuga, lokuta da dama lalurar ciwo zata sakaki gaba wacce wallahi wani lokaci ko Maigidan bazai riga kishiya kawo agaji zuwa gareki ba, yau ko ciwo kike ta taimakeki da ak’alla ko ruwan sha ne to kinci cikin kishiya kuma ta yi maki rana, wani lokaci ciwo zai zo maki na ko wayar ba zaki iya d’agawa ki kira Maigida ko wani d’anuwanki ba, a wannan lokacin ke kanki ba zaki san yanda akayi kika k’walla mata kiran neman agaji ba, in kinyi tunani nan ma ta taimakeki.
Wasu suna amfani ne da cewa naga anyiwa wance kishiya ta wulakanta, ko Aah a gidanmu an yiwa Mamata kishiya ta wahala, ko K’awarki da sauransu wannan ba hujja bace kowa da yanda aka rubuto tashi k’addarar, abu d’aya nakeso kuyi amfani dashi addu’a da kuma tawakkali, addu’ar kuwa itace in har ina daga cikin mutanen da zasu zauna da kishiya Allah ka datarda ni data gari, kuma kar ka bani ikon zalunci akanta ko ka bata ikon ta zalunce ni, kuma ki zauna da ita da zuciya d’aya wallahi wallahi wallahi Allah bazai barta ta zalunceki ba, in ma tayi to kad’an ne kuma zai bi maki bashi, saboda haka don Allah mu rage zafin kishi da zai iya kaimu ga halaka.)
Tun tana tunani a ranta har bacci ya d’auketa wanda kiran Assalatu ne ya tada ita har tayi sallah ta koma bacci wanda ba ita ta tashi ba sai wuraren k’arfe goma inda taci karo da Zainab ta fito daga d’akin Abban Farha tana wani yatsina an shar6ar da gashi da ruwa ana gogewa da towel, saurin kautar da kanta tayi ta shige kitchen domin d’ora ko ruwan tea ne ta walwale hanjinta.

[4/14, 11:18 AM] Sady Jegal: CANJIN YANAYI

{2}

®NWA

DAGA ALK’ALAMIN Y’AR MUTAN JEGA

©SADY JEGAL

           Ganin cewa ta shiga kitchen (madafi) d’in ne ya saka Zainab ta biyo ta daga baya d’in’ “Maman Farha kiyi hak’uri sai yanzu na samu Abban Farha ya sakoni, gashi ko Breakfast (karin safe) ban samu na d’ora ba, sauk’in abin yau weekend (k’arshen sati) ne su Farha na gidan Hajiya”.
“Uhmm”, shi kawai ta samu furtawa ta koma d’akinta ta fasa dafa ruwan tea (shayi) d’in, saboda sanin doka ce daga Abban Farha ba za’a yi mashi girki biyu ba. Amma hak’ik’anin gaskiya ana shiga hakk’nta ita da yaranta, sai dai tunaninta d’aya duk abinda kayi hak’uri watarana zai zamo labari, kuma tasan ranar da duk Zainab ta haihu dole ta rik’a shiga kitchen cikin lokaci. Akan hakan ne yasa ko yaushe bata rabo da d’an lemu da cin-cin ko don yaranta.
*****
Yau kam ta saka ma ranta duk tsiyar Abban Farha sai ta yi wanka a toilet (bayi) d’inshi, saboda haka bayan ta gama girkinta ta yi wanka suka had’u suka ci abinci dukansu har yaran, suna gamawa tayi masu shimfid’a suka kwanta shi ko ya d’an fita Exercise (motsa jiki), sai wuraren 11:00pm sannan ya shigo gidan.
Da fara’arta ta taryeshi sannan ta shiga bayi ta had’a mashi ruwan wanka ya shiga ya fito, saman kujera ya ganta kwance sagale da towel d’inta alamar shi take jira ya fito ita ma ta shiga wankan saboda yanayi na zafi dake addabar mutane.
Murmushi ya sau mata kana ya kautar da kanshi gefe yana mai goge jikinshi, “wai ni Hafsat har sai yaushe ne zaki daina rigimar cewa sai kinyi wanka a bayina?”.
Maganarshi ce ta doki dodon kunnenta da tayi sanadiyyar dawowa a hayyacinta, fuskar ta k’ara had’ewa tamkar hadari ya had’o kayanshi daga gabas.
“Bansan me kake yimin 6oyo abayinka bane da baka so nagani, kuma ina ganin kullum ranar girkina sai nayi ma shara da wankin bayin, amma duk nace zan shiga wanka a cikinshi sai ka nuna min baka so, bayan can farko ba hakan bane saboda da kanka ka koyan hakan na buk’atar nayi wanka a bayinka wanda wani lokaci ma muke yi a tare”.
Tana kai k’arshen maganarta sai ga hawaye suna ambaliya daga fuskarta, wanda ke nuna alamar cewa abin ba k’aramin zafi yake mata a zuciya ba.
Towel (shawul) d’in ya sagale a k’ofa sannan ya tako gurinta ya zauna a gefenta, hannunta ya rik’o yana wasa da yatsunta had’e da kai masu kiss (Sumba), harara ta sau mashi sannan ta fisge hannun nata daga nashi ta mik’e sagale da shawul d’inta zata bar d’akin.
Saurin taryota yayi yana mai bata baki kamar kullum in har irin wannan rigimar ta taso a tsakaninsu, “haba Maman Farha ki daina damar da kanki kan wannan abin, ina so ne a fahimci cewa yanayi ya canja, kuma na gaya maki cewa lokaci zai wuce”.
“Ni fa in har kana so na fahimceka to ka gayamin me yasa lokacin sanyi ko lokacin yanayin ruwan sama baka hana min wanka a bayinka?”.
“Zan gaya maki amma ba yanzu ba, haba Hafsat ya kamata ki fahimce ni mana, ke kanki kinsan bazan ta6a sauya maki ba har abada, saboda kinsan cewa ke ta dabance har yau har gobe kuma har jibi…..”.
Saurin taryar numfashinshi tayi tana mai d’aga mashi hannu alamar bata ma son cigaba da sauraren kalamanshi, sannan ta furta’ “a da can farko na yarda da way’annan kalamai naka, amma a yanzu jinsu nake yi tamkar d’an koyo ya d’auki sarewa yana busa”.
Dariya yayi sosai har da had’awa da rik’e ciki kana ya furta’ “miye banbancin zamantakewata ta farko dake data yanzu?”.
Wani kallon jin haushi ta bishi dashi wanda ke nuna kalamanshi sun fara ginsar da ita. “Ai ina ga tamkar bayanin a bayyane yake ba sai na wahalarda kaina ba”.
“Amma k’aramin misali, a da can farko ina manne dakai a koyaushe, inyi yanda naso dakai, muyi hira a lokacinda muka so, bani da shamaki da kai, yanzu fa gayamin haka ne?”.
Hannunta ya rik’o ya zaunar da ita saman cinyarshi yana wasa da jelar gashin kanta. “Hafsat ina so ki fahimci cewa har yanzu way’annan abubuwan basu sauya a tsakanina dake ba, amma me yasa yawancin Mata kuke tunanin da miji ya auri wata Mace ya daina son ku?”.
Sai da ta rik’o gabanshi mai nuni da cewa taci kwalarshi ne sannan tace’ “close the chapter (a rufe zancen) in har ba so kake yau mak’ota su shigo k’watarka a hannuna ba, don haushin maganarka nake ji”.
Sai da ta kai k’arshen zancen sannan ta cire hannunta daga kwalarshi data rik’e ta dawo tana wasa da sajenshi daya kwanta lub dashi, cakul_kuli ya rik’a yi mata sai da ta kai k’asa tana dariya.
Tallabota yayi kana ya marairaice yana mai rok’onta data gaya mai CANJIN YANAYIN da take ganin can farko da yanzu ba d’aya bane.
“Ai ko kanada aiki Yalla6ai, sai ranar da ka gayamin dalilinka na korata daga bayinka wanka”.
Ido ya d’an zaro kana ya furta cewa’ “wannan sirrina ne bazai yuyu na sanarda ke ba”.
Cikin damuwa ta zare jikinta daga nashi ta shammaceshi ta fice daga d’akin domin yin wanka su fita waje su kwanta.

Muje zuwa.✍🏻

[4/14, 11:18 AM] Sady Jegal: CANJIN YANAYI

{3}

®NWA

DAGA ALK’ALAMIN Y’AR MUTAN JEGA

©SADY JEGAL

        Sai da tayi wanka daga ɗakinta ta kimtsa sannan ta dawo ɗakin nashi, da murnarshi ya taryota suka k’arasa gefen gadon. Ita kanta in tace ta samu CANJIN YANAYI ta wannan ɓangaren to bata yiwa Kabeer adalci ba, sai dai ita a tunaninta wace irin haɗama ce ke sanya maza tara mata dayawa, wata zuciyar ce ta tunatar da ita cewa faɗar Allah ne maɗaukakin sarki.
Tun tana tunanin har bacci yayi awon gaba da ita. Kiran asuba na farko ne ya tayarda ita inda ta zame jikinta daga jikin Kabeer ta fice daga part (ɓangaren) nashi, saboda wannan na daga cikin al’adarta sai dai bansani ba don yara take hakan ko ra’ayinta ne.
Bayan tayi wanka ne tayi sallah ta zauna lazimi wanda ba ita ta tashi ba sai da gari ya yi haske misalin 7:15 kana ta shiga kitchen (madafi) domin haɗa kalaci. Zuwa 9:00 ta kammala komai har tayi wanka ta kimtsa Farha, Suleiman da Azeema sun fito fes dasu sai k’amshi suke zubawa.
A falonshi ta shimfiɗa babbar dadduma sannan ta jera duka kayan, Farha ta kallo tana mai bata umurnin taje ta kira Zainab suci abinci ita ko ta shiga uwar ɗaka domin fito da maigidan.
Yana jin motsinta ya yi lamo tamkar mai bacci, bakin gadon taje ta zauna sannan ta had’a hannunshi da nata tana murza ɗayan hannun, saurin janyota ya yi ta faɗo saman jikinshi sai sissinarta yake yi ta ko’ina.
“Haba Abban Farha karka ɓatan kwalliya don Allah, kuma ka tashi abinci ya kammalu kai muke jira”.
“Kwalliyarki ko tawa, saboda wa dama ake yin kwalliyar?”.
“Tabbb na yima kwalliya sanda nayi yanzu kam ina yine kawai saboda sabo da hakan”.
Murmushi ya yi kana ya mik’o hannu ta kama ya tashi zaunen yace’ “Hafsat rigima, gaki kullum sai kyawo kike k’arawa tamkar wata sabuwar amarya”.
“Uhmmm wai daga baya kenan anyi sadaka da karuwa, ni dai muje karka fara zantukan naka da ba tasiri zasuyi ba”.
Hannu ya mik’a zai cafkota ta yi saurin fita daga ɗakin tana murmushi inda shima ya fito falon fuskarshi a sake cikin walwala da nishaɗi.
Cikin wani irin ɗaure fuska ta gayar da shi tana cin magani tana kimbure_kumbure tamkar mai ciwon hak’ori, amsawa ya yi yana mai ɗan ɗauke kanshi zuwa ga yaran yana gaisawa dasu da ɗai ɗaya sannan ya ɗauki Azeema yana mata wasa har yakai zaune ya ɗorata saman cinyarshi.
Mamaki ne kwance fal a fuskarshi haɗe da y’ar damuwa, ya rasa sanin har sai yaushe ne zata fahimci cewa akwai CANJIN YANAYI, har kullum sai ya yi yunk’urin yin magana sai yaga abin tamkar cin fuska ne, yafi so ta fahimci yanayi ya canja da kanta.
Hakan suka ci abinci cikin kwanciyar hankali har suka yi hamdala. Suleiman ya kalla yace’ “ya kamata yau muɗan fita yawon shan iska ko?”.
Farha ce ta karɓe da cewa’ “Abba shan ice cream dai”.
Dariya suka yi dukansu banda Zainab data ɗauke kanta tamkar bataji me suke faɗa ba.
Tsam ta tashi ta shiga ɗaki ta ɗauko babban gyalenta ta fito da k’aramar jaka a hannunta. “Abba kai kace Umma ta bimu can ashkilim?”.
“Kai Azeema ba dai kishi ba, to ni gidan Anty Sis (Mama Sultan) zaku sauke ni ba can ashkilim ba, ai bakin naki ne ashkilim”.
Nan dukansu suka dinga mata dariya ita ko ta wangale baki sai kuka sai da Abban ya lallasheta sannan ta nutsu.
Nan ya cewa Zainab “to mu zamu fita, ko akwai wani abin na buk’ata da za’a siyo maki?”.
Kai kawai ta girgiza sannan ta tashi fuu tayi ɗakinta. Hakan suka haɗa suka fice daga gidan aka sauke Hafsat gidan Anty Sis su ko suka wuce gurin tasu siyayyar shi da yaranshi.
Da sallama ta shiga gidan inda Anty Sis ta saki baki sannan ta taryota tana mai yi mata kirarin’ “uwargida sarautar mata, an buga an barki uwa gun Farha madubin Abban Farha, farar mace alkyabbar mata haska gida komai duhunshi”.
Dundu Hafsat ta kaiwa Anty Sis tana murmushi, “bansan lokacin da kika tashi daga Anty Sis kika koma marok’iya ba, wannan kirarin ai sai amarya Zainab don mu yanzu mun tsufa”.
Harara ta sau mata kana ta rik’a hannunta suka k’arasa falon ta kawo mata ruwa da lemo sannan Anty Sis tayi gyaran murya, “kinsan wani abu Maman Farha?”.
“Sai kin faɗa Maman Sultan”.
“A duniya ina bak’in cikin naji mace tace wai ta tsufa don an mata Amarya, ballantana ke da banga abinda amaryar zata fiki dashi ba, kina sane da irin so, tattali, kulawa da kike samu gun Kabeer ko amarya bazata same shi ba, kuma…..”.
Saurin tarar numfashinta ta yi tace’ “wannan ada can baya ne da nake ni kaɗai, yanzu kam way’annan abubuwa an rabasu kashi biyu an bawa amarya ɗaya”.
Hannu ta ɗaga zata make mata baki taja baya tana dariya, kana Maman Sultan ta ɗora da cewa’ “ya kamata kiyiwa Kabeer adalci don ni dai iya sanina banga CANJIN YANAYI a zaman takewarku ba, duk da yawancin mata suna ik’irarin cewa da wuya Namiji yayi aure baki ga canji ba, in har zakiyi la’akari yau shekararku ɗai_ɗai har shekara goma sha shida da aure, zuwan Zainab shekara biyu amma baki da wani laifi da zaki kama Kabeer dashi”.
“Ita kanta Zainab gwargwado kuna samun zaman lafiya tsakanin zamanta kewarku saboda bata da irin rainin nan da jin kan wasu amare”.
“A ganinki ba, tabbas bazan ce maki tana da raini ba, kuma gwargwado tana bani girmana, amma babbar matsalata da ita duk ranar girkinta sai naga CANJIN YANAYI daga gurinta tana wani iyayi a dole miji ya dawo hannunta, kuma sai kiga ranar nawa girki tana wani cin magani da wani ɗaukar kai irin tana nuna jin zafin kasancewarmu a tare dashi, har yaran sai kiga tana wani basar dasu”.
“Wannan na banza ne, in ma sanin daɗin Miji ne ai kin fita keda kika raineshi a hannunki tazo gidan ta hau naki rainon, ni fa kinga inda za’a samu matsala in Abban Sultan ya yi aure Amarya tace zata nuna min wannan iyayin ko jibgarta zan iya yi”.
Dariya sosai Hafsat ta dingi yi har da rik’e ciki, “to kinga nama fiki hak’uri anan don ni ko harara bata taɓa shiga tsakanina da ita ba sai dai na basar kawai”.
“Kai ke dai bari kawai kishi halitta ce da Allah ya jefo Mata dashi a duniya, amma wallahi sam kishiya bata da daɗi sai ka jure, kinma san me?”.
Kai Hafsat ta girgiza alamar a’ah, “zan so watarana ki tambayi Abban Farha mu kaiwa Anty Jidda ziyara kiji lakcar kishi da zama da kishiya kanta”.
“Ai kinsan ma ba zai hanani zuwa ba, saboda kaf cikin K’awayena yafi yarda dake, kinsan yanda akayi kika samu wannan matsayin?”.
“Sai kin faɗa”.
“Tun lokacin auren Zainab da kishi ya dinga saka ni k’aramar hauka, wanda a wannan lokacin ba wanda yayi nasarar kwantar min da hankali sai ke, to tun wannan lokacin yake baki babban matsayi wai kin ciri tuta”.
Nan suka yi dariya dukansu wanda yayi dai_dai da hon ɗin Abban Farha, nan suka tashi suka fice tare har suka gaisa da Kabeer ya bada ɗayan leda cewa a bawa Sultan su ko suka wuce Anty Sis ta shige gidan.

Muje zuwa.✍🏻

[4/14, 11:18 AM] Sady Jegal: CANJIN YANAYI

{4}

®NWA

DAGA ALK’ALAMIN Y’AR MUTAN JEGA

©SADY JEGAL

Kwanaki sun ja ba wani CANJIN YANAYI daga zamantakewar gidan, yanda aka saba tafiya hakan ne har yanzu, sai dai ni kaina na rasa gano wane irin yanayi ne yake so agano ya canja, inda nayi bibiya ko zai furta abin in kwashe amma abin ya faskara.
******
Kamar yanda suka yi alk’awari tsakanin Anty Sis da Hafsat kan cewa zasu kaiwa Anty Jidda ziyara hakan ta kama yau suke ta shirye_shirye inda suka kira Anty Jidda suka jaddada mata cewa zasu kawo mata ziyara.
Da Abban Farha aka shiryar da tafiyar saboda shi zai kai su, sai da ya sauke su Farha gidan Hajiyarshi sannan suka ɗauki hanyar Kano daga katsina har suka kai Kano taɗin kishiya suke yi wanda yake saurarensu yana murmushi k’asa_k’asa.
Da murna Anty Jidda ta taryesu tamkar ta haɗiyesu, Anty Jidda ba dai iya tarbon bak’i ba, sai da ta cika masu gabansu taf da kayan tanɗe_tanɗe da lashe_lashe har zuwa kayan abinci, bayan sunci sun k’oshi ne sunyi hamdala sannan suka lula hirar duniya.
Anty Sis ce ta kai dubanta zuwa ga Anty Jidda kana tace’ “Anty na rako k’awata ne domin ta ganki kuma ki bata lakca akan zaman kishi da kuma kishiya kanta”.
Murmushi Anty Jidda tayi tana mai furta’ “kai Anty Sis ni fa ba Malama bace da kika ɗoran wannan nauyi, sai dai kuma mu’amala da mutane yau da gobe yasa mun ɗauki wasu darussa. Amma ke Maman Farha me yasa kike so a taɓo wannan topic (maudu’i) ne?”.
“Ba komai Anty, inaso ne dai nak’ara ilmin yanda zan zauna da tawa abokiyar zama ne cikin aminci babu cuta ko cutarwar”.
“Alhamdulillah Maman Farha, da za’a samu mata ashirin tamkarki da abubuwa sun rage da dama”.
“Da farko dai inaso musan cewa shi kishi halitta ce, kuma kowane ɗan Adam an halittashi da wannan kishin, sai dai na wani yafi na wani ta yanayin hak’urinshi ko kauda kanshi”.
“Wani haɗuwa ta farko dashi zaki iya fahimtar kalar nashi kishi, zaki ga wani duk tsabar kishinshi yana k’ok’arin dannewa, wani kuma nan take zaki fahimci yana kishi kan abu”.
“Akwai kishi na hankali akwai na rashin hankali”.
“Zamu fara da kishi na hankali irin wanda addini ya yarda dashi. Abu na farko shine, in har Allah ya haɗaki da abokiyar zama to ki fara kwantar da hankalinki har ki gama fahimtar wacece ita da kuma halayyarta sai uwa uba yanayin zamantakewarta da Mijin”.
“A wannan ɓangaren in har kin gama fahimtarta to ki bi tako zaman da ita, duk abinda ta yiwa Mijin na kyautatawa to ki ninka irinshi ta hakan zaki samu babban matsayi a gurin maigidan”.
“Kishi na rashin hankali kuwa shine wanda zaki ga Mata da ance za’a yi masu kishiya kiga suna hauka da zage_zage da cin zarafin Mijin wanda har zai kai baya da sauran mutunci a idonta, a tunaninta hakan zai sa ya fasa auren, wannan kuwa ba shine mafita ba saboda shure_shure baya hana mutuwa duk haukanki ba zai saka ya fasa auren ba, a wannan lokacin ma zai k’ara samun k’warin gwuiwar auro wata saboda yana hango kwanciyar hankali gurin Amaryar”.
“Kuma muddin kika yi sake Amarya ta samu labarin kalar haukarda kika yi da za’a aurota to har abada girmanki zai faɗi a idonta kuma raini zai shiga tsakaninku wanda lokacin da kika so ku fahimci juna hakan ba zata yuyuba saboda an baro kyawo tun ranar haihuwa”.
“A lokacinda duk Amarya ta shigo gidan to uwargida itace tubalin zaman lafiya, saboda a nawa tunanin duk kalar masifa ko wani ji da kai da Amarya ta shigo dashi muddin uwargida na kauda kanta to Amarya zata yi ta gama ne cikin k’ank’anin lokaci saboda ance k’arfe ɗaya baya amo”.
“Amma da wuya asamu uwargida masifaffiya duk kauda kan Amarya gida bai tarwatse ba, saboda tun tana kauda kai zata biyewa Uwargidan ne saboda rashin jan girmanta”.
Gwauron numfashi dukansu suka sauke alamar sun gamsu da zancen nata, sannan Anty Sis ta jefo mata tambaya kamar haka’ “to Anty me yasa naji mutane da dama na furta cewa in gida ya gyaru Maigida ne kuma in ya ɓaci shi ne?”.
Murmushi Anty Jidda ta yi kana ta kurɓi lemun da ke gabansu ajiye ta ɗora da cewa’ “in kinga hakan an samu munafukin Miji ne”.
Maman Farha ce ta yi saurin karɓewa da cewa’ “Anty kamar ya munafukin Miji?”.
“Eh munafuki kam, shine mai ɗaukar hirar Amarya ya kaima uwargida ko mai ɗaukar ta Uwargidan ya kaima Amarya”.
Ido suka gwalo dukansu tamkar k’wank’walati (marfin mirinda).
“Eh mana kuna mamaki ne da kasantuwar hakan?. To bara kuji akwai Namijin da ke ɓata gidanshi da kanshi, saboda kaiwa ɗaya gulmar ɗaya, kuma hakan na tasiri ne da yanda zai samu mai ɗaukar maganar, da idona naga Matan da ke turkar Mijinsu in yaje ya cewa ɗayar wance tace maki abu kaza, tun suna ɗauka har suka fahimci shi ke haɗa husuma tsakaninsu suka fara turkarshi sannan aka zauna lafiya”.
“Kai Anty amma tir da halayya irin ta waɗannan Mazajen kuma ya rabamu da zamantakewa da irinsu”.
Nan Anty Jidda ta amsa da Ameen.
Kusan a tare suka jefo mata tambayar har suna haɗa baki’ “Anty to meke kawo CANJIN YANAYI in har mutum ya k’aro aure?”.
“Wannan yana faruwa ne saboda zank’in Amaryar kuma tana saman kanshi, in har Uwargida ta ɗauke kanta na kwana biyu zata ga cewa Amaryar ma bata taka matsayinta ba, ku auna da kanku kuga yanda in kuna da sabuwar sutura kuke matsuwa baku sanyata ba, kuma in kuka saka ta ɗin zaku jiku wasu daban tamkar kuna saman iska, to ku auna hakan da Miji ya yi sabon aure, kamar yanda suturar nan zata zo ta zama tsohuwa to haka Amaryar zata koma nan gaba kaɗan, kuma har kizo cikin tsofaffin kayanki ki samu wacce kika fi so akan sabuwar nan da kika yi so”.
“Wani CANJIN YANAYIN kuma in kika duba da kanki zaki fahimci yana da asali, wala allah daga uwargidan ne kp kuma Maigidan na da hujjar yin hakan, a koyaushe dai anaso mutum ya kasance mai kyautata zato da kuma kauda kai kan waɗannan abubuwan kuma ya dage da addu’a da tawadu’u a zuciyarshi, in har ya kasance mai kusanci da ubangiji to bashi ba matsalar rayuwa sai dai jarabta ta ibangiji da yake auna k’arfin imanin bayinshi”.
Su dukansu shuru suka yi suna dogon nazari a ransu, nan Anty Sis ta fitar da waya tana kira kan ta shiga Maman Farha ta karɓe tana mai hararta tace’ “wai me kike shirin yi ne?”.
“Ni fa Daddyn Sultan naso na kira”.
“Akan me zaki kira shi bayan kinsan Abban Farhan na jiranmu gidan abokinshi da mun gama zai zo mu wuce?”.
“Ni fa so nake na gaya mai ya fara neman mata daga yau, saboda na fahimci sai ma kanada ita zaka k’ara tantance matsayinka gurin Maigidan”.
Ba Hafsat ba Anty Jidda kanta sai da ta yi dariya sosai sannan ta furta’ “ki barshi hakan in lokaci yayi kina zaune zai zo maki da batun, kinsan shi aure da haihuwa lokaci ne dasu”.
“Allah Anty yanzu na daina jin tsoron kishiya akan wannan bayanin na ki, ko yau zata shigo bana fargaba da hakan”.
“Dace da ta gari shine fatanmu a koyaushe, don haka kiyi ta addu’a”.
Nan suka k’ara tattaunawa kana suka kira Abban Farha yazo suka wuce kowannensu fuska a sake cikin walwala da nishaɗi, tare da ɗinbin tsarabarsu daga Anty Jidda (Allah yasa Anty Sis kar ki manta dani gurin rabo, _lolx_).

Muje zuwa.✍🏻

[4/14, 11:18 AM] Sady Jegal: CANJIN YANAYI

{5}

®NWA

DAGA ALK’ALAMIN Y’AR MUTAN JEGA

©SADY JEGAL

         Haka kawai yau taji tana son shiga gidan mak’ociyarta kuma k’awarta Bahijja (Bebeelo) nan ta figi gyalenta ta faɗa gidan da sallamarta.
Sororo tayi tana kallonta, “kai Zainab daga ina kike hakan kika baro mijinki cikin daren nan kika zo shiga hakk’in nawa Miji?, kuma fa kinsan cewa wannan lokacin bani bawa kowa shi sai Baban Iman”.
“Haba abin har da kora K’awata, naga fa kinci kwalliya kin gama aikinki yanzu da Maigidan ya dawo akaci abinci sai hira da kwanciya, ko fita za kuyi ne naga kinci kwalliya hakan?”.
“Ni kikasan cewa ina fita bayan magrib?, ai duk yawo na to da rana ne Baban Iman yana office, kan ya dawo niko na dawo daga unguwa nayi girki na gama”.
Suna cikin hakan ne suka ji hon na dawowar Baban Iman, Bahijja ce ta rik’a hannun Zainab tace ko ki tashi kiyi gidanki ko ki koma part (ɓangare na) ki zauna har in gama taryon maigidana”.
Fuska ta haɗe kana tace’ “wallahi bazan shiga gidan ba yanzu, waccan sarkin iyayin na can tana shirin tarairayar miji, bazan zauna bak’in ciki ya nemi salwantarda ni ba wallahi”.
Wani mugun kallo ta bita dashi tana mai girgiza kai kana ta turata ɓangarenta sannan ta fita ta taryo Baban Iman inda suka haɗu a falon. Da saurinta ta k’araso zata rungumeshi ya juya ya bata baya, gabanshi ta koma ta durk’usa tana mai rik’e da kunnenta alamar ban hak’uri, murmushi yayi yana mai rik’o hannunta ta mik’e tsaye.
“Me yasa kina jin horn ɗina yau bakije get kika taryoni ba?”.
“Sorry Baban Iman wallahi Zainab ce tazo shiyasa, inata sauri sai gashi har ka shigo falon”.
Tana kai k’arshen magana ta rik’a hannunshi suka yi ɓangarenshi, sai da ta haɗa mashi ruwan wankan ya shiga sannan ta zuzzuba abincin saboda yaɗan huce akan Baban Iman ba gwanin cin abinci mai zafi sosai bane.
Da fitowarshi ta ɗauki shawul tana mai taya shi tsane jikinshi, sannan ta bashi kayanshi marasa nauyi ya saka suka zauna suna cin abincin.
“Bak’uwarki ta wuce kenan?”.
“La haula kaga wallahi na manta da ita”.
Ido yaɗan zaro yace’ “je ku gama da ita, kar taga kin mata wulak’anci, ɗaukomin Iman ta tayani hira kan ku gama”.
“Iman ta gama rigima fa ta yi bacci”.
Laptop ɗinshi ya janyo yace’ “to kije na baki minti 30 zuwa lokacin nasan na k’arasa wani aiki”.
Sumba ta kai mashi tana godiya kana ta fice zuwa ɓangarenta. Zaune ta tarar da Zainab tana ƙlatsar waya tana sakin hamma. “Ga alama dai kishi ko abincin bai barki kika tsaya ci ba ko?”.
“Wallahi kamar kin sani, ke fa da mun zauna cin abinci zaki ga tana wani iyayi ita a dole ga mai Miji, don haka ni gaskiya ma na soke wannan zaman cin abinci tare, ranar girkinta su haɗu da yaransu ni ko ranar nawa girki abarni da Mijina”.
Abinci ta tashi ta sako mata sannan ta nemi guri gefenta ta zauna, “wai ni zainab na tambayeki, har yaushe kika san daɗin Mijin da kike kishi da Uwargidanki hakan?”.
Sai da ta saka lomar abinci a bakinta tace’ “wallahi baki ga shi kanshi rawar kan da yake akanta ba, dole ko kece kiji zafi”.
Murmushi tayi sannan tace’ “irinku ne masu fatan in sun shigo a gida Uwargida ta zamo abar tausayi a dinga nuna rawar kai a kanku ku gaku amare ko?”.
“To wallahi tun wuri ki canja wannan bak’ar ak’idar taki, yanzu ki k’iyasta akanki ace kece uwargidar aka yiwa kishiya miji ya sauya maki zaki ji daɗi?”.
Kai ta girgiza sannan tace’ “to amma sunyi nasu lokaci ya kamata yanzu abarni naci nawa”.
“Ok inna fahimce ki so kike taja gefe ta bar maki miji hannunki ita tace duk ta tsufa da kula da mijinta, kuma ta gaji da bautar ubangiji ke kije ki kwashe ladar?”.
“Ni fa bance ba”.
“To miye nufinki akai mai son miji?”.
“Kawai dai ta rage saboda kinga yanzu nice Amaryar kuma….”.
Saurin taryar numfashinta tayi sannan tace’ “wannan duk zancen banzane kike yi baki da makama ko rabi ballantana ɗaya, ni kinganni nan ko jikanyata aka yiwa aure k’arewar tsufa indai ina numfashi a doron k’asa bazan k’i bawa Mijina kulawa ba”.
“Wannan bak’ar ak’idar taki irinta ce ke tsorata uwargida muddin yace zai yi aure, bawai kishiyarce basa so ba a’ah bak’ar ak’idar da zata zo masu da ita ne basa so, saboda wasu da kaga yanda kansu ke rawa kasan da biyu suka shigo gidan, ko su fitar da kishiyar ko ta zamo shara a gidan”.
“Amma in har amarya tazo da niyyar alk’hairi to zaki ga zama yayi daɗi ana mutunta juna, saɓoda ba wanda ya shiga sabgar wani, kowa k’ok’arinshi ya kyautatawa Mijin dai_dai k’ima yanda zai samu gurbi a zuciyar maigidan, wannan shine kishi na asali, saboda haka don Allah ki ɗauke idonki akanta da yaranta, ki daina kula dame take yi har abin na damunki”.
“Abinda nake so ki kula dashi anan shine, misali ace in kuka zauna cin abinci ita Maman Farha saka mai abincin take yi yaci da kanshi, to ke sai ki kwatanta bashi a baki, in ruwa wanka take kai mashi ta fito to ke ki dinga taya shi da sauransu, ta hakan kishin y’an zamani da suka san kansu suke yi ba irin yanda kike yi ba, saboda haka don Allah ki gyara wannan halin naki”.
Shiru tayi alamar duk wani zance nata na shigarta da kyau, “insha Allah zan gyara, kuma nagode sosai da shawara Allah yabar zumunci”.
“Ba komai zaman tare ne, in kin ɗauka ta hakan ma zan samu nawa kason lada, don haka tashi kiyi gidanki ni zan shiga wanka inje mu kwanta ni da oga”.
“Wanka fa Bebeelo, yanzu fa na shiga na ganki da kwalliyarki kuma har wani wankan zakiyi? Bakya tsoron murar zafi ne gata da shegen kamu?”.
“Kina nufin yanzu hakan sai naje na rungumi Mijin hakan ina bashi_bashin zufa?, ai koke kika ga zan aikata hakan kya yimin faɗa Zainab”.
Zurum ta yi na y’an dak’ik’ik’i ta shiga dogon nazari akai. Bebeelo ce ta taɓota tace’ “Zainab lafiya?, ni fa kinga a cikin lokacinda Baban Iman ya bani saura minti bakwai, kuma wallahi yana cika zan ware na barki ne in kin fita kija min k’ofa”, ta k’arasa maganar tana murmushi.
“Maganarki ce ta sakani shiga wani nazari yanzun nan, saboda ni dai wallahi a yini wanka ɗaya nake yi kuma shine har dare in zamu kwanciya”.
“Suɓhanalillah!, Zainab kanki ɗaya kuwa, wane irin wanka ɗaya kina matar aure kuma a cikin CANJIN YANAYIN nan na zafi ace kina wanka ɗaya kije ki rungumi miji a hakan, wallahi ko Abban Farha ya zama ɗan halak daya juri zama dake shekara biyu a hakan”.
“To bara kiji wallahi ko ni da nake mace zamanin ina makaranta bana iya jurar zama kusa da k’azamai musamman lokacin, ashe ke felek’e ne kawai kike yi bakisan ma kan zama da Miji ba har kike kishin uwargidanshi”.
“Ba mamaki kwanaki kika zomin nan da wani banzar k’orafi naki wai Mijnku bai damu da kiss da romance ba, tun kina nuna mishi ra’ayinki kika ga baya yi kika hak’ura, a hakan zai iy haɗa baki dake tun brush ɗin safe har lokacin kwanciya, haba Zainab ina ilminki yake, ina wayewarki ina iyayenki da y’anuwanki abokanai na k’urciya da basu zamo makaranta a gareki ba?”.
Idon Zainab ne ya ciko da k’walla ta fara raina kanta da muzanta a idon Bebeelo.
“Ki saki ranki muyi magana ta fahimta saboda bama ɓoyewa juna abu na k’aruwa a tsakaninmu. Ki k’iyasta ke da kanki kiga in har kikayi wankan jikinki zakiji iska na shigarki ta ko ina kuma zakiji jikinki ya cire bashi musamman lokacin zafi”.

Muje zuwa.✍🏻

[4/14, 11:18 AM] Sady Jegal: CANJIN YANAYI

{6}

®NWA

DAGA ALK’ALAMIN Y’AR MUTAN JEGA

©SADY JEGAL

          “Wannan ɓangaren wani lokaci wasu iyaye ke cutar yaransu da kansu wallahi, saboda uwa itace makarantar yaranta, abinda suka ga kina yi shi zasu ɗauka, ko kuma ki koyar dasu duk daren Allah suyi wanka kamin su kwanta bacci, in har suka saba da hakan to zaki ga ko basa yi a koyaushe zakiga sunyi saboda CANJIN YANAYI na zafi domin suji daɗin kwanciya su kansu, amma ke uwa kinzo kin dunk’ula kin kwanta da k’arnin hayak’i ga zufa me zai hana yaranki bazasu ɗauki ak’idarki ba”.
“Wata uwa ma yaran na son suyi wankan zata rik’a hanasu da cewa wallahi ku raba kanku da muguwar murar zafin nan bata wasa da kama mutum, daga hakan sai kiga yaro ya ɗauka ya zauna akai”.
“Tabbas hakane”, faɗar Zainab, kana ta ɗora da cewa’ “kinganni nan Anty na tayi silar hakan a gareni, saboda iyayenmu sun rasu tun muna yara a hannunta na tashi, wallahi bata wanka hakan take kwanciyarta ina gidan yayi aure suka dinga gwabzawa da kishiyar har Mijin ya ɗauke amaryar yaje garin da yake aiki da ita, ko wannan kishin da kike gani itace ke k’ara zugani akai wai in nayi sake dai naga yanda aka yi mata”.
“Ai ko dukanku kunyi sake wallahi, don hanyarda kuka hau ba mai ɓullewa bace, sai dai sauk’in abin ke kina da sauran dama ta gyara kuskurenda kika tafka don haka ki kula ki natsu kigane tsabta itace mataki na farko a zamantakewa ta aure, in har baki da tsabta wallahi duk wani felek’enki na banza ne, kuma za’a yi babu ke”.
“Yanzu abinda nake so ki rik’e shine ki kula da wankan jikinki ak’alla sau uku a wuni musamman lokacin zafi, kuma kowanne wankan ki haɗa shi da brush ke kanki zakiji sauyi ba mijin ba kaɗai”.
Hakan dai ta yita ɗorata a hanya har ta fahimci komai wanda yasa take k’ara jin Bebeelo har cikin ranta, da hakan ta rakata ta wuce gida wurin k’arfe 9:00pm.
*****
Samui-samui ta shiga gidan tana sanɗa har ta faɗa ɗakinta, wanda bata son kowa ya ganta daga Mijin har kishiyar tata, sai yanzu take nadamar felek’enda tayi ta yiwa Maman Farha da iyayi, ashe duk na banza ne don ta fita matsayi gun Mijin, abinda yakamata ace tayi ta kula dashi ba shine gabanta ba sai ɗan banzan kishi da Anty Aisha take aon ɗorata akai.
A yanzu ne ya kamata ta fahimci biyu babu ne Antyn takeson ayi, yanda ta kasa gane gidan aurenta itama ta ɓata mata nata, don haka yanzu ta k’uɗurtama ranta zama da Maman Farha da zuciya ɗaya ita da yaranta, sai kuma uwa uba Maigidan da kanshi da zata zage damtse wurin kula da kanta kyautatawa da sauransu.
****
Washe gari da yamma ta gama girkinta taje ta tsala wanka da kwalliya taji ta gani sai k’amshi take zabgawa. Falon nashi tayi zaune tana jiran shigowarshi, bayan ya shigo ne ta tashi ta taryoshi da murnarta da fara’a kwance a fuskarta, sai dai kan datake nok’ewa alamar jin kunya.
Kallon mamaki yaa bita dashi inda ta tayashi cire kayan jikinshi yana biye da ita tamkar rak’umi da akala har ya shiga bayi wanka, tunani ne fal ranshi har yayi wankan ya fito ya saka jallabiyarshi.
Fita tayi ɗakin Maman Farha ta kirata, sannan ta rungumo Azeema saman kafaɗarta tana yi mata wasa har suka zo falon, ita ta sakawa kowa abinci sannan ta ɗora Azeema saman cinyarta in taci cokali ɗaya ta saka mata itama a baki.
Ta wutsiyar ido ya dinga kallon Hafsat yaga wane yanayi take ciki, inda suka haɗa ido kowannensu yayi murmushi mai nuna alamar jin daɗin CANJIN YANAYIN da aka samu sannan suka ɗauke kansu, saboda yau ba wani felek’e ko iyayi daga Zainab, kowannensu yana mamakin hakan har suka k’are cin abincin inda Azeema tayi bacci saman jikinta.
Hafsat ce ta mik’o hannu zata karɓeta Zainab ta mik’e tace’ “muje ɗakin na shimfiɗe maki ita”. Hakan ta wuce Hafsat ta bita a baya tana rik’e da hannun su Farha suka wuce ɗakin nata.
Sai 11:00pm taga ya gama ayukkanshi na office ya yi shirin bacci, hakan yasa yana shiga wanka itama taje ɗakinta ta darje jikinta da kyau. Wurin brush ne ni kaina na dinga yi mata dariya, saboda inaga ta saka makilin yafi sau uku tana wanke bakin sannan ta kammala ta fito ta kimtsa ta wuce ɗakinshi.
Yau waje yace suyi shimfiɗa saɓanin kullum da suke shigewa uwar ɗaka a kunna A.C, bayan sun kwanta ne ta shige cikin jikinshi ne ta kira sunanshi yana amsawa ta fara da cewa’
“Yanzu Kabeer a tunaninka wannan abin da kayimin haka zamantakewa tace?, a tunanina kaine mutum na farko da zai fara hango kuskurena yace min Zainab abu kaza da kikayi bai dace ba ki gyara kiyi kaza kiyi kaza, amma ka zubamin ido inata felek’e akai ashe aikin banzane ga inda ya kamata nayi gyara nan domin shine tubalin zama”.
“Kiyi hak’uri Zainab a kullum inaso nayi maki magana sai inga abin tamkar cin fuskane ko cin zarafi, shiyasa nayita aikata wasu abubuwan ko zaki fahimci CANJIN YANAYI ki gyar amma kuma sai abin ya faskara, amma wallahi ina gab da zaunarda ke mu fahimci juna in gaya maki abinda ke raina, sai gashi kin hango kin gyara da kanki, kuma gaskiya naji daɗin kasancewar hakan”.
“Aka dai lurar dani”.
“Bangane aka dai lurar da ke ba”.
“Eh to tunda kai da hakkin yake saman kanka ka kasa to ansamu wacce ta lular dani kuma naji daɗi da hakan sosai wallahi”.
Lallashinta ya dingayi sannan ta gaya mai yanda sukayi da Bebeelo bata ɓoye mashi komai ba, ba k’aramin daɗi yaji ba har yana halayyar wannan matar saboda ba k’aramar lada ta samu ba da yin hakan, nan dai suka tattauna ya k’ara bata hak’uri kan laifinshi data gani na rashin gaya mata kuskurenta. Ni dai Jegal can na hango bakinsu a haɗe nayi saurin fitowa na ja masu k’ofa saboda kar su cinye halshen juna a gaban idona, _lolx_ Asuba tagari.
****
Washe gari ma hakan suka ga CANJIN YANAYI sosai, don kayan baccin da har ta haɗa kalaci suna saye a jikinta yau babu su sai dai wankan da tayi ta saka kayanta marar nauyi suka zauna kalaci kowa na zabga k’amshi.
****
Bayan ya fito wanka ne ya matsawa Hafsat kan cewa ta shiga bayinshi tayi wanka inda itako tayi tsaye kan cewa ba zata shiga ba har sai ya gaya mata me yagama ɓoyo a bayin tukuna.
Zaunar da ita yayi yana gaya mata CANJIN YANAYIN da ya samu daga Zainab, ya ɗora da cewa’ “ba da wata manufa na hanaki wanka a bayina ba, nayi hakan ne ko Zainab zata fahimci cewa sai kinyi wanka kike shigowa ɗakina itama ta dinga yin hakan”.
“Shimfiɗa da kike mana a waje ranar girkinta kuma mu kwana ɗaki shine….”.
Saurin tarar numfashinshi tayi da cewa’ “wannan sirrinka ne tsakaninka da matarka bai dace ka gayamin ba, yanzu dai na fahimci dalilinka na hanamin shiga bayinka”.
Tsam ta tashi ta faɗa bayin domin yin wanka. Tunani yake aranshi da za’a samu mata masu halayyar Hafsat da zama ya wuce inda ake tsammaninshi, shi dai har gurin ubangiji ba ɗabi’arshi bace ta kaiwa ɗaya maganar ɗaya ba, ko yanzu yayi hakan ne saboda fita zargin Hafsat na yana hanata wanka bayinshi yana bari Zainab nayi, saboda ko kwanciyarsu ɗaki da Zainab dole ce saboda sanyin A.C zai rage mashi jin bashin jikinta ne.
Tun daga wannan lokacin zaman lafiya ya ɗore tsakanin Zainab da Hafsat, ba wai basa kishin junansu bane a’ah sunayi sai dai cikin hikima da hankali tunda Zainab ta fahimci CANJIN YANAYI tsakanin zafi da sanyi da damana na kula da jikinta.
TAMMAT BI HAMDILLAH
Anan na kawo k’arshen wannan gajeren labari nawa, kuskurenda ke ciki Allah ya yafemin, ku kuma ya baku ikon ɗaukar darasin da ke ciki.
MASOYANA
Na gaisheku a duk inda kuke, ina k’aunarku! Ina k’aunarku!! Ina k’aunarku!!!.

SANNU SANNU MMN JAFAR 1-END

LAHADI

[9/04, 6:00 p.m.]

 SANNU SANNU…

      

            1
Daga alkalamin

Maman Ja’afar

“Zulai! Zulai! Can na jiyo muryar Gaji nata faman kirana d’aya daga cikin kishin balbalina kenan yayinda suke tunkaro k’ofata ita da amaryarta wato Maryam
“Kema kinsan ba son wannan sunan takeyi ba yanzu hakama tana jinki tayi shuru ta k’yaleki, bara kiji na kirata da sunanda takeso kiji idan bata amsa ba
Ina jinsu daga cikin d’akina nayi kamar bana jinsu
“Zulaihat! Maryam ta ambaci suna mafi soyuwa acikin raina, wacce ta kasance amarya ga Gajin yayinda sukazo dab da k’ofar d’akin nawa
Murmushi nayi kana na amsa mata cikin fara’a kamar yanda na saba
“Au ashe dama kina jina kikayi banza dani ko?” Cewar Gaji kenan
“To ba dole nayi banza dake ba, kyace mani wai wani Zulai sai kace wata miyar da babu gishiri a ciki”
Dariya mukayi muduka, kana daga bisani suka k’araso cikin d’akin nawa suka zazzauna.
“Yauwa Zulaihat labarin littafin nanfa mukazo ki k’arasa mana wanda kika fara mana, tun rannan da kika fara bamu labarin a k’ofarmu kika gudu baki k’ara dawowa ba har yanzu, to yanzu dai gashi mun biyoki har k’ofarki sai ki k’arasa mana muji yanda za’a k’are soyayya tsakanin mutum da kuma aljani” Cewar Gaji uwar gida kenan
Tashi nayi daga kwancen da nake akan katifata kana na gyara zama
“Ni ba wai zuwa k’ofarku ne matsalata ba a’a naje naita baku labarai ina 6a66aka dariyata kuce da wata daga cikinku nake bayan kun riga kunsan ni dama bakina kamar gonar auduga yake ba rufuwa yakeyi ba, ko kuma labarina yayi kama da halin wata daga cikinku kuce habaici nakeyi maku, shiyasa nace bazan k’ara zuwa k’ofar taku ba, mai son labarin yazo ya sameni inda nake, idan kuma labarin ya ciyoni da kaina zanje k’ofar Hajiya(Sirikarmu kenan) na zazzage masu ita da autarta Aisha”
Da k’yar dai suka shawo kaina naci gaba da basu labarinda na fara basu wato Aljani ya taka wuta na Nazir Adam Salihi.
Munyi nisa acikin labarin namu munata k’yak’yata dariya muka jiyo muryar Baba(Wato Sirikinmu kenan)
“Zulai! Zulai! Zulaihatu!
Dariya sukayi su duka kana Maryam ta dubeni

“Ga Baba can yana kiranki da Zulai sai kije shima ki gyara mashi sunan”
Ban tsaya ida saurarenta ba na zari hijabina nayi gaba abina wajen kiran Baba
“Yauwa Zulai wani nono ne mai kyau naga ana siyarwa shine nace Y’ata kuwa na son nono sare, to gashi na siyo maki k’warya guda ke kad’ai, k’ar6i abinki kije ki juye” Ya fad’a tare da mik’o mani k’waryar nonon
Cikin ladabi na durk’usa na kar6a tare dayin godiya, na kamo hanya na dawo ina mai jinjinawa wannan irin karamci da mutanen gidan nan suke nuna mani, musamman ma Baban
Bayan na kawo masa k’waryar ne ya zura hannunshi a aljihu ya zaro nera d’ari
“Ungo wannan anjima ko balango kya siya ko tsire dan naji mutanen gidan nan na cewa tuwon biski zasuyi ke kuma nasan ba iya cinsa kikayi ba”
Kar6a nayi cikin ladabi kamar dai d’azu, nayi godiya kana na dawo k’ofata
Da gudu Gaji da Maryam suka nufi inda Baban yake domin dama suna jiyo abinda muke tattaunawa
“Baba mu ina namu nonon?” Cewar Maryam kenan
“Baba muko hamsin hamsin ce  dan Allah muma ka bamu”Gaji ce mai fad’ar haka
Dariya Dattijon yayi kana ya juya abinsa, yana tafiya ne yake basu amsa da cewa
“Zulai itace batada miji a gidan nan shiyasa kukaga inayi mata dukkan abinda nakeyi mata, kuma kuje wajen mijinku ya baku babu ruwana”
Gwalo nayi masu kana na ruga cikin d’akina dan nasan idan suka rutsani sai nasha mintsini.
*******
*Bayan wani lokaci*
Kowa ka gani a gidan yana gefe guda yana sharar hawaye domin jimamin rabuwa dani da zasuyi, saboda jiya-jiyan nan Bisata ta fito, kuma jibi muke sa ran jirginmu zai tashi zuwa Saudiya inda mijina yake da zama kenan, shiyasa yau d’in nan dole zan bar Fotiskum domin kwana a Kano.
D’akin Hajiya(Sirikarmu)na fara zuwa domin neman yafiya da kuma saka albarka
Ta dad’e tana yi mun nasiha, wanda kamin ta gama nasihar dagani har ita hawaye sun dad’e suna malala a fuskokinmu saboda tsananin sabo da mukayi da kuma jin dad’in zama da juna.
Daga k’ofarta ban zame ako ina ba sai k’ofar d’akin Baba.
“Allah sarki Zulai, lokacin rabuwa kuma dad’a yayi?”
Murmushi nayi tare da k’ara duk’ar da kaina kasa, yayinda hawaye bai daina safa da marwa akan fuskata ba
“To ni dai banida abinda zan baki face nasiha, kibi mijinki sau da k’afa dan Allah, yi nayi bari na bari, karki yarda mahassada magulmata su shiga tsakaninku dashi, kinga dai garin nan da zaki tafi baki da kowa shine kowanki, saboda haka ku had’u ku rufawa kanku asiri, a jure kinji? duk wuya duk dad’i wata rana sai labari”
Qur’ani ya d’auko daga cikin inda yake ajie-ajiyen kayansa masu mahimmanci ya mik’o mani
“Ga wannan nasan duk sadda kika d’aukosa zaki karanta sai kin tuna dani, saboda haka idan kika tuna dani kiyi mani add’a kinji Y’ata? Tashi ki tafi Allah yayi maku albarka Allah ya bada zaman lafiya
Kar6ar Qur’anin nayi hawaye na zuba a fuskata nace “Nagode nagode Baba insha Allahu zan kiyaye”
Jakata na d’auko na mik’a masa wacce na tattara dukkan wasu tarkace nawa a ciki masu mahimmanci,  kama daga littatafan addini zuwa na hausa, da sauran abubuwan dai tarihi da nake adanawa na mik’a masa
“Baba ga wannan ka ajiye mani kamin Allah ya dawo damu, dan nasan duk gidan nan babu inda zanyi ajiya tsawon shekaru nadawo na sameta lafiya inba gurinka ba”
Kar6a yayi tare da yin Murmushi
“To Zulaihatu Allah yasa rai yakai”
Haka mukayi bankwana da mutanen gidan cikin alhini gami ga jimamin rabuwa da juna.
******
*Bayan shekara* 1
Waya ce a kunnena cikin farin ciki da annashuwa nake gaisawa da Baban nawa wato Sirikina kenan
“Zulaihatu wai waza aba ajiyar nan taki ne ya ajiye miki?”
Murmushi nayi tamkar yana ganina”Baba karka damu da wannan ajiyar insha Allahu yanda na baka ajiyar nan da hannuna haka kaima da hannunka idan na dawo zaka maido mani”
Ajiyar zuciya naji yayi kana daga bisani yace”To Zulaihatu Allah yasa rai ya kai”
******
*Bayan shekara*4
Kwance nake akan doguwar kujerata nayi rigingine hawaye na bin fuskata yayinda wasu baitoci na ban tausayi ke fita daga bakina

_Fitar rai wajibin abu ne mai rai bazaya d’ore ba_
_Ita cuta ba ajali ce ba_

_Lafiya ba rayuwa ce ba_

_Wuya ba mai kisa ce ba_

_Duka tsarin jalla ne rabbi_
_Ta aziya xan a baitina_

_masoyana da dangina_

_mun asarar jijiya babba_

_Samunta bazamu sake ba_
_Ita adduniya aqallil qalil_

_wa asshukuha azallil zalil_

_Mai sonta bashi hangen jamil_

_Aikinsa bazaya d’ore ba_
_Wayyo Allah ka yafemai_

_Kwanciyar kabari ka gyara mai_

_Gidan Aljanna saka mai_

_dan kaine mai rahama rabbi_
_Wayyo Allah ka yafemu mu_

_mun tuba ka yafe sharrinmu_

_Bala’i duk ka tserar damu_

_Dan tamu bazamu haure ba_
Ji nayi Aminiyata kuma Mak’wabciyata tana dadda6ata alamun na tashi, ga dukkan alamu ta dad’e a tsaye tana kallona
“Maman Ja’afar wai lafiyanki kuwa naga tun dazun sai faman wak’e-wak’e kikeyi kina zubar da hawaye? Anya lafiya kuwa?”
Ajiyar zuciya nayi kana na tashi zaune gami da gyara zaman nawa
“Ina Sirikina da naketa baki labarin irin kirkinsa da kuma karamcinsa gareni..?”
Cikin sauri ta katseni
“Naganesa, bamai baki kud’in abinci ba ranar da ba’a girka abinda kikeso ba?”
“Yauwa Shifa”
Ina hawaye nake shaida mata yanzun nan aka kiramu a waya ake shaida mana rasuwarsa….
Da wannan nake ta’aziyya ga dukkan iyalan gidan Alhaji Muhammad Garba
Allah ya jik’ansa yayi nasa rahama ya gafarta masa ya kyautata makwancinsa, ya yalwata kabarinsa, ya tsaresa daga azabar kabari da kuma azabar jahannama, kana ya sakashi a cikin aljanna badan ayyukansa ba sai dan rahamarsa ya rabbil-alameen
Ina rokon Allah yasa mutuwar nan ta zama hutu agaresa mu kuma ya bamu hakuri da kuma juriya na wannan babban rashi da mukayi kana ya kyautata namu karshen idan tamu tazo.
Sannu sannu bata hana zuwa inji yan magana, wai sai dai a dade ba’a je ba
Muma nan bada dad’ewa ba muna nan tafe inda ka tafi Baba
😭😭😭😭😭😭

   ZULAIHATU

(MAMAN JA’AFAR)

INA DA BURI 1-28

[4/4, 6:49 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI* 

   

®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©{SAFHA}

SADY JEGAL
FEENAT JAFAR

            &

 HAFSAT ISMA’IL (MMN HANEEP).
 Bismillahirrahmanirrahim
Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata Ala daya bamu ikon fara rubutu lafiya ina rok’on Allah yasa mu gama lafiya, Ameen.
1_Babbar rigar sa ya sab’e tare da sa hannu ya bankad’e labule idonshi akan uwargidansa wacce suke kira da Mamy. Da d’an jimami ya soma magana 

“Kinga mutanen nan ko? har yanzu shuru ba busu babu dalilin su. 

Baki Mamy ta d’an ta6e
“Uhm to ni meye nawa a ciki Alhaji? In dai Khadija ce toh idone nawa in an maimaita irin ta wancan karan.. 

Da sauri ya daga mata hannu tare da fad’in

“Kar ki mana mugun fata,tuntuni nake fad’a miki wannan zantutukan naki su suke tasiri akan Deeja”..
Baki taja ta rufe fuskantar bazai gane inda ta dosa ba.

“Ka d’ai kirata ka ji ta bak’inta, dan na tabbatar tasan abinda ta kulla..

Jim yai tare da sawa Mamyn ido,zancenta da kamshin gaskiya,dan haka wannan karan sai ya kwala kiran Deejan.
Da nutsuwa ta fito fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna gaban iyayen nata.

Abba ne ya gyara zama tare da fad’in

“Nace ya kukai da shi Aminun kinji da kyau kuwa yau din za suzo akan maganar auren naku?”. 
Kai ta dago tare da d’an sato kallon Mamy dake kallonta sai tai da kai kasa.

“Abba ni banyi waya dashi ba tun shekaranjiya, jiya ma naita kiransa kuma bai d’aga ba… 

“Hmmm,kuma dai..

Mamyn Abba ya kallo
“Meye na wani hmm? Kinga indai bazaki fadi Alkairi ba to kiyi mana shiru”.

Hannu ta aza bisa bak’inta halamun tai shiru.

Shi kanshi Abban al’amarin Deeja na bashi ciwan kai,sai dai so ya hana ganin laifinta.
“Ni fa bansan me naiwa Aminu ba shekaranjiya k’alau muka rabu dashi da yamma wallahi Mamy”..

Baki Mamyn ta ta6e halamun meye nata aciki duk Abban na kallon su.

Chan dai ya ce
“Kinga bani lambarsa nakirashi da kaina, in aka bibiya ma suna hanya gosulo ya tare su”…

Baki Mamyn ta saka tana duben Abban lokacin da Deejan ke miko mishi waya d’auke da numbern Aminu bisa screen.
Aminun ya kira,sai dai har ta gama ringin ta katse Aminu bai dauka ba har karo na uku.

Cike da mamaki ya sauke wayar tare da ciro tashi ya hau diban numbern zuwa tashi.

Deejan ya mika wa tata tare da sanya tashi bisa kunne halamun calling.
Bugu d’aya biyu Aminu ya d’aga wayar wanda ke kwance saman gado ya tasa hotunan Deeja a gaba yana jero mata Allah ya isa tun a daren jiya.

Sallama yai yi cikin sassanyar murya,take Abban ya shanye mamakinshi ya amsa sallamar.
Daga can b’angaren Aminu ya gyara zaman wayar a kunnan sa

“Wa ke magana?”.

Cike da kunar rai Abba ya ce

“Isma’il ne Mahaifin Khadeeja…

Mike wa Aminu ya yi cike da girmama wa yana gaida shi.
Sassauto wa Abban yai tare da amsawa,

“Dama munji shiru ne ga jama’a na jira daga chan gurin naku..

Jim Aminun ya yi,bai isa ya cewa Abba kanshi tsaye ya fasa auren Deeja ba,dan haka sai ya hau kame-kame

“Um dama Abba cewa nai a bari na kuma shisshiryawa a tsanake in yaso in Allah ya kaimu wani watan sai naturo ayi maganar auren ina neman wannan alfarmar Alhaji”.
Jim Abban yai,tuni ranshi har ya fara kuna jin zancen Aminun naso ya mayarshi karamin yaro,dan haka ya ce

“Shekara biyar tayi maka?

Kai Aminu ya girgiza da sauri kamar Abban na kallonshi

“A’a Abba,hak’uri za ayi akwai shirin da nake yi insha Allahu…
Kit ya kashe wayar ba tare da ya jira zancen Aminun ba rai na tafasa,tabbas yasan karan nan ba laifin Deeja ba ne.

Kallota yai yadda ta fara waro ido tana kallonshi.
“Ke dama wannan yaron d’an k’ananun mutane ne masu baki biyu baki sanar da niba tun wuri sai da na tara jama’a yanzu?

Kasa tai da kai, sai ya kallo Mamy wacce nata ido da kunnuwa.

“Mey zanje na cewa mutanen nan?

“Tabbas wannan abu akwai rashin kyauta wa aciki.
“Alhaji.

Ido ya sa mata

“Ya fa kamata ka tuhumi Khadija ko akwai tsiyar da ta shukawa yaron nan,ni nasan Aminu yaron kirki ne kasan babu yanda za ayi haka kurum yace ya fasa auren nan..
Ido Deeja ta zaro tare da kallo Abban,haka yasa a hassala ya ce 

“Mey ki ke nufi kenan? Kina nufin laifin Khadija ne duk da kinji abinda ya ce?

Kai Mamyn ta girgiza tare da fad’in

“A’a, ni bance ba,dan haka Allah ya baku hak’uri..
Fuska Deeja ta marairaice tare da yin narai-narai ido kamar za tayi kuka 

“Abba,wallahi ka yarda bansan me naiwa Aminu ba shekaran jiya k’alau muka rabu fa…

Harara Mamy ta doka mata cike da takaici,kan ta kai ga magana Salis ya shigo.
“Abba su Baba Zubairu fa sun k’osa da jira. 

Ajiyar zuciya Abban ya sau,nan ya sanarshi abinda ya faru.

“Abba to ajira shin kamar yanda ya ce d’in ko akwai matsalar data tsai dasu”.
Kai ya hau girgiza wa,

“A watan nan da nai alkawari a shi zan  aurar da Khadeeja bazama takai watannin daya d’iba ba balle yayi tunanin jiransa ta zauna yi, in alfarmar yake nema meya hanashi ya nema tun kwanaki sai yau da muka zau… 
Hannu Deeja ta aza bisa kai tana kallon Abba ido a ware wanda ke sababin zai bawa Aminu mamaki.

Tuni taji gabanta na fad’uwa ganin a yau tai gudin gara gashi zata tadda zago.

Mamy ta kallo wacce ke murmushi tana kad’a kai tare da bin su Abban da ido.
Tabbas yau karya ta k’are.

Sumumu ta mike tana tafe tana had’a hanya,

“Yaushe za a gane wai ni Deeja *INA DA BURI* ne?

Da6ar ta zauna bakin katifar d’akinta hawaye na zuba.
 Hannu ta aza bisa kai tare da sakar ihun kuka na tuno da shin wa Abba zai bata?

Tasan ta kad’e har ganyenta in har aka bata wanda bashi take da buri ba.

****
Hak’uri Abba ya bawa yayun nashi da sauran y’an uwa had’i da sanar su abinda ya yanke,a take su ka goyi bayan shawarar kan a aurar da Khadija dan huce takaicin Aminu da ‘yan baya.
***
Futowar shi kenan daga d’aki kasancewar asabar ce ba zuwa aiki ya jiyo fad’an Mamyn, ko ba’a fad’a ba yasan itada Khadeeja ne don haka kai tsaye ya nufi cikin parlourn. 
Kuka wiwi ya samu tanai a gaban Mamy,da ido ya bita yana mai kallon Mamy da halamun tambaya.

“Ai dama nasan bani da kaffara Kamal,tabbas Khadija na da hannu gurin rushe duk wani shiri na aurenta in har ya taso.
“Dan bani da abinda zan iya miki,dan fa duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwan kan doka..

Kai Deejan ta dago ido jajir tare da maka mishi harara,in har taki jinin wani a gidan,toh Kamal ne,dan haka cike da kara tusa haushi ya sau mata murmushin mugunta Mamy na kallonsu.
Tashi Mamyn tayi tare da yin hanyar kitchen, cike da keta ya kallota wacce har yanzu hawaye take goge wa kanta kasa.

“Irin ku ai dama a auren sadaqa ku ke karewa garin ruwan idon *INA DA BURI*..
Chak kukanta ya tsaya tare da kalloshi ba koh kiftawa.

Kai ya d’auke daga kallonta, dan haka sai tai murmushi irin wanda yau tare da fad’in

“Ban yi kama da matan da za ai sadaqa dasu ba kasan wannan.
“Sannan duk halina bai kai na mai auren auri saki ba dan haka bazai zama laifi ba in har na ce nima *INA DA BURI*…

Da sauri ya kallota,tabbas yasan magana ta ya6a mishi had’i da gori kamar yadda ta saba in taso sa shi a bakin ciki.
Yau ma kamar kullum yai tsam tare da kallonta,bai san meye laifin Babanshi zai rika zama makamin da za’a rika dukanshi dashi a kullum ba yana jin haushi..

Duk tsiya yasan iyaye-iyaye ne,ba kuma a sauya musu suna,dan haka yana jin ciwo in har Deeja ta ci mishi fuska akansu..
Murmushi ya yi tare da gyad’a mata kai.

“Hakane,zan so ya kasance a ni za a bawa sadakar aurenki Deeja.

Rai ta had’e kamar yadda yai tsammani da sauri,dan haka sai ya girgiza kai tare da fad’in
“Mai da wukar,dan koh a k’afa aka d’aura min ke bazan iya ja ba,sannan nima *INA DA BURI* bana jin kina daga cikin shi..
Tashi yai ya batta baki sake dan tsabar takaici, da kallo Mamy ta bishi wacce ta fito a kitchen sarai ta ji su har ya fuce.

 Deeja ta kallo wacce ke kumfar bak’in
“Ubangiji ya tsareni ni Deeja,koh a mafarki ba za kaga wannan ranar ba wallahi, mugu kawai mai mugun fata..

Tashi tai tare da shiga d’akinta cike da kukan takaici.
Tsam Mamy tai tana tunanin wani abu cike da sarkakiya,kai ta jijjiga tana murmushi dan jin shawarar zuciyarta.
Ku jira mu.

By

      {SAHAF}..✍🏾

[4/4, 6:49 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION
©(SAFHA)

FEENAT JAFAR
SDY JEGAL

         &

HAFSAT (MMN HANEEP)
2_Idonta yayi jajir don tsabar kukan data sha, shikuwa Najib tsohon saurayin ta dake gefe yana faman aikin lalashin sahibar tasa, ya sauke gwauron numfashi kana ya ce
“Ni yakamata nayi kuka bake ba Deeja, ni banga ta inda Allah ya kuskuroni ba da kika kasa tsayar dani matsayin mijin aurenki.

Ido ta dago tana dubenshi galala,dan haka sai ya cigaba da fad’in
“Wai shin,ni soyayyar ce ban iya ba kome? 

Wani mugun kallo ta sauke masa cike yatsine fuska.

“Ka ga,nifa ban kiraka don ka zauna kanaimin shirme ba, kabani shawarar yanda zanyi donni gaskiya bazan yarda ayimin auren dole ba dan wannan baya cikin buri na”.
Tsayuwa ya gyara,

“To ni yanzu mezan ce miki khadeja? Kawai kije kicewa Abba ni ki ke so kinga kin huta da fargabar Wanda za a aura miki…

Shiru sukai ganin Abba zai shige kowa ya saukar da kai kasa.
“Abba ina yuni..

Dan rissina wa yai Abban yana binsu da ido.

“Lafiya Najib,ya mutan gidan?

Har su ka gama gaisawa Abba na hasaaso wani abu cikin ranshi.
Kai ta dafe tare da fad’in

“Ya ilahi..

Fatan ta Allah yasa kar Abba yai wa zancen su na yau fassara,dan haka da sauri ta ce

 “Kaga shikenan jeka inna nutsu zanneme ka,dan yau ba wani aikin da zaka min..
Kai ya kad’a yana mata wani kallo na Allah kai damo ga harawa ta shige ciki.

Kicibis su ka ci da Kamal a bakin kofar parlour duk su ka kallo juna rai a had’e.
Kauce wa ya yi da niyar ya bata guri itama ta koma inda ya koma,harara ta maka mishi da zummar sauya gu ya sake yin wajen dan haka a masife ta ce

“Malam ka ban waje na wuce..

Rai ya had’e ganin zata raina mishi hankali ya ra6a ta gefe ya wuce tana mishi harara.

****
“Ni fa ina ga yaran nan son juna suke Mamyn su..

Da mamaki Mamyn ta kallo Abba.

“Su wa fa?

Murmushi ya yi tare da gyara zama.

“Najib da Deeja nah..

Ido ta sa mishi,jin ba wanda ta hasaso ya hasaso ba.
“Najib kuma?

Kai ya jijjiga mata.

“Ina ga na samo mafita, abu d’aya nake tunani bai da aikin yi ban san da mey zai riken Deeja ba..

“Ni fa Alhaji ba Najib ya dace da Deeja ba,kamata ya yi ka had’a Deeja da wanda zai iya seta tunaninta ya juyata ba wai ita ta juya shi ba.
Ido ya sa mata yadda take bayanin,yasan inda ta dosa tunda an ta6o kishiyarta Deeja.

Dan haka da sauri ya katseta.

“Ban san mey Deeja ta tsare miki ba,kullum burinki ki ga yarinyar nan na kuka tamkar ba ke ki ka haifeta ba.
Baki ta saka tana kallonshi,daga fad’in gaskiyar?

Kai ta kad’a tare da jan bak’inta ta rufe,tasan yanzun tata zatai zafi.

****
Aure kam Abba bai fasa ba,duk wata dabararta ta kare daga Najib har Mariya kawarta ba mai wata shawarar da zata bulla mata.

Yau tafi kullum kuka ganin gobe iyanzu ta zama matar Najib.
Zumbur ta mike tare da fita a d’akinta ta nufi d’akin Abba,tabbas wannan ce damarta ta karshe,in ta bari aka aura mata Najib tasan tai babbar wauta a rayuwa.
Kuka reras ta tasa shi gaba tana yi,dan haka tuni ya rikice ya hau tambayar mey ne ne?

“Abba ni fa ka had’ani da kowa amma banda Najib…

Harshe ta datse jin ta kwafsa.

Murmushi Umman tai tana cigaba da dama furarta.
Kai Abban ya girgiza, 

“Matuka zan sa6a miki wannan karan Deeja,dan babu abinda zai sa na warware auren nan tunda har gobe ne za’a d’aura..

Bori ta hau mishi harda su shusshura k’afa.
Ya sani da matuka yana ji da ‘yarshi tilo d’aya mace tamkar tsoka daya cikin miya.

In har ba so yake zancen Baba Zubairu ya tabbata ba na tsoron Deeja yake toh kwa dole ya nuna mata aure ba fashi,dan haka kawai sai ya tashi tare da shige wa band’aki ran shi na kunar jin kukan nata.
Rarrafo wa tai gaban Mamyn.

“Dan Allah Mamy ki taimake ni kar a ban Najib,ni wallahi nafi karfin Najib,na yarda ni nake korar samarina amma dan Allah kar a ban Najib..
Baki Mamy ta saka,fatan ta Allah yasa Alhaji yaji wannan batu na Deeja.

“Na sani ai,ki d’auka wannan ne sakayyar su gare ki da Allah zai musu,baki fara kuka bama sai in kin ganki a gidan Najib din.

Kuka kam Deeja tasha shi,hannu bisa kai ta fio a dakin Abban.
Duk da kallo su ka bita duk su na sauraron ihun nata daga saman Abban.

Murmushi Kamal ya yi tare da girgiza kai.

A gaban yayun nata ta zube.

“Ya Salis dan son ku da Allah kar ku bari a min auren nan da Najib,wai ni yau Abba ya fatattaka…
Kuka ta sa musu,dan haka masu harararta nayi,masu kunshe dariya nayi.

A kaf gidan da wanda bai san halin Deeja bane,ai a ganin su wannan ne dai-dai tunda dama bata da abokin shawara sai Najib,dan haka a hankali kowa ya fara zame wa tana binsu da ido.
Kamal ne kad’ai ya rage wanda yasha mur yana kallonta.

Harara ta sau mishi duk da kuka take kamin ta mike tana goge hawaye zata wuce

“Ni kad’ai zan iya taimakon ki Abba ya janye auren Najib kin san wannan..
Chak! Taja ta tsaya ba tare da ta juyo ba,ta sani da tabbas matuka Abba yana jin shawarar Kamal.

“Ki sauke komai ki bishi ya taimake ki..

Kai ta kad’a jin shawarar zuciyarta.

A hankali ta juyo tana mai goge hawaye.
Ya hakimce a kujerar tamkar wani sarki yana dubenta,wannan ce yasan damarshi ta karshe da lalle Deeja zata shigo hannunshi.

Kasa ta zauna tare da kura mishi ido.

“Toh ka taimake ni..

Kallon tara saura kwata yai mata.
“Wannan ba ladabin roko bane..

Harara ta sau mishi tana had’e rai,sai dai tuno da shine damarta ta karshe yasa ta mike bisa gwiwarta tare da yin kalar tausayi da yanayin roko

“Dan Allah ka taimake ni yaya Kamal..
Murmushin mugunta ya saki tare da jijjiga kai ya mike

“Ashe kin iya ladabi yarinya..

Wuce wa yai ba tare da ya sake kallonta ba saman Abba,cike da takaici ta mike ji take tamkar ta shako shi ta huta,sai dai dole tai ladabi dan ita zai taimaka.

By
{SAFHA}.

[4/4, 6:49 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©{SAFHA}

SDY JEGAL
FEENAT JAFAR

          &

HAFSA ISMA’IL(MMN HANEEP).
3_Washegari sai baza ido take taji ance an fasa aure shiru,sai ma shiri da kowa taga yana yi baki a washe.

Gabanshi ta sha ganin yana neman fita tana dan satar kallonshi ganin sosai yau yai kyau tamkar ango.
“Ina kwana..

A ciki-ciki ta gaida shi,murmushi yai tare da hard’e hannu yana kallonta.

Baki ta zumburo jin yai mata banza da wannan munafukin murmushin nashi,dan haka sai ta hau yatsina tana fad’in
“Ni fa ban gane ba,koh ka fasa taimakon nawa naga kowa na shiri?

Tsayuwa ya gyara yana kallonta,dan haka tuni ta sake kulewa.

“Ladabi shi yai miki karanci..

Rai tai saurin had’e wa tare da mishi kallon sama da kasa cike da kar ka rainan hankali..
Ajiyar zuciya ya yi tare daga kafad’a

“Koh da yake,kar kiji komai,na gama taimakon ki tunda kin roka jiya,ki sa ido babu aurenki da Najib Insha-Allah..

Fuska ta saki ganin ya juya ta sake yin saurin shan gabanshi,Abba da ya sakko yana kallon yadda take farin ciki,hala koh ta san abinda ke gudana?
Murmushi ya yi ganin yadda Kamal din ma yake mata murmushi har ya fuce.

Juyo wa tai,da mamakin shi harda gaidashi ta shige d’aki,ita fa a dole sunyi wa Abba wayo.

Ta sani Kamal in ya ce toh ya ce,bai da karya a lamuranshi,dan haka tasan aure babu.
Da kallo kawai Mamy ke binta ganin yadda take rawar kan,sai ta girgiza kai da murmushin mugunta,tasan karyar y’arta kam ta kare.

Dan haka da ido kawai take binta.
Kasantuwar aure babu wani shiri yasa gidan ba jama’a sosai,har kawayenta ta ce kar wanda yazo.

Kasantuwar a unguwar Baba Zubairu ake taro bata san wainar da ake toya wa ba sai da suka dawo kusan sha biyun rana.
Tana d’akin Mamy sai alkawari take mata akan Insha-Allah ta kusa samun cikar burinta tai mata adu’a kawai.

Kai Mamyn ta kad’a tana murmushi, kai daga gani na baki da wayo ne.
Yayunta ne suka shigo da sallama,kowa bakin nan har k’unne.

“Kun dawo?

Kai su ka jijjiga

“Eh Mamy.

Deeja su ka kalla tare da fad’in

“Congratulations toh Deeja…

Baki ta wage harda fad’in

“Thanks..ina yaya Kamal?
Leko wa yai yasha shadda fara ganin d’akin ya cika bai shigo ba.

Hannu ta daga mishi tare da fad’in

“Na gode

A hankali.

Kai ya karkatar halamun u r welcome.

“Ai Najib Mamy yana chan sai bori yake wai akan ba dashi aka d’aura ba sai da wani…
Da sauri ta kallo Salis wanda ke magana.

“Ban gane ba?

Kallonta su kai ganin yadda ta sa mishi ido.

“Kwarai, ba’a d’aura da Najib ba,na cikin gida akai..

Ido ta zaro tare da fad’in

“Waye wani?

“A ina yake?
“Kamal man,waye na cikin gida in ba shi ba…

Kamal din ta kallo da sauri cike da tuhumar haka mukai da kai? Tana had’iye wani d’ad’d’acen yawu jiki na ka’rkarwa,a zabure zatai kanshi taji ta kasa motsi ganin yana mata murmushin mugunta,kan ta farga har ta fara ganin duhu.
A hankali ta fara tangad’i kowa hankalinshi yai kan Mamy su na mata dariyar keta,luu ta tafi zata fad’i da azama ya turo ciki tare da rukota.

“Deeja..

Gaba d’aya suka kallosu har Mamy jin kiran da Kamal d’in ke mata suka rufa kanta.

Jijjigata su ke,sai dai Deeja ba sauran numfashi.
“Mamy fa suma tai inaga..

Cicci6arta ya yi tare da d’aurata gadon Mamy Zaid ya tafi fridge dan d’akko ruwa sai ganan sun shigo shi da Abba a sukwane.

“Ku matsa,garin yaya ta suma?

Kauce wa sukai Abban ya hau gadon,yayyafawar ruwan duniya Deeja taki motsi dan haka dole su ka danganta da asibiti.
Yasan tai nisa a suman da tai dan likitoci sun tabbatar shock ne ya jawo mata haka anjima kad’an zata farfad’o.

Kowa yai jigum ana jiran tsammanin tashin Deeja.

Gida suka tafi jin numfashinta ya dawo normal amma sun mata allurar bacci.
Kamal ke kanta dasu Mamy a waje.

Ido ta fara juya wa da kok’arin zata bud’e su dan haka sai ya matso yadda in ta bud’e ta fara kallonshi.

Warai ta bud’e dan tuno da abinda ya faru dazun tare da kallon d’akin, akanshi idonta ya sauka.
Hannu ya dago mata halamun hi! Yana murmushi mugunta.

“Kin tashi?

Ido ta sa mishi tana mai tunano abinda da ya faru.

“Ba suma ba ai koh mutuwa ki ke kina dawo wa dole ki kar6i taimako na..
A zabure ta tashi daga kan pillown tana dafe kai jin komai ya dawo mata,a take ta fara yarfo mishi ruwan bala’i

“Wallahi Allah ya isa bazan ta6a yafe maka mugun kawai maketaci,dama wannan ne taimakon naka? Toh wallahi baka isa ba,dole ka sake ni..
Dariya ya fara irin wacce bata ma san ya iyata ba,dan irin ta ketar nan harda rike ciki.

Dan tsabar takaici kawai sai ta sau mishi kuka tana mai sake maimaita Allah ya isa ba iyaka yana dariya.

By
{SAFHA}..✍🏾

[4/4, 6:49 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©{SAFMA}

SDY JEGAL
FEENAT JAFAR

          &

MMN HANEEP
4_Mamy ce ta shigo dan duba koh ta farka taji kukanta da Allah ya isan da take surfa ma Kamal.

Dariyar ya kunshe tare da gyara tsayuwa jin bud’e kofar.

Da harara Mamy ta bita,dan haka sai ta daina Allah ya isan ta hau kuka iya karfinta.
Fita yai ya basu guri, dan haka sai Mamyn ta sa mata ido cike da tuhuma.

“Kina nufin wai mijinki ki ke wa Allah ya isa?

Kukanta kawai take baji ba gani,dan haka kai kawai Mamyn ta jijjiga tare da fad’in

“Ya miki kyau. 

Fita itama yi,ba daban kanta dake sarawa ba da ba abinda zai zaunarta asibitin nan.
Tare da likita su ka dawo sai harara take sau mishi,ganin haka yasa likita ya kalloshi tare da fad’in 

“Mey aka mata ne?

Kallota ya yi duk yau d’aya ta fita a kamaninta.

“Ai da surutai ta tashi ne likita ni da na ma zata koh ta…
“A’a ka manta da hauka na tashi,mugu kawai,wallahi bullukututu dan bazan ta6a yafe maka ba har sai ka sakeni..

Kuka ta sake sawa baji ba gani dan haka ido kawai su ka sa mata.
Rokon Allah da annabi ta rika yiwa Abba akan auren nan ya raba in har yana sonta,ita a bata kowa ta yarda har Najib da dai a had’ata da Kamal.

Lallashinta ya rika yi da fad’in toh,tai hak’uri a koma gida sai ai batun,karshe sai da aka mata allurar bacci ta bar kowa ya sarara. 
Washegari fur taki zaman asibitin a dole su ka sallameta,burinta kawai taje gida ayita ta kare.

****
Duk ta dawo kalar tausayi ganin babu sarki sai Allah,dan karan nan sosai Abba ya d’auke mata wuta,ga kyara gun Mamy,ga ketaka ta gun Kamal,bata da sauran dabara a yanzu dan koh Muneera Mamy ta dakatar ta da zuwa.
Kamar wanda aka tsikara ta mike zaune tare da kallon agogo.

Waya ta d’auka tare da danna kiran Najib.

Tsaki tai jin bai daga ba ta sake buga wa.

“Meye kuma?

Fuska ta marairaice kamar yana kallonta.

“Haba d’an uwana yanzu yau sati ina a bala’i amma koh ka kira balle kaji ya na kare?
Zurmashi ta rika yi kamar yadda tasan Najib kam akanta wawa ne har ya zirmu ya sakko.

“Yanzu ya ki ke so ayi toh?

Zama ta gyara tare da sanarshi taimakon da zai mata in dai har zata rabu da auren nan.
Gyale ta dakko tare da fito wa tana leke kamar munafuka, koma wa yai ganin tana sand’a lokacin da ya fito a kitchen da gorar ruwa a hannu.

Ruwan ya ajiye tare da binta ganin ta fice.
A tsaye suke ita da Najib din a bayan gida duk ya dawo wani soko a gabanta.

“A’a Najib,ka yarda dani karan nan in har ka taimakeni toh da wannan kaddarar auren gwara naka ka yarda da dan…
‘Yar dariyar da su ka ji a bayan su ne yasa tai shiru tare da juya wa.

Kallonsu yake had’i da dan jijjiga kai yana yar dariya jin yadda take raina wa Najib d’in hankali.

Harara ta sau mishi tare da juya wa ga Najib.
Murmushi Kamal din ya yi tare da kad’a kai,

“Bana tunanin na ta6a gamuwa dirinka ba sam Najib wanda karamar kwanyar mace ke badda tunaninshi 6at cikin lokaci kad’an..
Juyo wa sukai fuskar Najib din d’auke da mamaki.

“Mey ka ke nufi? 

Deeja ya kallo tare yana murmushi,har mamaki yake yadda ta d’auki sa6a Allah a matsayin hanya mai 6ellewa a gareta,wannan mummunar dabi’ar tana d’aya daga cikin abinda yasa bai shiri da ita koh kad’an.
“Amma Deeja bakya tsoron Allah fa..

Ido ta zaro da sauri tare da bud’e baki.

Kai ya jijjiga.

“Da kina tsoron Allah da kin sanarshi cewa da kanki ki ka bada kwangilar rushe aureku saboda shima baya daga cikin burin ki wanda nasan shima yasan da haka..
Kallo Najib din ta danyi a sace,shima idon ya zuba mata kir dan gaskata gaskiyar lamari.

Sam bata iya karya ba musamman in an mata kamun kazar kuku irin haka,dan haka tuni ta hau mishi kame-kame yai saurin daga mata hannu.
“Ba ki da abin fad’i Malama, dan sai yanzu na sake tabbatar da ba karamin rainan tunani ki kai ba tun da..

Da sauri ta katseshi da fad’in

“Kadan ba karya bane..

“Dallah rufe min baki..

Baki sake take kallonshi da mamaki,wai yau ita Najib ke hantara bata da ta cewa.
“Wato bani da amfani sai in bukatar korar samarinki tazo koh?

Shiru tai ba bakin magana,dan haka tuni ya hau huce haushin shi kanta Kamal na gefe yana kallo jin yadda yake zazzageta gabanshi had’i da tonan silili.
Da kallo ta bishi baki sake har ya 6acewa ganinta ba bakin magana.

Kamal din ta kallo tamkar ta d’aura hannu bisa kai ta sau ihu koh ta shake shi ta huta.

Kafad’a ya daga mata tare da juya wa ya batta nan tsaye baki sake.
Koh ba komai ya toshe wannan 6arnar da ya jima tana kona ranshi ta tsakanin Najib da Deeja.

Ido ya rufe lokacin da yake tuno shan mintin nasu na karya da wai su ka d’auka abin dogwaro duk da su na cin nasara.
Abu d’aya su ka kasa gane wa,shine sa6on Allah sa6on Allah ne duk kuwa da K’ank’antar sa6on toh ya zama zunubi.

Iskar bak’inshi ya furzar tare da zama gefen katifa,fatanshi yasa daga wannan sun rabu kenan.

A fili ya furta zanyi maganinki!
*****

Ganin kunci yana neman hallaka ta yasata futowa falo inda take jiyo hirar su mariya da sauran yaran yan uwa da Abba ke rikon su, Sakina da Maryam sai Mariya datafi kowa kaudi a cikin su,.

Suna ganin ta suka saki murna don dama suna cikin damuwa ganin ta cikin kunci taki kula kowa sunai mata magana ta hausu da masifa, yanzu kuwa da suka ganta cikin walwala har rige-rige rikota sukai cike da murna suna karai mata sannu da jiki,
Nan ta sake cikin su suna hira shakiyancinsu harya fara batar mata da damuwar ta, Mamy data leko ta gansu haka saita bisu da murmushi taji dadin ganin yanda tasoma sakin jiki sakamakon kwanakin baya da take yini a d’aki cike da kunci da damuwa.
Shigowar sa falon ce sanadin dakushewar farin cikin ta,
Shikuwa ko kallon inda take baiba illah sabon darasin hira da suka bud’e da yaran yawan cin hirar tasu akan ‘yan matan yanzu ne, jin an tab’o inda ke masa k’aik’ayi yasashi gyara zama don ganin yasamu damar goga mata zana.,
Saida yakai lomar Abinci bakin sa” kuna jina? Wasu fa ‘yan matan na yanzu ba gwara garin kwaki da suba, a arha b’agas ake tafiya dasu kuni wacce igiyar soyayyata ta zargomin ko naira hamsin kabata kana iya sumbatar kuncin ta ko fiye da haka ke alakoro ma inta yaba murmushin ka saita baka ka tsotsa”,
Dif! Sukai danjin yanda akalar zancen nasa ya dosa duk da basu fahimci ainihin meyake nufi ba sunsan dai da Deeja yake, don haka sukai kallon kallo a tsakanin su sukai dariya tareda canja akalar zancen.
Deeja kuwa? Jitai marar ta takulle hankalin ta yatashi shikad’ai yajiyo sautin da cikin ta yabada kullllll!! Alamun tsurewa da batun sa,
Don haka ya gumtse dariya ganin duk ta firgice tayi narai- narai da ido tamkar tasaki kuka don tasan Kamal zai iya tona asirinta gurin k’annan ta don kirki bai isheshi ba,
Duk da ya kunshe dariyar sa saida takai da kubucewa don ganin tamike tsam tana b’arin shigewa band’aki da gudu.
*****
Cikin wannan kwanaki ya hana kansa sukuni a sakamakon abinda yayi mata rannan a gaban su Sakina, don haka yafaki idon mamy dake kicin ya fad’a mata d’aki ya maida kofa yarufe.,
Zunbur tamike a razane don bata tab’a tsammatar zai bankado mata d’aki cikin irin wannan lokacin.,
Ganin ta taso masa yasashi dakatar da ita, 
“Kinga karki tareni da hayagaga Abu d’aya zuwa biyu yakawoni gareki,
Yafara magana cikin tausasa murya.,
“Na farko naga kwana biyu kina boye kanki a d’aki bayan naga rannan kece harda zaman hira a falo shine nazo naji ko lafiya?
” sannan kuma intayaki jajen Abinda yafaru”,
Shuru yai yana saurarar cewar ta, 
Shuru ta shareshi, ya tsira mata ido da kyau yana nazarin ta, ta rame sosai damuwarta na tasowa ne tun daga tsakiyar zuciyar ta a lurar da yayi mata kenan, yajima bai mata irin wannan kallon kurillar ba yanzu sai yaji miliyoyin sonta na tasomasa muryar ta kawai yake da muradin ji gashi kuma taki magana,,
Ya sake gyara tsayuwa yanai mata dariyar tura haushi,,
“Au na manta naga kwana biyu kun bata da me debe miki kewa ni kuma dazan debe miki ta ainihin kin nunan iyaka ta”
A kufule tace”
“Burinka yacika to yanzuma zaman nan da nake ubangiji nake kaiwa k’rarka kuma gashi tun ba’aje ko inaba yasomai min sakayya”
“Amma yakamata ace cikin kunya kikayi maganar nan”
Duban rashin fahimta taimasa,,
“Yanzu duk rashin tsarkin ki bakiji kunyar gurfana gabansa kina kai karar mutumin kirki irina? Ko bakya tuna abinda kukai da Najib?
Ta kasa magana,,
“Da kinada hankali da tunani jinjina ya kamata kimin dana taimake ki na aure ki donni naganki yakai sau dari a yanayin dabai dace ba tare da Najib,, 
“Amma bantaba fasa sonki ba Deeja, kinga shi Aminu gani d’aya yayi miki kuna asha ruwan tsintsaye ya zargawa Karen sa igiya to kice da yaga Najib sakale da kugun ki yana kokarin zira miki harshe a baki had’iyar zuciya zaiyi ya mutu”
Ba shiri tamik’e zaune cikin haki tana waige-waigen don tsoron kar wani yajiyo su,,
Kamar zata rushe da kuka tace” kai Kamal kaji tsoron Allah yaushe kaga Najib sakale da k’uguna?
“Kina nufin sak’ale k’ugu baikai tsoma harshe cikin baki bane?to ai naga abinda yafi haka ma kuma ko agaban wanene zan bada shaida”
Kofa tanuna masa cikin tunzura, “tafi bayan duniya kabada shaida”
“Aiba saikin sani ba ko rakiya kika gayyace ni lokacin da kuke sheka ayar ku?.

“Ni yanzu Alfarma nazo nema tunda Najib yagudu nasan kina cikin damuwa don haka ki taimaka kibani dama na maye gurbin Najib duk Abinda kike zaton ya iya dama wanda kike bukata babu wanda ban iyaba har karima sai kinsamu”.
Hawaye tasoma tana marmasa ido tsoro fal ranta,
“Kamal Dan Allah kafuta kabani guri inhar ka gwada kanason tarewar mu Allah ya isa ban yafe ba haka inka kuma shigo min d’aki,,
Yana dariya ya amsa,,
“Allah ya isar shigowa daki kawai zan guda amma maganar tariya banida matsala inhar zan dinga zagayowa koke ki faki ido kuzo tomu shekara a hakan”
Zuwa yanzu tafara kuka wiwi,
Duk da yalura kamar numfashin ta zai dauke don kuka da tashin hankali amma bai fasaba,,
Yanzu nazo kinsame ni a b’agas haka zaki barni natafi a bagas? Kibani dama ko d’aya ce Najib bazai nunamin iya shan minti ba donni ma ba baya bane”
Tariga tagama kaiwa karshe don haka ta d’ora hannu a ka ta kwarma uban ihu, tuni kamal ya b’ace,,
Mamy da Abba ne sukai rige rigen shigowa suga wanne hali ‘yarsu tashiga data cika gidan da wannan uban ihun…..,
Tsaki mamy tasaki tai komawar ta kicin cike da takaicin khadeeja, 
Shima Abba rufeta dafada yayi kana ya futa yana fadin nasan ”

matakin da zan dauka akanki”

****

SAFMA

[4/4, 6:49 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©{SAFHA}

SDY JEGAL
FEENAT JAFAR

          &

HAFSA ISMA’IL(MMN HANEEP).
5_Ba koh sallama aka bankad’o kofar d’akin nasu sai huci take kamar ta ci babu.

Ido ya sa mata fuskarshi ba yabo ba fallasa,har mamakin zuciyarshi yake in ya tuno wai tana kwadaituwa da son Deeja.

Yarinya da ciwan kanta ma a ganinshi bata sani ba balle tasan na wani.
Ya sani a in da wanda Deeja taki jinin gani a yanzu toh bai wuce shi ba,dan tana mishi tsanar da k’arara kowa ke iya ganinta kwance bisa fuskanta.

Murmushi ya yi a zuciyarshi, abu daya ne bata sani ba,aurenshi da ita shi ake kira *Mutu ka raba, wai takalmin kaza*.

***
Fushi ta diba yi da kowa cikin gidan har Abba,dan ya sake jaddada mata hukuncin shi na nan bisa kanta.

Ba ruwanta da sha’anin kowa,kamar yadda kowa ya d’auke mata wuta,abinci sai ta ga dama zata ci.
Kusan wata guda kenan da auren,dan haka Abba ya ce su tattara a tare haka nan kila in ta bar gida zata saduda.

Ranar taci kuka jin da gaske zata tare gidan Kamal.

Kamal d’in ne ya samu Abba da zancen kaita garin su.
“Abba ina son muje chan Kogar gun Abba kamin..

Kai ya dan sosa yana sinke kai,dan haka sai Abban ya kad’a kai yana murmushi.

“Ai munyi waya na sanarshi komai,dan haka ka tafi da iyalin naka chan dan su santa.

Kai ya sake duk’arwa yana godiya.
Deejan ya kwad’a ma kira,chan ciki ta amsa tare da fito wa tana chunno baki a dole ita fushi take dashi.

“Ki kimtsa za ki bi mijinki ya nuna miki ‘yan uwa kamin ku tare chan Kogar da sauran su.
Kai ta dago da sauri tana kallon Abban kamar ta sau kuka,dan haka sai Kamal din ya basu waje.

“Khadija..

Nan a ciki ta amsa.

“Na baki dukkanin wani so da kulawa,ban ta6a neman wata alfarma a gareki ba sai wannan.
“Ki min alfarmar yi wa aurenki biyayya,kar ki bani kunya in kunje gun abokina koh danginshi..

Jinshi take kawai har ya gama,ita tunaninta ya ma zata iya rayuwa cikin kauyen su Kamal koh ta yini ne,dan haka ba komai taji ba illa tunanin abinda zata riska.

***
A Kogar.
Kallon kowa take a raine, duk da su sun mata tar6ar kirki da karamci barin su Badiyya k’anwar Kamal.

Duk ido ya sa mata yana karantar ta,hatta abinci taki ci sai yatsine fuska take halamun ta raina muhallinsu.
Tunani take yanzu kila wannan matar har ita auren Baban Kamal ya kusa sittin..

Kai ta girgiza,

“A’a na barshi a talatin..

Nutsuwa tai tare da kallon ko’ina, d’aki ne na kasa yasha leda sabuwa ko’ina kal-kal.
Baki ta dan ta6e,duk yana kallonta ta window.

Kai ya jijjiga tare da shiga d’akin.

Rai tai saurin had’ewa tare da mike wa.

“Na fa sanar ka ni ban son shisshigi ka rika yin nesa-nesa dani da inda nake.

A raine yake kallonta, chan dai ya jijjiga kai tare da fad’in
“Ki shirya gobe riga zamu dama,da sannu zan karad’e miki kauye nah kamar yadda Abba ya ce.

Harara ta maka mishi,sai ya jijjiga kai ya fuce.

***
Kwanan su d’aya a Babban gida washegari ranar kasuwa ya samu ‘yan uwan Mamanshi sunzo cin kasuwa dan haka tare zasu bisu.

Ido ta zaro ganin motar da ake d’anewa wai nan zata hau.

Da hannu ta nuno mishi motar.
“Wai kana nufin a wannan akori kurar motar zamu tafi?

Kai ya d’auke tare da sanya jakar su,

“Malam da fa kai nake..

“Ki jira sai na miki bayani.

Motar ya d’ane kamar yadda yaga sauran sunyi ya batta baki sake tana sake karewa buddadiyar motar kallo.
Masifa ta fara a kan fafur sai ya sauke mata kayanta dan fa ba ta6a hawa ba,ba kuma zata hau ba.

Kai ya jijjiga

“Toh ki san inda dare ya miki tun wuri..

Harara ta galla mishi tare da rike k’ugu tana masifar dole ne sai taje?.

Jin mota na dirin tashi ga wasu gunguma gunguman shanu na taho wa yasa ta fara raba ido.
Banza yai mata har aka tada mota,

“Toh ta ina zan hau?

Juyo wa yai tare da kallonta,kan ta aune har ya sau dariya.

Dakyar ta iya hawa shima sai da ya taimaka mata.

Tafiya akai mai d’an nisa tana gani ya tushe rabin fuskarshi.
Sosai yau ta jigata, harda kukanta lokacin da za a sauka taga wai ba’a zo ba an tsayarda babur wai mota bata shiga wajen.

Haka tana ji tana gani ta d’ane babur ga magriba ta sanyo kai sai dariyar keta yake mata.
Duhu cur suka isa rigar Mongwano,ga bakar yunwa,ga gajiya,tun kan aje ko’ina har ta tantance Kogar babban birni akan nan ganin yadda take cin karo da bukka.

Cikin yaren fillanci suka kewaye su da fitulu cike da murnar zuwan Kamalu.
A jigace ta kalloshi,

“Ruwa..

Ido ya sa mata,tun kan aje ko’ina har ta shiga hankalinta.

A ‘yar karamar kwarya aka kawo mata ruwan dan haka kawai sai ta daga ta hau kwankwad’a.

Tasha kusan rabi taji ina ba gama ga wani karni da ruwan yake.
Sauke wa tai tare da haska shi.

Gaba d’aya bai mata kalar ruwa ba,yafi kama da lamurje,dan haka da sauri ta ajiye tare da fara yatsine fuska kamar tai amai.

Kai ya jijjiga, yana auna bata ma ga komai ba..
Abinci kuwa loma d’aya ta cire hannu tana kallonshi yadda yake shan nono.

Harara ta galla mishi tare itama d’auka ta ture abincin.

Kur6a d’aya tai saurin furzarwa jin tai karo da tsami da wani dogon abu.

Nonon ta haska,sam ba irin na gari bane duk ba kyan gani.
A marairaice ta kalloshi jin yadda yake sakar dariyar keta.

“Amma dai dama kashe ni kazo yi garin nan koh?

A dirare ya kallota ba kiftawa,kan ta farga ya sake ke cewa da dariya.

“Welcome to Mongwano city..

Kuka ta saka mishi cike da jigata ga yunwa.
“Yarinya baki ga komai ba ma,a gaba akwai inda zamu koh wannan din ma ba zaki samu ba..

Baki ta ta6e tana mai sake artayo kukanta har mutanen gidan su ka fito ganin koh lafiya.

Lalle yau ta sake yadda da bakar muguntar Kamal mai yawa ce.
Da fillanci yai musu magana,dan haka sai d’aya ya koma tare da dakko mata kosai da fanken da ya siyo a kasuwar Babban guda ya bata su na mata dariya da fulanci.

Dama-dama, dan haka tana ji tana gani wannan taci yana ta kela mata dariyar mugunta.
Gado aka bata a cikin ‘yar dukurkurar bukkar wanda sai ta tsuguna take tsayuwa.

Ajiyar zuciya ta sau tare da kallon ‘yan matan dake gulmarta su na kunshe dariya.

Kaya ta cire tare da sanya na bacci ta daura zani a kai.

Zani ta sake shimfida wa bisa gadon jin yadda yake sukarta tamkar da kaya akayi shi.
Chan taji abu na dan zubo mata bayan ta kwanta.

Waya ta haska tana tsaki a zatonta koh kasa ce.

Wasu k’ananan kwari ne da gara ashe da wasu bak’ak’e suke zubo wa daga sama.
Baki ta ta6e da zummar sakar kuka dan bakin ciki,ina wai Kamal ya kawo ta?

Gyalenta ta dakko tare da lullu6a tana tsaki ita kad’ai tare da kallo y’an matan da suka kwanta abin su.

Abu taji yana yawo bisa kanta a saman gyalen,dan haka tuni ta fara raba ido tare da janyo waya a hankali.
Gyalen ta yaye tare da haska wa,wata bakar katuwar kunama ce ta daga kari sama,da karfi ta yar da gyalen tare da dira a gadon ta ari na kare ta fuce tana ihu

“Wayyo kunama…

Tashi yai tare da saurin zuwa inda take kukan,tana ganinshi ta rukunkumeshi tare da fad’in
“Wallahi bazan kwanta a d’akin nan ba..

Mutanen gidan ne suka fito jin ihun nata.

Hannu ya kai kan bak’inshi yana fad’in

“Shshhh,to anji, bata cije ki bade koh?

Kai ta daga da sauri tana maida numfashi.

Fur taki koma wa,karshe inda ya kwanta da Buba nan ya ra6a mata ta raka6e daga zaune shi kuma ya shige makwancinshi.
Yadda take rike da hannunshi kam yasa ya sa mata ido,yau d’aya har ta dawo abin tausayi.

“Ki ma ware,dan sati muka zo yi a nan.

Ido ta zaro tare da marairaice fuska,da sauri ta hau burburwa fad’i take

“Wallahi baka isa ba gobe zan bar garin nan.
Kai ya girgiza tare da fad’in

“Toh mu zuba,ai sai randa naga kinyi ladab.

Ranar kam tasha kuka da kiran Mamy,tasan in tai sati a garin nan kila sai dai a d’au gawarta. 

Karyar raina mishi muhalli yasan ta kare.

By
SAFHA..✍🏾

[4/4, 6:50 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©{SAFHA}

SDY JEGAL
FEENAT JAFAR

          &

HAFSA ISMA’IL(MMN HANEEP).
6_Da asuba ta farka,duk da dama baccin rabi da rabi tayi tana tashi yin dube-dube na dangin kunama,ga duk ya cinye wajen kad’an ta samu ya bar mata ta ra6a.
Juyi yake shirin yi duk wuyanshi ya k’age da kwanciya gu d’aya.

Ido ya sa mata ganin yadda zauna tare da sanya kanta bisa kafafunta a haka take bacci.

Tausayi ta bashi ba kad’an ba,dan yasan tabbas ba tai wani baccin arziki ba yau.
Dan haka hannu ya kai da niyar kwantar ta kwala ihu tana raba ido.

Harara ya sau mata tare da fad’in

“Wai ke abin ihu bai miki kad’an ne?..

Da sauri ta ce

“Eh d’in..

Kai ya jijjiga tare da tashi tai zirif ta mike.

“Ina zaka?
Banza yai mata tare da d’aukan buta sai ta bishi tana wai waye.

“Mey ki ke nufi ne wai?

Rai ta had’e tare da fad’in

“Abinda ka ke nufi,kana nufin ni kad’ai zaka bari a kurumin dajin nan?

Ido ya sa mata,karshe sai koma wa yai sai da gari yai sha ta barshi yai alwala.
A kan su ta tsaya ana tatsar nono ‘yan mata sai kwankwad’a suke,fuska ta hau yatsine wa tamkar tai amai yana kallonta yana jijjiga kai.

Karshe itama sai wannan d’in tasha,dan fa biskin jiya aka sake kawo wa wai dashi za ai break.
Deeja kam taga rayuwa,wacce take ga in ta kara kwana uku tabbas sai dai a d’au gawarta.

Rafi ta raka ‘yan matan rike da abin diban ruwa.

Ido tai saurin zaro wa ganin ruwan da zasu dina ga nan shanu sunyi layi su na sha,su na k’auce wa karnuka su ka hau layi.
K’ak’arin amai ta fara tuno da jiya tasha ya kai rabi,dan takaici har da kukanta ‘yan matan na mata dariya.

Su na dawo wa ta tubure mishi ita fa sai an tafi sam shi kam yaki kula ta.
‘Yan matan ya tambaya sai su ka mayar mishi abinda ya sata kukan,wai akwai rijiyar dad’i tai hak’uri an jima za su je su debo mata sai dai da nisa ne.

Rayuwa kam Deeja ta ganta a rigar Mangwano,shi da kanshi daurewa kawai yake,kwanan su hud’u sukai haramar tafiya.
Daga wannan lokaci bata sake tanka mazauninshi ba koh kiran shi da d’an kauye,dan ya sanarta akwai rigar da tafi wannan, chan zasu.

Da harara kawai ta bishi,dan tasan tsaf zai aikata,mugu kawai.
Koh sati basu fi ba su ka tare a gidan hayar da ya kama kamin ya idda gininshi.

Ranar ansha kuka,sai dai fur iyayen su ka ce zamansu kam a nan ya k’are,haka tana ji tana gani aka tasa keyarta gidan Kamal.

****
“Bana jin zan ta6a yafe maka dan kai sanadin da duk wani hangena ya rushe.

“Ka sani *INA DA BURI*, amma ba irin wannan ba..

Baki ya ta6e yana gyara kwalar rigarshi.

“Chan ta matse miki kuma wannan, dan yanzu babban burinki ki san hanyar faranta min in har kina so na daga k’afa..
Harara ta sau mishi tare da fad’in

“Allah sauka min ni Deeja,ai yadda kai sanadin komai,dole komai ya shafe ka..

Murmushi ya yi tare da jijjiga kai tare da daga kafad’a ya fuce.
Da yamma Muneera tazo kawarta,

“Iyanzu kam ya kamata ki ajiye makaman yakin ki Deeja,ina gudan miki ranar da zaki kasance baki a tsuntsu baki a tarko,ki yarda ke ce ke da mukulin saita duk wani Burinki ya koma yadda ki ke so,dan za ki iya saita tunanin namiji ta yadda ba kya tsammani..
Baki ta ta6e halamun abin bai ahigeta ba.

“Muna nan da ke da sannu cikin ruwan sanyi sai Kamal ya gane bai da wayo..

Hannunta ta riko.

“Yanzu yana a matsayin mijinki ne,dole ki bishi in dai kina son ki tsira gurin Allah..
Hannun ta zame tare da fad’in

“Toh uztaza,mu bar wannan layin kawai..

Kai Muneeran ta jijjiga, tasan kawarta kam tai nisa, zai wuya taji kira cikin sauki.

Har ya dawo su na nan tare kamin tai musu sallama ta tafi.
Da harara ta bishi bayan ta dawo a rakiya ya bita da kallo,kai ya jijjiga,ya kusa saita tunaninta lalle.
Kimanin sati biyu kenan da tarewar su amma kullum sake 6otsare mishi take da wani salon.

Da dare ya yi zata sakace d’akinta sai dai yai kwanan parlour.

Abinci sai dai ya dafawa kanshi,yau dai ya kudiri aniyar saita wasu abubuwan,dan haka ya ce 
“Ina abinci na?

Sama da kasa ta kalleshi a wulakance tana shafa mai

“Kai da wa?

Ido ya sa mata sam bai da walwala yau,dan haka a tunzure ya shige ciki tuni ta mike tsaye.

“Nai miki hak’urin sati biyu da kawaici ba kya gani koh?
Rai ta had’e da sauri ganin ya karaso tai band’aki da sauri ta datse tare da fad’in

“An fad’a baza’a dafa ba d’in.

Yin duniya taki ta bud’e, karshe 

 kamar kullum yau ma shi ya dafa.
Da daddare ta gama shirin kwanciya kamar kullum ta tashi zata rufe kofa ya danno kai.

Rai ta had’e da sauri had’i da rike k’ugu.

“Lafiya?

Juya wa yai tare da maida kofa ya rufe had’i da cire mukulli ya juyo yana kallonta.
Cike da in ina ta fara fad’in

“Na..na..ce lafiya?

Hannun riga ya fara tattare wa yana murmushin mugunta.

“Ki bari ai zan nuna miki koma meye..

Baya ta fara ja tana had’iye yawu kwat tana raba ido.

Kanta ya yi dan haka da sauri su ka fara ‘yar tsere cikin d’akin, fad’i yake
“Yau zan maganin ki,dan ni kad’ai zan iya miki kin sani,wannan fitsarar yau zata tafi garin su..

“Ba haka mukai da kai ba,bana ciki da mugunta…

Shiru tai ganin ya damko ta da duk karfinshi,tuni ta fara kukuwar kwace wa tana masifa.
“Wannan ai iskanci ne..

“A gunki na gani ai na koya..

Magana zatai yai saurin toshe mata bakin ta hau mutsu-mutsu, tun tanai har tai lakwas,dan haka da sauri ya janye kanshi su na maida numfashi.

Yawun bakin ta tattaro tare da tofarwa tana goge bak’in.
“Mugu kawai…

Murmushin mugunta yai tare da jijjiga kai

“Ke kuma munafuka ba,ai gwara ma ki shanye,tun dama abin neman ki ne ya samu,a kuma yau mai gaba d’ayan zai zo..

Matsa wa tai tare da nuno mishi kofa.

“Ka fitar min a d’aki malam..
“Kin biya kud’i ne da ya zama na naki?

Matso wa ya fara tana ja da baya,sosai yau kam ta gano ketar ce ta motsa,in kuma batai da gaske ba haka zai shata a banza, dan haka da sauri ta dawo sabuwar masifa.

Muje zuwa
SAFHA…..✍🏻

[4/4, 6:50 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©{SAFHA}

SDY JEGAL
FEENAT JAFAR

          &

HAFSA ISMA’IL(MMN HANEEP)

7_ Pillow ta fara hullo mishi tare da d’ane gadon ta tsaya,duk huci suke ganin yadda sukai ta tsere tana zille wa.

“Dama kin bar wahalar da kanki,dan kinji na rantse yau saina seta tunaninkin nan..
“Ka fara saita naka,amma ba dai nawa ba..

Tsalle ta doka da niyar sauka a gadon ganin ya kawo mata raruma ta gurd’e,duk da haka da karfin hali tai hanyar kofa tana cije le6e ya cimmata kamar wasu yara.
Tamkar masu tseren gaske haka suke sauke ajiyar zuciya ya gamata da kofar d’akin.

Ido ta tamke kam ganin yana niyar gama fuskar su ta fara tuttureshi.

“Wane irin mugu ne wai kai?

Murmushi ya yi yana kallon bakin tsiwar.

“Ki tsaya ki amsa da hankali..
“Bana so.. Allah tsare ni ka do6an baki.

Yin duniya ta kasa kwatar kanta,dan haka batai wata-wata ba ta gartsa mishi cizo a hannu iya karfinta da ba shiri ya sauta.

Da dingishi ta nufi hanyar band’aki tana mako mishi harara tare da yarfe hannu jin zugin kafarta. 
Kai ya jijjiga shima yana yarfe inda ta cije shi, yau kam wallahi yaso koya mata darasi amma taci sa’a ba wai dan bazai iya kamota ba ta karfi.

“Gobe in na ce ki min girki ki kiyi ki ga yadda zamu karke dake..
 Harara ta maka mishi ganin yana bud’e kofar zai fita.

Ajiyar zuciya ta saka tare da dafe kirji.

“Mugu kawai,cizo yai rana.

     

****

Kitchen take tana dafa indomie da zata ci, ta tsinkayo muryar Zainab mak’ociyarta dake shigowa gidan wasu lokutta. Falon ta fita suka gaisa ta kar6i y’arta Ihsan tana mata wasa.
“Ya naji gidan shiru, ko maigidan baya nan ne?”.
Yatsine fuska ta fara yi kana ta bata amsa da cewa’ “ya fita, yo ma ko yana gidan me zai k’ullata min ne daya wuce takura”.
Murmushi Zainab ta yi tana mai mamakin halayya irin ta Khadeeja, saboda d’an shigowarda take yi ta fahimci cewa akwai takun sak’a tsakaninta da Kamal.
“Gaskiya Khadeeja ni ko ina hango wautarki a wani 6angaren”.
Kallo ta bita dashi mai alamar tambaya, cikin halin ko in kula ta furta’ “wauta fa kika ce Maman Ihsan?, kamar yaya?”. Ta furta hakan tana mai wasa da kalabarda ke saman kan Ihsan.
“Wauta mana, saboda in ba wauta ba mai sankacecen Miji kamar Kamal har zai yi mai rik’on sakainar kashi, kar ki manta yanda tsadaddin Maza suke wuya a wannan lokacin”.
Dariya ta kece da ita har da ubar k’wallarta, saboda yanda maganar ta bata dariya, wai sankacecen Miji, “Kamal baya gabana, saboda INADA BURIN da ba lallai ne Kamal ya iya cikamin shi ba”.
Bud’ar bakin Zainab za tayi magana kenan ta tsinkayo muryar Kamal taja bakinta ta tsuke, nan ta kar6i Ihsan daga hannunta had’e da furta’ “ni zan wuce sai wani lokaci in kin samu lek’o gidan namu”.
A k’ofar shigowa ne suka ci karo dashi ta rakota, nan ya ra6e ya basu hanya suka fice shi ko ya k’arasa daga ciki.
K’amshin girkin da ta d’ora ne ya ja hankalinshi ya fad’a kitchen d’in. Ganin k’aramar tukunya akai ya bashi tabbacin ko miye take girkawa ba dashi take girka shi ba, kuma gashi ya kwaso yunwa da zafin rana.
Filet ya d’auko ya juye indomie d’in ya d’auka ya shige d’aki har da murd’a key, sai da ya rage kayan jikinshi sannan ya yi zaune ya fara kai loma.
****
Baki ne ta saki saboda hango y’ar k’aramar tukunyar da ta d’ora ajiye a gefe, wanda ke nuna an juyen abincin. Dakin kawai ta tunkara ta murd’a k’ofa ta jita a rufe, ji ta yi tamkar ta kurma ihu saboda tabbacin Kamal ne ya juye mata indomie ya shige d’aki yana ci.
“Wallahi ka bud’e k’ofar ka bani abincina, in ba zalunci ba haka kawai za ka zo ka tararda na yi girkina ka juye, hala ni baiwarka ce, ko kuma an kawo ni gidan ne domin in yima girki?”. Masifa take yi tana bugun k’ofar tamkar za ta 6allata.
Yanda kasan bebe haka ya koma mata, sai da ya cinye abincin tass sannan ya fad’a toilet ya yo wanka ya fito ya kimtsa cikin k’ananan kaya sannan ya bud’e d’akin ya fice.
****
Wata indomie ce take dafawa ta yi tsaye tana gadin abarta sai cizon yatsa take yi tana huci tamkar wata kasa.
Cikin sand’a ya k’arasa kitchen d’in wanda dama ta jiyo k’amshin turarenshi, tana batun juyawa ta balbaleshi da masifa taji ya sagalo hannunwanshi duka biyun ya rik’e k’ugunta had’e da kwantar da kanshi saman kafad’arta.
“Yanzu don kin girkawa mijinki abinci ya ci shine abin masifa, ya kamata fa yarinya ki bada kai bori ya hau, saboda nasan kinyi kewar wannan”.
Yana gama fad’a ya juyo da kanta saitin fuskarshi. Baki ta bud’e da niyyar masifa karaf ya had’e bakinsu guri d’aya yana juya halshenshi cikin bakinta, jin cewa jikinta ya saki gaba d’aya ya sake ta had’e da ja baya, sai gashi ta fad’o mai saman jiki.
“Haba Yarinya, karki cemin d’an wannan abin yasa kin kasa d’aukar kanki, wannan ai shafar mai ne”.
Cikin borin kunya ta fizge jikinta daga gareshi ta yi mai wani mugun kallo, sannan ta juye abincinta ta bankad’eshi ta fice inda ya bita da dariyar k’eta.

Muje zuwa

Daga Alk’alamin (SAFHA)….✍🏻

[4/4, 6:50 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©{SAFHA}

SDY JEGAL
FEENAT JAFAR

          &

HAFSA ISMA’IL(MMN HANEEP).

 

*_Naki ne wannan, our dorling Dota Feedoh,(‘Yar Fichika)..saura 4😹*_
8_”A’a, Aunty amarya ce a gidan namu?

Murmushi tai tana d’aukan Ihsan.

Bayan sun gaisa ta d’au littafin da ta gani bisa kujerar Maman Ihsan na hausa tana duba wa,sosai ta nutsu cikin shi sai murmushi take ita kad’ai.
Kai Maman Ihsan din ta girgiza mata tana murmushi tare da ajiye mata plate din hannunta mai d’auke da ruwa.

“Haba,haba Malam,ki duba irin wannan soyayya da ake shinfid’awa a littafin nan exactly irin wacce nake da *Buri*.
Littafin ta ajiye tare da ta6e baki da marairaice fuska,

“Bana tunanin mugun nan zai iya rabinta,dan har gwara ma gidahuman chan su Aminu dashi…

Shiru tai ganin yadda Maman Ihsan din ta sau baki tana kallonta.
“Na tambaye ki man Deeja?

Kai ta jijjiga halamun tana ji.

“A yadda na fuskanta ke burinki a soyayya ya k’are,ba ruwan ki da sauran burin gidan aure sai wannan koh?

Kai ta daga mata da sauri.
“Sosai kuwa,dan ni fa akan wannan burin nawa bansan adadin samarin da na fatattaka ba,sai gashi yanzu wannan mugun a araha ya sameni sidan..

Ido ta sa mata,

“Amma kuna da alaka da Kamal?

Kai ta girgiza da sauri.
“Bamu da wata alaka sai ta nesa.

Murmushi tai ganin yadda take yatsine fuska.

“Amma zan so jin tarihin ku da yadda wannan auran ya kullu Deeja,kin san har yau mamakin ku nake wallahi.
Baki ta ta6e tare da gyara zama.

“Kamal fa mu karu yake zaune a gidan mu,Abban mu ne ya rike shi tun zamanin yana shekara 10 yazo Kano,Baban shi abokin Abban ne,sai shegen auri sakin bala’i kin san dai mutumin kauye..
“Tare toh su ka taso da yayuna maza dan ni kad’ai ce mace sai yaran riko yanzu gun Mamy.

“Allah ya gani tun tashina jini na bai ta6a gamuwa da shi,gashi shi yafi kowa sanin wani halina da koh a gida basu sani ba,dan fa kusan duk a idonshi ya wakana..
Shiru tai jin ta kwafsa,dan haka cike da halamar tambaya Maman Ihsan ke kallonta,ya ta iya,ta riga da tayi subutar baki.

“Ban sanki ba,sai had’uwar makotaka, haka kawai naji na aminta dake,shi yasa ma ban boye miki zaman mu ba,dan wallahi ni bana sonshi..
Ido Maman Ihsan din ta zaro,

“Toh wa ki ke so?

Ita ma idon ta sa mata,kamin daga bisani ta girgiza kai.

“Ba kowa,abu d’aya na sani shine *INA DA BURI*,burin da har yau ni banga wanda zai iya cika shi ba…
“Dan tsaya dan Allah..

Shiru tai tana kallon Zee din,

“Meye burin naki? Dan Allah ki sanar ni..

Murmushi tayi tare da sake muskutawa.

“Burina nai auren soyayya,irin soyayyar da nake gani a India da littafan soyayya..

“Irin soyayyar da mijina zai ji ina ma ya bani ranshi dan so..

“Irin soyayyar da kullum zan rika jina a sama,ya zamana ni dai d’an soyayya na aura.
Yadda komai ya wakana ta sanar mata har zuwa aurenta da Kamal da yadda aka fasa da Najib.
Ajiyar zuciya tai tare da furzar da iska tana marairaice fuska.

“Sai dai fa ban samu abinda nake son  ba,dan kusan duk samarin da nai kidahumai ne,ba abinda su ka iya sai bud’e hakori,da naga ba haza zan ma kora da hali,in ka ki abu d’aya zanyi wanda koh a hanya ka ganni bani ba kai..
Zama Maman Ihsan ta gyara,

“Wani abu ne wannan? Allah yasa ba abinda nake tunani bane..

Da ido su ka kafe juna,ita kanta tana kunyar tuno da wautar da ta shuka ita da Najib dan kawai bukatar ranta.

Kai ta sunkuyar tana murza yatsa.

“Ina jin ki..
Kasa ta kara yi da kai tare da fad’in

“Soyayyar minti ne muke yi ni da Najib cousin na,wannan ce kawai in nayi nake rabuwa dasu a cikin ruwan sanyi,toh shine,shine fa…

Shiru tai sake yi tana dan sosa keya ganin yadda zee din ta kafeta da ido.
“Ni fa har ga Allah Maman Ihsan ta karya muke yi,amma Kamal da yasha kamamu yaki yarda a hakan,shine kullum sai nasha gori gunshi..

Kasa tai da kanta tana chunno baki.

Ajiyar zuciya Maman Ihsan din tayi.
“Tab,lalle wannan shine kwamachalar..

Kallota ta danyi da halamun tambaya, dan haka sai ta gyara zama.

“Gaskiya kinyi shirme, babba kuwa..

“Sannan ki gode Allah da Kamal din ya taimake ki baki auri Najib ba shi ya aureki..
Kai ta dago da sauri tare da sakar baki,dan haka sai ta kad’a mata kai.

“Kwarai kuwa,koh kina tunanin duk abinda ku ka shuka ba zaki girbe ba a gaba?

Kir ta kafeta da ido,dan haka sai ta cigaba.
“A fa gareki ne abinda ki kai ki ka d’auka a wasa,amma ga samarinki da kuma Allahnki ba wasa bane,dan Najib ba muharamminki bane,koh hannu ya rike miki zunubi ne babba balle azo ga su runguma..
Kai ta sake sunkuyar wa halamun ta gamsu.

“Ita rayuwar nan yanzu da ki ke kallonta wallahi Deeja samari kiris suke jira ki samu tabo,dan fa ko wani saurayin ne yazo a barshi a kin samu dai dai ke,shin bakya tunanin wani yazo ya fad’i halinki wanda a shine silar rabuwar ku?
Shiru tai mata halamun ba gaskiya.

“Dan haka ni a gani na Kamal taimako yai miki da bai barki da Najib ba dan fa a tsakanin ki dashi ba wani sauran mutunci dan ya gama gogar ki da shafar ki a sunan mafita.
Sosai tai mata fad’a, kuma ta gane kuranta har tai istigifari.

Abu d’aya ne bata yarda ba wai Kamal taimako yai mata,abu d’aya ta sani ya taimake ta ne dan ya taimaki kanshi,dan tafi kowa sanin ketar Kamal da bakar muguntar shi.
Sallama sukai ta fito,a bakin kofa ta tararshi ya bake hanya.

Kallon sama da kasa ta mai ta kautar da kai.

“Da izinin wa ki ka fita?

A yatsine ta kalloshi,

“Ji wani karfin hali,toh kai a wa?

Ido ya sa mata,ya ma rasa amsar bata,dan haka kawai sai ya wuce ciki ta bishi da harara.
Sosai ta kunnoshi,dan haka da yaje d’aukan pillow ya tsaya bisa kanta.

“Ya zama rana ta karshe da zaki sake fita ba tare da izini na ba dama..

Kallon tara saura kwata ta fara mishi,a haka ya iya kama kai da iya fad’a, amma a soyayya an baro shi baya…
“Mtsww.. 

Tsaki ta sau mishi tare da mike wa ta zauna.

“Ka fa daina d’aukar kanka a matsayin miji, wallahi darajar Abba kad’ai ke zaunar ni,da kai baka isa ba wallahi..

Kanshi ya nuno da hannu tare da fad’in

“Ni ki ke wa tsaki?

Da sauri ta ce

“Eh din,dan baka isa ba..
Jim yai yana kallonta baki sake.

“Ban isa ba koh?

Cike da tsiwa ta ce

“Sosai,toh kai a wa?

Kai ya jijjiga tare da hulla pillown da ya d’auka ya nufi bakin kofa.

“Yau kwa zan banbance miki tsakanin tsaki da tsakuwa.. 
Zumbur ta mike ganin ya dannawa kofa mukulli ya cire,ido ta waro tuno da artabunsu na ranar chan,tabbas in ta sake ya risketa tasan sai wata ba ita Deeja ba,dan haka da azama ta sakko da niyar shiga band’aki ta kulle ya riko hannunta kam.
“Yau zan nuna miki yadda zaki koyi ladabin dole ga ni mijinki na koh kin so koh kin ki..

“A mafarkinka kenan wannan, amma wallahi baka isa ba..

Shiru tai ganin ya sunkumeta sama ba tare da ta shirya ba duk da gabanta na matukar fad’uwa amma hakan bai hanata surfa tsiwa ba.
A gado ya direta tare da riketa kam yana dubenta ta inda ba yadda za ai ta kwace.

“Sosai ban isa ba,ba har yanzu da guntun bakinki ba?

Kuka ta sau mishi ganin tai duk dabara ta kasa motsi..

“Ka isa wallahi, dan Allah kai hak’uri…
Dariya ya sa tare fara abinda yai niya,ganin da gaske yake yasa ta kara jiniyar kukan nata.

“Ki adana hak’urinki,dan yau sunanki ‘Sorry’…

Cizo ta kai mishi yai saurin kauce wa,dan haka da sauri ta ce

“Mugu kawai,wallahi bana ciki da iskanci…
Kai ya dago tare da fad’in

“Ai iskanci kin barshi a baya,yanzu wannan ita ce sunnar ki mai lada in kin sa niya..

Kukan gaske tasa tare da fara roko ta Allah da annabi tana kiran Mamy.
Kamal kam yau tasan namijin duniya ne,dan tun tana da bakin roko da fitsara har cikin nutsuwa yasa tai ladab da kanta halamun ya zurmata da yawa,sai ga nan su Deeja an sau jiki ana kwasar hot messages,da sannu ya sassauta rokon da yai mata ganin ta bada gari tai surrender.

Ku biyo mu.

{SAFHA}…✍🏾

[4/4, 6:50 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION
©SAFHA
FEENAT JAFAR
SDY JEGAL

        &

HAFSAT(MAMAN HANIF)
*Na gaida mutanen kirki ma’abota sada zumunci, princess Hassy, Autar Hajiya, FIdo sodangi, Sadiya Stylish, Allah yasaka da Alkairi ykr dankon zumunci AMEEN*
9
      Yanayin da ya fuskanci ta shiga ne yasa wani b’angare na zuciyarsa ya soma k’aryata d’ayan sashen dake tunatar dashi k’iyayyar da Deeja ke masa.
Cikin k’warewa da son nuna mata k’warewarsa ya shiga sarrafa Deeja, wacce tunda tayi surrender ta shiga kokawa da zuciyar ta wacce ta soma k’ayatuwa da sak’onnin da Kamal yaso aika mata. Duk yanda taso ta kame kanta don gudun gori irinna Kamal amma ta kasa, a dole ta biye masa don ta kasa sarrafa kanta ji take ma tamkar ba ita bace, a yayin da Kamal ya sabunta mata duniyarta gaba d’aya.
Cikin nishad’i da matuk’ar farin ciki yake jin kansa, Kalmar hamdala ke wanzuwa cikin bakinsa tare da nanata “Ina sonki Khadeeja”. Cikin wannan yanayin mai cike da d’unbun dad’i da farin ciki ya raya darensa, wanda farin cikin ya k’ara armashine a yayin da ya samu tabbacin a iya shan mintin da suke ambata Najib ya tsaya, don haka ya k’ara d’aga darajarta ya kuma k’ara marta bata, wanda ko iya nan ya tsaya ya san baiyi zab’en tumin dare ba.
*Asuba ta gari*
Garin ya waye masa da Alkairi don wata nutsuwa yaji tana shigarsa yanajin tamkar dala da gwauran dutse ya sauke saman kansa.
Tun dawowar sa daga masallaci ya soma jiyo sautin kukanta, nan yayi turus yana kallonta, miliyoyin k’aunarta na k’ara nunkuwa cikin ransa, cikin wannan kukan bacci ya sure ta a daren jiya, gashi yanzu ma dashi ta farka, don haka ya shanye mamakinsa ya k’arasa cikin d’akin ya zauna yana saurarar kukanta wanda yai masa kama dana nadama koma kai tsaye yace na k’iyayya, duk da ya soma k’aryata wannan batun a daren jiya.
Kuka take sharb’a k’wakk’waran motsi ta kasa yi, ci kanki Kamal bai ce mata ba shi bai San dame zaiji ba, da farin ciki daya cika ransa koda rarrashin da yasan ko ya yi ba gwaninta zai mata ba? Koda murnar bata fad’a tarkonda ta shiryawa kanta ba?.
Tayi kukan ya isheta har ta sami sarari a zuciyarta, Allah ya isa kuwa babu kalar wacce batayiwa kanta ba, kuma taji kullacin tana kuka bai rarrasheta ba, bayan yasan tana buk’atar rarrashin yayi biris da ita.
Sai da ya tabbatar ta tsagaita kukanta sannan ya taso ya zauna gefenta tare da kamo hannunta ya shiga murzawa, maimakon yayi rarrashin ko yayi banbaki a’a sai ya jefeta da bak’ar magana.
“Yanzu mun zama d’aya ko? Ya juyo da fuskarta sosai suna fuskantar juna ya shiga zagaye fuskarta da yatsansa yana faman murmushi.
Bai sake tanka mata ba, kuma bai damu da sai ta bud’e idonta data rintse ba. Haka yake kalle fuskarta tare da shafa duk inda yaso a fuskarta k’aunarta na fizgar sa.
Maimakon ya fad’i kalmarda za ta sa mata nutsuwa ko su fallasa mata sirrin zuciyar sa sai ya kuma kunno ta.
“Wai me yasa ba zaki bud’e ido ki kalleni sosai ba, ko kunyata kike ji ne? ni ne fa Kamal wanda ban isaba waye ni da zaki ji kunya ko mamaki kike?.
Hakanan taji tanason kecewa da kuka don takaici da k’uncin da Kamal ya haddasa mata ga bak’ak’en maganganunsa, har wani murmushin mugunta yake mata don dai kawai ya nuna mata yaci moriyar ganga….
Don haka ta daddage k’arfin da ya rage mata ta tureshi tayi wurgi da bargon, aguje ta nufi band’akin tana gurshek’en kuka, ya bita da kallo yana dariya.
Taji dan sanyi data futo daga wankan taga d’akin a gyare hatta kayan baccinta daya dinga watsi dasu ya tsince su d’akin sai k’amshi yake.
Cikin shirin futa aiki ya shigo fuskar sa d’auke da murmushi yake duban ta harda kashe mata ido a yayin da ya matso daf da ita yakamo hannun ta ya manna mata Sumba wacce hatta yan cikin ta saida ya amsa.
Don haka ta nemi nutsuwarta ta rasa kawai sai tayi zaman d’abaro a bakin gado tana maida numfashi to baki ya mutu muruss.
cikin tattausan lafazi ya furta’ “Ina sonki, zanta sonki Khadeeja tun a daren jiya na k’udiri a niyar bautawa soyayyarki, ina so ki nutsu ki kwantar da hankalinki ki bani dama, ni nayi alk’awarin zan jagoranci cikar burin ki”.
Ya d’anyi shuru don saurarar cewarta, tayi shuru don batada abin cewa.
“Ina Neman Alfarma a gunki Deeja ki sanya mafarkina ya zama gaskiya, a daren jiya naga wani abu tare dake me kama da k’wayar sonda nake nema a gunki don Allah karki k’aryata mafarkina”.
Anan ne tasamu damar tofawa, “in dai Abinda nake ji a k’irjina na bana son zama dakai a matsayin miji ba k’iyayya bace to a gaskiya bansan kaina ba”.
Tana kai aya ya amshe, “Haka kika tab’a ganin aurenk’i? Haka kika tab’a ganin amarya bata tab’a yaji ba? Haka kika saba ganin auren k’i amarya da ango a daren farko sun raya daren salim alim tamkar wanda sukai auren soyaiya?, duk tambayarki nake yi haka kika saba gani?”.
Kunya, haushi, takaici duk ya hade mata, koma me zaice mata ita ta bada kanta daya zo da buk’ata ta biye masa har yayi galaba akanta cikin dad’in rai.
Kamar yasan abinda take rayawa a ranta, yace’ “ba kece da zuciyarki ba ba kece da gangar jikinki ba bare in nazo da buk’ata ki bijiremin, amma ko yaya so da k’i suna nuna kansu in an kasance tare”.
A zuci ta raya, yi ka gama cimun fuska kawai ka kauce”.
Siraran hawaye ne ya shiga sirnano mata bai bata damar magana ba yaci gaba.
“Ina sonki kuma zan cigaba da sonki ko yaushe, ki kwantar da hankalinki ki kori duk wata damuwa ki kwanta kiyi bacci mai dad’i a cikinsa kid’an bud’amin waje kad’an a zuciyarki da nuna so na samu na shigo, ta hakanne zamu samarwa iyayenmu farin cikin da suka zata daga garemu”.
Ya kai hannunta leb’ensa ya sunbata cikin gwaninta sannan ya saki hannun yana cewa’ “zan futa amma yinin yau aikin da na baki shine, ki lalubi zuciyarki kiji in akwai guntun sona koda jariri ne don Allah inna dawo ki sanar dani, ni nasan yanda zan raini abina ya girma”.
Wannan yad’an bata nutsuwa ta d’an rage cin magani ta kuma rage hawaye. Sai dai har wannan lokacin baiji furucinta ba.

Ya d’au tsawon lokaci yana zayyano mata bayanin da suke sata jin kunya da kuma jin ba zata yafewa zuciyarta ba, kafin yai mata sallama yabar gidan.

Nan dai ta zauna ta kimtsa kanta sannan ta futo falo, nan ma a gyare yake idon ta ya kai kan canter table wanda ke d’auke da break lafiyayye daya shirya mata, don haka bata tsaya b’ata lokaci ba ta hau ci don wata mahaukaciyar yunwa take ji, taji dad’in roman naman kajin da yayi mata wanda yaji kayan had’i tas ta shanye roman ta bar ragowar naman.
Komawa tai d’aki ta kwanta bayan ta gama break d’in don duk bata jin dad’in jikinta, duk jikinta yayi sanyi ta sawa ranta Kamal ya riga ya gama cutarta dole inya dawo ayita ta k’are.
Cikin wannan zullumin ta yini.
A nasa b’angaren kuwa? Yini yayi cikin nishad’i da begen matarsa don ta shayar dashi mamaki don haka yini yayi yana tunaninta, gangar jikinsa ce a gurin aiki amma hankalinsa na gida, har a gurin aikin abokansa sai da suka fahimci farin cikin da yake ciki, don shi kad’ai yake zuba murmushi a duk sanda ya tuna daren Alfaharinsa. 
Karfe hud’u na yamma ya had’o yanasa yanasa yadawo gida don ya kasa aikin kirki.

Ku biyo mu

SAFHA….✍🏻✍🏻

[4/4, 6:50 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION
©SAFHA
SDY JEGAL
FEENAT JAFAR

         &

MAMAN HANIF
10,

*godiya ta musamman gareku masoyan Ina da buri*
Cikin nishad’i yashigo gidan harda wak’ar gwanin sa Maher Zain a bakin sa yana rerawa hannun sa rik’e da lodoji guda biyu cike suke da kayan kwalam wanda yasan tanaso don ita inhar da kayan kwad’ayi to abinci ma bai dame ta,
Turus yaja ya tsaya don tsantsar mamakin ganin a yanayin daya barta haka yadawo ya sameta, gefe guda Kuma ga akwatina nan guda biyu cike da kaya,
 Saida yakare mata kallo tsaf yagama karantar rikicin data tanadar masa duk batasan yana tsaye yana kallon taba sai cika take tana batsewa ta had’a gumi sharkar idon ta face- face da hawaye, don haka ya dauke wuta ya murtuke fuska don yaga inbaiyi da gaskeba Deeja k’arfin sa zata fi.
Tun dazu take jiran dawowar sa da taji motsin dirar mota zata fara hade fuska tana yatsina tareda kirkiro rashin mutuncin da zata shuka masa harta gaji da jiran sa takoma d’aki ta kwanta bayan tagama fakin din kayan ta don tagama sawa ranta tagama kwana a gidan kamal 
Batai auneba saijin muryar mutum tayi akan yana magana fuska a had’e da cewa” 
Don Allah taimaka kid’an dauki hutun kukan nan kona minti goma ne ki duba kayan nan dana shigo dashi ciki akwai gasasun kifi ki zubomin naci yunwa nakeji, inna ci na kauce Alla bashshi saiki d’ora daga inda kika tsaya”,
A fusace ta taso masa” inna bar kukan sarari na zuci nake don nida hutawa da kuka ina zatan sai ranar da k’asa ta rufe ido na”
Cikin ko inkula yace” babu laifi had’iye kukan da dukkan damuwar taki kije ki zubomin bai kamata ace nikuma taki damuwar ce zata kashe Niba….. ta ina kukan ki ya shafeni da zan nemi abinda zanci na rasa?
A k’ufule tace” kaga malam niduk ba wannan ba jiran ka nake dama kadawo daga Yau nagama zama dakai don wallahi nagaji bazan iya cigaba da rayuwa da mak’iyi naba, Allah wadaran auren had’i da Wanda bai iya soba baisan soba kuma bai iya tarairaya ba saidai yasa k’arfi, to bari kaji a shirye nake dana karbi saki a hannun ka kuma Allah ya isa iddar da ka d’ora min”
Cikin salon shanye mamaki ya zaro ido? ” idda? Wacce idda kuma daga gwaji? Ai tukunnama yarinya wancen na jiyan ae sharar fage ne don haka karki damu kanki, so kuma ai gajen hakuri kikai bakiga komai ba ” 
“Mtssw ” tasaki tsaki, ” Allah ya kiyaye Kamal kayi kad’an ka siffanta kanka cikin wanda zanyiwa kallo irinna so kaikan ka kayi ganganci don kasan ban tab’a sonka ba kuma bazan tab’a son kaba, kullum addua nake Allah ya nunan ranar da zan wayi gari a gidan ubana ba a cikin wannan kurkukun ba”
Cikin yanayin tura haushi yace” dad’in abun dai babu Wanda aka kafe da k’usa a cikin gidan”
Zuwa yanzu kukan ta yakaru, ” Na shiga uku nidai Allah ya hadani da jangwam narasa wa zanyiwa Allah isa da aka dulmiyar min da rayuwa ta aka rushen buri na”!
” au da kinada aikin neman Wanda zakiwa Allah ya isa kika zauna aikin dabazai fishshe kiba?
“Kasake ni Dan girman Allah nakama gaba na kamal kowa yayi abinda zai fishshe shi,” 
“Kanki akeji”,” wlh da ace igiyar kadararran auren nan a hannuna take da tuni nai maka saki d’ari ma inda anayi”
“To dama wazai bawa mahaukaciya rikon igiyar aure?aike da igiya saidai igiyar gugan da Zaki  ja ruwa inna gaji da tab’ararki na maida ke k’auye”
Bak’in ciki ya kulle ta takasa magana, can dai ta Dora gannu aka ta kurma uban ihu” wayyo mamy!!!
“Allah ya tsinewa wanda ya aminta dani matar sace Allah ya isa ban yafe ba”

Cikin d’aurewar fuska ya daka mata wata razananiyar tsawa wacce bata ta’ba zatan ya iya taba, ” yimin shuru!! wawiya kawai wacce batasan ciwon kanta ba, ki tsaya kinutsu kisan mecece rayuwa don wannan kwanyar kan naki ni bansan menene a cikin sa, inataya  Abba jimamin asarar kud’in tarar da yayi akanki don wacce tafuto daga turu ma tunaninta yafi naki tsafta”
“Kuma wannan kashedin da zanmiki yazamo Na farko kuma na k’arshe inna kumajin bakin ki yafurta Kalmar saki ko Allah ya isa saina zubar miki da hak’ora”
Duk da tad’an tsorata da ganin b’acin ransa amma saita maze don batada tsoro.
Cike da tsiwa ta turo baki takama murgud’e shi tana fad’in” babu Wanda ya isa ya fasamjn baki in kuma mutum yasake ya tab’ani ya daki auren sa, aikin banza aikin wof….ae bata k’arashe ba yasa hannu ya gwab’e mata bakin, take tasaki k’ara harda buga tsalle ta dire tana rik’e da bakin” 
Wallah bazan yarda ba Saina rama aiki babu abinda mutum ya iya saicin zali da mugunta abin yayi tsamari harda duka toni a gidan mu ban saba ganin duka ba”
Ya tari numfashin ta” Nina saba kuma in kin isa kifad’i abinda abinda na hanaki fad’a”
Nan takasa magana takama k’unk’uni tayi hanyar band’aki tana kunkuni,” oho dai nafad’a kuma nak’ara kuma wallahi bazan yarda ba saina rama mugu azzalimi”  
Baijita ba sosai don tayi nisa dashi,” naam me kikace? Cikin murgud’a baki tace” saina rama”, ” zoki rama nisainazo ma har inda kike ki rama d’in”
“Ban yafe ba wlh har duniya ta nad’e, aikan yayi wani Abu ta afka ban’dakin ta murza key, ganin yayo kanta a fusace,
Gaban tane ya dinga fad’uwa don tasan jiran ta yake tafuto ba kyaleta yayi ba ga magriba takawo kai ga duhu yan NEPA sun dauke wuta.
Duk tsoro yacika ranta jin shuru babu motsin mutun yasa tayo alwala ta futo don tuni masallaci sun idar da sallah,
Cikin sand’a tafuto tana waige waige batai aune ba sai jitai an damko ta ta baya, nanfa ta kwalla ihu yayi saurin toshe bakin ta,
” meye na tsorata dawowa nayi kirama fa” cikin in ina tasoma” uhm un mefa? Ni aina hak’ura tun d’azu kuma ae ba canai zan rama ba”,
Rik’eta yayi sosai tana k’ok’arin kwacewa”ni ae yanzu nace kirama ko? Baki yarda da Abinda nace miki bako? Shine kika kuma yimin Allah ya isa”,
“Aa nifa ba Allah ya isa nayi ba canai ban yafe ba toma kayi hakuri Dan Allah sakeni nayi sallah tukun wallahi sub’ul da baka nayi, takama dukan bakin ta,

“Oh ni bansan me yake damun wannan bakin ba inaga ungozoma bata gasashi yanda Yakama taba”
“Tom shikenan yi sallar saina gasa miki”
Yana sakin ta batayi wata- wata ba takama sallah, yana tsaye ta idar, yayi zatan tana shafawa mik’ewa zatai aa saita kuma tayar da wata,
“Aa ikon Allah” yafad’a don ganin tanata jero sallah tun yana lissafawa harya b’ace a raka’a ta kusan goma sha biyu ya dakatar da ita da cewa”ke Dakata!!!

Kubiyo mu.

SAFHA

[4/4, 6:51 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©{SAFHA}

SDY JEGAL
FEENAT JAFAR

          &

HAFSA(MMN HANEEP)
     11_Sallamar da sallar tai tare da juyo wa.

“Ya isheki haka..

Ido ta zaro..

“Wa ya fad’a ma sallah na isa? Koh ka manta Nana Aisha cewa tai annabi har kumbura kafafunshi suke dan ibada?

Harara ya sau mata,

“Ji ta agun,kamar wata ta Allah..
Rai ta had’e.

”Mey ka ke nufi?

Banza yai mata tare da komawa ya kwanta ita kuma ta cigaba da jero sallah.

Ganin abin ba na hankali bane yasa ya raja’a a baccinshi.

Juyo wa tai tare da tashi cikin sand’a ta leka shi,ai ta gano take taken shi,anshata jiya,dan haka *Dan ba kara wai haihuwar shege*.

****
Duk yadda yaso ya samu kusanci da ita abin yaci tura,ya yi na Allah,ya yi ba annabi,ya sauke duk wani girmanshi gaban Deeja amma bai jin ya ta6a cin karo da mai taurin kan Deeja,gar da gar take nuna bai isa komai ba,dan haka ba karamin jin haushin kanshi yai ba da har ya iya tona mata sirrin zuciyarshi amma taki amsa.
A ganinshi ya bada kanshi gareta da har ya zamo soko.

Dan haka da bak’inshi ya hau warware cewar shi fa da wasa yake,ta ma daina wani rawar kai.

“Dan fa you’re are not my type..

Baki ta ta6e tare da daga kafad’a

“Daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa,dan soyayyar ka sani kad’ai a baki,amma baka iya ta a aika ce ba..
Murmushi ya yi tare da jijjiga kai kawai ya cigaba da abinda yake,ya sani da tai nisa,nisan da bazata ji kira ba,a ganinshi ta hanya d’aya zasu dai daita da Deeja,dan haka yasa kafar wando d’aya da ita.
Daga ranar ya fara seta kanshi da Deeja,bai sake sakacin sanarta yana sonta ba balle yasa dole ta sau ra’ayinta.

Dan haka yanzu aka dawo takun saka a tsakanin su.

***

Yau gida ya shirya ya ce suje gaisuwa tun bayan tariyarsu.

Sosai tasha fad’a da nasiha gun Mamy da Abba duk zancen d’aya ne,tabi mijinta sau da k’afa, dan haka a cike dam suka dawo gida duk yana hankalce da ita.
Baki a d’ane ta dubenshi ganin ya sakace d’akin tare da zuba mata ido.

“Lafiya kuwa? Kamar wanda ka ke bina bashi irin wannan kallon?

Kai jijjiga tare da murmushin mugunta.

“Bashi kuwa turum,yau kuma zaki sauke shi.
Yawu ta had’iye da sauri ganin ya fara kunce buttons na rigarshi yana murmushin mugunta in yaso mata keta yana karasowa,dan haka tuni ta fara raba ido da tunanin abinyi.

Hanci tai saurin toshe wa tare da k’ak’alo aman karya tana daga mishi hannu.
“Kar ka karaso, amai nake ji..

Tsaye yai tare da sa mata ido,da gudu tai hanyar band’aki tana k’ak’arin aman karya ta barshi baki sake.

Chan dai ta fito tana yatsine fuska,

“Zuciyata ke tashi in kana kusanto ni kamar nai amai..

Galala yake dubanta kamin daga 

“Mey ki ke nufi kenan?
Zama tai a bakin gado tana dan cije le6e..

“Wash Allah cikina,anya kuwa ba ciki gareni ba?

Ido ya zuba mata baki sake ganin zata raina mishi hankali.

“A sati biyu dama ciki yake baiyana ‘yar fama?
Rai ta had’e tare da kalloshi..

“Toh mey ka ke nufi? Karyar ciki zan maka komai? Kasan dai zanfi kowa bak’in cikin ace ina da ciki da kai..

Tsam yai yana tunani,so yake ya gaskanta amma ya kasa,sannan ya kasa karyata ta.
Baki ya ta6e,

“Allah raba lafiya,amma ba shi zai hana ki sauke bashin da ki ka d’auka ba..

Zirif ta mike tare da d’ane wa kan gadon ganin dabararta batai ba.

“Wane irin mugu ne wai kai? Na ce ma ban son ka rika kusanto ni zanyi amai..
Gadon ya d’ane tare da janyo hannunta ta fad’o kusa dashi.

“Karya ki ke yi,kuma wallahi sai kin amsa..

Kokawa suka fara sosai,amma dake ya gama gano lagonta da sannu ta bada kai bori ya hau,komai na lafawa ta hau kukan ya cuceta yai mata keta.
Harara ya sau mata lokacin da ya fito a bayan gida har lokacin tana kuka.

“Ki ma ware yarinya ki amsa da lada in kin sanya niya,ni bana ciki da kinibibin karya.

Jiniyar kukan ta kara yana tayata, dan haka sai ta hau hullo mishi pillow yana mata dariyar keta.
Washegari weekend ta kama,ba kero ba gas,dan haka dole ya d’au flaks dan koh motsi taki yi ta tafi gun mai shayin kwanar gidan da jarka a hannu.

Mai barkwanci ne sosai mai shayin, saurayi ne,amma tuzuru,auren ne bai da wuri ba.
Sosai sukai sabo dan a gunshi yake siyan biredi.

Dariyar keta yai ta mishi wai mey zai da flaks? Hala dan kuturin ya motsa?

Kai ya jijjiga yana murmushi

“Za fa kai auren nan ne,za ka gane komai yanzu koh na fad’a ma ba gane wa za kai ba.
Kai ya jijjiga yana zuba mai tea,har da su kwai ya dawo,Allah ya bashi Deeja sai dai ya gode.
Karfi da yaji ta tsiri mishi laulayin karya kawai dan ta wahalarshi.

Haka zai shiga kitchen ya zage yai mata girki wai wari kitchen din yake,haka zai dafo ya kawo mata.

Sai ya kauce tai ta dariyar keta.
Bawan Allah tun baya yarda har ya yarda da gaske ciki gareta,sai dai iskancin Deejan ya fara over.

Karfe takwas na dare yana zaune ta fito a d’aki tana yatsina fuska.

Da harara ya sau mata tare da d’auke kai yana sauya tasha.
Baki ta turo tare da ja ta tsaya a gefe.

“Ni fa d’an wake nake son ci,shi nake marmari..yanzu.

Kai ya dago tare da zuba mata ido,a gaskiya Deeja bakar muguwa ce,yanzu ya gama wanke-wanke bayan yai mata girki taci ta hantse.
Dan haka cike da hatsala ya ce

“Koh kinfi uwa yata mayya yau baki isa na sake shiga kitchen ba Wallahi kinji na rantse…

Juyo wa tai tare da had’e rai,

“Ba sai ka rantse ba,dan nima d’an cikin nawa d’an waken waje yake so na siyar wa ba naka ba,in ba zaka siyo ba sai na fita da kaina..
Jim yai yana k’are mata kallo,ganin yaki tashi yasa ta sau kukan karya tana buga k’afa,kwafa ya yi tare da tashi ya shiga kitchen ya d’akko flaks.
Harara ya dalla mata tare da d’aukan torchlight ya fita yana jijjiga kai,lalle dole ya d’au mataki dan gano shin cikin gaske ne koh kuwa karya?.

Dariya take harda rike ciki bayan ya fuce,harda y’ar kwallar mugunta.
Gabar ya kalla ya kalli yamma,ya ma rasa ina zai dosa?

Mai shayi ne ya fad’o mishi,dan haka kawai sai ya kad’a kai tare da nufar wajen.

SAFHA…✍🏾

[4/4, 6:51 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©SAFHA.

SADY JEGAL.
FEENAT JA’AFAR

         &

HAFSA(MAMAN HANIF).
    12_Ko da ya iso gurin a cike ya tarar da shi da mutane ‘yan zuwa domin fira wasu dan cika kundunsu da shayi,yayinda wasu ke musu akan ball.

Guri ya samu ya zauna yana saurarensu,har ya tuno lokacin yana single ba wata matsalar cikin gida kamar su mai shayi.
Ganin sun d’an ragu ne ya sa ya tambayi mai shayin inda zai je ya siyo d’anwake a yanzu.

Duk ido suka sa mishi da mamaki,

“Kai zaka ci?

Kai ya girgiza tare da fad’in

“Mai d’aki na ce..

Dariya sosai su ka harda kyakyatawa.
“Shi yasa nake jin dad’in gauranci watarana, in banda haka a wannan tsohon daren a ina zaka samo d’an wake?

Dariya suka sake sanya wa,dan haka tuni ya sake kuluwa iya wuya.

“Hadi,mu munyi nan,dan an kwaso maka aiki..
Hadi dake tattare kaya ya jijjiga kai,

“Yanzu Hadi ace kai ne a matsayin da nake a yanzu mey za kai wa matar ka?

Baki Hadi ya washe yaji anzo gurin,

“Jirani kai dai na gama had’a kayan nan.

Kai ya kad’a.

Nan ya had’a duk wani abin buk’atarshi sannan ya cewa Kamal ya biyoshi.
Yanda kasan rak’umi da akala hakan Kamal ya bishi har suka kai shagonshi.

Bayan ya sauke kayan sannan ya yiwa Kamal nuni da cewa ya zauna,ba musu ya zauna.
“Wato in ne a matsayinka abokina ka ga nan?..

Katifa ya nuna mishi da hannu,dan haka sai ya gyad’a kai.

“Zuwa zanyi na kwanta a nan,in safiya tai 

“Kawai shawara guda zan baka,kayi kwanciyarka anan,in yaso da safe sai na raka ka inda ake siya ka siyo mata,in ta tambayi dalili ka ce mata da kaje layi ka samu a cike,shine kabi sahu sai yanzu yazo k’anka…
Tsam ya yi yana tunanin dabara irinta Hadi wacce shi bai ma yi tunaninta ba,yasan in yai haka toh ba makawa ya toshe wannan bangaren,dan haka ba musu ya yarda.

“Kai Hadi na gode,lalle kasan takan mata.
Dariya ya yi sosai sannan yace

“Yo,ai ba banza naki aure da wuri ba,so nake nai degree a karatun dabiar mata da matsalolin su,ka ga yanzu ma na samo solution na had’i da wata formulan.
Da sauri ya ce

“Allah Hadi?

Pillow ya gyara tare da niyar kwanciya.

“Sosai kuwa,waya gaya maka cewa duk abinda Mata ke so ake yi masu? Ai inn ka biye musu da hakan zaka wahala wallahi, don ina mai tabbatar ma watarana har d’anwaken za tace ba zata iya taunawa ba sai ka tauna ka bata ta had’iye”…
Dariya suka sa harda tafawa,shi dai burinshi wacce ya yi dominta taji jiki,gaba ta gane akwai banbanci.

Hakan kawai yaji shawarar mai shayi ta kwanta mashi a rai, nan ya biye mai suka yi kwanciyarsu.
****
6angaren Deeja kuwa tana ganin cewa har k’arfe 11:00am ba Kamal ba labarinshi hankalinta gaba d’aya ya soma tashi,sai sintiri take yi daga falo zuwa d’an tsakar gidan.
Bata k’ara tsurewa ba sai da taga agogo ya nuna k’arfe 12:00am, nan ta janyo wayarta ta kira wayar Kamal wacce ranar ya kira ta da ita hankalinta a tashe.
K’arar wayar data jiyo d’aki ne ya yi dai-dai da sakin wani nadamammen kuka nata, yi take yi babu k’akk’autawa, duk inda hankalinta yake a tashe yake, ji take yi tamkar ta fita nemanshi.

Tayi da na sanin wannan karyar cikin gashi ta jawo Kamal ya 6ace.
Kukan da take yi,iyakar iyarta,chan ‘yan gida suka fad’o mata,dan haka da sauri ta hau kira.

Kashe wa tai da sauri dan tuno da mey zata ce toh in an tambayeta?
A tsohon dare ta sashi fitar dole ya siyo d’an wake koh mey?

Kuka sosai take,bazata iya ba,tuni  kanta ya fara sara mata, sai dai ita ba wannan ce damuwarta ba, damuwarta d’aya taga ta ina Kamal zai 6ullomata, nashe-nashe kawai take yi a ranta inda abin ya fi tsaya mata a Kamal ya rasu, nan ta sake tsallara kuka tamkar zata tsage mak’oshinta.
Ranar bacci sai 6arawo,bata san lokacinda ya yi awon gaba da ita ba. Kiran sallah ne ya tayarda ita sai wani jiri take gani kanta na mugun sara mata.

Dube ta fara ganin a parlour ma tai kwanan zulumi.
Hawaye ne ya zubo mata ganin kofar a garkame halamun bai shigo ba.

Hannu ta aza bisa kai tare da furta

“Wayyo ni Deeja.

Sai ta sake dasa sabon kuka,ranar har period d’in dole ne yazo da asubar.
Gari nayin sha ta fito dube Kamal kam wayam har karfe takwas.

Gida ta koma tana ta kwata kiran gida amma ta kasa da sauri tana ta katse kiran.

In ka ganta abin tausayi idon nan yai luhu-luhu.

Shin wannan din nadama ce Deeja? Koh kuwa Kauna ce?

SAFHA….✍🏾

[4/4, 6:51 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©SAFHA.

SADY JEGAL.
FEENAT JA’AFAR

         &

HAFSA(MAMAN HANIF).
     13_A zube take bisa kan tiles tayi d’ai d’aya cikin kukanta tamkar an aiko mata Mamy ta mutu,sai kunji kuka take.

Cike da sand’a ya turo kofar yana mai cije hak’ora kamar mai tsoron kar taji.
Galala ya yai ganin yana yin da take ciki,tuni ya fara kunshe dariya ta juyo.

Kukan ta bari tare da zuba mishi ido,kan yai magana har ta zabura tai yo kanshi da gudu ta ruk’unk’umo shi tana kuka.

Dariyar ya bari tare da sauya fuska cike da mamaki,tunaninshi shin mey hakan yake nufi?
Ba dai Deeja ta damu da rashin dawowarshi bane?

Dago kanta yai idonta rintse tana shesshekar kuka da fad’in

“Wallahi na zata wani abu ne ya faru,tunani na koh ka mutu ne…

Rai yai saurin had’e wa jin zancenta tare da maka mata harara.

“Muguwa kawai,in na mutu ai nasan bakki asara.
Ran itama ta had’e tare da kwace jikinta ta hau nad’e taburmar kunya.

“Da wa ya damu da ka mutu koh kai rai? Ka san dai ba damuwata bace,dan tabbas bani da asara.

Kai ya jijjiga tare da ajiye flaks din d’an waken,yasan koh ba komai ai taji jiki.
Wuce wa yai hanyar d’aki yana kunshe dariya,kan ya zata tasha gabanshi.

“Sai ka fad’a min inda ka kwana?

Rai ya had’e tare da dubenta.

“Ina ki ka aike ni?

K’ugu ta rike tare da fad’in

“Kana nufin tun jiya d’an wake ka ke nema?
Kai ya jijjiga da sauri tare da fad’in

“Shine amsar,dan cike na samu layi a gidan,kinga dole nabi sahu sai yau yazo kaina…

Kallon kar ka rainan wayo tai mishi.

“Gidan wace matar ne za’a je a samu d’an wake a wannan daren balle har a samu layi har yau?..
Kai ya ka’rkar da sauri tare da fad’in

“Oooo,ashe kin san ba a inda zan samo d’an wake cikin tsohon daren amma ki ka fidda ni?

Baki ta chunno tare da d’auke kai jin ta kwafsa.

Kai ya jijjiga tare da fad’in

“Good,dan kiyi wa kanki..
D’aki ya shiga ya batta sai masifa take na fad’in toh mey ya cinyeta? Mugu ai dama yasan mey ya had’a, kuma baza’a ci dan waken ba.

Kofa ya turo yana daga mata kafad’a, yasan yai mata d’aya, ba ta inda zata huce takaici,dan haka dariya ya rika dirka kan daga bisani ya bi lafiyar gado dan yasha shayi gun Hadi.
Bayan yaci abinci rana yai wanka ya fuce dan har lokacin da harara kawai take binshi da kwafa,yasan ba yadda zatai dashi sai hak’uri.
Maman Ihsan ce ta shigo jin ya fita da mota.

Cike da tuhuma take kallonta dan har kukanta na duben Kamal tana jiyo wa a tsakar gida.

Koh da ta tambayi ba’asi ba abinda ta 6oye mata.
Kai ta jijjiga,

“Mugun dad’i ne yai miki yawa,amma ki sani kina wasa ne da damarki,zan so kiyi amfani da ita tun kamin ta ku6uce miki,dan miji ba abokin hamayya bane,gashi a karshe ke ya bari da kukan da na sani..

Da sauri ta girgiza mata kai halamun a’a ne.
“Ni ba shi nake wa kuka ba,tsoron duk girman gidan nan yadda ni kad’ai aciki ne kawai ya sani kuka,amma dan tani ya mutu ma man shi ta shafa bani ba…

Murmushi Maman Ihsan din tayi tare da jijjiga kai,bata jin ta ta6a cin karo da mai shegen taurin kan Deeja,amma ta sani Kamal ne kad’ai maganinta,abu d’aya take guje mata yadda take wasa da damarta, dan in auren soyayya ne taga kawarta da mijinta, dan soyayya a titi har ‘love birds’ ace ce musu.
Kai ta jijjiga.

A rayuwa ta sani Deeja abinda ke gaba gareta kawai take duba,amma Insha-Allah wataran zata kai ta gidan k’awarta,tasan daga ranar Deeja sai ta sauke Buri da rayuwar soyayya zallah a gidan Miji.. 
Murmushi tai mata,dan a zahiri koh ita bata yarda cewar Deeja na da ciki ba,dan a d’an zamansu ta fara karantar halinta da tsabar kafiyar ta. 

Zancen tace a bari,dan wai koh sunan Kamal taji yana sa ta kara jin haushin shi.
Sallama tai mata lokacin karfe biyar da wani abu ganin Kamal din ya shigo.

Koma wa yai bayan ya d’akko mata hijab tare da fad’in da bako suke, sai murmushi yake yana jijjiga kai,da kallo ta bishi,tabbas da abinda yake neman had’a mata.
Nurse ne rike da yar akwati dasu abin auna ‘Bp’.

“Bissmillah karaso ciki.

Tsaye ta mike tare da fara raba ido had’i da tattaro yawun bakinta ji ka ke kwat! Ta had’iye. 

Kallota ya yi,a duniya yasan ba abinda ta tsana sama da allura,yasan ta hakan ne kawai zai gane gaskiyar lamari.
“Sannu madam..

Ido a ware take kallon Kamal din gabanta na fad’uwa ta kasa koh amsa sannun Nurse.

“Gata nan dai Ishak,ka ganta nan tun samun cikinta laulayi ta kasa sukuni,yau zazzabi gobe ciwan kai,gashi in ta fara k’ak’arin amai har tausayinta nake ji…
Wani yawun ta sake had’iye wa tana goge zufa tare da sake waro ido.

Lalle ne in baka iya kama barawo ba shi sai ya kamo ka..

Tsayuwa ta gyara ganin yana fito da ruwa na karin ruwa da allurai,da sauri ta fara in ina.
“Malam ni fa lafiya ta kalau wallahi, ba wani zazzabin da nake da amai..

Da sauri Kamal din ya amshe da fad’in

“Rabu da ita Ishak haka take in taga allura,amma mace mai lalurar ciki ai sai da protection,har da ta tetanus ma kai mata..
Lalle kam Kamal ya wuce tunaninta,dan haka gaba dole ta iya bakinta da tukunta,gashi yanzu yai mata back to sender,dan haka da azama ta karyata kanta da kanta.

“Wallahi ni k’arya nake,ni bani da wani ciki,dan haka ba allurar da za’a min da raina da kuma lafiyata..tab,humm.
Kai ta juyar tare da matsawa gefe tana aiko mishi da harara,shi kam bai mamaki ba,dama bai sa a ka ba,amma dan ya taka mata birki yake son sanin gaskiyar lamari,gashi tun kan ai nisa ta karyata kanta,dan haka da sauri ya ce

“Karya take,dan haka baki isa a fita daga gidan nan ba tare da an juna miki ruwa da allurai ba,dan kin san na sani da kullum sai kinyi amai kusan sau goma,koh so ki ke ki yanke jiki ki fad’i ruwan jikin ki ya kare?..
Murmushi Nurse din yai tare da kad’a kai,ya sani da mata akwai tsoron allura,dan haka sai ya ce

“Kiyi hak’uri madam ayi a nutse mu gama,guda uku ce kawai sai ruwa hud’u..
Ido ta zaro tare da bud’e baki,kamin ya sake magana har ta sau kuka,fad’i take ita sam karya take,lafiyarta lau dan haka ba mai kasheta da ranta.

Kanta Kamal din ya nufa batai tsammani ba ya chafko hannunta,

“Ai kinyi kad’an, naki wasa ne,dan fa ba kuka ba koh suma ki ke sai an miki..
“Wayyo Mamy na shiga uku.. Wallahi karya nake maka ka rufa min asiri Kamal,bazan sake ba kaji na rantse..

Kai ya girgiza mata yana mai kunshe dariyarshi dan kar ta gane,a take yai rantsuwa da sai fa an mata,zo ka ga Deeja gwiwa bibbiyu gaban Kamal tana rokon yai mata rai ganin Nurse na zoko ruwan allura.

SAFHA..✍🏾

[4/4, 6:51 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

© SAFHA
SADY JEGAL
FEENAT JA’AFAR

            &

HAFSAT ISMAIL (MMN HANEEF)

_Yan Uwa muna barar addu’arku zuwa ga yaronmu Muneeb, Allah ya bashi lafiya ya d’auke lalura, da sauran dukan musulmai baki d’aya_.

14_A tsaye yake hannu bisa ha6a yana dubenta fuska d’auke da murmushi lokacin da take kunjin kukan ruwan da tana ji tana gani ya matseta aka mamuka mata.

Kuka take harda shessheka,ta yarda Kamal ya wuce tunaninta,dan a fagen mugunta tasan in za ai competition toh ba abinda zai hana yazo 1st position.
Yau tun tana da karfi amma sai da ya nuna mata karfi gun amsar allurar karfi da yaji,Allah ya isa ta fad’eta tafi dubu acikin ranta,dan yanzu har tsoron fidda tsiwarta take a fili, dan tasan sai ya fanshe.
Tana nan har baccin dole ya sureta,in banda ‘yar harara ba abinda take aika mishi sai kuwa kuka,maganin karya kam,wai hallara.
Ido ta bud’e a hankali jin ‘yar hayaniya a kanta,Mamy ce da shi su na dubenta.

Baki ta fara ta6e wa halamun kuka ganin Mamyn.

Karaso wa yai hadda fad’in

“Sannu,kin tashi?

Kuka ta saka,dan haka sai Mamyn ta matso shi kuma ya hau k’ok’arin cire mata ruwan ya fuce.
Da dan tausayi Mamyn ta bita da kallo wanda ke nuna alamar duk ta fara zabgewa, nan kuwa Mamy bata san cewa zabgewar masifa bace da rashin kwanciyar hankali.
Sannu ta yi mata had’e da jefo mata tambayar lokacin Kamal ya dawo rike da kofin ruwa akan faranti 

“Koh dai laulayi ne ke damunki?…

Shiru tai,duk da Kamal din yaji zancen amma sai ya kalleta,da sauri ta girgiza wa Mamyn kai

“A’a ba shi bane..

Dariya Kamal din ya kunshe,a ranshi yana fad’in

”Wuya kenan..
Kai Mamyn ta jijjiga,

“Amma ance harda amai fa Deeja…

“Allah Mamy banda komai ciwo ne kawai, kuma ma naji sauk’i”. 

Kai Mamyn ta kad’a.

“Toh Allah ya kara afuwa.

Baki washe Kamal din ya ce 

“Amin Mamy, ga ruwa.

Ido Deejan ta kulle,koh kad’an bata son kallonshi tunda bazata iya gasa mishi magana ba.
Bayan Mamy ta d’an yi mata nasihar kula da kanta ta tashi Kamal ya rakata ta tafi, sannan ya dawo d’akin yana mai k’unshe dariyar mugunta.

Ido ta bud’e tare da kafeshi dasu.

“Wai mey ka ke nufi dani ne?

Zama ya yi tare da gyara mata filo.

“Abinda ki ke nufi dani My Deejalo.. 

Hannu ya kai gefen kumatunta zai ja tai saurin make hannun.
“Bazan ta6a yafe wa ba tunda ka zalunce ni, macuci kawai azzalumi mara tausayi, ai nasan fiye da hakan ma zaka aikata a kaina,mara tausayi, wallahi sai Allah ya saka min”..

Kuka ta saka,dan haka da sauri ya sha mur.
“Wato har yanzu kina da bakin tsiwa koh?

Banza tai mishi,cuta kam ya riga da ya cuceta,bakin cikinta d’aya kar wata cutar ta sameta tunda lafiyarta kalau.

Tun daga wannan ranar ta fara kama kanta,zai wuya ta tanka mishi sai dai harara daga nesa,dan ba karamin tsorata tai da sharrin Kamal ba da yafi na mata d’anuwa,ta nan kam ya samu sa’ida.

***
A gaban mirror take tana shafa mai had’i da dan harararshi,yayinda shi yake zaune kan gado sai murmushi yake yana shafa ha6a,yau kusan sati biyu tana mishi karyar period take,gashi yau ya kamata tana ruku’u.
“Wato baki daddara da karya ba koh?

Kalloshi tai tare da shan mur.

Shiru tai tare da cigaba da abinda take,dan ba karamin sanyi ake ba ga ta debo wankan da ya zame mata tamkar dole na dare.
Sakko wa yai,shi har ya yi missing tsiwar nan ta kwana biyu da ake mishi yanzu sai harara daga nesa.

Man ya dangwalo yana yana shima yana dan hararar tata.

“Ki sani lissafi za ai,dan wannan sati biyu sai kin ramata a yau…
Baki ta bud’e ganin wani karfin hali ganin ya riko hannunta yana shafa mata mai.

Zumbur ta mike tare da k’ank’ance ido zata fara bala’i ta tuno da karan baya dan haka sai ta matsa tare da fad’in

“Bana so,ka fita kuma harkata…
Tashi yai tare da janyota da d’an karfi ta taho gareshi.

“Karya ne wannan, dan haka kar ma ki wahalar da kanki.

Tureshi tai da sauri tare da matsawa ganin yana neman samo lagonta.

“Wai in ba kai mugunta ba baka jin dad’i ne?
Kai ya daga da sauri yana mai matso wa.

“Ai gunki na koya,koh kin manta?

Baya ta fara ja tana had’iyar yawu.

“Naji, duk da haka wallahi kar ka ta6ani..

Chafka ya kawo mata da sauri ta zille gefe.

Kai ta jijjiga,

“Wato so ki ke mu zama kullum Tom and Jerry koh? Wanda basa jituwa sai sunji jiki koh?
Kai ta kad’a da sauri

“Ai bazan ta6a jituwa da kai ba kasan wannan..

Tsalle ya doka tare da ritsata lungu.

“Nafi son haka,dan yana kara sa minke ladabin dole..

Magana zatai,sai dai kan ta kai ga furtawa ya chafkota,kamar kullum dai yau ma shi yaci nasarar sata lagwas,sanda komai ya lafa kamin ta hau kukan ya cuceta.

SAFHA…✍🏾

[4/4, 6:51 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©SAFHA.

SADY JEGAL.
FEENAT JA’AFAR

         &

HAFSA(MAMAN HANIF).
    15_Harara ya sau mata tare da fad’in

“Saura carry over..

Baki ta saka,kan tai magana ya chafki bakin dan sa mishi sakata,wuya kam tasha ta yau,sanda ta rika rokon ta daina karya dan Allah yai hak’uri tukunna ya kyaleta yana gyad’a kai na mugunta.
Gaskiya ta fara tsoron Kamal,ketakar shi mugun yawa gareta in har ya furta,dan haka tuni ta ajiye makamenta tai surrender, dan komai zata mishi,toh Insha-Allah kanta abin zai kare,dan ita ke jigata.

****
Zaune take bisa gado ta tankwashe kafarta tana dubenshi,da ya kallota sai ta dauke kai tare da ta6e baki.

Link yake sawa na riganshi gaban mirror yana dan mata murmushi, sosai yai kyau cikin fararen kayan halamun zashi sallar juma’a ne.
“Ki fito ki ce ‘Habeebi kai kyau’ kawai ba ki tsaya satar kallona ba..

Sama da kasa ta kalleshi kamar taga kashi tare da ta6e baki.

“Allah sauka min,dan ni dai banga kyau anan ba sam..
Murmushi yai tare da gyad’a kai tare da sanya hula ya tako gaban gadon tare da d’aukan sallaya.

“Kyaji da shi dai,wai gad’a a makabarta,ni na wuce,zamu dawo tare da su Salis.

Baki ta ta6e tare da shirin magana ya dan mako bakin yana harararta.
Da hararar ta bishi har ya fuce hannu bisa baki,a hankali ta ce

“Mugu kawai…

Kai ya leko dashi tare da fad’in

“Mey ki ka ce?

Ido ta waro, ba dai wai yaji ba?
Da sauri ta girgiza kai tare da fad’in

“A dawo lafiya na ce..

Murmushi ya yi tare da kanne mata ido d’aya

“Sai na dawo.

Yake tai mishi, dan haka sai ya tafi yana jijjiga kai,tabbas Deeja tai laushi wajen tsiwa,abu d’aya ne taki ta sauke,ta kuma ki ta kalleshi a matsayin masoyi sai babban makiyinta.

***** 
“Ni dai ina rabaki da wannan dabi’ar ta kafiya wallahi, ace ni na samu kamar mijinki k’awata wallahi babu mai jin kanmu..

Baki ta ta6e tare da gyara zama.

“Kin san Allah Kamal bai d’ad’ani da kasa ba,cuta ce an riga da an cuce ni,duk wata dabara da zai sauwake min nayi amma ban samu mafita ba..
Shiru sukai ganin Kamal din ya shigo koh bud’e kofa basu ji ba.

Da kallo ya bisu halamun kamar yaji zancen su.

Kai ta d’auke tana turo baki,yayin da Muneera ta duk’ar da kai tare da fad’in

“Ina wuni ya Kamal..

Fuska ya sake tare da amsawa yana fad’in ya gida?
D’aki ya shige ya bar Deeja da harara cikin duhu.

Kai Muneeran ta girgiza,

“Ba koh sannu da zuwa,wallahi ki sauya halin ki,ki guji ranar da zai gaji ya auro miki wata,gashi ni neman tsayayye nake na rasa ki fa gode Allah..

Banza tai mata kawai tana tunanin wani abu.
Kira ya mata,dan haka tana chunno baki ta tashi ta nufi d’akin.

Ido ya sa mata,tamkar dabi’a haka wannan shegen chunno bakin ya zame mata wanda yafi tsana shi kam,dan haka cike da shan mur ya harareta.

“Ina abinci na?

Rai ta had’e tare da rike k’ugu tana gunguni.
A ganinta wannan ai gadara ce,a zuciyarta ta ce wai ‘ina abinci na? Toh ban dafa ba..

“Da ke nake.

Juya wa tai tana bubbuga k’afa da kunkuni tai waje,dan haka da kallo kawai ya bita had’i da furzar da iska.
Deeja kam halinta sai ita,da ya toshe nan zata 6ullo ta chan,gaba d’aya ta dagula mishi lissafi da duk wani tanadinshi a gidan aurenshi.

Kai kad’a, gab yake da ya d’au matakin farko dan saita tunaninta..
Da ido ya bita ganin ta shigo rike da faranti a hannu da abinci bisa kanshi har lokacin bakin nan a d’ane.

Sakkowa yai tare da zama,dan haka sai ta kawo da zummar ajiye wa ya damko hannunta.

Kokawar kwacewa ta hau yi tana nishi jin kam ya riketa kawai sai ta sau mishi kuka.
Baki ya saka, tun ma kamin ya kwad’e bakin shine zata mishi 6aci?

“Mey yasa a gaban kowa sai ki nemi nunan ban isa bane Deeja?

Kukan gaske ta fara,tare da fad’in

“Saboda bana sonka ni,sannan ka sani *INA DA BURI* wanda kai ba zaka ta6a iya cika min shi ba,dan haka ka sallameni na samo mai sona..
Ido ya zuba mata rai 6ace,kan daga bisani ya sau mata hannun tare da tashi.

Da sauri ta cigaba da binshi da fad’in

“Koh kashe ni za kayi wallahi sai na fad’i dan dole nake zaune da kai,amma ka ki ka gane..

Waje yai ya batta nan tana kunjin kuka,tabbas Deeja bata sonshi, hasashen zuciyarshi kam yau ya karyata shi.
Da kallo Muneera ta bishi cike da bakin cikin halin kawarta.

Tsaki tai mata tare da zarar jakarta ta fuce itama a gidan,dan haka tuni ta kara jiniyar kukan nata a ganinta ba wanda zai gane inda ta dosa,kowa bai kaunarta.

SAFHA…✍🏾

[4/4, 6:51 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©SAFHA.

SADY JEGAL.
FEENAT JA’AFAR

         &

HAFSA(MAMAN HANIF).
    16_Glass din motar ta kwankwasa ganin ya jingina kanshi a jikin motar,a hankali ya zuge tare da kallonta yana k’ak’alo murmushi.

“Dan Allah kai hak’uri, nasan wataran zata daina.

Murmushi ya yi tare da kad’a kai,da ace Deeja na da hali irin na Muneera tabbas da yaji dad’in aurenshi.
A kance wai aboki na kwafar halin abokinshi toh tabbas Deeja bata kwafa ba,matuka yana son mace marar hargowa da ladabi had’i ga tarbiya.

Ba daban a gabanshi Deeja ta tashi ba, toh tabbas zai ce ba rainon Mamy ba ce.
“Ba komai Muneera,ba dai har kin fito ba?

Kai ta kad’a,

“Eh tafiya zanyi.

Motar ya bud’e mata tare da fad’in

“Shigo toh na sauke ki,dan hanyar gidan zanyi.

Jim tai tare da kad’a kai ta zaga bangaren da ya bud’e mata su na tafe su na tad’in Deejan.
Sai chan dare kusan goma ya shigo,lokacin tana zaune a parlour ta cika ta 6atse.

Koh ta kanta bai bi ba ya shige d’aki bai da walwala shima.

Tun daga ranar ya sauya mata,zai wuya taga fara’ar shi kullum a dunkume, baki ta ta6e,a ganinta wai tafi nono fari.
Kusan wata guda bai shiga sabgarta,iyakarshi da ita ido,in ta ga dama ta bashi abinci yaci,in abin ya motsa ta hana shi,dan haka shiga kitchen bai mishi wahala ya girka yaci ya fuce.
****

Tsam tai a band’aki tana wanka tare da saka kunne ta kofar band’akin jin yana dariya kasa-kasa.

“Oh no dorling, believe me,a satin nan kad’ai kin sanya na zurmada yawa…

Shiru yai halamun saurare,chan taji ya sake wata munafukar dariya cikin wani salo na so tare da fad’in
“I tell you..

Dariya ya sake yi,

“Ok,bari na duba zuwa gobe,Insha-Allah ki share min hanya…

A masife ta bud’e kofar band’akin ta fito tana huci daga ita sai towel.

Ido ya sa mata yana murmushi halamun yana sauraren ta wayar.

“Baby bani minti biyu zan kira..

Dariya ya danyi tare da kashe wayar yaci kunu kamar bashi yanzu yake dariya ba.
“Ni fa wallahi bazan d’au wannan wulakancin ba da rainin hankali,ban hanaka waya da koma wacce shegiyar bace amma ka yi a waje,banda cikin d’akina kuma bisa kan gadona…
Ido ya sa mata ganin wani karfin hali wai *Sadaka da d’an kishiya*.

“Ke a wa toh?

K’ugu ta kama tare da fad’in

“Oho,ni dai na fad’a maka,na daga ma k’afa amma naga abin sai gaba yake sake yi,ban hanaka ba,balle ka ce kishin ka nake,amma kai a waje.
Magana zai yi sai yai shiru tare da duba waya jin sako ya shigo,bud’ewa yai.

A hankali fuskarshi ta washe da murmushi.

Tuni ya sauka a gadon tare da fita yana reply ga text din da ya shigo ya batta nan tsaye.

Da harara ta bishi tare da ta6e baki.
Wannan dabi’a da Kamal ya koyo ta waya da budurwa ba karamin ci mata tuwo a kwarya take ba,tabbas ba kishi take ba,a’a, bakin cikinta d’aya da ita bai rabu da ita ta samo mai sonta da mutuwa a kanta ba kamar yadda taci buri.
Kwafa tai tare da k’arkad’e shimfid’a,dole yau ayita ta kare,sam bazata sa6u ba wai bindiga a ruwa,yau dole ya san yadda zai da ita.

Bargo taja jin an fara ruwa amma yana chan parlour har ta gaji da jiranshi.
Da harara ta bishi tare da d’auke kai,hararar shima ya bita dashi tare da ajiye wayar yana cire kayanshi,wanka ya shige bai bi koh ta kanta ba.

Bargon ta yaye tare da tashi ta d’au wayar ta shiga cikin chart nasun wanda network ya d’auke dole suka hak’ura ya dawo d’aki.
Tsaki taja ganin yadda yake zuba mata kalami tamkar wani na gaske budurwar na aiko mishi da kiss,maganar turo magabata yake network din ya d’auke.

Wayar ta ajiye jin zai fito tana aika mishi harara.

Jiki ya goge da towel yana yar waka irinta masoya.
“Bari kaji da wai,wannan ba shi zai sauya min Buri ba,wallahi in kaso ka auro hud’u amma in na fuce,dan fa dole ka sallameni nima na samo nawa masoyin..

Towel din ya ajiye yana jinta tare da fesa body spray yana murmushi.
Juyo wa yai daga shi sai wandon ball iya gwiwa tare da hayo wa gadon yana kallonta wani iri.

Bargo yaja yai mata banza,dan haka tuni ta kara kulewa ta hau bala’i wanda ya jima baijishi ba.
Tashi yai tare da zama ya jingina pillow ya sata a gaba kamar TV.

Bakin ya kalla sam koh coma batai balle ta sanya full stop a masifar duk rabi akan sai fa ya sallameta itama ta samo saurayinta mai sonta.
Bak’in yai saurin toshe wa da nashi tare da janyota gareshi ya kashe maganar.

Yau kam a gaske ya tura ta bango,dan haka dakyar ya saito da tuaninta ta sauke taurin kai tare bin ra’ayin zuciyarta kamin tai surrender.
Yafi kowa sanin alkibilar da Deeja dosa,dan haka cikin ruwan sanyi yake kashe bakin tsanyar.

Kuka take mishi tsakaninta da Allah bayan komai ya lafa, kam ya riketa yaki sakarta, dan haka cikin sassanyar iskar daminar had’i da sanyin ruwan dake busowa bacci yai awun gaba da ita a haka tana mitar ya cuceta.
Kai ya girgiza yana murmushi, bai jin zai iya rabuwa da Deeja duk rintsi kuwa,amma hakan bazai hana ya samu saukin rayuwa ba,dan haka ya riga da ya gama shawarar abin yi duk kuwa da yasan zai sa Deejan a tsaka mai wuya.
Dan haka akanta bazai hana zuciyarshi abinda tai niya ba koh da kuwa gangar jikinshi bata so.

Bakin yaja kad’an tare da fad’in

“Ni da ke ai takalmin kaza ne,in an mutu sai a raba, ki shirya kar6an haka.
Bargo yaja musu tare da gyara kwanciya yana jin saukar ajiyar zuciyarta.

Kai ya girgiza, a kullum ana kirarin ba’a sonshi amma hakan bai ki a lafe mishi jiki ba koh da kuwa ya sauta, matuka yana mamakin kalar rigima irinta Deejan shi.
Hannu ya kai tare da dungure mata kai a hankali yana dariya,cikin baccin ta chunno baki tare da dan motsa wa, kai ya kad’a, yanzu ya yarda a jininta abin yake.

SAFHA…✍🏾

[4/4, 6:51 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

©SAFHA
SADY JEGAL
FEENAT JA’AFAR

             &

HAFSAT ISMAIL (MMN HANEEF)

17_Jiki ya zare a hankali jin ana kiran sallah sai kwa warai! Ta bud’e ido tare da sauke shi bisa kanshi ciri da tuhuma.

Yake yai mata,dan haka tuni ta sau kuka tana tatta6e baki kamar na shagwa6a66un yara tana shusshura k’afa wanda ya sanya shi sauka da sauri yana dariyar keta ya shige band’aki ganin ta rarumo pillow.
Lalle kam Deeja ta iya salo na nad’e taburmar kunya,yanzun zata nutsu ta amshi messages daga baya ta hau mishi bori,sai dai yau yasan sai ya toshe kunne dan mita, dan dama shi din mai laifi ne.

****
Soyayya tsantsa Kamal ke zubawa da budurwarshi wacce yake nuna ma Deeja yadda yake sonta tamkar ranshi. 

Ya daina waya da ita a d’aki, koh ta kira koh shi ya kira sai ya fita parlour dan gudun masifar Deeja.
Sam ita ba wayarshi ba ce take bata haushi sama da yadda yaki zuciya ya sallameta.
Kwance yake saman kujera yana waya yana murmushi wanda daka nufo gunshi zaka fahimci tsabar walwala kwance a fuskarshi.

A kanshi ta tsaya rike da k’ugu tana hura hanci.
Ido ya sa mata tare da fad’in

“Bari zan kira ki..

Harara ya sau mata tare da kashe wayar saboda gudun kar ta kwafsa mashi. 

Tashi yai tare da zama yana latsa waya tare da fad’in

“Ya aka yi?
Baki ta ta6e tare da fad’in

“Ina zancen mu ya kwana? Dan kasan Allah? Toh na gaji.

Kai ta d’auke tana jijjiga rike da k’ugu.

Murmushi yai tare da jingina da kujerar yana kallonta.

“Toh ya ki ke so ayi?

A fusace ta ce

“Ka sallame ni kawai..

Ido ya sa mata hannu bisa ha6a.
“Shine matsalar?

Kai ta jijjiga da sauri

“Kwarai kuwa.

“Toh bazan sallama ba,sai mey kuma?

A zabure ta sau kugun tare da fad’in

“Ai kwa yau baka isa ba,dan bazan ta6a zama naga shirmen auren nan naka ba,bayan na tafi ka auro dubu chan ta matse ka bani ba.
Murmushi ya yi tare girgizaKai.

“D’aya ma ta ishe ni rayuwa, amma dole ki zama ‘yar kallo,dan fa bazan saki ba,aure kuma ba fashi.

Daga hakan ya tashi yana latsar waya ya barta gurin tsaye tana huci tamkar namijin zaki.

***
Bayan kwana biyu abubuwa sun k’ara jagulewa tsakanin Kamal da Deeja, kowa ya fita sabgar wani sai dai Deeja na da bak’in cikin abinda Kamal ke yi mata wanda take ganin tsabar mugunta ce. 
Da shirinshi ya fito na fita office ta tareshi tana masifar sai fa ya sallameta,dan jiya har tai bacci tana jiyo sautin dariyarshi.

“Kar ki 6atamin rai don Allah, saboda ina so na fita cikin farin ciki da annuri fuska na min walwali dan so nake in fara tozali da sahibata, Ok?…
Baki ta saka tana kallonshi,dan haka sai ya ware mata yatsunshi biyu tare da karkatar da kai ya ce

“Bye-bye..

Daga hakan ya ra6a ta gefenta ya fice daga gidan yana dariyar mugunta.
Wani irin bak’in ciki ne ya k’ara rufeta wanda yasa ta kai zaune bata shirya ba ta sau kuka.

Ba dan tuno da zancen Abba da yau ta tafka rashin mutunci tai gida.
Gidan Maman Ihsan ta shiga,ita kad’ai take ganin zata iya fad’i ma kukanta, duk da koh shawarar ta bata ba lalle ta dauka ba.

Ajiyar zuciya Maman Ihsan din tayi bayan ta gama saurarenta.
“Wannan ranar nake guje miki a kullum Deeja,sai dai ke abinda ke gaba gareki kawai ki ke yi,yanzu ne zaki rintse ido,dan fa zaki ga abu iri-iri.
Baki ta ta6e 

“Ni fa ba kishi nake ba,burina kawai ya sallameni.

Ido ta sa mata,ta ma rasa mey zata fad’a mata,dan haka ido kawai ta sa mata karshe dai da fad’a suka rabu.
Yinin ranar ko abinda zata ci bata tashi ta nema ba har Kamal ya dawo daga gurin aiki tana kunci.

Da sallama ya shigo yana yar waka,dan haka da harara ta bishi,daga shi har sallamar ta watsar su gefe.
D’aki ya shiga ya rage kayan jikinshi sannan ya fad’a kitchen saboda ganin gurin cin abinci wayam alamar bata girka ba yau.

Girkinshi yake yi hankali kwance yana waya had’e da murmushi cikin aminci rike da serving spoon.
Kwafa tayi tare da kunna tv amma har lokacin tana tsintar firarshi hankali kwance cikin ‘husky voice’.

“Kinga ai dole na shiga kitchen na girka tunda bani da mai yi min, sai dai nasan cewa daga ranar da kika shigo gidan nan ko spoon ba zan k’ara rik’ewa ba ballantana shiga kitchen girki”…
Dariya ya danyi tare da fad’in

“Of course dorling.

Dariya ya kyalkyale da ita,dan haka da sauri ta makawa kitchen din harara.

Tashi tai tare da isa kitchen d’in ta bud’e fridge ya dan juyo like da waya a kunne.
Harara ta sau mishi tare da tsiyaya ruwa a cup,dan haka sai ya juya tare da kok’arin juya abincin shi yana fad’in
“You know, when we’re together I can truly be myself, and that makes all the difference….

Kinsan dalili?

Ruwan take kur6a tare da kasa kunne tana kwankwada.
Jim yai tare da yin y’ar dariya halamun saurare tare da fad’in “Eh man,cos you’re are the girl of my dream,and I love yo..

Ruwan ta sauke tare da fara tari halamun ta kware jin wannan kalmomi.
Wayar ya cire a kunne tare da juyo wa yana kallonta, baki ta chunno tare da rufe fridge din da dan karfi taja tsaki ta fuce.

Wayarshi ya cigaba da yi ya batta da sintiri daga d’aki zuwa parlour.
Hakan ya gama ya tu6e ya shiga wanka, inda hankalin Deeja ya gaza kwanciya,yau dole ta takawa shegiyar nan birki domin taji ita ta kira,dan haka ta tashi ta d’auki wayar tare da duba last call nashi ta duba.
Cikin sauri ta d’auko wayarta tana kwashe lambar tana sakawa a tata wayar da niyyar kiran kowace ta ci mata zarafi,su kare a waje amma banda cikin gidanta.
Tana saka lambar tana ganin sunan Muneerat na appearing, idonta ta fara murzawa sannan ta k’ara duba lambar tana k’ara sakawa, again Muneerat ta gani. 

Wani irin uban ihu ta kurma wanda ya fitar da Kamal daga toilet d’aure da towel a k’ugunshi yana fad’in

“Lafiya?

SAFHA…✍🏻

[4/4, 6:51 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

©SAFHA
SADY JEGAL
FEENAT JA’AFAR

            &

HAFSAT ISMAIL (MMN HANEEF)

( _Muna mik’a sak’on godiya gareku masoya littafin *INA DA BURI*, sak’onku na zuwa muna a kowane lokaci, mun gode Allah yabar k’auna, SAFHA na gaida Ku all👌🏾_)

18_Ganin wayarshi a hannunta ne yasa ya karasa tare da warce wa ganin tana digar da kwalla tare da kallon wayar.

Ido ta dago tare da kallonshi,da sauri ta ce

“Munafuki,mayaudari, maha’inci, azzalumi kawai…
Ido ya waro tare da bud’e baki.

“Yanzu ace duk duniyar nan ka rasa wa zaka aura sai makusanciyata? K’awata?

Shiru yai nashi ido,dan haka sai ta cigaba.
“Lallai na ya yarda da d’a namiji munafuki ne.

Ita kuma munafukar ashe shi yasa kwana biyu ta d’auke k’afa 6at! Da zuwa ashe cin amana ake kulluamin..Toh wallahi sai ta gane shayi ruwa ne dan ub..
“Ke! Maintain wallahi..

A zabure ta ce 

“Bazan yi ba,munafuki kawai algungumi.. Toh yau dubunka ta cika..

Rai ya had’e

“Kar fa ki nemi rainan hankali, dan ina da right na neman matar da ta dace da rayuwata,na duba kaf banga kamar Muneera ba…
“Karya ne wallahi, dan kuwa baya kaci ba gaba ba,da har ka kare a wacce nafi kyau da fasali,shegiya mummuna kawai..

Dariya yasa harda kyakkyatawa

“Eh a haka nake son abata tamkar na zauce.
“Kuma ke ki ka gano muninta,amma ni a gareni she’s gorgeous,dan banga amfanin kyaun d’an micijiji ba,kyau ba kyan hali..

Ido ta sa mishi,

“Ka fito ka ce bani da kyaun hali kawai,amma haka ai ka gagara sallamata dan naci,yanzun ma ba zama zanyi ba,wallahi gidan mu zani..
Kayanta ta shiga had’awa tana mai zubarda hawaye tamkar famfo tana surfawa Muneerat tofin Allah tsine.

Kaya yai saurin zirawa ganin da gaske take tafiya zatai.

“Kar ki fita daga gidan nan..

“Sai na fita,in yaso ka jika gidan ka kora da ruwa,amma sai na tafi,daga baya ka biyoni da takkada ta..
Yin duniya taki ta tsaya dan haka sai ya kullo gidan ganin ta tari Napep ta hau yabi bayanta.

Kuka reras ya tarar tana yi tare da tsarawa Mamy abinda ya faru, ga chan mey Napep a waje sai masifa yake ba’a biyashi ba.

Koma wa yai tare da sallamarshi ya dawo gidan.
Waje ya samu ya zauna tare da gaida Mamyn ta amsa.

Magana zai yi Mamyn ta ce yai shiru tana zuwa.

Sama tayi d’akin Abba,dan haka sai yai kwafa.
“Lalle kin kawo kuka gidan mutuwa,dan kin san da kowa ya gaji da halin ki a gidan nan ni kadai nake iya maleji da ke..

Harara ta kwad’a mishi ido yai jajur,kamin tai magana sai ga nan Mamy ta sakko.
Iya had’e rai Mamy tayi har ta tsorata da ganin yanayin nata,dole ta kara jiniyar kukan nata ganin dakyar ta samu nasara.

“Ki tashi bakin ki alekum ki 6ace min da gani,ki kuma tabbatar da d’akin mijinki ki ka koma in dai kin yarda ni din ni na haifeki..
Gwiwa biyu ta zube halamun roko.

“Mamy k’awata fa zai auro..

Da sauri ta ce

“Koh ‘yar uwar ki ce sai kin koma,ka min dai dai wallahi Kamal,ki kuma ji da wai ni na goya mishi baya ya auro ta..
Kukan ta bari tare da kallo Mamy baki sake.

“Mamy kina sona kuwa?

Kai ta girgiza

“Bana sonki,dan kin san ni bana shiri da mai shegen taurin kai,kowa yasan irin zaman da ki ke a cikin gidan ai mun zuba miki ido.
Sabon kuka ta saka ganin Abba na sakkowa, tasan dole karan nan ya goya mata baya.

Zama yai kawai yana mai sauraren kukan nata,sai da ta tsagaita ya ce

“Ya mukai da ke lokacin tariyarki? 
Shiru tai tana jan zuciya.

“Toh har yanzu sharad’ina na nan,in har ki ka kaso aurenki wallahi Khadija bani ba ke,zance na karshe kenan,ruwan ki kibi mijinki koh kisan inda dare ya miki..

Rigarshi ya k’arkad’e tare da fita ya batta da kukan kiran Abba.
Haka tana ji tana gani ta koma dan yadda ran Abba ya 6aci tsaf tasan zai sallamata,dan haka dole tazo tai yakin ita kad’ai.

Ba shiri ya fita dan yadda take sauke mishi ruwan bala’i cikin kuka,shi har tausayi ma ta fara bashi,amma fa ba shi zai hana abinda yai niya ba.

****
“A gaskiya ki sauya tsari Deeja,ina fa jiyo muryar ki sama da ta mijinki kuna ka ce na ce wannan sam ba halin kwarai bane,wallahi zaki sha wuya randa zai gaji da halinki ya auro wata..
Hawaye ta goge,hamuryarta ta dashe dan kukan da tasha daga safe zuwa daren yau.

Zama ta gyara tare fad’in

“Na nawa kuma…

Da rashin fahimta ta kallota,

“Ban gane ba?
Wani hawayen ne ya sake zilalowa,dan haka murya na rawa ta fara magana.

“Aure zaiyi,amma wallahi karyar kuturu tai kadan balle ta makaho,yaje gida ya kalamence su,yau naga warewar launi ta fata,ni Deeja kowa ya tsane ni,a ciki harda k’awata aminiya..
Kuka ta sa,dan haka baki sake take kallonta dan bata fahimci inda ta dosa ba.

Shin kishi take da auren koh mey?

Koh kuwa ta fara son Kamal har kishi yasa ta fara hauka haka da surutai?

SAFHA…..✍🏻

[4/4, 6:51 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©SAFHA.

SADY JEGAL.
FEENAT JA’AFAR

         &

HAFSA(MAMAN HANIF).
19_ “Ban fa gane inda ki ka nufa ba?

Yadda abin yake ta sanarta,dan haka baki kawai ta saka tana kallonta,tasan makamancin haka zai iya faruwa da Deeja,amma koh ita taji shocked da taji k’awarta yake nema.
Ido ta rintse tare da matso kwallar dake idonta ta zubo kuncinta,dan haka tuni sai ta fara bata tausayi.

“Tabbas anci amana ta,Insha-Allah kuma Muneera sai taga karshen cin amana,dan zata gwammaci da kid’a gwara karatu,mu zuba ni koh su..
Harara ta sau mata.

“Ki ajiye cika baki yanzu ki hau gyaran dabi’unki,sauran abin ki tsimayeni gobe zan zo dan yanzu Abban Ihsan zai dawo,dabara ta rage gare ki,walau ki sauya hali koh yanzu ki ka fara ganin tasku.

Tashi tai ta tafi tana mata sai da safe,da kallo kawai ta bita hawaye na zuba.
Tabbas bata son Kamal,amma wani tokararren d’aci ke tokare makoshinta mud’in ta tuno da zai aure,auren ma da Muneera.

Kai ta gyad’a, dan haka sai ta bi zancen Maman Ihsan na dabara ta rage nata,dan haka hawaye ta goge tare da fad’awa wanka dan wanke hawayen.
Da sand’a ya shigo gidan har wata fad’uwar gaba yake dan tuna da bala’in da ya fita ya batta tana yi bai san da wacce zata tare shi ba.

Kai ta dago jin bud’e kofar ta zuba mishi ido,dan haka da sauri ya sha mur tare da d’auke kai ya shige d’aki yana furzar da iska.
Har ya fito a wanka bata shigo ba,ganin yaci abinci kawai sai yabi lafiyar gado tare da d’akko waya tare da fara dailing ta shigo da sauri ya sauya maganar zuwa ta soyayya har wani lumlumshe ido yake.
Baki ta ta6e tare da yin wajen kamar mai shirin kwanciya ta warce wayar ta zuba waje da gudu.

Biyota yai lokacin tana surfa bala’i.
“Shegiya wacce ta rasa mashinshini a gari ai dole ki koma kwatar mazan jama’a, karya kawai shasha maciji da baka ramin k’anka sai na wasu,toh wallahi baki isa ba dan kinyi kad’an.. 

Baya tai ganin ya taho,dan haka sai ya tsaya tare da fad’in
”Ki bani wayata..

Da sauri ta ce

“Bazan bayar ba din,wallahi sai na ci ubanta tukunna..

“Auxubillah… Ke fa ina ga notin kanki ya since?..
Kai ta gyad’a tare da yin bayan kujera.

“Ai kasan daga turu na fito.. Ke kuma bari kiji,in har kin cika Muneera ki yarda mu had’a ido dake,wallahi sai na lahira ya fiki kwanciyar hankali, karya ka…

Ritsata yai a bayan kujerar tare da kai ma wayar chafka ta rike kam.
“Ki ban wayata..

“Wallahi bazan bayarba.. 

Hannunta d’ayan ya murd’e marar wayar,dan haka batai wata-wata ba ta dakarkare ta makata wayar da kasa tana huci.

Da ido yabi wayar,kan da sauri ya cikata ya nufin gun wayar da tai filla-filla ya hau tattare wa.
Kai ya dago yana muzurai.

“Ni ki ka fasawa waya?

Zani ta tattare tare da chunno baki.

“Eh din na fasa,a gaba ka sake hawa gadona kana waya da wata she..

Na kare taci ganin ya yo kanta,ganin kan ta isa d’aki zai iya cinmata yasa suka hau zagaye parlourn da gudu har lokacin bakinta bai mutu.
Huci suke gaba d’aya na gajiya su na kallon juna had’i da maida numfashin gajiyar da sukai na tsere amma ya kasa kamata.

“Ai dama na fad’a maka duk ranar da zaka sake min waya da wata ‘yar katuwa a d’aki zan d’au mataki..

“Ba dai ni ki ka fasa wa waya ba? 
K’ugu ta rike tare chunno baki,dan haka sai ya jijjiga kai.

“Wannan ba zai sauya komai ba daga kaunata da Muneera ba ki san wannan.

“Oho dai,waya ce kuma na fasa..

Hannu ta tafa harda su murgud’a baki tana fari da ido irin na sarakan iya tsiwa.
Tsalle d’aya ya buga ya isa ga bayan kujera dan haka da sauri ta zille ta nufi d’aki tana ihun wayyo Mamy a taimaketa ganin ya biyo ta da gudu.

Bayan gida ta shige tare da kok’arin rufe wa ya danno kai tare da sa sakata.
Baya tai chan jikin shower ta kulle tare da marairace fuska ganin yana tattare hannun rigarshi,dan haka cike da marairaita ta hau fad’in
“Dan Allah kai hak’uri na tuba.

Murmushin mugunta yai yana matsowa.

“Ba ni ki ka fasawa waya ba?

Kai ta girgiza da sauri tana sake makuruwa jikin bangon har yai mata dabaibayi,dan haka da sauri ta rintse ido kawai ta sadakar jibgarta ma zaiyi.
Dan haka bakinta kad’ai ke furta

“Na tuba..

Ido damk’e kam.

Ido ya zuba mata,sai shegiyar tsiwa ga iya tsoro kuma,bakin ya kalla,yau kam karya take tace mishi wannan ba kishin shi bane kwance fuskarta yake gani har kawo ga fasa waya.
Kai ya daga ganin shower kawai ya murd’a ta zubo kanta bata zata ba,dan haka jin sanyin ruwan da sauri ta zabura ta kankamoshi tana jan zuciya.

Dan kwali ya fara zamewa,dan haka sai ta dago kai tana dan ta6e baki kamar zata sau kuka.
Hannu ya kai bisa bak’inshi tare da fad’in

“Shhhh..

Halamun ta rufe mishi baki.

Kukan ta had’iye tare da turo baki gaba,da sannu cikin iya sarrafa fitinar Deeja abin ya wuce ga wankan gaske,da zatai magana zai sa hannu a baki halamun tai shiru,ranar taga salon da bata ta6a tunanin Kamal zai iya shi ba,har Allah-Allah take su dauwama a hakan.
Zo ka ga wai yau su Deeja ne da kunya,sai sissinke kai take kasa-kasa,yau d’aya yasa ta fara tunanin sauya Buri, sosai ta yarda da Kamal namijin duniya ne.

Dago da kai tayi lokacin da yake goge jikinshi jikin mirror,kai tai kasa dashi ganin ya hararota kad’an.
Kirar karfafan maza gareshi,irin dai kirar da take bida dan taki jinin sokon namiji mai kirar mata jiki a sake.

Kai zata iya fad’in yana da duk wasu qualities da su Aminu su ka rasa a baya illa abu d’aya..

Jim tayi, dan a yau ta karyata abu d’ayan nan,dan yanzu kad’ai taga gundarin salon so gun Kamal wanda har yasata taji kunya.
Baki ta chunno gaba tuno da yadda yake zuba ma Muneera kalam na tsantsar so da kauna,a ganinta ita ya dace yai ma,ita ta chanchanci jinsu ba wata chan Muneera ba..
Ido ta k’arkad’e tare da d’auke kai a kallonshi ta tur6une fuska tare da fad’in

“Deeja dawo hankalinki ki saita tunanin ki..

“Ya akai Deeja dorling? Uwar gida sarautar mata..

Fuska ta yamutse tamkar taji abin ki.

Wai uwar gida? How boring..
Dan haka harara ta sau mishi tare da kulewa cikin bargo.

Kai ya girgiza, lalle yaro man kaza,da sannu ya fara saita tunanin kwanyar Deeja.

Kai ya rausayar tare da fad’in

”Hooo ni Kamalu..Ni kad’ai ma gayya ce guda.

A hankali.

SAFHA…✍🏾

[4/4, 6:51 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©SAFHA.

SADY JEGAL.
FEENAT JA’AFAR

         &

HAFSA(MAMAN HANIF).
20_Washegari Maman Ihsan ta shigo jin Kamal din bai fita ba tasan yau week end.

Su na zaune Kamal din ya fito zai tafi.

Bayan sun gaisa zai wuce ta zunguri Deejan dan haka da sauri tabi bayanshi dan tambayarshi fita kamar yadda ta ce tayi.
A dan zaman su sosai ya fuskanci Maman Ihsan mai son zaman lafiyar su ne,dan haka yake maraba da zuwanta a kullum.

Gyale kawai ta d’auka su ka fuce tare da tarar Napep.
A wani kofar gida suka tsaya tare da sallamar mai Napep.

“Ina muka zo?

Hannunta ta kamo,

“Ke dai muje kar ki ce komai..

Ciki su ka shige, sai kwa akai sa’a mijin na gidan,dan haka tun tsoma kafarsu su ka fara jiyo hayaniya halamun gidan ba lafiya.
“Kullum magana d’aya zanyi ki rika daga min murya tamkar wani d’anki,ba ta yadda za ai muyi sati ba tare da makota sun jiyo ba,

na fa gaji da halinki, gab nake da na d’au mataki..

“Ni kuma na gaji da kai,dan a kullum baka kaunar zaman lafiya,abu kad’an zaka fara mita kamar wani tsoho akan abinda bai kai ya kawo ba..
“Ba zaki daina min ihu?

“Eh bazan daina ba,wani irin zama ne wannan, ni wallahi na gaji..

Maman Ihsan ta kallo ido ware.

“Koh dai mu koma?

Kai ta girgiza mata,

“Ai dan wannan na kawo ki,na gode Allah da muka tarar da haka,dashi zan baki darasin farko..
Shiru sukai ganin mai gidan ya fito a fusace yana huci amma duk da haka matar ta biyo shi tana fad’in

“Kai ne kaddara wallahi ba aure na ba,samari nawa na ture na aureka? Kuma wallahi ni ba marar kunya ba…
Shiru tai ganin su Deeja na kallota,koh ta kansu bai bi ba ya fuce dan fa ta kunno shi.

Yawu Deejan ta had’iye tana waro ido, sam bata ji dad’i ba,ashe haka fad’a da namiji yake bai da dad’in ji balle gani?

Wayancewa matar gidan tayi had’i da sosa keya cike da kunya.

“Bissmillahn ku..
Yak’e Maman Ihsan din tayi tare da fad’in

“Sannu Ummi..

Tasan gatse tai mata,dan haka sai tai shiru.

“Har yanzu kuna nan da hali koh?

Kuka ta sa ma Maman Ihsan din bayan sun zauna.
“Wallahi na gaji da auren nan,aure koh na kiyayya albarka, kullum rashin jituwa muke tamkar wasu makiyan juna?

“Yanzu wa ye zai ta6a cewa Abbakar ya ta6a nuna min so a baya?

Kai ta girgiza.
“Babu,auren mu yafi kama da wacce aka lika mishi ni dan dole,dan haka na gaji,na gaji Zainab..

Murmushi tai tare da jijjiga kai.

“Ni dai har kullum ina mamakin ina dumbin wannan soyayyar da aka gina a baya taje? Ina wannan tattalin da mutunta juna yaje kamin ayi auren?

Kiyi wa kanki fad’a, shima yai kanshi ku gyara aurenku,dan kun fara tara iyali.
Shiru tai mata kawai tana kuka,har kullum in ta tuno baya koh ita tana karyata sune masoyan nan a baya wanda ake kiran su da ‘Love birds’ dan tsantsar son da suke gwada ma junan su.

Ita dai Deeja ta sai binsu take da ido,dan  ita sam bata gani akasa ba,sannan wannan suna bai kamaci gidan nan ba na ‘love birds’.
Fad’a tai mata kamar kullum in tazo gidanta kamin su ka fito.

A kalla sun shiga gida kusan uku tukunna su ka dawo gida.

Ajiyar zuciya tayi,yau d’aya ta fahimci wani darasi duk da Maman Ihsan bata ce komai ba.
Zama ta gyara tare da kallon Deejan.

“In zaki karad’e garin nan Deeja toh za ki sha mamaki acikin gidan auren jama’a, kowa da matsalarshi,ba wai kuma dan babu soyayya ba.

Kai ta girgiza

“A’a, koh d’aya, wallahi zaman ne kawai bamu iya ba,abin da nake so ki fahimta soyayya ita kad’ai bata wanzar da farin ciki.
“Idan soyayya kad’ai ke gyara rayuwar aure Deeja nai imani ba mai jin kan Habu da Ummi,sunyi soyayya irin wacce ba kya zaton zasu iya.

Hakan yasa muka musu lakabi da sunan “Love birds” dan tsantsar so da tattali.
“A gare mu Ummi sunanta ‘Ta Habun’, yayin da Abbakar ake kiranshi ‘Na Ummi’.

Duk yadda zan kwatanta miki ba zaki gane ba,amma nasan a wachan lokacin Habu zai iya mutuwa akan Ummi,haka itama.
“Yanzu fa?

Kallonta tai tara da girgiza kai.

“Ba ta inda zai yu,tunda gashi a gaban ki kowa ya furta ya gaji da d’an uwanshi..

Kai ta jinjina tare da dukarwa.

“Dan haka Deeja soyayya ba koh mai bace a gidan aure mud’in ma’auratan ba su iya zaman ba.
“Kiyi kok’ari kiyi nazarin gidajen da muka shiga kad’ai, nai imani in zaki karad’e garin nan gida d’ai-d’ai ne akai aure ba soyayya, amma yanzu soyayyar an matsar ta gefe, an ari abubuwan nan an lullu6a mata 

Hak’uri

Sadaukarwa

Tattali

Biyayya

Mutunta juna.
“Su ke haifar da iya zama,idan wannan suka shiga toh lokacin soyayya ke da tasiri a gidan auren ku.

Kinga kenan ashe soyayyar titi bata da wata fa’ida,ta gidan aure kad’ai ke da tasiri idan har kun iya zaman.
“Ina so ki zubda makaman yakinki ki amshi aurenki hannu biyu ki bashi daraja,ki koyi ladabi,da iya tauna harshe a gaban miji, yanzu ne zaki gina soyayyar da ki ke muradi ba wai a titi ba,mijinki yana kaunar ki,ga tattali,amma da halamun kin fara tsire mishi tunda ke baya gaban ki.
“Shin irin soyayyar su Ummi ki ke bid’ar ki samu koh wacce zata wanzar miki da durewar zaman lafiya?

Kiyi tunani Deeja,nasan a yau kin samo darasin rayuwa,ki ajiye *INA DA BURI* ki kama gyaran gidan ki,na tabbatar a gaba shima Burin zai baiyana.
“In kuwa ba haka ba,ki cigaba daga inda ki ka tsaya,akwai mata a gari wanda suke neman kamar Kamal ido bud’e sun rasa irin Muneera,nai imani da gudu zasu zo bauta mishi koh da baya son su..
“Kiyi tunani,sannan in kin kashe auren,shin kina da lasisin za ki samu saurayi mai jini ajika da zai kwashi bazawara har ya gwada mata irin son da ki ke da Burin?

“Ki tuna yanzu farashinki ya sauka,sannan zawarci tsada yake,ruwanki ki rike mijinki,ruwanki kar ki rike,ni dai nayi iya wanda zan iya,na kuma fita hakkin makotaka da ‘yan uwa a musulunci,na barki lafiya.
Da kallo ta bita har ta fuce kamin ta tsunduma tunani,ba zata ce ga ahalin da take ciki ba,abu d’aya ta sani ta zubda makaman yakinta daga yanzu zata gyara kuskuren da ta tafka,a shirye kuma take da ta sauya halinta,a shirye take da ta nuna ma Kamal lalle *Mata suna suka tara*
Ita Deeja ta fice tunaninshi,dole ta nuna mishi Muneera ba tsarar jerawarta bane.

Mike wa tayi tare da rike k’ugu, tamkar mai magana da wani ta fara masifa.
“Wallahi kinci karya kin kwana da yunwa Muneera,Kamal na Deeja ne ita kad’ai,daga yanzu zan nuna miki da banbanci.

Anya Deeja?

*Toh ayi dai mu gani in basilin zai soya kosai*😜.

SAFHA..✍🏾

[4/4, 6:52 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©SAFHA.

SADY JEGAL.
FEENAT JA’AFAR

         &

HAFSA(MAMAN HANIF).
21_Agogo ta kalla,shida saura an kusa kiran magriba kawai ta nufi kitchen.

Abincin mai rai da motsi ta d’aura wanda bata ta6a yin irinshi ba sai dai tai ma cikinta kamin ta wuce sallah ta sake koma wa.
Tsadadden flaks nata ta fito dasu har bayan isha’i tana abu d’aya.

Tsaf ta gama tare da jere su bisa center table akan faranti ta shige wanka.
Gashi ta sharce tare da zama gaban mirror tana kallon jeren kayan kwalliyar wanda bata ta6a bud’e wasu ba ma,iyakarta powder da mai.

Murmushi tai tare da gyad’a kai,dan haka sai ta gyara zama ta hau tazar gashi da kyali.
Mudubi ta d’auka bayan ga wani a gabanta tana duben tsaruwar da kwalliyar tayi sai wani turo baki take kamar zatai selfie,tabbas dole ya tantance tsakanin zare da abawa,a yau ita koh Muneera?
Sabbin kayan da ya ta6a kawo mata na riga da skirt ta dakko bayan ta tufke kan da ribbon cikin style.

Ainun ta kashe kyau,sai tsabar kamshi ke tashi ko’ina yai tsaf.

A yau take cikkakiyar matar gida,dan har su burner aka jona amma har tara da wani abu shiru ba Kamal.
Ta fa fara kulewa,kawai daurewa take,dan sai yanzu zuciya ta fara rayo mata tabbas in yai dare zance yake zuwa.

Kai komo ta fara a tsakanin parlourn, wani irin tsanar Muneera take ji a kasan ranta,ta aminta tsananin kishin Kamal take a yau,musamman in ta tuno kila yana chan yana watsa mata kalaman soyayya sai taji kamar ta zunduma ihu.
Kukan zuci take,ga ta fasa waya balle ta kira taji a inda yake har wannan lokacin, yau d’aya ta damu da rashin dawowarshi gida.

Kwafa tai tana kallon agogo,9:32pm,kai ta jijjiga tare da tsiyaya ruwa a kitchen koh ta ji saukin wani abin.
Da sallama ya shigo had’i da wakar

_’Rai da Buri,duniya kuma labari’_

Da cup ta fito a hannu da sauri tana kallonshi da tuhuma.

Chak! Yaja ya tsaya tare da barin wakar yana dubenta daga kasa har tsakar kai baki sake..
Matuka tai kyau,irin kyaun da bai ma tunanin ta iya ba,gidan ya kalla,tabbas akwai sauyi a yau daga ita har gidan,lalle ne wanda yaki sharar masallaci zai ta kasuwa, dan haka dariya ya fara neman kunshe,yayinda ta had’e rai maimakon ta tar6o shi kishi ya hana,sai ma fad’in
“Daga ina ka ke?

Dariyar ya had’iye tare da saita kanshi cike da mamaki,yau ce rana ta farko da yai dare ta tambayi daga ina yake,kai ya jijjiga, lalle kwalliya ta fara biyan kud’in sabulu.

“Daga zan..

Shiru yai jin Nokia da ya siyo mai torchlight na kara halamun an kira.
Kai ya dago tare da kallota,dan haka sai ta tabbatar da zarginta Muneera ce.

Kofin ta ajiye tare da isa jin ya d’auka ta kai hannu zata warci wayar ya kauce tare da hararota,bata daddara ba ta sake kai wa wayar chafka tana zunguro baki ya ruko hannun.

“Toh Abba..
Jin ya ce Abba yasa ta dan tsaya had’i da kasa kunne.

“Ok,Insha-Allah goben zan kai shi..

Sallama sukai cike da girmamawa tukunna ya sauke wayar yana aiko mata da harara.

“Wai mey ke damunki ne?
Baki ta chunno tare da kok’arin kwacewa jin ya matso hannun.

“Bar fa ganin na kyaleki jiya in ki ka sake fasan waya zan dau mataki ne..

Kalloshi tai tare da sake d’ane baki.

“In dai naji kana waya da wata ‘yar katuwa a turmi ma zan dakata 

kowa ya huta..
Hannun ya cika yana kwafa,dan haka kawai sai ta kai hannu kan kayan hannunshi ta amsa tare da da yin gaba tana kunkuni.

Da kallo ya bita baki a sake,tabbas da sauyi a gidanshi ba kad’an ba,koh da tsiwar yau hankali ya dira tsakar kan Deeja kad’an, amma dole ya zuba ido dan ganin kamun ludayinta.
Kan center table ya kalla ganin jere da flaks,dariya ya kunshe ganin ta shige kitchen ya nufi d’aki yana jijjiga kai.

D’akin ta biyo shi,dan haka sai ya juyo jin ta rufe kofa bata karaso ba.
A jingine take jikin kofar tana dubenshi,bai 6arke da lamarin ba sai da yaji ta ce

“Sannu da zuwa..

Ido ya sa mata baki sake.

“Mey ki ka ce?

Ba musu ta sake fad’in

“Sannu da zuwa na ce.
Kai ya jijjiga tare da cigaba da abinda yake,dan haka sai ta fuce dan zuba mishi abinci.

Parlourn ya fito rike da laptop da waya a hannu ya nemi waje ya zauna.

Abincin ta tura mishi a hankali tare da koma wa ta zauna.
Kallonta ya sata,kawai sai yai kamar bai ga ba ya fara latse-latsen system.

“Abincin naka zai huce fa..

Kai ya dago tare da sa mata ido.

“Nawa?

Kai ta jijjiga tana d’an 6ata fuska gudun kar yai mata gori.
Murmushi yai tare da jijjiga kai.

“In tambaye ki man..

Juyo wa tai tare da kafeshe da ido,dan haka sai ya cigaba.

“Hope ba wai cin hanci ke ki bani ba?

Baki ta saka tare da mishi kir! Da ido.

“Dan in shine toh ki sani ba abinda zai sauya akan niyata,gwara ma kiyi dan Allah kila ki samo lada…
Galala take kallonshi ganin ya cigaba da abinda yake.

“Tabdijam! Toh wallahi sai ka ci,dan bazan shiga kitchen tsawan awa ta uku da rabi a tsaye ba kazo ka ce ba zaka ci ba,aure kuma ban hanaka ba,dan ai na fad’a maka bai dameni ba in zaka auro dubu ma ni koh a kwalar rigata..
Ido ya sa mata yana kallo ganin ta matso gabanshi tare da tasashi gaba wai sai yaci kamar wani d’anta.

Dariya ma abin ya bashi,a jininta yake,kila ita nata salon nadamar daban yake da na sauran mutane.
Laptop din ta d’auke daga durkushen tare da had’e rai ta kara turo mishi plate tana chunno baki.

Hannu biyu yasa ya riko ha6arshi yana dubenta,bai ga irin Deeja ba har yau, karshe bai san ya sa hannu ba jin zata sau mishi kukan 6aci.
Ruwa ta d’akko had’i da cup ganin ya kusa ya cinye ta durkusa gwiwa biyu tana tsiyaya mishi.

Jarkar take rufe wa lokacin da ya d’auka ya kai bak’inshi zai sha waya tai ringing.

Gaba d’aya su ka bita da kallo na wani dan lokaci, kan cikin zafin nama ta kaima wayar raruma ganin sunan da ya baiyana jiki da sauri ya rigata ya d’auke yana hararata.
Huci take tamkar kububuwa,cike da neman magana ya kara wayar a kunne,dan haka da sauri ta dangwarar da jarkar tare da nufar d’aki tana ta6e baki halamun zata sau kuka.
Gado ta fad’a tare da sakar kuka tana tatta6e baki ba koh hawaye.

Anya zata iya wannan wulakanci kuwa? Jikinta har tsuma yake ganin sunan “SAHIBATA” a jikin screen,bata ta6a cin karo da tsinanniya irin Muneera ba,naci tamkar bakar mayya,gashi zata sa plan nata ya rushe.
Shi kwa yana d’auka ya sau dariya.

“Kai ban ta6a ganin mai daru irin na kawar ki ba sam,she’s very stubborn,yanzun ma riga ta nayi da tuni ta sake fasan waya.

‘Yar dariya itama tai daga chan bangaren.

Iska ya furzar tare da sakar ajiyar zuciya tare da fad’in
“Hoho,Deeja dorling, Allah ya nuna min ranar da zamu tashi bata chakali fad’a ba,ga tsoro yadda ki ka san farar kura…

Zancen shi kawai yake tana yak’e cikin waya,amma chan a kasan ranta wani kishin Deeja ke ratso mata a yau dinnan.
Dan haka firar yau tuni ta gundureta jin duk kusan labarin na Deeja ne,komai ya ce Deeja,dan haka sai ta hau hammar karfi da yaji wanda yasa yai mata sallama.

Ya dan jima dan so yake ya kunnota da tabbatar da ina ta dosa,in ta shirya sauya hali ta nan zai gane.
D’akin ya tura har ta kashe fitila ta kwanta,sai dai yana kunna fitila ta mike ta zauna tare aika mishi kallon tuhuma.

Komai ya ajiye tare da kok’arin hayo wa gadon ta ya ye bargon ta mike durkushe a gadon da kayan bacci.
“Ka fad’a min da mey Muneera ta fini da har ka mato haka a kanta?

Da wani yanayi yake kallonta ganin yadda ta rike k’ugu kayan sun lafe jikinta,matuka sun tafi dashi har yaso kasa controlln kanshi yana had’iyar yawu,chan dai ya cije tare da had’e rai ya d’auke kai.
“Bana ciki da neman fitina ki banni nai bacci dan nasan kin san amsar ba sai an fad’i ba.

Baki ta saka ganin ya kule bargo ya batta,

“Kana nufin kenan ta fini?

Kai ya jijjiga daga cikin bargon,kamin ya nufa kawai ta sau mishi kuka harda su bige-bigen katifa da shura k’afa.
Bargon ya yaye yana dubenta,yadda kasan goyon kaka haka Deeja take wajen 6aci,bai gajiya wa da kallonta,ga nan bakin nan a d’ane tana mishi kunkuni ido ba koh hawaye.

Kai ya jijjiga.

“Toh naji,mey ki ke so na ce yanzu?
Ba musu ta ce

“Ka ce na fita kawai..

Ido ya sa mata,dan tai mishi shiru ya ce

“Toh kin fi..

Kukan ta bari,kan tai magana ya ce

“Amma fa iya tsiwa ki ka fita..

Ido ta sa mishi,dan haka yana kunshe dariya ya miko mata hannu halamun tazo.
Kan ya nufa har ta kaiwa hannun hak’ori ta cije dan takaici,da sauri ya zame yana yarfewa tare da fad’in

“Kai..kai..kai,ki ka cizan?

Da sauri ra ce 

“Eh din..

Raruma d’aya yai mata ya chafkota,dama kiris yake jira,dan haka ya hau wayencewa da sai ya rama,daga nan kid’an ya sauya.
#Team Deeja👎🏾 anyi d’an abin kai,da halamun an soma sauya hali,yau 10%✅

SAFHA ne…✍🏾

[4/4, 6:52 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©SAFHA.

SADY JEGAL.
FEENAT JA’AFAR

         &

HAFSA(MAMAN HANIF).
22_Monday take yau,zo ka ga wai yau su Deeja ne da tashi sassafe d’aura ma miji breakfast.

Yaso makara, dan haka a gurgguje ya fad’a waka ya fuce kitchen dan wai koh dan kwai ya soya da tea.
Kamshi ne ya fara bugarshi tun kamin ya isa kitchen din,dan haka da sand’a ya leka.

Tsaye take tana soya doya da kwai halamun kamshin source ke tashi.

Ciki ya karasa jin tana rera ‘yar wakar
   _’A gonata nayi shukar dashe na so bazan cire ba,dole in bata kulawa domin baza naso ta mace ba.. Hmm,umm, hmm’.._

 A cikin make murya ,ga nan earpiece a kunne.
Cikin sand’a ya lalla6a tare yi mata dabaibayi ta baya kanshi bisa kafad’arta.

Ihu ta maka da sauri tare da sakar chokalin hannun.

Cika ta yai tare da ja baya ganin ta juyo a dole ya tsoratar ta.
Harara ya d’an sau mata, dan haka da sauri ta chunno baki gaba had’i da cire earpiece din a kunne.

“Har ka tsorata ni..

Doyar d’aya ya ra6a yana juya wa.

“Da ke tsoron bai da wuya ba..

Shiru tai tare da kok’arin kashe wayar,kan ya nufa ta ce 

”Ina kwana..
Juyo wa yai had’i da kallonta baki sake.

Iya tsawon watannin da sukai a cikin gidan nan koh da tuntu6en harshe bai jin Deeja ta ta6a yi mishi ina kwana,ya kuma fara tsorata da lamarinta a yanzu ba mamaki ba.
Dan haka kai ya kad’a mata tare da ra6awa ya fuce,tunanin shi d’aya, ace ya fasa auren Muneera yai imani daga ranar Deeja zata dawo mishi gidan jiya,dan wannan ladabin da ta tsiro yafi daukanshi a matsayin toshiyar baki ba wai gaske ba.
Dan haka sai jikinshi yai sanyi,hakan yasa har ya tafi office da ido kawai yake kallonta,duk da bakin nan yana nan d’ane a gaba kamar na gado amma a yau har takalmin da zai sa aka goge mishi,bai son ya saki jiki da yaudarar nan ta Deeja,dan haka dole ya iya takunshi dan sanin inda ta dosa.
Har bakin kofa ta raka shi tana a dawo lafiya,kai kawai ya kad’a mata, har zai fita ta ce zata gidan Maman Ihsan.

Jim yai kad’an, kan daga bisani ya jijjiga mata kai halamun sai ta dawo.

***
“Naji dad’i da har ki ka gane kurenki, amma ya dace ki bashi hak’uri domin wanke laifin ki na baya,a hankali sauran aiyukan ki zai sa ya gane kinyi nadama.

Dabaru ta sake bata,wanda sosai ta san wasu,taurin kai ne ke hanata yi.
Sai bayan azahar ya shigo fuska sake tai mishi sannu da zuwa,shi dai nashi ido,dan haka da kai ya amsa bai da walwala.

“Tare muke da bako,bari zan shigo dashi ki sako hijab..
Bai jira amsar ta ba ya koma waje,ya sani in har ya sanarta da wa suke tare yanzu zai ga sauyi,dan tun ba yau ba in taso ta bakanta ranshi koh a da kamin auren su toh ta kushe halin Abban shi(mai auri saki),dan haka ma yasha mur yanzu,dan yasan ta ganshi sai ta tofa.
“Bissmillah Abba..

Fuska sake su ka shigo da Abban nashi.

Zai nufi d’aki sai ga ta nan ta fito a kitchen sanye da hijab,ja tai ta tsaya tana duben Abban da ke mata murmushi.

Kallota Kamal din ya yi,sai dai da mamakinshi yaga ta sau fuska harda duk’ar da kai na kunya tana fad’in
“Sannu da zuwa Abba..

Da kallo ya bita ganin ta juya kitchen din,da faranti ta fito d’auke da lemon kwali da ruwa da cup tana murmushi,shi dai sai binta yake da kallo.

A gabanshi ta ajiye tare da zama cike da ladabi tana gaidashi,harda tambayar su Badiyya.
Lalle abin kai,wai fitsari da kumfa su Deeja.
Abinci ta koma ta zubo mishi,shi kanshi ya yi mamakin Deeja,dan in yazo rai take had’e wa koh a gida dakyar take magana sai dai ace mishi ai miskila ce Deejan.

Yaji dad’i da d’anshi yai dacen macen kwarai, Insha-Allah yasan zaman zai d’aure.
Koh minti goma bai ba ya ce ai zai tafi a bisa hanya yake,tunda ya wuni ya sake wuni.

Tayi-tayi ma koh abincin bai ci ba,su Deeja harda tsarabar su powder da sarka da gyale wai a kai ma Badiyya.
Da yunwa ya shigo cike da kuma farin cikin tar6ar da Deeja tai ma mahaifinshi,ya sani da uba,uba ne,komai kuwa mugun halin shi,dan haka a yau kad’ai Deeja ta kuma kima a idonshi,dan ta martaba mahaifinshi.
Sai dai yana shigo wa yaga ta rike k’ugu rai had’e sanda zuciyan shi ta tsinke, yasan kenan akwai magana.

Da ido yake kallonta,dan haka sai ta ce

“Wato har Abba yazo garin nan ya kwana ya yini, ya sake yini amma baka sanar ni ba?
Yawu ya had’iye tare da sakar ajiyar zuciya ya ce

“Thank God”

A zuciyarshi.

“Toh daga ina ka ke kai mishi abinci kenan? 

Da ido ta tsare shi,dan haka sai ya samu waje ya zauna tare da fad’in

“Gidan Mamy..
Baki ta chunno,har ga Allah bataji dad’i ba,a ganinta ita ya dace ta kai mishi abinci,amma saboda bata isa ba shine bai ma sanarta yazo garin ba.

Hijab ta cire tare da yin d’aki ita a dole yai mata laifi.

Da kallo ya bita tare da jijjiga kai,gaba d’aya ta sauya,sauyi ma na ban mamaki.
Abinci ya janyo tare da daukan chokali yana sake kallon d’akin da ta shige, yasan fushi tai a dole,shi kam mutunci ya kare bai san zai samu hakan ba,dan haka sai yai murmushi tare da kai abinci baki.

Deeja kam she’s impossible a gareshi.

SAFHA..✍🏾

[4/4, 6:52 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©SAFHA.

SADY JEGAL.
FEENAT JA’AFAR

         &

HAFSA(MAMAN HANIF).
23_D’akin ya shiga bayan ya gama cin abinci ya hau rage kayan jikinshi ya d’an kallota ganin yadda ta turo baki kai gefe.

Ba sai ta fad’a ba,halin da ta nuna zai gane fushi take,har da su juyar da kai halamun baza ma ta kalleshi ba.
Kai ya girgiza, in Allah ya gama ka da rigimammiya ai sai godiya kawai.

Dan haka iska ya furzar tare da zama bakin gadon.

“Naji ban kyauta ba,a gaba zan sanar ki,shikenan?
Juyo wa tai tai tare da sakar fuska ta kad’a kai.

“Zan huta ki tada ni in an kira sallah, and ki shirya zamu wani guri anjima da yamma.

Kai ta sake kad’awa tare da gyara mishi ya kwanta duk da bai fi 

Kamar mai gadi haka ta sashi a gaba tana dan satar kallonshi ganin yai bacci.
Tsam tai,taurin kai yasa ta kasa kare ma Kamal din nata kallo,tabbas ya yi ne,yai mata karshe,duk da mutum tara yake bai cika goma ba amma a gunta Kamal ya cike,a baiyana ne dai an tsaya taurin kai da jan aji..

Ke ki ka sani,bari Muneera ta shigo

#Tean Deeja 💃🏾.
Ido ya bud’e a hankali tare da kannewa ta yadda ba zata gani ba jin an fara kiran sallah, sai hannu ta ke kaiwa amma ta rasa ina ma zata ta6a.

Hannu ta mika kan pillown da zummar ta buga duk yana kyallota.
Ido ta zaro jin an chafki hannun kam,dan haka sai ta kafe mishi da ido.

Kanshi ya d’aura bisa hannun yana murmushi, dan haka sai ta dan duk’o jin matsewar hannun tana dubenshi.

Ido rufe ya ce
“Gadin mijinki ki ke hala?

Baki ta turo gaba tare da dan 6ata fuska kamar gaske.

“Gadi kuma?

Kai tai saurin girgiza wa halamun ba a’a.

Ido ya zuba mata jin tana gunguni baki a d’ane,kai ya girgiza.
Ya riga da ya zama jinin jikinta wannan turo bakin,dan haka bata nufa ba ya dan make bakin da yatsunshi tare da sauka ya shige band’aki ya batta da gunaguni rike da baki.

****
Gida ne dai-dai misali dan duf dashi mai upstair ya kawo ta.

Ba wani babba bane,dan tsakar gidan bai da fad’i, amma sosai tsarin ginin yai mata,dan matuka tana son gida mai bene marar fad’i dad’in shara.
Kallota ya yi,kamar yadda take kallonshi da halamun ina ya kawo ta?

Murmushi ya yi tare da miko mata hannu halamun ta sako nata.

Hannun ta kalla,kamar ba zata sa ba sai dai ta mika mishi ya had’e su gu d’aya tare da fad’in su shiga.
Ba musu ta bishi hannun su sakale da na juna.

Ba wata karya a gidan na tarikice,sai dai an gama komai har fenti da su sa tiles,matuka ya tsaru asiri a rufe.

Ba komai cikin parlourn sai labule da dispenser da a.c standard. 
“Gidan ki ne…

Juyo wa tai da sauri jin ya rad’a mata,cike da murna ta wangale baki harda dan tsallenta ta nufi d’akin dake kallonta.

Shima labule ne kawai a ciki sai bathroom.
Shima d’ayan, sai dai d’aya yafi d’aya girma.

“Kai,amma yai masifar tsaruwa, muje sama toh..

Da kallo kawai yake binta ganin yadda take murnar, da yasan za tai murna haka ai da tun tuni ya kawota.
Binta saman ya yi ganin ta haye da dan gudunta cikin murna,sai ya girgiza kai.

Ciki ne shima da parlour sai bathroom kawai,labulen ta zuge tare da shakar iskar da ta buso tana lumshe ido.
Komai tamkar ya tambayeta,bata ra’ayin tafkeken gida da wasu alatu,tafi bukatar rayuwar sauki in dai akwai soyayya.

Dan haka hannu ta hau yarfe wa cikin murna har bata san ma ta riko hannunshi ba.

“Tamkar ka shiga cikin raina Allah yai min kyau sosai.
Murmushi ya yi had’i da girgiza kai, kenan yanzu ta shirya zama dashi?

Ido ya sa mata tamkar mai son karantar zuciyarta,jin ya yi shiru sai ita kawai ke zuba yasa ta kalloshi.

“It means kin shirya zama dani kin ajiye Burin naki gefe?
Kai ta saukar,mey za ta mishi ya gane duk abinda ya faru ya wuce,ta zubda makamen yakinta ta hak’ura?

Bata sani ba,dan haka jin tayi shiru yasa ya zame hannunshi da ta rike.

“Ki zabi wanda ki ke so,sama koh kasa,Insha-Allah tare da amarya zamu tare..
Da sauri ta kalloshi tare da yin kicin-kicin da fuska tana sau mishi harara.

Ganin haka yasa ya sauko kasa,yana jiyota tana fashewa da kuka mai sauti ba koh hawaye.

Da sauri ta d’auro a bayanshi tana fad’in

 

“Wallahi bata isa ba,ai gidana ka ce, dan haka ba abinda ya dameni da wata amaryar ka ni kad’ai ce mamallakiyar cikin gidan nan ba wajen zaman wata ‘yar katuwa..

Ja yai ya tsaya tare da juyo wa bayan ya gama sauka had’i da hard’e hannu a kirji.
“Gidan ki koh nawa?

Cikin sauri ta karaso tare da fad’in

“Nawa.. Dan yanzu ka gama fad’a a nan wajen zai iya mana sheda..

Wajen da suka tsaya dazun take nuna mishi ya kalla,dan haka sai ya hau girgiza kai tare da fad’in
“Toh su6utar baki ne,amma ni ne mai gida,ni kuma ke da iko da gida in sarrafashi yadda nake so..

Ido ta sa mishi ba koh kiftawa, kamin ya gama bayanin nashi ta sau mishi bori akan afafur ba fa zata yadda ba.
Karshe da rigima aka dawo gida tana ta mishi bori had’i da kuka ba hawaye,kai ya jijjiga, yasan nata wasa ne,amma zai nuna mata shi kam aure ba fashi,dan baiga halamun ta damu dashi ba,da kishiya kawai ta damu.

SAFHA ne…✍🏾

#Team Deeja get ready🤣🤳🏾.

[4/4, 6:52 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
©SAFHA.

SADY JEGAL.
FEENAT JA’AFAR

         &

HAFSA(MAMAN HANIF).
24_Da safe yana fita gurin aiki ta figi hijab d’inta sai gidan Maman Ihsan, da shigarta kuka ta sau mata tamkar wata k’aramar yarinya. 

Sai da ta kimtsa Ihsan sannan ta zo ta zauna tana kallonta tana sauke ajiyar zuciya.
“Yau kuma wace rigima aka d’auko? Saboda nasan keda mutumen kun koma tamkar wasu Tom da Jerry, bansan iya lokacin da matsalarku zata zo k’arshe ba..

Ido ta matso duk da hawayen ya kafe.
“Ke fa ki ka ce na sauke komai na kyautata mashi duk wani abu zai wuce, kuma gashi nayi d’in,amma sai wani kalar cin fuska ke k’ara kunno kai.

Ajiyar zuciya Maman Ihsan din tayi tare da girgiza kai.
“Deeja laifinki ne koma meye, amma nasan Kamal bashi da matsala dai-dai gwargwado, amma duk da hakan gaya min mey ya faru?

Zama ta gyara tare zum6oro baki.
“Duk fa abinda kika ce har wanda baki ce ba ina k’ok’arin yi mashi,shine fa jiya ya ce in shirya zamu je unguwa, nan ya kaini gidan da ya gama gini wai na za6i d’aya,sama koh kasa wai ni da Muneera ne,ji fa dan Allah.
Wani kukan take neman saka tai saurin riko hannunta.

“Kin san mey?

Kai ta girgiza mata,dan haka sai ta cigaba.

“Abu d’aya nake so dake ki kauda kanki akan maganar aurenshi, kici gaba da….
“Haba Maman Ihsan,in fa kauda kaina kika ce? K’awata fa zai auro,koh kin manta?

Baki sake Maman Ihsan din take kallonta,jin batai magana ba yasa ta cigaba.
“Ni bama wannan ba, duka-duka aurenmu wata nawa ace Kamal zai min kishiya? Ki fa duba,wannan ai cin fuska ne da abin fad’e a gari,kowa tambayarshi mey nake mishi? Mey zance?
Numfashi ta sauke tare da furzar da iska,ta ma rasa mey zata ce,dan haka sai Deejan ta cigaba.

“Haka fa naci borin kukana amma yana sa min ido,wallahi toh gab nake da na tafka mishi tsiya..
Ido da sauri Maman Ihsan ta waro,harara ta sau mata tare da fad’in

“To shikenan ki sauke komai kiga hakan zai hana shigowar kishiyar inda muga.
“Ina fa son ki gane cewa shure-shure baya hana mutuwa, amma kyautatawar zai ja maki wata martaba a idonshi koda kuwa bai nuna maki hakan ba,kije ma kila gwada hankalin ki yake da kinyi kuskure d’aya zai gane naki wasa ne..
“Sannan ina son kigane cewa Kamal bazai iya gane cewa sauyawarki ta har abada bace har sai kin jure da hawa hanyar da kika dosa, kuma kinsan da bakinki kika furtan cewa yana maki kallon tamkar duk abinda kike yi don ya fasa aure ne koh?
Jim tai tana nazarin zancen,dan haka sai ta daga mata kai halamun hakane.

“Amma ke a naki tunanin me kike gani a zuwan mafita yanzun? 
Zama Maman Ihsan din ta gyara ganin ta sakko da ita,

“Yauwa,haka nake son ji..

“Mafita d’aya ce ki k’ara kulawa dashi sama da yadda kike yi a da, kuma ki ajiye maganar Muneerat a gefe, a kullum ana so Mace ko su hud’u suke gun miji to kowacce ta sakawa ranta tamkar ita kad’aice a gidan, da hakan zaki samu nutsuwar kulawa da mijinki..
Jim tai tana tunani,anya zuciyarta zata iya nutsuwa in ba taga karshen scene din nan ba?

Kishi ne,ta sani kishi ke matukar damunta, dan da kyar ya bari ta iya bacci.

Ajiyar zuciya tai tare da fad’in

“Toh,Insha-Allah.

Hakan ta yiwa Maman Ihsan godiya ta koma gida.
****

 Sosai ta dane kishi ta rika ta cigaba da  bawa Kamal kulawa kamar yadda Maman Ihsan ta ce.

Yau kawai taji tana sha’awar yi masu d’anwake da garin da Maman Ihsan ta basu, hakan ta zage damtse tayi d’an waken da yaji kayan yaji sannan ta shiga toilet ta tsalo wanka.
Gaban dressing mirror taje tayi kwalliyarta dai-dai misali ta dawo falon ta zauna tana zabga wani uban k’amshi.

Haka kawai take jin wani nishad’i cikin ranta.
Murmushi tai tare da kallon agogo,tasan gab yake da zuwa,a yau ta shirya nuna ma mijinta tar6a ta ban mamaki,a yau Insha-Allah zata nuna mishi ita Deeja ta banbanta da saura,bata bukatar rigima a yau sai nishad’i da tsantsar kulawa.
Dan haka take ta Allah-Allah ya dawo tai ar’ba da Kamalunta,duk da bazata ce abin so bane,amma tabbas tasan a shirye take da ta kare rayuwarta tare da Kamal.

Kai ta jijjiga cikin lumshe ido lokacin da ta tuno iya salo na Kamal.
A karo na uku kenan tana kaiwa agogo kallo had’e da sake kiran wayar amma bata shiga.

Baki ta chunno gaba tana mai nazarin mey ya tsaida shi har 03:00pm?
Mike wa tai jin an bud’e kofar gidan had’i da taku.

Rai ta dan had’e tare da sake d’ano bakin gaba halamun tai fushi.

Sai dai ganin wacce ta bud’e labulen ne yasa ta gyara tsayuwa tare da had’e girar sama da ta kasa.
“Assalam Alaikum…

K’ugu ta kama tare da mata kallon sama da kasa cike da baki isa ba.

“Babu aminci a tare da ke,dan haka bazan amsa ba..

Kofa ta nuna mata da yatsa.

“Tun muna iya shaida juna dake ki fuce min a gida dama..
Murmushi ta dan yi lokacin da ta kare mata kallo,tabbas a da bata zata za m ta iya had’a ido da Deeja ba dan kunya,amma a yanzu dai-dai take da ta fuskanci zahiri,dan haka cike da kishi take kallonta itama.
“Dama ba zama nima nazo yi ba,magana nazo…

“Ki fuce na ce,munafuka bakar algunguma,wallahi kinyi asara,ke kinsan nafi karfin na had’a miji dake,wannan sai dai cikin mafarki..

Rai ta had’e
“Gaskiya kar ki kara ce min munafuka…

“An fad’a munafuka, maci amana,wacce tai kwantai babu mashinshini kawai..

Ido Muneeran ta rintse da sauri jin maganar kamar dirar mikiya, sai dai dama ta kwan da sabon Deeja ba kyal ba ce.
A zabure ta nufi kitchen ganin zata tsaya 6ata mata lokaci ta hau dube.

Kan wata duk’urk’urar ta6aryarta idonta ya kai,dan haka cikin zafin nama ta sungumeta fatanta shine ta riski Muneera yau zata ga karshen iskanci.
Jaye yake da akwatuna seti shida tare da wasu almajirai uku duk sun taya shi d’auka.

Da tsabar farin ciki ya iso,sai dai jin ihu yasa da hanzari ya karasa.
Tsere ake tsakanin Deeja da Muneera wai a dole sai dai ta tsaya ta kwad’a mata,dan haka su ka fara kewaye round na kujerun parlourn Muneera na ihun a taimake ta.
“Shegiya bakar algunguma kadan ba sai kin tsaya ba,yau zan nuna miki karshen iskanci,ba mijina ki ke so ba?…

“Subhanallah… 

Duk juyawa sukai bakin kofar jin maganar..
“Kanki d’aya kuwa?

Kai tai saurin girgiza wa tare da fad’in

“A’a, dubu ne,amma yau sai dai a ni koh ita..

Da gudu ta sake yin kan Muneeran da ta6arya yai hanzarin isa,kan ta farga ya shige gaban Muneeran ya kare mata.
Ido ta k’ank’ance da zummar surfa bala’i su ka ji ana fad’in

“Ina zamu ajiye akwatinan?

Da sauri ya warce ta6aryar lokacin da ya ce

“Ku shigo dasu ciki.. 

Yana hararar Deejan.
Mutuwar tsaye tayi baki sake daga ita har Muneeran su na bin akwatinan da kallo wanda almajiran ke sauke wa.

Kamal din ta kallo tare da nuna akwatinan da hannu bakinta na ka’rkarwa ta ma rasa mey zata furta.
“Eh kayan aure ne,na fad’ar kishiya,ki ma ji da wai,abu har ina murna ya fara saituwa ashe kina nan da…

Shiru ya yi ganin hawaye na ziraro mata ta kuma kafe akwatuna da ido.
Kai ta dago da zummar mishi magana taji wani abu ya tokare makoshinta.

“Muneera zo ki wuce,sannan ki sani aure kam ba…

Luuu tai baya da halamun fad’uwa tana rike da kai da azama ya taro ta wanda hakan ya hana ya k’arasa maganarshi. 
“Innalillahi… Deeja!!!!

Jijjiga kafad’unta yake ganin jikinta ya sake ga nan hawaye na tsiyaya wanda su ka makale a idonta,Deeja kam da halamun an sume.
 #Team Deeja kuyo agaji da ruwa k’ank’ara kar ta lula, dan aure ba fashi😜

SAFHA…..✍🏻

[4/4, 6:52 AM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.

©SAFHA.

25-“lnnalillahi…..” 

Jijjiga kafad’unta ya kuma yi tare da kiran sunanta duk ya kid’ime ya rud’e ya rasa Abinyi sunan ta kawai yake ambata, “Deeja!!!
Ganin rud’ewar da Kamal yayi yasa Muneera tayi hanzarin d’auko gorar ruwan dake saman center table, bai bari ta bud’e ba ya amsa cikin hanzari ya bud’e ya shiga yayyafa mata ruwan a hankali yana shafe mata fuskar da ruwan cike da tausayawa.
Ganin hakan yasa Muneera ta nufi k’ofa ta sallami Almajiran da sukai tsaye carko- carko suna ganin ikon Allah.
Ganin Kamal rungume da Deeja hankali tashe gashi har zuwa yanzun bata farfad’o ba ya sata d’aukar gorar ruwan ta shek’awa Deeja a fuska take taja dogon numfashi ta sauke, 

A hankali ta bud’e idanuwanta wanda ke lumshe,

Saida ta bude idon tangargar ta shiga binsu da kallo d’aya bayan d’aya, 

take  Abun da ya faru ya shiga dawo mata d’aya bayan d’aya, a k’arshe ta sauke idonta akan akwatinan da Kamal ya kira da natane na fad’ar kishiya.
Nan ta daddage ta d’ora hannu aka ta kurma uban ihu tare da sassank’amewa tamkar wacce zata tada Aljanu.
Shure-shure take tana wani sassank’amewa tana kurma uban ihu tana ture Kamal wanda yake k’ok’arin rik’eta yana ambatar sunan ta.
Amma ina harbe- harben da take ya hana shi kamota duk tabi ta rud’ashi ya rasa ta inda zai kamota, daya ruk’ota tanan ta zille ya kuma ruk’ota ga sambatun data shiga zayyano masa kusan ma shiyafi d’aga hankalin sa.
Duk wannan dramar da suke Muneera na gefe tana kallonsu cikin k’unshe dariya don tasan wannan yana d’aya daga cikin tab’ara irin ta khadeeja inhar tana son Abu to babu kalar rigimar da baza tai ba a kansa.
Don haka cikin sanyin murya da nuna Alamun jimami ta karya wuya ta shiga fad’in,
“Sannu Deeja. Kamal ni fa gani nake kamar Aljanu ne da Deeja kaga fa abinda take mai Aljanu zam”.
Kashe masa idon da tayi ne yasa ya gano zolaya ce take kuma yagano bakin zaren don haka ya k’unshe dariya,
“Kinsan kuwa nayi zargin Aljanun gareta don naga haka masu aljanun suke suita fizge- fizge sai an musu ruk’iyya suke denawa”.
Jin hakan yayi matuk’ar kad’a cikin Deeja don ita a duniyar nan babu abinda tafijin tsoro irin Aljani, duk da ta tsorata dajin ya ambaci ruk’iyya bata fasa sassank’ame wa tana haure-haure ba.
“Kasan kuwa Malam Audu na bayan layinmu yana ruk’iyya har zane aljanu yake inba dama kawai mu kaita can”.
Dariya yake mata k’asa-k’asa don ganin ta kasa kunne ta gama nad’e abinda suka fad’a, suna kaiwa aya kuma ta d’ora daga inda ta tsaya.
“Ai kawai ruk’iyyar zamu kaita don wannan Abu na Deeja bafa na lafiya bane”.
Jin da gaske anfara taga-tagar d’aukar ta za a kaita gun ruk’iyyar ya sata daddage k’arfinta ta hankad’a Muneera ta gwarata da bango jikak’e k’um! K’eyar ta tabada sauti.
Shikuwa Kamal tureshi take amma ta kasa kwacewa saida ta daidaici dantsensa ta gasa masa cizo aekwa babu shiri ya saketa tai baya tana huci.
“Saidai kiga Aljanu akanki bak’ar munafuka algunguma maciya amana butulu kawai” ta fashe da kuka.

” kuma ni saina nuna miki k’arshen rashin mutunci ba dai ni Deeja kika ciwa Amana ba sannan kika tako kika zomin har gida? To yau sainai miki Abinda zaki nadamar cin Amanar da kikai min”.
Tajuyo kansa “kai kuma tunda kaga wannan matakin daka d’auka to shine dai-dai a gurinka to nima zan d’auki nawa matakin”.
A fusace ta fuce daga falon suka bita da ido duk sun tsorata da ganin yanda ta birkice musu Ashe darun Deeja na baya wasa ne? Yau dai sunga b’acin ranta, Adalilin me? Kishi, kishin Kamal?
Tabbas amsar haka yake.Cikin rawar murya Muneera tace’ “yaya Kamal ni fa na tsorata da Deeja ka bita kar muje wani Abu yafaru azo ana nadama agarin neman k’iba a samo rama”.
Baiko tankata ba yabi bayan Deeja don shima ya tsorata da ganin yanda ta fusata duk wani karsashi nasa ya k’are, tausayinta shike lugude cikin ransa, yasan duk abinda takeyi donshi takeyi kishinsa take nunawa k’iri-k’iri don tak’i yarda da hakanne.
A bakin k’ofar falon sukai kacib’us, gabansa ya yanke ya fad’i don ganin hannunta d’auke da jarkar kananzir ga ashana a d’ayan hannun.
Cikin karsashi yayi kanta ta dakatar a tsawace, ” karka kuskura kayi yunk’urin hanani kana k’arasowa ina shek’a maka kuma babu abinda zai hanani kyatta ashana gwara na kashe ka nima na kashe kaina kona huta da wannan azababbiyar rayuwar da nake ciki”.
“Dan Allah kar kiyi Deeja tsaya ki saurareni kar kiyi abinda zaki yi nadama a gaba”.
Hannu Muneera ta d’ora aka tana kiran sunan Allah idon ta a waje tamkar ya fad’o k’asa don tsoro, ” tsaya Deeja karki k’onamu tsaya kiji gaskiyar lamari wallahi ni ba aure miki miji zanyi ba kitsaya nai miki bayanin komai karkisa mu shiga uku wayyo Allah na”.

Wani mugun kallon rainin hankali Deeja ta watsa mata mai fassarar, k’aryar ki tasha k’arya Muneera.
Cikin zafin nama yayi kanta da nufin ya murd’eta ya k’wace, kan ya k’arasa gareta ta daka tsalle tayi gefe bai samu damar rik’eta ba.
Cikin hanzari ta shiga kici-kicin bud’e jarkar Muneera ihu take tana fad’in ” wayyo mun shiga uku Deeja kitsaya kiji karki bud’e jarkar nan”.
Cikin zafin nama yayi kanta saidai kan ya k’arasa ta bud’e ta fara tuttulawa akwatunan yana zuwa daf da ita ya daki jarkar tayi gefe tana d’agowa ya wanke ta da kyawawan mari har sau biyu.
Cikin wani irin yanayin daya fad’ar masa da gaba ta d’ago dafe da kunci, zazzafar k’wallar data dinga rige-rigen sauka kan kuncinta ita tafi kashe kuzarinsa yasan lallai yau yayi laifi ga Deeja don duk rigimar Khadeeja bata kuka mai hawaye sai dai tagama bige-bigenta da zunb’ure-zunb’ure da k’unkuni.
Cikin rawar murya da rawar baki duk jikinta rawa yake ga hawaye shab’e-shab’e “bantab’a dana sani ba irinta yau tunda na tsinki kaina cikin rayuwarka, haka za nayi alkawaririka na k’arya duk a dalilinka, to kasani yau ce rana ta k’arshe da zaka k’ara tozali da k’wayar idona, zan barka kayi rayuwa da Muneera don zuwa yanzu nagane ta taka matsayin da nayi kad’an ni nasameshi a gurinka tunda gashi kad’au hannu ka mare ni sabida ita”.
Ta juya gun Muneera, “ki zuba ruwa a k’asa kisha kinyi nasarar rabani da duniyar ma baki d’aya ba Kamal kad’ai ba, inhar nacika y’ar halak nabarku har gaba da Abada”.
Da gudu ta kwasa tayi d’aki da gudu ta mayar da k’ofa ta rufe ta murza key.
Hawaye keson zubo masa yana cijeshi da dauriyarsa amma sai da guda d’aya ya d’uso kan kumatunsa, cikin k’araji Muneera ta shiga yimasa magana da cewa’ “Meyasa kayi haka Kamal?”.
“In banyi hakan ba so kike na k’yaleta ta halakamu?”.
“To ni dai zanje na fad’awa Deeja gaskiyar Abinda yake faruwa zuwa yanzu yaci ace tasan komai ko nafuta daga zargi tadena tsinemini daga Abin arziki”.

K’arar da sukaji ta kwallane yasa suka nifu k’ofar da gudu har yana ture Muneera ta fad’i akan hannun ta takwa saka k’ara ta rik’e hanun.
Kamal kuwa bai ma san abinda yayi ba hankalinsa yayi gaba ya tsorata da k’arar Deejansa.
Itama daurewa tayi ta mik’e ta isa k’ofar d’akin suka shiga bugu tareda kiran sunan ta.

” Kiyi hak’uri ki bud’e Deeja kar kiwa kanki illah in har akan maganar aure ne na fasa bazanyi ba ki bud’e kofar kiji nayi Alk’awarin dake k’adai zan rayu, matsayinki na nan yanda yake ada, nai miki rantsuwa da Allah har yanzu ina sonki banida tamkarki ni Kamal naki ne ke kad’ai ki bud’e dan Allah”, bubbuga k’ofar suke amma shuru kakeji wai malam yaci shurwa.
Kuka sosai Muneera take, ta mafi Kamal tsorata da lamuran Deeja don duk inda akaje aka dawo itace a cikin rikici itace zata shiga uku daga abin Arziki ya zama na tashin hankali.
Don haka batasan sanda tasoma warware k’ullin ba.
“Wayyo Deeja ki saurareni wallahi ba da gaske auren Kamal zanyi ba niba maciya Amana bace bazan tab’ai miki butulci ba, babu komai tsakanina da kamal sai plan wanda shida kansa ya shirya hakan, ni kuma na amince sabida dalilan daya kawo min, amma wallahi ba aurensa zanyi ba  bazan tab’ai miki wannan cin Amanar ba ko wata naga zatai miki sai inda k’arfi Na ya k’are”.
Surutai maganganu rantsuwa babu kalar wacce basu yi ba amma shuru, wannan ya kuma d’aga hankalinsu, suka k’ara k’aimi wajen bubbuga k’ofar ko zata bud’e nan ma shuru.
Saida suka gama jigata sannan ya tuna da safayar muk’ullan don haka ya nufi d’ayan d’akin da gudu don d’auko muk’ullan.

#Team Deeja yau ranar takuce😜

SAFHA……✍🏼

[4/4, 8:12 PM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

©SAFHA

26-Tana murza key d’in tazare tayi wulli dashi ta kifa kan gado ta k’udundune cikin bargo zuciyarta nai mata d’aci yayin da ta shiga kukan zuci hawayen ma ta nemeshi ta rasa.
Dafe k’irjin ta tayi don wani irin nauyi taji zuciyarta tayi ta kasa banbance meke damun zuciyarta, k’uncin dake dank’are cikin ranta shiya tokare mak’oshinta tagagari ko shak’ar iskar kirki.
Ganin tana neman hallaka kanta yasa ta yunk’ura ta tashi hannunta dafe da k’irjinta, tana k’ok’arin ziro da k’afafunta ta soma jiyo sautin maganganunsu,

Nan ta kuma kasa kunne don taji abinda suke fad’a rad’au kuwa tana jiyosu.
Mamakin jin furucin sune ya mantar da ita halin da zuciyarta ke ciki sai ma ta kinkimo tunanin rainin hankaline suke son yimata, yama za’ayi su canja magana bayan tana sane da hatta manya sun shiga cikin maganar ko gidan daya gina yayi shine sabida ita da Muneera sai yanzu rana tsaka don ta birkice musu sai su nemi raina mata wayo?.
Amma kuma rantsuwar da taji sunayi bilhakki babu batun wasa a cikin ta bare ma intai la’akari da yanda Muneera ke zayyano Abinda ya faru wanda zuciyarta ta kasa k’aryata Muneera don tasan Muneera bata k’arya kuma ko cikin wasa ne baza tai maka rantsuwa akan k’arya ba.
Jinsu kawai take ta rasa me ya kamata tayi sai canki-canki take tsakanin k’arya da gaskiya, take ta yanke shawarar kiran Mamy don tasan Mamy ce ta bashi goyon bayan auren Muneera kuma babu ta yanda za’ayi Mamy taimata wasa.
Bugu d’aya ta d’aga kiran ko sallama babu ta rushe da kuka wiwi, sanin hali irinna da Deeja yasa Mamy bata damu da kukan nata ba, ta tsaya tana sauraran kukan har ta tsagaita ta samu damar magana.
“Yanzu Mamy dasa hannunki Kamal da Muneera suka dinga Kwallo da zuciya ta? Ashe duk maganar aurensu shiri ne Mamy amma baki fad’amin ba? Ni bansan sanda Kamal ya tsige matsayina ba ya kafa kansa gurinki yanzu ko Abba baya sauraro na sai kamal”.
Murmushi Mamy ta saki dama tasan za’arina don tunda Kamal da Muneera suka kawo mata akwatunan kayan da yayi mata tagani a madadin kayan laifenta dabai samu damar yinsa ba a wancen lokacin tasan yau k’wan zai fashe fatan ta dai Deeja tayi karatun ta nutsu tasan ba itace autar mata ba, ba kuma don ya nemi wacce zata soshi yarasa bane yake zaune da ita tana shuka masa rashin mutunci,

Don haka tun d’azu take sauraran kira daga Deeja sai gashi kuma ta kira d’in.
“Kina jina Deeja? nasan komai akan hakan kuma nina bada goyon baya don inaso naga rayuwar d’ana ta inganta, Kamal Namijin duniya ne a yanzu duk duniya baki da tamkar sa, basai nace ki sauke abinda ke kwanyar kanki ba, kinga dai misali yanzu ko? To sati biyu na baki kacal in har kika koma ‘yar gidan jiya ba sai na fad’a miki hukuncin da zan zartar ba, ince dai kina sane da Kamal mijin mace hud’u ne? to Allah ya taimaka”. Tana kaiwa aya ta katse kiran.
Kusan mutuwar zaune tayi don tsananin mamaki bin wayar take da kallo bayan ta sauke ta daga kunnenta cikin sanyin jiki.
Murna za tai ko kuka ko haushin rainin hankalin da sukai mata? Tsam tai da ranta tana tunanin wani abu, So! Tabbas Kamal k’waro ne a wannan fagen, cijewar da take ne ke sagar da karsashinsa, to in kuma ta bada nata gudunmawar kuma fa? Ya abin zai kasance? “Tabbas zaifi armashi”. tabawa kanta amsa a sarari.
Habawa ai batasan sanda ta buga tsalle ba harda k’ara “yes”, nan ta shiga kwaso shoki da itigi duk wata damuwar ta tayaye.

Jin k’arar mukullayen da suke gwadawa yasa tayi sauri tai zaman dab’aro tareda dafe kirji ta shiga hakin k’arya harda kiran wayyo.
Zaman ta yayi dai-dai da bud’ewar k’ofar don haka sukayo kanta cikin hanzari har rige-rigen d’agota suke tare da kiran sunanta duk sun damu mutuk’a.
“Sannu Deeja” da hannu ta dakatar dasu, “Karku kuskura ku tab’ani kubarni na mutu na barmuku duniyar kucita da tsinke”.
Sororo yake bin ta da kallo don ganin ta k’ak’alo damuwar dole tana shimfid’ata kan fuskar sa.
Sosai ta matso kusa da ita ta kamo hannayenta duk da tana fiffizgewa.
“Ki yarda dani k’awata, nisam banci Amanar kiba Deeja kitsaya ki saurareni na rantse miki da Allah babu wata maganar soyayya tsakanina da mijinki balle maganar aure, shi da kansa ya buk’aci mu shirya hakan don kigyara gurb’atattun halayenki, wanda kika k’agawa kanki, amma kisani ni Aminiyar mai k’aunar ki mai son ci gabanki, bazan tab’a bari abu mara dad’i ya same ki ba, wannan dalilin yasa na amince da buk’atar Kamal kuma ban yarda kai tsaye ba saida Mamy tasa baki, kiyi hak’uri Deeja kar kimin wata fassarar daban nayi hakanne domin Allah don kuma na ceto rayuwar aurenki daga lalace wa kuma ina son martabar ki tak’aru gurin mijinki a maimakon ta ragu”.
Cikin harara da murgud’a baki had’i da murmushin daya taso tun daga cikin ranta ya fallasa asirin zuciyarta, ta matso kusa da Muneera sosai suka rungume juna suna murmushi.
Kallonsu kawai yake yana daga gefen hagun ta, suna cika juna ya mik’o mata hannu tareda cewa” saura ni”.
Juyar da kai tayi ta cunno baki, alamun har yanzu bata huce ba.
“Yanzu in banda abinki Deeja inhar naso mijinki yaya zanyi da yaya Salis Wanda baikonsa ke kaina? Zaro ido tai had’a da dafe goshi kana tace’
“Yanzu har da yaya Salis a had’a bakin?” “Kwarai kuwa don yana son kwanciyar hankali gaba d’aya, bari nakira miki shi ya kuma jan wannan kafaffen kunnan naki”, ta d’anja kunnen, “wayyo”.
Ta saki k’ara cikin salon shagwab’a, hakan da tai yayi matuk’ar tasiri agunsa har yaji wasu lamura sun motso masa ya sakar mata murmushi ta kuma kauda kai bakin nan kamar ya tab’o hanci.
Shima yaya Salis fad’a ya k’arai mata harda had’awa da baraza na, karshe dai Muneera ta amshi wayar tayo falo don tabasu guri itama tasamu damar ganawa da masoyin ta.
Hannu ya mik’a mata “zo nan Deeja”, bakin ta kuma turawa gaba harda mak’e kafad’a.
“Kizo kinji Deeja na,

Ina buk’atar batutuwa da dama daga gareki, kisani, yanzu duk wata hayaniya tazo k’arshe tsakanina dake, akwai damar da nake nema a gareki a yanzu, ki tausaya mini ki tausayawa zuk’atanmu ki dena wahalar dasu ki basu abinda suke buk’ata fiye da komai cikin duniyar mu Deeja”.
ta soma ‘yar dariya cike da kunya ta sunk’e fuskarta cikin tafin hannun ta.
Ganin hakan ya k’ara masa k’warin guiwa ya kuma samu tabbacin Deeja na sonshi don haka cikin kuzari irin wanda farin ciki yake haifar wa yace,
“Deeja d’ago idonki ki dubeni”.
Da k’yar ta sarrafa kanta ta d’ago ta dubeshi jikinta na tsuma a sanadin kusancin dake tsakaninsu, k’wayar idonsu ce ta hard’e ya shiga wani matsanancin yanayi ta kwaci idon ta da kyar cikin shauk’in dake tunzura zuciyar ta.
Cikin dabara ya lalubo hannunta ya shiga murzawa “tafuka masu laushi”, murya tausashe yace’
“Kimin Alfarmar so Deeja zumunta tajamin sonki mai k’arfi ya kusanci zuciyata, ina neman raddi don Allah, ki taimakeni Deeja ina neman soyayyarki,

Don Allah karki zauna dani don alfarma”.Yai mata rad’a a kunne, 

“So nake naji so a bakinki, so nake ki bayyana min so”.
Ta d’ago da kanta sosai ta kalleshi hawaye na taruwa a idonta murya na rawa.
‘Duk Abinda kake so na zama zan kasance zanyi ba bisa Alfarma ba bisa cancantar ka”.
Jintai shuru, ya gyad’a kai, “ba buk’atuna kenan ba, amsar so nake so bana biyayya ba Deeja ina sonki!”.
Numfashinta taji na neman d’aukewa sabida murna da farin ciki, tace,
“Nima haka”.

Ya yawota jikinsa  ya rungume yana jiyo sautin bugawar zuciyarta wanda suke nuni da zallan soyayyar data bak’uncesu.
Cikin sassarfar numfashi yace” kema me? “Ina sonka! Ban tab’ajin son wani abu sama da kaiba, babu wani abu daya tab’a birgeni sama da kai, ni ba zumunta ta rayamin son kaba wayar gari nayi na tsinci kaina cikin son ba tare da nasan dalilin saba……in wannan ne buk’atar ka kayi farin ciki kasamu”
“Mafarki ko gaske?”.

Tana murmushin da bai tab’a ganin mai kyau irin saba, so kenan!

        “Dame kakeson na tabbatar maka ba mafarki kake ba?”.

   Ya kuma ware hannu, ” zo gare ni”,

Cikin hanzari da b’arin jiki ta kuma shigewa jikin suka  k’ank’ame juna tamkar su koma halitta d’aya.
kuka tafara a yayin dataji yanda zuciyarsa ke harbawa, hannu tasa ta dafe k’irjinsa “yaya kamal me yake faruwa da kai?”.
Ya amsa cikin shauk’i” sonki ne Deeja, zuciya na murna da samun Abinda takeso bazan iya dakatar da ita da farin cikin da take nunawa ba, ina sonki Deeja nayi murna da kika yarda kika aminta zaki rayu dani cikin so da aminci”.
Ta kuma b’arkewa da kuka, ” nayi nadama yaya Kamal ka gafarceni don Allah ban san sonka ke sani hauka ba tuntuni bansani ba, ka yarda dani ina sonka”.
Tuni yayi nisa dajin jiki a b’arinda masoya keyi idan suka tsinci kansu cikin na shauk’i, sunsunar ta yake tareda sunbatar ta yana numfarfashi ya rasa ta inda zai nunawa Deeja yanda ya kejin ta don haka ya soma nunawa a aikace…..

“Muneera”, ta ambata tare da janye jikinta tana haki.
“Sai yanzu kika tuna da ita?”.
Yana k’ok’arin mik’ewa tare da cewa’ “bari nadubota saina kaita gida na dawo”.
Nan ya gyara mata rigar ta ya d’aure mata gashinta da tuni ribom din ya cire, shima ya daidaita kansa yayi gaba yana fad’in’ “minti biyu”.
Cikin sauri har tana tuntub’e tasha gaban sa, bakin da yaga ta cunno harda rik’e k’ugu yasa yasan akwai darun da zatai masa.
Cike da sha’awa yake dubanta, ganin bai ce komai yasa ta k’ara d’ane bakin cikin shagwab’a tace” ni gaskiya babu inda zakaje ba zaka kaita ba”, ta janyo shi ta zaunar kan sopa,

     “Zauna nan ni zanje muyi sallama in dawo”.

Dariya sosai yayi harda mirginawa don jin dad’i wai yau shi Deeja ke Adanawa a d’aki don kishi……

#Team Deeja ko tabarshi ya sauke ta?😜

SAFHA……✍🏻

[4/6, 8:52 PM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
©*SAFHA*
27-Tsaye tayi rik’e da k’ugu a tsakiyar falon tana bin ko’ina da kallo cike da mamaki, don ganin falon a gyare tsaf kamar ba wanda ta tuttulawa kananzir d’azu ba,
“Kenan gyaran gurin nan Muneera tayi shiyasa naji ta shuru tun d’azu?” Ta fad’a a fili, 
Nan ta sauke idon ta kan akwatunan dake jere a gefe an cire ledarsu data b’aci da kananzir an goge su sai zuba k’amshi suke kmr yanda falon ke k’amshi kamar kwayar kananzir bata zuba akai ba.
Cikin hanzari tanufi tsakar gidan waiko zata tadda  Muneera acan, wayam taga filin tsakar gidan, tad’an kira sunanta taji shuru wannan ya nuna mata Alamun ta tafi kenan, don haka tai murmushi cike da nishad’i takoma ciki.
A tsaye jingine da jikin k’ofar d’akin baccin su ta taddashi don haka saitayi tsaye takasa k’arasawa inda yake ta kuma kasa komawa inda ta futo,
Wani mayen kallo yake binta dashi Wanda ya saukar mata da kunya ta sunkui dakai tana murmushi ta gefen ido take satar kallon sa,
Cikin muryar da yasan zata kwance notikan nutsuwar ta ya soma magana a yayin daya tunkaro ta,
“Ki bud’e idonki ki kalleni da kyau ni Kamal nakine ke d’aya kikau da kunyar ki ki bani abinda nake buk’ata” zuwa yanzu ya iso gabanta ganin yazo daf tai saurin juya baya don wata kunyar sace ta dirar mata,

     Ganin hakan yasa ya rungumota ta bayan yana goga fuskar sa jikin wuyan tana murmushi,
” najima da sanin Deeja na tana da buri hakane?” Yaciga ba” ki bani had’in kai nacika mana burin mu nima yanzu *INA DA BURI*”
     Cikin sassafar numfashi don wasan daya somai mata yafara sanyata jin sauyi, da kyar ta furzo kalmar,

” meye burin ka?”

A yanda tai maganar ne yak’ara kunno shi don haka ya canja salon wasan a yanai mata rad’a a kunne,
Cikin jin kunya ta tsille tana ‘yar dariya ya rik’ota, ” ki tunan naki burin”

“Aa nayafe” tafad’a tana son zame rik’on dayai mata,
Sosai ya kuma rungume ta, ” kinji nawa burin ina son jin naki”
,”Burina a yanzu ina son naga kana farin ciki, inason nai maka biyayya Donna fahimci hak’uri ladabi biyayya suke inganta soyayya, rashin su na gurb’atata kuma ba soyayya kad’ai ake buk’ata kad’ai cikin gidan aure ba kamar yanda nake d’auka ada ba”
Ya gyad’a kai” uhm ina jinki”

“Shikenan buri na nidai”

    “Aa ban yarda ba akwai wani, buri na shine naki, bazan bari kunya ta danne muradin kiba kamar yanda take danne muradin wasu ma’auratan’
Zuwa yanzu batada damar magana sai” hmm” Kamal d’inta yawuce duk inda take zaton sa.

      Yacigaba” kifad’amin me kika tanadarwa soyayyata?”

    Runtse ido tayi ta had’iye yawu da kyar ta saita nutsuwar ta”

   “Zanyi tattalin ta, zan raineta, zan ingantata,zan shimfid’a mana rayuwa mai dad’i wacce zakai alfahari da ita, zan so nafika son kanka domin kai nawane zanfi samun tagomashin soyayyar ka kasancewar ka mallaki na, zan baka duk soyayyar da kake buk’ata koma fiye da hakan nidai ka rik’eni amana na sadaukar da burina gareka, jin dad’ina Kaine, farin ciki na kaine, kai ni komai nawa nakane ina sonka Jamal!”

   Tsam ya rungume kayan sa, yana share hawayen ta da harshen sa,

Murmushi tasaki donjin furucinsa,

        ” nasani Deeja na aminta dake zaki aikata abinda bakinki ya furta, ina sonka Deeja na,’yar soyayya mai son soyayya mai iya soyayya mai burin soyayya, ina Alfahari da wannan na kasance d’an gata inaiwa Allah godiya daya bani Deeja mai sona mai son abinda nakeso kuma nake buri, kisa mana ranar tariya wasu lamuran sai a sabon gidan ki ko?”
Cikin murna da farin ciki tareda nishad’i suke darawa junan su,

   ” kasa mana rana mai sona”

      Kyautar sumba yabata don jin dad’in sunan data kirashi dashi.

“Kwana biyu yayi miki Amarya ta?”

      Ta zaro ido,” saurin meye hakan?”

      “Rayuwar soyayya” yabata amsa cikin kashe ido,
“Sati d’aya mai sona kafin sannan mungama shirinmu ko?”

   “Hakan yayi muje ciki kiji wasu batutuwa”

 Nan tasoma zamewa tana fad’in” ainaji komai anan ni a falo zan kwana ma”
Cak ya d’auke ta ganin jan zare zatai tareda fad’in,
“Darasin ciki yafina nan dad’i”

  Ta sak’alo hannayen ta wuyan sa cikin salon so tace” katuna kai yaya ne fa”

   “Bazan gane ba hakan ba yanzu muk’arasa ciki ki ganar dani”
Dariya sukai baki d’aya a daidai lokacin dayasa k’afa ya turo k’ofar,
      Asuba tagari.

****
Cikin wannan satin suka tsara yanda tariyar zata kasance, suka tsara walimar taya murna shagalin da ba’ayi na auren suba shine zasuyi k’ara’i ranar  don haka cikin satin basu samu zama ba, sunata zirga-zirgar k’ara gyare sabon gidan su tareda k’awata shi don Sufi jin dad’jn more lokacin su,

Kuyi hakuri da wannan, rashin caji yasa,
*SAFHA*✍🏼

[4/7, 8:41 PM] Sdy Jegal: *INA DA BURI*
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION
©SAFHA
28-Walimar tariyar tasu ta tsaru yanda suke buk’ata, anci ansha anchashe don har y’an kid’a suka dauko suka wak’esu, walimar ta k’ayatar anyita cikin nishad’i da kwanciyar hankali, kulawar da suke bawa junan su cike da mutuntawa da d’inbin k’auna tareda soyayya yasa ‘yan uwa da abokan arziki da sukasan badak’alar da akasha da Deeja akan auren da kuma wahalar da Kamal yasha gun Deeja duk adalilin Burin ta yasa su mamakin k’aunar da tashiga gwada masa a wannan lokaci,
Hakan yayi musu dad’i don Mmn Ihsan dasu Muneera kusan sunfi kowa murna, sai kuma su mamy da labarin yaje kunnan su tunkan atashi daga walimar, 
Duk wani masoyin khadeja zai tayata murnar samun gwarzon Namiji kamar Kamal wanda ya nunawq duniya Deeja tasace mallakin sa mai sonsa kuma abin Alfaharin sa.
Sun tsinci kansu cikin rayuwa mai dad’i wacce ko a mafarki basu tab’a tsammanin zasu riski kansu a cikin taba, wacce ta shallake tunanin Deeja ta tsere rayuwar da burin ta ke gwada mata.
A nasa b’angarenma yana jinjinawa jarumtar ta don Deeja maca ce d’aya tamkar da dubu babu inda ta kuskuroshi Ashe da kallon kitse yakewa rogo?.
***

Suna tsaka dajin dadin rayuwar su ne tafara zazzafan laulayi wanda ko minti biyar kukai tare da ita saika san halin da take ciki, 
Cikin wannan tsakanin aka fad’a hidimar bikin Yaya Salis da Munneera, taci burin bikin taso tayi yanda takeso ayi sha’anin biki da ita kasancewar tana tsaka da laulayi a kwance cikin k’uryar d’akin Mamy tayi bikin ko futowa batasan yi sabida tsiyar da abokan wasa ke mata,ga kamal dake manne da ita a waya shiga d”ari futa d’ari saiya lek’ota shiko kunyar tsiyar da jamaar gidan suke masa bayaji da anyi magana yace” nifa banason sa ido” da wannan yake kashe bakin tsanya.
*****
Bayan shekara biyu.
Zaune suke saman kafet sunsaka yaran su a tsakiya Wanda suke zagaye da kayan wasa duk Wanda ka kalla cikin su kasan basa tare da matsala sunyi wani irin kyau Alamun Hutu da kwanciyar hankali ya bayyana a jikin su,

    Dukkan kulawarsu na kan yaransu wanda suke kira da Shuraim d’ayan kuma Aeman, kyawawan yara masu kama da Mahaifin su, babu inda suka barshi siffar shi ta dogon bafulatani mai d’an haske da kwantacciyar suma sun kwafeshi tas, 
K’auna,Soyayya,Aminci, ladabi biyayya da kuma mutuntawa ita tajagoran ci dorewar farin ciki cikin rayuwar su mai inganci, suna Alfahari da junan su sun kuma tabbatarwa da juna ruhi d’ayane gangan jikince ba d’aya ba,

     Deejan kamal, kamal na Deeja, kai Allah yakara dankon soyayya yabarmu da masoyan mu na gaskiya.
Tammat bihamdillah,
Anan muka kawo k’arshen wannan littafi INA DA BURI!” ku tareshi a gaba cikin labarin KE CE TAWA!.

ALHAMDILILLAH.
godiya ta tabbata ga ubangiji sammai da k’assai majib’icin lamuranmu da kabamu ikon kammala wannan littafiKuskuren dake cikin sa Allah ka yafemana, Allah kabamu ladan alkairan dake cikin sa.
  SADAUKARWA,
Ga d’aukacin masoya wannan littafi da wanda muka sani dama wanda bamu saniba, Allah yasaka da Alkairi yabar kauna ya kara kusantamu da masoyan mu na gaskiya ya nesan tamu da mak’iyan mu.
   JINJINA GAREKU.
Iyalan gidan nagarta,Allah yasaka muku da Alkairi yakara hade kawunanmu ya doramu akan makiyanmu.
GAISUWA TA MUSAMMAN.
SDY JEGAL FANS

MOMHANIF NOVELS

ZAUREN MOMHANIF

FEENAT JAFAR FANS

ZAUREN KARATU

MUSHA KARATU

MOM FARTY NOVELS

MUMBARIN JABO
Dama sauran grps din da ban samu damar sawa ba, godiya muke Mara adadi👍
Sai munhadu a littafi nagaba!!!

SAFHA✍🏼

MAHABU 1-15

[3/18, 7:41 PM] Mmn Jafar M: 🌻MAHABU🌻
            1

 Daga Alkalamin

Maman Ja’afar✍

*GODIYA*
_Ina farawa da godiya ga Allah (S.W.A) mai kowa mai komai daya bani dama da kuma ikon fara wannan littafi na Mahabu lafiya, ina rok’onsa kuma yabani ikon kammalasa lafiya batare da ansamu wata tangard’a ba_
_Da wannan zanyi amfani wajen bawa masoyana hak’uri, kasancewar ba kullum zaku dinga samun Mahabu ba domin nasha fad’a maku dama typing ga mai iyali yanada matuk’ar wahala, amma dukda haka dai zanyi iya bakin k’ok’arina wajen ganin abinda ya turewa buzu nad’i_
_Da banyi niyar fara tura maku ba har sai na kammala, to amma sai naga yin hakan kamar zai d’aukeni tsawon lokaci, shiyasa naga gara inayi ina tura maku a hankali yanda zai kasance harma na kammalasa batare dana ankara ba_
_Masu neman nasakasu a group da masu sakani ina fita, ina mai baku hak’uri wallahi bana yin group  kuma banida group amma badan bana so ba sai dan wani dalili na daban_
_Hakan nema yasa nake saka lambata a k’arshen littafin nawa saboda mai buk’atar ci gabansa_
_Ina masu cewa bana saka soyayya a cikin books dina ko kuma bana canza salon rubutuna? Kuyi hak’uri dukda har yanzu ni d’aliba ce acikin rubutu amma na fahimci cewa dukkan wani marubuci yakanyi rubutu ne akan abinda yake damunsa kuma yakeda ilimi akansa domin yaji dadin isar da sakon da yakeso ya isar, to nima ta wannan bangaren nake da ilimi kuma matsalar da nake yin rubutu akai itace tafi damuna a cikin zuciyata_
_Taya zanyi maku rubutu akan abinda banida ilimi akansa? Ina fatan zaku fahimceni?_
_Nagode da irin k’aunar da kuke nuna mani ko nace kuke cikin nuna mani, ni kuma insha Allahu bazan baku kunya ba_👏

 *SADAUKARWA*

_Wannan littafin Sadaukarwa ne ga K’asashe guda 2 wato Nageria da Nijar_
_Ina rokon Allah ya k’ara had’a kanmu ya kuma ha6ako mana da tattalin arzikinmu kana ya kawo mana zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali a cikin K’asashenmu da sauran K’asashen musulmi baki d’aya_
_Muje zuwa cikin Mahabu gadan-gadan._

*Mahabu*
Malam Audu ne zaune acikin d’akinsa yayinda ya saka ‘yarsa Indo a gaba yana yi mata nasiha gami da jan hankali akan sa6alli-kitar da takeso ta aikata da sunan soyayya
“Yanzu Uwata yin wannan auren kina ganin bazai haifar mana da d’a marar ido ba? Nida zaki bi ta tawa wallahi da Hashimu kika aura d’an gidan sarkin noma, amma ina amfanin ki auri mutum ko gama cin amarci bakuyi ba ya kama hanya ya tafi wata uwa duniya? Uwata kodai Hashimun ne baiyi maki ba?”
Ya k’arashe maganar tasa cikin alamu na lallashi, dayake sunan Mahaifiyarsa aka sakawa Indo d’in shiyasa yake kiranta da Uwata
Shuru Indo tayi na d’an wani lokaci, kasancewar duk wani abu da zai fito bakinta sa6anin abinda Mahaifin nata yake buk’ata ne shiyasa ta rasama abin cewa
“Uwata ki bani amsa mana kinyi shuru” ya sake maimaitawa karo na ba adadi 
“Baba nidai gaskiya da son samu ne da Mahabu d’in  kuka barni na aura domin yafi kwanta mani a acikin rai, amma Idan kunce Hashimun kukeso babu komai Baba sai na hak’ura da Mahabu d’in akwai”

Ta fad’a muryarta na sassark’ewa ga dukkan alamu dai inaga kuka take shirin yi
“Malam kaddai maganar nan da muka gama yi da kai d’azu itace kake maimaitawa yarinyar nan?”
Abinda Mahaifiyar Indo Inna Rabi kenan ta fad’a cikin alamu na fusata bayan ta d’aga labulen d’akin mai gidan nata Malam Audu, kana ta k’ara da cewa
“Ni banga illar auren wannan yaro Mahabu ba da kaketa k’ok’arin dak’ilewa, ai ni a ganina abin murna ne kuma abin farin ciki ne ace yau ga ‘yarka ta cikinka tana auren d’an Libi (dayake haka ake kiran hausawanmu maza mazauna kasar ta Libiya)
Ta k’ara da cewa 
“Malam indai ba so kakeyi na sakaka a cikin layin masu yi mana bak’in ciki ba dan Ya rasulullahi ka daina tada maganar nan ya isa haka, Indo dai Mahabu takeso shima Hashimun Allah ya bashi wadda ke sonshi ba shikenan ba?”
Tana gama fad’ar wa’yannan bak’ak’en magan-ganun nata ta saki labulen ta wuce abinta band’aki domin dama can ta nufa ta jiyo magan-ganun Malam d’in yayinda tazo giftawa ta k’ofar d’akin nasa.

****

Yau jumma’a da misalin kusan k’arfe takwas na dare a k’ofar wani gida mai farin fenti na hango dandazon ‘yan mata da samari kowa yaci kwalliya ya k’ure adaka abinsa sai hidimar gabansu sukeyi, wasu na fira da ‘yan matansu, wasu kuma samrin gabzar rake kawai sukeyi, yayinda wasu kuma sigari suketa faman busawa, kowa dai da kiwon da ya kar6eshi wai mak’wabcin mai Akuya ya sayi Kura.
Ga dukkan alamu dai ina tsammanin wani gagarumin biki ne suke gudanarwa a cikin wannan K’auyen nasu na Mayi wanda yake cikin K’asar Nijar
A  irin haka ne na hango wasu matasa guda biyu kyawawa kuma ajin farko
D’an bakin shine Mahabu yayinda Abokinsa Mamman shi kuma ya kasance fari, dukkansu ina tsammanin  shekarunsu bazasu gaza Ashirin da biyar biyar ba, inma zasu haura hakan to da kad’an ne nakega.
 Zaune a gefe guda bisa wani dakali suna d’an ta6a fira jefi-jefi, a 6angare guda kuma suna jiran k’arasowar Indo wacce ta kasance budurwa ga Mahabu kuma nan bada dad’ewa ba suma ake shirye-shiryen gudanar da nasu shagalin
A tsammanina zamansu anan su kad’ai yasamo asali ne na rashin hayaniya da basa so domin a kullum su basa yiwa kansu kallon yan K’auye, kullum su gani sukeyi hakan tamkar wani k’ask’anci ne agaresu.
“Kasan miye Mahabu?” Mamman ya tambaya tare da duban fuskar babban Aminin nasa cikin kulawa 
“Ina kuwa zan sani tunda ba fad’a mani kayi ba”

Ya fad’a a  tak’aice kuma cikin alamu na nuna basarwa
“Wallahi da ace nikeda budurwa zankad’ed’iyar zankad’aziya mai sona da k’aunata  kamar Indo wallahi da babu abinda zai kaini yin wata tafiya koda kuwa nanda Yamai ne neman kud’i bare kuma wai har nayi tunanin haurawa wata uwa duniya wai ita LIBIYA, anan kam gaskiya ina ganin wautarka abokina”
Murmushi Mahabu yayi, kana cikin isa da tak’ama  na yabon masoyiyarsa da akayi yace 
“Kace da ace kaine ko?”
Gyad’a kai Mamman yayi alamun amsawa
“To kuma sai akayi sa’a ba kai d’in bane ni ne, kaga kenan bai kamata ace kana damun kanka akan wannan ba ko?” Ya fad’a shek’ek’e cikin nuna alamu na ko in kula, kana ya k’ara da cewa 
“Kai Abokina har yanzu baka gane halin mata ba ne? Wallahi duk sanda mace  takeyi maka idan dai bakada kud’i wallahi a banza ne, kana ji kana gani zata gujeka  ta tafi gurin mai kud’in, ka fahimceni abokina? kud’i ba k’aramin k’arawa soyayya dank’o da k’arko sukeyi ba, saboda haka gaye ka nemi kud’i kawai kaga yanda mata zasu ringa bika, a lokacinma har yanga zaka dinga yi masu. 
Cikin sanyi jiki Mamman ya dubi abokin nasa domin ya fahimci Mahabu yayi nisa kuma ga dukkan alamu ba jin kira zaiyi ba 
“To nidai shawara ta k’arshe da zan baka itace, kawai ka hak’ura da auren yarinyar mutane tunda tafiya zakayi, kaga duk sadda kadawo sai kayi auren ka, karka fitar da yarinya cikin sahun ‘yan mata kuma bata shiga layin matan aure ba bare kuma a sakata layin zaw…
Katseshi Mahabu yayi domin ba jin dad’in zancen nasa yakeyi ba
“Babu abinda za’a fasa daga cikinsu insha Allahu, nanda wata 2 zan auri Indo kuma nanda wata 3 zan tafi Libie” Ya fad’a tare da wurgawa Mamman wata uwar harara 
“Ka tafi d’in, sakarai kawai banza, ni kuma ina mai tabbatar maka indai katafi Wabillahillazi ganima zamu  kwasa dani da sauran masu rabo” Ya fad’a yayinda yake yiwa abokin nasa dariyar k’eta 
Jijjiga kai Mahabu yayi tare  da ciza le6e, kana yace 
“Aiko da sai naci kut…
Kafin ya k’arasa ashar d’in da ya lailayo ne sukaji sallamar Indo a cikin zazzak’ar muryarta mai kama da ana busa sarewa
Mahabu ne ya rik’e baki tare da dukan bakin nasa lokaci guda”Shege baki mai yanka wuya, zaija mani masifa ina zaman zamana, Allah yasa dai bataji firar tamu ba kasan k’arya na shek’a mata akan cewa na fasa yin tafiyar”
Ya fad’a murya can k’asa-k’asa domin gudun kada masoyiyar tasa Indo tajiyo abinda yake fad’a dan dab take dasu
“Ko shanya ce aka shanya anan ai yaci ace ta bushe wannan zamanda mukayi anan” Abinda Mamman ya fad’a kenan yayinda ya mik’e tsaye yana dubanta tare da kakka6e k’urarada rigarsa ta kwasa a gurin
“Dan Allan kuyi h’akuri wallahi yanzunma da k’yar na samu na fito, kunsan babbar k’awa ita da Baranya koda yaushe anaso su kasance ne manne da amarya”
Ta fad’a yayinda ta langa6ar da kai alamun ban hak’uri tattare a fuskarta da kuma nadama sai kace wacce ta tabka wani babban kuskure 
Murmushi Mahabu yayi irin na masoyan da suka dad’e da macewa akan so da k’aunar junansu
“Nidai bani da matsala ta 6angarena domin kinsan bakya laifi a gurina, idanma kinyi laifin nakanyi sauri ne na d’auko yafiya gami da afuwa na ajiyesu a mazaunin da kikayi mani laifin, mita da k’ananan magan-ganun ai sai su o’i sai kace wata mace”
Ya fad’a yayinda yake duban fuskar abokin nasa Mamman gami da yi masa gwalo a kaikaice 
Shi dai Mamman baiyi yunk’urin mayar masa da wata amsa ba saima k’arawa gaba da yayi abinsa domin neman tasa masoyiyar Binta 
“To ya gajiyar biki” ya fad’a yayinda ya tattaro hankalinsa zuwa gareta
“Alhamdulillahi” ta fad’a a tak’aice
“Amma dai ai daga yau kun gama bikin naku tunda amarya ta iso gida ko?”
Zaro ido tayi cikin alamu na mamaki ta dubesa

“Inafa aka gama? Ka manta gobe ne zamu fara fita Gudun San Doki?”
“Gudun San Doki kuma? Mi ake nufi da ita wannan kalmar kuma ta gudun san doki?”

Ku biyoni domin jin ko menen gudun san doki, nasan da yawanku ‘yan burni baku san wannan kalmar ba ko?

Bara naga Comment dinku kun yaba da Mahabu ko kuwa dai bai gamsar da ku ba kamar sauran?👂
   Nice taku

 Maman Ja’afar

+966592551785

[3/19, 8:53 PM] Mmn Jafar M: 🌻MAHABU🌻
           2
Daga Alkalamin 

Maman Ja’afar✍

Gudun San Doki wata al’ada ce ta 6uya da amare kanyi suda k’awayensu yayinda aka kaisu gidan mazajensu
Sukan tafi ne gidajen tsofi su 6uya a k’ark’ashin gadonsu ko kuma cikin Rumbu da garken awakai ko mak’abartu da cikin gonaki da sauran dai guraren 6oyo inda baza ayi tsammanin suna nan ba
Yayinda su kuma dangin ango zasu bazama nemansu babu ji babu gani, wani lokacin su ganosu wani lokacin kuma har sai sun bayar da cin hanci a wasu daga cikin k’awayen amaryar su nuna masu inda suke suje su d’auko amaryarsu su dawo da ita

Sukanyi kamar kwana 5 zuwa sati suna wannan guje-gujen, idan an ganosu nan su koma can idan an gano can d’inma su k’ara yin gaba.

****

Langa6ar da kai tayi kana cikin zun6uro baki tace”Kai Mahabu yanzu tsabar gudun k’auyen da kakeyi har yasa ka fara mantawa da al’adunmu kuma?”
“No ba haka bane Indo kinsan tun tasowata ban cika zaman gida ba, nine bani Yamai bani Maradi bani Agadas wata ran kuma ina Nageria, sannan duk sadda zanzo gida cikin Damina nake zuwa kuma ke kanki kinsan ba aure akeyi ba cikin Damina ko?”
Sai yanzu tayi murmushi da ya bata hujjojinshi gamsassu, saboda ita a tsarinta ta tsani taji wata magana makamanciyar ta raini ga k’auyen nasu na Mayi 
“Wannan gudun na 6uya da akeyi idan aka kai…
D’aga mata hannu yayi alamun dakatarwa cikin murmushi
“Ba sai kin k’arasa ba nama  tuna, amma dai ai idan akayi bikinmu bazaki bisu wannan gudun haukan ba ko? Ko baki matsu ki ganni a matsayin mijinki ba kamar yanda ni na matsu ki zamo mallakina?”
Rufe fuskarta tayi da d’an yalolon mayafinta alamun kunya tare da yin murmushi 
“Kenan kanaso a sakani a gad’a kenan ana terere dani nakai kaina gidan miji ko?”
“Hakanefa kuma, na tuna har wata wak’a kuke yiwa wacce batayi ba ko? Um..Um.. yama wak’ar?”
Yayi shuru alamar tunani, zuwa can yayi  tsalle cikin murna sai kace wani d’an k’aramin yaro ya amsa tambaya dai-dai a makarantarsu

“Yauwa wallahi na tuna”
_*Ayye wance tayi abin kunya*_
_*Gudun san dokinma batajeshi ba*_
_*Ayye tayi abin kunya*_
_*Jaraba ce koko rashin kunya tayi*_
_*Ayye tayi abin kunya*_
_*Kodama fanko ce bamu lura ba*_
*Ayye…..*
“Dan Allah Mahabu wak’ar ta isa haka karka sa cikina ya k’ulle dan dariya”
Ta fad’a yayinda taketa faman k’yak’yata dariya harda dafe ciki
Shima dai cikin dariyar yace”To shikenan na daina, ai bazanso na k’ullarwa da masoyiyata ciki ba, wallahi Indo kullum haka nakeso naita ganinki cikin farin ciki da annashuwa, shiyasa nake k’ok’arin faranta maki duk ta hanyar da zan iya tunda Allah baiyoni mai kud’i ba”
B’ata rai tayi  kana ta dubesa ido cikin ido “kafara ba”
“Allah ya huci ran gimbiya na daina”
Cikin farin ciki da annashuwa suka gama firarsu irin ta masoya sukayi sallama kowa ya kama gabansa Indo ta koma ciki gurin amarya yayinda shi kuma Mahabu ya nufi Majalissarsu domin shan Ataye
Ataye wani shayi ne mai d’an karan dad’i da mutanen K’asar Nijar sukeyi, yana korar bacci kuma yana k’ara k’arfin jiki, amma dukda haka su Mahabu sai sun k’ara Alabukum a ciki ko kuma dai wata k’waya mai sa aji garau

*****

“Kai!Kai! Mahabu zo nan, ina zaka kaketa faman yin wani sand’a sai kace 6arawo? Kai a tunaninka nayi bacci tun d’azu ko? To idona biyu kuma badan komai nak’i yin baccin ba sai dan naga iya gudun ruwanka”
Cewar dattijo Malam Shehu kenan yayinda yake duban d’an nasa  cikin 6acin rai
Sosa k’eya nayi yayinda nake sissinar da kai alamun rashin gaskiya, domin a zahirin maganar gaskiya banyi tsammanin zan tarar da wani mahaluk’i idonsa 2 a cikin gidan nan ba, musamman ma  idan akayi la’akari da kusan k’arfe sha biyu na dare  yanzu, watak’ilma harda ‘yan mintina
“Wato ashe tun yamma da nace kabawa Tumakan can abinci k’in jin maganata kayi kasa k’afa kayi ficewarka ko? Shiyasa nace bazanyi bacci ba komin dare zakazo ka sameni kuma sai ka basu abincin sunci”
“Dan Allah Affa kayi hak’uri, wallahi bazan iya shiga wancen k’azamin garken ba duk ca6i yayi yawafa aciki” Na fad’a yayinda  nake zuzzun6uro baki
“Ba ca6i ba ko kwata ce yau sai ka shiga, yau inaso na gane ko wane ne uban tsakanina da kai” Ya fad’a rai a 6ace
“Allah ya baka hak’uri” na fad’a  a tak’aice tare da tattare sabon wandona na shige cikin garken
Nan dai bada dad’ewa ba zan huta da wannan wahalar insha Allahu, ina amfani mutum yana zaune a gari K’adago ma wannan ta gagaresa (Nera ashirin) mutum bazai samu kud’i ba har sai kaka tayi angama d’ebe amfanin gona, kome kakeso sai kaje kayi ‘yar murya kana a baka, ni wallahi ma har na matsu a gama bikin nan nawa nasan inda dare yayi mani.
Ina nan inata faman surutai na na zuci har nagama bawa tumakan abinci da ruwa na share gurin batare dana ankara ba.
Gun Karhi (randa) na nufa na d’ebo ruwa na shiga kewaye na wawwanke jikina kana na nufi d’akina domin kwanciya.
*Bayan wata biyu*
Dandazon  mutane ne na  hango a k’ofar gidansu Indo mata da maza yara da tsofi sai faman turereniya sukeyi domin ganin wani abu, wa’yandama tsawonsu bai kai ba har d’orasu naga anayi a kafad’a domin suma su ganewa idanuwansu….
Gaskiya kaina ya kulle, wai mike faruwa ne haka?
Kuyi hakuri da kadan👏
    Nice taku 

 Maman Ja’afar

+966592551785

[3/21, 4:47 AM] Mmn Jafar M: 🌻MAHABU🌻
            3
Daga Alkalamin 

Maman Ja’afar✍

Mutane ne na hango dank’am sun cika sun batse, kowa soyake ya ganewa idanuwanshi abinda ke faruwa a gurin
Can cikin gidan na k’ara hangawa, Indo ce na gani zaune tsakar gida akan d’an k’aramin turmi daga ita sai ‘yar shime da d’an kamfai sai faman rabsa kuka takeyi tamkar ranta zai fita
Yayinda na hango wata ‘yar tsohuwa mai kimanin kusan shekaru sittin a duniya rik’e da wata k’warya sai ya6a mata lalle takeyi ta ko ina, tana yi tana had’awa da ‘yan wak’e-wak’ensu irin na sakun lalle
*Dangani daure d’iyar Nana*

*Dangani daure d’iyar Nana*

*Aure ba mutuwa bane*

*Shi kuma ba yak’i ne ba..*
Yayinda su kuma k’awayen amarya da sauran ‘yan kallo sukeyi mata amshi.
And’au kusan minti ar’ba’in ana yin wannan wanka a bainar jama’a kana daga bisani aka kammala amarya ta nufi d’aki domin ta saya jikinta.
Mahabu ne zaune akan k’atuwar tabarmar kaba dashi da abokinsa Mamman , kowa yaci kwalliya ya k’ure adaka da k’ananun kaya har wani tokewa da zanzaro sukayi
Suma dai nan 6angaren angon gabatar da nasu shagul-gulan bikin sukeyi, sai dai su Inga tsiyar dangi suke gudanarwa yau, ga dukkan alamu an dad’e da sawa ango lalle ta 6angarensu, sa6anin gidansu Indo da akeyin sakun lalle yau.
Inga tsiyar dangi itama wata al’ada ce da akeyi tsakanin duka gidajen guda 2 sai dai kowa da ranar da yake gudanar da nasa inga tsiyar 
Tabarmar kaba k’atuwa ake shinfid’awa a tsakar gida, yayinda ango ko amarya zasu zazzauna dasu da makusantansu guda d’aya ko biyu, ‘yan’uwa da abokan arziki kuma kowa zaizo ya ajiye gudunmuwarsa a wannan tabarmar, yayinda mai shela shi kuma zai d’inga d’aga sauti yana fad’awa jama’a adadin kud’in da kowa ya bayar domin ango ya hardace saboda ranar mayarwa.
Sai zubawa Mahabu kud’i akeyi amma a yanda na fahimta kwata-kwata shi hankalin sam bama akan kud’in yake ba
Cikin damuwa Mahabu ya dubi Mamman tare da yin K’asa-k’asa  da muryarshi domin gurin dank’am yake da cukowar jama’a 
“Mamman yanzu hakafa k’artin banza suna can suna kalle mani matar da za’a kawo mani gobe ko?”
Harararsa yayi cikin wasa domin indai da sabo yaci ace Mamman ya saba da ‘yan k’orafe-k’orafen Mahabu
“Matarka ita kad’aice mata? Sauran matan da akeyiwa fa? Kosu ba mata bane?Karka manta tun kamin a haifemu akeyin irin wannan al’adar kaga ko dolenka ko kanaso ko bakaso a gane maka mata tunda an saba anayin abu baka isa kazo rana tsaka kace kai ba za’a ayi maka ba, duka matar takama a nawa take? Shekara sha biyar ta wuce wanka ne a tsakar gida?”
Mintsininsa yayi ta yanda jama’a bazasu ganshi ba
“Kaifa wani lokaci mahaukaci ne, bansanma me ya kaini fad’a maka damuwata ba”
Murmushin k’eta Mamman yayi “To kai abokina me ya hana ka fad’awa iyayenta tun farko bakason ayi mata wanka?”
Bai ce masa komai ba saima duk’ar da kansa da yayi k’asa na d’an wani lokaci, kana daga bisani yayi k’wafa 
“Allah dai ya tsinewa wannan shegiyar al’adar ya nuna mana ranar da za’a dainata” Ya fad’a a bayyane 
Dariya Mamman ya bisa da ita
“Yekuwa jama’a! Tanimu wanzan abokin ango ya bada jaka biyar” Cewar marok’in kenan yayinda yake d’aga kud’in sama domin nunawa jama’a kowa ya gani
Da wannan suka maido hankullansu gurin inga tsiyar dangin da ake gudanarwa
“Ammafa mutumina Tanimu ya k’ok’arta ba laifi fa” 
“Dayake kyauta ya bani ba, ko ka manta ga bikinsa jaka hud’u na saka mashi a inga tsiyar dangi?” Ya fad’a rai a 6ace
“Allah ya huci zuciyar ango, maida wuk’aken domin nidai muna nan tare dakai tun d’azu bare ko kayi tunanin nima naje kallon sakun lallen ne da kaketa faman yi mani muzurai”
Yana gama fad’ar haka ya mik’e tsaye yana lalubar aljuhunsa domin bayar da tashi gudunmuwar shima.

*****

*Washe gari da daddare*
Indo ce goye a bayan wata tsohuwa tayi luf sai kace wata ‘yar k’aramar yarinya, yayinda ‘yan rakiyarsu suke biye dasu a baya suna tafiya suna raira ‘yan wak’ok’insu irin na rakiyar amarya d’akin mijinta

Su kuma ‘yan rakiyar amaryar suna biye dasu abaya suna amsawa
A haka har suka iso k’ofar gidan na Malam Shehu tsohuwar ta sauketa a k’ofar gidan aka mik’a mata tsintsiyar laushi a hannun dama hannun hagun kuma aka bata Sahwani ta rik’e (buta) kana daga bisani aka bata umarni da tayi bisimillah kana ta fara shiga da k’afarta ta dama.
Kamin kace me gidan anguna ya kaure da gud’a ta ko ina, kowa ka kalla a wannan lokacin fuskarsa na cikin farin ciki da annashuwa, sai ‘yan d’ai-d’aikun mutane da ba’a rasa ba daga 6angaren su Hashimu.

****

*Washe gari*

Akayiwa amarya jerenta mai d’an karen kyau, Samiru kusan saiti ashirin aka jejjera mata a cikin kwabet d’inta, yayinda su kuma K’waraye aka jejjera matasu a can saman kwabet d’in, sai ‘yan fanteku da kuma languna nacin abincin yau da kullum
Gado kuwa guda biyu akayi mata dan gata, da babba mai rumfa sai kuma d’an  madaidaici a K’asa, tabarmin roba ma har uku aka kai mata, ta kaba kuma guda d’aya, d’aki dai ya had’u iya had’uwa sai fatan su Indo Allah ya bada zaman lafiya da kuma zuri’a d’ayyiba.

*****

Washe gari akayi tuwon uwar d’iya tare da unbande(kayanda ake rabawa ango da ‘yan’uwansa daga gidansu amarya)da daddare kuma k’awayen amarya sukayi da huwarsu ta 6arna inda komai suka zubashi oba, suna ci man shanu na bin hannayensu
“Yanzu Lantu a ina zamu fara zuwa 6oyon kenan?” Cewar d’aya daga cikin k’awayen amaryar kenan yayinda dafa dukan shinkafa ya kai mata karo
Wacce aka kira da Lantu shuru tayi alamun nazari kana daga bisani kuma tace

“Ina ganin kawai mu fara ta gidan gwaggo, kunsan ta tsufa sosai ba gani takeyi garau ba barema idan anzo nemanmu har tayi tunanin fallasamu”
Da wannan shawarar ‘yan matan amarayar sukayi sauri suka gama abinda sukeyi suka fice daga gidan a lokacin kusan k’arfe sha biyu na dare
Inna Fure maihaifiya kenan ga ango, tsohuwa yar kimanin shekaru hamsin abduniya ta fito zata zagaya ta gansu suna sand’a d’aya bayan d’aya suna ficewa daga gidan batare da yin ko k’wak’waran motsi ba
Batayi tunanin ce masu komai  ba saima  murmushi da tayi ta wuce band’aki abinta.

 *****

Gudun san dokinsu Indo bai wani d’au lokaci ba suka gamasa kasancewar ba wani goyon bayan kirki amaryar ke basu ba, a k’arshema ita tabada shawarar aje 6uya gidan Yayar Mahabu, batare da 6ata lokaci ba kuwa aka ganosu a can aka mayar da amarya d’akin mijinta 
Badan komai Indo tayi hakan ba sai dan sanin kanta ne Mahabu ba san wa’yannan  ‘yan guje-gujen yakeyi ba, itako ta tsani abinda  zai 6ata ran Mahabu duk k’ank’antarsa kuwa.

******

*Bayan sati uku*
Mahabu ne zaune a

gaban Indo sai faman dibi-dibi yakeyi, yanaso ya fad’a mata maganar  tafiyarsa Libiya nanda sati d’aya kuma yana jin tsoron abinda ka iya biyo bayan  furta zancen nasa da yaketa faman 6oyewa domin tun kamin d’aura aurensu ya tabbatar mata da yafasa yin wannan tafiyar, shiyasama ta saki jiki sosai dashi
“Mahabu lafiya kuwa ka tasani a gaba  sai faman kallo kake? Tun d’azun nace maka na zuba surfen tsaba (gero) a turmi, yanzu hakama ya kusan jik’ewa, kai baka barni naje nayi surfen ba kuma kai baka fad’a mun abinda  kakeso ka fada mani ba, ko so kake nayi daren tuwo ne yau?”
Sosa k’eya yayi kana daga bisani yayi k’arfin hali ya daure yayi ta maza ya dubeta jiki a sanyaye
“Dama..kan maganar tafiyata..Libei ne nakeso na fad’a maki..ina ganinma indai tafiyar ta  tabbata ran kasuwar tasawa nake ganin zamu wuce (ranar lahadi kenan) Yana magana yana inda-inda sai kace wani marar gaskiya
Duk’wa tayi a gabansa ta d’auki k’waryar furarda ke gabansa wacce ya shanye furar tun d’azun amma bai daina juya ludayin a cikin k’waryar ba saboda jimamin magan-ganun dake shirin fitowa daga bakinsa
Saida tayi murmushi  kana ta nufi bakin k’ofar d’akin, d’aga labulen d’akin tayi kana ta waiwayo ta dubeshi
“Yau kuma zaulayar ta wannan 6angaren ta motsa maka? To a canza wani salon wasan domin wannan wasan bai gamsar dani ba….

Har yanzu dai shinfid’a mukeyi domin  bamu shigo cikin labarin Mahabu gadan-gadan ba
    Nice taku 

  Maman Ja’afar

 +966592551785

[3/22, 5:52 AM] Mmn Jafar M: 🌻MAHABU🌻
            4
Daga Alkalamin 

Maman Ja’afar✍

“Kinga Indo dawo dan Allah ki zauna magana ce zamuyi ta fahimta, karki damu da jik’ewar hatsi ai a kwai wani a runbu idan ya jik’e sai a d’ebo wani”
Da jin wannan kalamin nasa jikinta yayi sanyi, hakanan a sanyaye ta dawo d’akin ta zauna dab dashi tayi tagumi da hannayenta duka biyun, ga dukkan alamu shi take sauraro
“Indo dan Allah idan na fad’a maki kada kiyi mani mummunar fahimta kinji?”
“Uhm ina jinka Mahabu fad’a  mani abinda kakeson fad’a mani kawai basai ka tsaya yin wani dogon sharhi ba”
Baiji dad’in ganin yanda yanayinta ya sauya lokaci guda ba, amma sai dai bashida mafitar da ta wuce ya sanar mata d’in, domin ko bata sani ba yanzu dolen sa dai ranar da zaiyi tafiya sai yayi mata bankwana 
“Maganar tafiya Libei ce dama nakeso nayi maki kin mayar da ita wasa, wallahi fa da gaske nakeyi rana yata yau zan tafi insha Allahu”
Fad’uwar gaba taji likaci guda tare da zubar wasu zafafan hawaye batare da ta ankara ba
“Yanzu Mahabu hakan da kayi mani yaudara za’a kirashi ko kuma rashin adalci? Kasan kuwa irin yak’inda nayi kafin na zamo matarka? Haba Mahabu dan Allah karka yi mani haka mana wallahi zanji kunya agurin Affana idan ya samu wannan labarin”
Ta fad’a yayinda ta rungumesa tare da sakin wani tsanancin kuka mai ban tausayi sai kace wacce  aka aikowa da sak’on mutuwa
“Haba Indo ki fahimceni mana, tafiyar nanfa da zanyi badan buk’atuna kawai zanyita ba ni kad’ai a’a harda naki buk’atun da kuma na yaran da zamu haifa nan gaba, ni a ganina tafiyar tamkar wani rufin asiri ne agaremu dagani harke baki d’aya, kina ganifa idan akace maki garin Allah ya waye ko Biye(Nera ashirin) da zan baki ki siyi ‘yar tsala(wainar cikin mai)bani da ita sai kinje gurin Affa ya baki, banida ikon cin abinda nakeso a gidana sai wanda akaga dama aka girka, ko salla tazo Affa ne keyi mani kayan salla, idan kin ganni cikin kud’i  to kaka ce tayi an gama kammala amfanin gona zan dinga d’iba ina sayarwa domin saka canjin a aljihuna, yanzu inba dan rashin kud’in ba taya zan zauna gida d’aya da iyayena Indo? Maganar gaskiya Aisha sai dai ki sawa ranki hak’uri amma tafiya kam babu fashi”
Da gama jin wannan dogon sharhin nasa wanda ya tabbatar mata da cewa lallai bata isa ta hanashi yin wannan tafiyar ba ta k’ara rushewa da wani uban kuka tamkar ana yayyanka naman jikinta
“Yanzu Mahabu kana nufin kaima idan ka tafi sai nayi shekara da shekaru ban ganka ba kenan? Haba Mahabu  kaji tausayina mana karkasa duniya tayi mana dariya, Mahabu ka tuna so da k’aunar da ke tsakaninmu mana, ko har ka manta ne? Wai Mahabu  kodai har kafara gajiya dani ne tun yanzu? dan naji dama wasu matan suna cewa wai amarcin yanzu dama na wata d’aya ne, har a lokacin ina k’aryatasu ina cewa nidai namu amarcin dani da kai na har abada ne insha Allahu, kaddai kace mani maganarsu ce ke shirin tabbatuwa akanmu?”
Jawota yayi ya k’ara rungumiwa a jikinsa yana bubbugar bayanta alamun rarrashi, domin ga dukkan alamu wa’yannan  sabbatun da takeyi sun kusan fitar da ita daga cikin hayyacinta
Ba shakka yarinyar ta basa tausayi, sai dai da zama cikin irin wannan k’asurgumin talaucin ya gwammace ya jure tausayin nata nad’an wani lokaci, domin nanda gaba kad’an saita fi kowa murna da yin wannan tafiyar insha Allahu.
“Mahabu lafiya kuwa nake jiyo wani abu kamar tashin kuka daga d’akinku?”

Cewar mahaifiyarsa kenan yayain da ta raka6e daga bakin k’ofar d’akin tare da jimamin abinda ke faruwa a cikin d’akin 
“Ina Indo d’in take ne ko itace mai yin kukan?”
“Inna babu komai fa, kilanma kukan D’an marak’i(Sa)ne kikaji kike tsammanin kukan mutum ne” ya fad’a yayinda yake yiwa Indo nuni data goge hawayenta domin kada Inna ta fahimci abinda ke faruwa
“To shikenan”

“Indo! Dan Allah zo ki tayani sissika kinji? tun d’azun naketa famanyi amma har yanzu dawar tak’i k’arewa sai kace k’arota akeyi”
Simi-simi Indo ta fito daga cikin d’akin ido jawur sai kace anyi mata feshin barkono
“Ja’irin Yaro, kace mani ba a d’akinku nake jiyo tashin kukan ba? Ga idanuwan yarinya nan sunyi jajir sai kace wadda aka bad’awa tasshi(yaji) kodai kaima irin mazan nan ne masu dukan matayensu?”
“Haba Inna, Allah ya sauwak’e na d’aga hannuna da sunan zan daki mace barema matar da nake aure, kawai kan maganar tafiyata Libei ne danayi mata maganar shine take kuka” Ya fad’a yayinda yake shirin fitowa daga d’akin
“Wai da gaske haka ne Indo?”
D’aga mata kai tayi alamun amsawa 
Nan take tsohuwar ta d’aure fuska tamau tamkar ba ita bace ta gama duban  Indo da sigar tausayi d’azu ba
“Inma zaki daina wannan kukan shagwa6ar garama tin wuri ki daina domin dagani har babanshi babuwanda bai amince masa yayi wannan tafiyar ba, sai ke rana tsaka zakizo mana da wani kinibibi?”
Rik’e baki tsohuwar tayi kana ta k’ara da cewa
“Ni tunda nakema nata6a ganin jarababbiyar yarinya irinki Indo? ‘Yar mitsitsiyar yarinya dake amma kullum kina nane da miji? harda wani iya yin wai bakiso ya tafi nema? Wannan zamani! Allah dai ya fitar damu lafiya daga cikinshi”
“Inna ayi mata a hankali  har yanzu Indo yarinya ce fa” ya fad’a cikin yanayi na 6acin rai, dan dai ba yanda ya iya ne amma da yanada iko da ya dakatar da Mahaifiyar tasa wad’annan ‘yan magan-ganun da takeyiwa abar k’aunarsa
“To tantabara sarkin aure ai sai kazo ka dakeni sabida na ta6a maka ‘yar lele ko?
Indo dai bata tsaya ta ida jin k’arshen maganar tata ba, ta kaikaita ta shige d’akinta tare da d’auko mayafi ta yafa ta kama hanyar gidansu, tana tafiya hawaye na bin fuskarta
“Ke Indo zo mana, ina zakije ne haka kina kuka? Dan Allah dawo karkije kiyi mani bak’in fenti a wajen iyayenki” Mahabu ne mai fad’ar haka yayinda yake binta a baya
“Barta ta tafi mana ai bamu kad’ai za’a zaga ba harda ita, ace aure ko wata guda baiyi ba har ta fara yin yaji”
Bai bi ta kan uwar ba saima k’ara azama da yayi wajen k’ok’arin dakatar da Indo d’in abinda take shirin aiwatarwa.
 ****

Inna Rabi ce na hango k’ark’ashin bishiyar da ke tsakar gidan d’aure da d’aurin k’irji, kan nata kuwa ko d’ankwali babu, tana daka cikin k’warewa tana tilla ta6aryarta tana cafewa cikin nishad’i abinta, wani lokacin ma harda ‘yan wake-wakenta na habauci take had’awa
Tana cikin haka ne ta hangi tahowar Indo ta bayan zanar da aka kewaye gidan da ita, dayake zanar ba wani tsayin kirki ne da ita ba shiyasa wani lokacinma zaka iya hangen mai wucewa ta k’ofar gidan, musamman ma dogaye irinsu Indo
Da shigowar Indo ta sake rushewa da wani sabon kukan
Cikin tashin hankali uwar ta tarota da sauri”Indo lafiya dai ko? Ko mutuwa akayine a gidan naku? Kai ina tsammanin ba mutuwa bace domin da ace mutuwa ce na tabbata koke-kokenda za’ayi a gidan naku muma zamu iya jiyowa daga nan tunda ba wani nisan kirki ne a tsakaninmu ba”
Uwar sai faman jero mata tambayoyi take amma Indo babu abinda takeyi face rabsar kukanta
Saida uwar ta daka mata tsawa da k’arfi tukunna ta dawo hayyacinta 
“Dama Inna ashe wai Mahabu bai fasa yin tafiya Libei d’in ba k’arya yayi mun yace yafasa? wai sai d’azu ne yake shaida mani wai wai yau saura sati d’aya ya taf…
“Shine ke kuma kika kwaso tsumman k’afarki  da nufin yin yaji ko kuma kawo k’ararsa gurinmu ko?”
Cewar Malam Audu kenan Wanda shigowarsa gidan kenan yanzu….
  Maman Ja’afar 

+966592551785

[3/23, 6:50 AM] Mmn Jafar M: [23/03, 6:36 a.m.]

🌻MAHABU🌻
           5
Daga Alkalamin 

Maman Ja’afar✍

Malam Audu yaci gaba da banbamin fad’ansa
“Tun farko saida nayi k’ok’arin tunatar dake irin wannan ranar tana zuwa amma kikayi kunnen uwar shegu da magana ke ga ‘yar sarkin masu soyayya, saboda haka tun wuri ina mai gargad’inki tun kamin na zuciya na 6a66ala maki k’afafuwa garama ki bar gidan nan tun wuri, kije can soyayyar taki tayi maki maganin matsalarki”
Yana gama fad’ar wannan maganar ya shige d’aki abinsa ko kallon inda matar tasama take baiyi ba
Cikin d’aga sauti Inna Rabi ta bisa da “Aiko babu inda zata tafi batare da anzo anyi bikonta ba, ehe”
Kana ta juyo kan d’iyar tata
Cikin siga ta lallashi ta dube ta tare da yin kasa-kasa da murya
“Keko Indo me ya kaiki dawowa gida da sunan yin yaji bayan bikinki duka-duka ko wata d’aya bai cika ba? A gaban idonki dai idan aka kai amarya wata saita shekare cur bata fita ko nan da can ba, mai d’an sauk’in kunya ce zata fita bayan wata shidda, so kike ki jamana abin magana ne a gari? Ki dubafa ki gani yayunki Hansatu da Rakiya yau kusan shekarunsu hud’u-hud’u a d’akin miji amma babu wacce kika ta6a ganin  ta lek’o gidan nan da sunan yin yaji, sai ke da suke ganin kamar nafi fifitaki akansu ace an fara samun 6araka daga gareki? Haba Auta a dinga hak’uri mana”
“Inna idan ya tafi fa sai yayi shekara da shekaru bai dawo ba ni shine damuwata fa” ta fad’a tare da zuzzun6uro baki harda wani harba k’afafuwa
“Idan kikayi hak’uri kuma Indo ai shekarar kamar kwana ce, kuma nasan dai yanda Mahabu yake matuk’ar k’auanarki na tabbata bazai wuce shekara d’aya zuwa biyu ba zai dawo gida”
“Inna to idan ya tafi ni miye matsayina kenan?”
Cikin alamu na 6acin rai uwar ta dakatar da ita
“Ni kam Indo matsalata dake shegen tambayoyin bin k’wakk’wafin tsiya, ke inma baya ga wauta dake damunki tafiyar tasa ba gata bane agareki? Ki duba kiganifa duk wa’yanda mazajensu suke Libei zaki gansu sunsha banban da sauran mata, saboda kusan duk wata d’aya biyu sai sunyo masu aiken kud’i atamfofi sabullai mayuka, ke har turarema aiko masu sukeyi, to me yafi wannan jin dad’in duniya? Bakiga wasu matanma har bak’in ciki sukeyi maki ba dan kin auri wanda zaya Libei? Dan Allah Indo ki kwantar da hankalinki ki bashi goyon baya d’ari bisa d’ari yayi  wannan tafiyar kinji Auta? Wannan tafiyar fa idan yayi bake ba harma mu iyayenki sai mun amfana da ita, ko dai nakison ganinmu cikin farin ciki ne?”
Murmushin yak’e tayi wanda  naji hausawa suna yi masa kirari da kafi kuka ciwo
“To Inna babu komai na amince Allah ya kaishi lafiya ya dawo mana dashi lafiya”
“Yauwa to koke fa ‘yar albarka? Shiga d’akina akwai Hura na nan a saman Ragaya ki d’auko kisha yanzun nan na gama damata kuma taji kindirmo sosai harma mai zaki gani a samanta ya d’an  kwanta, irin damunki ne nayi yanda kikasan dama kin sanar dani zakizo”
Dayake Indo masoyiya ce ga hura wacce taji nono sosai shiyasa da gudu ta shiga d’akin ta  sauko hurar daga kan ragaya inda aka d’orata ta zauna k’asa dirshan ta fara kwankwad’ar furar abinta.
Da wannan uwar ta samu ta lalla6a ta shawo kan ‘yar tata har zuwa dare lokacin da ‘yan biko sukazo aka basu ita suka d’auketa suka mayar da ita d’akin  mijinta.

****

Tun daga wannan lokacin Indo ta daina nuna damuwarta akan tafiyar da Mahabu zaiyi

Sai dai hakan bawai yana nufin da ta daina damuwar bane kwata-kwata, a’a  damuwa na nan dank’are a cikin zuciyarta dandai kawai bata da mai share mata hawayene shiyasa ta bar abin iya ranta, dan hakanema duk ta wani rame ta fige ta lalace dama gata ba wata k’ibar kirki ba, kuma sai gashi damuwa tazo tayi mata yawa ga kuma alamun shigar sabon ciki a jikinta na kusan wata d’aya

Ana dara ga dare yayi.

****

Tafiyar Mahabu ta rage saura kwana 3 Mahaifinsa ya basa umarni da yashiga runbu ya d’ebo wake kimanin buhu uku yaje kasuwar Isawan ya siyar domin k’arin guzurin tafiyarsa
Itama Mahaifiyar Mahabu ba a barta a baya ba domin k’aton d’an marak’inta ta kwance ta siyar ta mik’awa Mahabu kud’in domin ya k’ara yayi guzurin tafiyar da ke gabansa.

****

Yau mun wayi gari ranar Alhamis wanda gobe Jumma’a kenan mukesa ran tafiyar Mahabu ta kama
Har Indo tayi nisa a cikin baccinta taji Mahabu na tashinta
“Indo tashi muyi magana kinji?”
Dak’yar ta samu ta wartsake daga nannauyan baccinda yayi awon gaba da ita, cikin layi irin na mai jin bacci ta dubesa
“Lafiya dai Mahabu ko?”
“Lafiya lau Indo, kinsan gobe ne zan tafi ko?’
“Eh” ta fad’a a tak’aice 
“Dan Allah Indo ki cire damuwa a cikin ranki, insha Allahu kamar yau ne zakiga nadawo munci gaba da zamanmu cikin so da k’aunar juna kamar yanda muka fara kinji?”
Duk da k’ok’arin da tayi wajen takawa kukanda ke yunk’uro mata birki amma hakan bai yiyu ba saida kukan ya kubce mata ya fito
Yarfa hannuwa yayi kana yace
“Kinga irinta ba? Shiaysa hankalina ya kasa kwanciya wallahi, saboda kullum tunani nakeyi da zarar na sa k’afa na tafi baki da wanda zaki mayar abokinki face kuka, dan Allah Indo ki daina kada kije garin kuka wani kije wani ciwoma yazo ya sameki”
D’ankwalinta tasa tana goge hawayenda keta faman shatata a fuskarta
“Indo so nake kiyi mani alk’awarin bazakiyi kuka ba ko bayan na tafi, kiyi mani alk’awarin zakici gaba da mu’amalolinki tamkar ina nan kinji? Ni idan kikayi mani haka kin gama mani komai”
Ya fad’a yayinda ya rungumeta a jikishi yana mai dadda6ar bayanta alamun rarrashi
Cikin shesshek’a tace”insha Allahu bazanyi ba, amma Mahabu idan ka tafi sai yaushe zaka dawo kenan? K’ilanma har sai na haihu yaron ya girma baka dawo bako?”
Jikinsa yayi sanyi matuk’a da jin wannan kalamin nata
“Nidai kwanciyar hankalinki kawai shine damuwata Indo, amma maganar dawowata ai ba dad’ewa zanyi ba, kika sanima ko ina can na aiko kud’i a d’auko mani ke?” Ya k’arashe maganr tasa cikin murmushi
Itama dai murmushin ta mayar masa dashi, kana yaci gaba da cewa
“Ko bayan na tafi idan kina da buk’atar wani abu ki nemi Mamman zai baki, domin akwai kud’in da nabashi dan kawai kula dake, saboda nasan idan na bawa Inna ba lallai ta bakisu a sadda kike buk’ata ba, har kud’in ragoma duk na bar masa suna hannunshi, addu’a kawai ta rage mana, muyi fatan Allah ya kaini lafiya ke kuma Allah ya saukeki lafiya koba haka ba?”
A ranar dukkansu babu wanda yayi wani baccin kirki, kawai dai sun kwanta ne amma kowa da tunaninda ya addabi zuciyarshi.

*****

■Washe gari■
Tun safe Mahabu ya gama kimtsa komai nasa Amalanke kawai yake jira
 Mamman da Tanimu ne sukazo da Amalanke, batare da 6ata loakci ba suka d’ebi Mahabu dashi da Mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa
Indo dai bata samu damar zuwa yin rakiyar ba saboda tun cikin dare ta tashi da wani matsanancin zazza6i.
Har zuwa cikin garin tasawa ‘yan rakiyar suka kaisa, tunda dama tsakanin Mayi da tasawa indai a amalanke ne tafiyar batafi ta mintin arba’in zuwa awa d’aya ba…..
A garin tasawa ne tushen labarin tafiyar Mahabu K’asar Libei ya fara

 Maman Ja’afar

+966592551785

[3/25, 8:08 AM] Mmn Jafar M: 🌻MAHABU🌻
            6
Daga Alkalamin 

Maman Ja’afar✍

Cikin  jimami gami da kewar juna sukayi sallama yayinda su Mamman suka nufi hanyar komawa gida shi kuma Mahabu ya k’ara nausawa cikin tasha domin neman motar da zata sadashi da Damagaran
Bai wani 6ata lokaci ba gurin samun motar “Dan Allah wannan motar Damagaran zata tafi?”

Ya tambayi wani d’an saurayi wanda yake jingine a bayan wata rakwa6a66iyar mota
“Eh can zata tafi saidai ba yanzu take tashi ba”
“Kamar ya? bayan naga kuma motar a cike?” Ya fad’a cikin alamun mamaki
“Kai karka dameni da tambayoyi mana, to ba yanzu take tashi ba sai bayan sallar juma’a, shikenan ko?”

Da gama fad’ar haka saurayin ya zagaya ya shige cikin motar abinsa ya zauna
Shima dai Mahabu bai tsaya k’ara neman ba’asi ba ya d’auki jakarshi gari yayi zafi shima ya shiga cikin motar ya zauna.
Kamar kuwa yanda karen motar ya fad’a, ana tasowa daga sallar juma’a motarsu Mahabu ta tashi, kamin wannan lokacin dama ta riga ta gama cika da mutane.
*****

“Inna har kun dawo daga rakiyar ‘yan Libei d’in?” Cewar Indo kenan wacce tun tafiyarsu take kwance a bakin k’ofar d’akinta sai faman murk’ususu takeyi
“Eh wallahi, ke dai bari ‘yar nan abin gwanin tausayi, yanda kikasan ince yafasa yin tafiyar nan mu dawo gida tare”
Da jin wannan maganar aiko sai hawaye shar-shar tamkar dama jira takeyi
“A’a kaddai kice mani zazza6in ne har yanzu bai sakeki ba?”
“Eh amma da d’an sauk’i yanzu” ta fad’a a tak’aice
“To sannu, shiga d’aki  kid’an mik’e ko kya samu kiji d’an dama-dama kamin Affanku ya dawo daga daji na jik’a maki hararra6i da sabara dama kamin ya tafi na bashi sallahunsu(Sako)
“To Inna”
Da k’yar ta samu ta rarrafa ta shiga d’akin, tana shiga kuwa batai wata-wata ba ta fara sana’ar tata wato kuka.
******
Dukda motar da su Mahabu suka shiga rakwa6a66iya ce amma hakan bai hanasu tsula gudu a hanya ba
Sunyi nisa sosai a cikin tafiyar tasu suka hango Jandarmomi tsaitsaye akan hanya (Gate)
“Ina masu karti? (Takardar zaman k’asa) kuyi sauri ku fiddo kamin mu k’arasa gunsu”
Cikin sauri kowa ya firfitar da takardar daga aljihunshi, banda Mahabu wanda ya baro tashi gida a tsammaninshi takardar batada wani amfanin kirki akan hanyar Libei d’in
Suna k’arasowa dab dasu Jandarmonin basu nemi wani k’arin bayani ba sai neman takardun kamar dai yanda dama direban ya fad’a masu tun abaya
Masu takardu suka babbayar suko su Mahabu da basu da ita aka cajesu jaka d’aya- d’aya(jaka d’aya ta nijar kimanin dari biyu kenan koda hamsin amma yanzu bansani ba tunda nerar tamu har yanzu batada tsayayyen farashi)
Da isarsu cikin garin Damagaram basu wani tsaya 6ata lokaci ba suka nemi masallaci sukayi sallar la’asar, amma shi Mahabu harda azahar ya had’a yayi dayake dama a tasawa bai tsaya ya sallaci jumma’a ba
Da gama sallarsu suka nufi wurin mai abinci aka zubo masu farar shinka da miyar yakuwa (abinci mafi soyuwa kenan ga mutanen garin) suka shararra6i abinsu, suka k’ara nausawa tasha domin neman motar da zata kaisu garin Adarbiso
Basu sha waa wahala sosai ba wajen samun motar Adarbiso d’in, shima d’an zagayen da sukayi cikin tasha dandai basu san cikin garin bane ba shiyasa.
“Adarbiso! Adarbiso! Saura mutum hud’u ta cika” cewar wani k’aren mota  kenan yayinda yaketa faman safa da marwa a tsakanin motocin
Dayake dama su uku ne kad’ai  zasu shiga motar Adarbiso d’in  sauran mutanen duk iya Damagaran dama tafiyarsu ta tsaya
Wasu sunzo neman kudi, yayinda wasu kuma zumunci ne ya kawosu garin na Damagaran d’in. 
“To kai Kare mu nan mu uku ne ya za’ayi? Zaku jamu mu wuce Adarbiso d’in ne ko kuwa a dole sai kun sami cikon mutum d’ayan?”
Cewar Sa’adu kenan d’aya daga cikin abokan tafiyar na Mahabu
Ko kallon inda sukema baiyi ba saima ci gaba da neman fasinjansa da yaci gaba dayi
“Bawan Allah maganafa mukeyi maka ka mayar damu wasu dutsina” cewar Mahabu kenan bayan ya dafa Karen motar
“To ai ji nayi yace kare! Ni kuma na tabbata duk nan cikinmu babu kare inba shiba shiyasa na ajeshi a jerin mahaukata naci gaba  da abinda ya dameni tunda ni inada aikin yi”
“Allah ya baka hakuri, yanzu ma iya shiga mu zauna daga ciki ko kuwa?” Cewar Abashe kenan cikon na ukun wanda zasu wuce Adarbiso d’in tare
“Kwa iya shiga, amma dai kai yakamata kaje ka koyo magana dan na lura ba iyata kayi sosai ba” ya fad’a  tare da duban fuskar Sa’adu wacce tayi bak’i ta rine dan tsabar shan sigari.
Koda shigarsu mai motar bai tsaya ida jiran mutum d’ayan ba ya tada motarsa suka lula.
******
“Ummaru! Ummaru! Indo ce kwance a tsakar d’akinta tana kiran d’aya daga cikin yaran gidan nasu, da yake gidan nasu babban gida ne amma kowa da nasa 6angaren ita kad’aice aka ajiye dab da Inna wato sirikarta kenan
Da gudu yaron d’an kimanin shekaru shidda yazo, domin yasan indai ya shigo 6angaren Indo bazai rasa d’an abin sakawa a bakin salatinsa ba
“Dan Allah Ummaru jeka yi sauri ka kira mani Mamman kaji?”
Dayake yaron yasan Mamman d’in saboda yana yawan shigowa gidan shiyasa bai 6ata lokaci wajen tambayarta ko wanne Mamman take nufi ba.
Can k’ark’ashin wata bishiya ya hangoshi zaune sunata fira  suna korawa da ataye cikin nishad’i shida abokansa
“Mamman wai Indo tace kazo” abinda yaron ya fad’a  kenan bayan ya isa inda suke
Cikin mamaki Mamman ya dubesa “lafiya kuwa Indo ke nemana yanzu?”
“Nima ban sani ba” ya fad’a a tak’aice 
Sallama yayiwa abokan nasa kana yabi Ummaru suka juya
Da isarsa ko 6angaren Inna bai lek’a ba ya wuce kai tsaye 6angaren su Mahabu
“Yanzu Ummaru yazo yake cemani wai nazo kina nemana lafiya  kuwa?” Cewar Mamman kenan bayan ya samarwa kansa matsugunni a cikin d’akin
“Lafiya za’ace, amma dai ba lau ba, zazza6i ne ke damuna sosai wallahi shiyasa nace yayi mun l kiranka ko zaka taimaka ka siyo mun magani wajen Iliya mai tireda”
“Assha! Ashe bakiji dad’i ba?”
Tasowa yayi yazo dab da inda take kwance ya kai hannunsa zuwa ga jikinta
Cikin alamu na tausayawa ya dubeta
“Gashi nan kuwa jikin zafi rau sai kace garwashi”
Taso ta taka masa birki tun lokacin da ta lura da so yakeyi yakai hannunsa zuwa gareta, amma kuma sai ta tsinci kanta tana mai jin dad’in hakan
Saboda ita wata mace ce da Allah yayita mai tsananin buk’ata, shiyasa tayi k’ok’arin  nusar da iyayenta da kuma Mahabu wannan matsalar amma kowa ya kasa fahimtar ta.
Cikin wannan tunanin  Mamman ya barta ya nufi gun Iliya mai tireda domin siyo mata maganin.
Sai yanzu ne da ya dawo sukayi kici6is da Inna
“A’a Mamman ne? Kace har ka fara kewar aminin naka tun yanzu?”
“Ya za’ayi Inna ai sai hak’uri, yanzunma wai magani ne nasiyo Indo tana zazza6i shine zan mik’a mata na wuce”
“Wallahi kuwa tun safe take fama da zazza6in nan, yarinya duk tabi ta sakawa kanta damuwa ina dalili ina d’an mafari? shiga tana ciki” ta fad’a  tare da shigewa nata 6angaren…

_Har yanzufa wayar ba daina suma tayiba, dana fara typing sai dai naga tayi Luuuuuum_

_Kuma nace maku kuyo mani karo-karo ko ba mai tsada ba ‘yar ta dubu dar’i biyu ma ta isheni, sai ku had’a kud’in jirgi ku bawa d’aya daga cikin ku ya kawo mani amma naji shuru har yanzu_😭😭😭😭

 Maman Ja’afar 

+966592551785

[3/26, 6:42 AM] Mmn Jafar M: 🌻MAHABU🌻
             7
Daga Alkalamin

Maman Ja’afar✍

Sai cikin dare su Mahabu suka samu isowa garin Adarbiso d’in, amma duk da hakan basuyi tunanin tsayawa su kwana a hanya ba, a cikin daren dai suka nemi motar da zata sadasu daTanik.
Sunsha wahala mat’uk’a kamin su sami motar Tanik d’in, sai daga bisani suka samu, saidai a dole shatarta suka dauka su ukun tunda yanzu cikin dare ne ba wasu fasinja za’a samu masu zuwa ba.
Daga Adarbiso zuwa Tanik ba wata tafiya mai nisa bace domin tafiyar ‘yan mintina kad’an ce zata kaika
********
Da shigar Mamman d’akin  baiyi wata-wata ba ya nufi bayan k’yaure ya d’auko mod’a ya d’ebo ruwa a cikin karhi, kana ya taimaka mata ta tashi tasha maganin da ya kawo, kana daga bisani ta koma ta kwanta tunani fal a cikin zuciyarta 
Shima dai Mamman a nasa 6anagaren hakan take, domin shima tunanin Indo d’in ne ya addabi zuciyar tashi
“Shege Abokina ashe dai yasan abinda ya hango ajikin  yarinyar nan shiyasa mukaga ya nanik’e mata”
Abinda yaketa faman fad’a kenan a cikin zuciyarshi

*****

Dab da shiga garin Tanik nanma su Mahabu suka had’u da hukumomin masu tsaron gate, suma dai kamar na bayan, mai takarda ya huta wanda ko bashida ita jaka biyu ce zata rabaku dasu.
Bayan sun gama daidaitawa da hukumomin ne suka umarce su da su tsaya anan su kwana inyaso da safe sai su ida shiga cikin garin Tanik d’in tunda yanzu dare ne
Haka kuwa akayi, nan gindin motarsu kowa ya shimfid’a ‘yar rigarsa ya kwanta, kusan tafiyar maza dama ba wasu kayan kirki suke rik’owa ba.
■Washe gari■
Bayan sun gabatar da sallar asuba hukumomin suka basu d’an abin ta6awa suka lallasa badan ank’oshi ba, bayan sun natsu direba yajasu har cikin garin na Tanik.
Garin Tanik ba wani gari bane mai girman gaske, hakan nema yasa indai mutum Libei yakeson tafiya baya tsayawa a garin domin kwana.
Da dai su Mahabu suka samu suka cika tankin cikinsu basuyi wata-wata ba suka natsa cikin tasha domin neman motar da zata kaisu garin Agadas.
*****
Indo ce na hango tsugunne a Makewaya jini sai faman kwarara yakeyi daga jikinta, ga dukkan alamu dai ina tsammanin 6ari ne tayi, tun tana nuk’u-nuk’u ita kad’ai tana 6oyewa har ta kai ciwon yayi tsananinda baza’a iya 6oyeshi ba
“Inna! Inna! Da k’arfi Indo take k’walawa Surukar tata kira
“Kina ina ne Indo? Kamar naji kira kuma ga d’akin nata babu kowa”cewar Inna d’in kenan yayinda take ‘yan waige-waigenta
“Gani nan a Kewaye”
“Subhanallahi! Lafiya dai ko Indo?” Abinda tsohuwar keta faman fad’a kenan yayinda take tunkarar magewayar
“Subhanallahi! Indo haka abu ya faru kuma? Gaskiya zubar jinin nan yayi yawa ina ganin bama jin ‘yan jik’e-jik’e zaiyi ba, kawai a nemo Mamman ya d’auro mana Amalanke akaiki Likita (Assibiti) kona Kanan Bakashe ne”
Ai kuwa batare da 6ata lokaci ba Mamman yazo da Amalanke suka wuce.
“Saidai kuyi hak’uri domin cikinda ke jikinta ya zube” Abinda likitar ta fad’a kenan bayan ta gama duddubata
Jiki a sukwane suka dawo gida bayan anyi mata alluran tsayar da jini, an kuma bata ‘yan magun-guna.
Koda Mamman ya saukesu a gida bai zame ko ina ba sai wajen Mati mai balango ya siyo mata na dala d’ari, harda awara da zo6o ya biya bakin gari duk ya siyo mata kana ya dawo gidansu Mahabu d’in
Ba k’aramin jin dad’i tayi da irin wannan karamci da Mamman ya nuna mata ba, hakan nema yasa take rayawa a cikin ranta wannan kulawar inama ace Mahabu ne yakeyi mata ita?
******
Tafiyar kwana d’aya da wuni d’aya ce ta kawo su Mahabu cikin garin Agadas.
Garin Agadas babban gari ne mai tarin Sahara, mai d’auke da mata farare kuma kyawawa, gashin nan nasu kuwa har gadon baya
Mazanma a gurin kyawu ba’a barsu a baya ba domin suma farare ne gashin nan kuwa bak’ikk’irin akansu yayi luf tamkar larabawan Saudia

Saidai duk namijin da ka kalla indai ya kai munzalin zama saurayi zakaga kanshi nad’e da bak’in rawani, harma da way’anda basu kai samarin ba dan karanbani sakawa sukeyi tunda yin hakan a wajensu tamkar wani ado ne na musamman
Idanuwansu da kuma bakinsu ne kawai zaka gani a waje amma komai na fuskarsu a lullu6e yake da wannan bak’in rawanin.
A wannan garin su Mahabu suka yada zango sukayi kwana 2 a cikin garin batare da samun wani masaukin kirki ba
A kwana na ukun ne suka nausa a cikin gari domin harhad’a kayan guzuri wanda da wannan guzurin ne suke saka ran zasu d’auki hanyar Libei.
Duk abinda sukasan zasu buk’ata a hanya saida suka sayeshi, kama daga garin kwaki, madara, suga, tafiyoka biskit da dai sauran abubuwa marasa nauyi wanda sukasan matafiyi zai iya buk’ata
Ruwa kuwa saida kowa daga cikinsu ya sayi irin k’atuwar jarkar nan ta masu ga ruwa d’aya-d’aya, domin a hanyar Libiya babu babbar matsalar da ta wuce ace ruwan mutum ya k’are a, idan kuwa hakan ta faru komai na iya faruwa.
Saida suka k’ara yin kwana d’aya  a garin na Agadas kana suka samu hawa motar Libei d’in kai tsaye, sun k’ara kwana ne saboda rashin cika da wasu motocin nasu basuyi ba
Dayake  motoci ne masu yawa ak’alla zasu kai kusan ashirin ko kuma sama da haka, kuma a jere akeso su tashi kuma a rana d’aya
Manya-manya ne irin na d’aukar shanu d’in nan koko nace maku irin na d’aukar itace.
Saida kowannensu ya bayar da jaka goma goma kud’in hukuma bayan wanda suka bayar na mota, kana motocin suka samu lulawa.
Tun asuba motar su Mahabu ta d’au hanya, babu abinda direban yakeyi face sharara gudu.
*****
Tunda Indo tayi 6ari Mamman keta faman yin zarya a gidan da nufin wai yana zuwa ganin jikinta ne, kuma duk sadda zaizo baya zuwa hannu biyu sai ya sami wani d’an abin ta6awa ya taho mata dashi.
Yauma kamar kullum, bayan sun gaisa da Inna shashin Indo d’in ya wuce kai tsaye dayake dama bashida wani shamaki a ko ina na cikin gidan.
“A’a! Alhamdulillahi jiki yayi sauk’i kenan tunda har gashi naga anata faman goge-gogen kayan d’aki”
Ya fad’a bayan ya k’araso ya zauna akan tabarmar robar da ke shinfid’e a tsakar d’akin 
Da murmushi ta dubesa
“Jiki kam Alhamdulillahi  yayi sak’i sosai d’an yauma da safe har bayan gari naje na tsinko Kalgo na gasa, yanzuma da ka ganni nan ban dad’e da dawowa daga rijiya ba nayi wannan wanke-wanken, shine fa kaga ina gogewa” ta k’arashe maganar tata cikin murmushin dai
“Ai haka akeso, Allah ya k’ara sauki”
“Ameen” ta fad’a a tak’aice, kana ta k’ara da cewa 
“Nafa gode sosai da irin d’awainiyar da kayitayi dani, Allah ya bada ladar zumunci”
“Babu komai Indo, ai kinfi k’arfin komai a gurina, kuma duk abinda nayi maki ai ban fad’i ba, dan wallahi jinki nakeyi tamkar matar da nake aure kinga ko kome mutum yayiwa matarsa ai bai fad’i ba ko?”
Bata bashi amsa ba saima murmushi nan dai data saba ta bishi dashi
“Wallahi ina mamakin Mahabu da yayi watsi da irin duk baiwar da Allah yayi mashi na samun mata kyakkyawa mai hankali da natsuwa irinki, inda ace nine mijinki.. Aradu da k’yar ma idan zan iya fita ko nan da waje gurin abokainaina, ai kullum ina d’aki ina lalla6a kayana koba haka ba?”Ya fad’a tare da rungume hannayensa a k’irji
Maganarsa ba k’aramin fami tayiwa Indo ba, domin sai yanzu ne take jin haushin abinda Mahabu yayi mata, wanda a yanzu ne take buk’atar kulawarsa sosai da sosai
Murmushin k’arfin hali tayi kana tace “Kaima Allah ya baka kamata ko kumama wacce ta fini komai”
“Ai Indo baza’a samu kamar ki d’in bama bare kuma wacce ta fikin, me za’ayi da Binta wacce ko wankan kirkima bayi takeyi ba, amma ke duk sadda na ra6eki wani k’amshi mai d’ad’i nake jin yana ratsa mani har cikin kwanyata”

Ya fad’a tare da matsawa dab da jikinta, waishi a dole k’amshinta yake sansanowa…
 *Maman Ja’afar*

 +966592551785

[3/27, 6:47 AM] Mmn Jafar M: [27/03, 3:35 a.m.]

🌻MAHABU🌻
            8
Daga Alkalamin 

Maman Ja’afar✍

Motocinsu Mahabu gudu sukeyi ba kakkautawa, har zuwa lokacin da suka samu isowa wani gari mai suna *Kwarin Kantana*
Wani k’aton kwari ne mai tsananin yashi da kuma  k’ura, wanda tsananin k’urar dake cikin kwarin ko idanuwan mutum bazaka iya gani ba, k’ura ce mai tsananin gaske wadda zata rufeku ruruf
Gari ne Kwarin Kantana amma ba wani garin kirki ba tunda babu wasu gidaje sosai a cikinsa duk daji ne, saifa ‘yan bukkaye da wasu Buzaye sukayi, ina tsammanin sunyisu ne domin su dinga yada zango a gurin
To shinefa mutanen Nageria suke d’an ra6awa a cikin bukkunan suna yin abinci suna sayarwa matafiya da tsada tsugugu(Dayake kunsan kud’in Nijar sunfi na Nageria daraja, a Saifa kad’an sai abaka nerori masu yawa idan ka canza)
Anan su Mahabu  suka tsaya suka shisshiga Bukkunan domin cin abinci
“Nifa Sa’adu wallahi ba ganin gabana nakeyi sosai ba, nikad’ai wannan matsalar ta sama ne ko kuwa har ku?”
Cewar Mahabu kenan yayinda  yaketa faman murzar idanuwa
“Kaima Mahabu  da neman magana kake wallahi, wane kai kad’ai kuma bayan kana ganin tare mukayo wannan tafiyar”
Shiko Abashe babu abinda yakeyi face murzar idanuwa da gefen rigarsa, wanda a hakanma ba wani sauk’i yakeji ba, dan tamkarma ank’aro mashi azaba a idanuwan nasa yakeji.
A haka su Mahabu suka gama cin abincinsu mai shegiyar tsada kuma suka k’ara sayen ruwa jarka-jarka suma ruwan mau duk domin k’arin guzuri dana kada ruwa su k’are masu a hanya
Bayan sun d’an natsu ne suka kokkoma cikin motocinsu suka d’au hanya.
A wannan k’ungurmin dajin haka sukaita wuce namomin daji kala-kala wanda tunda sukema a rayuwarsu basu ta6a ganin irinsu ido da ido ba sai dai ko a cikin Tele(TV) idan ana fina-finan ban tsoro irin na namun dawa.
Basu k’ara tsayawa a ko ina ba sai a cikin K’auyen Turayya a Turayya nanma sun had’u da Gate d’in Jandarmomi, inda Jandarmomin suka tsaitsayar dasu
“Yauwa Direba ku sassauko kubi layi” Cewar wani Jandarma kenan yayinda yake lellek’a cikin motar
Haka sukabi su Mahabu d’aya bayan d’aya suna k’ar6ar jaka-jaka a hannunsu, da mai takardar da wanda bashida takardar kowa sai da ya bayar da jaka jaka kana daga bisani kuma Jandarmomin suka umarcesu da su tsaya su kwana domin dare yayi washe gari sai su wuce.
Wan shekare(Washe gari)Motar su Mahabu ce a gaba shiyasa sahiya nayi sukaja sukayi gaba yayinda sauran motocin suma suka rufa masu baya.
******
“Haba Mamman d’an matsa mana, baka tunanin Inna zata iya fad’owa a kowane lokaci cikin d’akin nan?” Ta fad’a yayinda take ja da baya da baya
“Karki damu Indo babu wata Inna da zata shigo yanzu, dan shigowata d’in nan naganta tayi arwallar Lisha ta shige K’ofarta”
B’ata rai tayi kana ta sake cewa”A’a nidai gaskiya ka matsa wallahi tsoro nakeji”
K’ara matsawa yayi dab da ita har jikinsu yana gogar juna
“Wane tsoro Indo? Wallahi babu wanda zai shigo, ina mai tabbatar maki koda wani abu zai faru a tsakaninmu babu mai sani wallahi, idan kuma baki yadda ba bari na k’ara lek’awa tsakar gidan naga inda wani a kusa”
Da gama fad’ar haka ya nufi tsakar gidan yana duddubawa, kamar kuwa yanda tsammata babu kowa a tsakar gidan, domin duk sun nufi sashinsu dan gabatar da sallar Isha
“Kin gani ko? Wallahi babu kowa a tsakar gidan barema kiyi tunanin ko wani zai iya shigowa ya ganmu”
Ya fad’a bayan ya dawo cikin d’akin, inda ya tsaya dab da ita jikinsa har gugan nata yakeyi
“Amma to Mahabu fa?” Ta fad’a yayinda gabanta ke ci gaba da dukan tara-tara
“Manta da Mahabu dan Allah, inda yana sonki har ya kama hanya ya tafi wata uwa duniya ya barki ba tare da tunanin halinda zaki iya shiga ba? Ko an gaya masa dutsi ya ajiye a gidan ne?”
Magan-ganunsa ba k’aramin tasiri sukayi a zuciyar Indo ba, domin dama a matse take wata ‘yar dama kawai take jira ta samu
“Amma dai a rufe k’ofa ko?” Ta fad’a cikin murya mai tattare da shagwa6a
“Ai yanda kikeso haka za’ayi amaryata”Ya k’arashe maganar tasa tare da nufar k’ofar d’akin
“Amaryar Mahabu dai zakace ko?” Itama ta fad’a  cikin murmushi
“Dan Allah manta da wannan bahon” Ya fad’a  tare da rungumota a jikinsa.
_Gaskiyar Allah (S.W.A) daya fara ambatar mace gurin aikata zina kana ya ambaci namiji saboda anan mace itace jagora domin itace mai bada k’ofa, a gurin Sata kuma sai ya fara ambatar namijin kana ya ambaci mace dayake a wannan gurin aikin k’arfi ne.Ya Allah ka tsare mana zukatanmu daga bin hud’ubobin shaid’an la’anannen Ubangiji_
Nidai ban tsaya na ida ganin  k’arshen wannan ta’asar da ake shirin aikatawa ba na gudu daji abina zuwa wajensu Mahabu.
******
Daga Turayya su Mahabu basu k’ara tsaya a ko ina ba hanya kawai suke kwasa
 Kusan kwanansu hud’u a hanya suna tafiya a cikin wannan saharar mai d’auke da matsanancin zafi da tarin rairayi, wannan dalilin nema yasa duk ruwan wasu daga cikin matafiyan ya k’akk’are saboda zafin rana da kuma tsananin k’ishirwarda ke kama mutum a wannan hanyar
Suma su Mahabu da sauran way’anda ruwan nasu bai k’are ba badan wai k’ishirwar tasu ta mutu ba suke daina shan ruwan nasu, a’a suna barin ruwan ne kawai domin gudun kada suma ruwan nasu ya k’are mai afkuwa ta afku, saboda indai ka yadda ruwanka ya k’are a wannan hanyar to sai dai abinda Allah yayi da kai kawai.
Da yake motoci ne masu yawa suka d’auki hanyar ta Libei d’in shiyasa mutanen da suka mutu dalilin k’ishirwa suka yawaita dan sunfi a k’irga.
Da mutum ya mutu a hanya ba’a tsayawa wani 6ata lokaci domin binnesa sai dai kawai daga cikin motar a tillosa waje, kuma mintina kad’an yashi ya rufesa ruf ko d’an yatsansa bazaka iya gani ba
Idan kuma ta baya mutum yayi ya fad’i daga cikin motar inma da rai inma matacce shima haka za’a wuce a barsa a gurin har k’asa ta rufesa ruf shima
“Kasan miye Abashe?” Mahabu ya fad’a  tare da dafa kafad’ar Abashen
“A’a sai ka fad’a Mahabu”
“Wallahi duk yanda nake jin Malamai suna kwatanta mana tashin alk’iyama ban ta6a yadda da maganarsu haka take ba sai a wannan tafiyar tamu ta zuwa Libei, wallahi wannan tashin hankalinda nake gani a yanzu tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin irinsa ba”
“Kai kaga tashin hankali ko ni? Yo nifa tunda nake a rayuwata ban ta6a ganin gawar mutum ido da ido ba sai a wannan tafiyar, kaga dai yanda ake watanda da gawarwakin mutane sai kace wasu gawarwakin ‘yan tsaki” Abashen ya fad’a tare da duban fuskar Sa’adu

Cikin Sanyin jiki da kuma jimamin abin Sa’adun yace

“Kawai dai muyi fatan Allah ya kaimu lafiya domin muma bamu da tabbacin zamu ida isa Libei d’in lafiya ko kuwa mumu a hanya za’a yada gawarwakinmu kamar sauran?” Ya fad’a  yayinda hawaye ke bin fuskarsa shar-shar sai kace wata mace
“Wayyo Allah jama’a! Wayyo mak’oshina zai tsage! Ku taimaka mani da ruwa ko yaya yake dan Yarasululluhi, ku taima mani dan Allah  kada nima na rasa rayuwata, wayyo Allahna! Shikenan nima mutuwa zanyi”
Abinda wani matashi d’an kimanin kusan shekaru 30 yake ta faman maimaitawa kenan daga cikin motar da su Mahabu d’in suke
“Bari na bashi ko a tafin hannu ne, dan shimafa inaga mutuwar yake shirin yi”
Cewar Mahabu kenan yayinda yake lalubar jarkar ruwansa
Zaro ido Abashe yayi kana ya dubesa cikin 6acin rai
“Ka bashi? To bashi d’in kaima  kuma ka mutu kamar yanda shima yake shirin mutuwa ba”
Abinda Abashe ya fad’a  kenan yayinda ya k’ara matse yar  jarkar ruwansa data kusan k’arewa a tsakan-kanin cinyoyinsa
Shiko Sa’adu d’an Saurayinma ko kallon tsiya bai ishe shi ba, domin a wannan tafiyar nafsi-nafsi ne kawai, idan jifa ta wuce kanka to kan kowama ta fad’a kai bakada matsala….

*Maman Ja’afar*

+966592551785

[3/29, 6:58 AM] Mmn Jafar M: 🌻MAHABU🌻
            9
Daga Alkalamin 

Maman Ja’afar✍

Tun daga wannan lokacin Mamman ya mayar da Indo tamkar wata matarsa ta sunna, duk dare sai yazo mata, kodai ya shigo ta k’ofar gida ko kuma wataran ya hauro ta katanga.
******
Tafiya takeyi a hanya sai faman surutai take ta faman yi ita kad’ai sai kace wata zararriya
“Oni ‘yasu! Wannan irn cin amana dame yayi kama?”
Har ta shigo gida bata daina ‘yan surutan da takeyi ba
Da yake yau rana ake zabgawa mai d’an karan zafi shiyasa kowa na gidan ya kasance a tsakar gida  k’ark’ashin bishiya suna d’an jin iskanda ya ke busowa kad’an-kad’an
“Inna lafiya kuwa naga kin shigo kamar ranki a 6ace, kodai yauma a gun shari’ar taku ba’a dace bane ba kamar kullum?”
Indo ce ta d’ago da kai daga yankan akaifar(k’unba ko farce) da  take yi ta fad’i hakan yayinda take duban fuskar sirikar tata
Dayake tun bayan rasuwar Mahaifin su Inna Furen taketa tabka shari’a tsakaninta da yayanta wanda yake k’ok’arin handame mata nata gadon Shanun da kuma Gonakin da mahaifin nasu ya rasu ya bari, to yanzunma ga dukkan alamu daga  gun shari’ar ta fito
Girgiza kai tayi cikin jimamin abinda zai fito daga bakinta
“Wai ashe lalacewarda duniya tayi yanzu har ya kai haka? Yoni Indo tashin hankalindama nagani a gidan Kashen (Sarki) ai yafi wanda na tafi dashi”
Matar Bala K’anin mijin Inna Fure ce ta mik’e  tsaye tare da gyara d’aurin zaninta da alamun tambayoyi tattare a fuskarta
“Wai Fure mike faruwa ne haka? har yanzu dai baki fad’a mana abinda kika gani a gidan Kashen ba”
Ajiyar zuciya tayi kana ta dubesu
“Wato wasu maza ne nagani a gidan Kashen kusan su uku, kuma kowannensu wai k’arar matarsa ya kawo, kunsan me matan sukayi?”
Ta fad’a yayinda take duban fuskokin matannda ke zazzaune a tsakar gidan
Jijjiga kai sukayi alamun basu sani ba amsarta kawai suke jira
“Waifa a cewar mazajen nasu tafiya sukayi zuwa Libei, ko shekara nawa sukayi a can? Oho! Wallahi na manta ko nawa suka ce”
“Muna jinki dai Inna Fure” Cewar d’aya  daga cikin matan da ke gurin kenan
“Tofa shine bayan sun dawo daga Libei din suka tarar da matayen nasu wasu da ciki wasu kuma da goyo, kai intak’aice maku labari watama har yara biyu mijin ya dawo ya sameta dasu”
Salallami  matan suka farayi tare da tofin Allah tsine ga matayen da suka aita hakan
Yayinda ita kuma Indo tayi wani fik’i-fik’i sai rarraba idanuwa takeyi a tsakaninsu sai kace wacce aka kama tayiwa sarki k’arya
“Wannan abin kunya dame yayi kama haka?” Cewar d’aya daga cikin matan kenan
“To Inna Fure shi kuma Kashen yaya zaiyi ya taro kan wannan shari’ar kenan?”
Cewar wata mata kenan wacce ta lek’o ta katanga tana sauraren firar tasu
“Ina kuwa zan sani tunda ba tsayawa nayi na ida jiyo k’arshen shari’ar ba”
“Nifa dama ba yau na fara jin wannan labarin ba, nasha ji yafi a k’irga kuma a cikin garin nan, wasuma matan tare muke yin mu’amala dasu, dan dai kawai baka kama suna ba tsoron kar a kiraka sheda a gaban Kashe”
Cewar Laure kenan d’aya daga cikin matan gidan
“To ai ke Laure in baya ga abinki idan 6era da sata to ai daudawa ma tanada nata warin, saboda haka ni ban ware kowa ba acikin mazan da matan, inda kashe zaibi ta tawa dukkansu kamata yayi ayi masu hukunci”
Cewar matar K’anin mijin Furen kenan
Ita dai Indo bata tsaya ta ida jin k’arshen firar tasu ba ta tashi sumui-sumui ta shige d’aki abinta
******
Suna ji suna gani wannan d’an saurayin ya shid’e ya mutu batare da kowa yayi tunanin taimaka masa ba.
Wata Inyamura tana gefe itama tanata faman murk’ususun k’ishirwa, koda taga abinda ya faru da wannan saurayin batayi wata-wata ba ta d’auko kofinta ta tsugunna tayi fitsari aciki ta kwankwad’e kayanta(Wuya koda magani ba dad’i)
Dariya Abashe yayi kana ya dubi sauran abokan nasa
“Ammafa ‘yar inyamurar can tayi dabara, kaga shima wannan da haka yayi k’ilan da ya kai labari” Ya fad’a yayinda yake duban gawar wannan saurayin
Muskutawa Mahabu yayi

“To ya za’ayi da k’aran kwana? Dama Allah ya k’addara badashi zamu ida isa Libei d’in ba”
*****

Saida su Mahabu suka k’ara kwana da wuni kana suka samu isowa Rijiya Mai Tol
A lokacin ruwan mutane da dama ya k’are a hanya, sai dai Allah yayi da sauran kwanan wasu a gaba basu riga sun mutu ba amma dai sun jigata sosai
Rijiya Mai Tol wani guri ne da yafi ko ina Sahara a hanyar ta Libiya, domin idan ka hanga sosai zaka iya hango nisan da ya kai kusan tsakanin Katsina da Kano
Domin tsabar saharar da ke gurin ko bishiya d’aya babu bare kuma duwatsu ko kuma gidaje
Kuma indai dare yayi maku a wannan gurin akeso ku kwana kamin zuwa safiya ku k’ara gaba
Akwai wata Rijiya a gefe guda wacce itace ake kira da Rijiya Mai Tol, kuma a wannan Rijiyar ne wasu masu motocin sukan zuba mutanen da suka mace masu a hanya (Masu d’an sauran imanin kenan)
Kuma dai har wa yau a wannan Rijiyar wad’anda ruwansu ya k’are a hanya suke shan ruwa
Idan Allah ya k’addara kanada sauran rayuwa agaba idan kasha ruwan ka tashi, idan kuma dama kwananka ya riga ya k’are tofa da kasha wannan ruwa ko miniti biyar bazaka k’ara ba zaka shid’e, kuma a dole kasha d’in domin a wannan lokacin k’ishirwar da ke tattare da kai ko ruwan guba ne aka baka da sauri zaka kar6a ka kwankwad’e.
“To jama’a nanfa zamu yada zango saboda dare yayi, dan idan mukace zamu wuce k’arshenta muyi 6atan kai a hanya” Cewar direban su Mahabu kenan
A wannan filin Allahn ta’ala matafiyan suka rarra6a domin yin bacci, yayinda su Mahabu da Sa’adu da kuma Abashe suka ra6a guri guda su kad’ai,  saboda tunda suka had’u a hanya suka jone suka zama tamkar ‘yan’uwan juna
“Nikam wani mugun wari nakejifa a nan kusa dani, hancina ne ko kuwa dai kuma kun jiyo shi?” Cewar Abashe kenan yayinda yake toshe hanci
Tocila Sa’adu ya fiddo daga cikin aljihunshi ya fara hahhaskawa
“Wallahi gawa ce a gurin, kuma ga dukkan alamu sabuwa ce” Abinda Sa’adun ya fad’a kenan yayinda yake duddubawa
“Gaskiya ku tashi mu canza wuri dan nagaji da ganin gawarwakin nan hakanan, wannan ai sai imanin mutum ya ida fita gaba d’aya” Cewar Mahabu kenan yayinda ya mik’e tsaye ko kallon inda suke nuna masan ma baiyi ba
Suma sauran ba tare da 6ata lokaci ba suka rufa masa baya
■Washe gari ■
Tun dugu-dugu kowa ya nufi hanyar motarsu, dama ba maganar salla akeyi ba a wannan lokacin 
Anan d’inma saida suka bar wasu mutanen a kwakkwance suka wuce, wasu sun mutu, wasu kuma na shirin mutuwar, ga dukkan alamu dai inaganin wad’anda sukasha ruwan Rijiya Mai Tol ne….

Wannna bala’in da nake baku labari na hanyar Libiya ni Maman Ja’afar ina mai tabbatar maku da babu k’arya a cikin zancena
Domin har rantsuwa zan iya yi maku akan hakan, saboda a nawa tsarin bana baku labarin da ban tabbatar da sahihancinsa ba
Tabbas hakan ke faruwa kuma hakan keci gaba da faruwa
Ina mai shirin tafiya Libiya? To ka shirya tarbar wannan Bala’in kaima.

Muje zuwa Mahabu Number 10
*Maman Ja’afar*

 +966592551785

[3/31, 5:01 AM] Mmn Jafar M: [31/03, 4:51 a.m.]

🌻MAHABU🌻

           10
Daga Alkalamin

Maman Ja’afar✍

Daga rijiya mai tol su Mahabu basu sake yada zango a ko ina ba sai a wani d’an k’aramin gari mai suna DURKU adaidai inda hukumomi suke
Durku gari ne sai dai ba wani garin kirki ba, dan dai kawai gurin akwai ‘yan duwatsu kuma babu sahara sosai  shiyasa wasu ‘yan tsirarun mutane sukazo suka kakkafa ‘yan gidajensu a gurin
“Ina masu takardu” Cewar Jandarmomin kenan yayinda suke fitar dasu Mahabu daga cikin motar daya-bayan daya
Direban ne ya umarci masu takardu da su ware gefe guda, marasa takardunma haka
Masu takardu jaka goma-goma Ikon (hukuma) suka kakkar6a a hannunsu, marasa takardu kuma jaka sha biyar-biyar
Wanda kuma bashi da takarda kuma bashi da kud’i a dai-dai nan Iko zasu rik’eshi su mayar dashi baya, ma’ana ya koma inda yafito, waccen wahalar da yayi ta tashi a banza
Idan kuma dama tun a Agadas iya kud’in  motar Durku ka biya, to sai a ajiyeka anan kayi ka biya Iko kud’insu kana ka zauna anan kayi neman kud’i, irin wanki da guga, noma, gini, da saida ruwa na ‘yan watanni kana ka ida haurawa Libei d’in(Koko nace kusa da Libei din)
Daga garin Durku tafiyar da su Mahabu sukayi batafi ta ‘yan awanni ba suka sami isowa wani d’an k’aramin gari na Buzaye mai suna LATTAI
Basu dad’e da wuce garin Lattai ba dare yayi masu a hanya, kuma dama ak’a’idar tafiyar ba’aso ana yinta da daddare saboda tsoron 6ata a hanya, saboda indai kuka yarda motar ku ta 6ata a hanya to saidai kuyita gararanba, baku Chadi baku Algeria har ruwanku ya k’are a hanya ku mutu ku duka.
Daidai wasu duwatsu motocinsu Mahabu suka faffaka, kowa ya firfita domin mik’e hak’ark’arinsa kamin safiya a d’ora daga inda aka tsaya
Cikin way’annan duwatsun suka shisshiga domin kwanciya kamin safe
Idan lokacin zafi ne duwatsun sukanyi tsananin zafi ne tamkar garwashin wuta, idan kuma lokacin sanyi ne nanma duwatsun sukanyi tsananin sanyi ne tamkar K’ank’ara, koma dai yaya ne abin ba wani sauk’i ne dashi ba
A haka su Mahabu suka rarra6a acikin duwatsun nan
“Wai!wai!wai! Wannan irin zafi ai sai mutum ya k’one, gaskiya bazan iya kwana a nan ba, gara na kwanta a saman yashin nan k’ilan ya d’anfi sauk’i-sak’in azaba”

Cewar Sa’adu kenan yayinda zafin dutsen ya kusan toya mashi k’afa
“To in baya ga abinka ai babu wani banbancin azaba tsakanin yashin da kuma dutsin, nanfa inda ka ganni tsaye rigata ce na cire na d’ora a k’asan takalman nawa dan naji yar dama-dama”
Cewar Mahabu kenan yayinda yake d’aga k’afa d’aya yana ajiye dayar duk dan ya samu sauk’i-sauk’i 
Abashe ko rugawa da gudu yayi ya d’ale motar da suka baro
“Nikam gara na kwana anan dana kwana acikin wannan azabar, dan har naji mak’oshina ya fara bushewa wallahi, inama ruwan nawa yake?”
Ya fad’a yayinda yake ‘yan dube-dubensa a cikin motar
Wata uwar ashar ya lailayo ya sauke, kana da k’arfinsa yake fad’ar
“Shi kenan wallahi sun kasheni, sun sace mani ruwana kuma nasan ba mayar mani za’ayi ba dama y’an kad’an ne suka rage  mani”
Yana magana muryarsa na rawa tamkar mai shirin yin kuka, domin babu abinda yake tunawa sai irin yanda mutane sukaita mutuwa a hanya dalilin k’ishirwa
“Mahabu kaji abinda Abashe yake fad’a kuwa?”
Sa’adun ya fad’a tare da kallon fuskar Mahabu wacce ta jik’e sharkab da zufa saboda tsananin zafinda ke gurin
“Naji mana, kai ya kake ganin za’ayi?” Ya k’arashe maganar tasa yana kallon fuskar Sa’adun domin jin amsar da zai mayar masa
“Ya kuwa za’ayi? Kawai hak’uri zaiyi ya bar mana wasiyya idan mun samu saduwa da ‘yan’uwanshi mu fad’a masu, domin ya kusan zama gawa shima, inkuma zaka sammashi naka ruwan ne ban hanaka ba”Ya fad’a yayinda shima ya haura gurin motar domin samun sauk’i-sauk’i 
Jiki a sanyaye shima Mahabu ya shiga motar ya zauna
“Dan Allah ‘yan’uwana kud’an yi mani karo-karo mana”Ya fad’a yayinda hawaye ke bin fuskarsa
“Nikam bazan baka ruwana muyi mutuwar kasko gaba d’ayanmu ba, saboda daga nan bansan iya nisan da zai kaimu Libei d’in ba, gara dai d’aya ya rayu d’aya kuma ya mutu kada asarar rayukkan tayi yawa”
Cewar Sa’adu kenan fuska a d’aure sai kace dama can bai ta6a sanin Abashen ba
Jiki a sanyaye Abashen ya juyo wajen Mahabu”Kaima Mahabu bazaka taimaka mani ba ko?” Ya fad’a murya na rawa
“Nima dai gaskiya Abashe sai dai nace kayi hak’uri dan ban shirya mutuwa yanzu ba, ko amarci bamu gama ci da Indo ba na hak’ura na barota gida domin neman abinda zamu rufawa kanmu asiri, haka kawai sai dai aje mata da labarin na mutu? Ina! Kawai kayi hak’uri Abokina kaita yin kalmar shahada kurun tunda dama ba wasu iyali ne da kai ba”
Bai k’ara ce masu komai ba ya samu guri ya kwanta abinsa.
Sai kusan Asuba rahama ta fara mamaye gurin, daga bisani kuma sanyi mai tsanani ya maye gurbin wannan tsananin zafin, tsabar sanyin gurinma har kyarma zakaga mutane sunayi.
****

Daga wannan gurin su Mahabu basu k’ara tsayawa a ko ina ba sai a wani gari waishi SIGIDIM, a Sigidim ma saida Iko suka kakkar6i jaka-biyu-biyu a hannunsu kana suka barsu suka wuce
Tun daga wannan lokacin kuma motocinsu Mahabu suka fara gudu baji ba gani, basu k’ara fakawa a ko ina ba sai a wani daji gindin wata tsohuwar rijiya
Danma dare yayi masu ne suka tsaya a nan d’in badan haka ba da sai inda mai ya k’are(Inda direba ya gaji)
“Ina way’anda ruwansu ya k’are? Ku firfito ga wata rijiya a can kuje kusha”Cewar direban kenan yayinda yake sank’amar biredinsa yana korawa da ruwa
Cikin murna Mahabu ya bugi kafad’ar Abashe”Abokina gafa ruwa can ansamu, yi sauri kaje kasha kafin mutane su cika wajen”
Ga mamakinsa sai ya ga Abashe ya 6ingire, cikin kid’ima yake jijjigashi

“Abashe! Kaddai ace kaima mutuwa kayi?”
“Subhanallahi, badai ya mutu ba?” Abinda Sa’adu ya fad’a kenan yayinda ya k’araso gurin
“Wallahi ya mutu, ashe shiyasa tun d’azun naketa faman bashi labarin Indo naji shuru? Ni wallahi na zacima fushi yakeyi damu ashe rai har yayi halinsa?”
Cikin jimami suka kinkimesa zuwa bayan wasu duwatsu suka yada shi a can
*Washe gari*
Da suka d’au hanyafa basu k’ara tsayawa a ko ina ba sai wani gari MADAMA kafin shiga garin Madama d’inma saida Iko suka tsayar dasu suka kakkar6i na abinci kana suka ida shigowa cikin garin
Garin Madama babban gari ne ba laifi, wanda ko ananma mutum ya tsaya zai iya yin neman kud’insa
A wannan garin su Mahabu suka canzar da kud’insu daga kud’in Nijar zuwa kud’in Libiya, kuma dai har wayau kwana d’aya sukayi a Madaman suka wuce gaba
Saida sukayi tafiya mai nisan gaske inda babu hukumar Nijar bare ta Libiya kana suka samu isowa wani k’ungurmin daji
A cikin wannan dajin ne kuma suka tarar da wasu motoci manya-manya masu yawan gaske a gurin
Direban su Mahabu ne ya fara fita yayi magana da d’aya daga cikin masu motocinda suka tarar kana ya dawo bayan mota inda su Mahabu suke zazzaune
“Yauwa ku fito ga motar da zaku koma can, itace zata ida shiga daku cikin gari har kusa da Libei”
Ya fad’a  yayinda yake nuna masu inda motar take
Batare da 6ata lokaci ba suka koma cikin motar da ya nuna masun
Haka suma sauran motocin sukayi kamar yanda direban nasu Mahabu yayi.
Dayake motocin na y’an asalin cikin garin Libei d’in ne shiyasa tun daga cikin wannan dajin babu 6arauniyar hanyar da basu sani ba wacce zata iya sadasu da garin Libei din
(Su kuma irin sana’ar da sukeyi kenan suna samun y’an canjinsu suna sakawa a aljihu)
Tunda suka fara tafiya basu samu damar tsayawa ba har saida suka iso gurin hukuma
Wanda a tsammaninsu basu zaci zasuga hukuma ba a gurin domin ta 6arauniyar hanya suka biyo
Nanfa suka fara wasan tsere tsakaninsu da hukumomi, da harbi da komai amma saida suka 6acema hukumomin dayake kunsan ance dama da d’an gari akanci gari
Saida sukayi zagaye sosai kana suka dawo hanya kai tsaye saboda gudun koda za’a biyo sawun motar tasu
Sai cikin dare sosai su Mahabu suka iso wani gari waishi GATURAN dayake dama direbobin y’an gari ne shiyasa basu sha wata wahala ba wajen samun gidan da zasu 6oye fasinjojin nasu ba.
Gidane mai girman gaske, mai d’auke da wata doguwar katanga sai kace gidan yari (Shima a iya kiransa da gidan yarin) wanda ina ganin dama anyisa ne domin saukar bak’i irinsu Mahabu.
Saida suka samu natsuwa kana direban nasu ya fita ya kawo masu shayi da biredi
“Allah sarki Abashe, dafa yanzu dashi muke shan shayin nan ko?” Cewar Mahabu kenan yayinda ya sur6i shayin
“Nima tunanin da ke cikin raina kenan ka rigani furtawa”
Anan dai su Mahabu suka samu sukayi wanka suka d’an wanke kayansu duk a cikin wannan daren
*Washe gari*
“Ga motoci can a k’ofar gida na abokanmu zasu wuce daku SUBAHA yanzun nan, saboda haka kowa ya bada kud’in motarsa” Cewar mutumin kenan wanda yake magana fuska a d’aure ko alamun fara’a babu
Anan su Mahabu suka harhad’a masa kud’in motarsu suka mik’a mashi
Batare da 6ata lokaci ba ya kaisu gurin motocin suka shisshiga shi kuma ya dawo masauki abinsa.
Basuyi nisa sosai ba shima wannan direban ya k’ara juyesu a wata mota, nanma saida suka biya wani sabon kud’in, a haka saida akayi masu canjin mota kusan guda hud’u kuma kowacce sai sun bayar da kud’i  kana suka samu isowa garin Sabaha d’in
Garin Sabaha koko nace k’auyen Sabaha mai d’an girma ne babu laifi, anan ne kud’in su Mahabu kuma suka k’are suka zauna domin yin aikatau na d’an wani lokaci.
Duk wani aikin k’arfi da akeyi cikin wannan garin saida su Mahabu sukayishi, wanda mafi yawancinshi ma Noman abincin dabbobi ne.
Saida sukayi kusan wata 4 a wannan garin kana suka samu kud’in haurawa a hakanma dan yan garin suna dan k’wakk’wace masu kud’in nasu ne badan haka ba da bazasu kai tsawon wannann lokacin ba a wannan garin
Wani lokaci azo har gida ayi masu satar tunda ansan su duka bak’i ne, yayinda wani lokacin kuma a hanya nema za’a taresu da wuk’a koda bindiga ayi masu k’wacen kud’in.
*****
“Shin waini Laure kun lura da yan canje-canjen da Indo takeyi acikin gidan nan kuwa? Itace batason warin wancen abin, batason k’amshin wancen abin, ga wani uban shan yaji data tarka sai kace ‘yar gidan Alai (Mayu)
Lauren katse Kilima tayi

“Nifa ran nan naje kar6ar kanwa a d’akin ta naje na sameta tanata kakarin amai”
Zaro idanuwa Kilima tayi gami da rike baki alamun mamaki fal a fuskarta “Kai haba dan Allah Laure”
Buga hannayenta tayi a cinya “Fad’i da ihu k’ara da wayyo Allah, tabbas na gani da wad’an nan idanuwan nawa ba wani ya bani labari ba” ta fad’a yayin da take nunawa Kilimar idanuwan nata da yatsa
“Aiko indai hakane bamuga ta zama ba, dole muje mu samu Inna Fure da wannan maganar”
Dafe k’irji tayi kana tace “Wa? badani ba wai gad’a a Mak’abartu, baza’aji mutuwar sarki a bakina ba”
“Aikoni za’aji mutuwar uban sarkinma a bakina, kinmaga tafiyata” Tana gama fad’ar hakan ta nufi sashen Inna Furen

****

“Inna! sallama ashe kikeyi?”Abinda Lauren ta fad’a kenan bayan ta samarwa kanta matsugunni a cikin d’akin
Sallame sallar tayi kana ta fuskanci Lauren
“Nama sallame daga raka’a biyu idan muka gama maganar na k’arsa sauran raka’a biyun daga baya, tunda nasan ke tauraruwa mai wutsiya ce ganinki ba alheri ba, dame kuma akazo mani?”
Ta fad’a yayinda take duban Matar D’an d’an Bala Kanin mijinta kenan wacce zamuce kusan matsayinta d’aya da Indo a gurinta
(Nidai Maman Ja’afar tunda na fara zuwa islamiyya ban ta6a jin Malamai sunce akwai wata Mazhabar da tace ana iya sallame salla daga raka’a d’aya ko biyu daga baya a ida sauran ba, ban sani ba ko ku masu karatu kun san da wannan)
“Inna kin kuwa san Indo tana d’auke da juna biyu?” Ta fad’a murya k’asa-k’asa gudun kar wani yazo wucewa ya jiyota
Wani rugugin aradu Inna Furen taji ya sauko mata ak’irji har saida tayi k’ok’arin dafe k’irjin nata gudun kada kirjin ya tarwatse…

Muje zuwa Number 11

_Kuyi mani afuwa koda nayi kuskure a cikin rubutun nawa, domin yanzu haka kaina namun tsananin ciwo nakeyi maku wannan typing d’in saboda naji kunata tambaya ni kuma banaso na 6atawa masoyana rai_😭👏

Maman Ja’afar ce 

 +966592551785

[4/1, 6:32 AM] Mmn Jafar M: 🌻MAHABU🌻

          11

Daga Alkalamin

Maman Ja’afar✍

Zaune take a tsakar d’akinta ta tasa kwanon kwad’on yakuwa a gaba wanda yasha had’in daudawa da magi da yaji sai faman zak’a takeyi tana zare ido tana fyace hanci ga gumi nata bin fukarta sai kace wacce aka matsawa adole sai taci
Muryar Inna ce taji cikin d’aga sauti sai  banbami take, kuma ga dukkan alamu ba ita kad’ai bace kuma nan k’ofar tata suke k’ok’arin tunkarowa
“Ina Indon take? Fito nan munafukar banza munafukar wofi, ashe dama cin amanar d’ana kikeyi ban sani ba?”
Da jin wannan furucin nata Indo ta firgice ta gigice harma tana neman fita hayyacinta
Dayake babu riga a jikinta sai d’aurin gaba shiyasa batayi wata-wata ba ta jawo rigar Mahabu dake rataye a jikin k’usa ta zura, a zuwan wai ita nan rigarta ce ta saka, a sakun rigarma gaba baya ta saka dayake duk a rud’e take
Babban fatan da takeyi Allah yasa dai ba wani ne yaga Mamman lokacinda yake hauro ta katanga ba ya fad’a masu
Fitowa tayi daga cikin d’akin nata tayi tsaye a bakin k’ofa tana jimamin abinda ka iya zuwa ya dawo, a lokacinma har sun riga sun k’araso k’ofar tata
Da zuwan Inna batayi wata-wata ba ta kamo hannun Indo tana duddubawa, tana girgiza kai ta gwale idon Indon ta dudduba, kana daga bisani ta duba tafin k’afarta
Tana gama y’an dube-dubenta ta rushe da wani matsananci kuka tana fad’in
“Indo kin cucemu kin cuci rayuwarmu, kin ja mana abin kunyar da har y’ay’a da jikoki za’a dinga goranta mana, cikin shege a wannan gidan? Allah dai ya isa tsakaninmu dake Indo”
Babu abinda Indo take maimaitawa a cikin zuciyarta face kalmar cikin shege
“Hakan na nufin wai ina d’auke da cikin Mamman kenan a jikina?”
Nan take itama ta fara rusar kuka kamar yanda sauran matan gidan suma suketa faman yi gami da yi mata tofin Allah wadarai
Ana cikin wannan yanayin ne mahaifin Mahabu ya shigo gidan domin yin sallar magariba
Inda yaji koke-koken na fitowa can ya tunkara kai tsaye cikin yanayi na rashin sanini takamaimen abinda ke faruwa a gidan nashi a daidai wannan lokacin
Shi a tsammaninshi ma Indo d’in ce ta mutu, saida yaga Indon a durk’ushe tanata faman rizgar kuka kana ya musanta tunanin nasa
“Wai mike faruwa ne a cikin gidan naga sai faman kuka kukeyi ku duka? Kodai cikin yaran gidan ne wani ya rasu?”
Ya tambaya yayinda yake kallon fuskarsu d’aya bayan d’aya 
“Babu wanda ya mutu Affa Indo ce taje tayo cikin shege” Lauren ta fad’a cikin disashewar murya irinta wanda yaci kuka ya gaji
Salallami tsohon ya fara tare da rik’e baki alamun mamaki k’arara a fuskarsa
“Ai kuwa bazamu zauna dake da wannan d’ingimemen abin kunyar ba a cikin gidan nan, dolenki ki bar mana gida yanzu-yanzun nan dan haka kawai bazaki ja mana abin zagi ba a gari” Cewar Affa kenan
Kilima ce tayi farat”Ni ina ganin kawai Affa ka saketa sai taje can taci gaba da iskancin da ta sabayi”
_Wata sabuwa inji yan caca_

_Wani da sakin matar wani koya wannan lamarin yake?_
Affa baiyi wata-wata ba ya dubi Indo
“Kinga yarinya ji nan, ba kuka zaki tsaya kina yi mana ba jeki gidanku na sakeki saki d’aya” Yana gama fad’ar haka ya baza babbar rigarsa ya fice daga gidan rai a 6ace
Inna tana share hawaye tace “Inama ace uku yayi maki gaba d’aya? Dan zama da irinki ai tamkar zama da annoba ne, amma na tabbata idan Mahabu ya sami wannan labarin sai ya ida cikata maki biyun”
“Inna to ai bata fad’a mana wanda yayi mata cikin ba ko?” Cewar Laure kenan
“Ubanki ne yayi mata, ni ina ruwana da wanda yayi mata ciki da zakice na tambayeta? Kema munafukar Allah ta’ala” Da gama fad’ar haka ta wuce sashinta cikin matsanancin 6acin rai
Sumui-sumui Laure ta wuce sashinta itama jiki a sanyaye
Suma sauran kowa ya nufi nasa 6angaren suka bar Indo anan durk’ushe ita kad’ai sai faman rizgar kuka takeyi tamkar ranta zai fita….

_Jiya nayi maku kad’an yau kuma nayi maku da yawa ko? Karku damu halin yau da gobe ne_
 *Maman Ja’afar*

 +966592551785

[4/2, 2:11 AM] Mmn Jafar M: [01/04, 10:52 p.m.]

  🌻MAHABU🌻

           12

Daga Alkalamin

Maman Ja’afar✍

Su Mahabu kusan su 6 suka fito neman motar BARAK CHADI daga nan cikin garin Sabaha
Wani Balarabe ne yazo dab da inda suke tsaye ya faka da motarsa “Barak Chadi zaku tafi ne?” Ya fad’a da harshen larabci
Basuji abinda yake fad’a ba amma ga dukkan alamu sun fahimci abinda yake nufi domin daga masa kai sukayi suduka alamar “Eh”
Umarni ya basu da su shigo cikin motar, suko batare da 6ata lokaci ko wani dogon tunani ba suka shisshiga cikin motar suka zauna.
Balaraben nan bai zame dasu ko ina ba sai a k’ofar wani gida mai gate, umarni ya basu da su biyosa a baya zuwa cikin gidan
Sudai zungum-zungum suke biye dashi domin dukkan su wannan shine zuwansu na farko Libei shiyasa bawani sanin halin larabawan sukayiba bare har su san abinda ke shirin faruwa dasu yanzu.
Gidan k’aton gidane koko nace fili domin fili ne kawai aka d’iba aka zagayeshi da doguwar katanga ta yanda mutum bazai iya haurawa ba aka saka mashi gate

****

Mutane suka gani dank’am a cikin gidan farare da jajaye, hausawa y’an Nageria da y’an Ghana y’an Chadi da sauran k’asashen da dai mutane suke yawan fita ci rani
Wasu daga cikinsu nata faman ayyuka wasu kuma dukansu akeyi, wasu ana tsattsaga masu jiki da reza yayinda wasu kuma cikin nishad’i suke abinsu, abin dai babu kyan gani
_(Kamar dai wannan gidan da aka kai su Murjanatu na Yeman a cikin littafina Idan Kunne yaji)_ 
Cikin kid’ima Sa’adu ya dubi Mahabu”MAhabu wai mike shirin faruwa damu ne kuma anan?”
“To ai nima tambayar da nakeso nayi maka kenan”
Suko sauran wad’an da suka shigo tare dasu Mahabu d’in  hanyar k’ofar gida suka nufa domin k’ok’arin barin gidan
Wasu yarbawa ne k’atti majiya k’arfi suka dawo dasu baya, saboda naushinda suka kaiwa d’aya daga cikinsu a hak’ark’ari saida ya duk’e dan tsananin azaba 
Sunaji suna gani wannan Balaraben da ya kawosu ya kar6i kud’i a gurin Ogan gidan ya juya ya fice daga gidan abinsa
“Sa’adu anya mutumin nan ba sayar damu yayi ba kuwa? Kaga dai har wasu kud’i ya kar6a a hannunsu kana ya fita”
“Ina ganin mumafa namu kwanan ne ya kusan k’arewa, sai dai muyita addu’a kawai”Cewar Sa’adu kenan yayinda hawayen danasani ke bin fuskarsa.

*****

Wannan gidan ba wani gida bane face gidan da ake kasuwancin mutane, tamkar dai yanda ake Kasuwancin Bayi a zamanin da ya gabata
Idan kanada buk’atar mai yi maka aikin gida ko aikin gona ko kuma wanda zaka dingayin Luwad’i dashi idan kai mai yin Luwad’in ne, ko macen da take buk’atr lafiyayyen namiji kala kaza da kaza duk a wannan gidan zakazo ka cake kud’inka ka siya
Bazaka ta6a ku6ukata daga wannan gidan ba har saidai idan wanda ya sayekan yayi sakaci ka gudu daga hannunsa
Gidan ga tsananin yunwa da k’ishirwa, domin a kullum ta Allah biredi biyu ne ake baku, d’aya da safe d’aya kuma da daddare
Mutane da yawa suna mutuwa a cikin wannan gidan saboda tsananin azabar da akeyi masu ko kuma yunwa, saidai da ka mutu a cikin wannan gidan ba’ayin wata maganar yi maka wanka ko salla bare a binneka, yanda dai kukasan mushen Jaki ya mutu ana kaiwa bayan gari a yar, to haka kaima za’a kaika bayan gari a yar

*****

Kwanansu Mahabu arba’in a wannan gidan Mahabu yayi sa’a wani Balarabe yazo ya siye shi a zuwan zaije ya dinga yi masa Noman rani
Sunyi matuk’ar shak’uwa da Sa’adu shiyasa a lokacin da Mahabu zai tafi har kuka sukayi na rabuwa da juna, wanda ba mamakima daga wannan rabuwar mai yiyuwa bazasu sake had’uwa ba kuma har abada.
Da wannan damar Mahabu ya samu ya sulale daga hannun wannan Balaraben bayan yayi masa aiki na tsawon sati biyu
Batare da 6ata lokaci ba ya nemi motar BARAK CHADI, amma a gurin shiga motar saida yayi taka tsantsan sosai gudun kada a sake maimaita abinda ya faru a baya

*****

Tafiyar kwana d’aya ce ta kawo su Mahabu Barak Chadi daga nan kuma ya nemi motar zuwa QA’D’DAHIYA
Daga Qaddahiya motar GULULEK suka nema saboda tun a Barak Chadi ya samu abokan tafiya
Kwanansu Mahabu biyu a Gululek suka hau motar Shanu domin wucewa ZILLETAN
Shinfid’u ne direban yayi a bayan motar tamkar masu shirin yin bacci ba masu shirin yin tafiya ba
Cikin mamaki Mahabu ya dubi Qadiri d’aya daga cikin abokan tafiyar tasa kenan wanda shima ya kasance haifaffen k’asar ta Nijar
“Wai mai motar nan kodai shirin rena mana hankali yakeyi tunda kud’inmu sun riga sun shiga hannunshi? Dan ni yanzu na daina yarda da jajayen nan”
“Kaidai ka tsaya ka gama ganin sarautar Allah  mana” Ya fad’a a tak’aice 
Koda gama wannan shinfid’ar direban ya umarcesu da su shisshiga su kwakkwanta a ciki
“Ita dama motar taka ta kwanciya ce bata zama ba?” Cewar Mahabu kenan
“Baka ta6a bi ta wannan hanyar bane?” Cewar direban kenan
“Eh” Ya fad’a a tak’aice 
“To saboda tsoron hukuma ake kwanciya domin hukumar Libiya bata buk’atar bak’i a cikin k’asartata, shiyasa suke d’aukar k’wakk’waran mataki akan hakan, shiga idan zaka shiga, idan kuma motar zama kake nema zauna nan kaita jiranta kaji?” Yana gama fad’ar haka ya shigewarsa gaban motar yayi zamansa
Kamar yanda direban ya umarcesu haka kuwa sukayi
Kowa ya kwakkwanta akan wannan shinfid’ar daga bisani kuma aka kawo manyan Barguna aka lullu6esu, kana daga nan kuma aka samo Ganyayyakin Ciyawa aka d’odd’ora asamansu, a zuwan abincin dabbobi ne aka d’ebo daga Daji
******
“A’a Indo lafiya kuwa naga kin shigo mana da wannan irin kuka haka? Kefa matsalata dake kukan sakalci wallahi, ko duk kukan rashin Mahabu d’in ne ba’a gama ba har yanzu?”
Cewar Mahaifiyar Indo d’in kenan yayinda ta dakata daga wura wutar tuwon daren da takeyi ta kamo hannun y’ar lelen tata zuwa d’aki, dayake mahaifin Indo din yana gida kuma uwar baso takeyi yaji abinda zasu tattauna ba shiyasa taja y’ar tata zuwa d’akin.
Cikin kuka Indo ke labartama uwar abinda ya faru, tun daga farko har zuwa inda Affa yayi mata saki d’aya, abu d’aya ne kawai ta 6oyewa uwar wato sunan wanda yayi mata cikin
Itama uwar kuka ta saki mai tsananin gaske yazamana da uwar da d’iyar babu mai bawa wani hak’uri
“Indai auren d’an Libei ne kad’an ma kuka gani daga irin matsalolinda yake haifarwa, dama ai na fad’a maku wanda baiji bariba dolensa wata rana yaji Wohoho”
Cewar mahifin Indo d’in kenan wanda ya kasance a bakin k’ofar d’akin tun lokacin da suka fara maganar
Cikin hanzari ya koma d’akin sa ya d’auko wata tsaohuwar shar6e6iyar wuk’arsa data dad’e a ajiye
“Kodai ki fad’a mani wanda yayi maki wannan cikin ko kuma na kasheki na huta da bak’in cikin da kika dad’e kina dasa mani a cikin zuciyata, inyaso nima a kasheni na mutu gaba d’aya sai kowama ya huta” Yana magana hawaye na bin fuskarsa
“Mamm..man ne” ta fad’a cikin sassark’ewar murya
“Badai Mamman aminin Mahabu ba?” Uwar ta tambaya cikin kid’ima
Shuru y’ar tayi wanda hakan ya tabbatar masu da lallai shid’in dai take nufi
“Aiko wannan abin kunyar badai a wannan gidan ba wallahi sai dai ki san inda zaki nufa” Tsohon yana magana hawaye na bin fuskarsa abin tausayi……

Muje zuwa 13 domin jin chakwakiyar da ke gaba

*MAMAN JA’AFAR*

  +966592551785

[4/4, 6:08 AM] Mmn Jafar M: [04/04, 6:54 a.m.]

🌻MAHABU🌻

          13

Daga Alkalamin 

Maman Ja’afar✍

Mai motar nan bai zame dasu Mahabu ako ina ba sai a wani gari MUSRATA a k’ofar wani k’aton gida kamar dai yanda sukayi masa kwatance
Inda ya kasance matattara ne ga bak’in dake zuwa garin musamman masu son shiga cikin K’asar ta Libiya da kuma sauran mutane masu son haurawa Italiya ta jirgin ruwa
_(Ko a cikin satin nanma naji labarin ance wajen jirgin ruwa hud’u ne ya nitse a cikin ruwa na masu son haurawa kasar ta Italiya, wanda a dalilin hakan nema ya jawo asarar rayukkan mutane  sama da dubu uku.)_
_(Haba jama’a wai me muka dauki rayukkanmu ne? Na rasa gane mai laifin daga cikinmu, shin laifin na masu yin tafiyar ne ko kuwa na gwamnatocin da suka kasa sauke hakkinda ke kansu na al’umar kasarsu ne?_
Babban gida ne koko nace babban gari saboda girmansa yafi k’arfin a kirasa da gida ko wata unguwa saidai kawai akirasa da gari guda
Bene ne hawa d’aya a saman gidan kuma dai girman saman tamkar girman k’asan ne
Duk girman wannan gidan k’ofa biyu ne dashi, data shiga sai kuma ta fita
A cikinsa babu abinda ba’a sayarwa na buk’atun rayuwa shiyasama idan ka shigosa ba maganar fita, inama kaga hanyar da zaka fita d’in masu gadi tako ina?
Kuma duk girmansa da irin dinbin mutanenda ke rayuwa a cikinsa Band’aki 2 ne kacal a cikinsa.
Anan d’inma kasuwancin mutane akeyi aciki tamkar dai wancen gida dasu Mahabu suka baro
Sai dai wannan cinikin ya banbanta da wancen ta 6angare da dama
Misali dama tun farko kamin ka baro k’asarku zaka samu lambar wani d’an’uwanka ko kuma abokinka wanda ke zaune a K’asar ta Libiya kuyi yarjejeniya dashi idan kazo wannan gida zai fansheka daga hannunsu inyaso daga baya idan ka nema ka biyashi inma riba yake buk’ata sai ka k’ara mashi, duk dai kuyita dawajewa tun kamin ka taso daga gida
To da kazo wanann gida sai ka bada lambarshi suyi magana asakaka a mota a kaika har inda yake su kar6o kud’insu su dawo
Suma wannan ne kasuwancinsu kuma da wannan zalincin suke cin abinci.
******
“Qadiri kadai zo da lambar wani naka ko?”Mahabu ya tambayesa bayan shigowarsu da sukaga irin azabar da ake ganawa mutane a cikin gidan
“Alhamdulillahi nazo da ita, banida rabon wannan wahalar za’a shata dani, kaifa?” Ya tambaya yayinda yake duban fuskar ta Mahabu
Dafa kafad’ar Qadirin yayi tare da cewa
“Nima dai ka tayani murna nazo da ita, da harfa mantawa nayi da ita a k’asan katifa sadda zan taho Indo ce ta taimakeni ta tuna mani badan haka ba da ina ganin nan gidan ne ajalina tunda dama k’arfina duk ya riga ya gama k’arewa a hanya”
Wani k’akk’arfan matashi ne yazo inda suke, dayake Bayarabe ne cikin gwarancin hausarsa yake tambayarsu lambobin waya
Lambobin ya kakkar6a kana daga bisani aka umarceshi da ya kakkawo masu abinci
Cikin mamaki Mahabu ya dubi abokin nasa”Wato Qadiri indai mutum yana duniya zai dinga ganin abin mamaki kala-kala”
“Saboda mi kace haka?”
“Kallafa iya ganinka duk inda ka waiga jama’a ne dank’am y’an k’asashe daban-daban, wasu iyakarsu Libei wasuma Allah ne kad’ai yasan inda zasu tsaya, babban abindama yake d’aure mani kai Qadiri Kallafa mata da k’ananan yara ko ina birjik yanda kasan ba hanyarda na biyo mai had’arin nan suma suka biyo ba”
Yana magana yana waiwaigensa domin bawa idanuwanshi abinci a cikin gidan
Wani tsoho ne ya zo dab dasu ya zauna, wanda tun fara firar tasu yake gefe yana saurarensu
“Ai Malamai nanma kad’an kenan kuka gani tunda a kullum ta Allah ana d’ibar wasu ana kaiwa gun yan’uwansu, inda jibgewa akeyi ai duk girman gurin nan da kuke gani yayi mana kad’an sab….
Mahabu ne ya katsesa

“Amma bawan Allah su kuma way’an nan matan da k’ananan yara me sukeyi anan su kuma?”
“Eto wasu dai daga cikinsu mazajensu suka biyo, wasu kuma Karuwanci sukazoyi,  musamman ma irin wad’ancan arnan” Ya fada yayinda yake nuna masu inda arnan suke
“Wallahi duk daga Kudancin Nageria suke fitowa, wasu iyakarsu nan Libei wasu kuma karuwancin zasuyi su samu kud’in haurawa Italiya”
Ya k’ara da cewa
“Yo shuwagabannin K’asar tamu ne duk gasu nan dai abin sai addu’a kawai, saboda basu kishinmu bare kuma kishin rayukkanmu, kaga idan akace maka K’asar Nijar Nageria Ghana Chadi Kamaru Benin da dai sauransu…babu inda aka tattara 6arayin  gwamnati marasa kishin k’asa da kuma cigaban K’asar irin way’an nan k’asashen dana lissafa maku, shiyasa kullum mu bama gida muna kan hanyar bin K’asashen da suka samu cigaba neman arziki ta yanda zamu rufawa kanmu asiri da kuma iyalanmu, wanda inda za’a  baje abin a faifai wallahi tallahi ina mai tabbatar maku babu abinda K’asar Saudia ko Sudan ko Libiya zasu nuna mana barema har muyi tunanin tafiya K’asashensu neman kud’i muita rasa rayukkanmu a banza a wofi, wallahi ina mai tabbatar maku da sai dai azo nema a k’asarmu badai mu muje nema a k’asar wasu ba”
_Mutumin yana magana hawaye na bin fuskarsa abin gwanin tausayi Tamkar dai ni Maman Ja’afar da nake zubar da hawayena a lokacinda nakeyi maku wannan typing d’in_
Qadiri ne ya numfasa”Kabar ma maganar Nijar, dama kowa yasan mu haka muke kullum jiya i yau, ni babu ma irin mulkinda ke ci mani tuwo a k’warya kamar mulkin mak’wabciyarmu Nageria, sunyi sa’a Allah ya basu shuga nagari wanda wasu ke neman irinshi ruwa ajallo basu samu ba, amma su Allah ya basu sai faman wulak’antawa suke, gafa shugaba na gari amma y’an hana ruwa gudu sai dak’ile masa aikinsa sukeyi, kullum yana tubka su kuma suna warware, inko a na haka ai babu ranar da zamu daina fita ci rani kenan K’asashen wasu?”
“Allah dai ya kawo mana agajin gaugawa a cikin wannan lamarin” Cewar Mahabu kenan
******
“Haba haba Malam, idan kace Indo ta bar gidan nan ina kakeso ta nufa sabida Allah? Ai yin hakan tamkar  k’arin wani abin kunya ne agaremu, yanzu ba kowane ya san da wannan maganar ba amma barinta gidan nan shine zai jawo hankalin mutane zuwa garemu, wanda yin hakan kuma ba k’aramin gore-gore da habaici zaija mana a  cikin garin nan ba, k’arshentama nan gaba kad’an ko fita nanda k’ofar gida ya gagaremu dagani har kai”
Itama dai kamar Malam d’in tana magana hawaye na bin fuskarta
“Abin kunya kuma na nawa Rabi? Ai saidai kar a kuma”
Mai da wuk’ar yayi cikin kubenta ya fara wasu yan dibi-dibi na rashin takamaimen abinyi, ga dukkan alamu tsohon a rud’e yake, can dai ya numfasa yace
“Rabi bata gyale ta yafa muje gidan Kashe”
“Me kuma zakuyi a gidan Kashe wanda ya wuce tonon siriri Malam?”
“Ada ne kamin tayi wannan aika-aikar a sirinmu yake a rufe amma yanzu kam ai tamkar anbazashi a Faifai ne kowa ya d’auka”
Badan taso ba ta d’auko gyalen ta mik’awa Indo, itama nata gyalen ta d’auko ta d’ora a ka, danko tsayawa yafashima batayi ba tabi bayansu zungui-zungui
*****
Babban mutum ne d’an kimanin shekaru kusan hamsin a duniya
Kashe kenan zaune a fadarshi fadawa duk sun zagaye shi tako ina
Ya hango su Indo na tunkaro inda yake gadan-gadan
Yafito d’aya daga cikin fadawan nasa yayi, fuskar nan tasa tamke babu wani alamun wal-wala acikinta domin ya gaji da irin k’ararrakin da ake kawo masa a cikin y’an shekarun nan
“Na Amma gafa wata yarinya can iyayenta sun tasota agaba, Allah yasa dai ba irin k’arar matanda suka tashi d’azu ba suma suka kawo mani?”
Kan Bafaden a k’asa saboda tsananin girmamawa yace
“Allah ya taimakeka ai saidai aita hak’uri da yan tafiya Libei d’in nan domin ba dainawa zasuyi ba”
“Ai kuwa indai abinda nake tunani akansu ya tabbata  wallahi nasan matakinda zan d’auka, mataki ne zan d’auka k’wakk’wara wanda bazaiyiwa kowa dad’i acikin garin nan ba, inyaso…
Kamin ya k’asa maganar tasa ne su Malam Audu sukayi sallama a cikin fadar
Bayan Fadawan sun amsa masu ne suka basu umarni da su zazzauna
“Meke tafe daku Malamai?”

Cewar Kashen kenan ransa a 6ace
“Ranka ya dad’e k’ara ce na kawo” Ya fad’a tare da duban Indo
“Wato ranka ya dad’e wannan yarinyar da kake gani bayan bikinta da wata d’aya ne mijinta yasa kai ya tafi Libei, to bayan tafiyar  tasa ne aka samu wani tsinannen Abokinsa ya d’ika mata ciki, to shine nakeso ranka ya dad’e a taimaka a bi mani hakkina agun azzalumin yaron da yayi mata cikin saboda ya zalincemu sosai dan yanzu hakama sirikin nata har ya saketa saki d’aya” Yana magana muryarsa na sassark’ewa alamun yaci kuka har ya gaji
Wannnan bayani na Malam Audu ba k’aramin kara 6atawa Kashe rai yayi ba, domin dama ran nasa a 6acen yake
“Malam Audu kana jina?”
“Ina jinka ranka ya dad’e”
“Kuyi hak’uri ku koma gida insha Allahu gobe goben nan zan d’auki mataki na k’arshe akan wad’an nan matsalolin da suke faruwa a cikin wannan garin nawa”
Fadawan nasa ya duba d’aya bayan d’aya idanuwan nan nasa sunyi jajir sai kace garwashin wuta saboda tsananin 6acin rai
“Inaso a tara mani mutanen garin nan dukkansu gobe i wara haka anan gurin, kuna  jina ko baku jina?”
“Munaji ranka ya dad’e Allah ya kaimu goben lafiya” Suka amsa kusan a tare cikin ladabi….
MAMMAN JA’AFAR

+966592551785

[4/4, 5:52 PM] Mmn Jafar M: 🌻MAHABU🌻

            14

Daga Alkalamin

Maman Ja’afar✍

Kamar kuwa yanda Kashe ya buk’ata washe gari tun misalin k’arfe hud’u da rabi na yamma kowa ya hallara a gabansa, babu wanda aka bari a gida sai yara k’ananu da kuma tsofi marasa lafiya way’anda bazasu iya tashi ba.
 Saida dogarai suka tsawatar sosai akan hayaniyar da jama’a keyi kana suka d’an saurara Kashe ya fara bayaninsa kamar haka
“Assalamu alaikum jama’a”
Cikin hayaniyar tasu suka amsa sallamar kana kuma daga bisani aka tsawatar masu sukayi shuru
“Ba komai bane yasa na taraku anan sai wata k’wakk’warar doka danake son kafa maku, duk wanda ya bita ya tsira wanda kuma yabi akasin hakan zai kuka da kanshi, domin tarar da zan d’orawa mutum ina tsammanin sai ya sayar da dukkan gonakinsa da kuma garkunansa kana ya biya, mai yiyiwama a hakan sai na biyoshi bashi”
Da jin wannan lafazi na Kashe nan take jikin kowa yayi sanyi, domin duk abinda Kashe ya fad’a babu makawa sai ya aikata dan irin hakan ta ta6a faruwa dasu a wani lokaci da garin suka samu albarkatun gona da yawa har suka rasa yanda zasuyi dashi mutanen birni sukaita zuwa suna banzatar masu dashi a arha, domin a lokacin bana mantawa har nera 30 suke sayar da tiyar wake, saida Kashe ya tsawatar masu ya nuna masu illar abin da kuma saka tara mai tsanani ga wanda ya aikata hakan kana suka daddara suka daina sayarwa
Kashe ne ya katse masu tunanin nasu da cewa
“Doka ce mai tsanani zan saka ga dukkan wasu masu tafiya Libei ko suke shirin tafiya Libei, kai bama Libei kad’ai ba harda sauran K’asashe da mutanenmu suke zuwa ci rani, kuma dokar ba akansu kad’ai zata tsaya ba, a’a  zatayi aiki ne har akan iyayensu maza da mata”
Shuru yayi na d’an wani lokaci kana yaci gaba da bayaninsa
“Daga rana mai kama data yau duk wanda yayi tafiya zuwa wata K’asa yadawo ya tarar da matarsa da ciki ko kuma da goyo, to babu wata maganar jayayya ko saki ko kuma wata kawo k’ara gurina, cikin nan daya tarar ko kuma goyo ni Kashe Sumaila na mallaka masashi halak malak, kuma ko yanaso ko bayaso dole ya kar6a kuma ya rik’e a mutunce tunda ba uban wani ne ya tilasta masa cewa wannan tafiyar ala dole sai yayita ba”
Numfasawa yayi kana yaci gaba da cewa
“Kuma maganar ya aiko da takardar saki daga wata K’asa ko kuma ya saka mahaifinsa ya saketa koshi mahaifin ganin damar kansa ya saketa babu ita, na rushe wannan daga yau”
K’ara gyara babbar rigarsa yayi kana cikin tsananin fushi yaci gaba da cewa
“Da wannan nake bada umarni duk wata mata da mijinta ya saketa ko mahaifin mijinta ya saka indai ba saki uku uku bane ni Kashe nace ta koma gidan mijinta, inga ubanda ya isa ya sa6a maganata kuma”
Zama yayi akan kujerar katakonsa kana yaci gaba da cewa
“Kuma duk wadda ta koma gidan mijin nata akayi mata bak’ar magana ko habaici ko gori ko wani kallon banza k’ofata a bud’e take a koda yaushe tayi gaggawar zuwa ta sanar dani ni kuma zakuga irin matakinda zan d’auka”
D’ora k’afa yayi d’aya  akan d’aya kana yaci gaba da cewa
“Wacce kuma akayiwa saki uku ina mai bata hak’uri tayi hak’uri ta zauna a gidan iyayenta amma duk ranar da mijin nata ya dawo tazo tayi gaggawar sanar dani domin ganin irin matakin da zan d’auka akanshi”
Numfasawa yayi kana yace
“Nagama maganata daga nan duk wadda ta san ansaketa ta wuce d’akinta kai tsaye”
Da wannan taron ya watse kowa ya kama gabansa, yayinda sakakkun irinsu Indo kowacce ta nufi d’akin mijinta cikin isa da tak’ama domin Kashe Sumaila ya d’aure masu gindi. 

*****

Wannan nema yasa Indo bata fuskanci wata tsangwama ko takurawa ba a wajen iyayen mijin nata da kuma danginsa, sai dai dukda haka babu mai shiga sabgar wani tsakaninta dasu.
*******
*MAHABU*
“Waye Mahabu a cikinku?” Cewar wannan Bayaraben kenan wanda yake kula da 6angaren shiga da ficen su Mahabu
“Gani ya” fad’a a tak’aice
Alamu yayi masa da ya biyosa a baya
A gaggauce sukayi sallama da Qadiri domin rabuwa ce ta ba lallai su sake had’uwa ba har abada.
Gurin su goma aka d’iba zuwa gurin wata Tasi, saboda dama gurin tamkar irin ace an ajiye mutum a Lagos ne wani zai tafi Kano, wani Katsina, wani Abuja, wani Mai Duguri.
Shiyasa sai a d’ebi kamar mutum 5 ko 10 cikin k’aramar mota wad’anda tafiyarsu tazo d’aya aje akaisu, kuma hukumomi bazasu fahimci komai ba tunda ba gayyar jama’a sukaga ankwaso ba .
*****
“Allah sarki Mahabu ashe rai kanga rai” Cewar Yusha’u kenan wanda ya kasance amini ga Mahabun tun suna yara bayan ya kar6osa gurin masu motar nan sun shigo gida sun zauna suna hutawa
“Wallahi ka cuceni, ka zalunceni iya zalunta Yusha’u”
Cewar Mahabu d’in kenan
Dariya matashin yayi sosai harda k’yak’yatawa wanda shekarunsa bazasu gaza na Mahabu d’in ba
“Da ace sadda kace mani zakazo na hanaka zuwa, ko kuma na fad’a maka gaskiyar matsalolinda ke akan hanyar, wallahi ko zan had’iyi qur’ani ina rantse maka da matsala ba yarda zakayi ba, shiyasa muna fara jayya da kai na sakar maka nace kataho d’in, yanzu ba gashi nan kagani da idanuwanka ba? Ni wallahi nazacima sak’on mutuwarka ne zai iso kunnuwana ba kai d’in ne zaka iso gareni ba”
Yana magana yana dariya abinsa, kana ya tsagaita da dariyar tasa yace
“Kudai kawai kuga mutu a wata K’asa indai tafiyar k’afa akace maku yayi har ya isa gareta, domin bakusan irin iya wahalarda ya sha ba kamin ya iso, ku matsalarku da kunga mutum yanata turo kud’i gida sai ku d’auka tamkar abin ba wata wahala ne dashi ba, yanzu ai gashi nan ka gani da idanuwanka nan gaba idan kaji wani yace maka zaizo Libei sai kasan irin amsar da zaka bashi”
Dukan bayansa Mahabu yayi cikin wasa
“Banza mugu kawai, nidai kira mun Tanimu a waya ya had’ani da Indona dan nasan wancen sakaran Mamman waya ba wani zama takeyi a hannunsa ba, ba wuya ya siya kuma ba wahala ya sayar….
Muje zuwa shafin k’arshe
*Maman Ja’afar*

[4/5, 4:22 AM] Mmn Jafar M: [04/04, 12:17 a.m.]

🌻MAHABU🌻
          15
      K’arshe

Daga Alkalamin

Maman Ja’afar✍

A lokacinda Mahabu yake k’ok’arin kiran Tanimu a waya a kuma daidai lokacin ne Tanimun yake k’ok’arin had’a Amalanke domin kai Indo assibiti, ina tsammanin k’ilan haihuwar ce ta taso (Domin Mamman tunda labari ya bazu a gari aka nemesa sama ko k’asa ka rasa) 
Wurin kwanansu uku a assibitin anata fama amma haihuwar tak’i zuwa, a cikon kwana na hud’un ne Allah ya taimaketa ta suntumo d’anta namiji kamarsa da Mamman kuwa harta 6aci domin tamkar an tsaga kara ne an ajiye kamannin nasa da uban
Sai dai abin farin ciki zance koko abin bak’in ciki yaron baizo da rai ba, domin a cewar likitocin wai watanninsa basu kai na haihuwa ba.
*****
Satin Indo uku ta samu lafiya ta dawo garau abinta tamakar ba itace ta haihu ba, a lokacin kuwa Mahabu har ya fara aiki a wani kamfani na gyaram motoci inda Yusha’u yake aiki
******
“Mahabu aradu wayar Tanimu ta shiga” Yusha’un yana magana wayar na a kunnensa ga dukkan alamu dama ya dad’e yana neman lambar
Cikin murna ya diro daga kan k’atuwar katifar mai kama da gado
“Da gaske? Banishi dan Allah” cikin sauri Mahabu ya kar6e wayar
A daidai wannan lokacin kuma Tanimun ya d’aga wayar
“Banza baho bokiti kawai, anata nemanka a waya amma kullum a kashe?”
Saida Tanimu yayi wani ihu gami da tsallen murna kana yace”Dan Allah abokina kayi hak’uri wallahi abubuwa ne sukayi yawa, kuma kasan dai ba wata wutace damu ba, kullum sai mutum ya bayar da kud’i anyi masa cajin waya, kud’in kuma basu ke akwai ba, ai nima gani nan zuwa gareku, yaushe zaka turo mani kud’i nima na taho?”
Wata muguwar dariya ce ta kunbcewa Mahabu, daidai kunnensa Yusha’u yazo yake rad’a masa “Karka fad’a masa barshi shima yazo ya d’and’ana yaji abinda muma mukaji a hanyar”
Baibi takan wannan zancen ba ya canza akalar firar tasu
“Tanimu ina Indona take? Muryarta kawai nakeson ji na fad’a mata na sauka lafiya naji irin farin cikinda zatayi”
Shuru Tanimu yayi nad’an lokaci, kana dai daga bisani yace “Yusha’u bai fad’a maka komai game da ita ba?”
“Bai fad’a mani ba, kaddai kace mani gurin haihuwa Indon tawa ta mutu?” Cikin rud’ewa yake fad’a wannan maganar
“A’a ba mutuwa tayi ba sai dai wani abu mai kama da mutuwar ya faru da ita, kai bama ita kad’ai ba kowama abin ya shafeshi..
Cikin rud’ewa Mahabu yake kallon Yusha’u duk da wayar da ke hannunshi
“Yusha’u wai meke faruwa da Indo ne kuketa faman yi mani k’unbiya-k’unbiya?”
“Saurari wayar dai Tanimun ya fad’a maka, amma ni kam wannan labarin k’wad’on bakajishi a bakina ba”Ya fad’a yayinda yake nuna masa wayarda ke hannushi
Da k’yar dai Tanimu ya kwashe labarin komai ya sanar dashi, tun bayan tafiyarsa har zuwa haihuwarda Indon tayi d’an baizo da rai ba
Bai k’arasa jin sauran bayanin daga bakin Tanimun ba yaga wani duhu-duhu ya rufe masa idanuwa, nan take ya sulale ya fad’i k’asa a sume
Dama tun farko abinda Yusha’u ya guda kenan shiyasa bai tunkaresa da wannan mummunan labarin ba
Da k’yar Yusha’u ya samu Mahabu ya dawo hayyacinshi tare da taimakon wasu y’an garin nasu
“Mamman ka cuceni, kaci amanata, ka lalata mani rayuwa, ka kafa mani tarihinda zai dinga bibiyata har y’ay’a da jikoki”
Sabbatunda Mahabu keta famanyi kenan, sauran jama’a nata rarrashinsa gami da ban hak’uri
“Dama saida Indo tace kar nafi kar nafi, nayi biris da ita, yarinyar nan har kwanciya rashin lafiya tayi saboda tafiyar da zanyi na rufe ido nak’i tausaya mata bayan nasanta sarai nasan tafi son kusanci dani fiye da komai a rayuwarta, wani lokacima idan dare yayi har fad’a mukeyi inace mata nida nagaji bazan….
Yusha’u ne ya dad’e masa baki saboda lura da yayi da abokin nasa yana neman fita cikin hayyacinsa
“Yusha’u wallahi komawa gida zanyi, zanje nabawa Indona hak’uri domin kome ya faru da ita nafi kowa sanin nine sila, wallahi tallahi ko duniya zan samu da abinda ke cikinta wannan bak’in cikinda Indo da Mamman suka k’unsa mani nasan bazai ta6a goguwa a cikin zuciyata ba, saboda haka na hak’ura da neman kud’in, zan koma gida idan talauci na kashe mutane nima ya kasheni”
Da k’yar dai suka samu suka shawo kansa ya daina sabbatunda yakeyi.
******
Washe gari tun safe yake damun Yusha’u akan ya kira masa Tanimu a waya 
“Nifa ba waya ce bana son baka ba, banaso kaita jin labarai marasa dad’i ne a gida shiyasa”
“Kaidai bani dan Allah” Cikin zak’uwa yake maganar
Zaro wayar yayi daga aljihunsa jiki a sanyaye ya mik’a mashi
Bai dad’e yana daddannawa ba wayar ta shiga
“Yauwa Tanimu kaiwa Indo waya”Abinda ya fad’a kenan bayan ya daga wayar
“Au har yanzu dai baka daina yarda da abokai akan iyalanka ba ko?”
Ajiyar zuciya yayi kana daga bisani yace”Wane abokai kuma? Ai aikin gama ya riga ya gama kaima idan kanada wata k’ulalliya a cikin ranka ai gaka ga ta nan” Ya fad’a cikin 6acin rai
“Allah ya huci zuciyarka bara na ruga na kai mata”
******
Indo tana k’ofarta tana sana’arta da ta saba wato kuka taji sallamar Tanimu
Cikin sauri ta d’auko hijabinta ta saka domin abinda ya faru agareta ba k’aramin darasi ya koyar da ita ba, shiyasama tad’aukarwa kanta alk’warin insha Allahu har abada abokin miji ko hak’orinta bazai ta6a gani ba bare kuma har a kai ga…
“Indo fito ga waya Mahabu ya bugo maki”
Wani fad’uwar gaba taji lokaci guda har saida ta dafe k’irjin nata
Jiki na kyarma ta k’ar6i wayar, bata samu damar ko yin sallama ba saima wani matsanancin kuka daya kubce mata
“Dan Allah Mahabu kayi mun rai, dan girman Allah karka sakeni, wallahi tallahi har yanzu banida tamkarka a cikin zuciyata, sharrin shaid’an ne kayi mani aikin gafar…
“Kinga yi shuru  daina kukan ya isa haka kinji? Share hawayenki”
Kamar kuwa tana kallonsa tasaka gefen hijabinta ta share hawayen nata
“A cikin abinda ya faru kowa yanada nasa laifin daga cikinmu, amma nawa laifin yafi na kowa yawa, karki damu Indo na yafe maki, kuma aurenmu yana nan nidake mutu ka raba insha Allahu”
Numfasawa yayi kana yaci gaba da cewa
“Da wannan labarin ya riskeni naso dawowa gida, to amma sai su Yusha’u suka bani shawarar akan na tsaya ko neman shekara d’aya ne nayi nasamu kud’in da zan hawo jirgi na dawo ta sama, kiyi hak’uri, ki k’ara hak’uri insha Allahu bad’i kamar yanzu Indo na tare da mijinta, gatanta kuma uban y’ay’anta”
Yana magana hawaye nabin fuskarsa, dukkan abokansu way’anda ke zazzaune a cikin d’akin saida suka tausaya mashi, kuma suka jinjinawa wannan k’arfin soyayya dake tsakaninshi da Indo.
Suko mutanen gidansu Indo har rige-rige sukeyi wajen sauraron irin hukuncin da Mahabu zai d’auka akan Indon, a ciki kuwa harda surukarta Inna Fure
Da suka fahimci masoyan suna k’ok’arin sasanta junansu ne sai kowa ya dinga sulalewa da d’ai d’ai da d’ai d’ai gudun karsu furta wani abu akan Indon Kashe ya d’au mataki akansu kamar yanda ya ambata.
******
_BAYAN SHEKARA D’AYA DA Y’AN WATANNI_
Mahabu ne na hango zaune akan babban hadonsu a d’akin uwar gidansa kuma amarya wato Indo, sunata faman fira abinsu cikin nishad’i da walwala tamkar dai dama can babu wani abu marar dad’i daya ta6a faruwa a tsakaninsu
Amma dukda hakan Indo bata saki jikinta ba sai faman wani nonnok’e fuska taketayi sai kace wata tsohuwar munafuka
“Waini Indo dan Allah yaushe zaki daina jin wannan kunyar tawa ne? Haba kullum abu yak’i ci yak’i cinyewa sai kace cin K’wan Makauniya?”
Ita dai murmushi tayi gami da k’ara jawo mayafinta ta rufe fuskarta
“To shikenan tunda har yanzu kin k’i sakin jiki dani bara kiga nayi abinda zai fissheni”
Saukowa yayi daga kan gadon nasu mai runfa ya fara rausayawa a hankali yana tafa hannuwansa duka biyun yana dukan cinyarsa yana raira wak’arsa kamar haka
_*Ayye wance tayi abin kunya*_
_*Gudun san dokinma batajeshi ba*_
_*Ayye tayi abin kunya*_
_*Jaraba ce koko rashin kunya tayi*_
_*Ayye tayi abin kunya*_
_*Kodama fanko ce bamu lura ba*_
_*Ayye tayi abin kunya*_
Dariya ce ta k’wacewa Indo taci gaba da k’yak’yatawa harma batasan lokacin da mayafin nata ya fad’o daga kan nata ba.

K’arshe
Tammat Bi Hamdullah

Kuyi mani hakuri banida lafiya ne shiyasa na d’an takaita maku labarin kunsan komai saida lafiya.

_Allah sarki_

_Soyayya babu yafiya babu mantu babu afuwa bai kamata mu kirata da sunan soyayya ba. inji ni Maman Ja’afar_

_Idan da za’a sami wanda zai tambayeni yace mani Zulaihatu miye babban burinki a duniya?_
_Zan amsa masa da cewa_
_Babban burina a duniya bai wuce ace mutanen Karkara sun samu cigaba a rayuwarsu ba, musamman ta 6angaren ilimin addini dana zamani_
_A sama masu assibito da kuma k’wararon likitici domin kula da lafiyarsu_
_Sannan kuma asama masu Kwarirrika ajawo masu ruwa ta ko ina, ta yanda ko babu noman damina zasu dingayin noman rani, wanda hakan ba k’aramin aiki zai samawa mafi yawancinsu ba, a haka har asamu rarraguwar masu fita k’asashen waje nema suna mutuwa a banza a wofi_
_Idan har wannan burin nawa yacika to kuwa bani da sauran wani burin da ya wuce ace na samu cikawa da imani_

*GODIYA*
      1
_Godiya da yabo da jinjina sun tabbata ga Allah (S.W.A) mai kowa mai komai da ya nufeni da fara wannan littafin lafiya har gashi cikin ikonsa da kuma yardarsa na kammalasa lafiya batare da ansamu wata tangarda ba_
 _Ina rokonsa ladarda yake cikin wannan d’an sakon nawa yasa muyi tarayya dani daku a ciki, kuskurenda kuma nayi ya gafarta mani_

    *GODIYA*
          2
_Ina mik’a godiyata ta musamman ga Malamata acikin wannan tafiyar wato *SADIYA JEGAL* da taimakonki da shawarwarinki na fara wannan rubutun har gashi cikin ikon Allah na kammmala litattafai har guda 3 lafiya kuma Alhamdulillahi dukkansu sun samu karbuwa a gurin al’umma_
_Nagode sosai Malamata Allah ya kara girma da daukaka ya bar so da kaunar da ke tsakaninmu_

*GODIYA*
      3
_Ina godiya marar iyaka a gareku Yan’uwana wato *TANIMU* da kuma *SULEMAN* dake K’asar Libiya_
_Kun bani gudunmuwa sosai a cikin wannan tafiyar bansan ma da bakinda zan iya gode maku ba, sai dai nace Allah ya saka da alkhairi ya kara dankon zumunci a tsakaninmu kana ya dawo mana daku gida lafiya_

*GODIYA*
      4
_Ina mika godiyata ga masoyana masu bin litattafaina maza da mata musamman ma wadan da suka juri bina tun daga littafina na farko Kalubale sukaita bina har littafina na 2 Idan kunne yaji, gashi kuma sun juri bina tun daga farkon MAHABU har zuwa karshensa, kai godiyata bazata misaltu agareku ba_
_Sai dai nace nagode nagode Allah ya bar so da kaunar da ke tsakaninmu da ku_
_Da wannan zanyi amfani wajen neman afuwa agareku ga wanda na batawa ko nayiwa ba daidai ba, ina fatan zaku yafe mani? Nidai dama bakuyi mani komai ba kuma babu wanda na rike a cikin zuciyata, idanma kunyi mani to na yafewa kowa_
_Sai kuma Allah ya sake hadamu a cikin wani littafi na daban mai dauke da labarin wata kasar kuma ta daban idan munada rai da lafiya_

*TAMBAYAYOYI*

_Shin littafin MAHABU a naku ganin wane sako yake son isarwa ga al’umma?_
_Mekuka karu dashi acikin wannan d’an takaitaccen littafin na Mahabu?_
_Shin sabon salon rubutun da nazo maku dashi na tafiye-tafiye da kuma zak’ulo maku wasu matsalolinda suke addabarmu yayi maku naci gaba da yin irinsa ko kuwa dai na canza wani salon na daban kamar yanda wasunku suka bukata?_

_Shin acikin litattafan da nayi guda uku_ 

*_KALUBALE_*
*_IDAN KUNNE YAJI_*
*_MAHABU_*
_Wanne yafi kayatar daku?_

_Bani wadannan amsoshin masoyana shine zai tabbatar mani da cewa lallai kuna tare dani dari bisa dari a cikin wannan tafiyar_

_SAI NAJI DAGA GAREKU MASOYANA_

🏵Y’AR GHANA🏵
                1
Daga Alkalamin 

Maman Ja’afar✍

“Azumi! Azumi! Daga tsakar gida uwar taketa faman k’wala mata kira
“Iye Ammah” y’ar ta amsa daga can cikin band’aki inda take k’ok’arin yin wanka
“So nawa zan fad’a maki bana son wannan wankan naki da kika tsira a cikin Makewaya iye? Duka dukanki a nawa kike? Shekarunki fa basu wuce 14 ba amma ke har kinsan ki wani shiga makewaya kice zakiyi wanka, kodai so kike asakaki a bakin duniya ne ana cewa kin matsu kema ki zama budurwa?” Cikin matsanancin 6acin rai uwar takeyiwa y’ar tata fad’a 

“Haba Ammah haba Ammah, nifa wallahi kunyar yin wanka nakeyi  a tsakar gida, dan Allah kidinga barina inayi a Makewaya d’in  kawai” tana magana tana had’awa da y’an dire-direnta murya na rawa tamkar mai shirin yin kuka
“To way’anda suka fikima anan tsakar gida sukeyin wanka bare keda kika fara k’irgar dangi yanzu, zaki fito daga Makewayar nan ko sai nazo na bad’a maki tankwa a gabanki?” (Barkono)
Da gudu y’ar ta sa6o bokitin wankan nata tayo waje, domin har yau bata manta tankwan da Ammah ta bad’a mata ba sadda  ta aiketa yin nik’a takai gurin k’arfe goman dare bata dawo ba
“Haba! Yarinya tun kina k’ank’anuwanki (k’arama)sai shegen kinibibin tsiya, ina kuma ga kin girma?”
Itadai Azumi wankanta taci gaba dayi tana rurrufe k’irjin nata da soso saboda kunyar da takeji kar agani 
Har ta gama wankan nata uwar data baje a bakin k’ofar d’aki bata daina y’an surutanta ba.
Bayan Azumi ta gama y’an shafe-shafenta ne ta dauko riga da zani zata saka wanda yayarta Baraka ta kawo mata daga Nageria, harta ware zanin uwar ta lek’o ta gani
“Azumi! Bana hanaki saka zanin nan ba ne wai? Wai meyasa kikeson rayuwa irinta manyan mata ne? Idan mutane suka ganki da zani ai sai suyi maki dariya, maza ajiye zanin nan d’auko riga da wandonki da kika saba sakawa kisaka”
Cikin k’unk’uni y’ar ta d’auko dogon wando
“Bashi zaki saka ba, mayar d’auko gajeren”
A haka badan tanaso ba ta d’auko wata y’ar fingilar riga ta saka gami da d’an guntun wando, ta d’auko hularta hana salla ta d’ora akanta, tadaiyi shiga tamkar dai yanda mahaifiyar tata ta buk’ata
K’aton tire d’in biredinta ta d’auko ta d’ora aka wanda yake ajiya a gefe guda na cikin d’akin
“Ammah na tafi sai na dawo” Y’ar ta fad’a  a tak’aice 
“Saura kuma ki dawo mani baki sayar ba, Ciiiiii Lalado”(Banza kawai sakarya)

Y’AR GHANA KENAN

Zaizo maku nan bada dad’ewa ba idan Allah ya bani lafiya

*NICE DAI TAKU*

*HAR KULLUM* 

*MAMAN JA’AFAR*

+966592551785

IDAN KUNNE YAJI 16-30

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                 15
                 NA
     MAMAN JA’AFAR

*Lifahir*

Ba wani babban gari bane can sosai ba, hasalima na iya cewa ba gari bane domin a iya ganina dai a inda muke yanzu banga gida ko d’aya ba a gurin sai motoci, alamun dai kamar tasha ce kawai akayi a gurin
Amma mai yiyuwa akwai gidaje a gaba dan dai bamu shiga cikin garin sosai bane
****
“Ina na Tahir? Ina na Tahir?”

Abinda kwandastan motar yaketa faman maimaitawa kenan tamkar anbashi hardar karatu, sai dai da harshen larabci ne yake fad’ar hakan

 
“Kungama Alhamdulillahi ga motar Tahir d’in can mun samu basai munsha wata wahala ba”
Cewar matar nan wadda tasan hanyar kenan tare da nuna mana wata
Wata zungureriyar mota ta nuna mana mai kama da jirgi wacce ak’alla zata iya cin kamar mutum hamsin
“Yanzu baiwar Allah kamar daga nan zuwa Tahir d’in zamuyi kamar awa nawa ne kafin mu isa?”
Fad’ar wata jibgegiyar mata kenan a cikinmu wacce taketa faman nishi sama-sama alamun gajiya sosai a tattare da ita

Dariya tayi kana ta mayar mata da amsa “Ai garama ki k’ara shiri sosai domin Muda isa garin Tahir inaga sai gobe, gobenma bada safe ba, shiyasa yanzu kamata yayi mu d’an zagaya cikin tashar nan mu d’an sayi  abin ta6awa wanda bazaiyi saurin lalacewa ba har mu isa saboda halin tafiya, musamman ma a ku masu yara”

ta fad’a tare da kallon inda muke mu masu goyo.
“Tunda ga Murjanatu nan kuma itace k’arama a cikinmu ai bama d’unguma mu duka mutafi sayen wani abu ba ko? ni ina ganin kawai mu had’a mata kud’in ga wani shago can na hango sai taje tasiyo mana yan kayan toye-toye da ruwa ko kuma d’an so6o, ko ya kukace?”
Tuni duk suka amince da wannan shawarar ta Baabata kowa ya kawo yan canjinsa suka had’o mani nima na had’a da nawa na nufi shagon domin siyo abinda mukeda buk’ata
“Ish tibga?” *(Me za’a baki) abinda mai shagon ya fad’a kenan da harshen larabci
Dibi-dibi na farayi domin ban fahimci abinda yake son fad’a mani ba

Ba kuma wai dan ban iya larabcin bane a’a ni larabci na na Tiyna na iya, shi kuma larabcin nan inaga na Sudan ne
Wani kyakkyawan saurayi na hango  wanda tun da zan shigo na gansa can zaune akan dogon benci yana cin biskit yana korawa da lemun kwali
Ga dukkan alamu yana lura da abinda ke faruwa tsakanina da mai shagon
Daga can naga ya taso ya tunkaro inda muke
“Allah sarki! baiwar Allah hala bakya jin larabci ne?”
“Eh wallahi, dan Allah ko zaka taimaka mani ka fad’a masa abinda nake buk’ata?”
“Babu komai, ai taimako lada ne dashi musamman ma taimakon mace kyakkyawa irinki”
Murmushi nayi domin tabbas naji dad’in wannan yabon da yayi mani
Bayan na gama sayayyar ne na fiddo kud’i da niyar zan bawa mai shagon
“Bar kud’in ki Kyakkyawa na riga na biya,  domin kamarki bai cancanci ace tana biyan kud’i idan tayi sayayya ba”
Nanma dai Murmushi nayi, domin wani farin ciki nake jin yana ratsa zuciyata idan ya kirani da kyakkyawa wanda bansan dalilinsa ba, dan tabbas nasan ni kyakkyawa ce amma koda wasa Haro bai ta6a kirana da suna kyakkyawa ba
Duk’awa nayi da nufin zan d’auki kayan, sauri yayi ya rigani d’auka tare da d’orawa bisa kai
“A’a Malam ya haka kuma? shisshigin nakafa yana nema yayi yawa”
“Laifi ne dan na d’aukarwa kyakkyawa irinki kaya?” ya fad’a yana wani kashe mani ido
“A’a ba laifi bane amma dai kabarsa kawai zan d’auka da kaina, nagode d’awainiyar ta isa hakanan”
Bai kulani ba saima rik’o hannun Hamza da yayi 
“Abokina miye sunanka?”
“Sunana Hamza”
“Hamza zakayi abota dani?”
“Eh” yaron ya fad’a tare da d’aga masa kai alamun amsawa

Da dai na lura zasu 6ata mani lokaci tafiyata nayi na barsu a gurin, amma bana yin sauri sosai dan kada na 6ace masu su kasa hangoni
“A’a Murjanatu! ya akayi na ganki hannu ba komai? kodai baki samo bane? ina kuma kika baro Hamzan?”
Tambayoyi kusan guda uku Baaba ta jero mani yayinda ta ganni ni kad’ai zik’au
Kafin na bata amsa tuni har sun k’araso
Sallama yayi masu kana cikin ladabi ya duk’a ya gayar dasu su duka
Cikin shakku da Kuma mamaki fal a fuskokinsu suke amsa gaisuwar tasa
Mik’o mani kayan yayi tare da yi mani sallama ya tafi abinsa
Amma ga mamakina motarda muke niyar shiga ita naga wannan saurayin ya shiga, ga dukkan alamu shima inaga Tahir d’in yakeson tafiya.
Muma cikin sauri muka gama cin biredin da na siyo mana da lemu muka isa inda motar take muka biya kud’in mu muka shiga muna jiran ta ida cika mu ganmu a Tahir
“Abokina! zo nan mana kusa dani ka zauna Ko har abotar ta warware ne?” Ya fad’a tare da mik’owa Hamza hannu alamun yaje gunsa
Juyawar nan da zanyi sai ko ganin wannan kyakkyawan saurayin nayi mai arhar Murmushi yana zaune a kujerar bayana yanata faman Murmushinsa kamar yanda ya saba
Shiko Hamza da murnarsa ya zagaya inda Abokin nasa yake yayi d’are-d’are a bisa k’afafuwansa sunata fira abinsu, dayake Hamza akwai shegen surutu idan yasamu sarari.
Saida muka 6ata kusan awa guda a tashar nan kana motar ta samu cika muka kama hanya ba ji ba gani tafiya muke ba kakkautawa, salla ce kawai ke tsaida mu.
Muda muka baro Lifahir tun safe bamu muka samu isowa garin Tahir ba sai washe gari wajejen k’arfe 12 na rana……

Kai Murjanatu bakida dama, ana ruwa yaci makad’i ke kuma kina cewa gangarsa ta jik’e.
Ana wata ga wata…

Kardai ku gaji kuci gaba da bina domin jin yadda wannan Chakwakiyar zataci gaba da kasance wa

    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                  16
                  NA
     MAMAN JA’AFAR

*Garin Tahir*
Shima dai babban gari ne ba laifi kamar sauran, na iya cewama duk yafi sauran garuruwanda muke yada zango girma da Kuma cikowar mutane, badan ma naji masana hanyar suna cewa daga nan sai Sudan ba da in suka barni sai na iya cewa nan ne Sudan d’in.
Sassaukowa mukayi a motar kowa ya kama gabansa, sai iya muda muka taho tare mukayi ayari guri guda muna nema n motarda zata kaimu Zangon
Nura ne yaje ya taro mana motar da zata kaimu cikin gari kamar yanda naji ya fad’awa Hamza sunansa a cikin mota
Babbar mota ce wacce zata iya kwashemu mu duka, sukayi ciniki da Nura yazo ya fad’a mana yanda sukayi, muka harhad’a kud’in muka mik’a masa shi kuma yaje ya kaiwa mai motar.
Sai dai me? lokacin da su Baaba suketa shiga cikin motar  a dai dai wannan lokacin ne Hamza yace mani zaisha ruwa, sauke jakata nayi da nufin zan d’auko masa ruwan, kafin na basa ruwan ne naji carab an rik’e mani hijabi daga bayana, juyawar nan da zanyi kawai sai mukayi ido hud’u da Yan sanda, nagane yan sanda ne ta irin kayanda ke saye a jikinsu, kuma dama tun a Tiyna mun sami labarin ana yin kame a garin Tahir kamar dai yanda ake yin kame a K’asar Saudiya
Juyowa nayi da nufin ko d’aga murya nayi saboda su Baaba su san halinda nake ciki, amma ga mamakina sai naga gurin wayam babu su babu alamarsu.
Ni ina kuka Hamza yana kuka dani dashi babu mai lallashin wani
Amma saboda rashin tausayi da rashin imani irin nasu a haka suka tasa k’eyarmu har ofishinsu na yan sanda
“Fiyn raha” (Ina zaki tafi)

Abinda babbansu ya fad’a kenan bayan an gabatar dani a gurinsa
Bance masa komai saboda banji abinda ya fad’a d’in ba
Kusan sau uku yana maimaita mani wannan tambayar amma ko amma ko uffan bance masa ba, saima hawaye dake bin fuskata na rashin sanin takamaimen inda rayuwata ta dosa, saboda nasha jin ana cewa yan sanda iyayen sharri, shiyasa bansan abinda ka iya zuwa ya dawo ba
Da dai ya fahimci ban gane abinda yake nufi ba sai yayi mani ta kurame, nima da kwatance-kwatancen nake mayar masa da amsa
Juyawa yayi gurin wa’yanda suka kamoni suka tattauna wasu maganganun da bana fahimtar abinda suke cewa saboda duk da larabci suke yin maganar tasu
Kwatsamun tsawa d’aya daga cikinsu yayi, kana yamun alamu dana mik’e na biyosa, jikina na kyarma na mik’e Hamza na biye dani muka bi bayansa har zuwa wani babban guri inda mata da yawa suke aciki, kowace tayi huri-huri da ita tamkar ank’watota daga bakin kura
Nima tullani yayi a cikinsu kana ya mayar da k’ofar ya rufe da wani k’aton kwad’o
A rud’e na nufi gun matanda na tarar a gurin ina tambayarsu
“Dan Allah bayin Allah ina ne nan gurin kuma me nayi suka kawoni nan suka rufe?”
Idan dutse ya tanka to itama matar da nakeyiwa magana ta tanka, ido kawai ta bini dashi
Nan take lamarin ya k’ara bani tsoro, can na hango wasu matan hausawa su 2 a gefe sunata fira a tsakaninsu suna dariya tamkar dai basu da wata matsala dake damunsu a duniya
“Dan Allah bayin Allah me nayi suka kawoni nan suka rufe?” na fad’a yayinda nake shesshek’ar kuka ina fyatar majina
Dariya naga sunata famanyi su duka biyun hadda k’yak’yatawa, can dai yar farar wadda a tsammanina zatayi irin shekara talatin d’in nan a duniya ko sama da haka ta tsagaita da dariyar tata gami da dubana
“Amma dai ke bak’uwa ce a garin nan ko”
Kukan da nakeyi baisa na iya bata amsa ba sai d’aga mata kai da nayi alamun amsawa
Nanma dariyar suka k’arayi
“To ai Malama mai idanun kuka, nan basai mutum yayi komai ake kawosa ba a’a indai suka fito kamensu suka had’u da kai kawai kamaka sukeyi saboda basaso irinmu bak’i masu wucewa Sudan wai su cika masu gari”
Cikin kid’ima na sake dubanta 
“Yanzu kina nufin nan zamu cigaba da zama kenan ko kuwa k’asarmu zasu mayar damu?”
Yanzu d’ayar ce ta bani amsa, yar bak’ar kenan wacce ga dukkan alamu zasuyi sa’annin juna ita da farar
“Ina kuwa zamu zauna anan sai kace munyi kisan kai? in kuma sukace zasu mayar damu najeriya ai saidai suyi su gaji domin  ba fasa bin wannan hanyar za’ayi ba har abada, sati biyu kawai zamuyi su sakemu musan inda dare yayi mana, in kuma bazaki iya zama anan har na tsawon sati biyun ba sai ki biya tara na *June* d’ari uku sai su sakeki yanzu yanzun nan…..
D’ayar ce ta katseta
 “Inba asara ba me zaisa na bayar da kud’ina hakanan kawai dan asakeni, bayan ba dukana akeyi ba, ba zagina akeyi ba, inma da matsala guda d’aya ce  bata wuce ta yunwa ba, ba gara na jurewa yunwar ba inyaso su kud’in nawa na adana abina sa rage mani hanyar zuwa Sudan, ko ya kikace K’awalliya?”
Ta fad’a tare da mik’awa k’awar  tata hannu suka ta6a tare da yin shewa
“Iko sai rabbani” Abinda na fad’a kenan a cikin zuciyata kana na samu gefe guda na zauna ina shawarwarin abinda ya kamata inyi
Shin kud’in yakamata na bayar tunda da kud’i a tare dani su sakenin, ko kuwa na hak’ura d’in kamar yanda wa’yancan matan suke fad’a nayi zaman sati biyun anan domin na tsira da kud’ina?????

Hmmm shawara dai ta rage ga mai shiga rijiya, inma ta kai zai fad’a, inma ta K’afa, duk shi dai yasan wanne ne yafiye mashi sauk’i

    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          jiki ya tsira
               17
               NA
 MAMAN  JA’AFAR

*A cikin mota*
“To wai ke Talatu miye dalilinki na cewa mutafi mu bar Murjanatu tare da yan sanda? Karki mantafa Murjanatu duk garin nan bata san kowa ba sai mu kad’ai, anya munyi mata adalci Kuwa?”
Abinda Baaba Habiba taketa faman maimaitawa kenan tun lokacin da suka tafi suka bar Murjanatu tanata faman kokawa tare da yan sanda
“Nifa bada wata manufa nace mu tafi mubar Murjanatu a wannan gurin ba, dole ce tasa, dan inba dole ba yaza ayi mutaho tare kuma mu barta a wani guri? ko so kike su had’a hardamu suje su kulle? to wannan tafiyar da kikaga sunyi da ita ina mai tabbatar maki sai tayi sati biyu cur a hannunsu kana su saketa, haka nan kawai su 6ata mana lokaci”

Lokaci guda kuma ta mayar da fuskarta abin tausayi

“Allah sarki baiwar Allah gashi bata san kowa ba a kusa bare a samuma mai kai mata abinci” 

Ta k’arasa maganar tata cikin alamun tausayawa
“Karku damu Mama Insha Allahu da mun sauka Zango ni d’in nan zan dawo naje na dubota” Cewar Nura kenan wanda yake a gaban mota tare da wasu maza su hud’u
“Kujini da sakaran yaro, kai wani irin mara hankali ne da ana gudun yan sanda kai kuma kana k’okarin kai kanka inda suke?”
“Ai yan sandan nan ba irin na k’asarmu bane da idan suka kama mai laifi suke had’awa da wanda babu ruwansa, su wa’yan nan wad’anda kika gani  wanda keda laifi shi kawai suke kamawa, bare ita kuma da batayi masu laifin komai ba, kawai kamen gari ne suka tashi ya rutsa da ita” 

Cewar matar da aka kira da Talatu kenan, wato masaniyar garin
“Ai Mama komu duka muka d’unguma mukaje ganinta ba wanda zai kulamu daga cikinsu, tunda ba aiki suka fito yi ba, kuma su anasu sakarcinma wai duk wanda sukaga ya kawo kansa a gurinsu wai a tunaninsu nan mai gaskiya ne”
Dariya suka kwashe da ita su duka kana kuma daga bisani aka tsaida magana akan idan ansamu natsuwa Nura zaije ya kai mata abinci tare da dubo halinda take ciki.
*****
*Ofishin yan sanda*
Ada kam zuciyata sai raya mani takeyi akan gara na bayar da kud’in na fita salin alin, amma kuma daga baya da nayi lissafin irin kwanakin da zanyi kana na mayar da kud’in da zan bayar d’in sai nabar maganar fitar na mayar da hankalina wajen k’irgen iya kwanakin da zanyi nabar wajen
Wata zuciyar kuma cemani takeyi to Murjanatu idan kika bar nan ina zaki tunkara keda bakisan kowa ba agari?

Nayi nisa a cikin tunanin nawa kukan Hamza ya dawo dani hayyacina
“Mama Inwa nakeji, cikina ciwo”
“Daina kuka zo ka kwanta kaji D’ana? Yi hak’uri yanzu zan nemo maka abinci kaci kaji Hamza na?”
Lamo yayi a jikina ina shafa kansa, a zuciyata kuma ina tunanin inda zan nemo masa abinci bayan gani a kulle.
Wani d’an gajeran d’an sanda ne naga yana k’okarin bud’e magark’amar tamu 
“Ummu Hamza”

Abinda ya fad’a kenan yayinda yake tsaye a bakin k’ofar
Kallon kallo muka farayi a tsakaninmu duk cikinmu an rasa wanda zai amsa masa
Cikin tsawa ya k’ara maimaita abinda ya fad’a d’azu
” Wai Yaron gurinki ba shine Hamzan ba?”
Abinda d’aya daga cikin matan da muke tare dasu ta fad’a kenan bayan tazo dab dani
“Eh Hamza sunansa, amma ai shi Ummu Hamza naji yana tambaya” 
Murmushi tayi kana ta dafani”To ai baiwar Allah ke ake nema a waje, mahaifiyar Hamza fa kenan yake nufi”
Zungum-zungum na bisa a baya har zuwa inda wannan babban teburin yake, inda nake tsammanin nan ne babbansu yake zama
Abinda nagani ya bani mamaki matuk’a domin na dad’e da fidda ran zan sake ganin Nura a rayuwata
Cikin tausayawa ya dubeni

“Murjanatu Kinga kuwa yanda kika zama cikin awannin da basufi uku ba?”
Banyi mamakin sanin sunana da yayi ba domin ina kyautata zaton Hamza ne ya fad’a masa
Bance masa komai ba inbaya ga Murmushi da nayi
Duk’awa yayi tare da kama hannayen Hamza
“Abokina waya ta6a mun kai naga hawaye duk sun bushe a fuskar taka?” 
“Inwa nakeji tun d’azu, kuma na fad’awa Mama amma bata bani abincin ba”
“Allah sarki! To yi hakuri kaji? ga abinci nan na kawo maku” Ya fad’a tare da mik’awa Hamza kular da yazo da ita
“To ni Murjanatu zan koma, sai kuma dare idan Allah ya kaimu zan dawo na k’ara kawo maku abincin, dan Allah ki kular min da Abokina sosai”
Godiya nayi masa kana ya juya ya tafi.
Har ga Allah na jidad’i matuk’a yanda Nura yake kula dani da Kuma D’ana, ban ta6a tsammanin kulawar tasa ta kai k’ololuwa haka ba sai yau
 Inama ace ni ba matar aure bace? “Astagafurullah” abinda na fad’a kenan a fili kana d’aya daga cikin yan sandan ya tasa k’eyata har zuwa inda na baro ya dannani tare da saka wannan k’aton kwad’on ya rufe kamar dai yanda yayi d’azu.
****

Tun daga wannan lokacin Baabata take dafa abinci tana bawa Nura yana kawo mani dayake masaukin namu  danasu Nura kusa da kusa yake kamar yanda Nuran yake bani labari, har zuwa lokacin da na cike kwanakina a Sijin (Magark’ama) aka sallamoni.

****

Yauma dai Nura ne yazo ya d’aukeni muka tafi, saboda idan aka barni ni kad’ai bansan inda zan tunkara ba.
Nayi mamaki k’warai yanda na sami masaukin namu, domin wannan karon ba irin gidajen Ledoji bane dana saba gani a’a gida ne lafiya lau amma d’akunan da ke ciki sun tasanma sha biyar

D’akin tsakiya Nura ya nuna mani kana yayi mun sallama ya juya abinsa.
Sallama nayi tare da kutsa kaina a cikin d’akin

Da hanzari Baaba tazo ta tarbeni tare da d’aukar Hamza
“Sannunku da zuwa, sannunku da zuwa”
“Maraba da bak’in Sijin” Abinda Talatu ta fad’a kenan cikin zaulaya
Suko sauran yan d’akin ko kallon tsiya ban ishesu ba, da yake d’akin kusan mutum bakwai ne a ciki.
****

Duk irin neman da muka tarar anayi a Jammaina da Kusuri gami da Tiyna nanma shi muka samu akeyi, na nanma d’in ma har yaso yafi na sauran garuruwan wuya domin daga nan ne muke saka ran haurawa Sudan, tudun na tsira kenan.

***

Dayake Nura yazo da yan kud’ade a tare dashi shiyasa zaman da yayi a Tahir baifi na wata biyar ba ya haura Sudan abinsa tare da yi ma su Murjanatu cikakken bayanin inda zasu samesa idan sunzo Sudan d’in, inaga harma lambar waya ya rubuta a takarda ya basu suka ajiye sakamakon irin zaman dad’in da sukayi dashi.
Suko su Murjanatu dayake babu wasu kud’aden kirki a hannunsu saida suka kusan shafe shekara guda cur a Tahir kana suma suka samu damar haurawa garin Sudan….

 Wannan kenan.

Wasa farin girki, yanzu ne zamu shiga labarin IDAN KUNNE YAJI JIKI YA TSIRA gadan-gadan. Ku dai ku biyoni kusha labari

Afwan masu karatu, kuyi mani hakuri zan d’an tafi d’an tak’aitaccen hutu na yan kwanaki badan naso ba sai dan na kara ja baya na d’aura d’amarar kawo maku labarin Sudan yanda yakamata, yanda kuma zakuji dad’i

Ayi mani afuwa kunsan abin na yan koyo ne sai a hankali😭👏👏

    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                18
                NA
    MAMAN JA’AFAR

 *KHARTOUM*
Babban birnin Sudan kenan, garinda tun ina yar mitsitsiyar yarinya nake mafarkin zuwansa, yau dai gani a cikinsa kwatsam kamar a mafarki burina ya kusa cika, dan banace ya cika ba sai sadda na ganni ina da Motoci anayi mani haya, gidaje da Kuma shaguna nasaka yan haya, garkunan shano da na awaki gami da Raguna su kuma na wakilta wani wanda zai dinga kular mani dasu.
“Allah Ameen ya Allah”
Abinda na fad’a kenan a fili bayan na gama tsara dukkan yanda rayuwata zata kasance nan gaba
“A’a Murjanatu kedawa kike ta faman surutu ne naji kinata fad’in ameen?”
Abinda Baabata ta fad’a kenan yayinda take d’auke da murmushi a fuskatarta
“Wallahi Baaba babu komai, hakanan kawai nake jina yau cikin farin ciki, wani sakayau nake jina tamkar an sauke mani wani k’aton gungumen dutse da na dad’e d’auke dashi bisa kaina”
“Ai dole kiyi murna yarinya, nima murnar nakeyi saboda daga yau munyi bankwana da irin wa’yancan wahal-halunda muka baro a baya, yanzu duk abinda zamu nema namu ne na k’ashin kanmu ba tarawa zamuyi dan mu haura wani gari ba”
 Cewar Talatu kenan yayinda  take sauke jakar ta daga cikin motar da muka firo
“Ina kuwa muka huta bayan ba zama mukazo yiba nanma d’in ai  neman zamuyi, ko ku mik’e k’afa kukazo yi?” Cewar Baaba Habiba kenan yayinda ita kuma take k’okarin d’ora jakarta aka
“Kumafa hakane da gaskiyarki, Allah dai yayi mana jagora”
Kafin mu gama surutan namu har abokan tafiyar tamu da muka taho tare dasu daga Tahir tuni har sunyi gaba
“A’a Iya Talatu! gasu canfa sun tafi kada suyi mana nisa muyi sauri mu cimmasu” Na fad’a yayinda nake nuna mata ayarin matanda sukayi mana nisa
“Rabu dasu, dama mun riga munzo iyaka dole kowa ya kama gabansa, dan Zango a wannan garin ai yafi a k’irga”
K’ara nausawa mukayi a cikin tashar domin neman motar da zata kaimu *Mayu goro* kamar dai yanda naji   Iya Talatu ta fad’a, da yake a *Shabi Indirman* motar da ta d’aukomu daga Tahir ta ajiyemu.
Nidai sunan munzo Sudan ne amma har yanzu ni ban yardarwa zuciyata akan cikin Sudan d’in muke ba, saboda wata k’azamar unguwa ce marar tsari da kuma rashin  kan gado motar tamu ta ajiyemu, yanzuma d’in motar da muke ciki irin unguwannin da take ta ratsawa kenan
Tun a cikin motar nake k’arewa Unguwannin kallo, Unguwanni ne masu yawan cikowar mutane da Kuma hada-hadar jama’a, sai dai kash: yanda na tsammaci mutanen garin ba haka na samesu ba, domin ni a tsammanina mutanen K’asar Sudan gaba d’ayansu farare ne tamkar larabawan Saudiya, amma saidai ga mamakina sai na sami garin akasin haka domin bak’ak’e ne wuluk na tarar dasu tamkar yan Chadi, sai dai ba’a rasa d’an banbanci a tsakaninsu da yan Chadin ba kamar na kyau haka da kuma laushin fata
Inaga bak’in nasu nema yasa mafiya yawan kayan mazajen nasu suka kasance farare tas, domin wata faffad’ar riga ce naga suna sakawa kamar shakwara haka, wandon ma mayalwaci ne dan fad’insa ina tsammanin zai kusan kai wani bujen.
Suko matan garin ba hijabi naga suna sakawa ba kamar mu yan najeriya, a’a wai bayan sun saka kayansu lafiya lau wani k’aton gyale ne kuma suke d’aukowa su zagaye dukkan jikinsu dashi tun daga saman kansu har zuwa tsinsiyar k’afafuwansu, idan ban manta ba naso naga irin wannan shigar a Mai duguri lokacin da mota ta ajiyeni a tasha.
Ina can ina tunane-tunane na har bansanma lokacin da muka iso Zangon ba
“Murjanatu kodai motar tayi maki dad’i ne shiyasa kika k’i saukowa” Cewar Baaba Habiba kenan yayinda take rik’e da hannun Hamza
Sai yanzu na fahimci ashe su harma sun sauka daga cikin motar ni kad’ai suke jira.
Tafiyar da mukayi ba wata mai nisa bace muka samu isowa Mayu goro wato zango kenan
Dayake muna tare da yar gari shiyasa bamu sha wata wahala ba wurin had’uwa da Sarkin Zango
“Ranka ya dad’e bak’i ne mu, zamu d’an zauna anan ne kamar na tsawon sati d’aya zuwa biyu kafin dai mu samu gidan haya, shine nace bara mu tambayeka kamar nawa zamu bada kud’in hayar?”
Abinda Iya Talatu ta fad’a kenan bayan an gabatar damu a gurin Sarkin Zango
“Karku damu bayin Allah, dan dai sati d’aya zuwa biyu ai ba wani abu bane da har sai kun bada kud’i, kuyi zamanku kawai badamuwa Allah yasa mu dace”
Godiya mukayi masa sosai kana muka koma ciki.
Gaskiya gidan bashi da wani cikakken kyawu bare kuma tsari, sai yanzu ne na fahimci dalilin da yasa Iya Talatu tace masa sati d’aya zamuyi zuwa biyu anan
Haba gida sai kace assibitin marasa galihu, assibitin ma a 6angaren yan haihuwa, saboda fili ne kawai aka d’iba kowa ya kakkafa runfarsa kamar dai sauran wad’ancan zangunan da muka baro, ina tsammanin ma wad’ancan d’in zasu d’an fi wannan yar dama-dama kad’an.
A daddafe nidai na daure har mukayi kwana 5 a gidan kana muka samu wani gida acan nesa da nan inda duk wata zamu dinga biyan Alif 2 (Kimanin dubu biyu kenan na najeriya) 
Shima dai Sammakal, dan shima ba gidan bane kamar yanda na tsammata, wargad’ed’en fili ne mai d’auke da d’akunan rakubobi barkatai (D’akunan leda) barkatai kamar dai gidan da muka baro yanzu, na iya cewama yafi gidan da muka baro kwamacalar jama’a,  da kuma tarin k’azanta.
Sai da nagama k’arewa gidan kallo tsab kana na dubi Iya Talatu nace
“Iya Talatu! anya kuwa Sudan mukazo? kodai daga nan sai Sudan d’in?”
Murmushi tayi kana cikin Murmushin ta dubeni ” Nan ne mana Sudan me kika gani ne?”
“A’a ba komai nagani ba Iya Talatu mamaki ne nakeyi wai ace wannan ita ce Sudan d’in da naketa jin labari tun farko, wallahi indai itace to jinta yafi ganinta dad’i”
Dariya tayi kana tace “A’a karkice haka Murjanatu domin tunda muka shigo garin nan cikin Unguwar yan Hajjoji muke (Mazauna k’asar batare da izini ba) suko yan k’asar da sauran masu hannu da shuni ai suna can gefe abinsu, babu abinda ke had’amu dasu face mu bisu gida-gida munayi masu aikatau suna biyanmu…
Baaba Habiba ce ta katse mana firar tamu
“Kinga Talatu rabu da  shirmen Murjanatu dan Allah kizo mu k’ok’arta ko ma had’a d’akuna guda uku yanzu yanzun nan”
Zaro ido nayi gami da dafe k’irji alamun mamaki k’arara a fuskata
“Baaba kina nufin d’akunan ledojin zamu had’a mu zauna? kenan hakan na nufin nan shine mazaunin mu na har Illa masha Allahu?”
    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira

 

                 19
                 NA
       MAMAN JA’AFAR

Ko hutawa bamuyi ba muka hau had’a d’akunan da zamu zauna domin samun matsugunni
Dayake d’akunan Bakura (ledoji )ne bamu wani dad’e ba muka kammalasu duka ukun, da nawa dana Baaba Habiba sai kuma na Iya Talatu.
“Wallahi nagaji lik’is, dan Allah Iya Talatu ina ne band’aki nasamu ko ruwa ne nad’an warwatsa ko nasamu yar rahama-rahama ajikina?”
Ban jira ta kai ga bani amsa ba na dubi Hamza “To acici sarkin cin tsiya, sai wani rarraba idanuwa kakeyi kana kallon mutane nasan dai k’arshen zancen cemani zakayi kana jin yunwa ko? to maza oya cire rigarka muje muyi wanka na koma Zangon Malam Tukur na nemo mana abinda zamuci”
“Iya Talatu bakice mani komai ba ko nan d’inma sayen ruwan akeyi?” Na fad’a tare da sake dubanta
“A’a sarkin mak’o, ba siya akeyi ba dan na fahimceki sarai yarinyar nan ba son kashe kud’i kikeyi ba. Kinga ga rijiyar can an zagayeta da dangar kara” ta fad’a tare da nuna mani inda rijiyar take 
“Wato Baaba lamarin K’asar nan yana bani mamaki, ada can baya idan naji ana labarin K’asashen waje ban ta6a tsammanin ana samun irin wad’annan gidajen namu ba bare kuma wai har asamu wata aba wai ita rijiya a ciki, ni wallahi na zacima daga shigowarmu zamu fara cin karo da irin manya-manyan benayen nan, gidaje masu Tayis da A.C, Gurin  kashi irin na turawan nan irin wanda ake zama a…
Iya Talatu ce ta katse mun zancen nawa
“Kinga Murjanatu surutan ya ishemu haka, sai faman zuba kikeyi sai kace Kanyar da ba dad’i, dan Allah hanzarta ki gama abinda zakiyi ki nemo mana abinda zamuci”
Shima wannan band’akin kamar dai wanda muka baro a Zangon Malam Tukur, domin shima wannan babu inda ruwa ke tafiya sai dai idan zakayi wanka kayi da Bokiti guda biyu, d’ayan da babu ruwa ka zauna aciki, shi kuma d’ayan wanda yake da ruwa cikin shi zaka dinga d’ebowa kana wanke jikinka har ka gama, idan ka idar sai ka d’auki Bokitin wanda yake da ruwan dattin kaje can nesa da mutane ka zubar, maganar wurin yin kashima bata taso ba, domin rabona da yin kashi akan Masai inaga tun barowarmu  Kusuri.

****

Tun ina k’yank’yamin mazaunin namu har dai yakai ga nasaki jikina na manta da komai na fuskanci abinda ya kawoni k’asar wato neman kud’i.

****

A kwana a tashi yau kusan watana guda kenan a Sudan, kuma Alhamdulillahi kwalliya tana biyan kud’in sabulu, saboda a kullum rana ta Allah idan na fita gari yin bara ak’alla ba akasara ba ina dawowa da kud’i kimanin Alif biyu zuwa uku, wata ran ma idan Barar tayi kasuwa har Alif hud’u nake dawowa dasu gida (Alif d’aya idan aka lissafa da kud’in Nigeria yakan kama kusan dubu d’aya kenan)
Shiyasama yau tun a gari na yanke shawarar siyo wayata dalleliya tare da layinta domin na kira yan gidanmu tunda duk na rubuto lambobinsu a takarda sadda zan taho, koba komai sa san halinda nake ciki daga baya  kuma idan kud’in nawa sun rage sai na kira Nura.
Wayar Tsalha na fara kira tare da yin addu’ar Allah yasa bai canza layi ba, saida ta dad’e tana ringin kana ya d’auka
“Salamu alaikum” ya fad’a tare da yin kasak’e domin jin mamallakin wannan kira kuma a cikin wannan daren
“Yaya Tsalha! Nice Murjanatu”
Murya cike da mamaki yace 

“Wace Murjanatu? badai Murjanatu tamu ba?”
“Nice dai Tsalha, ina Innata take?”
Da sauri ya ruga da gudu sashensu Innar tawa, inaji yana cewa”Inna yau dai Kukanki ya k’are ga Autar taki ta bugo”
“Kai Tsalha dan Allah banason zaulaya, da gaske kakeyi ko kuwa dai irin wasan da yaranku suka saba yi mani na cewa sunga Murjanatu kaima kakeso ka d’an ta6a yau?”
“Wallahi Inna ba wasa nakeyi ba, gatama ki jita” Ya fad’a tare da mik’ama tsohuwar waya
“Alo Murja! da gaske kece?” Ta fad’a tana washe baki
Da jin muryar Innar tawa bansan lokacin da kuka ya kubce mani ba
Itama kukan naji tanayi, zuwa can ta tsagaita”Murjanatu abinda kikayi ko kad’an baki kyauta ba, kuma wannan ba irin  aikin masu hankali  bane kika aikata..
“Inna dan Allah kuyi hak’uri ku manta da komai, insha Allahu sai kunyi farin cikin zuwana K’asar Sudan”
A sanyaye tace”To Murjanatu Allah yasa”
“Inna wai ya labarin Haro kuwa? Anya yasan natafi Sudan kuwa?”
“Ya sani mana, hasalima a gunsa muka samu labari muma,  wai Huwaila ce ta fad’a masa”
Nan take naji gabana yana fad’uwar da bansan dalili ba, murya a sanyaye nace
“Inna ya damu kuwa bayan da ya samu labarin na biyo hanyar Sudan”
“Shashashar banza, kin ta6a ganin miji ya nemi matarsa lokaci guda ya rasa kana kuma ace bai damu ba? Amma yanzu naga ya rungumi k’addara tunda har gashi yayi auransa ga kasuwancisa kuma Alhamdulillahi yana ja…
Ban jira ta k’arasa maganar tata ba na datse wayar.
Yanzu irin cin amanar da Haro zaiyi mani kenan? To wallahi bazan yadda ba, koma me zai faru sai dai ya faru amma ni ba zanci gaba da zaman aure da shi ba, dama k’addara ce duk ta k’addara hakan.
Da wannan tunanin na manta da komai na danna lambar Nura, bata dad’e tana ringin shi ya d’auka dayake wayayye ne shi
“Hello! wake magana?” Abinda ya fad’a kenan bayan ya d’aga wayar
Murmushi nayi kana nace”Wata bak’uwa ce kayi daga Tahir”
“Haba dai” Kaddai kice mani Kyakkyawa ce?”
“Nice mana Kayi mamaki ne?”
“Gaskiya nayi mamaki domin ni a zatona ma kin dad’e da yada lambar da na baki”
“Hmm to yanzu dai ai ka yadda ban yadata ba ko?”
“Na yadda kam, wannan nema ya tabbatar mani da cewa kema kina tare dani a cikin zuciyar ki kamar yanda nake kwana ina tashi dake a cikin tawa zuciyar”
Ya k’ara da cewa
“Gaskiya Murjanatu daga yanzu bazan k’ara bari ki kubce mani ba domin nasha wahalar rashin ki matuk’a, shiyasa yanzu kawai abinda za’ayi kiyi mani cikakken kwatancen inda kike domin a shirye na nake tsab da gurin mallakarki a matsayin matata kuma a d’an k’ank’anin lokaci ammafa idan kin amince…..

   *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          Jiki ya tsira
                 20
                 NA
     MAMAN JA’AFAR

“Ban tari lumfashinka ba Nura, amma a tsammanina zaka tambayeni ne inada aure koko bani dashi kafin ka fara wata magana ta daban ko?” 
Na fad’a yayinda zuciyata take ci gaba da dukan tara-tara na rashin sanin takamaimiyar amsarda ka iya fitowa daga bakin nasa
Shuru yayi nad’an wani lokaci, har saidama na fara tunanin ko ya kashe wayar ne kana na jiyo Ajiyar zuciyarsa daga can 6angaren
“Murjanatu kaddai kice mani kinada aure kuma Hamza d’an ki ne na cikin ki?”
“K’warai kuwa Nura wannan magana haka take”
Ajiyar zuciya ya kuma yi

“To yanzu Murjanatu micece mafita agaremu?”
“Mafita Nura ta wuce mu manta da komai muci gaba da gaisawa a matsayin Yan’uwa? ko kata6a jin inda akayi aure akan aure?”
“Ban ta6a ji ba, amma naji wasu Malamai suna halatta hakan, kuma sunada tasu hujjar suma, kuma koke kanki idan kikaji bayanin nasu nasan zakiyi amanna da hakan, ni nan a gabana naga sun d’aura aure sama da d’ari, tun bana gamsuwa da hujjojin nasu har dai nakai ga ina fahimtar su domin suma a yanda na lura bada ka sukeyin abin nasu ba, a’a sunada hujjoji kuma a cikin Alqur’ani mai girma da Kuma hadisai ingantattu”
Cikin mamaki gami da shakku nace

“Anya kuwa Nura wannan hanyar mai 6ullewa ce? duk da banyi wani karatun addini mai zurfi ba amma gaskiya bana tunanin yin hakan zai iya halatta, kuma nifa gaskiya ko a mutanen garinmu da Malamai da kowa da kowa ban ta6a jin sun fad’i magana makamanciyar wannan ba ka dai k’ara yin nazari sosai”
Cikin k’warin guiwa yaci gaba da cewa
“Karki damu Murjanatu ki kwantar da hankalinki, insha Allahu zanzo gobe na d’auke ki na kaiki gurin Malamin kiji cikakken bayani daga bakinsa k’ilan kyafi gamsuwa”
“To Allah ya kaimu” na fad’a jiki a sanyaye
Domin wannan soki burutsunsun ko a tatsuniyoyin mutanen baya ban ta6a jin irinsa ba.
Da wannan tunane-tunanen bacci 6arawo ya sace ni
 *Washe gari*
Tun safe muna shirye-shiryen fita Bara mukaji sallamar Nura
Da gudu Hamza yaje ya rungumesa, wannan ne ya tabbatar mani da har yanzu Hamza bai manta da Abokin nasa ba
“Abokina baka manta dani ba” ya fad’a d’auke da murmushi a fuskarsa
“Aiywa, Ban manta da kai ba, kusan kullum ma sai na tambayi mamata inda kake sai dai tamun k’arya tace..
Da gudu nazo na rufe masa baki “To chakwai-kwaiwa, fad’i ba’a tambayeka ba sarkin surutun tsiya, ai dai ka bari ya zauna Ko ruwa ya fara sha ko?”
Da yake gidan namu bashida wata doka bare kuma oda shiyasa kowa ke shigowa yanda yaga dama a kuma lokacin da yaga dama kai tsaye
Dayake dukkan mu’amalolinmu a tsakar gida mukeyi kwana ne kawai ke sakamu a Akurkin namu, koko nace d’akunanmu, shiyasa yanzuma da Nura yazo a tsakar gida ya samemu mu duka kowa na haramar fita neman abin rufin asiri.
Bai damu da sauran matan da ke tsakar gidan ba, shiyasama ko gaidasu bai tsaya yayi ba kansa tsaye ya tunkaro inda muke dani dasu Baaba
“Sannunku Mama, An tashi lafiya?”  Ya fad’a cikin ladabi yayinda ya k’araso inda su Baaba suke ya durk’usa
Cikin murna da farin cikin sake ganinsa suka amsa gaisuwar tasa a mutunce.
Gefe guda Baaba ta jani inda bazasu iya jiyo abinda zamuce ba
“Wai ni kam Murjanatu bakin ta6a cemani kinada aure ba? idan ko haka ne danmi zaki dinga jawo wancen yaron a jikinki? ko ke bakisan haramun kike aikatawa ba?”
Inda-inda na farayi na rashin sanin takamaimiyar amsarda zan bata, can dai wata dabara ta fad’o mani
“Baaba sadda nake baki labarin inaga hankalinki ba a kaina yake ba, domin ce maki nayi, nata6a yin aure amma mun samu sa6ani dashi harma mun rabu ko kin manta?” Na fad’a ina wani Murmushin yaudara
Na k’ara da cewa “Kin manta har nace maki wannan shine yayi dalilin biyowata hanyar Sudan? Tuna dai sosai kiji”
Na tsaro mata hakan ne dan banaso ta dinga bibiyata ko kuma shisshigi a cikin lamurrana na nan gaba
Shuru tayi tana kallon sama alamun nazari, sauko da kan nata k’asa da tayi shi ya tabbatar min da bata tunano komai ba
“Kenan she wancen D’an tsamurmurin bak’in yaro kina nufin aurensa kikeso kiyi kenan?” Ta fad’a tare da nuna mani inda su Nura suke da baki
“Insha Allahu kuwa Baaba” Na fad’a a tak’aice
Ajiyar zuciya tayi kana tace “Allah ya taimaka” jiki a sanyaye
Komawa nayi inda na barsu shida Iya Talatu da Kuma Hamza suna k’ara gaisawa
“To Murjanatu mu zamu fita,  Kinga yau hutu ya sameki kenan tunda kinada bak’o”
“Kai Hamza maza d’auko takalmanka mu wuce ko zaka zauna tare da abokin naka ne?” Cewar Iya Talatu kenan yayinda ta maida hankalinta akan Hamza 
Da sauri ya d’auki takalminsa ya bisu a guje domin kuwa har sun riga sun fara yi masa nisa.
“Murjanatu kodai zamu shiga ciki ne? Idanuwa sunyi yawa anan bakiga matan can sai faman kallona sukeyi ba?” Ya fad’a tare da kutsa kansa a cikin rumfar tawa, inaga ya fahimci rumfar tawa ce ne saboda Hamza da yagani ya d’auko takalma a ciki.
Saida na bari ya natsu ya sha ruwanda na kawo masa yana fuskantata kana na jifo masa tambayar da tun jiya take kai komo a cikin zuciyata
“Uhm! Ina jinka jiya kana yi mani bayani akan aure ko? amma har yanzu nakasa fahimtar inda zancen naka ya dosa fa”
Murmushi yayi, irin wanda ako da yaushe yayisa yake canza mani tunanina a cikin k’ank’anin lokaci
“Murjanatu bazan k’ara cemaki komai akan wannan maganar ba, sai dai kawai nace maki ki tashi ki d’auko mayafinki muje ki ganewa idonki saboda hausawa suna cewa wai gani ya kori ji”
A tsorace na dubesa” Ina zamuje kenan Nura”
“Gurin Malamin mana, koko nace maki Malamai domin sunada yawa a gurin masu irin wannan fatawar, Oya tashi d’auko mayafin ki mashin d’ina na can a k’ofar gida muyi sauri mu dawo kafin su Mama su kai ga dawowa….
     *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

            jiki ya tsira

     

                 21
                 NA
      MAMAN JA’AFAR

Tun kafin mu k’arasa gindin bishiyar da suke na amince a cikin raina cewa lallai wad’annan Malamai ne,domin babu wata suffa ta Malamai wacce basu suffantu da ita ba
A saman wata k’atuwar tabarma suke a zazzaune kusan su shidda, kuma ko wannensu yana saye da irin Alkyabbar nan wacce naga Malamai na yawan sakawa, a gefe guda kuma Alqur’anai ne lodi da sauran littatafan addini.
Cikin ladabi muka durk’usa har k’asa muka gaishe dasu
“Allah ya gafarta Malam wannan itace Murjanatun wacce na shaida maka inaso in aura alhali tanada wani mijin a Nigeria” Ya fad’a yana mai duban d’aya daga cikin Malaman wanda a tsammanina shine shugabansu, fuskarsa duk tayi dumu-dumu da gemu babu gyara sai kace tsohon Bunsuru
Gyara zama ya sakeyi tare da ajiye tulin carbin da ke hannunsa gefe guda, ya fuskancemu alamar ya tattaro hankalinsa gaba d’aya zuwa garemu kenan
“Am Malama Murjanatu tun kafin kizo nan wannan bawan Allahn ya riga yayi mana bayanin komai” Ya fad’a tare da nuna Nura

Ya k’ara da cewa

“Yanzu ta bakinki kawai muke so muji, yaya kina sonsa ko kuwa a’a?”
“Allah ya jik’an Malam! bawai na k’i ta taku bane, inaso ku fahimci inada aure ne shiyasa”
“Mun san kinada aure Murjanatu amma idan baki sani ba bara mu sanar dake yanzu, a addinin musulunci akwai maz’habobi da dama, kuma kowace Maz’haba akwai yanayin tsare-tsarenta, koba haka ba?”

Ya fad’a tare da duban sauran Malaman wad’anda tunda mukazo kansu yake a k’asa sunata faman Jan carbi
Saboda tsabar ladabi basu iya ce masa komai ba, sai d’aga kai da sukayi alamar maganarsa haka take
“To saboda haka Malama Murjanatu mu Maz’habar da mukebi ta koya mana za’a iya jinginar da aure ayi wani auren, ina nufin ba kince kinada aure a K’asarku ba?”
“Eh haka ne Allah ya gafarta Malam” na fad’a a tak’aice
“To akwai wasu ayoyi da za’a karanta a gurin d’aurin aurenki da Malam Nura wanda hakan ke nuni da cewa anjinginar da auren wancen mijin naki dake kanki, ke barama kiji ko bayan kin auri Nura kuma kikayi sha’awar auren wani namijin daban za’a iya jinginar maki da auren Nura ki auri wani, daga haka har zuwa maza goma duk zaki iya yi ko ba haka ba D’aliban Malam?”
Sai yanzu d’aya daga cikinsu ya sami damar yin magana

“Haka yake Hakaramakallahu, aishi addinin musulunci abu ne mai sauk’i gaske, kuma babu takurawa a cikinsa shiyasa Allahma da kansa yace LA IKRAHA FIDDINI”
 _Oni Maman Ja’afar! Indai da ranka kasha kallo, yo irin wannan ta’asar da akeyi a ban kasa badan-badan ba aida sai nace ranar gobe k’iyama akwai kallo, to sai dai ranar kowa ta kansa yakeyi, muma bamu san tamu makomar ba bare har muyi tunanin ganin ta wasu_.
 *Ya Muqallubul-qulub, sabbit qulubina ala dinuka*

***

Tun dai ina k’ok’wanto akan magan-ganun Malaman hardai daga bisani na amince dasu sakamakon ayoyinda saketa jawo mani gami da Hadisai tare da Kuma son zuciyata, na amince na  jinginar da auren Haro akan sadaki Alif dubu ashirin 20K (Jahilci baiyi ba a rayuwa) aka tsaida ranar d’aurin aurenmu sati mai zuwa

****

“Su Baaba! nifa aure zanyi rana yata yau” abinda na fad’a masu kenan a lokacin da muke cikin fira muna nishad’i
“Aure kuma Murjanatu sai kace wacce tazo da yunwar abin?” Cewar Iya Talatu kenan Dayake tsohuwar kunya bata gama isarta ba
“Ke rabu da ita Talatu, kinsan Murjanatu bata rabo da zaulaya”
“Wallahi Baaba da gaske nakeyi Nura zan aura rana yata yau insha Allahu”Na fad’a babu alamun wasa a tattare da fuskata
“Ammako Murjanatu indai kikace aure zakiyi ni a ganina bakiyiwa kanki adalci ba, duka-duka yaushe kikazo garin, me kika tara da har zakiyi wani tunanin yin aure? Nifa banma yadda akan cewa baban Hamza ya sakeki ba kawai dai kinaso ne ki aikata son zuciyarki” Baaba Habiba ce ke fad’ar wanann maganar ranta a 6ace
“Kinga Habiba! yi hak’uri zauna dan Allah” 
Zama tayi amma har yanzu bata daina hucin fad’an nata ba sai kace wacce akace za’a yiwa kishiya
“Wato Habiba damafa ita Sudan ta gaji haka, zama ne na bariki ma’ana kazo-nazo, babu mai ikon saka wani bare ya hana wani, kowa kika gani abinda yaga dama shi yakeyi kuma a lokacinda yaga dama, garin nan babu wanda ya isa da wani, saboda haka Murjanatu ko zaman dadiro tace zatayi iyakarki da ita ido, idonma idan bazaki iya sakawa ba sai ki kauda kai, ina fatan kin fahimceni?”
Ajiyar zuciya tayi mai k’arfi kana tace”Na fahimceki Talatu” Kana ta juyo guna
“Ke kuma Murjanatu Allah ya sanya alkhairi a cikin wannan aure da zakiyi, kuma Allah yasa ya rik’e amanarki har k’arshen rayuwarku”
Yau dai haka firar tamu ta watse batare da wani armashin kirki ba

*****

Rana dai bata k’arya sai dai uwar d’iya taji kunya inji masu iya magana…..

Duk wanda baiga IDAN KUNNE YAJI 22 ba to yayi tunani baya ce mani Sannu ne shiyasa, ni kuma sai hakan ya tabbatar mani tamkar littafin ya daina yi masa dad’i ne, kunga ko ai gara na turawa masu so ko? 
Typing da wahalafa musammn ma idan akace mai yinsa yanada iyali😫😭
    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                  22
                  NA
      MAMAN JA’AFAR 
Masu iya magana sukace wai rana bata k’arya sai dai uwar d’iya taji kunya, to kuwa wannan maganar haka take, domin kuwa a yau ne Laraba wasu Malamai tare da taimakon wasu tsirarun mutane suka shaida d’aurin auren Murjanatu tare da sabon angon nata wato Nuradden akan sadakin June Alif dubu ashirin amma abisa sharad’in jinginarwa.

***

Yan kud’in dake hannuna wad’anda na tara dasu nayi amfani wajen siyen kayan buk’atar kicin irinsu tukwane da murhu da dai sauransu, inda abinma yad’an zo mani da sauki dashi Nuran yace zaiyi mani kayan d’aki, wanda yin hakan kusan al’adar garin ce.

*****

“Am su Mama nace yaushe yakamata Murjanatun ta tare a gidan nata ne?” Nura ne mai fad’ar hakan bayan sun gaisa shida su Baabaa Habiba, yana wani sissinnar da kai yana sosa k’eya wai nan alamun kunya yake nunawa
“To ni kuwa Nura me zance maku bayan ko ranar  d’aurin auren baku fad’a mani ba saida aka riga aka daura kana Murjanatu tazo take shaida mana? aida kun d’aukeni wata tsiya bazakuje kuyi gaban kanku ba, saboda haka yanzu amsa tana gurin Gimbiyar taka, ka tambayeta sai ta fad’a maka ranar da zata tare” Ta fad’a tare da mik’awa tsaye ta nufi inda igiya take tana nannad’e shanyar da tayi d’azu
Banji dad’in irin amsoshin da Baaba Habiba ta bawa Nura ba, amma dukda hakan sai na dake na dubi Iya Talatu
“Toke Iya Talatu miye shawararki tunda na lura ita Baaba Habiba bataso tace wani abu aciki?” Na fad’a raina a 6ace
“Aishi irin wannan auren Murjanatu ai ba sai an wani saka ranar tariya ba tunda dama can ba shirya masa akayi ba, saboda haka ni ina ganin kawai indai shi Nuran ya gama kammala d’akinsa ai ko ni nan zan iya rakaki, ko ba haka ba Nura?” ta fad’a tana mai duban Nura d’auke da murmushi a fuskarta
“K’warai kuwa Iya Talatu, ai shi irin wannan auren na Sudan ba’a cika yin wani shagule-shagule kamar na gida Nigeria ba, to saboda Allah Iya ni banida kowa a nan itama batada kowa anan danmi zamuce sai mun wani wahalar da junanmu? d’akin da zata zauna dai da izinin  Allah na riga nagama kammasa ni inda son samuna nema duk basai kun wani wahalar da kanku gun yi mata wata rakiya ba, da mashin d’ina ma sai na d’auke ta na kaita koba haka ba Murjanatu?”
Ya fad’a tare da dubana yana min wannan kalar Murmushin nasa mai sanyaya ga6o6i
Bance masa komai ba saidai k’okarin mayar masa da martanin Murmushin nasa da nayi
“To Nura mudai babu abinda zamuce sai dai kawai muce Allah ya bada zaman lafiya da Kuma hak’urin zama da juna” Cewar Baabata kenan yayinda ta duk’a tana k’okarin shiga d’akinta domin ajiye kayanda ta linko.

******

*Bayan sati biyu*

Yau ranar jumma’a kuma yau ne da misalin karfe 8 na dare na tare a gidan Nura a matsayin amarya batare da d’an rakiya ko d’aya ba, saboda Nura nakeso kuma shi na aura don haka da ayi mani rakiya da kar ayi mani, ni a ganina uwarsu d’aya ubansu d’aya a wajena.
Gidan da Nura ya kama mana haya k’aramin gida ne mai d’auke da d’akuna guda 4 kowannensu kuma da akwai mata da miji acikinsa, babban abinda ya k’ara burgeni a gidan duk ginin bulo da bulo ne, d’akuna irin na Nigeria sa6anin sauran sauran gidajen da muke yada zango da babu d’akin gini ko d’aya a ciki saidai d’akunan Bakura.
Dai dai tsaruwa Nura yayi k’okari wajen tsara mani d’akina yanda ya kamata, ba wani tarkace bane a d’akin daga Ledar k’asa sai yar katifa da Kuma labule sai yan kayan girki na da nazo dasu, dukda dai ko rabin-rabin d’akina na Nigeria baiyi ba amma  naji dad’insa sosai saboda ko ba komai nayi bankwana da zama a d’aki leda.
Mun gurji amarci iya san ranmu yanda ya kamata dani da angona abin k’aunata Nura, yayinda ya mayar da Hamza tamkar d’an da ya haifa na cikinsa, babu irin gata da kulawa wanda Nura bai nuna mani ba, ya shagwa6a ni ya sangartani fiye da kima dan hatta bara daina zuwa nayi
Wayyo sabuwar duniya, sai yanzu ne na tabbatarwa kaina da nayi auren soyayya, ashe dama can baya shirme nakeyi ba zaman aureba?

*****

*Bayan wata biyar*

Bayan wata biyar da yin aurenmu abubuwa suka fara caccanzawa, canjin yau daban na gobe daban, amma canjin wannan karon duk yafi sauran canje-canjen damuna domin tun jiya da safe da Nura yasa k’afa ya fita ban k’ara ganin k’eyarsa ba har zuwa yanzu da aketa kiraye-kirayen sallar mangariba, tun ina danne damuwata har dai ya kai ga damuwar tawa ta fito fili.
Kashe wutar Makanin da na d’ora nayi dukda bai ida dahuwa ba
Na d’auko Lafayata na nad’a tare da zura takalmana na lek’a d’akin mak’wabciyata wacce muka d’anfi shiri da ita wato Lantana
“Dan Allah Lantana ga Hamza nan a d’aki yana bacci ki kular mani dashi idan ya tashi zan d’an fita neman Nura ne saboda abin ya fara bani tsoro har yanzufa shuru babu shi babu labarinshi”
Zaro ido tayi tare da dafe k’irji lokaci guda alamun kid’ima
“Murjanatu kaddai kice mani har yanzu  mai gidan naki bai dawo ba” Ta fad’a tare da nuna alamun jimami a fuskarka k’arara
“Wallahi Kuwa Lantana har yanzu dai shuru shiyasa nace bara dai na fita na d’an dudduba koba lafiya ba tunda bai ta6a kwana a waje ba” Na fad’a d’auke da damuwa a fuskata
Har nakai bakin k’ofa na jiyo muryar Lantana k’asa-k’asa tana cewa
“Allah dai yasa d’an banzan yaron nan ba halin tsiyar ne ya tabka mata ba. Inma baya ga irin wannan zaman namu na Sudan na kara zube, tayaya kina ji kina gani dan kawai ba a gaban iyayenki kike ba ki auri mutumin da bakisan asalin waye shi ba bare kuma wani nasa ko daga garin da ya fito ba? yanzu hakama ba sunansa Nura ba k’arya ya tabka mata, dama sauk’i-sauk’i tunda na lura babu alamun ciki a tattare da ita”
Da yake nayi nisa kuma hankalina ba a jikina yake ba shiyasa ban fahimci inda zancen nata ya dosa ba na k’ara gaba abina…..

Wannan wane irin hali ne wanda Nura yake shirin tabkawa Murjanatu?

Kudai biyoni domin jin abinda ke shirin faruwa.
    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira 
                 24
                 NA
    MAMAN JA’AFAR

“Salamu alaikum! Sannunku dai” na fad’a ina washe baki yayinda na k’arasa da sauri  inda matan suke
“Yauwa sannunki kema” Suka fad’a kusan a tare gami da yi mani kallon rashin sani
Gyara tsayuwa nayi kana na fuskancesu
“Dan Allah idan bazaku damu ba wata yar magana ce nakeso mud’an tattauna daku”
“Allah sarki ba damuwa, amma mud’an k’arasa gurin duhu-duhun can saboda nan akwai mutane da yawa”
 Cewar yar doguwar fara kenan wacce ke d’auke da wushirya a bakinta
Tattaki muka k’arayi kad’an, can gaban wani mai Tukubar Tsire inda keda d’an duhu-duhu muka tsaya
“Baiwar Allah lafiya dai ko dan kin d’an bani tsorofa?” Abinda yar bak’ar siririya ta fad’a kenan bayan mun jingina a katangar k’ofar wani gida
“Wallahi lafiya k’alau, d’azu ne ina can zaune bisa wancen dakalin naji kuna maganar Saudia, shine nace bara nayi maku magana naji ya tsare-tsaren tafiyar yake ga wanda yakeda buk’atar zuwa?”
Murmushi yar farar tayi gami da ta6e baki”wannan maganar kam ba tawa bace, amma ga Uwani nan ku tattauna” Ta fad’a tare da nuna mani Uwanin da yatsa
Sai a sannan ne na rarrabe wace ce Uwani kuma wace ce Tsahara a cikinsu
Uwanin na duba fuskata d’auke da murmushi nace
“To Uwani koko nace K’awata (saboda kusan su duka ukun  sa’annin juna ne) ina saurarenki, domin na fahimci kusan ra’ayina da naki iri d’aya ne koba haka ba?”
Rik’o hannuna tayi cikin fara’a tace
“Yauwa yar gari, yanzun nan kuwa zan koro maki bayanin yanda abin yake, amma kafin hakan nawa kike dashi yanzu a hannu”
Nan take gabana ya yanke ya fad’i domin a zahirin gaskiya ko June dubu biyu tawa ta kaina bani da ita yanzu
“Maganar gaskiya indai da kud’i masu yawa ake bin wannan hanyar to bazan 6oye maki komai ba wallahi kud’in hannuna ko June dubu biyu basu kai ba” Na fad’a jiki a sanyaye
“Daina damuwa Yar’uwa ai kinma ta6uka wani abun, yanzu dubu uku da d’ari biyar kawai zaki k’ara a kai shikenan kud’in ki sun isheki hawa Sunbuk” ta fad’a tare da dafa kafad’ata
Ita dai Tsahara babu abinda take binmu dashi face ido gami da girgiza kai, kome take tunani? ohonmata dai
“Yanzu Uwani yaushe ne tafiyar kenan idan kud’in sun gama had’uwa?” na fad’a a tak’aice
“Cikin satin nanma idan kika shirya sai mu tafi tunda Ejojin ba wahala sukeyi ba dan yanzu hakama inada Nuhu Ejan a hannu”Ta k’ara da cewa
“Badanma ina neman K’awar tafiya ba aida yanzu nayi gaba abina tunda nasan hannunsa baza’a rasa wasu fasinjan ba, amma nasan duk abokan tafiyar tamu bazasu wuce manyan mata ba, ni kuma nafison tafiya da sa’ata koba komai mad’an ta6a fira a hanya, shiyasama d’azun kika ganni inata k’okarin shawo kan waccen bak’auyar” ta fad’a tare da hararar Tsahara cikin wasa
“Insha Allahu dani za’ayi wannan tafiyar, yanzu dai bani lambar ki kuma kiyi mani kwatancen gidanda kuke saboda idan na shirya ko nan da kwana biyar ne Kinga sai na tuntu6eki”
Batare da 6ata lokaci ba ta bani lambar tata tare dayi mani cikakken kwatancen inda suke zaune kana mukayi sallama kowa ya kama gabansa.
“Salamu alaikum” Na rabka sallama a k’ofar d’akin Lantana, yanzu banyi gigin d’aga mata labule ba saboda ina tsammanin mai gidanta ya dawo tun d’azun, saboda yanzu gurin k’arfe sha biyun dare kenan muke 
“A’a Murjanatu har kin dawo ne? Allah yasa dai kin samo labarin Nuran?”

Ta fad’a tana wani k’umshe dariya, batasan tuni na harbo jirginta ba
Ban mayar mata da amsa ba saboda yanzu haushinta nakeji saima canza akalar firar da nayi
“Allah yasa dai kin bawa Hamzana abinci? dan wallahi shaf na mantama da yunwa na barsa d’azu kafin na fita”
“Nabasa wani d’an sauran kwad’on zogale da Laminu ya shigo dashi d’azu, yanzun nan ma yagama ci yad’an ta6a wasan sa yayi bacci bara na mik’o maki shi ko?”

 ta fad’a tare da cicci6o Hamza dayake ta sharar bacci abinsa

*******

Cikin kwanaki uku kacal nagama tattara dukkan wasu kaya nawa da na mallaka na siyar, kama daga kan katifa, labulaye, tukwane, kuloli, su ledar k’asa, kai hatta kayan sawarmu nida Hamza ban bari ba sai biyu-biyu kawai, harda wasu kayan salla da Nura ya siya masa guda uku masu shegen kyau ina ji ina gani na sayar dasu a arha bijik
Kuma sai daga baya nake damuwa  ina tunanin kayanda zan saka masa idan sallar tazu
“Hmm Inma baya ga abinki Murjanatu, kuda zaku d’au hanyar Saudia ta ruwa ina ruwanki da damuwa da wasu kayan salla? mai yiyuwa ma akan hanya zakuyi babbar sallar taku, inma ba’ayi sa’a ba har k’aramar tazo ta riske ku anan” abinda wata zuciyar tawa take sanar dani kenan.
Nan take na manta da komai naci gaba da shirye-shiryena na tafiya Saudiya.

*****

“To masu gida! mudai zamu tafi, wanda muka yiwa ba daidai ba ya yafe mana” Abinda na fad’a kenan a tsakar gida bayan nagama kulle d’akina na mik’awa Lantana makullin
Lantana ce kad’ai ta nuna jimaminta na barin gidan da zanyi, amma sauran matan ko kulani ma basuyi ba dayake dama jininmu bai had’u da na juna ba, hasalima ina fita dariya suka bini da ita.
Da fitowata daga gida ban zame ko ina ba sai gidansu Uwani, ban nufi gidansu Baaba Habiba bane saboda nasan ko naje can ba wani tarbar kirki zan samu ba, kasancewar bata dad’i muka rabu dasu ba a lokacin da zan tare a gidan Nura.
“Am K’anina zo mana” Na fad’a yayinda na tunkari wani yaro da yake a kusa dani yana wasa da taya
“Dan Allah d’akinsu Uwani da Tsahara nake nema ko kasanshi? na fad’a tare da suffanta mashi kammaninsu Uwanin
Shuru yayi nad’an wani lokaci alamun tunani kana daga bisani ya d’aga hannu sama yace
“Aiywa! naganesu, su biyu da wata mai kyau da Kuma mummuna ko?”
Dariya maganar tasa ta bani, domin shi yana nufin wai Tsahara tafi Uwani kyau kenan
“Yauwa su nake nufi dan Allah nuna mani d’akin da suke”
Tiryan-tiryan muka bisa a baya nida Hamza har bakin k’ofar d’akin su Uwanin kana ya nuna mana d’akin ya juya da gudu abinsa
Cikin sa’a kuwa na samesu a d’akin

Da murnarsu suka tarbeni tamkar dai mun dad’e da sanin juna
Saida suka bamu abinci mukaci muka k’oshi kana na zubewa Uwani June dubu biyar da d’ari bakwai a gabanta.
“Yauwa yar gari! kice har kin had’o kawunan su? to yanzu abinda za’ayi bara nima na d’auko nawa kud’in mu tafi Zangon Malam Tukur mu nemo Ejan d’in, kinsan ance da zafi-zafi akan bugi k’arfe” ta fad’a yayinda take binciko kud’in a cikin kayanta
“Amma dai bada wannan yaron zaku tafi Zangon Malam Tukur d’in ba ko? dan naga yau rana akeyi sosai kuma Zangon da nisa” Cewar Tsahara kenan yayinda take shafa kan Hamza
“Indai bazai takura maki ba ai sai mu bar maki shi anan d’in kafin mu dawo” na fad’a tare da mik’awa tsaye, nabi bayan Uwani domin ita har tamaayi gaba
“Mama ki siyo mun goruba idan zaku dawo”
“Karka damu Hamza zamu biya ta wajen Laraba mai Gyad’a idan tanada gorubar sai mu siyo maka kaji?” Na fad’a yayinda nake k’okarin ficewa daga d’akin

*****

“Malam Tukur dan Allah yau Nuhu Ejan yazo nan rumfar kuwa?”Abinda Uwani ta fad’a kenan bayan mun gama gaishe shi
“Ai ko kun taki sa’a domin baiyi nisa sosai ba dan yanzu nan yabar gurin nan” ya fad’a yayinda yake waige-waige alamun Nuhun yake dubawa inaga
“Yauwa kunganshi canma d’an halak zai shiga mota, kuyi sauri ku cimmasa kafin ya kai ga shiga motar” Ya fad’a yayinda yake nuna mana inda Nuhun yake da hannu
Dayake dukkanmu ba wani nauyin kirki ne damu ba, da gudu muka k’arasa inda Nuhun yake
“Nuhu Ejan” Abinda Uwani ta fad’a kenan yayinda yake k’okarin shiga motar
“A’a Uwani kece a gari? to sannunku, me zan samu” kakkauran mutumin fari ya fad’a cikin yanayi na zaulaya, ga dukkan alamu dai dama sun dad’e da sanin juna shida Uwanin
“Dama maganar rannan ce ta sake dawo dani gurinka, yanzu dai nagama shiryawa harma ga K’awar tafiya nasamu” ta fad’a tare da dafa kafad’ata 
“Ok to badamuwa, aidai kin riga kinsan kud’in basai na k’ara yi maki bayani ba ko? saboda haka ku kawo kawai” Ya fad’a tare da mik’o mana hannu alamun dama can a matse yake
Mik’a masa kud’in tayi ya saka aljihu, kana ya sake duban Uwanin karo na barkatai
“Itama K’awar taki bata dai da goyo ko? dan tafiya da mai goyo sai a hankali wallahi, yaro yaje yaita yi mana kuka a hanya gashi kuma tafiyar nan ta 6oyo ce so akeyi kowa yayi tsit babu wata hayaniya Kinga inda yaro ai tona mana asiri zaiyi ko?” Ya fad’a yayinda yake rarraba idanuwa a tsakaninmu
“Gaskiya Nuhu Ejan tanada yaro, amma dai bana goye bane, shekarunsama nawa?” ta fad’a tare da dubana
“Shekarunsa biyar, inagama harda wani abu” na fad’a a tak’aice
“Ok! Indai kin tabbatar wuya bazatasa shi yayi kuka ba ai shikenan, amma dai duk da hakan ki tabbatar kin tafi masa da maganin Mura maisaka bacci sosai saboda ki dinga d’ura masa, kunsan fa tafiya ce mai hatsarin gaske, hukumomin Sudan suna neman irinmu, hakama na Yeman da Kuma na Saudia, shiyasa saida taka tsantsan, kunsan tafiya ce ta saida rai”
Nan take naji gabana na dukan tara-tara, a zuciyata nace Anya kuwa ba fasa tafiyar nan zanyi ba? amma kuma dana tuna irin wahalar da nasha tun daga barowata K’auyen K’wadage har isowata nan k’asar ta Sudan kawai sai na manta da komai na fara hangoni a K’asar Saudiya…..

     *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                 23
                 NA

 

     MAMAN JA’AFAR

Duk inda nake tsammanin Nura yana zuwa babu inda banje nemansa ba, amma har yanzun da dare ya tsala shuru kakeji babu shi babu labarinshi tamkar dai an aiki loma gewayar mak’oshi

Batun lambobinsa kuwa dama tun jiyan suke a rufe.

Bayan nagama yawona nagaji nayi liki’s nasamu gefen wani dakali dab da wata mata mai siyar da shayi na zauna(dayake kunsan a Sudan matane ke siyar da shayi)
Cikin sa’a kuwa na hangi wani abokin Nura mai suna Musah shima yazo shan shayi a gurin matar
Da gudu naje na samesa inda yake zaune, tsabar rud’ewama ko sallama ban tsaya yi masa ba na fara koro masa jawabi
“Sannu Malam Musah! Dan Allah Baka gane mani abokin ka ba kuwa? wallahi tun jiya bai dawo gida ba, yanzu hakama daka ganni nan daga gun nemansa nake nagaji na zauna a wancen dakalin, ashe rabon zan ganka ne anan?” Na fad’a kusan a rud’e
Murmushi naga yayi tare da nuna alamun ko in kula yaci gaba da kur6ar shayinsa, saida ya gama yangarsa kana ya dubeni
“Waike yanzu nan neman Nura kika fito yi sai kace wani k’aramin yaro ya 6ata?” Ya fad’a a shek’ek’e cikin rashin kulawa
“Eh wallahi Musah ko kasan inda yake ne dan Allah naga alamar kamar baka damuma sosai ba?”
K’ara kur6ar shayinsa yayi kana ya sake dubana a banzace
“Kema da zakiji shawarata da kin daina wahalar da kanki gurin neman wancen d’an iskan, dan wallahi ina mai tabbatar maki har abada ba ganinsa zaki sakeyi ba, tunda dai kema ya riga ya d’and’ana ai shikenan magana ta k’are kema kin shiga cikin lissafin…
“Dakata Musah! wai mikake son ka sanar dani ne dan Allah? wai kanaso kace mani wai dama Nura guduwa yayi da kansa ba 6ata yayi ba?” Na fad’a a birkice yayinda hawaye keta faman safa da marwa akan fuskata
Murmushi yayi cikin rashin kulawa da zancen nawa yace
“Inaso ne na sanar dake cewa kema kinbi layin sauran matayenda Nura ya aura wad’anda ya gudu ya bari a cikin irin wannan halinda kike ciki yanzu, ina fatan kin fahimci wannan  gwari-gwarin da nayi maki yanzu tunda dai bada wani yare nakeyi maki maganar ba da hausa nakeyi maki kuma a zatona ke bahausa ce ko ba haka ba?”
Yana gama fad’ar haka ya mik’e yayi gaba abinsa batare da ya tsayama ya ida shanye shayin nasa da ya siya ba
Wani jiri-jiri da duhu-duhu naji suna neman kayar dani, da k’yar nasamu na lalla6a gefen dakalin da na baro d’azu na zauna na had’a kaina da guiwa nafara rabsa kuka babu ji babu gani domin bani da wani za6in da ya wuce yin kukan, a wannan lokacin kukan ne kawai nake ganin zai iya sanyaya mani zuciya.
Wai Mike shirin faruwa da rayuwata ne? ya akayi abubuwa saketa zo mani ba yanda na tsammata ba? kodai banida nasara a rayuwa ne? wad’annan tambayoyin kawai ke kai komo a cikin zuciyata.

******

“Nikam Uwani da zaki bi ta tawa da kin daina maganar tafiya Saudia d’in nan, saboda nasha jin labarin irin had’arurrukan ke tattare da wannan tafiyar musamman ma a  _Yeman_ kafin ka k’arasa k’asar Saudiya

Wallahi a yanda nasamu labari Yamanan nan har kashe mutane wai sukeyi, nidai Uwani da zaki bita shawarata da kin daina zancen tafiya Saudia ta k’asa d’in nan, ni agani na da zamanki kikayi anan tunda ana samu bawai samu ne ba’ayi ba, ki d’an tara abinda kika tara inyaso daga baya sai ki koma gida Nijar ki taho Saudiyan ta jirgin sama, amma a nawa haukan kenan dan  bansan romon da kika hango a can d’in ba”
Dariya wacce aka kira da sunan Uwani tayi hadda k’yak’yatawa kana daga bisani ta tsagaita da dariyar tata ta maida dubanta ga d’ayar matar
“Wallahi Tsahara ban ta6a sanin ke cikakkiyar matsoraciya bace ba sai yau, kuma da kiketa faman fad’in wai akwai had’ari a hanya-akwai had’ari a hanya, babban had’ari ya wuce wanda muka baro tun daga Nijar har zuwa nan k’asar ta Sudan? saboda haka indai ke bazaki tafi ba to banga dalilin da zaisa kike nema nima kiyi mani salalar tsiya ba, Allah nagani na gaji da wannan wahalar ta Sudan wanda da k’yar da ji6in goshi mutum yake had’a kimanin dala d’ari biyar a wata. ina! gara natafi inda cikin shekara guda zan iya sayen gida k’erarre nawa na kaina harma na rage yan canjina
Uwani! ya kike tsammanin zaki ganni idan na shekara biyar a Saudia? ai saidai kiji ana sakowa dani a cikin jerin mashahuran masu kud’in da ke cikin garin Mayi ta Jamhuriyar Niger ko ya kikace?” ta k’arasa maganar tata tana wani juyi tana k’wanbo sai kace rufe ido kawai zatayi kamin ta bud’e ta isa k’asar Saudiyan
“To nidai wannan tafiya badani ba, dan ban shirya mutuwa a Sunbuk ba (Jirgin ruwa) Cewar wadda aka kira da suna Tsahara kenan.
Ina gefe guda zaune a bisa dakalin gefen mai shayi nake jiyo firar matan guda biyu sama-sama,saboda babu wata tazara mai nisa a tsakaninmu
A tsammanina suma matan shayin sukazo siya dayake mutane sunyiwa matar yawa shiyasa suka matsa gefe guda suna tattauna abinda ya damesu.
Firar matan guda biyu ba k’aramin ratsa zuciyata tayi ba musamman ma da naji suna ambatar mak’udan kud’aden  da mutum zai iya samu a cikin shekara guda kacal a K’asar Saudia
Nan take zuciyata ta fara kissima mani abubuwa kala daban-daban a tattare dasu
Dariya nayi tamkar babu wata damuwa a tattare dani kana a fili nace “Wayaga su Murjanatu a Saudiya? Allah Ameen” 
Idanko na wayi gari na ganni a Saudia aini shikenan mafarkina ya kusan zama gaskiya, Kakata ta kusan yanke Sak’a.
Nan take na nemi damuwar da nake ciki ta Nura na rasa, tunda dama ai aure ne na jingina duk sadda na tashi yin wani ko kuma zan koma K’asarmu sai shikenan sai na bayar a jinginar min dashi kafin nasan abinyi kuma.
Da wannan tunanin na tunkari matan guda biyu wad’anda suka riga suka sayi shayin suna k’okarin kama hanyar tafiya….

Ta6d’ijan ana dara ga dare yayi. Maman Ja’afar wai ina kike shi kaimu ne kuma?
Karku damu masu karatu kudai kuci gaba da bina domin jin chakwakiyar da ke gaba

    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                  25
                  NA
     MAMAN JA’AFAR

“To yanzu Nuhu Ejan yaushe kake ganin zamu d’au hanya kenan?” Uwani ta fad’a tana wani rausaya da jikinta harda wani yin fari da idanuwa
Shuru ya d’anyi na wasu yan dak’ik’u alamun nazari, sai daga bisani can dai ya lumfasa yace
“Ina ganin idan a shirye kuke ko zuwa jibi sai mu wuce kawai ko?” Ya fad’a yana mai kallon fuskokinmu, sana ya k’ara da cewa
“Idan kuma baku shirya ba, ba damuwa sai naje nakai wasu fasinjan nawa inyaso daga baya idan na dawo sai na wuce daku, tunda wannan karon inagama bazan wani dad’e sosai ba sati biyu kawai zanyi nadawo nake sa rai”
“A’a ba wani sati biyu muma a shirye muke kawai ka wuce damu ko ya kikace K’awata” ta fad’a tana mai duban fuskata
Ban amsa mata ba sai d’aga mata kai da nayi alamun amsawa 
“To babu matsala, ku shirya zuwa jibin da safe idan na d’auko wasu mata a Markaz-Arabi sai na biyo nan d’in kuma na d’auke ku mu wuce”Yana  gama fad’ar hakan ya shigewarsa mota ya tada yayi gaba abinsa.
A akan hanyarmu ta komawa gida ne na dubi Uwani”Ni kam K’awata badan karki ce nayi maki shisshigi ba dana tambayeki wani abu?”
“Karki damu ‘yar’uwa fad’i zancenki gaba gad’i kai tsaye ai yanzu mun riga mun zama d’aya” 
“Dama cewa zanyi, kin ta6a bi hanyar nan ne? Naga da yana fad’in matsalolin dake kan hanyar tamkar baki damu ba”
“Wallahi ban ta6a bi ko hanyar Sudan ba bare kuma ta zuwa Saudiya, wannan zuwan shine zuwana na farko Sudan kuma shine farkon da zan fara bin hanyar Saudia”

Ta fad’a yayinda muke ci gaba da tafiya
“Amma ke kam bakida tsoro wallahi, yoni da naji acikin bayanan nashi babu alheri ko kad’an aciki wallahi a lokacin wallahi tamkar nace masa nafasa tafiyar naji”
“Da kuwa kinwa kanki bak’in ciki” ta fad’a yayinda muka k’araso k’ofar gidan nasu.

******

*Ranar tafiya*

Kamar yanda yayi alkawari bai sa6a ba kuwa, domin tun safe mukaji Kiran wayarsa wai gashi nan a k’ofar gida ya iso
Dayake dama tun jiya da dare mun riga mun gama had’a kayan tafiyar tamu da guzurinmu da komai yana guri guda, shiyasa koda yace mu fito batare da 6ata lokaci ba muka sa6i yan kayanmu da basu kai sun kawo ba muka samesa a k’ofar gida inda ya faka motarsa
Irin motar nan ce bud’dd’iya wacce take iya shiga ko ina batare da wani dirin kirki ba

Mata bakwai ne muka tarar a cikin motar amma duk cikinsu babu sa’anninmu, wasu daga cikinsu sunyi ‘ya’yaye damu  wasuma inaga zasuyi jikoki damu, watama daga cikinsu ko gani sosai batayi saboda tsufan da tayi sosai
“Uwani kalli waccen Tsohuwar dan Allah”Na fad’a  tare da nuna mata inda tsohuwar take da bakina a lokacin da muke k’okarin shiga motar
Dariya nayi kana na k’ara da cewa”Itamafa inaga Saudian takeson zuwa, kome zatayi da kud’i a irin wannan shekarun nata?”
“Inbaya ga abinki Murjanatu su kud’i wanene baya buk’atar su? shiyasama zakiji ana cewa wai tsohu da kud’i yaro, yaro kuma babu kud’i tsoho” Ta fad’a k’asa-k’asa domin mun riga mun shiga cikin motar
Direban yana niyar shiga mazauninsa na sunkuyo da kaina daidai saitin da zai iya ganina
“Nuhu Ejan zan iya basa maganin yanzu kosai zuwa anjima?”
Dariya tambayar tawa ta bashi, a cikin dariyar yake bani amsa
“Aiko zaki bashi magani ba yau ba, ina ganinma sai zuwa jibi”
“To Allah ya kaimu lafiya” 
“Ameen ya fad’a a tak’aice tare da shigewa motar ya bata wuta muka d’au hanya
“Mama banida lafiya ne naji kina cewa za’a bani magani? Hamza ne mai fad’ar hakan yayinda muke ci gaba da tafiya
“Maganin k’arin lafiya ne za’a baka ko bakaso ka k’ara lafiya?”
Baice mani komai ba saima kwanciya da yayi akan cinyata yayi lamo tamkar marar lafiyar gaske.

*****

Wannan karon tafiyar kwana d’aya ce da wuni ta kawomu garin *BARSUDAN*duk da hakanma sai yamma lis muka samu isowa.
Garin Barsudan babban gari ne wanda yake a bakin ruwa,  mutane da dama suna hada-hada a cikinsa, musamman ma bak’i wad’anda ba ‘yan k’asar ba,  ko dayake ai kusan K’asar ma gaba d’ayanta ta bak’i ce, bak’in ma kuma hausawa, dan a yanda nasamu labari tun ina k’arama Hausawanmu ne irin na Nigeria da Nijar dana Chadi da Kuma Kamaru tun asali suka fara kafa K’asar ta Sudan, saboda suna biyo hanyar ta Sudan ne da nufin zasu haura Saudiya, daga bisani kuma sai suyi zamansu anan da haka-haka har suka kafa K’asar ta Sudan
Shiyasa yazamana hausawa kuma bak’ak’e sunfi yawa a cikin K’asar, duk da dai ana samun farare a cikinsu amma d’aid’aiku ne, sai dai da fararen da bak’ak’en badai gashi ba, kusanma zan iya cewa gashi da Kuma shek’in fata ne kad’ai zasu iya nuna mana mu ‘yan Nigeria.
Ammafa shi wannan garin na bakin ruwan Barsudan kenan wad’anda suka fi zama a cikinsa sune masu son haurawa Saudia, inma kazo ne ka kwana d’aya ka wuce ko kuma kazo ne ka zauna na ‘yan watanni kayi neman kud’i idan Allah ya hore maka sai ka haura.
To sudai su Murjanatu suna daga cikin wad’anda zasuyi kwana d’aya su wuce d’in shiyasama Nuhu Ejan ya kaisu wani gida ya ajiye su kafin zuwa goben.
“Kinsan me za’ayi kuwa Murjanatu?” ta fad’a bayan mun gama natsuwa a d’akin da ya saukemu tare da sauran matan
“Ban sani ba sai kin fad’a Chakwai-kwaiwa” Na fad’a a tak’aice saboda bana son surutun a gajiye nake sosai
“Nace ko zamu d’an je bara ne a *Dam Arab* mud’an k’ara samun guzuri?” ta fad’a da murya k’asa-k’asa saboda bataso na kusa damu susan abinda take fad’a barema har suyi tunanin binmu
Gyara kwanciyata nayi akan kwalayen da suke jere a k’asa a matsayin shinfid’u
“Ke inmabaya ga abinki Uwani yanda nagaji d’in nan ina zan iya zuwa wata bara yanzu? ga Hamza yana bacci koke zaki goya mani shi?”Na fad’a yayinda nake shafa kan Hamza, na k’ara da cewa”

Ni ina mamakinma yanda akayi kikasan wannan garin da har kike k’okarin tafiya wata unguwa wai dam arab yin wata bara? To sai kin dawo ni ina nan” Na fad’a yayinda na jawo bargo na rufemu nida Hamza dayake lokacin sanyi ne sosai
“Zauna nan kifin rijiya, nikam ai bara babu inda bata kawoni ba a wannan K’asar” Ta fad’a tare da mik’awa tsaye alamun tafiya

●Washe gari●

Tun safe Nuhu Ejan yazo ya kwashe mu daga wannan garin na barsudan a cikin motarsa, ya dinga laluk’a uwar tafiya damu babu ji babu gani kuma batare da munsan inda zai kaimu ba
A tunanina zamuyi awa 3 haka zuwa 5 muna sharara gudu akan hanya babu kakkautawa
Saida mukazo wani K’ungurmin daji inda babu gida ko d’aya a cikinsa sai manyan bishiyoyi da kuma duwatsuna, Nuhu Ejan ya saukemu
Dajin wani uban duhu ne dashi, kuma shuru yake babu abinda kakeji a cikinsa face kukan tsuntsaya da k’arar itacen da iska take kad’awa.
“Alhamdulillahi mun iso gurin 6oyo yanzu, saboda haka nan zaku zauna har na tsawon lokacin da jirgin ruwa zai k’araso, kunsan shima jirgin ruwan hukuma ta hana tashinsa a garin saboda wai yawan rasa rayuwakka da akeyi a cikinsa, shiyasa shima jirgin a 6oye zaizo, kuma ku d’inma a 6oye zaku shigesa cikin dare batare da sanin hukuma ba, ina fatan kun fahimceni?” Ya fad’a yayinda yake k’okarin shiga motarsa
“Bawan Allah! to kuma har kwana nawa zamuyi anan d’in kafin jirgin yazo, sannan kuma a cikin dokar dajin nan waye zai bamu abinci da zamuci bare kuma ruwan sha?” Na fad’a yayinda zuciyata ke dukan tara-tara, jikina har wani kyarma yakeyi idan na tuna kalamin Nuhu Ejan na k’arshe da Kuma adadin iya kwanaki daya ambata mana zamuyi anan
“Karki damu yarinya duk ni zan kula da wannan, kudai kawai abinda zan fad’a maku ku guji abinda zai jawo hankalin hukuma zuwa gareku, domin kusan kullum ba dare ba rana suna nan suna zagaya dazizzika domin neman irinmu”
Yana gama fad’ar haka ya shigewarsa mota abinsa yaja yayi gaba mu kuma ya barmu muna  rarraba idanuwa acikin k’ungurmin daji wanda Kuraye da namun daji yafi cancanta ace suna rayuwa a wannan gurin……

Uhmm neman halak da wuya yake. 6arawo yace ai haram d’inma ba baya ba Maman Ja’afar
Muje zuwa masu karutu. Murjanatu dai nacan na barota a daji mai kama dana Sambisa kome zai faru kuma a can?🤔

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                 26
                 NA
    MAMAN JA’AFAR

Nuhu Ejan bai dad’e da tafiya ba muka dinga jiyo sautin kukan jariri can k’asa-k’asa
“A’a jama’a kamar kukan jaririfa nakeji a gurin nan kodai kunne na ne yake  jiye mani ba dai dai ba?”Cewar wannan tsohuwar kenan wacce muka taho tare
“A’a ba kunnanki bane Tsohuwa nima kamar naji hakanfa” Fad’ar wata Dattijuwa kenan yayinda ta mik’e tana ‘yan dube-dube
Yafitoni Uwani tayi dayake muna gefe ne a zaune nida ita
“Murjanatu nimafa kamar kukan jaririn nan nakeji, ke bakiji ba ne?” ta fad’a tare da k’ara kasa kunne domin ta tabbatar
Saida na saurara sosai kana nima na jiyo abinda suke fad’a wato kukan jaririn
Bamu gama tantancewa ba Kukan ya ida bayyana cikin sauti mai k’arfi
“Wayyo Allah jama’a ku taimakeni, na shiga uku na bani na lalace ni Murjanatu yau kuma ina na kawo kaina?”
Babu wanda ya kulani domin suma sauran matan dake gurin duk warewa sukayi
“Murjanatu ki dai..na i..hu kada hukuma su jiyomu” Cewar Uwani kenan yayinda take a tsaye jiki na kyarma saboda tsabar tsorata ma  kasa guduwa tayi, saima fitsari dana hango yana bin k’afafuwanta
Mata d’aya ce bata gudu ba a cikinmu, saima faman safa da marwa takeyi tsakanin can da nan
“Karku ji tsoro jama’a, ku dawo ku zauna ba komai bane kukeji kukan jaririna ne, ban fad’awa Nuhu Ejan bane dan..
“Dan kan ubanki ba” Cewar wata doguwar mata kakkaurar kenan wacce ke cikin tawagar tafiyar tamu, sana ta k’ara da cewa 
“Yanzu saboda da Allah wannan abin da kikayi me sunansa kenan? rashin hankali ko ganganci koko tsautsayi za’a kirasa? kin sani sarai kinada jariri sabuwar haihu madadin ki hak’ura da tafiyar har sai lokacin da yayi k’wari kana ki tafi, amma  saboda shegen kwad’ayi kin kwaso jariri sabuwar haihuwa kin taho mana dashi, bayan kina ji da kunnenki  irin kashedin da Nuhu Ejan yayi mana, yanzu ai sai kisan yanda zakiyi dashi ” Cewar matar kenan wacce taketa faman yin fad’a tamkar zata doki uwar jaririn
“Ya kuwa zatayi dashi wanda ya wuce ta koma inda ta fito da abinta, dan nidai bazan yarda ta jawo mani salalar tsiya ba inrasa kud’ina” Cewar d’aya daga cikinmu kenan itama
“Nifa da zaku nemi shawarata dace maku zanyi kawai mu kar6e yaron mu shak’esa har ya mutu kana mu tillar da gawar a bakin wancen ramin inda nayo kashi d’azu koya kuka ce?”

Cewar wannan tsohuwar kenan wacce nake ganin tamkar neman kud’i bai dace da ita ba
Nidai dani da Uwani bamuce uffan ba idanuwa kawai muke rarrabawa a tsakaninsu, amma kalamin tsohuwar yaso ya bani dariya, taya za’ayi a shak’e d’an mutum har ya mutu sai kace wani d’an tsako? to Allah dai ya fitar damu lafiya  domin nima inada yaron kuma bansan abinda ka iya zuwa ya dawo ba.
Itako matar babu abinda takeyi face rabsa kuka tamkar ranta zai fita musamman ma lokacin da taji wannan kalami na tsohuwa sai kukan nata ya k’ara tsananta
“Mama yunwa nakeji zanci abinci” Cewar Hamza kenan yayinda yake bud’e idanuwansa kad’an-kad’an alamun ya farka daga bacci kenan
“Kai! wannan yawan jin yunwa naka Hamza yana damuna, daga tashi bacci sai Kiran yunwa to…
“Kinga Murjanatu ba surutu ba, idan kinada abin bashi kawai ki bashi a zauna lafiya, kinga dai yanda wa’yancan matan suka hayayyak’oma waccen matar kamar zasu cinyeta kar kuma su lura da namu yaron su dawo kanmu dan naga alamar babu tausayi ko kad’an a fuskokin su”
Da sauri na fitar da garin kwaki na wanda na cuso acikin kayana, na yayyafa masa ruwa na bad’a masa k’uli-k’uli nabasa ya hau ci.
Sai da rana ta kusan fad’uwa kana muka hangi motar Nuhu Ejan ta tunkaro mu
Biredi ne ya kawo mana da miya, sai kuma ruwan sha daya d’uro mana a cikin jarkoki
“Nuhu Ejan gafa wata can tazo mana da jariri batare da ta sanar da kai ba, ko muma da muke tarema bata sanar damu ba saida mukaji kukansa da kanmu kana muka ankara” Cewar wannan kakkaurar matar kenan
Cikin alamu na mamaki Nuhu Ejan yace “jariri kuma?” 
“K’warai da gaske gaya canma tana goye dashi a bayanta” ta fad’a yayinda take nuna masa inda matar take harda wani cokaro d’ankwali a gaban goshi tamkar zatayi fad’a da kishiyarta
“Baiwar Allah ai kin jaza mana bala’i mu duka” Ya fad’a rai a bace 
“Wallahi ba…
Bata kai ga k’arasa zancen nataba ya wanketa da wani kyakkyawan mari ji kake fau
“Wallahi me? Banza dak’ik’iya jahila dabba kawai dake, inbaya ga baki da hankali taya kinsan kinada jariri kika 6oye mani har saida na kawoki nan?”
Cikin kuka taketa basa hak’uri, amma bawan Allahn nan bai saurareta bama bare har yaji uzurinta
“Ba wani uzuri da zanji naki baiwar Allah, ina ‘yan kayanki suke? d’aukosu ki gani nan”
Cikin firgici ta d’auko kayan nata tazo ta durk’usa a gabansa “Gasu Ranka ya dad’e”
“A’a ai ba tsugunnawa zakiyi ba, Kinga wannan hanyar? ya fad’a yayinda yake nuna mata wata ‘yar siririyar hanya da hannunsa wacce shukokin bushiyoyi suka kusan rufewa
“Ita zakibi na tabbata zata kaiki har Barsudan dagan ana sai ki nemi Motar Sudan”
Ihu da kururuwa matar takeyi tana rok’onsa akan ya taimaka ya mayar da ita da kanshi koda bai bata kud’nda ta bashi na hawa jirgi ba, amma mutumin nan fafur yak’iya tamkar babu d’igon imani a cikin zuciyarsa, haka ya tasa k’eyar matar nan tana kuka jaririn na kuka har tayi nisa muka daina hangota.
Koda nagama kallon wannan dirama dake faruwa bansan lokacin da wani zazzafan hawaye ya fara sintiri akan kumatuna ba, gaskiya nayi dana sanin biyowa wanann hanyar ta Saudiya, yanzu ko tunanin irin had’arurrukan da zata iya  fuskanta akan hanya ita kad’ai baya yi? kenan nima hakan zata iya faruwa a kaina wani lokaci kenan? wallahi da inada dama da maganar gaskiya cewa zanyi nafasa yin wannan tafiyar a mayar dani gida kawai, to amma ina! aikin gama ya riga ya gama tunda mun riga munyi nisa
Koda nagama wa’yan nan ‘yan tunane-tunanen nawa sai na d’auko maganin Hamza mai saka bacci na d’ura masa domin gudun kada abinda ya faru a waccen matar nima ya faru dani.

******

Yau kusan kwananmu goma a wannan k’ungurmin dajin kuma yau ne muke saka ran zamu barsa, muma mu huta da kwanan daji sai kace…
Hakanan mukayi wayan nan kwanakin babu abincin kirki bare kuma ayi batun wurin kwana, ga uban sanyi da akeyi amma babu maganar abin rufuwa, kashi kuwa da fitsari saidai idan munjisu mu nausa a cikin dajin muyi kayanmu, maganar salla kuwa dama sai a hankali
Hamza kam duk ya rame acikin wad’annan kwanaki da mukayi a nan, ya bushe ya wani fige tamkar ba shi ba, idan na kalli yaron har wasu hawaye nakeji suna bin fuskata na tausayinsa
Nakanso na tuno rayuwata a gidan Haro, amma da zarar tunanin ya fad’o mani sai nayi saurin kawar dashi domin a zahirin gaskiya banason abinda zai sanyaya mani guiwa daga yin wannan tafiyar yanzu

●Da dare●

Har mun kwkkwanta ak’asa mun lullu6a da zannuwanmu munata kyarmar sanyi kamar yanda muka saba mukaga hasken fitilar Cocila

Bamu wani tsorata ba domin dama Nuhu Ejan ya shaida mana da dare zaizo mu wuce domin a cikin daren akesa ran jirgin zai k’araso
Mimmik’ewa mukayi muna jiran abinda zaizo mana dashi
“To ku mutanen Saudiya bakuga ta bacci ba domin jirgi ya riga ya iso tun d’azun, yanzu ku d’auko kayanku kawai mu kama hanya kunsan tafiyar ba ‘yar k’arama bace a gabanmu, dan wannan tafiyar da mukayi daku a mota na kawo ku nan, to ina mai tabbatar maku irinta ce zamu maimaita yanzun nan har zuwa inda jirgin ruwan yake….
Bansan lokacin da bakina ya su6uce ba nace “A cikin wannan daren kuma Nuhu?”
“Inbazaki ba ai sai mu barki anan mu muwuce inyaso daga baya kya taho” Ya fad’a a tak’aice, kana yayi gaba abinsa alamar mu biyosa kenan inaga yake nufi….

   *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          jiki ya tsira
                 27
                NA
      MAMAN JA’AFAR

Haka mukaita tafiya a cikin wannan k’ungurmin dajin, ga duhun dare kuma ga duhun daji, baka jin motsin komai a gurin sai kukan tsuntsaya
Ko Cocilar ma wannan karon bai haska mana ba saboda wai tsoron kada hukuma su ankara.
Tafiya mukeyi amma ko junanmu bama iya gani sosai saboda tsananin duhun da ke gurin, kawai saka k’afafuwan mu mukeyi batare da sanin inda muke sakasu ba
Ni abinma biyu ya zame mani, ga tafiya cikin wannan uban duhun kuma gani d’auke da goyon Hamza wanda na d’ikawa maganin bacci yasha yayi mankas sai faman shek’a bacci yakeyi abinsa, inaga wannan dalilin nema yasa naji ya k’ara yi mani nauyi a bayana
K’ayoyi kuwa wad’anda suka sossoke mani k’afafuwa sunfi a k’irga, tun ina Duk’awa ina cirewa har dai yakai ga bana samun damar Duk’awar barema har na ciresun, saboda idan na biyewa cire k’aya ba mamaki abokan tafiyar tawa su yi mani nisa ko kuma fushin hukuma ya fad’a mana tunda ba wani ganin juna mukeyi sosai ba
Sauk’i-sauk’inta ma hannayenmu rik’e suke da juna nida Uwani 
Mun d’au lokaci mai tsawo muna d’ikar tafiya acikin wannan duhun dajin batare da mun cimma inda mukeso mu cinmma ba Uwani ta sulale ta zube a k’asa
Acikin rad’a-rad’a nake tambayarta
“Uwani kardai kice mani gajiya ce tasa kika zauna anan? dan Allah ki daure ki tashi mu lalla6a kar abokan tafiyar tamu su 6ace mana, nima na gajin bawai gajiyarce banyi ba, amma kinsan ba imani ne dasu ba idan muka zauna sa iya tafiya su barmu anan, ko Kura ta cinyemu ko Zaki su ba damuwarsu bace, tashi dan Allah Uwani sunfa kusan yi mana nisa”
Ina magana Ina k’okarin kama hannunta domin ta mik’e
Da k’yar ta samu ta bud’i baki tace

“Karki damu Murjanatu yi sauri ki bisu kar suyi maki nisa, nikam bazan iya k’ara matsawa ko ina ba daga nan, saboda ina tsammanin Kunama ce ta harbeni ko kuma Maciji, bakiji irin rad’ad’i da zugin da nakeji ba, daure kawai nakeyi shiyasa banyi ihu ba dan nasan idan nayi ihu abinda zai iya biyo baya sai yafi harbin kunamar nan tashin hankali agareni, Murjanatu jeki zasuyi maki nisafa”
Ta fad’a yayinda take shesshek’ar kuka
Nima kukan nakeyi amma ba mai sauti ba, wannan wane irin bala’i ne na jawowa kaina yau? garin shegen son kud’ina har gashi na kawo kaina inda kud’i sukafi bil’adama daraja
“Wayyo Allahna! Inama ace duk wad’annan abubuwanda suke faruwa a cikin mafarki ne?”
Ina ji ina gani badan raina yaso ba dole na tsallake Uwani a inda take kwance magashiyan tamkar ranta zai fita natafi domin riskar abokan tafiyar tamu
Kwance na barta tana shar6ar kuka batare da tsammanin samun wani mataimaki ba anan kusa.
Yanzu kam nima abokan tafiyar tawa sun  riga da sun 6ace mani danko motsinsu ma bana iya jiyowa yanzu, nasan tabbas idan na k’wala masu kira zasu jiyoni, sai dai kash babu damar yin hakan

Hakanan naita tafiyata batare da nasan inda nake nufa ba.
“Wayyo jama’a ku taimakeni, bana ganin hanya ko kad’an, duhu kawai nake gani a cikin idanuwan nawa, dan Allah yara ku taimaka Karku barni acikin dokar dajin nan ni kad’ai komai zai iya faruwa”
Abinda kunnuwana suke jiye mani kenan a gefen hanyar da nake bi
Ba shakka ina kyautata zaton wannan tsohuwar ce wacce taketa faman masifa dan anzo da jariri
Ta bani tausayi matuk’a musamman yanda naji sai faman magiya takeyi tana neman taimako muryarta har ta fara disashewa
Itama ina ji ina gani nayi kunnen uwar shegu da ita, saima sauri dana k’arayi domin nima a lokacin inda zan samu mai taimakona so nakeyi.
Abin  kamar wani bala’i koko nace tashin duniya, a gabama kukan dai nasake jiyowa na masu neman taimakon, sai dai wannan neman taimakon nata ya banbanta da wacce na baro a baya domin ita jinayi tana cewa wai
“Bayin Allah ku taimaka mana kamar yanda Allah ya taimakeku, ku sakani a hanya domin bansan inda nake ba a yanzu”
K’ara saurarawa nayi kad’an naji taci gaba da cewa
“Niko bazaku taimaka mani ba ku taimaka ku wuce mani da gawar jaririn nan karta fara wari…
Ban tsaya na ida jin k’arshen maganar tata ba sauri-sauri gudu-gudu na wuce inda nake jiyo sautin nata, domin Allah nagani a duniya babu abinda nake tsoro fiye da gawa, shiyasa tsabar tsoronda nakewa gawa ko giftawar Makara bana son gani, idan ko har akayi katari hanya ta had’amu da ‘yan d’auko gawa to rufe idanuwana nakeyi har sai sunyi nisa nadaina ganinsu, shiyasa ko hanyar Mak’abarta ma bana son bi, badan komai ba sai dan gudun kada na hango Kabur-buran nan a jejjere
Yau gashi shegen son kud’ina ya had’ani da gawa k’iri-k’iri
Wannan gudun dana sha shiya taimaka mani wajen jin takun takalma da yawa wanda nake kyautata zaton abokan tafiyar tawa ne na fara cimmawa
Da jin haka banyi wata-wata ba na k’ara hanzartawa, ai kuwa kwatsam sai jina nayi a cikinsu muna tafiya a tare
Wani dad’i naji ya ziyarci zuciyata domin koba komai nasan banida rabon shan wahala kamar wa’yanda na baro a baya suna neman taimako, kowa zai taimaka masu? Tambayar da na dad’e inata faman maimaitawa kenan a cikin zuciyata

****

Bamu mu muka samu isowa bakin ruwa ba sai dab da sallar asuba, a lokacin ma har haske ya d’an fara bayyana kad’an-kad’an, amma duk da haka Nuhu Ejan bai bamu damar yin magana ba har yanzu, saboda suma hukumomin tun dare idan suka fara aiki basa tsayawa har safe, shiyasa muketa yin taka tsan-tsan
Tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin jirgin ruwa k’iri-k’iri ido da ido ba sai yau, yau d’inma wai gashi a  gabana ina kallo ni Murjanatu kuma wai shigarsa zanyi
K’atoto ne wanda ya kusa yin girman babban d’aki, yayinda kusan rabinsa ya kasance a rufe  tamkar gida-gida haka, shi kuma sauran rabin a bud’e yake wangayam tamkar dai kwale-kwale irin na kamun kifin nan
Wata murd’ed’iyar igiya ce nagani a jikinsa a d’aure kuma doguwa wacce tsayinta har yazo dab da inda mukayi layi layi a bakin ruwan, wani bayan wani, wani bayan wani, layin maza daban na mata ma daban
Yawanmu yafi a k’irga domin Ejojin namu sun kusan 30 a gurin kuma kowanne Ejan da nasa fasinjojin daban
Wannan murd’ed’iyar igiyar wacce nagani muke kamawa muna rik’ewa gagam yayinda su kuma masu Jirgin ruwan suke jawomu da k’arfin tsiya har cikin jirgin, saidai kawai ka ganka tim ka fad’o a cikin jirgin ruwan komin nauyinka kuwa
D’aya bayan d’aya sukaita jawo mutane a cikin jirgin ruwan nan har layi yazo kaina
Oni Murjanatu dame zanji? Ga goyon Hamza a bayana, ga jakar kayana wacce ke d’auke da guzurina a rataye a d’ayan hannun, d’ayan hannun kuma tattare zanina nayi saboda tsorata da nayi ainun da ganin girman ruwan, ruwan da ban ta6a tsammanin ganin irinsu ba ko a mafarki
To da wanne hannun zan kama Igiyar kenan???
Hhhh ana dara ga dare yayi

*Badan-badan ba..*
Tabbas badan-badan ba dana daina rubutun nan haka, badan komai na fad’i hakan ba sai dan yawan tambayoyin da nake fuskanta daga masu karatu, ta wani 6angaren ma zan iya kiran hakan da suna cin fuska
*(Kalubale) kodai akanki labarin ya faru?*
*(Idan kunne yaji) kodai kece kika bi hanyar Sudan d’innan?*
Wad’annan sune tambayoyin da nake fuskanta daga masu karatun litattafaina.
Kuyi hak’uri. Da inada wata amsar da zan iya baku dana baku, saidai kuma kona bakunma ba lallai ku gamsu da amsar tawa ba, amma nima ga tawa tambayar zuwa gareku
D’an Jarida musamman mai d’auko Rahoto, abinda ya d’auko rahoton nan ya faru a kansa ne ko kuwa ya abin yake?
Bincikensa zakayi abinda ya d’auko d’in nan akansa ya faru koko ta yaya abin ya faru ko kuwa tsayawa zakayi ka fahimci abinda akeso a fahimtar da kai?
Misali Malami mai koyar da karatu musamman ma na addini idan yace maka Qalallahu au Qala Rasulu..zaka cemasa ne shi aka yiwa wahayi, ko zamani yayi da Annabi har yasan haka? 
Ni a tsammanina abinda ya kamace ka idan kanada hankali shine  ka natsu ka koyi abinda Malamin nan yakeson koya maka, domin amfanin kanka ko kuma wani naka, koma ba hakan ba na tabbata ilimin nan zaiyi maka rana a gaba
To nima a tawa fahimtar haka na d’auki Marubuci, domin shi Marubuci a ganina tamkar wani Malami ne mai koyar da darussa kala-kala kuma daban-daban, saboda duk abinda zai rubuta yakanyi k’okarin rubuta abinda ya faru ne, ko kuma yake faruwa, ko kuma wanda zai iya faru nan gaba

Kuma duk abinda zai rubuta d’in nan yakanyi k’okari ya binciko abinda ya shige masa duhu domin yaji dad’in mik’a sakon a inda ya dace
Su kuma masu karatu ya rage nasu, inma su d’auki wannan karatu dayake koyarwa a matsayin tatsuniya, ko kuma gargad’i da Jan hankali, ko nishad’i, koma dai miye ya rage nasu
Shiyasa da raina ya 6ace nace badan-badan ba dana dakatar da rubutun nan haka tunda babu wanda ya tilasta mani yinsa
Sai dai kuma nasan bayan masu bin littafin nan  domin yin tambayar kwakkwafi da sanin ko akanwa ya faru nasan akwai masu sonsa kuma da gaske har cikin ransu badan komai ba sai dan Fadakarwa, nishadantarwa da Kuma ilimantarwar da ke cikinsa
To ya zanyi kenan???😭
   Maman Ja’afar ce

    +966592551785

[3/10, 1:01 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira 
                 28
                 NA
    MAMAN JA’AFAR

Tattare zanin nawa nayi zuwa sama, kana na d’aure shi guri guda gam, dayake dama akwai dogon wando a jikina wanda Tsahara ta bani, a cewarta wai saboda tsallaka duwatsu, har yanzu dai ni ban fahimci wannan kalmar tata inda ta dosa ba
Kayan hannun na kuwa  wani namiji ne ya kar6a ya tilla mani su a cikin jirgin.
Tun k’arfina na daddage na rik’e igiyar katakam, su kuma masu jawowar suka fizgoni da karfi, sai gani tim a cikin jirgin
A tsammanina wannan d’an gida-gidan dana gani wanda ke cikin jirgin a ciki ne zamu zazzauna, amma sa6anin hakan sai naga a cikin wannan d’an kwami-kwamin mai kama da k’aton Baho suke taramu
Haka akaita jawo sauran mutanen a ciki har kowa ya gama shiga.
Tun kamin jirgin ya fara tafiya na fara jin wani jiri-jiri na d’iba ta, sabo tsananin girman ruwan,  wanda fad’in ruwan da kuma tsayinsa ya kai yanda duk iya hangen mai hange bazai iya hango k’arshen sa ba
Saida masu kula da jirgin suka tabbatar da mun gama daidaituwa a ciki kana suka fara aikinsu na tuk’i gadan-gadan
Ai kuwa da fara tuk’in nan me zai faru? wani tashin zuciya da Kuma yunk’urowar amai naji duk a lokaci guda, batare da 6ata lokaci ba kuwa na duk’ar da kaina saitin ruwan naci gaba da kwarara amaina a ciki
Abin mamaki sai naga bani kad’ai naketa kwarara aman ba hadda wasu daga cikin d’aid’aikun mutanen da muka shigo jirgin tare dasu
Yayinda wasunmu kuma babu abinda sukeyi face kuka da kururuwa na ganin mutuwa da sukeyi k’iri-k’iri
Sai a sannan ne na fahimci k’aryar da Nuhu Ejan yayi mana, na cewa wai ba’a tafiya da masu k’ananan yara, domin kuwa k’ananan yaranda nagani a cikin jirgin sun kai kusan goma shiyasa na k’aryata zancen nasa

******

Kwananmu uku a cikin wannan jirgin ruwan muna tafiya ba dare ba rana har muka samu isowa bakin ga6a, ma’ana mun samu damar shigowa K’asar *Yaman*
Kafin sannan abubuwa da dama sun faru acikin wannan jirgin, a ciki kuwa hadda rasuwar wasu k’ananan yara guda biyu da Kuma tsofaffi guda uku, wanda babu yanda aka iya da gawarwakin nasu a cikin jirgin sai dai tullasu da matuk’an jirgin suka dingayi a cikin ruwan
Hamza dai bai mutu ba amma kam yasha wahala iya wahala kafin daga bisani kuma ya warware harma yana mik’a hannunsa a cikin ruwan yana wasa dasu.
Da isarmu ga6ar ruwan batare da 6ata lokaci ba wasu mutane Yamanai sukazo suka taryemu da motocinsu
Batare da wani 6ata lokaci ba suka bamu umarni akan cewa mu shisshiga motocin da sukazo dasu(Kunsan Ejojin nasu badasu a kayi wannan tafiyar ba)
Wani babban gida suka kaimu mai d’auke da d’akuna barkatai kuma ginin k’asa, a can gefen d’akunan kuma garken tumakai ne wanda hakan ya tabbatar mani da cewa suma Yamanan makiyaya ne, a can k’urya kuwa 6angaren matansu ne.
Saida suka bamu abinci mai rai da lafiya mukaci muka k’oshi kana suka fara gabatar da aikinsu akanmu, ma’ana ainahin dalilin da yasa suka d’aukomu daga bakin ruwa
Cikin kakkausar murya d’aya daga cikinsu yakeyi mana bayani kamar haka
“Kunsan dai gaba d’ayanku nan badan mu tasaku a gaba muyita kallonku muka d’auko ku muka kawo ku nan ba ko? mun d’auko ku ne kawai domin gudanar da kasuwamcinmu, sabida haka batare da 6ata lokaci ba zan fara da mata domin a jikin mata and’anfi samun abin arziki, kuko maza idan har na juyo zuwa gareku kuka tabbatar mani da cewa babu wani bayani a tattare daku basai na fad’a maku abinda zai boyo baya ba kunfini sani” Ya fad’a yana mai wani zazzare idanuwa a tsakanin mazajen
Duk yana wannan bayanin nasa ne da harshen larabci domin yanzu nad’an fara jin harshen larabci kad’an-kad’an.
D’aya bayan d’aya ya d’in ga bin matan yana kakkar6ar lambobin wayar ‘yan’uwansu wad’anda suke zaune a K’asar ta Saudiya, a zuwan su bayar da kud’in fansar Yan’uwan nasu kana daga bisani su kuma Yamanan su sakesu kuma su d’ora su a hanyar Saudiyar
Masu lambobin sai bayarwa sukeyi, ga dukkan alamu dama a cikin tsarin tafiyar tasu sun tsara da wanann lokacin
Yayinda kusan mu sha biyar mukayi tsuru-tsuru domin daka kawai muka tunkari tafiyar batare da munyi mata wani tanadi na musamman ba, saboda nidai a iya sanina duk cikin dangina karan katakab babu wanda ya ta6a yin Fasfot ma bare har yayi tunainma zuwa wata K’asa ta daban.
“Hee tawila! addini rugum haggik” (Ke doguwa bani taki lambar wayar)
Abinda ya fad’a kenan da harshen larabci yayinda yake duban fuskata alamun dai dani yake zancen nasa
“Billa Abuya, Sa’iduniy, ana mafi ayyi shai’in fis-saudiya”(Dan Allah Baba ku taimakeni domin wallahi banida kowa a cikin Saudiya)
Bai sake bin ta kaina ba ya juya zuwa ga sauran, saidai suma sauran duk Kanwar ja ce, domin duk mu sha biyar d’in nan babu wani mai lamba a hannunsa, kowa zik’au d’insa yake.
Taramu sukayi guri guda, mu matan da bamu da lamba, yayinda su kuma masu lambar suka tarasu guri guda suma, kana kuma daga bisani suka juya gurin mazan
Suma d’aya bayan d’aya sukaita kar6ar lambobinsu, sai dai su mazan wad’anda basuda lambar sunfi masu lambar yawa, suma rabasu sukayi gida 2 da masu lamba da Kuma marasa lamba
Igiyoyi masu yawan gaske naga sun fiddo dasu daga wani d’aki daga cikin d’akunan da ke zagaye da gidan
A zuciyata har ina tunanin wad’annan uwayen igiyoyin kuma kome zasuyi dasu kodai…
Kafin na kai k’arshen tunanin nawa naga sun fara bin mazan d’aya bayan d’aya suna da’dd’aurewa tamkar dai wasu itacen sayarwa, ban kai ga gama al’ajabin wannan d’auri ba, naga sun fara tabkarsu da wasu shar6a-shar6an bulalai tamkar Allah ya aikosu
Kafin kace kwabo k’aton gidan ya kaure da ihun maza da Kuma koke-koke gami da kururuwa, babu abinda suke fad’a face neman d’auki da Kuma taimakon jama’a, su kuwa Yamanan sai faman dukansu sukeyi tamkar mai gida ya kama k’aton kwarto a d’akin matarsa.
Muma matan da bamu ake duka ba Kukan mukeyi, domin matuk’a abin yanada ban tausayi ganin irin dukan da ake yiwa mazan, yara, Samari, da kuma iyaye.
Domin muma tabbas babu makawa munsan ba tausaya mana zasuyi ba idan suka juyo zuwa garemu.
Ina can inata faman kukana bansan lokacin da Hamza ya ruga a guje ya k’ank’ame wani tsoho da ya fad’i yana birgima a k’asa ba, ina tsammanin tsananin dukanda akeyi masa ne harma ya tsittsinka igiyar da aka d’aure shin da ita.
Aiko d’aya daga cikin Yamanan nan yana hango Hamza a jikin wannan tsoho ya rugo da gudu yayi wani kukan kura ya d’aga Hamzan da hannu d’aya ya watsar dashi a k’asa sai kace ya samu wani k’ato, ji kake K’um k’arar buguwar kan Hamza kenan da ya had’u da gini
Da gudu naje na ruk’unk’umesa ina kuka ina share masa jininda ke kwarara daga goshin nasa
“Ni dai kam na hak’ura da wannan tafiya Saudiya d’in, tunda na baro Sudan naketa fuskantar abubuwa masu kama da tashin alk’iyama kala-kala, kuma duk wanda zan tarar a gaba yafi wanda na baro baya tashin hankali, to yanzu na tarar da wannan a gaba kuma bansan me zai faru ba, wannan bala’i dame yayi kama?”
Ni kad’ai naketa faman sabbatuna ina gunshek’in kuka, yayinda sauran matan da basu bada lamba ba suka zuba mani idanuwa sunata faman Jijjiga kai alamun tausayi saidai babu damar zuwa su taimakeni
Ban ankara ba saidai jin saukar wata uwar bulala nayi a bayana, daga nan kuma a kaci gaba da dukana ta ko ina…
“Ya Allah kayi gaugawar d’aukar raina kona huta da wannan azabar danake sha”
“Wayyo Innata, Wayyo Haro, ina Iya da Tsalha? Huwaila! kuzo ku taimakeni zan mutu fa, bakusan halinda nake ciki bane wai?”
“Ya Alllah karka kasheni batare dana nemi yafiyarsu ba”
Abinda naketa faman maimaitawa kenan a cikin kukan nawa, yayinda naketa faman birgima a k’asan yashin da ke baje a tsakar gidan Yamanan….

Bara na d’an barta ta gama kukan nata ta natsu, inyaso idan ta dawo hayyacinta sai muci gaba daga inda muka tsaya

*Ina nan tare daku masoyana*
Nagode k’warai da gaske da irin so da kauna da Kuma shawar-warinda kukaita bani akan cewa zama da mutane sai anyi hak’uri kuma ankai zuciya nesa

Nagode sosai masoyana Allah ya bar kauna a tsakaninmu
Kuma nayi maku alkawari insha Allahu bazan k’ara yin fushi akan wani cece-kucen wasu yan tsirarun mutane ba, indai kukaga kun jini shuru to ina mai tabbatar maku da wani uzurin ne ya taso mani, domin na yadda kuma na amince kowace nasara bata ta6a samuwa da sauki dole sai an had’a da hak’uri.
Nayi mamaki k’warai da gaske yanda wannan littafin ya samu kar6uwa fiye da yanda nake tsammani a wajen Al’umma, hakan nema ya k’ara tabbatar mani da cewa lallai sakon nan da nakeson isarwa yana isa a daidai a kuma inda yadace.
Alhamdulillahi kwalliya ta kusan biyan kud’in sabulu, dan banace ta biya ba tunda ban ida gamawa ba, amma ga dukan alamu zata biya d’in.
Allah ya bamu ikon amfani da daidan da ke ciki wannan littafin, kuskuren da yake cikinsa kuma Allah ya bamu ikon kiyayesa, sana kuma ya bani dama da kuma ikon kammala makushi lafiya kamar yanda na farasa lafiya
*Ina nan tare daku masoyana*😘😘
Maman Ja’afar ce

 +966592551785

[3/10, 1:01 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          jiki ya tsira 

     

                29
                NA
    MAMAN JA’AFAR

“Yarinya! kice masu kinsan Ummu Yasir zasu sassauta maki kinji?” wata mata ta fad’a tana mai duban fuskata
Cikin kukan nawa nace”To aini bansan wata Ummu Yasir ba”
Tsawa ta daka mani kana tace”Kedai kawai kice masu kinsanta mana”
Kana ta dubi sauran matan da basu da lamba irina
“Kuma idan sun zagayo kanku kuce masu kunsan Ummu Yasir kunji?” ta fad’a da harshen hausa, domin su Yamanan ba wata hausa sukeji ba, daga yarensu na Yamanai sai kuma larabci da suke ta6a kad’an-kad’an
“Ya Hammad! Ana aarif Ummu Yasir” (Mahamman nasan Ummu Yasir) na fad’a da muryar kuka domin har yanzu kukan nawa bai tsaya ba, saboda bayan nawa tamkar zai 6alle nake jinsa
Murmushi naga mai dukan nawa yayi, kana kuma daga bisani ya zaro waya a cikin aljihunsa ya daddanna wasu  lambobi ya kara a kunnensa
Sallama yayi kana daga bisani kuma yace
“Ummu Yasir ga wata yarinya nan harda yaro a gunta wai tace mana ta sanki, kinsan da batunta kuwa” Duk yana wannan bayanin nasa ne da harshen larabci
Daga  can 6angaren Ummu Yasir dake kwance akan gadonta faffad’a na alfarma wanda tsabar k’iba da tayi mata yawa har taso ta kusan cika gadon, lokaci zuwa lokaci kuma tana taunar Tuffar da ke hannunta (Apple)
“Ya girman yarinyar yake?” Ta fad’a a tak’aice kuma cikin k’asaita
“Ina ganin zatayi irn shekara 23 d’in nan haka ko 25” Ya fad’a yayinda yake k’ara dubana domin tantancewa
“Babu matsala kubar mani itan zan baku kud’in belin nata”
Murmushi naga yayi kana kuma ya k’ara da cewa
“Bayan itanfa akwaima wasu matan wa’yanda basu da mai fansarsu da yawa, ko zaki had’a da sune ranki ya dad’e?”
Tashi tayi zaune saboda maganar kayan kud’i dataji
“Zasu kai su nawa matan kuma ya kaga yanayinsu? zasu iya aikatuwa ko kuwa dai?”
“Gaskiya kalar wad’anda kikeso anan basufi su 8 zuwa 9 ba, amma sauran kam duk girma ya fara kamasu” Ya fad’a yayinda yake k’are mana kallo d’aya bayan d’aya
“To shikenan, su guda 9 d’in ku sakesu ni zan aiko maku da kud’in belin nasu, sauran kuma kwa gyarota a tsakaninku”
“Ummu Yasir bakya buk’atar maza? suma akwaisu da yawafa” Ya fad’a cikin zaulaya
Tsaki tayi gami da kashe wayar lokaci guda, domin ita bataga wata mamora a jikin namiji ba, ko ba haka bama maza shegen wayo ne dasu gami da taurin kan tsiya, bazasu bari a juyasu a bautar dasu kamar yanda ake juya mata ba.
■UMMU YASIR■
Wata shahararriyar mata ce K’asaitacciya wace take zaune a garin Riyadh na cikin k’asar Saudiya
Ummu Yasir ta shahara matuk’a wajen gudanar da irin wannan kasuwancin na haramun tare da had’in kan Yamanan
Ba wani kasuwanci bane illa idan Yamanan sun kwaso mutanen da suka shigo K’asar tasu ta 6arauniyar hanya, su kwasosu suzo su 6oye, a inda kowannensu zai fanshi kanshi da wasu yan kud’ade da suka gindaya masa wad’anda basu kai sun kawo ba, ko kuma ka bada lambar wanda zai fanshekan a K’asar ta Saudiya idan kanada shi
To idan duk hakan bai samu bane Ummu Yasir sai ta fansheka da kud’in da basufi jaka biyu ta Saudiya ba, idan ka iso Saudiyar sai ta dannaka gidan aikin larabawa inda duk wata za’a dinga biyanka kud’i kimanin jaka biyu ko kuma d’aya da rabi, a haka zaka zauna kayita neman kud’i tana kar6ewa har saika biyata kud’in da ta gindaya maka ma’ana jaka 25 ko kuma 30, kuma duk jaka d’aya idan ka canzata zuwa kud’in Nigeria tanada kimanin dubu d’ari harda yan kai a yanzu, koda ka biya hakanma sai taga dama take Iyantaka, Inko bataga dama ba haka zaka zauna kanayi mata bauta har wahala ta kasheka, ko kuma a zo lokacin da ga aikin kana gani amma bazaka iya yinsa ba saboda yin aiki saida lafiya.
Ada can kafin ta samo wannan hanyar ta neman kud’i gidan aikin larabawa take zuwa, amma tunda tayi cuku-cukun samun wannan hanyar shikenan babu ruwanta da zuwa gidan wani aiki bare har tasha wuya, saidai tana kwance kud’i suyita shigo mata tako ina.
Ya Allah kayi mana maganin ire-irinsu Ummu Yasir domin mu bazamu iya ba, kuma hukumomima basu san da zaman irinsu ba bare har su d’auki mataki, mai yiyuwa ma nasan ba ita kad’ai bace mai yin irin wannan haramtacciyar sana’ar akwai ire-irenta da yawa
Ko dayake idan 6era da satama nasan daudawa ma bata rasa yin wari ba, domin laifin ba nasu bane ba su kad’ai, hadda na wad’anda suka biyo ta 6arauniyar hanyar da Kuma Yamanan da suka basu mafaka, nifa aganina amma bansan ko laifin wa masu karatu suke gani ba
Ya Allah ka kawo mana agajin gaugawa a  a cikin wannan lamarin

******

Koda gama wayar tasa sai ya daina dukan nawa, abin mamaki ma wai har wankewa Hamza jinin yayi kana ya saka mashi magani gami da d’aure masa ciwon da bandeji, shima Hamzan naga yad’an samu sauk’i-sauk’i domin ya daina kukan yanzu.
Iya wad’anda tace a ware mata su suka ware mata, tare kuma da wa’yanda suka biya kud’i suka fanshi kansu ko kuma wa’yanda yan’uwansu na Saudiya suka fanshesu
Sauran kuma da basuda wani mataimaki sai Allah sukaci gaba da dukansu ba ji ba gani, a tsammaninama wasunsuma ko lumfashi basa iya yi domin naga sun daina ihun neman taimakon
Ni dai kam yau naga tashin hankali iya tashin hankali
Acikin wannan bala’in mukayi kwanan zaune

■Washe gari■

Bayan sun bamu ruwa munyi wanka munci abinci mun k’oshi, sukace kowa ya d’auko kayansa domin yanzun nan zamu d’au hanya, kuma sune zasu rakamu har zuwa *Gezan* hasalima dan wannan rakiyar ne suka kar6i kud’in mu kuma suka wahalar damu har haka.
Kusan su 6 suka shirya domin yi mana wannan rakiya, sai dai ba yagaggun kayanda ke jikinsu bane suka bani mamaki a’a illa Bindugogin danaga kowannensu ya rataya a kafad’arsa da Kuma ‘yan sauran makaman da ba’a rasa ba.
Ra6awa nayi gurin wannan matar wacce tace mani nace nasan Ummu Yasir d’azu
“Baiwar Allah naga duk sun d’auki makamai harda Bindugogi, anya wannan tafiyar ta lafiya ce kuwa?”
Na fad’a murya a k’asa-k’asa domin ina tsoron kar su jiyoni na k’ara shan wata uwar mazgar tun ban warke daga waccen da sukayi mani ba
“Dama kinsan K’auyawan Yamanan nan haka suke da shegen son tashin hankali tamkar wasu ‘yan ta’adda, yanzu wad’annan makaman da kikaga sun d’auka to indai muka had’u da hukuma akan hanya saidai suyi bata kashi dasu, mai rabon hayewa cikinsu ya haye wanda kuma bashi da rabon hayewa yayi kwanan lahira”
Zazzaro idanuwa nayi cikin firgici tsoro fal a cikin idanuwana nace
“Amma baiwar Allah kina nufin akansu kad’ai dai rigimar zata k’are bandamu ko?”
“Kinga yarinya! wannan tafiyar fa da zamuyi tamkar sirad’i ce, wanda keda rabon hayewa zai haye, wanda kuma bashida rabo saidai ya tsinci kanshi a hannun hukuma ko kuma cikin kabari na fad’a maki”
Nan take naji cikina ya wani k’ugi ya murd’a, da gudu na nufi band’aki domin gudun kar nasaki zawon da ya kusan kubce mani a cikin jama’a
Shima Hamza da gudu ya bi bayanta, yana kuka yana fad’in
“Mama dan Allah ki tsaya, karki tafi ki barni a hannun wad’annan azzaluman ni kad’ai, wallahi zasu iya kasheni, Kingafa goshin nawa har yanzu bai daina yi mani ciwo ba” Yana magana shima yana bin bayanta da gudu tare da shafa goshin nasa inda ya fashe
“Kai zo nan” Cewar wata mata kenan daga cikin abokan tafiyar tamu tare da rik’o hannunsa, dayake ta fahimci inda Murjanatun ta nufa
“Zauna nan ka jirata kaji? babu abinda zasuyi maka domin wuya bata ta6a kawo mutuwa dole sai kwana ya k’are” 

Ta fad’a tare da zaunar dashi a gefenta
Zama yaron yayi a inda matar ta zaunar dashi, amma dukda da hakan jikinsa bai daina kyarma ba, alamun dai har yanzu yaron a firgice yake…..

Lallai hanyar zuwa garin *Gezan* tanada matuk’ar had’ari ba d’an kad’an ba

Amma dai Karku gaji ku biyoni domin jin chakwakiyar da ke can gaba

*Maman Ja’afar*

+966592551785

[3/10, 1:02 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                30
                NA
   MAMAN JA’AFAR

Muna ji muna gani suka tasa k’eyarmu muka d’au hanyar zuwa garin Gezan a k’afa

Yayinda muka bar ‘Yan’uwanmu da dama a hannun wad’annan Yamanai batare da munsan makomarsu ba, saboda salo-salo suke gana masu na azaba.
Hanyar da mukebi ba hanya bace ba shantal kamar sauran hanyoyi, a’a wannan babu wata hanya sai uwayen duwatsu manya da k’ananu da muke hawa muna sauka, wani gurin ma idan mukazo rami ne, sai munshiga ta cikinsa kana kuma mu nemo hanyar da zamu fice mu gangara
Kuma dai duk da wad’annan Yamanai muke yin wannan tafiyar, domin K’asarsu ce kuma garinsu ne, su suka san duk wani lungu da sak’o dake cikinsa.

Sai da mukayi tafiyar kusan awa 4 kana muka samu isowa *Shabaka* Shabaka a larabcinsu na Yamanai yana nufin wani guri da hukuma batason abi shiyasa aka zagaye illahirin wurin da wata doguwar waya mai raga-raga, kuma anzagaye ko ina da wayar mai raga tamkar dai yanda mutum yake yiwa filin da ya siya idan yana tsoron kada ayi masa rinto nan gaba ko kuma a k’wace masa.

Indai kazo gurin babu wata hanyar da zaka bi ka canza wata hanya sai nan d’in dai, Idanko ba haka ba saidai ka koma baya inda ka fito

“Mai yaro ya rik’e yaronsa sosai, mai kaya kuma ya rik’e kayansa domin mun iso bakin daga”
Abinda d’aya daga cikin

Yamanan yaketa faman maimaitawa kenan tun kamin mu k’arasa gurin Shabakar
Dukda mun tsorata ainun da jin wannan kalami nasa, amma bamu bari jikinmu yayi sanyi ba.
Da d’ai d’aya-da d’ai d’aya Yamanan suke tuntud’amu muna haurawa Shabakar har layi ya iso kaina
Wuri-wuri na farayi da ido domin bansan yanda zanyi na hawo wannan doguwar katangar ta waya da goyon Hamza ba
Ban ankara ba naji k’ato d’aya ya d’agani sama, niko banyi wata-wata ba na mak’ale a saman katangar wayar sai kace Biri ya mak’ale a saman bishiyar ayaba, na fara haurawa a hankali
Kamin na ida direwa naji k’arar bindiga tako ina, alamun dai hukuma sun hangomu lokacin da muke k’etara wannan shamakin da suka sanya tsakanin hanyar Yaman da Kuma Gezan
Tunda uwata ta haifeni ban ta6a jin k’arar bindiga ba sai yau, aiko ban tsaya wani bin wayar a hankali ba naita k’abar-k’abar sai kace k’adangaruwa a jikin bango har na dire
Amma har yanzu ban daina jin k’arar tashin harbe-harben nasu ba
Ina dirawa nabi abokan tafiyar tawa a guje domin dama suna fara jin k’arar harbe-harben suka falla a guje
Cikin Yan mintina kad’an na cimmasu, sai yanzu na yadda idan ka hango mutuwa k’iri-k’iri duk abinda kake tunanin bazaka iya ba sai kaga kayishima batare da ka sani ba
Inba gudun mutuwa ba taya zan iya yin gudu irin wannan d’auke da goyon Hamza a bayana? lallai mutuwa ta daban ce
Kusan mu 30 muka baro K’asar Yaman d’in hadda ‘yan rakiyarmu mutum 6 amma yanzu kwata-kwata bamufi mu 15 zuwa 20 ba, sauran duk sun mace a wajen d’an k’aramin yak’in da akayi tsakani Yamanai da Kuma Hukumar Saudiya, a ciki kuwa harda ‘yan rakiyar tamu guda 2
Da tsallaka wannan Shabakar tafiyar da muka k’ara batafi ta awa d’aya ba muka samu isowa garin Gezan.

*******
■Gezan■

Babban gari ne na larabawa, mai girma gaske wanda ake hada-hadar kasuwanci a cikinsa, dan idanma baka ta6a zuwa Saudiya ba idan kazo Gezan sai ka d’auka Saudiyar ce ka iso, domin suma mutanen Gezan sunada arziki iya nasu bakin gwargwado sai dai duk da haka ko k’afar Saudiya basu kamo ba.
Da isarmu Gezan bamu zame ko ina ba sai wajen Sarkin Zango, suko yan rakiyar tamu suna kawomu bakin Zango suka juya abinsu.
Hannu bibiyu Sarkin Zangon ya kar6emu domin dama tun kamin muzo ya riga ya san da zuwanmu
Zangon nasa ba laifi yanada d’an kyau iya nasa bakin gwargwado, domin duk yafi sauran Zangunan da nasani kyawu da Kuma tsaruwa.
Bayan munci abinci mun ne natsu ya kiramu falonsa
“Daga cikinku ina mutanen Ummu Yasir suke?” Ya tambaya tare da duban fuskokinmu
Kusan mu biyar muka d’aga hannu domin sauran duk sun riga sun mutu a hanya wajen wannan bata kashin da akayi
Bai tambayemu sauran ba domin a tsammanina ga dukkan alamu ya riga yasan abinda ya faru dasu a hanya
Gyaran murya d’an tsamurmurin mutumin yayi kana yaci gaba da cewa
“Idan kun gama hutawa zuwa gobe idan Allah ya kaimu zan saka mai mota ya d’aukeku iya ku biyar d’in nan ya kaiku Riyadh ya damk’aku a hannun wacce ta fansheku a hannun Yamanai, kun fahimceni?”
Gyad’a kai mukayi mu duka alamar amincewa
Kana daga bisani ya bamu umarni da mu koma masaukinmu koma k’ara kikkimtsawa kafin zuwa goben.

******
A 6angaren Haro kuwa yanzu arziki yaci uban na da, domin sana’ar Shanu ta kar6esa alhamdulillahi saboda yanzu haka ya k’ara aure bayan Masa’uda da ya aura tun barowar Murjanatu gida da shekara d’aya, yanzu kuma ga amarya Farida da ya k’ara, harda  albarkar yara 3 a tsakaninsa da uwar gida, ga kuma amarya da bamusan iya alkhairanda tazo masa dashi ba
Yanzu haka ya bar wancen gidan nasu ginin k’asa yayi ginin bulo da bulo, da motocinsa guda biyu, d’aya ta d’aukar shanu yayinda kuma d’aya ta kasance ta hawa idan yana gida

Arziki fa ya zauna su Haro anzama Alhaji Haruna
Ita ko Iya mahaifiyar Haro kullum cikin farin ciki da godiyar Ubangiji take kasancewar ta samu Sirikkai yan albarka masu yi mata biyayya, domin a kullum matan Haro basu da wani gurin da ya wuce su kyautatawa Mijinsu dashi da mahaifiyarsa wacce suka d’auka tamkar uwa a garesu, kansu a had’e yake babu wani kishi ko bak’in ciki ko k’yashi a tsakaninsu.

Muje zuwa Gezan…..
Maman Ja’afar ce

 +966592551785

🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

            jiki ya tsira
                  31
                  NA
     MAMAN JA’AFAR

■Washe gari■
Kamar yanda muka saba tun safe iya mu biyar d’in muka gama kikkimtsawa muna jiran umarni daga Sarkin Zango
“Yauwa, kuna ina? ku fito ga mai motar  da zai kaiku Riyadh d’in nan ya k’araso”
Da sauri kowaccen mu ta d’auki jakarta, ni kuma na kama hannun Hamza muka rufa masa baya.
Dab da zamu shiga motar na juyo na dubi Sarkin Zango 

“Baba ana samun garin kwaki kuwa nan kusa? wallahi tun a Gezan nawa guzurin ya k’are”
Maganar tawa dariya ta basa dariyar da bansan dalilin yinta ba, can dai yaga dama yace
“Ai baiwar Allah daga wannan Zangon kunyi bankwana da cin garin kwaki, domin tafiyar da zakuyi daga nan zuwa Riyadh batafi ta awa 2 zuwa 3 ba”
Nan take naji wani farin ciki ya mamaye mani zuciyata, domin nasan wahalarmu tazo k’arshe insha Allahu
Ban mayar masa da amsa ba saboda dariyar da yayi mani d’azu na shigewata cikin mota, batare da 6ata lokaci ba direban nan yasawa mota wuta.
Gudu yakeyi na fitar hankali, ba tsaitsayawa, a cikin wannan halin ne mai ya k’are masa muka tsaya
Na fahimci hakane saboda gani da nayi ya faka a gidan mai.
Sai dai abin mamaki Kyawawan gidaje da Kuma kasuwanni gami da assibitoci masu kyawu muketa wucewa tun d’azu
Abin ya d’aure mani kai matuk’a, har dai nakasa 6oye al’ajabina na tambayi Mai motar da harshen larabci
“Ya Hammad! Ish ismu hadal balad” (Ya Mahamman ya sunan wannan garin ne)
Murmushi yayi tare da dubana ta Madubin gaban motarshi 
“Jiddah” Ya fad’a a tak’aice
Da sauri na dubesa “Ya’any hina fis-Saudia?” (Kana nufin har mun shigo Saudiya)
“Aywa Sah” (K’warai hakane)
Nan take murna da farin ciki suka kamamu, bani kad’ai ba harma sauran matan abokan tafiyar tawa.

Yana gama shan mai a Mahatta (Gidan mai) yaja motar mukayi gaba…

Sai dai abin mamaki ji mukayi yanata faman yin salati batare da munsan dalili ba
“Ya Hammad Ish mishkila?” (Mahamman meke faruwa ne) Cewar d’aya daga cikin abokan tafiyar tamu kenan
“Tabtish” (Yan sanda masu binciken kan hanya)Ya fad’a a tak’aice tare da dukan sitiyarin motar alamun dai yana cikin damuwa
Dukda bamusan dalilin damuwar tasa ba amma muma hankullanmu ya tashi matuk’a
Gashi babu wata hanya a kusa damu balle ya canza wata hanya, inaga shima irin tunanin da nakeyi shima shi yakeyi shiyasa naga yanata faman waige-waige
Bamu ankara ba mukaji yan sandan suna k’wank’wasa k’ofar motar tamu ta wajen direba
“Jib hawuyya” (Bamu takardar izinin zaman k’asarka) d’an sandan ya fad’a bayan direban ya zuge gilashin motar
Jiki na kyarma direban ya ciro takardar daga aljihu ya mik’a masa
Umarni yabawa direban daya saukemu, muko allanbaran muka tu6ure mukace bazamu sauka ba, shi Hamza dayaga anata rigima kuka ya fashe mana dashi.
“Kunga ku rufa mani asiri ku sauka Karku ja su 6ata mani igama” (Takarda)mai motar ya fad’a da harshen labarci kuma cikin fushi
Bamu da za6in da ya wuce sauka, muna ji muna gani yan sandan nan suka tasa k’eyarmu har cikin motarsu mai raga, ma’ana ta kamo masu laifi ko kuma wa’yanda suke zaune a K’asar ta Saudiya batare da takardar izinin zaman k’asa ba.
A cikin motar ne nake tambayar d’aya daga cikin abokan tafiyar tawa wacce taci kuka ta k’oshi har idanuwa sunyi mata hulu-hulu kamar zasu fad’o k’asa

 

“Yanzu baiwar Allah nan d’in ma inda zasu kaimu sai munyi zaman sati biyu kana su sakemu mu tafi Riyadh d’in”
Na fad’a ina cizon le6ena alamun zasu rusa mani bajat
Cikin matsanancin kuka d’ayar ba wacce na tambaya ba take bani amsa
“Ai inma sati biyu ne da sauk’i, yama za’ayi hukumar Saudiya su kamaka kuma su sakeka batare da sun danganaka da K’asarku ba? ai yanzu kam saidai mu wakkala domin cikin ‘yan kwanaki kad’an zasu sadamu da k’asarmu”
Tashin hankali ba’a sa maka rana, wane irin tashin hankali kuke tunanin Murjanatu zata shiga?

******

Ai kuwa haka akayi, domin iyakacin mu garin Jiddah, ko Makkar ma da muke yawan jin labari bamu k’arasa ba suka zarce damu Tarhin(Gun da ake ajiye wad’anda aka kamo marasa takardar izinin zaman k’asa ko kuma wani abin na daban kafin a kaisu K’asarsu)
■Tarhin■
Babban guri ne dan ya kusan kai girman wani k’aramin garin, yayinda suka d’ebi wani guri daga ciki da ya kusan kai girman wata unguwa suka rufesa suka jejjera gadaje da sunan wai  d’akuna
Hmm rayuwar Tarhin batayi ba danma dai yanzu an d’an samu gyara ta wasu 6angarorin
******
Satinmu d’aya a cikin Tarhin suka kwasomu da motocinsu na hukuma sai Iyafot d’in Jiddah
Da ace bak’in ciki yana kisa, na tabbatar daya kashe Murjanatu a wannan lokacin, saboda bak’in cikin da ta shiga bazan iya fasaltawa masu karatu irin shi ba
Cikin mintinan da basu wuce 30 ba aka iza k’eyar mu zuwa cikin jirgi.
Hhhh ta lek’o ta koma kenan
Da shigarmu jirgi bamuyi awa 6 cikakkiya ba jirgin Saudiya ya diremu a Kano
Garin da na bari ina d’oki da mazakwad’i yau gashi na dawo masa ina dana sani, domin ko kad’an kwalliya bata biya kud’in sabulu ba
Ni babbar matsalatama inda zan samu ko dubu d’aya ce wacce zata kaini K’auyenmu na K’wadage
Shin Bara zanyi koko maula zanyi?
Abinda naketa tunani kenan a cikin zuciyata
“Kin manta Nigeria mutum lafiyayye baya yin bara? Da dai hanyar Sudan ne kota Saudiya wannan sai kiyi”
Abinda wata zuciyar tawa take ta faman maimaita mani kenan.
Da k’yar nasamu kud’in motar da zasu kaini Tashar K’ofar ruwa daga Iyafot d’in na Kano.
Wajen Hajiya Mai Tuwo na nufa d’auke da goyon Hamza a bayana kai tsaye
Da k’yar nasamu ta ganeni bayan nasha faman yi mata kwatance-kwatance
Dukda hakanma saida ta gaigaya mani bak’ak’en magan-ganu kana ta wurgo mani dubu d’ayar
Wannan dubu d’ayar na cincinta har nasamu ta kaini K’auyenmu na K’wadage

*******
■KOWAT TUNA BARA■
Hausawa sukace wai bai ji dad’in bana ba
Abin mamaki wai yau Murjanatu ce nake hangowa a K’auyensu na K’wadage bayan ta shafe sama da shekaru biyar batare data waiwayesa ba
Hmm Wuya koda magani ba dad’i inji masu iya magana
******
Da k’yar iyayenta suka ganeta saboda uwar wahalarda tasha, mafi yawan jikinta ita da Hamza ma duk ciwuka ne da basu ida warkewa ba, inaga ciwukan da sukaji ne wajen k’okarin hawa Shabakar Gezan.
******
Bayan koke-koke da Kuma jajantawa juna ta nemi da a taimaka a mayar da ita gidan tsohon mijinta wato Haro dukda baizo biko ba
Sai dai ba a nan gizo yake sak’arsa ba, wancen auren jingina da Murjanatu tayi minene matsayinsa?
To anan Malamai sun tabbatar da cewa wannan auren ba sunansa aure ba sunansa zina, shiyasama suka bata umarnin yin istibira’i kafin tayi wani auren ko kuma idan zata koma gidan tsohon mijin nata
*****
Da k’yar, da ji6in goshi, gami da lallami da lallashi tare da addu’oi Haro ya mayar da Murjanatu d’akinta a matsayin mata ta uku, a garesa, hakanma wai albarkacin Hamza taci Cewar Haron
*****
Murjanatu ce zaune a babban falonsu itada Haro tare da abokan zamanta wato Masa’uda da kuma Farida suna cin abincin dare, yayinda suma yara suka kasance gefe guda suna cin nasu abincin, kowa cikin farin ciki abinsa
Uwar gidan ce ta dubi K’aramar cikinsu wato Murjanatu kenan
“Dan Allah Murjanatu duk sadda kika tashi yin tafiya zuwa Saudiya ko kuma Sudan, dan Allah nidai ki taimaka ki sanar dani na biki kona huta da wannan bak’in talaucin nima” Ta k’arashe maganar tata cikin zaulaya tare da kannewa Haro ido d’aya
Dariya suka kwashe da ita gaba d’ayansu hadda k’yak’yatawa
Kana da k’yar Murjanatu ta tsaida dariyarta tace
“Ai Aunty bake masoyiyata ba ko mak’iyinama bana yi masa fatan bin wannan hanyar ta Sudan a k’afa”

K’arshe
Tammat bi hamdullah

*GODIYA*
_Alhamdulillah nagodewa (S.W.A) mai kowa mai komai daya nufeni da fara wannan littafi lafiya har gashi kuma cikin yardarsa da Kuma amincewarsa na k’aresa lafiya_
*SHARHI*
_Babban manufata tayin wannan d’an littafin itace_

*Fadakarwa*

*Nishadantarwa*

*Ilimantarwa*

*Jan hankali*
_Shiyasa zanyi amfani da wannan damar nayi kira a kan muhimman abubuwa guda uku, Murjanatu dai ba komai yasakata yin wannan tafiyar ba face abubuwa guda uku_

_Jahilci_

Talauci

_Rashin tawakkali_
1 _Jahilci wani ciwo ne mai wuyar magani, shiyasa zanyi amfani da wannan damar nayi kira ga manyan Malamanmu na Sunnah da su daure suyi jahadi su dinga zagayawa lungu da sak’o na k’auyukan da muke dasu a Arewacin Nigeria suna fadakar da mutanen ciki akan ibadu da sauran abubuwanda basu sani ba, musamman matan K’auyuka da yawa suna yin aure ne kawai dan sunga anayi batare da sanin minene matsayin shi kanshi auren a cikin addinin musulunci ba_

_Wallahi wasu mutanen karkararma ko alwalla basu iya ba bare aje kan maganar wanka da salla da Kuma sauran ibadu na yau da kullum_
_Dan Allah Malamanmu ku taimaka ku duba wannan matsalar kar Da’awarku ta tsaya iya Birane kawai k’auyuka da dama sunfi mu na cikin Birane buk’atarku_
2 _Talauci: wannan kuma wani hakki ne daya rataya akan Gwamnati_
_Dole Gwamnati ta kula tayi tsayin daka wajen ganin ta taimaki mutanen Karkara kamar yanda take taimakon mutanen da ke cikin Birni, domin suma mutane ne, me sukayi da za’a waresu gefe guda_?
_Mutanen K’auyuka ni aganina basu da wata buk’ata a gwamnati wacce ta wuce a taimaka masu wajen Noma da Kuma kiwo, idan aka taimaka masu wajen basu Takin zamani da sauran abinda ba’a rasa ba irin su Assibitoci haka da dai sauransu, a nawa zaton angama masu komai dansu dama zaman OFIS bai damesu ba, wannan saimu yan birni da bama son wahala_

3 _Rashin tawakkali_
_Dole mu zamo masu tawakkkali da Kuma yarda akan yanda Allah ya tsara mana rayuwarmu, da dad’i babu dad’i indai mun kasance muminai_
_Saboda a ganina da ace Murjanatu tayi hak’uri kuma tayi tawakkali akan halinda ta samu kanta na rashi da Kuma k’uncin rayuwa, aganina da duk wad’annan wahal-halun basu faru akanta ba, saboda na tabbata duk bakinda Allah ya tsaga bazai ta6a hanasa abinci ba, kuma arzikinka a duk inda kake zaizo ya sameka har gida_
_*Shiyasama Allah (S.W.A) Yace: Waman yattaqillaha yaj’allahu makraja wayar zuquhu min haisu la yahtasib*_

_Bi ma’ana duk wanda yaji tsoron Allah kuma yayi tawakkali ya mikama Allah dukkan lamurransa, to kuwa Allahn nan bazai bashi kunya ba, zai sama masa mafita, kana ya azurtashi ta inda baiyi tsammani ba_
_To da ace Murjanatu tayi tawakkali kuma ta barwa Allah jagorancin rayuwarta ni a ganina da duk hakan bata kai ga faruwa ba_
_Ni Maman Ja’afar ban hana a fita neman kud’i a K’asar Saudiya ko Sudan ba, amma gargad’ina anan dan Allah idan antashi yin wannqn tafiyar a a cije a biyo ta saman jirgi badan komai ba sai dan gudun fad’awa irin halinda Murjanatu ta sami kanta a ciki, kuma kamin azo d’in a tabbatar da hannunda za’a zauna na gari ne saboda gudun fad’awa a hannun 6ata gari irinsu Ummu Yasir_.

*SADAUKARWA*
_Wannan littafin Sadaukarwa ne ga dukkan hausawanmu mazauna K’asashe daban-daban_
_Ina rokon Allah ya daidaita mana k’asarmu Nigeria ta yanda saidai azo neman kud’i a K’asarmu badai muje neman kud’i a k’asar wasu ba_
_Naka naka ne komin lalacewarsa_

*GAISUWA*
_Ga dukkan ‘yan group dinmu wato *Musha karatu*_ Musamman

Auntynmu Jiddah

Aunty Yabi

Aunty Baraka

Aishatu (Chuchun gaye)

Maman Haneef

Safara’u Murtala

Wamcy(Maman Aneesa)

Maman Waleeda

Ummi Adamu Bauchi

Asiya(Maman Ihsan)

Mrs Zannah

Nafi Nijar

Mrs Farzanah

Maman Nasir

Na’ima Bature

Zaituna(Ummu Ammar wa Ashraf)

Maryama & Maryama
_Da sauran wadanda ban ambata ba, kuyi hakuri duk kuna raina kuma ban manta da ku ba, idan danbu yayi yawa ne baya jin mai_
_Yan group dinmu *Musha karatu* har yanzu dai da bazarku nake taka rawa😘_
*KE TA MUSAMMAN CE*
_Malamata *Sadiya Jegal* saboda da taimakonki da shawarwarinki na fara rubutu har gashi cikin ikon Allah na kammala littatafai guda biyu lafiya, kuma_ _Alhamdulillahi duk sun samu kar6uwa a wajen Al’umma, badan ke ba da sai dai na mutu da basirata acikin kai domin bansan taya za’ayi nayi rubutu ba_

_Nagode sosai *Aunty Sady* Allah ya kara maki basira da daukaka kana ya bar so da kaunar da ke tsakaninmu_.

*KWARIN GUIWA*
Khadija Katuru KT

Ummi Adamu Bauchi

Asiya (Maman Ihsan)
_Nagode sosai da irin kwarin guiwar da kukaita bani tun a littafina Kalubale har zuwa yanzu dana kammala Idan kunne yaji.. badan kuna karfafa mani guiwa ba da labarina sai dai ya tsaya a iya kaina_

_Nagode sosai da so da Kaunarda kuka nuna mani Allah ya barmu tare_.

*AMINAINA*
Aishatu Kn (Ayshanty)

Umma Salma

Matar Sudani

Aishan Ali

Ummin Usman

Rukayyar Auwalu

Maman Yasmeen

Maman Ma’aruf

Salamatu Gatafa

Rahinatu Dikko
_Zumuncin mu na har abada ne insha Allahu_

*GODIYA GA MASOYANA*
_Masoyana masu bin litattafaina babba da yaro samari da yan mata tsoho da tsohuwa maza da mata musamman_

Maryam Mustapha

Rabi’atu

Mrs Al’ameen

Fatima Ibrahim

Badiyyah Darma Kt

Maman Maryam

Maman Khalifa

Safiyya Muhammad

Maman Mu’azzam

Zainab Abdullahi

Aina’u Bukhari

Aisha Mustafa

Riley Teema

Ummu Hanan

Maman Yusra

Hadiza Aliyu

Sa’ida Abubakar

Ummu Sadiq

Samera Shu’aibu

Suhairat Bawadi
_Kai! wallahi idan danbu yayi yawa ba jin mai yakeyi ba, da wanda na ambata da wanda ban ambata ba duk nagode da Kaunar littafina a gareku,  Allah ya bar so da kaunar da ke tsakaninmu sai kuma Allah ya sake hadamu a littafina na gaba wato *MAHABU* labarin tafiyar Mahabu k’asar Libiya_

😘😘😘😘😘😘

👋👋👋👋👋👋
MAMAN JA’AFAR

+966592551785

IDAN KUNNE YAJI 1-15

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                    1
                   NA
       MAMAN JA’AFAR

Gafaranku dai! Gafaranku dai! a’a kodai Huwailar bata kusa ne naji shuru? Salamu alaikum masu gidan nan!
Can daga k’uryar d’aki Huwaila taji kamar ana magana ta leko
“a’a yaushe a gari inji mak’i bak’o?” ta fad’a tana washe baki cikin murna da farin cikin ganin babbar aminiyarta
“Tun d’azu naketa faman rabka sallama kinyi shuru a cikin d’aki sai kace matacciya, ko dai mai gidan naki yana ciki ne anata sebeyin da abeyin?” 
Dariya Huwaila tayi kana tace “kai Murjanatu Kedai bakya gajiya da tsokana, da sanyin safiyar nan ina zaki samu wani magidanci a gida? ai saidai tsofi ko kuma marasa lafiya” rik’e hannun Murjanatu tayi gami da cewa “tunda har na ganki da sanyin safiyar nan nasan da walaki wai goro a miya, mu k’arasa can gindin bishiya inji ko k’arar Haro d’in aka kawo mani, dan nasan dai tatsuniyar gizo bata wuce ta k’ok’i”
Fizge hannuna nayi cikin wasa “Kai Huwaila akwai ki da sharri, wato harma kin camfani kenan ko? to kwantar da hankalinki nan bada dad’ewa ba zaki nemi mai kawo maki k’arar ma ki rasa gaba d’aya ba shikenan kin huta ba?” 
Murjanatu da Huwaila K’awaye ne tun na yarinta, sun shak’u da juna matuk’a shiyasa ma duk abinda d’aya daga cikinsu zaiyi sai yayi shawara da d’an’uwansa
Ko bayan sunyi aure alak’arsu bata yanke ba saima k’aruwa datayi.
Dukkaninsu bazasu wuce shekara 18 zuwa 20 ba, saboda tun sunada shekaru sha shida shida aka kai kowace d’akin mijinta, har gashi Allah ya azurta Huwaila da yara biyu yayinda ita kuma Murjanatu take da d’aya

Sai dai so dayawa naji mutane suna cewa wai sai hali yazo d’aya ake abota, sai dai anan kam abin ya banbanta domin Huwaila Allah yayita saliha mai kamun kai da Kuma natsuwa, da d’in da d’awa kuma bata da son abin duniya shiyasama hankalinta yake kwance take tafiyar da rayuwata cikin kwanciyar hankali
Yayinda ita kuma Murjanatu tun tana k’arama ta kasance yarinya ce mai shegen son kud’i da Kuma rayuwa irinta hutu, shiyasama ko bayan ta  auri Haro take ganin tamkar bai dace da ita ba, a ganinta yanda take da kyaun nan kamata yayi ace wani hamshak’in mai kud’i take aure, sai dai ta kudiri aniyar neman kud’i kota wace hanya domin kece raini, da wannan tunanin ne har tasan yanda tayi ta nemo hanyar tafiya Sudan domin ta cika gurinda ya dad’e yana kai komo a cikin zuciyarta, tunda taji ance anayin kud’i a Sudan. Wannan kenan
**********
Bayan sun zauna a gindin bishiyar ne sun natsu Huwaila ta dubi Murjanatu cikin mamaki “Kika ce na kusa neman ki na rasa? kaddai maganar tafiya Sudan d’in ne baki fasa ba har yanzu?” 
“Yo me kuwa za’a fasa? mutuwar ko ginan kabarin? yanzuma da kika ganni nayo sammako gidan ki zuwa nayi ki ranta mani kud’i, kinsan irin wannan doguwar tafiyar saida kud’i isassu, saboda nayi lissafi da kudin kayan d’aki na da kud’in ‘yan awakaina da zan siyar idan na had’asu duka bazasu isheni yanda nake buk’ata ba, saboda kinsan D’ahara sadda ta tafi da kusan dubu talatin ta tafi amma tace wai basu wadaceta ba, shiyasa nakeso natafi koda dubu arba’in ne idan so samu ne” 
Tagumi Huwaila tayi gamida zubawa Murjanatu ido tana girgiza kai cikin takaici 
“Yanzu ke Murjanatu bazaki bi maganar mijinki da Kuma iyayenki ki hak’ura da wannan tafiyar ba? wallahi ina jiye maki dana sani nan gaba fa” 
“Kinga Tantabara sarkin aure ko nace maki daudawa, idan zaki ranta mani kud’i dubu biyar ko goma ki ranta mani idan kuma bazaki bani ba Karki tsaya 6ata mani lokaci da surutu marar Ma’ana, gara ki gaggauta sallamata na wuce, na baro Hamza gida nasan yanzu haka yana can yana tsandarawa Iya kuka” 
Mik’ewa Huwaila tayi cikin alamu na damuwa ta kalli Murjanatu “Ni kam banida wasu mak’udan kud’in da zan baki har dubu biyar ko goma tunda kinsan bana sana’ar fari bare ta bak’i, sai dai inada abu d’aya da zan iya baki idan kinaso” 
Cikin nuna ko in kula nace ” Ke Malama ana maganar kud’i kina maganar wani abu, to bani abin naga ko zai min amfani a hanya”
Ajiyar zuciya Huwaila tayi gami da dafa bishiyar darbejiyar da ke kusa dasu
“Ba komai zan baki ba sai abu d’aya wato nasiha, kuma a tunanina ayi maka nasiha yafi a baka kud’i ammafa ga mai hankali…
“Au dama tasani gaba zakiyi kina zagi sai kace wata ‘yarki har kike wani cewa zaki bani wani abu” 
“Yanzu Murjanatu nasihar da nakeso nayi maki itace zagi….
“Zagi mana gashi nan kin fara ce mani mahaukaciya” 
Murmushin takaici Huwaila tayi kana ta ci gaba da maganarta
“Murjanatu idan bazaki manta ba, tun farkon neman aurenki Haro yaketa hidima dake wani lokaci ma harda iyayenki, haka a bikinki ya dage yayo maki kayan aure na fita tsara, wanda kowa yazo bikin nan babu abinda yake fad’a sai alasanbarka, ki duba ki gani a haihuwar Hamza irin kayan yajin da yayo maki wanda ko d’iyar mai gari sai haka 

Murjanatu karki manta mafiya yawan matan garin nan su sukeyin daka da kansu wasuma harda zuwa gona, ammake Haro ya d’auke maki komai har dakau kai maki yakeyi, iya k’arfin bawan Allahn nan kullum so yake ya ganki cikin farin ciki, ki ganni nan sai nayi wata banyi miya da nama ba ammake duk bayan kwana 2 ko 3 sai ya siyo maki k’ashin miya, yanzu abinda kike shirin yi masa kinyi masa adalci Kuwa? anya kina ganin Allah ba zai saka masa ba Murjanatu nan gaba?” 
Gyara d’aurin zanina nayi gami da gyara zaman mayafinda ke kaina “To Malama sarkin wa’azi kin gama wa’azin na wuce ko kuwa da saura na tsaya?” 
“A’a na nagama Hajiyar Sudan tafi abinki, amma dai IDAN KUNNE YAJI…
“To ai kunnen nawama bai jiki ba bare har jikin nawa ya kasa tsira” ta k’ara da cewa ” ni zuwan nawama gidanki bai k’areni da komai ba sai 6acin rai, Kinga tafiyata ni, kar na biye maki na 6ata lokaci wajen shirye-shiryen tafiyata” tana tafiya tana surutanta har ta fice daga gidan

Murmushin takaici Huwaila ta bita dashi tare da cewa “Allah ya shirya”
**********
Murjanatu bata zame ko ina ba sai gidan Delu dillaliya, takoyi sa’a ta tarar da ita domin Delu da garin Allah ya waye take fita neman kayan siya a cikin gari
Bayan sun gaisa ne Murjanatu ta bijirowa Delu buk’atarta tason Delu taje taga kayan d’akinta domin suyi ciniki ko sa daidaita
Da mamaki Delu tace “Wai ni ban gane ba, aurenki ya mutu ne da Haro Murjanatu ko kuwa ci rani zaku tafi keda shi banida labari?” 
A zuciyata nace kaji tsohuwa da kinibibin tsiya, ko ina ruwanta da wani dalilin saida kayana?
Amma a zahiri sai nace “Eh ci rani zamu tafi Kano, Kinga ai bazan kwashi kaya na tafi dasu ba, kuma idan na barsu a gida nasan ba adana mani su za’ayi ba kafin na dawo shiyasa nace bara kawai na siyar saboda kud’in zasuyi mani amfani Acan d’in idan munje” 
Jijjiga kai tayi alamar gamsuwa, saida ta 6alli goronta ta fara taunawa kana ta dubeni tace “To yanzu zamu tafi tare kenan na gano kayan ko kuwa sai anjima zanzo na sameki a gidan naki?” 
Cikin nuna k’osawa da gajiyar tambayoyinta nace “a’a  Iya Delu tare zamu tafi yanzu kinsan sauri mukeyi dan inaga tafiyar bazata wuce kwana uku zuwa hud’u ba” 
Tashi tayi ta zura silifas d’in ta gami da d’aukar d’an buhun da ke kusa da ita wanda ga dukkan alamu inaga kud’i ne take ajewa a ciki saboda basaja, tink’is-tink’is muka d’auko hanya har gidana…..
   *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          jiki ya tsira
                  2
                 NA
      MAMAN JA’AFAR

Iya surukar Murjanatu na tsakar gida goye da d’an jikanta Hamza sai runtuma mata kuka yakeyi,  tanata faman kai da komowa tana Jijjiga shi gami da lallashi amma yak’i yin shuru tun d’azun, tun tana fad’anta a cikin zuciya har dai ya kai ga fitowa fili

“Yarinya kin raina kowa a gidan nan, bakyajin maganar kowa sai abinda kikaga dama zakiyi , wannan wace irin jaraba ce Allah ya had’a ni da ita da sunan Suruka? tun  da sanyin safiya kinsa k’afa kin bar gidan nan amma bakya ko tunanin halinda wannan yaron yake ciki…

Haro na can 6angaren su yajiyo Iya nata faman fad’a ita kadai yayinda shi kuma Hamza sai k’ara tunzurata yakeyi yanata rabka kuka ba kakkautawa

Fitowa yayi daga k’ofar tasu yazo yasamu Iya nata faman safa da marwa “Iya dan Allah kiyi hak’uri indai halin Murjanatu ne ai yaci ace mun saba dashi zuwa yanzu, haka zamuyita hak’uri muna binta da addu’a ko Allah zaisa ta shir….

Maganarsa ta mak’ale a mak’oshi lokacin da ya hango Murjanatu da Dillaliya suna shigowa gidan
Murya k’asa-k’asa nake cewa Dillaliya  ” Iya Delu gafa ‘yan sa ido nan a tsakar gida, saboda haka idan sun tambayeki dalilin sayar da kayan nawa kawai kice masu wasu nagani a gurinki zan siya, shiyasa zan baki nawa kayan sai nayi maki ciko” 
Murmushin jin dad’i Dillaliya tayi domin tunda har taji Murjanatu na ‘yan k’arairayi tasan bata da gaskiya, shiyasa da wannan damar zatayi amfani ta siyi kayan yanda taga dama. 
Ni dai kam 6angarena na wuce yayinda nabar Dillaliya itada Iya suna gaisawa, harma dillaliya nabawa Iyan labarin canjin kayan d’aki da zanyi

Iya dai bata ce mata komai ba saima mik’awa Dillaliya Hamza datayi”ungo d’an nan, dan Allah wuce mata dashi tun d’azun yaketa faman kuka yanzu haka nasan bazai rasa6 zazza6i ajikinsa ba saboda yasha kuka”
 Sumui-sumui ta kar6o Hamza ta shigo dashi 
“Haba iya Delu kinsan sauri nakeyi amma kika wani shantake gurinta kunata fira” na fad’a yayinda nake sauke samirunda ke cikin kwabet k’asa ina jeresu a gabanta
“Kinga d’iyar nan, niba surukarki bace da zaki tasani gaba kina yi mani fad’a, iyakar kayan kenan ko kuwa hadda kwabet d’in zaki siyar?” ta fad’a fuska a d’aure alamar babu wasa
Nan take naja bakina nayi gum dan na lura idan nace zan nunawa Iya Delu halina ba mamaki ta fasa siyen kayan nawa
Batare da 6ata lokaci ba muka gama cinikin kayan d’akin nawa duka da gado da komai da komai, da yake a k’auye ne kaya ba wani tsada sukeyi ba duka duka dubu 25 ta bani, nasan kud’in kayana sunfi haka amma da yake sauri nake naga na kawar dasu shiyasa tana tayawa batare da naja ba na bar mata a haka,

Sai yanzu naga tana washe mani baki, da kuwa tabi ta kwa6e fuska sai kace kashi.
*DA DARE*
Ina kwance akan tabarmata nida Hamza yayinda shi kuma Haro ya shinfid’a bargo ya lullu6a da babbar rigarsa, sharar baccina nakeyi hankali kwance har ina mafarkin gani nan nazama wata hamsahak’iyar mai kud’i, gidana mai kyawun gaske harda shuke-shuke ga motoci ko ina birjik sai wacce nakeso zan hawo,  abinci kowa gashi nan sai wanda nakeso zan saka masu aiki su dafa mani, ina kishingid’e a katuwar kujera mai numfashi ina canza tashoshi ina taunar naman kaza

“Murjanatu! Murjanatu! Haro ne yake dadda6ar Murjanatu da nufin ya tasheta 
Bud’e idona nayi a hankali domin na tabbatar da inda nake, ganin Haro da nayi kusa dani shine ya tabbatar mani lallai abinda nagani yanzu bada gaske bane mafarki ne, cikin 6acin rai na dubesa

“Haba Haro! miye haka dan Allah ina cikin baccina mai dad’i zaka wani tasheni?” 
“Kiyi hak’uri Murjanatu magana nakeso muyi dake ne shiyasa” 
“Kuma duk karasa lokacin da zakayi mani maganar sai cikin wannan tsohon daren saboda baka san darajar d’an Adam ba ?” tsaki nayi gami da gyara kwanciyata na juya masa baya
“Yanzu Murjanatu abin naki har yakai ki siyar da kayan d’akin ki duka sabida Allah?” 
Waigowa nayi dagakwancen na dubesa shek’ek’e 
“Bakaji abinda kace ba ne yanzu? kace kayana ko? to kuma dan mutum ya sayar da kayansa har sai anwani tsaya anayi masa tambayoyi, barama kaga zuwa safe suma awakin nawa siyar dasu zanyi duka inga wanda ya isa ya hanani” 
Hawaye ne yazubo daga idanuwan Haro domin ya tabbatar tunda har ta siyar da kayan d’aki kuma tana niyar siyar da kiwonta ya tabbatar babu abinda zai hanata yin wannan tafiyar sai wani ikon Ubangiji
“Murjanatu dan Allah kiyi hak’uri ki zauna tare damu nayi alk’awarin zan baki jarin dubu 50 kiyi duk sana’ar da ta kwanta maki a rai” 
Ni surutunsa ma dariya yake bani

 “inbaya ga abinka Haro me na sama yaci bare jeho mani? Kumama ai hausawa sunce idan mutum yace zai baka riga wai ka fara duba ta jikinsa tukun” na k’arasa maganata cikin dariya dan wallahi dariya yake bani, ko ina yaga dubu hamsin d’inda  zai bani indai ba sayar da kansa zaiyi ba, to wannan sai na kusa yarda
 Jiki a sanyaye Haro ya koma kan shinfid’arsa ya kwanta zuciyarsa sai faman k’una takeyi masa, ya rasa wannan irin son kud’i na matarsa wanda dalilinsu har take neman yin wasa da igiyar aurenta, “Ya Allah ka kawo mani mafita acikin wannan lamarin” cewarsa kenan bayan ya rufe fuskarsa da babbar rigarsa.
*WASHE GARI*
Tun dugu-dugu Murjanatu ta kammala duk wani aikin gida da yakamata ace tayi ta sa6a Hamza a baya batare da ta nemi izinin Mijinta ko kuma surukarta ba sai gidan Ummaru Mahauci

Basu 6ata lokaci sosai gurin cinikin ‘yan awakan nata ba dama guda 3 ne, saidai shima a son ransa yayi cinikin domin duka awakan dubu goma sha uku ya bata akansu.
Iya na gindin murhu tana k’okarin d’umama masu tuwonda zasuyi kalaci tunda yanzu Murjanatu ta daina yin komai na gidan, ta hangi shugowar Murjanatun tare da Ummaru Mahauci, bata kulasu ba domin tasan kwanan zancen, saima k’ara maida hankalinta da tayi gurin hura wutar d’umamenta dake shirin mutuwa 

“Sannu da aiki Iya” na fad’a tare da shigewata 6angarena, dan ba damuwata bace da amsawarta da rashin amsawarta duk wannan ita ya shafa
 Ban samu Haro a gidan ba dama haka na tsammata, saboda indai ya kwanta da 6acin rai kuma ya tashi dashi har Allah Allah yake gari ya waye domin yayu ficewarsa daga gidan gaba d’aya. 
*******
Yau ranar jumma’a, wacce tayi dai dai da ranar d’aurin auren Saudatu k’anwar Huwaila
Basai na fad’a maku ba domin kun san dai su Murjanatu sune k’irjin biki
Tun azahar ta gama shiryawarta tsab ita da yaronta tana jiran Haro yazo ya bata gudunmuwar da zata kai gidan bikin amma shuru gashi har La’asar ta gabato
Tsaki tayi gamida duba tsohon agogon da ke hannunta “Matsalar auren talaka kenan wallahi, inda mai kud’i nake aure ina zai 6ata mani lokaci haka akan ‘yan kud’in bikin da basu taka kara sun karya ba?” 
Rufe bakinta keda ta jiyo sallamar Haro can tsakar gida shi da Iya suna gaisawa irinta D’a da mahaifi
Baifi minti 5 ba ya k’araso  6angarenmu “A’a yayun amarya badai har an shirya ba?” 
Harara na rabka masa tare da juyar da kaina gefe guda 
“To Allah ya baki hak’uri, tuba nakeyi a gafarceni, wallahi na tsaya can jeji ne taya baba wasu ayyuka shiyasa kikaga ban dawo da wuri ba” 
“Hannu ya saka cikin aljihunsa ya zaro nera dubu daya kacal ya mik’o mani har wani murmushi yakeyi waishi a ganinsa yayi bajinta 

“To ga wannan sai ki kai gidan bikin ko?” 
Yatsuna biyu nasa na kar6i kud’in batare da nayi tunanin yi masa ko godiya ba na k’ara gyara goyona nayi gaba abina
*********
Ko hanyar gidan bikin ban nufa ba, tasha kawai na zarce domin neman motar da zata kaini Daura(dayake su a k’auyen Daurar suke)
Saida na k’ara laluba aljihuna na tabbatar kud’ina dubu arba’in ba d’aya suna nan daram kana na shiga motar muka d’au hanya, dama mutum d’aya kawai ya rage ta cika sai gashi Allah ya kawoni
Wani farin ciki ne naji ya ziyarci zuciyata lokaci guda domin wannan zaman da nayi a cikin mota alamace da ke nuni da cewa na hau hanyar SUDAN …….
Oni! Maman Ja’afar koya wannan tafiya ta Murjanatu zata kasance babu sallama da iyaye bare miji ko Yan’uwa da abokan arziki? Ku dai kuci gaba da bina domin jin yadda zata kasance  
    *NICE TAKU*

*MAMANJA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          _jiki ya tsira_
                  3
                 NA
     MAMAN JA’AFAR

*Gidansu Haro*
Tun bayan sallar isha suke tsammanin dawowar Murjanatu amma shuru kakeji tamkar an aiki bawa garinsu, wasa-wasa har kusan k’arfe goman dare babu ita ba labarinta
Tun Haro yana 6oye damuwarsa har dai yakai ga ya bayyanata. d’akin Iya mahaifiyarsa ya lek’a tare da yin sallama Cikin kulawa mahaifiyar tasa ta dubesa “A’a Haro! kaddai kace mani har yanzu Matar taka bata dawo daga gidan bikin ba?”
“Wallahi Kuwa Iya har yanzu shuru dai, kuma bamuyi da ita zata kwana gidan amaryar ba bare ko nace can zata kwana” 
“Haro kenan! har ka manta halin mutuniyar taka ne? ai indai Murja ce ko ka bata izini ko baka bata ba indai tayi niyar kwana saita kwana, tunda tasan kai sallamamme ne babu abinda zaka iya yi mata” 
Canza maudu’in firar tasu yayi domin duk yanda Murjanatu take 6ata masa rai bayaso yaji wani ya fad’i maganar da ta danganci aibu gareta
“Yanzu abinda za’ayi Iya bara naje gidan bikin tun wuri naga ko zan sameta acan d’in, idan kuma ban sameta ba nasan babu makawa gidansu ta wuce sai na biya ta gidan nasu na d’aukota mu dawo tare”
“To shikenan, a dawo lafiya Allah yasa a dace”.
*******
Tun a hanya yake tambayar matan da suke dawowa daga gidan bikin ko sunga Murjanatu, amma abin mamaki duk wacce ya tambaya sai tace kwata-kwatama bata ga Murjanatu a gidan bikin ba

A haka har ya iso gidan bikin , baiyi wata- wata ba ya kutsa kansa cikin gidan (dayake kunsan gidajen k’auye, yin hakan ba wani abu bane domin kowa yasan gidan kowa)

Huwaila ya fara samu a tsakar gida ita da wasu mata suna wanke kwanonin da aka 6ata na hidimar bikin, gefe guda ya kirata 

“Huwaila kaddai da gaske ne Murjanatu batazo gidan bikin nan ba?”
Cikin mamaki ta dubesa  “Tace maka zatazo gidan bikin ne? amma kuma da mamaki tunda har gashi kusan kowa ya gama watsewa amma ban ganta ba, kodai….
Da dai ya fahimci Murjanatu batazo gidan bikin ba sallama yayima Huwaila ya tafi ya barta cikin jimamin inda Murjanatu ta tafi cikin wannan tsohon daren.
Bai zame ko ina ba sai gidan Surukkan nasa wato gidansu Murjanatu, ya kuwa taki sa’a domin kusan kowa na gidan yana nan
Gidan nasu irin gidan family d’in nan ne amma kowa da 6angarensa, yayunta 2 maza Lado da Tsalha kuma kowannensu yanada mata a cikin gidan, sai Babansu wanda girma ya fara kamashi da mahaifiyarta wadda itama ta d’an manyanta d’in 
Sallama Haro yayi kana ya kutsa kai cikin gidan domin ba’a yi masa shamaki da ko ina na gidan ba
Dukkan su suna tsakar gida kwakkwance suna shan iska dayake lokacin zafi ne, amma ga mamakinsa ko alamun Murjanatu bai gani a cikinsu ba, jiki a sanyaye ya k’arasa cikin gidan
Bayan sun gaggaisa ne yake tambayar su “ko Murjanatu tazo gidan nan kuwa, tace mani ta tafi gidan biki tun yamma amma har yanzu shuru bata dawo ba, kuma naje can gidan bikin nemanta amma suma  sunce mani kwata-kwata ma basu ganta ba, shiyasa na biyo ta nan nagani kotazo”
Sallallami suka d’auka su duka, suna mamakin inda Murjanatu ta tafi cikin daren nan
“Bamuga ta zama ba Haro, gara mu tashi tun da wuri mu zazzagaya duk inda akasan tana zuwa ko Allah zaisa a dace” cewar Inna kenan Mahaifiyar Murjanatu yayinda take hahhaska tocila ga dukkan alamu mayafinta take nema.
Gaba d’aya suka fito suka bazama neman Murjanatu Matan su Tsalha kawai aka bari a gidan, sai ko babanta da girma ya riga ya kamasa, shiyasa ma yanzu uwar itace komai na gidan. Wannan kenan.
*Garin Daura*
Dab da mangariba muka iso cikin garin  Daura, dayake irin tsohuwar motar nance ta kasuwa muka hau shiyasa ba wani gudu ta cika ba
Bayan mun sauka a motar ne na tsaya waige-waige ba komai nake nema ba sai d’an abinda zan siya mana nida Hamza wanda zamu saka a bakin salatin mu saboda yanzu nakeso mu wuce Kano kar sai mun d’au hanya yunwa ta kamamu
K’ara tattaki nayi can cikin tashar domin naga abinda ya dace na siya
Wata mai nono na hango ta tasa k’warayenta a gaba, kuma ga dukkan alamu nonon Kindirmu ne mai kyau
“Iya kinada leda kuwa ki zuba mani na nera hamsin?” 
“Da akwai leda mana ‘Yata  bara a zubo maki” Ta fad’a yayinda take lalumo ledar cikin k’waryarda ke saman ta nonon
“Yauwa Iya!  karki juye nonon acikin ledar duka, ki rage mani kad’an zan bawa wannan yaron”  Na fad’a tare da nuna mata Hamza a bayana
Hamza na bacci a bayana na saukosa na Jijjiga shi saboda yasamu yad’an sakawa cikinsa wani abu, da k’yar nasamu ya wartsake saboda yasha Jijjigar tsohuwar mota
Nonon na basa yasha yayi nak kana na ida shanye sauran harda tand’e k’waryar da aka zubo mani a ciki (kusanfa nonon daura akwai dad’i da kyau da tsabta)
Tashi nayi na goya Hamza kana na kar6i sauran nonon na cikin leda na biya gurin wani mai tireda anan kusa na sayi Biredi da ruwa na zura a ‘yar k’aramar jakata na k’ara gaba.
****
Mota mota na dinga bi ina neman motar Kano, amma kowa na tambaya sai yace mani wai sai gobe yanzu dare yayi, niko inda son samu ne nafiso na bar Jahar Katsinar  kwata-kwata yau d’in nan basai gobe ba, saboda ina tsoron kar tunanin ‘Yan uwana yasa suzo nan tasha nemana, domin hausawa sunce wai idan Rak’umin ka ya 6ata har a bakin allura ma yakamata ka duba.
“Yarinya kece mai neman motar Kano ko?” Da sauri na juyo, wani Dattijo ne nagani sanye da kayan ‘yan yoniyan 
“Eh Baba nice, an samu ne?” 
“Ga wata can baya, ya fad’a tare da nuna mani inda motar take,  ina jin Kanon zataje, kije can ki tambaya ki gani ko zakidace”
“Nagode baba” na fad’a a tak’aice 
Sauri-sauri gudu-gudu na nufi inda ya nuna mani, ai kuwa na taki sa’a domin Kanon zata tafi sukace mani, saidai abin takaicin mutum 2 kawai na tarar a ciki, yana iya? da babu ai gara ba dad’i inji masu iya magana
Haka mukaita zama a cikin motar nan ba’a samu k’arin ko mutum d’aya ba, inaga hakan ya samo asali ne yanda kowa yake ganin motar a kwarra6e
Hakanan badan direban yaso ba yajamu mu ukun muka tafi, amma da sharad’in wai idan yasamu fasinja a kan hanya zai d’auka, dayake muma mun k’agu Mutafi muduka mukace masa mun amince, dayake babbar mota ce d’ari biyar biyar muka bayar muka d’au hanya sai Kano ta dabo tumbin giwa, mai dala da gwauron dutse, mai mata mai mota, yaro koda me kazo anfika
*******
Dukda agogon hannuna ta lalace amma a tsammanina zamuyi awa 2 zuwa 3 kana muka iso, saboda mun dade muna kwarara tafiya kana muka samu isowa.

 

Motar mu bata zame ko ina ba sai a tashar K’ofar ruwa a lokacin inaga kusan k’arfe goma da wani abu na dare
K’afafuwana duk sun rirrik’e sunyi mujirya saboda tsabar zaman mota, ga yunwa da k’ishirwa da gajiya duk sunbi sun rabkeni, Allah yasama Hamza sarkin bacci ne badan haka ba da yau na shiga uku da kuka
 Waige-waige nafara yi domin samun wanda zan tambaya, cikin sa’a kuwa na hangi wata yar budurwa mai saida awara sunata wasa da Karnukan motar dake wurin, da sauri na isa inda take
“K’anwata! Dan Allah ana samun motar Mai duguri kuwa anan?” 

Sai da ta gyara zaman bokitin awarar da ke kanta kana tace 

“Gaskiya ban sani ba saidai ki k’arsa can ofishin yan yoniyan ki tambayesu kiji” ta fad’a tare da nuna mani wani d’an k’ramin ofis da yatsanta
Wani matashi daga cikin matasan da suke wasa da ita ya dubeni yana wani washe hak’oransa duk sun dafe tsabar shan Sigari yace
 “Amma Uwata indai Mai duguri zaki tafi ai ina ganin kamar dare yayi, kinsan fa da nisa ko baki ta6a zuwa bane?”
Tak’aita maganar tasa nayi tare da cewa ” Nagode ‘yan samari, bara na k’arasa can d’in na tambayesu ko Allah zaisa a dace”

 da fad’ar haka nayi gaba abina……
Lallai sa kai yafi bauta ciwo inji y’an magana

Ina fatan kuna biye dani?
   *NICE TAKU*

*MAMANJA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          jiki ya tsira

                  4
                 

                 NA
     MAMAN JA’AFAR

Mutum biyu kawai na tarar a cikin ofis d’in, sallama nayi masu bayan sun amsa ne nace “Dan Allah Malamai ana samun mota mai zuwa Mai duguri kuwa yanzu?” 
D’an ba’kin ne ya dubeni

“Haba yarinya, wane direba mai hankali zai ja maki mota zuwa Mai duguri acikin wannan daren? d’aga kansa yayi sama ya hango agogon da ke manne ajikin tsohon shagon, ko ince ofis kamar yanda naji suna Kiran wurin 
“Duba agogofa ki gani kusan k’arfe sha d’aya na dare yanzu” 
“Yanzu dai kam bazaki samu direban mutane mai zuwa Mai duguri ba saidai ko direban aljannu, wannan kuwa ko k’arfe ukun dare ne zai jaki ku tafi” cewar wani d’an tsamurmurin saurayi kenan na kusa dasu 
Dariya suka shek’e da ita su su duka 
Can wani mutum na cikin mota wanda ke jiyo tattaunawar tamu yace “Yarinya ki d’aukeni shata kawai najaki mu ware yanzun nan ko ya kukace?”  
Da dai na lura nema sukeyi su raina mani hankali sai na k’ara gyara goyona nayi gaba, nabarsu sunata soki burutsunsu suna dariya
Can na hangi wata ‘yar lukutar mata mai abincin siyarwa a cikin tashar, wani dad’i ne ya ziyarci zuciyata domin nasan koba komai matar zata k’ara mun haske akan tafiyar da nakeso nayi, tunda mu mata munada kara koda kuwa bamusan juna ba
 banyi wata wata ba na tunkari inda take kai tsaye
“Salamu alaikum” abinda na fad’a kenan bayan nayiwa kaina matsugunni a d’aya daga cikin kujerun robar da ke jejjere a gurin
“Wa alai kumus salam” “abinci za’a kawo maki ne?  dan kinsan ba’a zama anan hakanan kawai inba sayen abinci zakayi ba”
Banyi niyar sayen abincin ba, saboda da gani ko ba’a fad’a ba nasan abincin zaiyi tsada, ni kuma ba son kashe kud’i da yawa nakeyi ba saboda abinda ke gabana na tafiya, amma danaga babu wata hanya da zatasa muyi fira da ita sai wannan bud’ar bakina sai kawai nace “Eh Iya” a kawo mani Tuwon Biski na nera 40″ 
Shek’ek’e ta kalleni kana tace “Hala daga k’auye kika fito” 
Ban nuna mata 6acin raina ba dukda nasan abinda take nufi, saima amsa mata da “Eh” da nayi a tak’aice
Murmushi tayi kana tace “Haba, koda naji, ki kalleni ki kirani da Iya sai kace wata tsohuwa? kodan kin ganni da k’iba haka gingirim? girman jikin ne kawai yarinya amma ba wasu shekarun kirki ne dani ba”
Dariya ce taso ku6uce mani Amma sai na wayance da yin tari hadda dafe k’irji
A zuciyata nace indai wannan guzumar ba tsohuwa bace aiko anci mutuncin yarinta, mata kin kusan yin jika dani kinaso ki kira kanki yarinya? gaskiya indai haka tsofin birni suke wallahi basuyi ba, sai yanzu ne na fahimci ashe wannan dalilin ne yasa tun daga nesa na hango ta sambad’a uban Jan baki a le6enta da Kuma saman girarta harda barbad’a kumatu
“Sannu yarinya! k’warewa kikayi ? bara na kawo maki ruwa” 
Niko hadda zazzare idanuwa kamar wacce tayi k’warewar gaske
Bayan nasha ruwan ne na natsu ta dubeni cikin kulawa
“Yarinya bamu da Tuwon Biski anan sai dai na Masara kona Shinkafa,  kuma Su d’inma babu na nera 40 sai na 100 muke sayarwa”
 “A bani na d’ari d’in” na fad’a a tak’aice domin Allah nagani bandan naso ba zan sayi wannan tuwon
Yanzuma dai saida na tashi Hamza na basa tuwon, saida na tabbatar yaci ya k’oshi kana na fara aikawa cikina nima
“Hajiya yanzu dare yayi ba’a samun motar zuwa Mai duguri ko?” Na fad’a yayinda nake kai lomar tuwon a bakina 
Murmushi naga  tayi alamar taji dad’in sunanda na kirata dashi
“Yanzu kam yarinya dare yayi bazaki samu motar Mai duguri ba, sai dai idan kinada wasu Yan’uwa ki nemesu kije ki kwana zuwa safe sai kizo akwai motoci birjik anan sai kin za6a ma” 
“Wallahi ban san kowa ba anan garin, hanya ce kawai ta kawoni” 
“Allah sarki! Hala sa6ani kika samu da mijinki zaki koma gida? ai mazan yanzu lamarin su har tsoro yake bani
A zuciyata nace kun jini da mata da shegen bin k’wakk’wafin tsiya ko ina ruwanta
Amma a zahiri sai nayi Murmushi nace ” A’a wallahi Hajiya babu ko d’aya, idan naje Mai dugurin ma wucewa zanyi gab” 
“Keko wane gari zaki tafi mai shegen nisan tsiya haka?” 
“Ba gari ba dai K’asa Hajiya…
Da mamaki fal a fuskarta tace “Kaddai kice mani Sudan kikeso ki tafi?”
Dariya nayi mai fidda sauti dayake naga yanzu ta fara sakin jikinta dani “Wallahi Kuwa can zani kamar kin sani” 
“Kinko san had’arinda ke cikin tafiya Sudan kikeso ki tafi?”
Cikin k’osawa da wad’annan surutan nata nace “Hajiya babu komai Insha Allahu, kawai kiyi mani fatan Alkhairi” domin duk wata magana da zata kawo mani cikas akan wannan tafiyar ba sonta nakeyi  ba 
Itama data lura ba son maganar nakeyi ba sai ta canza akalar maganar tata 
“Yaro ne ko yarinya kike goyo?”
Murmushi nayi  “Yaro ne sunansa Hamza” 
“Allah sarki! Allah ya mana Sahabin Manzo”
“Ameen” Na fad’a a tak’aice 
Saida naga ta sassallami mutanenda sukayi mata rumfa kana na dubeta d’auke da d’an Murmushi na nace “Waini ko Hajiya daga Mai duguri kuma ina za’a nufa a isa Sudan d’in”? 
Dariya ta fashe da ita hadda k’yak’yatawa, da k’yar ta takawa dariyar tata burki ta dubeni harda d’an guntun hawayenta tace “Waike yarinya kin zaci zuwa Sudan d’in tamkar zuwa k’auyenku ne?” Cikin dariya tace “Karki damu idan kikaje Mai dugurin nasan bazaki rasa abokan tafiya irinki ba sa baki labari acan” 
Dayake ta bani haushi shuru nayi bance mata komai ba 
“Amma idan kin hau Motar Mai dugurin kice su a jeki *Minna Mai Mad’aci* daga nan sai kuma a d’au hanya” 
Cikin sauri na dubeta nace “hanyar ina Hajiya?” 
“Kya tambayeni keda bason maganar kikeyi ba? idan kin had’u da abokan tafiyarki sa gaya maki ko hanyar ina ce…..

Kuci gaba da biyoni ni kuma ina bin Murjanatu domin ganin yadda wannan tafiya tata zata kasance

   *NICE TAKU*

*MAMANJA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

       _Jiki ya tsira_
                 5
                 NA
     MAMAN JA’AFAR

Hakanan mukaita firarmu jefi-jefi har zuwa lokacin da naga tana harhad’a kayanta alamun ta tashi kenan inaga sai kuma gobe
“Hajiya akwai gurin kwanan mata kuwa a nan tashar?” na tambaya danaga tana niyar tafiya tabarni nan ni kad’ai
“Gurin jama’a kuma har a rasa gurin kwanciya yarinya? ga wata babbar rumfa can, kin hangota? ta fad’a tare da nuna mani inda rumfar take da yatsa” to anan irinki wad’anda sukayo dare a hanya suke kwana” 
Gaskiya birni basu da k’ara ko kad’an, dan inda a k’auye ne akayi bak’o babu yanda za’ayi ace anbarsa a waje ya kwana, sai dai ko idan ana zargin mugu ne
Ko kad’an banji dad’in abinda tsohuwar nan tayi mani ba, domin ni a tsammanina zata gayyaceni zuwa gidan ta ne na kwana acan inyaso da safe sai na dawo nan tasha d’in na hau mota na tafi abina 
 Ajiyar zuciya nayi cikin sacewar guiwa nace “To Hajiya bara na k’arasa can d’in, nagode Allah ya tashemu lafiya” 
Itama sallama tayi mun gami da d’aukar tarkacen girkinta tayi gaba ta barni a nan zaune ina rarraba idanuwa
Da dai naga ba sarki sai Allah na kwashi Hamza dana shinfid’ar a saman wani tsohon buhu na tunkari rumfar da ta nuna mani 
Ban tsammaci zanga mata ba a gurin shiyasama gabana ke fad’uwa gami da tsoro fal a cikin zuciyata na kwana da zanyi a tsakiyar tasha, amma ga mamakina sai na hangi mata kusan su goma a cikin rumfar a kwakkwance, dayake akwai k’atuwar tabarma shinfid’e a gurin wacce aka ajiyeta dama saboda irinmu masu kwana, sai dai wanda yaga k’azantar tabarmar tayi yawa ya kan iya k’ara zaninsa a kai ko kuma mayafinsa.
Sallama nayi masu wad’anda basuyi bacci ba daga cikinsu suka amsa mani, kana daga bisani kuma kowacce ta juya baya abinta domin yin bacci 
Anya kuwa zan iya yin bacci anan? abinda nake fad’a acikin zuciyata kenan
Gefen tabarmar na zauna na d’auko dan bargon Hamza wanda na cuso acikin ‘yar k’aramar jakata na shinfid’a masa na kwantar dashi akai, kana na d’auko zani d’aya daga cikin zannuwana guda biyu dana taho dasu na lullu6a masa
 Ni kuma na zauna dab dashi na had’a kai da guiwa inata faman gyangyad’i dan ba nace bacci ba domin zuciyata bata gama aminta da wurin ba, Allah Allah nake gari ya waye  nakama gabana dan tamkar na jawo safiyar kusa nakeji.
Muna nan a haka bansan lokacin da bacci 6arawo ya sace ni ba, sai kiraye-kirayen sallar asuba da akeyi ne ya farkar dani.

***

Inda naga mutane suna tunkara domin yin alwalla nima can na nufa “Malama ya baki bada kud’in shiga ba kina nema ki wani wuce sai kace bakisan yanda tsarin yake ba?”
Juyowa nayi domin na tabbatar dani yake magana ko kuwa da wani na bayana yake
Ganin da nayi yanata faman hararata da jajayen idanuwansa shine ya tabbatar min cewa dani d’in yake 
“Malam kama ruwa fa kawai zanyi nayi alwalla shine har sai nabada kud’i dan dai ku birni komai naku na siyarwa ne?” 
“A’a ba kama ruwa zakiyi ba kama wuta zakiyi, dalla Malama idan bakida kud’in da zaki biya ki matsa gefe akwai masu jira karki 6ata mana lokaci” 
Tun jiya da na baro k’auyenmu na *K’wadage* ban k’ara tunaninsa ba sai yanzu, yanzunma Band’aki na na tuna na gida, inda idan na sharesa na wanke bana barin kowa ya shiga, dagani sai  Haro, dan ba k’aramin duka nakeyiwa yaro ba idan naga ya shigar man band’aki, suko manya idan sun shiga harara ce ke rabani dasu

 Sai gashi yau akan banza band’aki, band’akin ma k’azami ana neman a ci  mani mutunci
Muryarsa ce ta dawo dani daga d’an  gajeran tunanin da na tafi “D’an matsa haka gefe wasu zasu shiga ko?” Ya fad’a tare da bangajeni har ina neman fad’uwa
Kamar na fasa shiga band’akin amma kuma sai na tuna ai alwalla bata ta6a tabbata alwalla sai anyi tsarki
Shiyasa na daure cikin sanyin jiki na dubesa” To Malam nawa ne kud’in shiga band’akin naka kuma?” 
“Idan fitsari zakiyi nera talatin, in kuma kashi zakiyi nera hamsin ne” 
Yar k’aramar jakata na zuge na zaro nera talatin na basa kana na wuce band’akin.
Har nagama sallar zuciyata a cunkushe nake jinta, jikina duk yayi sanyi narasa miyake yi min dad’i gani nan dai kawai nake jina saboda na tasani wulak’anci a rayuwata.
******
“Ina na Borno! Ina na Mai duguri? Ina na Borno! Ina na Mai duguri?”  Can na tsinkayi muryar wani karen mota lokacin da nake tukarar dandazon motocin da niyar  yin tambaya
Banyi wata wata ba na tunkari inda Mutumen yake tsaye “Ya! ‘Yan mata  Mai duguri zaki tafi ne?”
“Eh can zan tafi” Na fad’a a tak’aice, saboda na matsu na ganni a cikin motar  zaune
“To zagayo nan baya ki zauna dan anriga ankama gidan gaba” 
“Kai kadamu da gidan ga kona baya, nidai buk’atata bata wuce Allah ya saukemu lafiya ba” 
Saida na sunkuya zan shiga motar kana ya lura da goyon da ke bayana”Dan Allah Hajiya kiyi hak’uri fa idan maganata tayi maki zafi, ban lura bane”
Bance masa komai ba saima samun guri da nayi na zauna, bayan na zauna ne na sauke Hamza saboda zafi da ake rabkawa a garin
Banfi minti talatin da zama ba motar ta cika muka lula sai Mai duguri.
A zatona nisan da ke tsakanin Kano da Mai duguri baifi nisan da ke tsakanin Daura da Kano ba, amma ga mamakina sai naga sai zuk’a uwar tafiya akeyi amma har yanzu shuru banji ance ankusa isowa ba
Wata mata na dafa wacce ke kusa dani “Dan Allah baiwar Allah yaushe zamu isa Mai dugurin ne? naga har yanzu bamu iso ba wallahi har nagaji da zama” 
Murmushi tayi kana ta dubeni ” Ai sai dai nace maki ki k’ara gyara zama domin ko rabi ma bamuyi ba” 
Bance mata komai ba saima k’ara muskutawa da nayi na gyara zamana saboda d’ayan gefen nawa ya gaji sosai.
********
Muda muka baro Kano tun safe bamu muka iso Mai duguri ba sai wajejen bayan Magariba.
Koda naji wad’anda muke tare dasu suna cewa saura mintina mu iso nacewa Direban”Akwai na Minna Mai Mad’aci idan anzo”
“Ni kam dare yayi babu wata Minna Mai Mad’aci da zan wuce duk a tasha zan zubeku, sai dai idan munje tashar kya nemi Motar Minna Mai Mad’acin ” 
“Indai ana samun motar ai shikenan tazo gidan sauk’i” 
Ban dad’e da rufe bakina ba motarmu ta faka a tashar Mai duguri, duk mutane suka sassauka kowa ya kama gabanshi, nima ba’a barni a baya ba wajen bin jeren gwanon mutanenda ke saukowa, sai dai banbancin da ke tsakanina dasu su sunsan inda zasu nufa ni kuma bansan inda zan nufa ba.
Yanzuma saida na tsaya cikin tashar na siya mana abinci dani da Yarona mukaci muka k’oshi kana na zuba sauran a cikin leda saboda anjima, na nufi gurin motocin da ke jejjere ina neman motar Minna Mai Mad’aci, ban dad’e ina nema ba na dace, kuma babbar sa’ar da nataka motar a cike take dama mutum d’aya kawai ake jira.
Bamuyi tafiyar minti 40 lafiyayyu ba muka iso, ni a tsammanina ma sai mun kai safe muna tafiya saboda sunan garin da naji kamar zaiyi nisa
Waige-waige na farayi bayan na sauka a motar, inaga mai motar ya lura da  bansan ko ina bane shiyasa yana daga cikin motar yace mani “Ko dai *Gamborin Gala* kikeson zuwa ne? dan na ganki bakida kaya kamar mai niyar zuwa Sudan”
Karab nayi nace” Eh wallahi kuwa bawan Allah kamar ka sani” na k’ara da cewa”dama sai anje  Gamborin gala kana a isa Sudan d’in ne?”
“K’warai kuwa, dama baki ta6a zuwa bane?” 
“Wallahi ban ta6a zuwa ba wannan shine zuwana na farko” 
“Allah sarki! Yanzu dai kam maganar gaskiya bazaki samu motar Gamborin gala anan ba, sai dai ki kwana anan Mad’aci zuwa safe sai ki wuce…..

Kardai ku gaji da bina, domin nima bazan gaji da bin Murjanatu tiryan-tiryan ba har sai na gano maku k’arshen tafiyar tata yanda zata kasance

   *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                    6
                  NA
       MAMAN JA’AFAR

*K’wadage*
Duk inda akasan Murjanatu na zuwa babu inda ba’aje nemanta ba, kama daga gidan K’awaye Yan’uwa da Kuma abokan arziki

Har garurran da ke kusa dasu mafi kusa inda akasan tana zuwa dama inda bata zuwa d’in duk anje, irinsu Kwarare, Mai Mujiya, Mai Aduwa, dasu  Hirji babu inda basu lek’a dan neman Murjanatu ba, amma shuru kakeji wai Malam yaci shurwa
Ita ko Mahaifiyar Murjanatu duk inda taji labarin wani sabon Malami ko kuma sabon Boka sai taje gunsa neman taimako domin a samo mata labarin ‘yarta mace tilo guda d’aya wadda tafi soyuwa a cikin ranta wato Murjanatu amma har yanzu shuru ba labari, duk ta kame yan awakinta da tumakanta ta siyar ta kai masu kud’in, amma kullum magana d’aya sukeyi mata wato Murjanatu tana nan lafiya k’alau kuma kwanan nan zata dawo gida da kanta
Tun su Tsalha sunayi mata fad’a akan wannan ‘yan biye-biyen da takeyi har sun gaji sun rabu da ita sun zura mata ido, dayake sun lura batada niyar dainawa domin kullum sa ran ganin Murjanatun takeyi kamar yanda bokayen suka fad’a mata.
*Gidansu Haro*
Shima Haro tun k’arfinsa yake neman Murjanatu amma abin tamkar had’in baki da gidansu Murjanatun shima dai shuru har yanzu bai dace ba, duk yabi ya wani firgice ya fita hayyacinsa, abincima wannan ya manta rabon da ya sakashi a bakinsa, bare kuma azo kan maganar wanki da wanka, ada d’an gayu ne na gaske amma yanzu duk ya wani susuce ya fita hayyacinsa ya zama tamkar wani mahaukaci-mahaukaci.

****

Yauma dai kamar kullum, Haro ya fita neman Murjanatu kamar yanda ya saba ya gaji yayi lik’is amma bata ba labarinta. 

Akan hanyarsa ta dawowa ne ya had’u da Huwaila, bayan sun gaisa ne take k’ara jajanta masa 6atan Murjanatu 
“Oni! Murjanatu dai shuru har yanzu ko?”
“Wallahi Kuwa Huwaila har yanzu babu wani labari gamsasshe akanta, saifa rannan dana had’u da Iya Delu takeyi mani wani soki burutsunta, wai sadda zata siyar mata da kaya ko tace mata zamu tafi ci rani nida ita ko me? Ohon mata dai” 
D’aga kanta tayi sama kamar tana kallon wani abu alamar tunani, kana ta Jijjiga kai 
“Tabbas Haro Murjanatu guduwa tayi, domin nima kafin ta 6ata tazo gidana akan na ranta mata wasu kud’i wai zata tafi Sudan, danace matama bani dasu ne ta fita rai a 6ace amma ina kyautata zaton ba shakka hanyar Sudan d’in ta nufa….
*****
*Minna Mai Mad’aci*
K’ara nausawa nayi cikin garin, domin neman inda zan kwana kafin zuwa safe.
Garin babu laifi yanada d’an girma saidai dukda haka ba’a kirasa da birni ba, amma zan iya cewa ya wuce k’auye.
Dai dai k’ofar wani gida na tsaya, saida na gama shawarwari na da zuciyata kana kai tsaye na kutsa kaina cikin gidan tare da yin sallama (Azamanin baya fa nake nufi ba yanzu da boko haram ta tarwatsa Bornon gaba d’aya ba)

Bayan sun amsa mani cikin ladabi na duk’a na gaishesu

Matar gidan ce ta dubeni
 “Baiwar Allah kiyi hak’uri wallahi ban wayeki ba” 
Murmushi nayi kaina a k’asa ina rubutu akan yashin da ke baje a ko ina na gidan

 in ina na farayi kana daga bisani nace

“Dama Gamborin gala nakeso na tafi, to kuma sai akace mani dare yayi wai bazan sami mota ba sai gobe, to shine nace bara na shigo nan na nemi taimako kona samu gurin da zan kwanta kamin zuwa goben” 
“Allah sarki, sai dai gashi kin taki sa’a domin kina gani gidan namu d’aki biyu ne rak a ciki,  daga nawa nida mai gidana sai kuma wancan d’an k’aramin inda yara suke kwanciya, suma naji suna kukan wai d’akin yayi masu kad’an sai dai nan gaba idan Allah ya hore mana sai a gyara masu shi ad’an bud’a masu shi”
Ko bata k’ara ce mani komai ba nasan inda wannan dogon sharhin nata ya dosa 
Godiya nayi mata kana na mik’e da nufin tafiya jiki a sanyaye
Har na kosan kaiwa bakin k’ofa naji tace
“Idan kuma zaki iya kwana a Mad’aci ga yaro nan bara nasa ya rakaki”
“Ko hakanma nasamu ai naji dad’i wallahi, Hajiya nagode fa”
 “A’a daina saurin yimin godiya domin ba’a kyauta ake kwana can d’in ba kud’i ake biya” 
Take murnata ta koma ciki domin ban cika son fitar da kud’i ba a irin wannan lokacin, ala dole na 6oye damuwata 
“To badamuwa Hajiya yazo ya rakani Mad’acin nagode” na fad’a jiki a sanyaye 
Wani yare naji tayima yaron wanda nake kyautata zaton barbarci ne domin tun a mota nakejin wasu nayin irinsa
Mik’ewa yayi yai gaba ni kuma na rufa masa baya, bayan na yiwa matar godiyar k’arfin hali tare da yi mata sallama
Wani wargad’ed’en fili ya kaini wanda aka zagayeshi da zana gindin wata babbar bishiyar Mad’aci, nuna mani gurin yayi da yatsa kana ya juya ya tafi da gudu abinsa yana yan wak’e-wak’e.
 Dai dai k’ofar gurin nayi sallama dan banace gida ba, amma ga mamakina babu wanda ya amsa mani, na dad’e tsaye a gurin inata rabka  sallama amma shuru kakeji wai Malam yaci shurwa

Da dai naga shurun yayi sai na kutsa kaina aciki
Ikon Allah! Ashe mutanen na daga can nesa shiyasa bazasu iya  jiyoni ba, saboda mata da maza ne sunfi d’ari a gurin kuma ko wannensu harkar gabansa yakeyi
Sai da na matsa dab dasu kana suka jiyo sallamar tawa, wad’anda ke kusa dani na gaisar domin sunyi yawan da bazan iya  binsu d’aya bayan d’aya ina gaisar da su ba
“Baiwar Allah! baki bada kud’in haya ba kuma naga kin samu wuri kin rashe” cewar wata ‘yar dattijuwa kenan da ta zauna dab dani 
“Zan bayar Baba, bansan ko nawa ake biya ba ne shiyasa”
Murmushi tayi kana tace”Allah sarki, ai nazaci bakisan ana biya bane shiyasa nazo dan na fad’a maki” 
Nima Murmushin nayi  “Nawa ne ake biya Baaba?”
Yatsa ta saka abaki tare da d’aga k’anta sama alamar tunani, kana daga bisani ta dubeni “Kwana nawa kikeso kiyi ne?” 
Tambayar tata dariya ta bani, domin duk wani mutumin da yasan ciwon kansa bazaiso ya wuce kwana d’aya anan ba, kwana d’ayan ma sai dai inda babban laruri, domin duk girman filin nan, rabasa kawai akayi gida 2 6angaren dama na mata, yayinda 6angaren hagu ya kasance na maza, kuma duk girman wurin ban d’aki 2 ne rak a ciki
“Kwana d’aya ne kawai zanyi Iya, gobe insha Allah tun safe nakeso na wuce”
“Kud’inki d’ari biyu ne yarinya” 
Muskutawa nayi na zaro canjin d’ari biyun da na soke a cikin zanina canjin da mai abinci ta bani d’azu na mik’a mata

“Gashi Baba, nagode”

Cikin taron matan naga ta koma alamar kud’in wata ta kaiwa, kana ta dawo kusa dani ta zauna
“Yarinya kinyi sa’a kinzo da isassun kud’i har gashi zaki wuce abinki ki barmu anan dukda mun kwana 2”
Mamaki fal a fuskata na kalleta, domin na kasa sanin inda maganar tata ta dosa

“Baaba ban gane abinda kike nufi ba”
 “Ina nufin duk wannan taron namu da kika gani guzurinmu iya nan ya ajemu, a hankali a hankali muna d’an tab’a sana’a anan duk wanda kud’insa ya taru sai ya haura Gamborin gala daga can yayi gaba har iya inda kud’in nasa suka tsaya kuma”
Wata sabuwa kenan inji y’an caca, ashe wannan dalilin ne yasa aka d’ebi k’aton fili aka basu a matsayin  masauki, domin yawan nasu ko ince namu yayi yawanda baza’a iya saukarmu a cikin gidaje ba domin idan suka ce zasu saukemu zamu cika masu gari ne shiyasa sukayi mana dabara suka barmu anan cikin wannan wargad’ed’en filin marar fasali
Inko haka ne lallai na tabbata mai kud’i tunda gashi a kwana d’aya kawai zan wuce na k’ara gaba na barsu suyita kwamacalarsu anan
“Gaskiya Baaba kunyi k’okari” abinda na fad’a kenan bayan na dawo daga dogon tunanin da na tafi
Nan dai muka d’an ta6a fira da Baaba kana daga bisani kuma ta tashi ta canza guri, a tunanina taga bazata samu sisi a gurina bane duk kuwa da dogon labarin da ta bani nata shiyasa tayi shawarar canza shek’a.
Yau kam sai dai Allah ya yafe mani lodin sallolin da ke kaina wanda banyi ba, domin harga Allah bazan iya shiga band’akin da mutum sama da hamsin ke amfani da shi ba, ban shiga nagani ba amma dukda haka nasan bazan gansa yanda nakeso ba.
Kukan Hamza ne ya dawo dani daga duniyar tunaninda na lula, mutsuniya naga yanayi alamun kashi zaiyi
 “na shiga uku, yanzu ya zanyi?” na fad’a a fili
Hakanan badan naso ba na tashi na shiga cikin taron mutanen nan domin na nema masa Fo d’in da zai hau, sai dai abin k’azantar duk wanda na duba kashi ne jajja6e a jikinsa, da k’yar na samu wani mai d’an dama-dama na d’orasa, ko wadataccen ruwanda zan wanke masa kashin ban samu ba, hakanan na jajja6a masa muka dawo inda kayanmu suke

Abincin da na k’ulle mana a leda na d’auko ina basa, aiko kan k’ibtawa da bisimillah tuni yaran da ke wurin sunyi mana k’awanya kowane yana tand’ar baki alamun yunwa, a hannunsu na bisu ina d’odd’ora ma kowanne loma d’aya d’aya, amma ga mamakina abincin ya kusan k’arewa amma yaran basu da alamar k’arewa
Ledar abinci na naja gefe guda muka fara ci nida yarona, domin na lura idan na biye masu ba wan kuma ba k’anin za’ayi, ma’ana su basu k’oshi ba mu kuma sun barmu da yunwa
Inaji sunata koke-kokensu nayi banza dasu, mukaci muka k’oshi abinmu.
A daddafe nakai safe a gurin, ko sallama banyiwa kowa ba na kama gabana na nufi tasha domin hawa motar Gamborin gala.
Cikin sa’a kuwa nasamu motar batare da nasha wuya ba

Yauma dai tafiyar bata wasa bace domin sai yamma lik’is muka samu isowa Gamborin galar  dani da abokan tafiyata domin tafiyar ta yau bani kad’ai bace inada abokan tafiya 
Mota na ajiyemu tasha bamu zame ko ina ba sai gurin ‘yan canjin kud’i, domin daga nan babu inda zamu zame sai *Kusuri* Kusuri kuwa iyaka yake da *Chadi*  da Kuma Nigeria kamar yanda naji suna fad’a, kenan za’a iya kashe kud’in Nigeria kuma za’a iya kashe kud’in Chadi, a yandama naji abokan tafiyar tawa suna fad’a wai anfi kashe kud’in Chadi a Kusurin.
Gaba d’ayan kud’aden da ke hannunmu muka canzar sai d’an abinda ba’a rasa ba na sayen abinci, kana muka dawo masaukinmu irin dai wanda muka baro a Minna Mai Mad’aci, muna jiran garin Allah ya waye musan inda dare yayi mana…..
Ina fatan zakuyi mani afuwa na rashin jina da zakuyi kwana 2 sakamakon wani d’an uzuri daya taso mani, amma zuwa ko litinin ko talata insha Allahu zakujini. Ayi mani afuwa👏
    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: *Muhimmin sako*
_Ina mika godiya ta ta musamman ga dukkan masu bin littafina_ _*Idan kunne yaji*_ _Sannan kuma ina mai baku hakuri akan dan jinkirin da aka samu na kwana_2 _hakan ya samo asali ne na wani muhimmin uzuri da ya fado mani kamar dai yanda ya gabata, amma yanzu komai yayi normal insha Allahu zanci gaba da suburbudo maku_ _*Idan kunne yaji* a ko wace rana da misalin karfe 6 na safe_

_Nagode_
_*Muje zuwa Kusuri*_

🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                 7
                NA
    MAMAN JA’AFAR

Bamu dad’e da dawowa masaukinmu ba wasu mutane kusan su biyar suka shigo mana, munyi mamakin ganinsu matuk’a domin daga ganinsu ba irin kalarmu bane, domin su a k’oshe suke mulmul ba kamar mu ba, kuma ko a yanayin kayanda ke jikinsu ma zaka fahimci babu wata wahala a tattare dasu
Buk’ata sukayi da muduka mu maido hankalinmu garesu
Bayan sun tabbatar da mun mayar da hankalin namu garesu ne d’aya daga cikinsu wani bak’i kakkaura mai zungureren sank’o aka kamar za’ayi sunuka ya fara bayani
“D’azu da kukazo gurinmu yin canji munji wasu daga cikinku suna cewa Kusuri zasu tafi ko? to shine mukeso muyi jinga da wa’yanda zasu tafin, ku biyamu kud’in motar da zamu kaiku Kusurin mu kuma munada manyan motoci masu lafiya wa’yanda suke shiga kwazazza6ai da Kuma Sahara,  ko ya kuka ce?” Ya k’arasa maganar tasa da tambaya gami da kallonmu 
Kusan mu duka dake gurin muka amince da wannan shawarar tasu, domin ko ba komai sun fimu sanin hanya da Kuma matsalolin da ke tattare da hanyar

Dama hausawa suna cewa wai da d’an gari a kanci gari
Bayan sun tafi ne na hangi wata mata can gefe ko kuma nace yarinya, domin zan iya cewa sa’ata ce, saboda a yanda na fahimta shekarunmu ba zasu gaza d’aya ba
Sallama nayi mata bayan ta amsa ne na  samu gefenta na zauna 
“Dan Allah baiwar Allah duba mani wa’yan nan kud’in ki gani ko sun kai yawan wa’yanda na basu, naga kud’in kamar sunyi kad’an  tun d’azun nake jajanta abin a cikin raina” Na fad’a tare da zuge jakata na zaro mata ‘yan kud’ad’en da suka bani domin ta duba
Zaro ido tayi alamar tsorata fal atare da ita koko nace mamaki, kana kuma daga bisani ta daure ta nemo natsuwarta tace dani
 “Da na tsorata da ganin ‘yan kud’in naki kad’an, amma kuma da nayi d’an guntun tunani sai naga ba abin tsoro bane ko kuma mamaki  mai yiyuwa iya kud’in da kika basu kenan suma su suka canzar maki a haka, amma ke sadda suna nera kafin su zama *Saifa* nawa kika basu ke?” 
D’an shuru nayi Jim alamar tunani ” Inaga zasu kai dubu ashirin da biyar ko kumama su haura hakan, na k’ara da cewa 
Baiwar Allah! Ina fatan dai masu tula-tulan cikin can ba cutata sukayi ba?” Na fad’a jiki a sanyaye tamkar zanyi kuka
Dariya maganata ta bata

“Ai ‘Yar’uwa sai dai kar a kuma, domin wallahi sun cuceki iya cuta ma, saidai kawai Allah ya saka maki
Saboda idan da canjin tsakani da Allah zasuyi maki, to kud’in ki har gaba da *JAMMAINA* zasu kai ki, amma yanzu inma sunyi maki k’okari sai dai su a jeki a Jammaina d’in, inyaso sai ki yada zango anan ki nennema idan kuma Allah ya hore maki sai ki wuce gaba” 
Lokaci guda na shiga tashin hankali marar misaltuwa bansan lokacinda wani matsanancin kuka yazo mani ba “Shikenan! sun kasheni! na shiga uku ni Murjanatu na bani na lalace”

Sabbatu kawai nakeyi acikin kukan nawa da k’yar Hanne ta rarrasheni na daina kukan, amma ban daina ajiyar zuciya ba
“Ke Murjanatu kima godewa Allah daga Kusurin kinada kud’in wucewa Jammaina ni kuma da zan yada zango a Kusurin fa nace me? ki kwantar da hankalinki indai cuta ce babu wanda basu cuta ba anan gurin, saidai kawai taki cutar ta k’azanta, kodan banga ta sauran jama’ar bane?” Ta k’arashe maganar tata tana wani k’umshe dariya
Tamkar na mak’ureta ta mutu nakeji, amma dai ban nuna mata ba 
Jiki ba k’wari na koma inda na shinfid’e na kwanta

Raina ya 6aci matuk’a game da abin nan da ya faru, amma da nayi wani tunanin sai naji lokaci guda wani farin ciki ya maye wannan bak’in cikin da ya mamaye zuciyata yanzu yanzun
 Murmushi nayi mai fidda sauti kana a fili nace “Duk wannan wuyar da nake sha ba mai dawwama bace, nasan nanda ‘yan watanni kad’an komai zai zama tarihi, domin dana isa Sudan magana ta k’are, mafarki na na zama Mai kud’in garin K’wadage insha Allahu sai ya tabbata”
 Murmushin gamsuwa nayi gami da gyara kwanciyata
 Acikin baccin nawa nema nayi mafarkin wai na sayi manyan motoci na bayar ana yi mani haya dasu.

****

Gari na wayewa wad’annan masu canjin ko kuma ince macutan suka kawo motocinsu suka ar-aje a bakin masaukinmu, mutane sai turereniyar shiga akeyi, acikin gwarancin hausarsu suka dakatar damu”Kai! bayin Allah! ya baku bamu kud’i ba zaku cika mana mota da hayaniya?”
Sassaukowa mukayi, kana muka jejjera mukayi layi, layin maza daban kuma na mata daban
D’aya bayan d’aya suka bimu suna kakkar6ar kud’in motar mu, ko nace suna kar6ar abinda yayi masu, domin babu shakka abinda suke kar6a yafi k’arfin kud’in motarsu dukda da kuwa ba sanin garin nayi ba
Nima da a kazo kaina kud’in jakar tawa gaba d’aya ya kar6e, ya d’ebi iya son ransa kana ya bani sauran, na mayar dasu a jakata ina hawaye domin babu shakka nasan an yayeni sai dai kawai Allah ya jik’ana.
Saida suka gama kar6ar kud’in kana suka umarce mu da mu shisshiga motar, aiko zo kaga turereniya tamkar motar Sudan d’in ce aka ajiye akace kowa yazo ya shiga kyauta
Garin turereniyar tasu ma har saida suka buge mani kan Hamza, haka muka shiga motar yanata k’wala kuka abin tausayi, domin Hamza bazaka ta6a jin kukansa ba inba gagarumin abu ne ya faru agaresa ba

*****

Lallai Kusuri ba k’aramin nisa ne da ita ba, domin tun safe da muketa tsuga gudu har  gashi yanzu mangariba ta gabato amma masana hanyar har yanzu banji suna cewa mun kusa isowa ba
 Gashi kuma inda nayi raggon azanci ban rik’o mana komai ba saboda halin anka, domin ni a tsammanina garin ba wani nisan kirki ne dashi ba
Hamza kuwa da sauran yaran da iyayensu basu ruk’o masu komai ba inbaya ga kuka babu abinda sukeyi Suko masu motar munaji muna muna gani suke sunk’umar shayi da biredi amma ko tunanin suyi mana tayi basuyu ba, hakama wasu daga cikinmu wa’yanda suka taho da abinci ko kallo bamu ishesu ba, domin a yanda na fahimci abin nafsi-nafsi ne kowa ta kansa yakeyi.
Allah sarki Hamza dai yaga babu sarki sai Allah ya gaji da kukan nasa yayi shuru har bacci 6arawo ya kwasheshi 
Na tausaya masa matuk’a, amma ya na iya? wannan tafiyar itace sanadiyyar ingantuwar rayuwarmu dani dashima gaba d’aya
 Tausayinsa yaso ya kashe mani guiwa k’warai da gaske, amma dana lura  wannan tausayin babu inda zai kaini sai rayuwar talauci da k’uncin dana baro, tuni nayi fatali dashi naci gaba da kallon shantalelen titin da muke bi da kuma manya-manyan itatuwanda muke wucewa.

****

Bamu muka isa Kusuri ba sai wajejen k’arfe goma na dare, a lokacin k’afafuwana gaba d’aya ji nake tamkar bazasu iya d’aukata ba saboda tsananin gajiya, ga yunwa da k’ishirwa, domin tunda muka baro Gamborin gala babu abinda muka sakawa bakin salatin mu

Muna ji muna gani masu motar ke sank’amar abincinsu amma ko ruwanda zamu bawa yara hanamu sukayi.
 Banyi mamakin girman garin Kusuri ba domin dama naji masana hanyar suna cewa da zarar mun shigo Kusuri to mun fara shigowa K’asar *Chadi* kenan, ai kuwa maganar tasu haka take domin tun saukarmu a mota nake ganin mutanen garin wani bak’kk’irin sai kace gawayi, dama so dayawa idan ina jin labarin mutanen Chadi nakanji ana cewa wai bak’ak’e ne na buga misali, domin duk bak’in nan namu mu ‘yan Nigeria sun fimu bak’i nesa ba kusa ba.
 Acewar ma wani Baban Kakanmu wanda ya ta6a zuwa Chadin neman kud’i tun shekaru aru-aru da suka gabata, wai sai ka kusan zagaye K’asar Chadi gaba d’aya ba tare da kayi tozali da farin mutum ko k’waya d’aya ba koda kuwa jariri ne, dan ko jariransu a bak’ak’ensu suke zuwa duniya.
A Kusuri ma masauki muka samu dai dai wanda muka baro, ba yabo kuma ba fallasa, domin bazamu ce mun samesa yanda muke buk’ata ba, haka kuma ba zamuce mun raina ba, domin a yanayin da muke tamkar ank’watomun nan daga bakin kura  ko acikin kashi akace mu kwanta kwanciya zamuyi.
Wannan masaukinma saida muka biya kana aka barmu muka shiga, da shigarmu bamu tsaya wani 6ata lokaci ba musamman ma irina masu yara muka nemi masana garin da su taimaka su rakamu cikin gari domin neman abinda zamuci muda yara
Tun a gurin saida abincin na sauke Hamza na fara tura masa, amma ga mamakina yaron fafur yak’i kar6ar abincin, nayi-nayi amma yak’i ci, dana matsa masama kuka ya saka mani

Hankalina ya tashi matuk’a na rashin cin abincin Hamza domin koni dake babba tamkar ‘yan hanjina su tsinke nakeji bare kuma yaron goye, da acema wani babba ne sai nace ko fushi yayi, to amma anya lafiya kuwa kodai l….
“Yarinya! D’an naki kodai cikinsa yakeyi masa ciwo ne?” Cewar wata tsohuwa kenan abokiyar tafiyarmu wadda muka fito tare da ita neman abinci, kuam tana gefena tana lura da dukkan abinda yake wakana a tsakanina da Hamza
“Wallahi Iya ban sani ba, amma lafiya k’alau muka baro Gamborin gala da shi” Na fad’a cikin muryar kuka
“Kawo shi mu gani” Ta fad’a tare da mik’o hannu lokaci guda
Mik’a mata shi nayi a lokacinma har hawaye ya fara bin fuskata
Zare idanuwa naga tanayi harda tand’ar baki, ta gama ‘yan surkullenta ta mik’o mani shi 
Ina dubasa naga ko numfashi baya yi sai wata uwar kumfa dake fita ta baki ta hancinsa, bansan lokacin da nasaka kururuwa ina neman d’aukin jama’ar gurin ba…..
Anya kuwa wannan tsohuwar lafiya kalau take? Koma dai minene ni aganina Murjanatu ce sila, amma dai ku biyoni domin jin yanda wannan Chakwakiyar zata kasance
   *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                    8
                   NA
       MAMAN JA’AFAR

Kafin kace kwabo tuni duk mutanen da mukazo dasu sun kewaye mu kowa yana tofa albarkacin bakinsa, nikam sai faman Jijjiga Hamza nakeyi ina kuka nakasama furta komai, can wata mata ta iso inda muke muna cacar bakin
“Kai jama’a ku saurara! ya zaku dinga dukan taiki kuna barin jaki? tun d’azu nake can gefe ina kallon abinda yake faruwa, saboda haka Karku zargi kowa ku zargi wannan matar domin itace take nema ta lashe mata yaro” ta fad’a tare da nuna wannan tsohuwar data kar6i Hamza d’azu da yatsa
Ai kuwa nan take hankulla suka dawo gareta, wasu na ganin kamar sharri ne akayi mata, yayinda wasu kuma gani sukeyi tamkar zata iya aikatawa
“Irin tsofin nan masu jajayen idanuwa babu tantama komai ma zasu iya aikatawa” Cewar Hanne kenan wadda tun d’azu bakinta yak’i rufuwa sai faman surfa masifa takeyi
Itako tsohuwar da ake zargi banda kuka babu abinda taketa faman yi 
“Allah ya isa tsakanina daku azzalumai, daga taimako sai ku nemi ku k’ala mani sharrin maita? Wallahi har kabarinku na balbala da wuta bazan ta6a yafe maku ba”
“Ji nan Tsohuwa! ba maganar balbalar kabari da wuta akeyi ba kin gane? maganar lafiyar yaro akeyi, saboda haka tunda kince sharri akayi maki ai ga fili nan kuma ga mai doki sukuwa kawai ta rage”
Matar ta dubeni cikin fusata “Ke yarinya ajiye mata d’an a gabanta ta tsallakasa mu gani ko zai tashi, idan ko bai tashi ba Hmm wallahi duk tsufan nan naki ba raga maki zamuyi ba” ta fad’a tana mai cin d’amara da d’ankwalinta tare da kallon tohuwar
Da K’yar dai muka samu tsohuwar nan ta tsallakasa, sai gashi kuwa yaro ya tashi yayi k’ememe yanata wasa abinsa tamkar komai bai faru ba.
Itako tsohuwar can muka barota tare da matasan da muka fita tare dasu suna shawarwarin yanda zasuyi da ita, nidai koma me zasuyi mata can su suka sani tunda dai D’ana ya dawo lafiyarsa lau
Garin kwakin da nasiya can cikin gari da k’uli-k’uli na d’auko a cikin leda na fara bashi
Sai yanzu hankalina ya kwanta danaga yana ta cin abincin sa kamar da
 “Astagafurullah” na fad’a a fili a lokacin da tunanin salla ya fad’o mani a rai kenan
Yauma dai kam sai dai a biyoni bashi na had’a da sauran na baya nan gaba idan na samu natsuwa sai na ramasu duka, saboda maganar gaskiya shima wannan band’akin ba iya shigarsa zanyi ba, shiyasa ma d’azu da ina jin fitsari na zagaya can baya nayo abina, shima Hamza a can nayi masa ‘yan dabarun da na saba yi masa idan inaso yayi kashi ko fitsari nasamu yayi muka dawo masaukin namu
Bayan nasamu yayi bacci ne na koma can cikin gari inda ake sayar da garin kwaki na siyo mana mai yawa da nik’akken k’uli-k’uli domin mu ajiye saboda tafiyar gobe idan Allah ya kaimu.
*Hattara Yan’uwana mata*
So da yawa wani lokaci muna tabka babban kuskure na rashin d’aukar salla da mahimmanci a lokacin da muke cikin k’unci ko kuma wata damuwa, wasunmu idan har suna cikin wani yanayi na damuwa ko kuma na k’unci, sukan d’auka ne tamkar an sauke masu nauyin yin salla akansu ne har sai bayan matsalolin nasu sun kau.
Karmu manta Annabi (S.A.W) cewa yayi, mu tuna da Allah a lokacin da muke cikin farin ciki, shi kuma zai tuna damu a lokacin da muke cikin hali na k’unci da Kuma damuwa

Kenan kuwa idan hakane a lokacin da muke cikin k’unci ko damuwar ne ya kamata ace munfi tuna Allah saboda a wannan lokacin ne muke buk’atar d’aukinsa na gaugawa 
Karmu manta Allah (S.W.A) yana cewa Innas-salata tanha anil fasha’i wal munkar, wato ita salla tana hani ne da dukkan wani aikin alfasha da Kuma dukkan wasu  ayyukan abin k’i.
K’in yin salla a lokacin da muke cikin k’unci ko wata damuwa, wannan ba wata hujja bace da zamu tunkari Allah da ita, domin shi Allah babu ruwansa da wani k’uncin mu ko damuwarmu saboda ya bamu maganin dukkan matsalolinmu a cikin Alqur’ani mai girma
Inma mukayi tunani ai ibada ba k’aramin farin ciki take sakawa mutum a cikin rai ba musamman idan kayita dai dai kamar yanda Alqur’ani da hadisan Annabi (S.A.W)suka koyar. Wannan kenan.
*Muje zuwa Kusuri*

*****

 Yau kam nashari bacci iya bacci, inaga hakan ya samo asali ne saboda matsananciyar gajiyar da nake tattare da ita
Tun asuba naji abokan tafiyar tawa na tashina akan mu tashi mu tafi lokaci na k’urewa, domin tafiyar tamu ta yau kusan tafi ta kullum nisa
Ruwa na samu nad’an wawwanke jikina da Kuma fuskata (Tsaka tsami kenan) Shima Hamza na d’an jik’o tsumman na goggoge masa fuskarsa da Kuma jikinsa na goyasa na sa6i yar jakata mukayi haramar tafiya neman motar da zata kaimu Jammaina domin wad’annan masu tula-tulan cikin tun jiya suna ajiye mu suka d’au hanya suka juya abinsu.
Kusan mu goma muka fita neman motar, yayinda muka bar mata kusan su 7 a wannan masaukin suna jiran gawon shanu saboda su iya nan kud’in nasu suka k’are sai sun tsaya sun nennema kana su haura Jammainan nan gaba
Allah sarki banso na baro Hanne a wannan gurin ba sai dai ba yanda na iya ne domin nima bansan iya inda kud’in nawa zasu ajiyeni ba dana ranta mata.
To nanfa ake yinta wajen shiga mota, domin fafur masu motar nan k’in d’aukata sukayi wai a cewarsu kud’in da ke hannuna ko rabin na motar ma basuyi ba
Kuka naketa faman rabsawa wiwi tamkar raina zai fita, domin harga Allah wannan garin na Kusuri ba garin zamana bane saboda tun jiya da mukazo har kawowa yau banyi tozali da wani abincin kirki ba sai garin kwaki da Kuma k’uli-k’uli 
Shima Hamza dayaga na fad’i k’asa sai faman birgima nakeyi ina kuka, a firgice ya rarrafo inda nake ya cukuikuyeni gagam shima yana rabsa nasa kukan
Inaga Hamzan ne yabawa masu motar tausayi har sukace natashi na shigo motar mu tafi
Ina murzar ido gami da fyace majina na shiga motar na zauna, yayinda matanda ke ciki ko kallon tsiya basu isheni ba, saboda ai suna gani naketa faman birgima a k’asa Amma babu ko gezau babu wacce tayi tunanin ta taimaka mani sai masu motar da ko hanyar K’asarmu basu sani ba sukaga Allah sukaga Annabi suka taimaka mani na shigo
“Ke Malama! yazaki tsaya kinata wani harararmu sai kace munyi maki laifi?” Cewar wata mai dogon baki kenan wacce muka zauna dab da juna 
Dariya naga sun kwashe da ita su duka, kana wata daga can gefe tace”Kuka sani ko haushin mu takeji dan bamu cika mata kud’in mota ba?”
Nanma dariyar suka k’ara kwashewa da ita “Wanda yayi maki cikin shege har iyayenki suka kasa zama dake suka kore ki kika nufo hanyar Sudan shi zaki tsaya kina harara bamu da muka had’u a hanya ba, kujini da yarinya! ai bamu muka kashe zomon ba rataya aka bamu” Cewar wata kenan wadda ke zaune a tsakiya bata samu zama a akan kujera ba saboda uwar k’ibarda ke gareta, dayake motar irin bud’dd’iyar nan ce
Bansan lokacin da wani matsanancin kuka yazo mani ba, domin tunda na d’auko wannan hanyar raina yake 6aci amma ban ta6a cin karo da mummunan 6acin rai ba irin na yau, wai yau ni Murjanatu ni ake shegantawa D’a kawai dan na fito neman kud’i? Kai! wani lokaci kud’i ma basuyi ba wallahi
“Haba bayin Allah! Ya zaku tasa yarinya k’arama a gaba kunata faman yi mata suruttai sai kace baku ta6a haihuwa ba? Ai shi Kare idan baka basa abinda zaici ba, bai kuma kamata ace ka koresa ba.

Ni a ganina mu duka Allah ne ya had’amu anan, kuma mai yiyuwa ma daga K’asa d’aya muka fito Nigeria ko Nijar, kunga ko in haka ne ai kamata yayi mu had’a kanmu karmu ware kowa a cikinmu, muzama tsintsiya mad’aurin ki d’aya” Fadar  wata mata kenan mai zubin Malamai-malamai wacce ga dukkan alamu  zatayi sa’a da Innata
Shuru naga sunyi alamun maganar matar tad’an shiga jikinsu.
*****
Tun safe muketa tsuga tafiya babu kakkautawa, dama da yake dagamu har masu motar ba salla ce ta damemu ba, sai dai duk wanda yaji yunwa a cikinmu ya d’auko garin kwakinsa ya murza ya sank’ama yasha ruwa, wannan dalilin nema yasa ko salla ba tsayawa yi mkeyi ba, duk wandama yace a tsaya ayi salla haushinsa akeji.
Dab da sallar asuba muka samu isowa garin Jammaina….
Ku biyoni Jammaina domin jin wainar da za’a toya a cikin garin
    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

         Jiki ya tsira
                  9

                NA

   MAMAN JA’AFAR

Jammaina babban gari ne ba laifi, domin duk yafi sauran garuruwanda muke yada zango girma, sai yanzu ne muka tabbatar da mun shigo K’asar Chadi tsundum, jama’a gasunan ko ina birjik sai hidimomin gabansu sukeyi

Kuma abin mamaki duk wannan ayarin da mukayo kowannenmu kayansa aka wasunmu ma harda goyon yara da Kuma ‘yan k’ananun da ake rik’e da hannunsu, amma abin mamakin ko kallo bamu ishi mutanen garin ba, inaga hakan ya samo asali ne na yawan ganin irinmu da sukeyi akai-akai ba kakkautawa
Gindin wata bishiyar darbejiyar muka zauna muna hutawa
“Ke yarinya! wama kike da suna?” Cewar wannan matar kenan wadda ta shigar mani fad’a sadda muna mota
Murmushin ankulani nayi kana nace “Murjanatu”
“Yauwa Murjanatu, Kinga ga wata rumfa can kin hangota?” Ta fad’a tare da nuna mani rumfar da hannu
“Eh na ganta” 
“To dan Allah jeki ki duba koda bahaushe a cikinsu, idan Kinga da akwai, to ki tambayo mana shi inda *Zangon D’an Daura* yake idan kin gane kwatancen sai kizo ki fad’a mana
Ai kuwa na taki sa’a domin bayan yan Chadin da ke zazzaune a rumfar akwai wani bahaushe k’waya d’aya a cikinsu
Sallama nayi masu suka amsa kana duk suka zuro mani na Mujiya
Ba-haushen cikin su na duba d’auke da murmushi a fuskata nace”Dan Allah Malam tambaya nakeyi?”
“Allah yasa na sani baiwar Allah”
“Dan Allah Zangon dan daura nake nema nida Yan’uwana gasu can zaune” Na fad’a tare da nuna masa inda Yan’uwan nawa suke
“Ai kun kusanma zuwa *Zangon* yarinya, hala bak’i ne ku a garin?”
A tak’aice na amsa masa da “Eh” saboda na lura tunda nazo rumfar yake wani washe mani baki sai kace gonar auduga, kodan yaga ban goyo Hamza bane yazaci budurwa ceni? Ohon masa
“Kinga nan, Kina kallo?”
“Eh”
“Idan kuka mik’e shantal, to akwai kwana hannun dama dana hagu to ta daman zaku shiga, da kunyi tafiya kad’an sai Zangon dan daura”
Godiya nayi masa kana na juya na tafi domin sanarwa abokan tafiyar tawa kwatancen.

******

Zangon babban guri ne kusan Unguwa guda, ko kuma nace gari guda, domin zai kai kusan girman Kusuri saboda a yanda naji labari wai har wani Sarki suke dashi a gurin  waishi Sarkin Zango.
Wani wawakeken fili ne aka d’iba akayi d’akunan Shimomi birjik a ciki, dan banace gidaje ba tunda nidai iya kallona banga gida ko d’aya ba a Unguwar sai wa’yan nan d’akuna na Ledoji ko buhunna da aka yiyyi a gurin, a kullum kuma ana k’ara yawan d’akunan saboda k’aruwar yawan bak’i da ake samu a gurin a koda yaushe kuma a kowane lokaci
Ajiyar zuciya nayi bayan na k’arewa mutanen kallo, a zuciyata nace lallai Sudan tana kwasar tarkace da yawa, to nanma na samesa a cike inaga kuma uwa uba Sudan d’in?
Gurin Sarkin Zangon aka fara kaimu domin mu gabatar da kanmu, koko nace domin yasan da zamanmu.
Zaune yake acikin d’aya daga cikin d’akunan Shemomin, mutumin bak’i ne dogo kakkaura mai gashin baki buzu-buzu sai kace Bayahude
“Sannunku da zuwa bak’i” 

Abinda ya fad’a kenan cikin tak’ama bayan mun gama gaisar dashi ya amsa
Mu duka muka amsa da”Yauwa ranka ya dad’e” kai a sunkuye
Gyaran murya yayi kana ya sake dubanmu karo na ba adadi”Mutum nawa ne zasu zauna anan su nemi kud’i kuma mutum nawa ne zasu wuce gobe?”
“Mu 6 ne zamu wuce gobe idan Allah ya kaimu” ta k’ara da cewa “su kuma wa’yannan anan zamu barsu har sai Allah ya hore masu sai suyi gaba suma” ta k’arashe maganar tata da nuna masa inda muke
“To kuda zaku tafi gobe, kud’in hayarku dala hamsin-hamsin ne (Ina nufin dalar nijar ba dalar Amurka ba) ku kuma da zaku zauna duk wata jaka hud’u ake biya ina fatan kun fahimceni?” Ya fad’a tare da kallonmu
Gyad’a kai mukayi alamar gamsuwa da bayanin nasa, nan take naga duk sun fiddo kud’adensu sun bayar, ni kad’ai ya rage ban bayar ba sai faman muzurai naketa ina rarraba idanuwa a tsakaninsu
“Kefa yarinya ina naki kud’in naga bakida niyar motsawa?”
Sunkuyar da kaina nayi k’asa domin bansan amsar da zan iya bashi ba
“Na fahimci dai baki da kud’i koba haka ba?”
Gyad’a kai nayi alamar amsawa
“To babu matsala, kya iya zama anan d’in har zuwa lokacin da zaki samu sai ki bayar, ammafa idan kin tashi bayarwa dala d’ari zaki bayar saboda alfarmar da akayi maki na sai kin samu, wannan adalci ne nayi maki ammafa idan hakan yayi maki,  kin amince koko hakan baiyi maki ba?”
A zuciyata nace ko jaka d’ari kace na biya Malam mai gashin baki ai biya zanyi tunda dai na riga na baro inda nakeda gata
“Kodai bakiji abinda nace bane” ya daka mun tsawa
“Naji ranka ya dad’e insha Allahu idan na samu d’in zan biya hakan” 
“Kai Musah jeka ka nuna masu d’akunan da yakamata su zauna” Ka wani tasani a gaba kana kallo sai kace kasamu tibi” Ya fad’a tare da kallon wani gurgu wanda ke zaune a kusa dashi yana yi masa fifita
Sumui-sumui muka bi bayan wannan gurgun, yana rarrafe mu kuma muna binsa a baya
“Oni Murjanatu! yanzu shima wannan d’in Sudan yakeso ya tafi ko kuwa dai iya karsa nan Jammaina? lallai Sudan tana kwasar yayi da yawa
Ina can ina zancen zucina ashema har mun iso masaukin namu ban sani ba
Ko wannenmu shima guda-guda aka basa

Ba wani girman azo agani shemar take dashi ba, iyakar girman filin tsakar d’akin shine inda zaka shinfid’a hak’ark’arinka da Kuma inda zaka ajiye kayanka idan kanadasu
Zanina na shinfid’a mana a ciki, dama zannuwan nawa guda 2 ne idan wannan yayi datti sai na saka wannan na wanke wancen, sune na sakawata kuma sune na shinfid’a ta, sai d’an bargon Hamza da muke lullu6a da shi idan muna jin sanyi
Band’aki na fara shiga domin naga yanayinsa, tunda wannan band’akin dai dolena na shigesa tunda bansan iya zaman da zanyi a wannan Zangon ba
Da sauki-sauki wai kibiya a ido, ya daifi sauran amma shima ba wata tsabtar ne dashi ba, sauk’inta ma ba band’aki d’aya bane sunada yawa a gurin, inaga hakan ya samo asali ne na daga yawan mutanenda suke yada zango a nan d’in
Wanka nayi kana nayiwa Hamza na d’aukosa muka dawo rumfarmu dan bana kira gurin da d’aki ba.
Saida mukaci garin kwakin mu mukayi hani’an kana muka sheme sai baccin gajiya.
*****

 “Assalamu alaikum” Shuru babu wanda ya amsa mani a cikin gidan, dukda haka dai ban daddara ba na k’ara cewa
“Fi qasil au dugu-dugu” (Kuna buk’atar mai yi maku wanki ko kuma dakau)
Rayuwa kenan! idan bakayi sharar masallaci ba sai kayi ta kasuwa batare daka ankara ba. Amma inji Maman Ja’afar
“Aywa” Fi dugu-dugu, dakkal” (Eh munada dakau shigo) Wata matashiyar mata ta amsa mani daga ciki, dukda ban fahimci abinda take fad’a ba amma na fahimci tana nufin tanada dakau d’in ne, saboda turmi danaga ta k’ara gyarama zama ta saka ta6arya a cikinsa
Shiga nayi na sauke Hamza dake goye a bayana na zaunar dashi a k’ark’ashin wata bishiyar mangwaro dake gidan, naja d’amara da hijabina ina jiran ta bani abinda zan daka matan nafara aikina
A al’adar garin Jammaina dama bak’i wad’anda hanya ta biyo dasu har suka yada zango a wanann garin basu da aikin da ya wuce su dinga bin gidajen yan garin suna yi masu wankau, ko dakau, ko kuma wasu ayyukan gida wa’yanda ba’a rasa ba, idan sun gama sai a biyasu su k’ara gaba, idan kuma basu samu a gidaje ba sukan bi kasuwanni domin neman aikinda ya dace dasu, to a irin haka ne itama Murjanatu ta fito domin neman nata rabon. 

Wannan kenan.
Wani kalar gishiri ne marar nik’a mai kama da duwatsu-duwatsu matar ta ajiye mani a gabana da nufin shi zan daka mata
Na tsorata k’warai da gaske da ganin irin dakan da nafara cin karo dashi, amma ya na iya? wannan ita kad’ai ce hanyar da zata iya sadani da Sudan dolena nayi
 Daka naketa famanyi ina sharce zufa, itako babu ruwanta hankalinta kwance sai faman wasa takeyi ita da yaranta a tsakar gida
Nafi awa guda ina dakan gishirin nan kana na samu ya daku

Can gun Hamza naje na zauna ina maida numfashi sama-sama saboda tsabar gajiya da nayi
A cikin yaren kurame takeyi mani sannu, saboda nidai ba jin yaren Chadin nakeyi ba bare kuma larabci da naji wasunsu suna d’an ta6awa kad’an kad’an, in baya ga Dugu-dugu da Qasil babu abinda na iya fad’a, shima wannan d’in koya mani akayi saida nasha fama kafin na hardace shi.
Shinkafa da jar miya matar ta kawo mani mai rai da lafiya, kuma ta had’o mani da ruwa mai sanyi hadda so6o
Bansan lokacin da dariyar farin ciki ta su6uce mani ba, domin rabona da kalar wannan abincin har na manta
Murnarda matar taga inayi ne yasa na bata tausayi, ina lura da ita ta gefen idona har wani k’walla naga tana gogewa
Bayan munci abincinmu mun k’oshi ne na ware hijabina nasaka domin nufar wani gidan kuma nagani ko za’a dace

Dala ashirin matar ta bani na kar6a nayi godiya na k’ara gaba
A ranar kusan aikatau d’in gida hud’u nayi na nufo gida ko nace masaukinmu da nufin hutawa
“Ke zo nan” Naji an fad’a cikin tsawa  daga bayana, juyawar nan da zanyi saiko mukayi ido hud’u da Sani K’aranbotuwa ma’ana Sarkin Zango
“Zo ki biya bashi ko yan mata? ko kina nufin bana lura da motsin dukkan wanda yake cikin gidan nan ne?”
Muje zuwa domin labari yanzu aka fara

  *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          jiki ya tsira
                 10
                 NA
     MAMAN JA’AFAR

“Barka da hutawa ranka ya dad’e” na fad’a tare da tsugunawa gefensa alamun ladabi
“Mik’o mani” Ya fad’a cikin nuna isa da Kuma gadara
Cikin alamu na rashin fahimta nace “me zan kawo ranka ya dad’e ?”
Wata uwar harara ya daka mani kana yace”Kinada abinda zaki bani ne wanda ya wuce kud’ina da nake binki?”
Jikina na kyarma na zaro dala tamanin d’in da nasamo a yawon aikatau d’inda na fita na mik’a masa
Amma saboda rashin  tausayi da Kuma imani irin nasa ya k’wace kud’in nan ina ji ina gani batare da yayi tunanin bani ko sisi a ciki ba
“Miye kuma kikayi wani tsaya kina kallona? ko sauran dala ashirin d’in ne zaki ciko mani? kinsan dai ai ba dala tamanin mukayi dake ba ko?” Ya fad’a yayinda yake tura kud’in a cikin aljihun tsohuwar babbar rigarsa
Kasa cemasa komai nayi, saima godiya danayi masa na k’ara gaba abina.
A ranar haka na kwana jiki a sanyaye, zuciya a cunkushe, narasa miyake yi mindad’i, shin nadama ce ko  kuwa gani nan dai nima ban sani kome ke damuna ba
*Washe gari*
Tun safe na gama kimtsawa domin yau ba cikin gari zan nufa ba, aikatau d’in kasuwa zan tafi domin naji ance an d’an fi samun kud’i a kasuwar, sai dai ba’a samun abinci kamar aikin gidaje.
Gun Habiba na nufa domin na lura duk cikin wa’yanda mukazo tare dasu tafi d’an sakar mani fuska(Mai zubin Malamai ta cikin mota)
“Baaba mu mun nufi kasuwafa ayi mana addu’a Allah yasa mu samo da yawa” 
Murmushi tayi kana da mamaki ta dubeni
“Kikace mani Sani K’aranbotuwa ya kar6e kud’in naki duka, to kuma idan haka ne ina zaki samu kud’in da zakiyi hayar turmi a kasuwa naji kina cewa aikatau din kasuwa zaki tafi?”
Saifa yanzu na tuna ashe haka nan nake (0)na, fankan-fayau kenan
Murmushi nayi kana nace”Baaba ko kinada d’an wani abu a gunki ki ranta mani kafin nadawo sai na baki?”
Dala goma ta d’auko ta mik’a mani tare da yi mani a addu’ar a dawo lafiya.
Ba kasuwar na nufa ba kai tsaye, saida na fara biyawa gidaje na d’anyi wankau d’ina kana na nufi kasuwar, saboda na gaji da zaman Jammaina d’in nan na matsu na tara kud’i domin na k’ara gaba ko a gaban nad’an huta.
Dakau d’in kasuwa yazo mani a baibai ba yanda na tsammata ba, saboda wani uban dakan ku6ewa ne na fara cin karo dashi kusan kwano biyar
Har kusan yamma nakai ina wannan aikin guda d’aya, ga zafin rana kuma ya had’u da zafin yunwa, danma Alhamdulillahi ina d’an samun ruwa ina korawa a mak’oshina
Kafin na gama wannan dakan saida duk hannuwana sukayi kanta sukayi ruwa suka farfashe saboda tsabar wahala da kuma rashin sabo.
Tun hannuwana suna zafi idan ina daka saboda kantar da ke hannuna har suka gaji suka daina, domin ko na zauna hutun jaki ne zanyi da kaya bisa kai.
Cikin watannin da basu gaza biyar ba dani da Hamza duk mun rame, mun jeme mun fita hayyacinmu, wani lokaci idan na kalli yanda Hamza ya rame duk awazunsa sun fito waje, k’afafuwa duk sun zama sirara tamkar wani mai shan inna, babu wani abu mai d’an kumari a jikinsa sai k’aton kai, nan take sai na fashe da kuka hankalina ya tashi, amma ya na iya tunda na riga na baro gida
Amma dukda wannan azabar fa da nake sha ban ta6a yin dana sanin biyowa wanann hanyar ba, saboda hausawa da naji suna cewa wai Bayan wuya sai dad’i.
*BAYAN WATA 6*
Alhamdulillahi bayan duk uwar wahalar da nasha yau gashi da ikon Allah na kammala kud’i na jaka goma sha d’aya cas wa’yanda zan haura dasu *GARIN ABASHA*
Allah sarki sabo turken wawa, ranar da zan tafi munsha kukan rabuwa da wa’yanda muka d’an saba dasu a wannan Zangon
Inda damuwar tawa ma ta d’anyi sauk’i da Baaba Habiba zamu wuce garin Abashan.
_GARIN ABASHA_
Babban gari ne tamkar dai Jammaina, kuma duk irin aikatau d’in da masu yada zango  sukeyi a Jammaina a Abasha ma irinshi akeyi babu banbanci
Mun zauna a Abasha na kusan tsawon wata biyar muna aikatau ba dare ba rana har Allah ya taimaka mana muka samu damar haurawa garin _TIYNA_ 

Ammafa ba mu duka ba, domin mun baro mutane da dama a can wad’anda kud’in su basu isa haurowa Tiyna ba
 *K’auyen K’wadage*
Cikin matsanancin 6acin rai marar misaltuwa Haro ya shigo gidan nasu
“Iya! Iya! kina ina ne wai?” 
A d’imauce ta fito daga band’akin duk da bata k’arasa yin abinda ya kaita band’akin ba
Na lura da hakan ne sakamakom fitsari da nagani yana bin k’afafuwanta shar-shar
“Haro lafiya, me ya faru? kaddai gawar Murjanatun aka gani?” Duk a birkice take fad’an wa’yannan kalaman ganin yanda hawaye ke bin idanuwan d’an nata
Dak’yar Haro ya tattaro natsuwarsa guri guda , kana ya dubi mahaifiyar
“Iya wai ashe Murjanatu Sudan ta tafi ta K’afa ta mayar damu mahaukata sai faman nemanta mukeyi?” 
Sallallami tsohuwar ta fara gami da ta6a hannaye alamun mamaki da tsoro k’arara a fuskarta
“Amma kau indai da gaske haka Murjanatu tayi gaskiya bata kyauta mana ba, ko kuma nace bata kyautawa kanta ba, ashe son kud’in Murjanatu har yakai ga haka? kai D’an yau ma abin tsoro ne wallahi”
Samun kujera tayi yar tsugunno ta zauna ta k’ara dubansa gami da cewa
“Yanzu kai D’an nan waya baka wannan labarin?”
Yana share hawaye da ha6ar rigarsa tamkar wani d’an k’aramin yaro yace
“Wallahi Iya wannan K’awar tata Huwaila ce ta fad’a man, kuma kinsan yadda suke ba zatayi mata k’arya ba”
Ajiyar zuciya yayi gami da jijjiga kai 

“Wallahi Iya har birni nasake komawa Assibiti Macuware inda ake ar-aje gawar-wakin mutane naje na dudduba a zuwan ko Allah zaisa naga ko gawarta ne, ashe ita tasan inda take ta barmu nan munata wahalar banza”
Gyara zamanta tayi kana ta fuskanceshi 

“Haro kaine har yanzu baka gama sanin halin Murjanatu ba, nida nake zaune da ita a cikin gidan nan ni nasan tsiyar da take tsulawa, bana fad’a maka ne kawai saboda a matsayina na babba bai kamata ace inata gutsiri tsoma ba, amma kome akace mani Murjanatu tayi tabbas bazan musa ba”
“To yanzu Iya ya kike ganin za’ayi?” Ya fad’a a tak’aice
“Me kuwa za’ayi wanda ya wuce hak’uri har muga abinda Allah zaiyi? Yanzu dai kaje ka gaggauta sanar da iyayen nata domin suma su san halinda ake ciki hankalinsu ya kwanta, dan nasan sunma fimu shiga tashin hankali”
“To iya bara na tafi can d’in”
Mik’ewa yayi ya shiga can sashin su jiki a sanyaye
“A’a Haro! kaida zaka nufi hanyar k’ofar gida mi kuma zakayi anan? kaddai ka fara zautuwa tun yanzu?”
“A’a Iya ina sane, takarda ce zan d’auko na rubuta mata saki na bayar gidansu a ajiye mata koda sadda zata dawo bana gari, dan nima inaga kwanan nan nakeso nafara bin Shamsu Legas inda yake sana’ar kai shanu mu fara kasuwancin tare kamar yanda ya buk’ata tun tuni”
Kallon mamaki ta bishi dashi, domin a yanda Haro yake tsananin kaunar Murjanatu bata ta6a tsammanin zai iya sakin Murjanatun ba kome kuwa akace tayi masa
Amma dukda hakan tayi alk’awarin bazata ta6a bari Haro ya aikata wannan kasassa6ar da yake shirin aikatawa ba
 Abinda ta fad’a kenan a cikin ranta, kana ta tashi ta nufi band’aki domin ta wawwanke jikinta inda fitsari ya 6ata mata d’azu…Wannan kenan.
*Muje zuwa Tiyna*
Can cikin daji na hango wata kamar Murjanatu janye da yaro d’an kimanin shekara biyu da rabi a hannunta tana tsittsinkar itatuwanTunfafiya  tana da’dd’aurewa tana ajiyewa a gefe guda…..
Oni🤔Maman Ja’afar cikin raina nace su Murjanatu kuma haka abin ya k’ara ta6ar6arewa?
Kuzo muje Tiyna domin mu tabbatarwa idanuwanmu irin wainar da ake toyawa a can
Amma duk wacce batayi mani sannu yayinda nayi posting bazanyi wannan tafiyar da ita ba, domin bazata k’ara ganin posting d’ina ba saidai ta tsinci Murjanatu can a wani group din

Typing da wahalafa😭

    *NICE TAKU*

*MAMANJA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          jiki ya tsira 
                  11
                  NA
      MAMAN JA’AFAR

*Garin Tiyna*
Murjanatu ce na hango acan cikin daji koko nace a can wajen gari, taci uwar d’amara da tsohon hijabinta wanda tun barowarta K’auyen K’wadage bata sake d’inka wani sabo ba, shi d’in dai shine tamkar na gado
Zaunar da Hamza tayi a k’ark’ashin inuwar wata bishiya, yayinda ita kuma ta dage sai faman tsinkar itatuwan tunfafiya takeyi, idan sun taru dai dai misali saita had’a ta d’aure su da igiya ta ajiyesu a gefe guda, a haka har naga ta tara d’auri kusan  hud’u, yanzu take k’okarin had’a d’auri na biyar, amma a yanda na lura kamar ta gaji sosai, na fahimci hakane ta yawan goge zufa danaga tanayi.
Bayan ta gama da’dd’aure itacen ne naga ta had’asu guri guda ta dauresu duka ta d’orasu aka
Kamar nace mata tayi mantuwa bata warware hijabin da ta d’aure k’ugun nata dashi ta saka ba, sai kuma nayi wani tunani nace bara na barta na gani ko a haka zata ratsa ta cikin garin babu lullu6i
Ai kuwa haka akayi, domin ko tunanin saka hijabinma batayi ba ta kama hanya abinta
“Hamza d’auko mani sauran igiyar can ka biyoni da ita kaji ”
“To Ijja” (Wai shi Murja yakeson cewa)
Buge masa baki tayi kana ta kama kunnen

“daga yau  Idan na k’ara jin ka kira sunana kai tsaye sai naci gwahor ubanka mi kunnen k’ashi kawai”
Kukan da naga yanayi yi ne ya bani tausayi, domin a zahirin gaskiya a halinda muke ciki yanzu nafi tausaya masama akan ni kaina.
Da shigowata cikin gari bansha wata wahala ba gurin sayar da iccen da nayo, domin dama a inda muka yada zango akwai masu yin tuwo-tuwo a cikinmu, shiyasa kai tsaye idan nayo icce su nake kaiwa su siya suka cake mani kud’ina na adana
A kud’in da suka bani ne na saya mana tuwo nida Hamza sauran kuma na ajiye domin fara tara kud’in da zan haura gaba
Bayan munci mun k’oshi ne na rama sallolin da ake bina sai kuma mukayi haramar tafiya bara a bakin danja
 A bakin titi muke zuwa yin barar daidai danja (gurin bada hannu) duk mai motar da yayi niya sai ya mik’o mana abinda ya sauwak’a.
Nayi nisa a cikin barar tawa naga wani mutum a zaune can gefen titin saman wani dakali ya saka kaya irin na hukuma yana d’aga mani hannu
Da gudu na k’arasa gurinsa domin tunda naga yana d’aga mani hannu nasan babbar sadaka ce zan samu
“Amshiyy” abinda ya fad’a kenan, kuma abin mamaki bai daina d’aga hannun ba
Da hanzarina na mik’a masa hannu alamar ya mik’o mani
“Amshiyy” Ya k’ara maimaitawa 
Ni kuma ban daina mik’a masa hannun ba 
Can daga nesa na hango  wani bahaushe sai 6a66aka dariya yakeyi, ashe ya lura da dukkan abinda ke faruwa a tsakaninmu
Tasowa yayi ya k’araso inda muke

Cikin dariyar yake ce mani
“Cemakifa yakeyi ki tafi daga nan, amma ke sai faman mik’a masa hannu kikeyi”
Cikin marairaicewar murya nace “Wallahi ina can tsallake naga yanata faman d’ago mani hannu, kuma da nazo yace mani Amshiyy, badan yace mani Amshiyy ba aida bazan mik’a masa hannu ba
“To ai baiwar Allah abinda Amshiyy yake nufi shine tafi”
Cikin harshen larabci naji yana yiwa wannan mutumin bayani yana basa hak’uri

Shima mutumin dariya naga yanata faman yi
Da haushi ya kamani ko K’ara kallonsu banyi ba nayi gaba abina na barsu nan sunata faman tuntsira dariyarsu sai kace wasu mahaukata.
Yanzunma a gajiye na dawo gida koko nace masauki, wanka mukaje mukayo kana muka ci abinda muka dawo dashi muka shiga cikin jama’a domin ta6a yar fira saboda d’ebe kewa.
“Aikuwa Murjanatu d’azu da baki nan wata mata tazo nan Zangon wai tana neman wa’yanda zasuyi mata Barema (Masu yin noma a biyasu) har wasu sukace zasu iya, nidai kam bazan iya ba amma nace idan kin dawo zan fad’a maki ko zaki iya tunda na lura kinada k’okarin nema”
Baaba Habiba ce mai fad’ar wanann maganar bayan na zauna a kusa da ita
“Gaskiya ban iya Noma ba Baaba Habiba saboda tunda nake a duniya ban ta6a yinsa ba”
“Amma kuma Murjanatu naga kinada k’okarin nema, mizai hana ki gwada ki gani ko zaki iya, saboda naji abinda zasu biya d’in yanada d’an afki-afki, nima badan banida lafiyar k’irji ba aida dana za’ayi”
Nan take yawuna ya tsinke dayake naji labarin kud’i masu tsoka
“Kin gane Baaba Habiba? Kawai ma zan iya, yaushe zasuzo mu tafi sukace?” 
Can wata mata dake gefe tana tsintar shinkafa naji tace “Yanzu ke inbaya ga rigima irin taki yanda kike langai-langai d’in nan ina zaki iya yin wani Noma inbaya ga shegen son kud’i irin naki”
“Alanqos kenan” Fad’ar wata mata kenan wacce ke shayar da yaronta nono
“Baaba manta dasu yan bak’in ciki ne,  kice ma Matar zanyi kawai kinji” Na fad’a yayinda nake dafa k’afafuwanta domin tamkar mahaifiya na d’auke ta yanzu.
****
_GONA_
Oni Murjanatu! saboda tsabar masifar son kud’i yau nice a cikin gona da zummar zanyi noma a biyani, wanda tunda nake a rayuwata ko gonar babanmu ban ta6a takawa da zummar yin noma ba, sai dai kawai naje domin nayi roron wake, shima badan komai sai dan na mik’e k’afata kawai
Bare kuma gidan mijina da ko misqala-zarratin bayaso yaga na wahala
“Hayya, hayya, bi sur’a ya jama’a”  (Kuci gaba, kuci gaba, da sauri mutane)abinda mai gonar taketa faman fad’a kenan tun d’azun tana kewaya masu yin noman
Dab dani ta tsaya tana k’are mani kallo sama da k’asa
“Ish sauyi shuqul ya bint?” (Me yasa baki fara aikin ba yarinya)
Banji abinda ta fad’a ba, amma na fahimci abinda take nufi saboda ta6a Haiwar hannuna da naga tayi (abin yin noma)
Allah na gani nafi awa guda ina k’okarin d’aga haiwar nan amma ina, nayi nayi ko dagata na kasayi aradu, to d’aga  haiwa ya gagara tayaya za’ayi na iya yin wani noma kuma?
Gurin sau uku tana zagayowa tana ganina tsaye, a yanda ta barni haka nan take dawowa tana samuna, nayi fik’i-fik’i da idanuwana sai faman muzurai nakeyi
Da dai ta fahimci ba zan iya ta6uka komai ba a cikin gonar,  kar6e haiwarta tayi tace na fice mata daga gona
“Tafi nono fari” abinda na fad’a kenan a cikin raina
Na ajiye mata haiwarta wacce nauyinta zaiyi nauyin buhun sukari na k’ara gaba abina
 Inda na kwantar da Hamza yana bacci naje na goyasa muka nufi zango masaukinmu.
 *Bayan kwana biyu*
Yau kam bazani barar danja ba domin na lura da wannan bahaushen mutumin tun ranar da abin nan ya faru har yanzu idan ya ganni dariya yakeyi mani, shiyasa yau na yanke shawarar kasuwa zan nufa ko gari da kayan miya nasamo na rage zafi.
Da k’aton bahona na tafi kasuwar domin zuba gari, sai Kuma wata yar roba madaidaiciya dana d’auko, ita kuma domin zuba cefanen da zan samo, na bawa Hamza ya rik’e mani ita yana biye dani a baya.
Kamar yanda na tsammata kuwa haka abin ya faru, domin saida na ciko k’aton bahon nan da garin Masara dana gero dana dawa, garin masararma yafi yawa a ciki shiyasa ya haskaka sauran garirrikan da na had’asu dashi, cefanen nema nad’an samu ba wani yawan kirki.
 Da k’yar na iya d’auko kayan muka dawo gida na sayarwa masu tuwo-tuwon gidanmu akan farashi mai sauk’i, suka bani yan canjina na soke a jakata
 *Da yamma*
Bayan na d’an huta daga gajiyar d’azu da safe da nayi na shirya nayi haramar tafiya qasil da dugu-dugu cikin gari kuma.
Gun Baaba na nufa inda take zaune tana wanke kwanukan masu tuwo-tuwo

“Baaba dan Allah ga Hamza nan na bari yana bacci a d’aki idan ya tashi kid’an kular mani dashi kafin nadawo dan Allah”
“Murjanatu dan Allah ki dinga sararawa ranki, wannan uwar wahalar tayi yawa, tunda kin fita da safe kiyi hak’uri mana sai Allah ya kaimu gobe, Kinga kuwa yanda kika k’ara bushewa? inaga bakya duba madubi ne shiyasa”
“Kiyi hak’uri Baaba, wallahi na matsu na ganni a Sudan d’in ne shiyasa kikaga inata neman kudi babu ji babu gani, amma da mun k’arasa Sudan zakiyi mamakin irin hutawar da zanyi”
“To Allah ya bada sa’a, a dawo lafiya”
Da gudu na ida fita daga gidan domin gara na hanzarta na wuce saboda naga Magariba na shirin gabatowa
Kallon mamaki Baaba tabi Murjanatu dashi…
 Hmm ko mamakin mi takeyi? oho

Zaituna kina ina? Zo ki raka Murjanatu cikin gari ta koya maki yanda ake yin Qasil da kuma dugu-dugu:mrgreen:

    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          jiki ya tsira
                 12
                 NA
     MAMAN JA’AFAR

Yau kam cikin murna nake domin ban had’u da daka ko d’aya ba, wanki kawai naita cin karo dashi.
Bani na dawo gida ba tun fitata sai wajejen k’arfe goma na dare shima bari nayi nadawo amma badan na k’arasa ba
Baaba Habiba na tarar tayiwa Hamza wanka ta bashi abinci yaci ya k’oshi yagama wasansa sai sharan bacci yake, dayake yaron bashida da d’afa halin babansa yayo, yanada son mutane sosai
Amma nikam inba dan dole ba gaskiya ban cika son hayaniyar mutane ba.
A irin wannan yanayin ne muka kwashe kusan tsawon wata 6 a wannan Zangon, babu laifi na tara yan canjina wanda nake sa ran zasu isa haurawa dani garin garin *TAHIR* saboda ina tsammanin kud’in da nake dasu sunfi k’arfin su ajiyeni a *UBAYYU* (Tahir garin na fasa) kirarin da masana hanyar kenan sukeyima garin
_*Da dare*_
Muna kwakkwance a tsakar gida kamar yanda muka saba dayake lokacin damina ne kuma indai ba ruwa akayi ana fama da zafi
Sarkin Zango Ali Rawayau ya aiko a kira masa Baaba Habiba
Dayake ta kama mutunci sosai shiyasa kowa na wannan Zangon yake ganinta da mutunci kuma yake girmamata
“Gani ranka ya dad’e” Abinda ta fad’a kenan bayan ta zauna a saman d’aya daga cikin tabarmin da ke shinfid’e a gurin
Gyaran murya ya farayi kana yaci gaba da bayani
“Habiba ba komai yasa na kiraki nan gurin ba sai abin alkhairi daya samemu” 
Cikin mamaki Habiba ta dubesa”Abin alkhairi kuma ranka ya dad’e?”
Jijjiga kai yayi alamun tabbatar da maganar da zai fad’a
“K’warai kuwa Malama Habiba, wani mutumi ne d’an azziki irin albarka da muke gaisawa dashi, to yanada mota mai shiga Sahara da Kuma Duwatsuna, yakan d’auko mutane daga Abasha ya wuce dasu Ubayyu ko Tahir, to jiya jiyan nan ya kirani a waya yake shaida mani wai yanaso na had’a masa mutane wa’yanda zasu tafi Tahir koda kuwa kud’in su bai cika ba zai kaisu a haka, a yanda yakeyi mani bayanin nasa na fahimci ba kud’i ne sosai a hannunsa shiyasa yakeso na had’a masa fasinja, Kinga ko idan hakane ai ya samu riba biyu, ga kud’i ya samu kuma ga d’unbin ladar da zai samu na taimako da yayi ko?” Ya k’arasa maganar tasa da tambaya yana kallon Habiban
Gyad’a kai tayi alamun gamsuwa da bayanin nasa
“To shiyasa na kiraki domin na sanar dake, kema ki sanarwa mutanen gidan, kowa ya harhad’o abinda ke garesa kafin ya k’araso saboda ina tsammanin jibi zai shigo garin”
“Cikin matsanancin farin ciki Baaba Habiba take yiwa sarkin Zango godiya 
“Karki damu Habiba ai yiwa kai ne, amma kije kiyi shawara da mutanen gidan duk abinda kuka yanke kya sanar dani”
Batare da 6ata lokaci ba Baaba ta taramu guri guda ta kwashe duk yanda sukayi da Sarkin Zango ta fad’a mana
Ranar dan tsananin murna har kasa bacci nayi, dana rufe idona babu abinda da nake gani sai gani a *KHARTUM* babban birnin Sudan
Washe gari kusan mu 100 kowa ya harhad’o abinda ke hannunsa muka damk’awa Baaba ita kuma ta kaiwa Ali Rawayau
Kowa ka kalla a cikin gidan bakinsa ya kasa rufuwa saboda tsananin murna da farin ciki, ranar dan tsananin murna mu duka kwana mukayi bamuyi bacci ba munata fira da tsara yanda rayuwarmu zata kasance a Sudan idan munje
Wasunmu kuwa rediyo suka kunna sai faman casu sukeyi 
Wasu ko kwana sukayi suna sallah suna mik’a godiyarsu ga Allah daya kawo masu wannan ranarda zasu bar Tiyna su haura Tahir, a cikin su kuwa harda Mamata wato Baaba Habiba.
*Washe gari da safe*
Ranar da yakama zamu bar Tiyna kenan
Tun safe muke sa ran ganin Ali Rawayau amma shuru har gashi rana ta fara fitowa
“Baaba! kodai gidansa zanje na duba k’ilan mai yiyuwa yana tare da mai motar acan”
“K’warai kuwa yarinya kin kawo shawara, maza dan Allah jeki ki dubo mana har rana ta fara fitowa fa” Cewar wata mata kenan wacce ta haihu shekaran jiya, da yake tare da mijinta suka taho
Da shigata gidan nasa ko gaisawa ban tsaya munyi ba na fara tambayarsu
“Dan Allah Baba Ali nake nema ko yana gidan nan kuwa?”
“Gaskiya baya nan domin muma tun jiya da dare muke cigiyarsa, ina dai lafiya?”
“Lafiya kalau” Na fad’a a tak’aice
Na dawo inda mukayi ayari muna jiransa
“Yarinya kin samesa? ya kukayi dashi?”
Tambayar da wasu daga cikin masu jiran dawowata sukayi mani kenan kusan a tare
“Wallahi suma yan gidan sunce basu ganshi ba, wai a cewarsu suma nemansa sukeyi tun jiya basu ganshi ba”
“Mudai k’ara jira mu gani” Cewar Baaba Habiba kenan.
Wasa-wasa har dare ba sarkin zango ba labarinsa, tun muna basa uzuri har dai abin yakai ga fara bamu tsoro mu duka
Kaddai tsohon nan guduwa yayi? abinda naketa maimaitawa kenan a cikin raina, sai  k’okarin kauda wannan tunanin nakeyi a cikin zuciyata Amma sai k’ara bijiro mani yakeyi.
Ko baccin kirki babu wanda ya samu a cikinmu, yanda mukaga rana haka mukaga dare
*Washe gari*
Muna nan zazzaune munyi tagumi muna jiran gawon shanu, kwatsam sai ga Abokin Sarki ya shigo Zangon namu, ganin duk munyi zugum-zugum yasa shi tambayar abinda yake faruwa
“Wallahi daka ganmu nan abokinka muke jira, tun jiya da muka harhad’a masa kud’in motarmu na zuwa Tahir muka nemesa muka rasa, dan Allah Malam ko kasan inda yake ne ka kaimu gunsa?”

Baaba Habiba ce mai fad’ar haka jiki a sanyaye
“Assha” Assha” Subhanallahi”
Abinda mutumin ya keta faman maimaitawa kenan
Can dai ya nisa “Amma indai kuwa haka akayi Malam Ali bai kyauta maku ba, domin jiya jiyan nan ya sameni a gida yayi mani sallama akan zai koma Nigeria yau da safe  wai zai d’auko d’ayar matarsa, harma wani abu ya d’auko ya bani inata faman godiya, ashe da walaki wai goro a cikin miya, dan ni nasan halin Malam Ali Mayen kud’i ne na k’in k’ari ba 6an6aruwa yakeyi ba, dan akwai…..
Kafin ya k’arasa dogon turancin nasa tuni mun cika wajen da kururuwa, masu ihu nayi, masu ambaton Allah nayi, yayinda wasuma fad’uwa sukayi k’asa a sume
Nima dai kad’an ya rage ban suman ba amma dukda haka numfashina baya tafiya dai dai domin sama-sama nake jinsa…..

Ina masu niyar zuwa Sudan ta K’afa? to ku shirya fuskantar irin wannan Kalubalen domin babu makawa sai hakan ta tabbata koma fiye da hakan. IDAN KUNNE YAJI…
Bara mu d’an barsu su sarara su gama jajantawa juna kana mu dawo muji kuma irin shawarar da zasu yanke a tsakaninsu

   *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                 13
                 NA
     MAMAN JA’AFAR 

Da k’yar nasamu kuka yazo mani, kana naji zuciyar tawa tad’an yi mani sauk’i-sauk’i

Mu duka kuka muketa rabsawa babu mai rarrashin wani sai kace gidan makoki, ai har garama gidan makokin, domin mafiya yawan gidajen makokin yanzu wad’anda mutuwar ta shafa su kad’ai keyin kuka, yayinda wasu kuma dariya sukeyi, wasuma har gulma suke d’an ta6awa idan sun samu sarari, saboda sun riga sun san wanda ya mutu ya riga ya mutu ba dawowa zaiyi ba.
Haka muka k’ara ci yan koke-kokenmu gamida jajantawa juna mukayi shuru kowa ya koma zancen zuci shi kad’ai.
“Dan Allah jama’a kuyi hak’uri ku yafe mani, wallahi nasan duk ni naja maku wannan ta’asar tunda ni nazo maku da wannan bayanin”
Cewar Baaba Habiba kenan yayinda take shar6ar majinar kuka tana gogewa da gefen zaninta
Tasowa nayi nazo dab da ita na zauna gamida rik’o hannayenta
“Baaba ki kwantar da hankalinki karki damu na tabbatar duk cikinmu nan babu wanda yake zarginki da cinye masa kud’i domin kowa acikinmu ya shedeki da kyakkyawan hali koba haka ba mutane?” na fad’a yayinda nake duban fuskokinsu
“K’warai kuwa yarinya haka maganarki take”
Cewar wata tsohuwa kenan yayinda take rank’washin kanta, a tsammanina kwarkwata ce takeyi mata zarya a cikin kan nata
Kamar had’in baki suma sauran jama’ar  babu wanda ya zargi Baaba Habiba, sai faman Allah ya isa da suketa bin Sarkin Zangon da shi
Yayinda wasu tsiraru daga cikinmu kuma suka yanke shawarar tunkarar iyalan Ali Rawayau da wannan maganar domin samun mafita.
******
Haka dai abubuwa sukaita wakana, tun su Murjanatu sunasa ran ganin Sarkin Zango yau ko gobe ko jibi har dai suka kai ga gajiya suka maida hankalinsu gaba d’aya gurin nemanda zasuyi nan gaba domin haurawa garin Tahir.
Tun Murjanatu najin wahalar irin ayyukanda takeyi na k’arfi har dai ta kai ga ayyukanma sun riga sun zame mata jiki inma batayi ba ba jin dad’in jikinta takeyi ba.
A irin wannan yanayin ne suka k’ara shafe tsawon watanni shidda a Tiyna suna bauta domin mayar da wa’yancan kud’aden da sukayi asara na baya.
Alhamdulillahi sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a dad’e ba’a je ba inji masu iya magana
Yau gashi kowa cikinsu ya tara abinda ya tara harma gasu Murjanatu can na hango suna niyar shiga motar *Tahir* (garin na fasa)

“Baaba anya motar nan batayi mana kad’an ba kuwa” abinda na fad’a kenan bayan na k’arewa motar dake gabanmu kallo, wacce muke sa ran zata d’aukemu kusan mu ashirin
“Wane mota tayi kad’an Murjanatu? kawai dai muyi fatan Allah ya saukemu lafiya tunda motar bata gidanmu bace, data gidanmu ce sai muce zamu sakata mu wala yanda mukeso”
Daga jin haka na kama bakina nayi gum.

Haka muka shiga motar nan muka zazzauna kowa a marmatse, danko gurin mik’e k’afama babu
“Mama an maceni” Hamza ne mai fad’ar haka da yaji takurar tayi yawa
Jawosa nayi a jikina ina dadda6arsa ina shafa masa kai alamun rarrashi
“Yi hak’uri kaji Hamza? yanzu nan zamu isa kaji D’ana?”
Yauma dai kamar sauran tafiye-tafiyenda mukeyi, domin tun safe muka bar Tiyna sai La’asar sakaliya muka k’araso wani k’ungurmin daji
Fakawa mai motar yayi a cikin dajin kana da harshen labarci yace “To jama’a nifa iya nan zan ajiye ku domin kuma kunsan babu yanda za’ayi na shiga garin Tahir daku a haka saboda tsoron hukuma nake gaskiya, dan muddin suka ganni na kwasoku a haka d’in nan kamar na kwaso dabbobi babu abinda zai hana su kamani su cini tara”
Da har mun tsaya yin jayayya dashi akan bazamu shid’a a wannan uban l dajin ba, wata mata daga cikinmu tace
“Bayin Allah inaga  kawai muyi hakuri mu sauka d’in kamar yanda ya buk’ata domin abinda ya fad’a tabbas gaskiya ne dan bana mantawa shekara goma sha biyar data wuce nata6a bin wannan hanyar kuma tabbas shima mai motar da ya d’auko mu a Tiyna irin wannan dajin ne ya ajiyemu”
Da jin wannan bayani na wannan mata nan take muka sassauko kuma muka sauke uwayen kayanmu dake kan motar, shi kuma mai mota ya tada motarsa yayi gaba ya barmu a wannan k’ungurmin dajin muna rarraba idanuwa.
“To jama’a cikinmu su wanene sukazo da kayan girki? Dole ku warware kayanku ku d’ora mana girki muci mu k’oshi kana mu kama hanyar tafiya, dan tafiyar da ke gabanmu ba yar kad’an bace, saboda a k’alla zamu shafe kusan awa 3 zuwa 4 muna tafiya a k’afa kafin mu samu garin da zamu yada zango……
 *K’auyen K’wadage*
“To Iya ni na fito, zan wuce can gidansu Murjanatun” Haro ne mai fad’ar haka bayan ya fito daga sashen nasu
“Zo nan ka zauna” Mahaifiyarsa ce mai fad’ar haka yayinda take nuna masa tabarma da hannu
Har ya kai bakin k’ofa ya dawo ya zauna kamar yanda ta umarce shi
“Iya gani” abinda ya fad’a kenan a tak’aice
Gyaran murya tayi gami da gyara zama
“Mik’o mani wannan takardar da ke hannunka”
Da kamar zaiyi mata musu, amma ganin yau fuskar tata ba wasa yasa yasha jinin jikinsa ya mik’a mata
“Yanzu Haro da hankalinka da tunaninka zakayi wannan aika-aikar? to Inko haka ne ina ilimin naka da hankalinka suka tafi? inace lokacin da kake koya mani karatu kata6a cemani duk duniya babu halak d’inda Allah ya halatta wanda kuma yake fushi idan an aikatata face saki?

Ko ka manta sadda ka ta6a cemani idan akayi saki tsabar fushin da Ubangiji yakeyi har Al’arshinsa girgiza takeyi? Haba Haro da iliminka karka maida kanka jahili mana

Kayi hak’uri ka kwantar da hankalinka a hankali komai zai wuce, yanzu kana cikin fushi ne shiyasa kake yunk’urin yin wannan aika-aikar, kuma kasan shi fushi mabud’i ne na dukkan sharri, haba Haruna a dingayi ana hak’uri mana duka rayuwar duniyar ma nawa take? ni nasan duk inda Murjanatu ta tafi da k’afarta zata dawo, domin bari ai ba shegiya bace da ubanta, wanda kuma yak’i jin bari nasan zaiji woho”
Nasihar mahaifiyar tasa ta ratsa masa jiki, nan take ya fasa aiwatar da abinda yayi niya, ammafa ya k’udurta a cikin ransa muddin ya dawo daga Legas kuma kasuwancin ya kar6esa sabuwar amarya dalleliya zai 6aro a leda.
*Gidansu Murjanatu*
Bai tarar da kowa a gidansu Murjanatun ba sai mahaifiyarta itama sallar isha ya samu tanayi

Saida ya jira ta idar da sallar kana suka samu damar gaisawa
“Lafiya dai Haro ko?”
“Wallahi lafiya k’alau Inna, dama labarin Murjanatu ne aka samu”
Baiwar Allah da fara’arta cikin zumud’i take tambayarsa
“Ina aka samu labarinta d’an nan? tana ina yanzu? a raye ko a mace? Muje ka kaini gurinta dan Allah”
Kusan a rud take furta wad’annan kalaman
Nan take ya kwashe duk yanda sukayi da Huwaila ya fad’a mata
Hannu ta aza bisa ka ta rushe da kuka
Shi dai dayaga yayi lallashin yayi rarrashin amma tak’iyin shuru yaja tsumman takalminsa ya k’ara gaba domin bazai iya jurar ganin hawayen tsohuwar ba, dan tausayi take basa matuk’a….
Ga dai su Murjanatu can a cikin k’ungurmin daji suna niyar d’ora girkin abinci, bayan sun gama dafa abincin kuma kome zai faru?
Kardai ku gaji ku biyoni domin ci gaba da jin yanda wannan doguwar tafiyar zata kasance
    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

          jiki ya tsira

                  

                 14
                 NA

Dab da mangariba muka kammala girkin namu mukaci mukayi haniy-an, dukda hakanma wai cikin sauri mukayi shi saboda gagarumar tafiyar da ke gabanmu
Kowa ya d’auki yan kayansa ya d’ora aka, nima dai nawa kayan aka na d’auke su na rik’e hannun Hamza muka kama hanya
Tafiya muke ba ji ba gani amma ko alamar gari bamu hango ba
Ga hanyar ko kad’an ba dad’in bi ne da ita ba saboda yawan Sahara (Yashi mai yawa) dan tsabar yawan yashinma har k’afafuwan mutum nutsewa sukeyi, shiyasa idan mukazo inda yashin yafi yawa nake goya Hamza dukda kuwa yanzu ya wuce goyon, saboda a k’alla yanzu Hamza zaiyi shekara kusan 3 harda kusan  wata d’aya.
Jikinmu duk yayi k’ura munyi bud’ubud’u damu tamkar an tono mu daga rami, wani lokaci ma idan iska ya hura k’asar har cikin idanuwanmu take fad’awa.
Tafiya muketa faman yi tun d’azu tak’i ci tak’i cinyewa, sai dai idan muka gaji mu samu wuri mu zauna mu d’an sha ruwa kana mu k’ara gaba kuma
Tun Hamza na kukan gajiya ina lallashinsa har ta kai ga na kasa rarrashin nasama, domin nima a zahirin gaskiya neman mai rarrashin nawa nakeyi.
“Kai jama’a! Nidai wallahi na kusan mutuwa dan Allah ku taimaka ku tsaya mu d’an huta” Ina magana Ina murzar idanuwana saboda wata uwar k’asa da iska ya huro ta fad’a mani a cikin idon
“Bazaki mutu ba yarinya insha Allahu sai Kinga Sudan da idanuwanki, dan haka idanma zaki ware kiyi tafiya gara ki ware kinji”
Wannan matar ce mai fad’ar haka wacce d’azu ta bamu labarin ta ta6a bi ta wannan hanyar
Ban mayar mata da amsa ba saima juyawa danayi gurin Baabata a rud’e
“Baaba wai kinji bamuma kusan zuwa ba, dan Allah Baaba tunda tafiyar tamu da saura d’an goya mani yaron nan mana, wallahi nagaji, ji nake bayana kamar zai 6alle k’afafuwana tamkar zasu tsinke wallahi”
Na fad’a yayinda nake kwanto Hamza daga bayan nawa wanda ya langa6e tamkar matacce
dakatar dani tayi ta hanyar d’aga mani hannu 

“A’a Murjanatu barshi karma kiyi wahalar kwantoshi dan kema kinsani sarai ba lafiyar k’irji ne dani sosai ba” ta fad’a cikin kasalalliyar murya mai nuna alamun gajiya
Bisa kafad’ata na d’orasa  mukaci gaba da tafiya amma hawaye bai daina bin fuskata ba
Da dai naga ba sarki sai Allah zama nayi a k’asa dirshan na saka masu kuka
“Nidai wallahi Allah nagaji daga nan babu inda zan iya matsawa, nidai nagaji ku maidani gida na rantse da Allah na fasa zuwa Sudan d’in na hakura talaucin ya kasheni….
“Kai kujimu da yarinya! da mu mukace ki biyomu? kuma da kike wasu surutai marasa ma’ana ke kad’ai ce mai rai anan gurin da zaki ishemu da raki? ko angaya maki muma bamusan zafin jikinmu bane? to tun wuri inma zaki ware gara ki ware, in kuma bazaki tashi ba mu tafiyarmu mu barki anan kamar yanda wa’yancan sukayi gaba suka barmu nan tsaye muna 6ata lokacinmu akanki”
Ta fad’a tare da nuna mani ayarin wad’anda sukayi gaba abinsu ko kallon azziki ma ban ishesu ba sadda na fad’i, dan mutanen da ke kan nawa a tsaye basufi su 5 ba
Da dai na lura suma sa iya tafiya su barni a wannan k’ungurmin dajin ni kad’ai, nan take na goge hawayena na k’ara goya Hamza na sa6i yan k’ullin kayana na bisu jiki a sanyaye
Amma har ga Allah yaudai nayi nadamar biyowata wannan hanyar Sudan d’in, gashi kuma mun riga munyi nisa, nisan da bazan iya komawa gida ba, tunda masana hanyar naji suna cewa da mun iso *Lifahir* daga nan sai Tahir daga Tahir sai Khartoum wato  babban birnin Sudan.

Can cikin dare muka samu barin wannan uwar saharar muka iso wata rumfa an shinfid’a tabarma a k’asanta ga dukkan alamu irinmu masu yada zango ne sukayi wannan rumfar domin huta gajiya.
Rumfar muka shiga muka sassauke kayanmu muma muka zauna domin hutawa
A cikin kayan namu dama akwai itace da dukkan kayan abinci saboda tsammanin irin wannan riskar
Nan take manyan mata suka ware kaya suka hau yin girki baji ba gani, kafin kace meye har sun gama dafa mana dafa dukan shinkafa ko mai babu a ciki, haka nan muka sassank’ameta
Allah sarki Hamza inata Jijjiga shi bai tashi ba, amma yana k’yalla ido ya hango abinci nan take ya wartsake.
Haka mukaita cin abincin nan hannu baka hannu akushi har muka cinyesa tas mukasha ruwa
Sai wannan lokacinma nasamu natsuwar ganin yanda dukkanmu mukayi bud’ubud’u sai kace antonomu a rami.
Hamza kuwa tsabar k’urar da mukasha k’asa har tsakar kansa ta shisshiga
“To jama’a! yanzu tunda munci mun k’oshi sai kuma mu kwanta kafin garin Allah ya waye mu k’arasa *Lifahir* domin anan ne mukesa ran zamu samu motar garin Tahir”
Cewar wannan matar kenan wadda tace ta ta6a bi ta wannan hanyar
“Haba Iya! wai kina nufin a cikin wannan k’ungurmin dajin zamu kwana? gaskiya ni tsoro nakeji wallahi, gara dai mu d’an k’ara gaba ko Allah zaisa mu musamu gari akusa”
“Kaji yarinya, sai kace ba ita bace wacce tayiwa mutane zaune a hanya tanata runtuma kuka ba, keda kikace kin gaji tunda anzo gurin hutu basai ki huta kwanta ki huta ba? in kuma  tafiya zakiyi  ga fili ga mai doki nan bamu hanaki sukuwa ba”
Fad’ar wata mata kenan mai goyon jariri yayinda jaririn nata yaketa  faman tsandara mata kuka, itako sai faman rirrigashi take tayi
Kumafa sai yanzu na tuna uwar gajiyar da nake tare da ita, inaga dan naci abinci ne nakejin d’an k’wari-k’wari a jikin nawa, koba komai nima zanso Hamza ya kwanta shima yad’an huce gajiyar da ke tare dashi, tunda kafin muzo nan wani lokacin idan na gaji da goyonsa saukesa nakeyi shima ya d’an taka, sai ya gaji ne nake goyasa kuma.
A wannan dajin muka kwakkwanta muka d’an ta6a bacci sama-sama tunda bamace munyi bacci mai dad’i har ba har asuba tayi mukayi alwalla muka gabatar da salla kana kuma mukayi haramar tafiya
“A’a ya naga kunata faman d’aukar kaya haka? nanfa ake barin kayan sai mun samu isa garin Tahir kana mu samu masu Amalanke mu biyasu suzo su d’aukar mana kayan mu basu lada”
“Anya baiwar Allah wannan hanya da kika d’oramu mai 6ullewa ce kuwa?”
Baaba Habiba ce mai fad’ar wanann maganar yayinda ta rik’e ha6arta da hannunta alamun shakku
Dariya tayi kana tace
“Karku damu insha Allahu babu abinda zai samu kayanmu, saboda barin nasu anan shine mafi alkhairi a garemu tunda yanzu da mun k’ara yin gaba kad’an hukuma zamu tarar kuma ire-irenmu suke kamawa, amma kunga idan basu ganmu da kaya ba ai bazasu tsammaci mu matafiya bane ba ko? amma wanda zai tafi da kayan nasa ban hanasa ba, nidai nawa a nan zan barsu”
Da jin wannan bayani nata sai duk jikinmu yayi sanyi muka ar-aje kayan namu duka muka d’au hanya.
Wannan karon tafiyar da mukayi a k’afa batafi ta awa 2 ba muka samu isowa garin *Lifahir* Inda muke sa ran zamu samu Motar Tahir kenan(Garin na fasa)

Da naso na tausayawa Murjanatu, amma dai nace bara  nayi shawara da masu karatu. Anya Murjanatu ta cancanci a tausaya mata kuwa????

     *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/10, 12:57 PM] Mmn Jafar M: 🌳IDAN KUNNE YAJI🌳

           jiki ya tsira
                 15
                 NA
     MAMAN JA’AFAR

*Lifahir*

Ba wani babban gari bane can sosai ba, hasalima na iya cewa ba gari bane domin a iya ganina dai a inda muke yanzu banga gida ko d’aya ba a gurin sai motoci, alamun dai kamar tasha ce kawai akayi a gurin
Amma mai yiyuwa akwai gidaje a gaba dan dai bamu shiga cikin garin sosai bane
****
“Ina na Tahir? Ina na Tahir?”

Abinda kwandastan motar yaketa faman maimaitawa kenan tamkar anbashi hardar karatu, sai dai da harshen larabci ne yake fad’ar hakan

 
“Kungama Alhamdulillahi ga motar Tahir d’in can mun samu basai munsha wata wahala ba”
Cewar matar nan wadda tasan hanyar kenan tare da nuna mana wata
Wata zungureriyar mota ta nuna mana mai kama da jirgi wacce ak’alla zata iya cin kamar mutum hamsin
“Yanzu baiwar Allah kamar daga nan zuwa Tahir d’in zamuyi kamar awa nawa ne kafin mu isa?”
Fad’ar wata jibgegiyar mata kenan a cikinmu wacce taketa faman nishi sama-sama alamun gajiya sosai a tattare da ita

Dariya tayi kana ta mayar mata da amsa “Ai garama ki k’ara shiri sosai domin Muda isa garin Tahir inaga sai gobe, gobenma bada safe ba, shiyasa yanzu kamata yayi mu d’an zagaya cikin tashar nan mu d’an sayi  abin ta6awa wanda bazaiyi saurin lalacewa ba har mu isa saboda halin tafiya, musamman ma a ku masu yara”

ta fad’a tare da kallon inda muke mu masu goyo.
“Tunda ga Murjanatu nan kuma itace k’arama a cikinmu ai bama d’unguma mu duka mutafi sayen wani abu ba ko? ni ina ganin kawai mu had’a mata kud’in ga wani shago can na hango sai taje tasiyo mana yan kayan toye-toye da ruwa ko kuma d’an so6o, ko ya kukace?”
Tuni duk suka amince da wannan shawarar ta Baabata kowa ya kawo yan canjinsa suka had’o mani nima na had’a da nawa na nufi shagon domin siyo abinda mukeda buk’ata
“Ish tibga?” *(Me za’a baki) abinda mai shagon ya fad’a kenan da harshen larabci
Dibi-dibi na farayi domin ban fahimci abinda yake son fad’a mani ba

Ba kuma wai dan ban iya larabcin bane a’a ni larabci na na Tiyna na iya, shi kuma larabcin nan inaga na Sudan ne
Wani kyakkyawan saurayi na hango  wanda tun da zan shigo na gansa can zaune akan dogon benci yana cin biskit yana korawa da lemun kwali
Ga dukkan alamu yana lura da abinda ke faruwa tsakanina da mai shagon
Daga can naga ya taso ya tunkaro inda muke
“Allah sarki! baiwar Allah hala bakya jin larabci ne?”
“Eh wallahi, dan Allah ko zaka taimaka mani ka fad’a masa abinda nake buk’ata?”
“Babu komai, ai taimako lada ne dashi musamman ma taimakon mace kyakkyawa irinki”
Murmushi nayi domin tabbas naji dad’in wannan yabon da yayi mani
Bayan na gama sayayyar ne na fiddo kud’i da niyar zan bawa mai shagon
“Bar kud’in ki Kyakkyawa na riga na biya,  domin kamarki bai cancanci ace tana biyan kud’i idan tayi sayayya ba”
Nanma dai Murmushi nayi, domin wani farin ciki nake jin yana ratsa zuciyata idan ya kirani da kyakkyawa wanda bansan dalilinsa ba, dan tabbas nasan ni kyakkyawa ce amma koda wasa Haro bai ta6a kirana da suna kyakkyawa ba
Duk’awa nayi da nufin zan d’auki kayan, sauri yayi ya rigani d’auka tare da d’orawa bisa kai
“A’a Malam ya haka kuma? shisshigin nakafa yana nema yayi yawa”
“Laifi ne dan na d’aukarwa kyakkyawa irinki kaya?” ya fad’a yana wani kashe mani ido
“A’a ba laifi bane amma dai kabarsa kawai zan d’auka da kaina, nagode d’awainiyar ta isa hakanan”
Bai kulani ba saima rik’o hannun Hamza da yayi 
“Abokina miye sunanka?”
“Sunana Hamza”
“Hamza zakayi abota dani?”
“Eh” yaron ya fad’a tare da d’aga masa kai alamun amsawa

Da dai na lura zasu 6ata mani lokaci tafiyata nayi na barsu a gurin, amma bana yin sauri sosai dan kada na 6ace masu su kasa hangoni
“A’a Murjanatu! ya akayi na ganki hannu ba komai? kodai baki samo bane? ina kuma kika baro Hamzan?”
Tambayoyi kusan guda uku Baaba ta jero mani yayinda ta ganni ni kad’ai zik’au
Kafin na bata amsa tuni har sun k’araso
Sallama yayi masu kana cikin ladabi ya duk’a ya gayar dasu su duka
Cikin shakku da Kuma mamaki fal a fuskokinsu suke amsa gaisuwar tasa
Mik’o mani kayan yayi tare da yi mani sallama ya tafi abinsa
Amma ga mamakina motarda muke niyar shiga ita naga wannan saurayin ya shiga, ga dukkan alamu shima inaga Tahir d’in yakeson tafiya.
Muma cikin sauri muka gama cin biredin da na siyo mana da lemu muka isa inda motar take muka biya kud’in mu muka shiga muna jiran ta ida cika mu ganmu a Tahir
“Abokina! zo nan mana kusa dani ka zauna Ko har abotar ta warware ne?” Ya fad’a tare da mik’owa Hamza hannu alamun yaje gunsa
Juyawar nan da zanyi sai ko ganin wannan kyakkyawan saurayin nayi mai arhar Murmushi yana zaune a kujerar bayana yanata faman Murmushinsa kamar yanda ya saba
Shiko Hamza da murnarsa ya zagaya inda Abokin nasa yake yayi d’are-d’are a bisa k’afafuwansa sunata fira abinsu, dayake Hamza akwai shegen surutu idan yasamu sarari.
Saida muka 6ata kusan awa guda a tashar nan kana motar ta samu cika muka kama hanya ba ji ba gani tafiya muke ba kakkautawa, salla ce kawai ke tsaida mu.
Muda muka baro Lifahir tun safe bamu muka samu isowa garin Tahir ba sai washe gari wajejen k’arfe 12 na rana……

Kai Murjanatu bakida dama, ana ruwa yaci makad’i ke kuma kina cewa gangarsa ta jik’e.
Ana wata ga wata…

Kardai ku gaji kuci gaba da bina domin jin yadda wannan Chakwakiyar zataci gaba da kasance wa

    *NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

RANAR RABO 1-END

🌲🐄 *RANAR* *RABO*🌲🐄

1 TO END

Daga taskar Y’ar mutan Jega.
       Gidan Alh Abubakar gida ne sananne a garin Jega.
Mutum ne da duk shekara yake yanka sa da rago kusan bakwai shida matan shi.
Yau ta Kama ranar rabo, ranar da mutanen Jega ke fitar da naman su na tare ni a yanka aba duk wani mak’oci ko d’an Uwa da sauran masu zuwa barka da sallah cikin gida.
Tun safe ta wanke tallen ta ta jicce.
Malam Yusha’u ya fito daga d’aki zai yi shimfid’a yasha iska ya ganta tana wankin talle.
Ya ce’

“Maimuna me zaki yi da tallen suya kuma?”.
Ta ce’

“Mal kasan mak’ota na aiko muna nama musamman gidan Alh Abubakar”.
“Ko kana nufin ka manta da cewa yau ce *RANAR* *RABO*?
Nan ya yi murmushi ya girgiza Kai, ya yi shimfid’a ya kamo radio d’in shi yana saurare.
Ya rasa gane a cikin mutane Maimuna wace iri ce.
Duniya akwai ta da saka ma rai Abu.
Sallamar da yaro ya yi yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka.
Tun kan taga Mai sallama ta zabura daga hura wutar da take yi.
Da saurin ta ta k’araso gurin Mal ta ce’

“Don Allah kaban hamsin gurinnan saboda kasan naman da ake kawomin daga gidan Alh yafi k’arfin tukwiycin naira ashirin”.
Murmushin da taga ya bi k’ofa da shine yasa ta juya itama, abinda ta gani ne yasa ta kasa cigaba da maganar ta.
   ******

Sai wuraren k’arfe goma aka yayyanka naman da akayi tareni dashi jiya.
Hafsat ta Kai duban ta gefen ta  ta ce’

“Anty amma gaskiya wannan shekarar ba zamu yi rabon nama ba ko?”.
Ta ce’

“Babu abinda zai hana, don ma Alh yace wannan shekarar zai fi raba nama akan kowace shekara”.
Nan tayi shiru duk jikin ta ya yi sanyi, har zata yi magana ko me ta tuna oho sai ta yi shiru.
Nan ta ja jiki ta fad’a d’aki ta d’auki wayar ta naga ta kamo lambar Maijidda Musa ta kira.
Ta yi Kira hud’u ba’a d’aga ba, har ta ajiye wayar zata fita sai ga kira ya shigo wayar ta.
Bayan ta d’auka naji ta ce’

“Anty Barka da sallah ya yara na?”.
Ba najin me ake cewa d’ayan 6angaren, amma ga alama gaisawa suke yi.
Can naji ta ce’

“Anty Maijidda ki ajiye min nawa nama fa”.
Ta yi shiru na y’an seconds sannan naji tana godiya ta d’ora da cewa sai kin aiko sai ta kashe wayar.
Ba ita ta fita daga d’akin ba sai da ta kira Anty Ybk, sai dai kash tayi rashin sa’a tace ai tana Ethiopia.
Nan ta yita kiran lambar mutane, ba ita ta fita daga d’akin ba sai da ta ji Alh na fad’a ta shige d’aki ta bar Safiya da aiki.
Nan ta fito sum-sum tamkar munafuka ta zauna suka cigaba da aiki.
Nan Alh ya had’o kan yaran kaf su tara, yaran Safiya shida na Hafsat uku aka fara yanka nama ana d’ora musu suna Kai mak’ota.
 *****

Ganin me malam ke yiwa murmushi yasa ta yi jugum ta bi yaron da kallo har sai da ya iso da hamsin a hannun shi.
Ya ce’

“Wai Mama ta ta ce ki bata yaji na talatin Magi na ashirin”.
Nan ta bi yaron da kallo ta ce’

“Ku da ke siyen yaji mudu d’aya da jakar Magi me za kuyi da yaji na hamsin?”.
Yaron ya ce’

“Ai wannan shekarar Rago kawai aka yanka mana”.
“Kuma ma Baban mu ya ce muyi hak’uri yanayi ne”.
“Shine Mamar mu ta ce bayan sallah za’a yanka mana wani Rago in an samu kud’i”.
Nan ta shiga d’aki ta d’auko Mai ta bashi ya fita da gudun shi.
Mal ya ce’

“Kin ga ma k’aramin yaro yasan yanayi amma ke tun safe kike Abu d’aya”.
“Ke bada layya ba amma kin dami mutane da wankin tallen suya”.
Ta ce’

“Ni dai nasan gidan Alh Abubakar da wuya layyar shi ta canza saboda duk garin nan an sanshi kan layyar shi da kuma irin *RABON* Namn da yake yi”.
Mal ya yi murmushi ya ce’

“Wallahi kiyi istigfari, domin wannan babban sa6o ne kika tafka zuwa ga ubangijin ki”.
“Alh waye shi da zai wuce jarabtar ubangiji? Wannan yanayin wallahi kowa ya ta6o”.
“Amma tunda naman gidan Alh kike jira to Allah ya bada sa’a, kuma aci lafiya”.
Nan yasa Kai ya fita saboda sallamar da yaji Ana yi daga waje.
Ita ko sai bam-bamin fad’a take yi har da d’ora wa da cewa, yau ko Mal ba zata ba naman ba in har an aikomata shi.
Ganin Mal ya dawo ne da Abu a hannun shi yasa tayi sakalo da baki ta bishi da kallo.
Nan Mal ya Kira yaron Maimuna d’aya Mai suna Usama.
Ya ce’

“Yi sauri ka kaiwa Hindatu naman nan, saboda nasan ko wannan shekarar Umar bai yi layya ba”.
Nan ta yi buttt zuwa rik’o ledar.
Mal ya ce ke!”.

Tsawa had’e da kallon da ya bita da shine yasa dole ta dawo ta zauna.
Ta ce’

“Malam me yasa kake nuna ban-ban ci tsakanin su usama da Hindatu?”.
Ya ce’

“Duka yara na ne, sai dai Ina tausayawa Hindatu akan maraicin ta, saboda haka kar ki k’ara saka min ido akan yara na”.
Ta ce’

“Amma fa kana sane da cewa muma baka yi muna layya ba, amma an baka sadaka kaba y’arka”.
Ya yi murmushi ya ce’

“Muda ke jiran na gidan Alh Abubakar, gashi har tallen suya an wanke mana”.
“Ina fatar dai akwai Mai na suya, kuma kin daka yaji da magi”.
   *****

    

 Hafsat ta Kai duban ta zuwa ga Alh ta ce’

“Ni fa na kasa ga ne wannan lamarin”.
“Wannan shekarar fa sa d’aya da rago biyu ka yanka Alh amma sai kwasar nama kake yi kana rabewa mutane”.
Alh ya ce’

“Dama sa da nake yankawa na al’uma ne, rago biyu kuma ya ishe mu muda yara”.
Nan tayi kicin-kicin da fuska ta cigaba da aikin ta.
Ana hakan sai ga yaro ya yi sallama ya shigo ya ce’

“Wai gashi inji Anty Maijidda”.
Nan tayi karaf ta kar6e taba yaro naira hamsin ta ce’

“Ka gaidamin da ita na gode”.
Bayan yaron ya fita ta kai duban ta ga Alh ta ce’

“Kaga wata Anty ta Maijidda ta aikomin da naman layya”.
Ya ce’

“Kin gode Allah amfana”.
Cikin hakan sai da ta kusa cika wata roba da nama na mutanen da ta kira su kawo Mata layya.
Nan ta Kai duban ta ga robar naman tana ta sak’e-sak’e cikin ranta.
Ta ce’

“Da ace Anty *Ybk* na Nigeria da k’ila ko bata bani k’afa ba zata bani rabin k’afa”.
Sai da Safiya ta ta6o tane sannan ta zabura da k’arfi.
Safiya ta ce’

“Ki duba kigani rabon da nayi in ya yi sai ki d’auki naku”.
Tana dubawa nan ta ke ta ce’

“Ai ya yi ma hakan Anty, Allah mai-mai ta mana”.
Ta ce’

“Ameen”.

Amma fa yau duk mamakin Hafsat ya cika Mata ciki, wadda duk shekara sai an yita rigima da ita tana cewa an zalunce ta ita da yaran ta.
Wani lokaci ma sai Safiya ta ebi nasu rabi ita da yaran ta ta k’ara Mata.
Sai gashi yau uffan bata ce ba, amma tasan hakan ya faru ne sanadiyyar naman da ta samu.
Alh ya shigo ya ce’

“Duk su kauda kayan su za’a shigo a wanke gidan sanadiyyar aikin da aka yi.
Nan suka had’a kayan su suka koma falo, sai magrib yaran suka k’are wankin gidan.
Nan Alh ya sallame su suka wuce don su takwas ne.
******
Tun tana jin sallamar mutane tana zabura domin dubawa har ta Kai ko taji sallama sai dai tabi k’ofa da kallo.
Har magriba ta ji shiru ba aike daga gidan Alh Abubakar, duk mamaki ya ishe ta ji take yi tamkar ta figi hijab taje gidan.
Usama ta Kira ta ce’

“Yaje gidan Alh Abubakar ya duba Mata sun k’are *Rabo* ko da saura”.
Ya ce’

“Wallahi Mama sun k’are har an Kira almajirai sun wanke gidan”.
Uban tagumi ta rafka ji take yi tamkar ta d’ora hannu a ka ta ta buga ihu.
••••••   ••••••  ••••••  •••••••
Safiya ta fito tana rafka salati ta ce’

“Kin ga yau anyi *Rabon* nama an manta da gidan Mal Yusha’u”.
Jin hakan yasa ta had’e rai tamkar ba zata yi magana ba.
Safiya ta ce’

“Ki d’an ebo naki mu had’a a aika musu”.
Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta wuce kitchen.
Uban salatin da ta rafka yasa Safiya ta bita kitchen d’in.
Ta ce’

“Meke faruwa hala?”.
Hafsat ta ce’

“Wallahi ko kaffara ba zanyi ba almajiran da suka yi wankin gida suka sace min robar naman *Rabon* da na samu”.
Jin hayaniya yasa Alh ya fito yana tambayar meke faruwa?”.
Nan ta Kora Mai bayanin abinda ke faruwa.
Bud’ar bakin Alh ya ce’

“Dama ba *Rabon* ki bane na mabuk’a tane, kwad’ayi kawai ya Kai ki”.
Daga hakan ya koma d’akin shi.
Nan dai Safiya ta ja-jan ta Mata ita ma ta Kama gaban ta.
“””   “””  “””  “””
Tana zaune ta rafka uban tagumi sai sauraren nasihar Mal take yi.
Sai ga yaro ya shigo da nama k’ulle ga farar Leda.
Bayan ya gaida su ya ce’

“Wai gashi Umma ta tace in kawo maku, kuma tace kuyi hak’uri mantawa aka yi”.
Nan maimuna tasa hannu ta kar6a ta ce’

“Kace mun gode sosai Allah ya nuna mana wata shekara”.
Fitar yaron kenan Mal ya bud’e baki zai yi magana Maimuna ta tari numfashin shi.
Ta ce’

“Ba sai kace komai ba wannan sallar ta zamo ishara a gare ni, tabbas Rayuwa juyi-juyi ce kwad’o ya fad’a ruwan zafi”.
  Daga taskar y’ar mutan Jega’

*SDY* *JEGAL*
*SADAUKAR* *WA* *GA* *MAKWAD’AITA*, “`LOLX“`
*HAPPY* *EID* *EL*- *KABEER*😘.

KALUBALE

​[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 
                1

A hankali nake saukowa daga matattakalar jirgin saboda tsoron kar kafata ta zame ko na fado, hannun damana ‘yar ‘karamar jakata ce wacce ake kira (Gari yayi zafi) na hagun kuma rike nake da Kawata Farida wacce muka hadu acikin jirgi , itama a hankali take takawa ga dukkan alamu itama tsorone fal a zuciyarta, ina ganin hakan ya samo asali ne dalilin wannan shine hawa jirginmu na farko  dagani har ita. 
Muna sauka na hango wata ‘katuwar mota mai kama da jirgi tazo daukarmu. Nace’ “Farida kalli wani dan karamin jirgi”  tace “ke dalla ba jirgi bane mota ce, saboda na tab’a ganin irinta a wani film na India tun sadda muna zuwa kallo gidan Asabe amaryar unguwar mu kafin Marka ta hanani zuwa , wai saboda taji ance… kafin ta ‘karasa mukaji wasu mata na cewa ” wai ku bazaku shigo bane kun tsaya surutu sai kace anan zaku kwana? 

Da gudu muka shiga , saidai abin mamaki ni banga gurin zama acikin motar ba , domin kowa a tsaitasaye na gansa , sai wani k’arfe da ake mika hannu arik’e gudun fad’uwa. 

Haka na mika hannu na na rik’e k’arfen nan d’ayan hannun kuma ina rike da Farida , itama gam ta rik’eni  saboda dukkanmu matsorata ne 

A tunanina zamu kai  minti goma zuwa sha biyar a motar nan , na matsu naga anzo  Makkar da nake ta jin labari agurin Uwani, da kuma abubuwan ci, da na sha ,da shinkafa kazar da naji mutane suna yawan fad’a

“Farida wai bamu iso makkan bane? Kiji Wasila da wata tambaya ” niko ina zan sani tunda ban tab’a zuwa ba, nace Allah ya baki hak’uri na san ba komai bane ke damunki face yunwa idan kikayi hak’uri mun kusan zuwa muci shinkafa kaza 

Na tab’o wata mata a kusa dani nace’ “baiwar Allah dan Allah bamu iso makkan ba ?”. 

 Tayi dariya tace’ “makka kuma yarinya? ai  tun d’azun muka iso makka jirgin da ya ajemu dazu ai Jidda ne ya ajemu  yanzu haka  gurin bincike zamu tafi kana kuma a kaimu masaukinmu”.

 

Ba afi minti 2 da yin wannan maganar ba motar ta tsaya muka sassauka 

Na tsorata sosai da ganin mazan gurin kowa da kayan sojoji , wannan karon bamu kadai muka tsorata ba harda wasu daga cikin matan da mu kazo  dasu……
*DAGA TAKU*

                *MAMAN JA’AFAR*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

    

            2 

     
Saboda  wani wargadeden fili ne kuma ko ina ka waiga wad’annan masu kayan sojojin ne suke kai komo 

Mudai sai zare idanuwa muke damu da kuma sauran k’auyawa irinmu 

Suko wayayyun naga gurin wata Kanta suke nufa suna mi’kawa sojojin wani litattafi   suna yin rubutu akai suna mayar masu 

Kai wai mi kuka tsaya yi ne? ba zakuje ku kai fasfot d’in naku a bige ba ku tafi ? Cewar mijin bizar mu kenan wato Abba.

Farida ce ta mayar masa da tambayar “ina zamuje? Tana ta zare idanuwa 
“Can zakuje inda ku kaga mata na layi, ba gurin mazan ba” ya fada yana mai nuna mana gurin da yatsa

 

“Farida zo mu tafi kinga gun da layi ma sosai, gashi  yunwa ta fara damu na”, 
 harara ta dalla mani gami da cewa ” keda d’azu kike gaya mani bak’ar magana a mota dan kinga nayi shuru shine yanzu zakice mani wai kina jin yunwa ? Nidai mutafi ”

Bayan dogon layi da muka bi aka karbi litattafin hannun mu wanda d’azu naji Abba ya kirasa da fasfot sojan yayi rubutu akai ya buga wanu abu kuma ya bamu muka tafi. 

To nanfa ake yinta domin bamu san inda zamu ba.
“Wasila ga wani dakali can zo muje mu zauna kafin mu samu aron waya mu kira lambobin da aka bamu
Bamu dad’e da zama ba saiga wani ba’kin mutum k’ato yazo kusa damu” Assalamu alaikum ‘ a tare muka amsa masa gami da yi masa  kallon tsoro 

Ku mik’o mani fasfot d’inku”. 

Da mamakin mu mukace
“Malam ya bamu sanka ba yau muka fara ganinka zakace mu baka fasfot?” To ai shikenan tunda baza ku bada ba ko kun tafi sai an maido ku nan,  

“Kinga Farida mu basa kawai tunda yace mu basa tunda kinga bamusan kan garin nan ba”. 

Muka mika masa ya tafi 

Ba afi minti goma da tafiyarsa ba saiga wata mota tazo aka ce mana mu shiga a kaimu masauki 

Dad’i ne ya lullub’e mu ganin mun samu mafita 

Saidai wannan motar sab’anin waccen domin ita wannan k’arama ce amma fa zata dauki mutum kamar 50

 Bata tsaya ko ina ba sai wani k’aton guri da naji wasu acikin motar suna cewa masa hotel, muka sauka wani ma’aikacin gurin yayi mana jagora gami da nuna mana dakunanmu 

Dakinmu mu 5 dani da Farida da kuma wasu mata su 3 wad’anda duk zasuyi sa’ar iyayenmu 

D’akin madaidaici ne domin katifa 5 ce a ciki sai wani fanfo a gefen d’akin sai kuma ban d’aki acan kuryar d’akin, da fanfuna, da wani k’aton baho, da kuma wani tiyo a can sama an mak’ala masa wani  abu ajiki kamar rariya 

“Farida Farida Farida ”  ce mani tayi “ke lafiya kike ta kwala mani kira bayan gani kusa dake”?. 
Nace’ “leko kiga wani kalar ban d’aki, aradu ko a cikin tv ban tab’a ganin irin sa ba”, 

Dariya tayi kana tace mani 
 “to aje jakar tukun sai muje mu kalla ” 

sai a sannan na lura ashe jakar tawa tana kaina ko ajeta banyi ba……..
*DAGA TAKU*

           *MAMAN JA’AFAR*.

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             

           3
Nasamu guri gefen wata farar kujera doguwa na aje jakara tawa,  muka samu gefen gadonmu muka zazzauna 

“Farida ya maganar yunwa nifa ta damen?i”

 “hmmm  ke yunwa ta dama koni? Tunfa a jirgi nake jin yunwa sosai saboda ni wannan abin da aka bamu a jirgi ban daukesa abinci ba , domin mu a garinmu wannan ciyawa-ciyawar abincin dabbobi ne ”

“nima gaskiya ban taba ganin ana cin kalar wannan abincin ba a garinmu , saidai kuma wannan ganyen yana yi mani yanayi da rama, da yakuwa,  da kuma ya’diya” 
“kinga Wasila yanzu dai wannan surutun bazai kaimu ba muyi tunanin inda zamu samu abinci kawai”

” hmmmm waike Farida  da kike maganar abinci  kinada kudi ne ? Bakiga kowa siyowa yakeyi ba?”

 “Ni matsalata ma bata wuce Uwani tazo ta daukemu ba .

Muna nan muna surutu har matan dakinmu duk suka watse, suka tafi gun wadanda suka kawo su , ga dukkan alamu su sunada waya 

Nace “kinga Farida munyi batan basira da mun sani da mun ari wayar wadannan matan mun kira su Uwanin  da kuma…… wama kika ce wacce ta kawoki?” 

” Harira” sunanta, 

“kinga Wasila zo mu sauka daga kan benen nan musami abinci kawai ”

Muka  rike hannun juna muka sauko kasa daga wannan benen mai tsawon gaske, saida muka sauko ne muka lura ashe wani abu mutane suke hawa mai kamar gida-gida yana hawa dasu yana sauka dasu

Mun ” karaci  yawonmu amma bamu samu abinci ba, muka dawo muka kwanta , saidai bacci ya gagaremu  domin sai ciki ya dauka ake samu ayi bacci
“Wasila yanzu haka zamu zauna bamu san mafada fa ba? 
“Nidai bara na tashi na nemo a ron waya na Kira Harira tazo mu tafi ” 
“ya zaki tafi ke kadai jirani mana mutafi tare nima ai ba zaman hotel ya kawoni ba” 
na mike gami da saka silifas dina da dan guntun hijabina ” itama ta saka nata muka fita muka tun kari wani namiji da yake tasaye yana waya
“Dan Allah malam aron waya zaka bamu mu kira wadanda suka kawo mu nan ” muka fada yayinda muka karaso gunsa
” ku baku iya sallama bane? Haiwanat” 
Mukai gaba muna kunkuni ” Kaine hawainiya ba mu ba……
DAGA TAKU MAMAN JA’AFAR

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

   

  

                 4
***Bamuyi nisa ba muka sake haduwa da wani saidai shi a zaune muka samesa” malam ina wuni? “Ke Farida kin manta saboda bamuyi sallama ba wancen mutumen yace mana hawainiya?” Gafara dai malam ” mutumin ya waiga baiga kowa ba daga mu sai shi ” Ish’mishkila? Cewar mutumin  ” Wasila wannan anya kuwa  bahaushe ne ?” kema da ganinsa ai kinsan ba bahushe bane  kodai inyamuri ko kuma wani yaren” , ke inagafa irinsu ne ake cema larabawa baki gansa fari tas ba kamar zabaya? Na kwashe da dariya harda rike ciki, “Inti Majnuna?” Cewar mutumin gami da kallona”  oho koma dai Mejo ne kai kasani ” kinga Farida zo mu’kara yin gaba ko masamu bahaushe.
Saida muka fita daga cikin hotel din kana muka samu wani mutum baki yana waya kuma da hausa yake magana awayar, ” Gafara dai Malam ” Sannunku ‘Yan mata daga ina haka? ” daga wannan gidan muke na fada gami da nuna masa kofar hotel din,  dan Allah aron waya zaka bamu mu kira Uwani da Harira ” su waye kuma Uwani da Harira ?” Sune suka kawo mu nan ” ok ku kawo lambobin nasu na gwada nagani ko zasu shiga”  Farida ce ta fara mika masa tata lambar ” ya karba gami da lallatsa wani guri acikin wayar tasa, ” na jawo Farida kusa dani  na rada mata a kunne , nace”  Farida kalli wayar tasa batada malatsai da hannu yake saka lambobin ” nima dai mamaki naketayi tun dazu Wasila” 

Kai kuna ina? Ina Farida take a cikinku?”muka rugo a guje Farida tace gani” yauwa karbi waya ana son magana dake ya mi’ka mata wayar” alo alo Harira kina jina? ”  Eh nice Farida Harira”,  gamu nan fa munzo makka din tun da safe muka iso ko abinci bamuci ba kuma yunwa mukeji” tadan saurara kadan, kuma sai taci gaba da cewa” nida wata ‘kawata ce Wasila a jirgi muka hadu” to gashi”ta mi’kawa mutumin wayar” 

Ehwa mafi mishkila” na’am”  suna nan Shar Mansur ne ” sai naga yadan saurara kuma yaci gaba da cewa ” sunan Hotel din Lu’ulu’u anwarul-rauda” sai kuma naji yace khalas ma’assalama sai kinzo” 

Nidai ban fahimci wasu kalaman nasa ba naga ya kashe wayar 

Ke ‘yar farar nan ya fada gami da nuno ni da yatsa kawo taki lambar”

Kubiyo ni donjin cigaban labarin!

Mmm jafar

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             

                 6

 

***”Dalla malamai kuyiwa mutane shuru , dabbobin ina ne ku?” 

Tsawar da ya daka mana ce ta dawo damu cikin hayyacin mu

Tuni na sakesa amma hannuna bai rabu dana Farida ba 

Ba’afi minti daya da shigarmu wannan gidan ba wanda acikin fadan mutumin  naji yakirasa da suna (lifta) sai gamu mun iso har kusan kofar dakinmu ya nuna mna dakin  yace “ku shiga yanzu zan kawo maku abinci ”
Muka shiga muka zazzauna muna tsammanin wa rabbuka  

“Farida kin lura da wannan kujerar ta kusa dake kuwa?” Na fada ina nuna mata kujerar
” a’a miye acikinta ?
” Ganinta nayi kamar za’a iya bu’deta” 
“Kai Wasila kujerar za’a iya budewa? To bara na gwada bu’dewa  nagani….katseta tayi tare da cewa 

“La ha ila”  Farida zo kiga abinda ke ciki” da mamaki karara a fuskarta

” dauko mani na  gani daga nan dan yunwa bazata barni na tashi ba” 

Rufe bakina keda wuya sai mukaji ana ‘kwan’kwasa mana ‘kofa natashi naje na bu’de wanda nake tsammani kuwa shine domin wannan mutumin na gani da leda a hannunsa ga dukkan alamu abincin ne aciki” 
“Ke! Basira kike ko Wasila karbi abincin nan, akwai sifra a ciki (ledar da ake shinfidawa azuba abinci akai)sai ku shinfida ku zuba abincin akai  kuci” 

Na kalli Farida itama ta kalleni alamar muna tambayar juna da ido” kuma ga tallaja nan a bayanki (Firiza) ke Farida ku bu’da akwai asir (lemun gwangwani) da ruwa aciki sai kusha” ya fada yana nuna mana firiza

“Farida kin gane abinda ya ke nufi?” A’a wallahi wasila ban gane ba” 

Malam bamu gane bayanin naka ba” ‘karasowa cikin dakin yayi gami da bu’de ledar abinci ya fiddo wata farar leda mai dan fadi ya shinfida, kana ya zuba shinkafar akai da kuma kazar 

Ya bude wannan doguwar kujerar wacce na aje jakata a kusa da ita ya dauko wadanan abubuwanda Farida take  ce mani nazo na gani ‘dazu 

Wata doguwar roba ce ya dauko guda 2 wanda ga dukkan alamu ruwa ne a ciki” sai kuma wasu gwangwanaye suma guda 2 amma ban fahimci miye a cikinsu  ba 

Mudai ba ta wannan mukeyi ba abincin kawai muke hari 
Nanfa muka fara ci haya yam  haya yam tamkar bamu taba cin abinci ba 
“Farida wannafa itace shinkafa kaza” cewar Wasila kenan bayan ta cika bakinta da cinya 

“haba?” Cewar Farida kenan bakinta cike da shinkafa
“Aiko taci sunanta” bakinta cike da loma take fadar haka , 

kamar yanda nima nawa bakin haka yake ” 
“To bayin Allah kusha ruwan mana ko asir din dan karku ‘kware” 

“ai bamu iya bu’dewa ba” inji Farida 
Ya bude mana muka fara sha, muna cin shinkafa kaza muna ha’dawa da asir  har muka gama  batare da munji kunyar mutumin da keyi mana kallon mamaki ba

“Malam mungama ina zamu samu almajirai mukai masu wannan sauran?” 
Yayi dariya gami da cewa  “Wasila ai nan babu almajiran da ake bawa abinci idan an rage,  sai dai akai zubala”  

Nace “minene zubala kuma ?” 

“Inda ake zubar a shara” ya fada yana murmushi
Na zaro ido waje nace “harda kazar?” Yana murmushin dai yace ” eh ko ‘dawisu nema” 
“Yanzu dai ba surutu ba , ku tashi kuyi sauri kuyi salla kafin azo daukarku” ya fada tare da daure fuska……
Kubiyoni donjin cigaban labarin

DAGA TAKU 

MAMAN JA’AFAR

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             5

***Natashi a hanzarce naje gunsa gami da mi’ka masa tawa lambar dukda bai tambayeni ba 

Ya karba gami da saka lambar acikin wayar tasa 

Can naji yace” Assalamu alaikum , Uwani ce (kamar yanda yaga an rubuta a jikin lambar tawa) ” sai kuma naji yace a’a ba shi bane , wata yarinya ce um…ke miye sunanki? ya fada gami da nuno ni da yatsa” Wasila zaka ce mata ai tasanni tun… ” ke yimana shuru ya fada yana kallona gami da ci gaba da wayar tasa 

Wasila sunanta” eh gata nan kusa dani” suna nan makka ne a shara mansur hotel din lu’ulu’u anwarul rauda ” ok gata nan “ke karbi waya” 

Na karba ina washe baki saboda ban taba rike irin wannan wayar ba tunda nake ” 

Eh Uwani nice Wasila ‘diyar Hajara ai kin ganeni ko?” Wasila kunzo lafiya ko?” Lafiya lau amma dai yunwa mukeji dan rabona da abinci tun ‘dumamenda Haja ta bani naci kafin su Affa su rakoni kano” kai Wasila ga dukkan alamu zakiyi shiririta, to yi hakuri yanzu zanzo in tafi dake 

Na mika masa wayar da naji shuru inata alo alo ba amsa”

Ya karba tare da sakata aljihu” to ai sai ku tafi masaukin naku kfin iyayen naku suzo ko?” To na fa’da gami da kiran Farida nace zo mu koma ciki ” tab aradu Wasila bazan iya hawa wannan benen ba saboda yunwa taci karfina” nima dai kam yunwar nan nadamuna” Au wai dama baku ci abinci bane tun zuwanku?” Cewar wannan mutumin  kenan wanda bamu sanma yanajin abinda muke fada ba saboda ‘yar tazarar da ke tsakaninmu 

Wallahi bamu ci ba, ko sallama bamuyi ba” 

Nawa ne lambar dakin naku?” Um..um.. Farida  kin rike lambar da Mijin bizarmu yace mu rike dan karmu ‘bata?”

Inafa na rike, wallahi na manta , saidai ga wata takarda nan wacce aka bamu ta lambar , ta cirota a hannunta da ta daure kamar dan hannu ta mika masa

Ya karba tare da dubawa, hawa na 10 ne kuke daki mai lamba 15 ko?” Eh muka fada gami da gyada kai kamar ‘kadangaru duk bamusan abinda yake nufi ba 
To mu tafi nakaiku dakin naku tunda nasan ba ganewa zakuyi ba 

Muka bisa zungui-zungui har muka shiga cikin hotel din 

Amma abinda ya bamu mamaki gami da daure kai shine 

Wani dan gida-gida ya shiga yace muma mu shigo” Wasila ina kuma zai kaimu?”hmmm Farida kenan ai saidai mu kwana muna tambayar juna , amma dai mu shiga mu gani 

Shigarmu keda wuya sai mukaga abin ya rufe da kansa , shiko wannan mutumi da bamu san sunansa ba ya danna wani madanni ajikin bangon dakin sai mukaji shuuuuuuu yana sama-sama  

Wayyyo Allah na fada gami da cukuikuyesa ”  itama Farida gam ta rikeni tana runtuma ihu 

Shiko abin sai sama-sama yakeyi
Kubiyoni donjin cigaban labarin!!

DAGA TAKU 

MAMAN JA’AFAR

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: [💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             7

  
***Bayan mun gama ‘kauyancinmu a ban’daki muka fito muka kwakkwa’ba sallarmu , duk dai mutumin nan yana nan zaune a gefen gadonmu 
Bayan mun idar ne yayi gyaran murya gami da cewa 

“Wasila da Farida ku natsu inaso nayi maku wata tambaya ”
Amma kafin hakan bara na fara gabatar da kaina agareku
“Nidai sunana Yusuf, shekaruna 28  asalina dan najeria ne ni,  a wani gari mai suna katsina,  a wata unguwa wai ita Sha’iskawa,  anan hotel din  nake aiki , yanzu haka shekarata 5 anan ku kumafa?” ya karashe zancensa da kallon mu ga dukkan alamu amsa yake jira .

*********************
“Nidai sunana Wasila nima kusan yar najeria ce amma kuma ta wani bangaren zan iya cewa ni yar nijar ce 
Domin kuwa garinmu ana kashe ku’din najeria  kuma ana kashe kudin nijar 

“Sunan garin namu DANKAMA  daga katsina zuwa garinmu kuwa baifi tafiyar awa daya da rabi ….” 
“Ok naji Wasila amma bantari hanzarinki ba ” yaya akayi kukazo nan ‘kasar ku ka’dai batare da kowa naku ba?”  

A’a ni ka’dai nataho ita Farida a jirgi ne muka hadu da ita 
Ok ina jinki, bani amsar tambayar da nayi maki ” 
Uwani anan makka take da zama amma tana zuwa najeria lokaci zuwa lokaci tana kawo mutane nan ‘kasar tana sakasu a gidan aiki ana biyansu 
Kuma wallahi Malam Yusuf suna samun ku’di sosai domin zakaga har dubu 10 ko 20 suke aikowa yan’uwansu duk bayan wata 5 ko 6 na fada tare da kallonsa” hmmmm ya fada gami da yin murmushin da bai kai zuci ba , ko kuma nace ya’ke ina jinki Wasila ci gaba 
To a irin hakane wata rana tazo ziyara kamar yanda ta saba, tazo gidanmu sayen alale,  da yake dama Hajara mahaifiyata alale ne sana’arta 

Ta cewa Hajara mizai hana ki bani wannan “yar taki  na kaita makka tasamu abinda zatayiwa kanta kayan ‘daki ta rufawa kanta asiri kuma ta rufa maku,  ke harma yan’uwanku zasu amfana da ita indai kuka amince ” 
Haka naji tana fa’dawa Hajara a daidai lokacinda nake zuba ruwa a randa wanda na ‘debo a rijiyar bayan gidanmu 
Aiko Uwani idan kikayi mana haka kinyi mana komai a rayuwa domin dama wahala ta ishemu abinci ma wannan gagararmu yakeyi bare kuma sauran bu’katunmu
Domin mahaifinta ma  ba wani abin kirki yake tsinana mana agidan ba,  dako ne sana’arsa amma duk da haka kullum cikin kiran babu yakeyi 
Haka dai naji mamata Hajara tana fadawa Uwani ina zaune gefensu ina saurarensu 
Uwani ce tace indai kin amince to kakarku ta yanke sa’ka 

Amincewa kai , bari ma Malam ‘din ya dawo yau yau ‘dinnan zan sanar masa gobe sai kizo kiji yanda akayi 
Baffa yana dawowa daga gun dakonsa Hajara ta samesa da wannan bayani ” da farko dai bai amince ba amma da ta kwa’daita masa alherin da ke cikin tafiyar ya gamsu kuma ya amince 
Niko ta ‘bangarena abun 2 ya zame mani ” inaso na tafi makka  domin na wataya naji dadi na huta da surfe , daka , “diban ruwa da sauran ayyuka 

Kuma ta wani gurin banaso na tafi nabar kawayena su Indo da Lantana da Sahura wa’dan da muke zuwa fage dasu da dare (dandali)
A haka ta gama shirya mana komai nida ita na tafiya 

Saidai kamar yanda naji yan garinmu na fa’da wai tata bizar ta riga tawa fitowa saboda haka zata rigani tafiya 
Bayan wata  ‘daya da gama shirye’shiryenmu Uwani ta taho nan 

Amma tana kirana da wayar Ado ‘dan mai gari , ta wayarsa ne ma ta aiko mani da lambar tata….. 

Ya katseni gami da tambayar baki da ‘kanne ko yayu ne?” 
“Inada yayu mana 2 amma duk maza ne ankaisu alamajiranci katsina ”
“Shekarunki nawa yanzu Wasila ?” Ya tambayeni gami da yi mani kallon tausayi 
“Nadai ji Hajara nacewa wai shekaruna 14” 
Hmmmm  lallai rayuwarku tana cikin garari, ya fada acikin ransa
“Ke kuma Farida ya akayi kikazo nana ‘kasar?” Ya tambaya gami da mayar da kallonsa gun Farida 

Ta numfasa tace 

Nidai…..
Labari yanzu aka fara kudai ku biyo ni

DAGA TAKU
MAMAN JA’AFAR

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

  

        10

      
Shigowa nayi ‘dakin tare da yin sallama kamar yanda Yusuf ya koya mana” 
Lale maraba da ba’kuwa’ cewar na cikin ‘dakin ” 
Sannunku ina wuninku ?” 
Lafiya lau ba’kuwa , ya hanya?” Suka amsa kusan a tare 
Lafiya ‘kalau na fa’da tare da zama a ‘kasa domin banga kujerar zama a ‘dakin ba , sai wasu ‘kana nan Katifu na gani kamar na yan makarantar kwana a gefe da gefe a shisshinfi’de, ga dukkan alamu wasu ne ke kwanciya a gurin” 
Sakina ga ‘kanwa kun samu dan baza a kirata da ‘kawa ba domin duk kun girmeta nesa ba kusa ba” cewa Uwani kenan .
Wacce aka kira da Sakina ta tashi ta kawo mani ruwa da asir nadan kurba ka’dan” 
Muna tare da manyan matan sai kuma ga wasu ‘yan matan su 3 sun shigo da murnar su suna yi mani sannu da zuwa ” 
Ni sunana Hadiza” inji yar gajeruwar” ta dafa kafa’dar ta kusa da ita  tace wannan kuma sunanta Aisha, waccen kuma ta gaban talmizon(Tv) sunanta Suwaiba” da fatan zaki saki jikin ki damu ?” Ta tambaya gami da dafa kafa’data.
Murmushi nayi gami da ce mata ai mun riga mun zama ‘daya tunda gamu ma a gida ‘daya” 
Khala Uwani (Aunty)ba’kuwar taki taci abinci kuwa?” Cewar Sakina kenan ” 
Eh taci amma ban sani ba ko tana jin yunwa”
ku tafi ‘dakinku da ita  ‘kilan zatafi sakewa acan”  cewar wata mata danaji suna kira da Khala Furera kenan” 
Suka mi’ke gaba ‘daya suka ce mani taso mu  tafi ba’kuwarmu” 
Haka na bisu zungui-zungui har ‘dakinsu” 
Babban ‘daki ne ba laifi sai dai babu wasu kaya acikisa sai diloli a jijjingine, sai ko yan katifun yan matan, da akwati nan su a gefe , sai kayan kwalliyarsu kowace nata na gefen jakarta”
Zauna mana ba’kuwarmu kin yi tsaye , ai kin zama yar gida yanzu” cewar Aisha kenan
Kishingi’da nayi abakin wata katifa domin bacci ne kawai a idanuwana gami da gajiya” 
Wasila bacci kike ji ne ?”  Ki bari kici abinci mana ga indomi can Suwaiba ta ‘dora maki” cewar Sakina kenan wacce duk tafi yi mani fara’a a cikinsu 
Wasila kodai zakiyi wanka ne kafin ki kwanta?” Aisha ce ke fa’dar haka yayinda ta ‘dauki jaka tana nema mata gurin zama ” 
To bara nayi wankan sai naci abincin kafin na kwanta dan bacci nakeji sosai wallahi, mu a garinmu ai kamar yanzu mun da’de da yin bacci , ku kalli fa agogo kusan  ‘karfe 1 na dare kenan , na fada ina cire hijabina ” 
Dariya naga sunayi su duka” 
Ai mu nan Wasila wani lokaci har safe muke kaiwa bamuyi bacci “cewar Aisha kenan 
Wai ! na zaro idanuwa, gami da ri’ke ha’ba, kuma duk me kukeyi har safe bakuyi bacci ba sai kace aljannu?” 
Suka kwashe da dariya” 
Fira kawai mukeyi ko kallo ko kuma catin da samarin mu” cewar Aisha kenan 
Tab ni kam inma badan wannan tafiyar ba kamar yanzu ai nayi juyawa 3″ 
Suka ‘kara tuntsirewa da dariya” 
Nidai yanzu ku nuna mani magewayin nayi wankan” 
Muje na nuna maki cewar Sakina kenan” 
Nashiga magewayin ina duddubawa kamar mai neman wani abu ” 

Ba komai nake dubawa sai ganinsa da nayi duk siminti ne ba wannan fari-farin abin ba irin na hotel” 

Hakanan na bu’da fanfo natari ruwa a bokiti na warwatsa na fito zuwa ‘dakinmu” 
Kafin nazo har Sakina tayi mani shimfida ta aje mani wasu kaya asaman yar katifar tawa” 
Na ‘dauki kayan ina duddubawa,  riga ce wata yar ‘karama sai kuma wani wando kamar na rana” 
Wannan kayanfa?” Na tambaya gami da kallonsu daya bayan daya 
Naki ne ki saka zakifi jin da’di ” cewar Suwaiba kenan dake gefe guda tana ta daddana wayarta ko mi takeyi oho” 
A haba sai kace wata  ‘yar iska,  nasak wa’dan nan kayan?” 
Wallahi Wasila kina bamu dariya saboda wannan ‘kauyancin naki” cewar Aisha kenan 
Ai maganar gaskiya ce , nidai ku barni nasaka kayana inada su acikin jakata” 
Dan Allah Wasila ki saka Allah anan ‘kasar kusan kowa irinsu yake sakawa , kodai riga da wando irin wa’dan nan ko kuma gamisa (doguwar riga) cewar Sakina kenan 
To ku bani gamisar nasaka zata dai fi wa’dannan ” 
Waike da kina nufin da riga da zani zaki kwanta bacci?” Suwaiba kenan ke fa’dar haka tana tuntsira dariya” 
Au ba’a bacci da riga da zani ne” 
A ‘kauyanku ne ake yi bacci da da riga da zani ko” Aisha ce mai fa’dar haka” itama dai dariyar takey i 
Wai ya zaku sakani a gaba kuna yi mani dariya sai kace wata mahaukaciya ?”  Na fada tare da ‘daure fuskata  
Allah ya baki hakuri ga gamisar ‘dauki ki saka ” cewar Sakina kenan 
Na’dauka na saka na ‘dora hijabina akai ” 
Indomi Suwaiba ta kawo mani da kwai, naci nayi nak” nace masu bara naje nayiwa su Mama Uwani saida safe suka amsa mani da to” 
Na le’ka ‘dayan ‘dakin inda manyan gidan suke tare da yin sallama” 
Ga mamakina sai naga su duka duk kallo sukeyi babu wata alamar zasuyi bacci yanzu” 
Mama Uwani zan kwanta sada safenku ” 
Har zaki kwanta  Wasila da wuri haka?” Cewar Khala Furera kenan 
Khala Furera yanzu fa kusan ‘karfe 2 na dare shine har zan kwanta da wuri na fa’da ina murmushi” 
Kai Furera kin manta ba’kuwa ce , sai a hankali zata saba,  ga kuma gajiyar tafiya, jeki ki kwanta Allah ya bamu alheri” 

Amma ki tashi da wuri saboda su Sakina zasu rakaki Harami ki kai Umra” cewar Mama Uwani kenan 
Na amsa da to gami da sakar masu labulen” 
Na koma ‘dakinmu na haye kan shinfi’data na kwanta” 
Ga mamakina sai naga Yan matan babu niyar bacci a tare dasu,  domin ganin Aisha nayi can a loko tana yin  waya  ‘kasa’kasa” 

Itako Sakina mutuniyata kallon Tamsiliya takeyi kamar yanda naji sun fa’di sunan kallon (fina finan Zee alwan)
Itako baiwar Allah Suwaiba qur’ani naga ta ‘dauko tana karantawa t abin gwanin sha’awa” 
Nidai banfi minti 10 da kwanciya ba bacci barawo ya saceni”

G

*DAGA 

  TAKU 

MAMAN JA’AFAR
Domin tsokaci ko gyara 

+ 966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             9

Au ashe bake ka’dai bace ba a ‘dakin ?” 
Sannunku dai yara ”

Yauwama mama  sannu ina wuni ” cewar Yusuf 

Lafiya lau yaro , ya aiki ?” 

Lafiya lau mama” 
Wasila wannan kuma wacece a zaune ko itace wacce kika ce mani kuna tare wama sunanta kikace?” Ta tambaya gami da kallona 

Sunanta Farida itace wacce muka ha’du a jirgi” 

Allah sarki ,sannu yarinya” 
Yauwa Uwani Uwani,  ina wuni ?” 
Waiku baku iya girmama manya bane , wannan ba ta haifi kamarku ko wa’danda suka fiku ba amma kuke kiranta da sunanta ba girmamawa bakomai?” 
Murmushi Uwani tayi gami da cewa ,  kasan mutanenmu na “kauye sai a hankali zasu fahimci komi” 

Ke Wasila daga yau karki sake kiranta da sunanta Uwani mama zakina kiranta” ya fa’da gamida kallona 
Na amsa da to” 
Malam ko kaine wanda ya kirani a waya ya kwatanta mani nan?” 
Eh Uwa…Au mama shine ya kiraki kuma hardama abinci ya bamu mukaci muka ‘koshi har mukayi saura muka zuba inama?” Na tambaya gami da kallonsa 
Shara ” 
Sannu da ‘kokari yaro angode k’warai Allah yasaka da alkhairi” 
To ke Wasila ‘dauko kayanki ki tashi mutafi mai lomazin yana jiranmu a waje (motar haya)” 
Idanuwana sukayi narai-narai  kamar zanyi kuka,  nace mama bai kamata mubar Farida anan ba da mun’dan jira ka’dan har azo ‘daukarta itama tunda itama Harira din yanzu tace zatazo” 
Gaski kam  , da babu damuwa sai ku’dan jira azo a ‘dauketa din itama” 
To babu matsala yaro bara mu jira ‘din 
Ita ko Farida gani nayi tayi shuru kamar me wani tunani,  nima dai na’dan shiga damuwa ganin nanda minti ka’dan zamu rabu” 
Wayar Yusuf ce tayi ‘kara ya dauka tare da karata a kunne” 

Eh nan ne, ‘daki mai lamba 15 ne ” 

Shigo nan ‘din ne ” 
Aje wayarsa keda wuya ta ‘kwan’kwasa ‘kofa” 

Dama shine a kusa da ‘kofar ya bu’de mata tashigo gami da sallama ” 
Sannuku bayin Allah ina wuninku?”

Lafiya lau ina gajiya” 
Wacece Faridan ne acikin ku na ga kusan duk girmanku daya” ta fa’da tare da rarraba idanuwa tsakanin nida Farida” 
Ga ‘diyar taki can ” wannan kuma Wasila sunata amma tare suke tun a jirgi ” cewar Uwani gami da nuna mata Farida 
Farida taso mana inganki kika la’be a loko sai kace baki murna da ganina ba ” 
Murmushi Farida tayi gami da fa’din a a ba haka bane Mama Harira banaso mu rabu da Wasila ne shiyasa tunda mamarta tazo jikina yayi sanyi” 
Allah sarki ai ba wanda zai rabaki da ‘yar’uwarki ki saki jikin ki yanzuma zan karbi lambar mamar taki idan nasiyawa Wasila waya sai ku ringa zumuncin ku ” cewar Uwani.
Da gaske Uwani zaki siya mani wayar?” 
Ja’irar yarinya da karya zanyi maki?” 

Mukasa dariya harda Yusuf” 

Nima mama Harira zaki siya mani wayar mu ringa gaisawa da  Wasila ?” 
‘Kwarai kuwa ‘yata , irin ta wannan mutumin ma zan siya maki musamman idan kikayi hakurin zama gidan aiki” 
Hmmm Harira muntsaya munata surutu yakamata mu tafi hakanan a waya sa ‘karada shiriritar tasu” 

Gaskiya kam Uwani” 
Harira a wace unguwa kuke ne?” Cewar Uwani” 

Anan kusa muke a ‘yalbarno”  ke kumafa?” 

Nima dai ba nisan ni dani ba , anan Billadi nake” 
To ku sai ku kwantar da hankalinku nisan da ke tsakaninku baifi tafiyar minti 5 zuwa 10 ba” cewar Yusuf yana murmushi 
To Uwani ga wayata saka mani lambar ki sai kiyi filashin  nima kiga tawa” ai yara sun ‘kulla zumunci.
Wallahi kuwa” 
Yauwa gata nan nasaka kuma nima naga taki lambar , kai ku dauko jakakunaku mu tafi ” 
Na’dauko tawa na azata aka kamar yanda nazo ‘dazu , itama Farida aka ta ‘dora tata” 
To bawan Allah mun gode sosai Allah yasaka da alkhairi ” cewar Harira gamida mi’kewa tsaye” 
Babu komai mama ai nima tunda akwai lambobin naku a wayata ma ringa gaisawa dasu ” 
Muka fito gaba ‘daya muka hau lifta ya sauko damu ‘kasa muka fito bakin titi domin tarar mota” 
Bamufi minti 2 da tsayuwa ba muka samu mota” 
Hammad,  billadi , kam?” (Malam billadi zaka kaimu nawa)
Ishirin riyal” (riayal ashirin)
La la gaalid marra, tayyib ashara riyal”? (Yayi tsada sosai ina laifin mubaka riyal goma)
Khalas maafi mishkila” (ba matsala)
Muna shiga naga Uwani ta rufe motar”  
Mama gasu Farida naga basu shigo ba kuma kin rufe?” 

Wasila kenan , ai anan Saudiya duk wanda ya tari mota shi ka’dai yake shiga akaisa har inda yakeso , suma su Faridan yanzu zasu shiga tasu motar” 
Haka muka tafi ina ‘dagawa Farida hannu ta madubi’ 
Uwani wannan motar kamar bata haya ba wallahi ki ganta sabuwa dal amma ana haya da ita” 
Wasila kinsan nan ‘kasar ba kamar ‘kasarmu take ba , nan suna kare hakkin mutane sosai ” 
Gaskiya kam,  nifa Uwani wani  sanyi nakeji sosai kamar ‘kankara kota ina yake shigowa?” 
Dariya Uwani tayi , Wasila wannan sanyi ai na mukayyif ne (A C) 
To a ina mukayyif ‘din take ?” 

Gata nan a gaban motarsa” 
Wasu lunguna lunguna naga tana kwatanta masa shi kuma yanata  shiga” 
Uwani nan ‘dinma duk cikin makkan ne?” 
Eh mana me kika gani”? 
A’a gani nayi gidajen gurin basu da kyau kamar na bakin titi yanda kika san ba makkan ba” 
Amma dai ai yafi “kauyanku ko?”
Naja bakina na tsuke danaga ankusa gaya mani ba’ka”
Daidai wani gida naji tace masa ya tsaya” 

Ya tsaya ta mika masa ku’dinsa muka shiga” 
Gidan ne naga wani ‘dan ‘kur’kubi kuma ‘daki 2 ne a cikinsa da ban’daki da kuma madafa” 
Bangama ‘karewa gidan kallo ba naji mutane nata faman yi mani sannu da zuwa ” 

Ga dukkan alamu mutanen gidan ne , nagane hakan ne saboda naga wasu na cin abinci,  wasu kuma suna shafa ,  wasu kuma inaga yanzu suka fito daga wankan” 
Cikin sakan daya nagama ‘kirgasu , zasu kai su 10″ 
A zuciyata nace kwamacala kenan” 
Ba’kuwa shigo mana kina tsaya daga waje cewar wata ‘yar budurwa wacce ga dukkan alamu  zata girmeni da kusan shekara 6 ko 7″ 

DAGA TAKU 

MAMAN JA’AFAR 
Domin gyara ko yabo ko kushe 

+ 966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             11
Can cikin dare na farka gami da duba agogo naga ‘karfe 4 a zuciya ta nace ashema asuba ta kusa” 

Amma ga mamakina sai naga su Sakina harkokinsu kawai sukeyi kamar yanda na barsu ‘dazu” 

Inaga don sun kashe wutar ‘dakin ne kuma sun rage ‘karar tv ‘din yasa nayi tsammanin suma baccin sukeyi” 

Gyara kwanciyata nayi naci gaba da baccina” 
Asuba nayi Sakina ta tadani” 

Mi’ka nayi da hamma da salati duk ajere” 
Wai da gaske baku kwanta ba ku har yanzu ?” Na tambaya gami da kallonsu ‘daya bayan ‘daya cikin sigar bacci 
Hmmm kedai jeki kiyo alwalla kiyi salla ki koma ki kwanta” cewar Aisha kenan dake shinfi’da darduma zatayi salla 
Magewayi na shiga na fito domin fara alwalla” 
Wasila dama haka kikeyin alwalla ?” Cewar Suwaiba kenan 
Eh haka naga su Yaya Habu sunayi da shi da yaya Tanimu ” 
Tab to ba haka akeyi ba, kinga yanda zakiyi nan…. anan ta koya mani alwalla” 
A gurin sallama saida Sakina ta gyara mani 
Anan ne na tabbatar ashe tun abaya kwa”ba nakeyi” 
Wasila ai salla itace cikon addini, domin ko a shika-shikan musulunci salla aka fara ambata kafin sauran

Kuma sai salla ta gyaru sauraan ayyuka suke gyaruwa,  

To bari kiji wani abu ko ranar lahira idan akazo hisabi sallarka ake fara aunawa idan tayi daidai ba sai an binciki sauran ba,  idan kuma aka samu akasin haka sai an binciki ayyukanka ‘daya bayan ‘daya” 

cewar Suwaiba kenan wanda ga dukkan alamu na lura itace malama a cikinsu ” 

Allahu akbar ” ya isa hakanan malama yanzu zaki damemu da kawo ayoyi da hadisai bayan kinsan bacci ne a idanuwanmu” 
Murmushi tayi gami da cewa , Allah ya ganar daku gaskiya”
Nikam abin nasu mamaki yake bani, kenan ga dukkan alamu basu son nasiha?” 
Bayan na idar da salla na je ‘dakinsu mama Uwani tare da sallama” 
Wa alaikumu salamu b’kuwa cewar wata mata kenan da naji suna kira da Khala Indo”
Shigo mana kya tsaya a bakin ‘kofa?” Inji Mama Uwani kenan
Ina kwananku ?”
Lafiya kalau, antashi lafiya, ya ba’kunta?”  Mama Uwani ce take fa’da tare da yin murmushi 
To jeki ku samu abinda kukaci, ku koma ku kwanta anjima idan su Sakina sun tashi sai su rakaki haramin”
Kwanciya kuma bayan wadda na tashi yanzu ?” Na tambaya ha’de da mamaki
Ke kam kin cika tambayar tsiya wallahi , to munan haka akeyi”
To natafi na fa’da murya a sanyaye” 
Nakoma ‘dakinmu na tarar har sun gama dafa shayi suna sha da gurasa” 
Nasamu gefe guda na zauna , nayi tagumi” 
Wasila taso mu karya mana kika tsaya a  wani gefe” 

Ai yakamata abar ba’kuntar hakanan ko?”  Sakina ce mai fa’dar haka
In kuma taga dama kiji baki rai rai sai kace aku ba” Aisha ce mai fa’dar haka 
Suka tun tsire da dariya” 
Ina saka hannu na a abincin nagansa wani kala kamar ba abinci ba” wannan kuma wane kalar abinci ne haka sai kacs na yan gidan yari?” 
Ful da tamisa kenan (wake da biredi) ‘dan’dana kiji akwai da’di” cewar Aisha kenan yayinda ta cika bakinta da loma 
Nidai gaskiya bazan iya cin wannan abincin ba , ni ‘kyan’kyaminsa ma nakeji wallahi” 
Ai sai kije ki ‘dora indomi mudai bacci zamuyi” cewar Sakina kenan
To ina indomin take, ina kuma murhu?” Na tambaya gami da mikewa tsaye 
Kije gurin Khala Uwani zata baki indomin,  nan kuma bamuda murhu sai gas” cewar Aisha kenan 
Itadai Suwaiba tayi nisa acin abincin nata” 
Wai niko ina wata da na ganku tare jiya um.. miye ma sunanta?” Yauwa Hadiza na fa’da  ina mai raba idanuwa tsakaninsu 
Oh Hadiza ai ba yar nan gidan bace , nan kusa damu take” cewar Suwaiba kenan kanta a ‘kasa tana kai loma

To bara naje na karbo indomin tunda na lura ku nan baku da wani abinci inba indomi ba na fa’da ina tafiya” 
Hmmm baki rai-rai kamar aku idan kikaga dama ,  in kuma kikaga hagu ki wani marairaice” cewar Aisha kenan yayinda bakinta yake cike da biredi”  suka tuntsire da dariya 
Salamu alaikum ” 
Wa alaikumus salam ” shigo mana Wasila lafiya?” 
Dama yunwa nakeji to kuma bazan iya cin biredi da miya ba shine Su Sakina sukace nazo gunki na kar’bi indomi”
Oh Allah sarki hakanefa” sai a hankali zaki koya” 
Ga ta nan acikin kwali zo bu’da ki ‘dauka” 
Na shiga na ‘dauko guda 2 ” 
Sauran matan naga duk sunyi bacci”  a zuciyata nace ikon Allah wai bacci da safe” kuma ko yaushe zasu tashi?” 
Nakawowa Sakina nace nidai da murhu na iya girki ban iya da wancen abin yan gayun ba” 
A hankali zaki koya idan kikaje gidan aiki muma da haka muka koya”  ta kar’ba ta fita waje da ita”
Niko badan karkuce na cika surutu ba dana tambayeku?”
Muna jinki” cewar Aisha kenan” 
Wai dan Allah kuma duk kawo ku akayi nan kamar yanda aka kawoni?”
‘Kwarai kuwa duk kawo mu akayi  amma ita mutuniyar taki Sakina anan aka haifeta” Aisha ce ke fa’dar haka yayinda take dafa kafa’dar Sakina 
Allah sarki,  kuce kuma duk iyayenku suna gida najeria?” 
‘Kwarai kuwa” cewar Aisha 
Muna nan muna fira har Suwaiba ta gama dafa indomin takawo mani naci nayi nak, naje na wanke kwanon nadawo na tarar har sun kashe wutar ‘dakin sun kwakkwanta”

Nima na ‘kara gyara shimfi’data nakwanta,  bayan na kalli agogo karfe 7 na safe”
A zuciyata nace wannan baccin larura ko yaushe kuma zasu tashi?”

DAGA 

TAKU

MAMAN JA’AFAR
+ 966592551785
Domin tsokaci ko gyara.

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             13

Daidai wani k’aton gida mai motar ya tsaya,  Khala Altine ce ta fara sauka (wacce ta kawoni gidan aikin) tare da bani umarnin nima na sauko, yan k’unshin kayana a hannuna muka shiga cikin gidan 
Tun a bakin k’ofar gidan zaka san gidan yakai matuk’a gurin tsaruwa da kuma had’uwa,  domin gurin ajiye motoci ne a farko,  nanma da fulawowi a shusshuke gwanin ban sha’awa,   cikin gidan kuwa nan kallo yake,  domin gida ne amma kamar ba gida ba tamkar wani k’aton shago ne da aka jerawa kayan siyarwa, d’akuna 5 ne acikin gidan kuma kowanne ciki da falo,  sai kicin wanda yakai girman gidanmu,  da kayan girki irin na zamani aciki, shiko band’aki tamkar ba band’aki ba domin wasu fararen kujeru nagani kusan guda uku aciki, sai madubi k’ato a bango,  da wata kwabet ta ajiye kayan wanka dana wanke baki, sai wani kwami na wanka k’atoto irin na hotel d’inda muka sauka 

Nayi nisa gurin kallon gidan naji khala Altine tana mun magana”kin tsaya kina wani kallekalle sai kace wata bak’auya ki zauna mana” 
A zuciyata nace to inba bak’auyar ba micece, afili kuma nace ” To” tare da zaunawa bisa luntsuma luntsiman kujerun 
Wata balarabiya ce  ta fito daga wani daki cikin jerin dakunan nan ta zauna a kusa da Khala Altine,  magana takeyi mata cikin larabci wanda bana fahimtar abinda suke cewa,  sai naga balarabiyar ta kalleni tace” Ish’ismik?”  Juyawa nayi bayana banga kowa ba,  saboda a tunanina badani take ba 
“Cewa tayi yaya sunanki kika tsaya kina zarewa mutane ido” 
“WASILA” nace ina kallon matar ina washe baki
“Wasila wannan shine gidan aikin ki , kuma anan zaki zauna tsawon wani lokaci inda bada wata matsala” ta nuna wannan balarabiyar wacce nake zaton zata kai kaman shekaru 30 tace”wannan itacce zakiyiwa aiki da yaranta guda 3 duk maza ne inaga suna makarantar yamma ne shiyasa baki gansu ba, kuma ki saurareni da kyau kiji abinda zan fad’a maki,  ba’a d’aure masu fuska,  domin basa so suga kina musu aiki kina fushi,  kuma ba’ayi masu gardama duk abinda suka sakaki, sannan kuma duk abinda suka sakaki kinayi cikin kazar-kazar, magana ta k’arshe kuma ba’a yiwa ‘ya’yansu tsawa ko zagi ko duka duk irin laifinda sukayi,  idan kika kiyaye wannan to zakiji da’din zama dasu idan kuma kika sa6a to wata ranma sai gidan aiki ya gagareki” Ni zan wuce sai kuma k’arshen wata idan nazo karbar kud’i

Ta tashi tasa6i jakarta ta hannu ta fice,  na bita “da Allah ya kiyaye ki gaida su Khala Uwani” 

“Zasuji” ta fad’a batare da ta juyo ba
Irin na kurame  balarabiyar tayi mani nagane tana nufin sunanta Hanan ne,  sai kuma yaranta yan k’ananu da Da Salman da Isah sai k’araminsu  Adnan.

 Da kurmancin dai ta nuna mani d’akina tace naje na ajiye kayana, ta mik’o mani wata gamisa (doguwar riga) tace odan naje nasakata nazo na fara aiki
***********
Lallai gaskiyarsu Sakina da sukace mani sai nayi kuka domim kad’an ya rage nayi kukan, wanke-wanke ne lodi natarar,  a zuciyata nace anya wad’annan mutanen suna yin wanke-wanke kullum kuwa?  Kai inaga sai wata-wata sukeyi, saboda ko tukanenda na wanke sun tasamma 20 kwanuka da kofuna da tangaraye kuwa sunfi 100,  kafin na gama har k’uguna  yafara rik’ewa, 

Ina cikin gyara inda nayi wanke-wanken naga ta mik’o mani wani inji-inji wai nayi shara dashi, da alamu irin na kurame na nuna mata ban iya shara da inji ba saidai da tsintsiya

Kunnawa tayi tare da nuna mani yanda akeyi,  bayan na gama gyara inda nayi wanke-wanken na shnare kicin d’in kamar yanda ta umurceni, ga mamakina kuma sai naji tace mani naje na wanke band’aki,  a zuciyata nace anya zan iya wannan aikin kuwa? Babu hutawa ba komai , ko ruwama bata bani ba bare kuma abinci sai had’ani da aiki taketayi,  tare muka shiga da ita ta nuna mani kayan wanke band’akin , nidai banga wani atti da band’akin yayi ba , kawai dai salon a wahalar da kai 
Ina fara wanke band’akin naji hannuwana sun fara zafi zafi,  tun ina daurewa har dai nakasa, naje nasameta na fad’a mata tare da nuna mata hannun nawa,  amma ga mammakina sai naga ko alamar jimami ma bata nuna ba sai cemun da tayi “Inti akal fulus balash?” “Yallah ruhu sauyi shugul” (angaya maki zakici kud’in ne a kyauta? Dalla tafi kije kiyi aiki)
A haka na daure na gama wanke band’akin,  nadawo d’akina ina maida numfashi sama-sama,  sai ganin baiwar Allahn nan nayi da kaya nik’i’nik’i,  wai kayan da zan goge ne yanzu,  kuka nasa mata ina cewa…….

*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*
EDITED BY *Sady Jegal*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: [💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             
       *15*

        

Zuwa nayi na sameta zaune tana kallo a tibin bango k’atuwa, na numa mata biredi da nonon da ta bani,  sannan na nuna mata bakina, nayi mata alama da bazai isheni ba
Murmushi tayi gami da tashi ta shiga kicin ta k’aro mani biredin  
A zuciyata nace wannan matar inaga baki gane abinda nake nufi ba,  ni nufina ki bani tuwo ko shinkafa ko wani abindai wanda ya danganci abinci
Hakanan na kar6i biredin na koma d’akina,  ina ci ina korawa da laban d’in , tamkar nayi kuka
Bayan nagama cin abincin ne naje band’aki nayo alwalla nazo na gabatar da sallolinda ake bina, tun akan abin sallar bacci ya kwasheni saboda tsananin gajiya da nayi 
Can wajen k’arfe d’ayan dare naji ana buga mani k’ofar d’akina da k’arfi,  ni abin tsoroma ya bani domin dana duba agogon d’akin nawa  k’arfe d’aya na dare nagani harda wasu mintina
A hankali naje na bud’e ina mai lek’a kain kad’an ta k’ofar d’akin
Uwar aikina na gani tsaye,  kana na ida fitowa,  fad’a ta farayi wanda ban fahimci komai acikin fad’an nata ba sai dai kawai lura da nayi kamar tanaso tace mani ne miyasa na dad’e ban bud’e k’ofar da wuri ba? 
Nidai shuru nayi bance mata komai ba tunda ba larabci na iya ba 
Indomi ta mik’o mani guda 2 wai naje na dafawa ‘ya’yanta suna jin yunwa 
Da alamun kurame kamar yanda muka saba magana da ita na nuna mata ban iya yin  girki da butgas d’in ba 
Tare muka shiga kicin d’in ta koya mani saboda gaba 
Har zan koma na kwanta, naji tace mani ga wani wanke-wanke can an tara naje nayi tukun na kwanta,  shima dai wannan  da yawansa amma bai kai na d’azun ba,  hakanan ina gyan-gyand’i na kammala aikin  naje na kwanta 
Tunaninda ya tsaya mani a rai shi ne,  anya kuwa zan iya yin wannan aikin? Wata zuciyar tace mani to idan bakiyi ba me zakiyi bayan dan shi aka kawoki nan k’asar?  Idan ko dan wannan aikin akeyi mani dad’in bakin wai nazo na huta, iyayena ma su huta,  wani nawa ya huta,  ni banga hutun anan ba,  babu komai acikin wannan aikin face wahala tsantsa,  amma zanyi hak’uri  kuma na jure har wahalar ta wuce idan mai wucewa ce , ko kuma nace har nasaba da wahalar,  yanzu a haka zan biya bashin kud’inda aka kawoni kusan miliyan 2 da wani abu? (Harda bashi da ruwa) to Allah ya bamu rai da lafiya,  tunda dai na riga nazo k’asar ai babu wata dabara kuma 
Acikin wannan tunane-tunanen ne bacci ya kwasheta…….

*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*
EDITED BY *Sady Jegal*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ
   *17*

Tsabar surutu na cina,  ni harma na manta ban bata kud’in aikin nawa ba

A ha6ar zani dama na d’auresu gudun fad’uwa,  kwantosu nayi na mik’a mata, ta kar6a tana washe baki ta fice.
Inata bawa Aisha labari,  amma banji tana bani amsa cikin kulawa ba kamar d’azu, juyawa nayi nakalli inda take domin naga abinda ya d’auke mata hankali,  ga mamakina wayarta naga ta tasa agaba sai faman sauraren maganganu takeyi aciki (voice recording) yayinda itama take danne wani wuri tana magana k’asa-k’asa tamkar dai suna ganin juna da ita da mai maganar

Matsowa nayi dab da ita na dafa kafad’arta gami da cewa” Aisha minene ya d’auke maki hankali haka a waya har inata zuba surutuna bakijini ba?” 
Batayi mani magana ba saidai ta nuna mani alamar nayi shuru har ta gama zata fad’a mani 
“Wasila bakisan me nakeyi ba ko?” Cewar Aisha kenan yayinda ta gama ‘yan ta6e-ta6enta a waya 
“Inako zan sani inata faman surutu kinyi shuru kin k’yaleni” 
“Catting mukeyi na rikodin a group d’inmu  *Ku fad’i komai ba komai*na wad’an da basu iya karatun hausa ba” 
Cikin alamu na rashin fahimta Wasila tace “nifa har yanzu bangane inda maganarki ta dosa ba?” 
Dariya tayi gami da cewa”masha Allah su Wasila anje gidan aiki ank’ara wayewa, saboda naga yanzu surutun naki k’aruwa ma yayi bai ragu ba,  ni nazacima wahalar aiki zatasa bakin nan naki ya mutu,  gashima naga sai abinda yayi gaba, ko d’an nok’e’nok’en nan da kikeyi na bak’unci yanzu naga duk babu shi” 
“Duk zaman gidan aiki ne ya jawo haka,  nidai bani amsata,  minene group? ” 
Murmushi Aisha tayi kana ta dafa kafad’ar Wasila tace “ba wani abu bane ba group illa kawai wata hanya ce ta sada zumunci da kuma d’ebe kewa,  musamman ma mu wad’anda ke gidan aiki, kinga nan a wayata inada groups kusan 20 kuma na mata da maza ne, kinsan irinsa yafi nishad’i, sai kiga kana aiki kana jin k’arfin jikinka,  idan kuma ka gama aiki kazo kwanciya kusha fira kaida masoyinka.

Ta k’ara da cewa “kiyiwa Khala Uwani magana Allah ta siya maki ko Musta’amal ce (Ta hannu) ta siya maki,  wallahi ina mai tabbatar maki zakiji dad’in amfani da ita” 
Abin ya burge Wasila matuk’a,  musammam ma da akace yana d’ebe kewa domin gidan aiki bakada wani abokin fira sai tulin ayyuka kawai,  numfasawa tayi kana tace “Nifa gani nakeyi kamar Khala Uwani bazat siya mani irin wannan wayar taki ba,  domin ganinta nakeyi kamar tanada d’an zafi”
K’ara dafata tayi kana tace” ai dad’in baki zakiyi mata sai kiga ta siya maki” 
“Kamar ya? Ban gane ba?” 
“Hmmm ina nufin kije anjima ki sameta,  kice mata kinji dad’in gidan aikin ki saboda haka idan kika koma bazaki dawo da wuri ba zaki kai kamar wata uku ko hud’u baki dawo ba,  kinsan ‘yan  Hajjojin nan (Masu kawo mutane suna k’ara masu riba) suna jin dad’i idan kika ce masu zaki dad’e a gidan aiki baki dawo ba,  saboda kinga idan kikayi wata 3 ko 4 zaki tara masu kud’i masu yawa,  to sai kiga har wani lalla6aki akeyi” 
Murmushi Wasila tayi mai nuna alamun ta gamsu da abinda Aisha ta fad’a mata
 “insha Allahu kuwa zan fad’a mata yanzun nan ba sai anjima ba,  saboda kwana 2 ne kawai zanyi na koma,  da nace zan d’an k’ara kwana 1 akai,  amma tunda su Sakina basu nan tafiyata zanyi” 
“To tsaya kiji dai tukun,  karki gayawa kowafa wannan maganar da mukayi, ki barta  kawai a tsakaninmu kinji?” 
Na amsa da “to”  tare da ficewa daga d’akin ina yan tsalle-tsalle na,  na nufi d’akin manyan matan.

“Wasila anata murna anga k’awaye harma anaso a manta dani uwar” Cewar Khala Uwani kenan  yayinda ta ajiye mani abinci a gaba na,  yaudai masha Allah shinkafa da miya ce akayi a gidan,  kuma taji nama zuk’u’zuk’u 
“Khala Uwani ! Dan Allah ki  taimaka ki kira mani lambar su Farida mana naji halinda take ciki” 
“Kinsan kuwa satinda ya gabata muka gaisa da Harira, har tace mani itama Faridar tana gidan aiki, wannan yaron ma…wama yake da suna wanda ya taimakeku a Hotel d’in nan?” 

“Allah sarki Yusuf shima ya bugo?” 
“Eh wallahi kusan sau uku ma muna gaisawa dashi yana tambayarki” 
Canza salon maganar tayi tace”amma nima Khala Uwani zaki siya mani waya muringa gaisawa dasu ko? Harma da su Hajar da Affa duk kinga zanji lafiyarsu” 
“Eh nima ina tunanin saya maki wayar nan kafin ki koma ko Abkashaf ce (rakani kashi)  ma ringa jin lafiyarki” 
Alamun mamaki fuskarta ta nuna kana tace” Khala Uwani minene Abkashaf kuma?” 
” ‘Yar k”aramar waya mana” 

“Dan Allah kisiya mani babba man irintasu Sakina naga makar zata d’anfi,  tunda kinga idan na tafi gidan aikin ba da wuri zan dawo ba,  so nake nayi kamar wata 4 zuwa 5 kinga idan da wayar zatana d’ebe mani kewa” 
Murmushi naga tayi mai nuna alamun taji dad’in maganata matuk’a tace “Allah ya kaimu gobe lafiya sai muje MAI CIZO na siyo maki kota Fan 30 ce (Kusan dubu 30 kenan) 
Da murnata na tashi na nufi d’akinmu domin na sanar da Aisha…………

Wannan shine tushen *K’ALUBALEN* Ku biyoni domin jin yanda wannan Chakwakiya zata kasance

   *DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

  +966592551785

             👆
Kyakkyawar gaisuwa ga dukkan ‘Yan’uwana na group d’in *Musha karatu*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             14

“Nidai wallahi nagaji bazan iya ba muguwa kawai,  wannan uwar wahala sokikeyi ki kasheni?” Dariya naga tanayi ga dukkan alamu bataji abinda nake fad’a ba,  waya naga ta buga tana magana,  ga dukkan alamu akaina takeyin maganar domin tanayi tana kallona,  zuwa can naga ta mik’o mani wayar gami da yi mani alamun na karata a kunne na 

“Ke Wasila bana son iskancin banza da wofi,  ya zaki tasa baiwar Allah agaba kina yi mata kuka sai kace wacce ta kashe maki wani naki?” Altine ce ke fad’ar haka cikin fushi” d’ora da cewa “kin zata gidan aikin da ake,  fad’a gidan hutu ne?” Ko kin zata bacci zakizo kiyi?” To ki fad’a mani idan bakiyi aikin ba ta wace hanya zaki biya Uwani kud’inda ta kawoki?” Ta ci gaba da suffa irin ta lallashi,  “kiyi hak’uri ki kwantar da hankalinki duk abinda suka sakaki kiyi masu kinji?” A hankali a hankali zaki saba,  harma ki kai kina jin dad’in gidan aikin,  ko bakiso ki ginawa iyayenki gida,  ki siya masu mota kuma ki kawo su nan?” 
A zuciyata nace saidai gidan da motar amma bana fatan wani nawa yazo yayi wannan bautar 
“Kina jina Wasila” ta tambaya da muryar lallashi 
“Eh” Inaji” na fad’a ina zuzzunb’ura baki 
“To kice wani abu mana ko hankalina zai kwanta” wallahi matar nan har kyautar Fan ashirin (20k)ta bani da taga nasamo mata yarinya wacce zata iya aiki sosai
“Insha Allahu zan kiyaye”na fad’a tare da mik’awa matar wayarta domin ba wani hucewa nayi ba

********
Ban iya guga ba domin ban tab’a yi a gidanmu ba,  hakanan na kwakkwab’a mata kamar yanda ta koya mani,  inayi ina rik’e k’ugu da baya,  saboda gajiya, domin na gaji matuk’a,  babu gugar da tafi bani wahala saita hirami ( abin nad’awa akai irin na larabawa) domin wata lank’wasa-lank’wasa ce akeyi masa gurin gugar tasa 

Bayan nagama na kwashi kayanda na goge d’in nakai mata a Sala (Falo) kamar yanda naji sun fad’a 

Hannu na ta kama muka shiga d’akinta,  wai ko a talabijin ban tab’a ganin d’akinda ya burgeni irinsa ba,  saboda ya tsaru iya tsaruwa,  Dolaf d’inta ta nuna mani,  da kuma nuna mani alamar cewa duk sadda nayi guga nan zanzo na jeresu

D’akina na koma na zauna akan katifata nayi tagumi, ga yunwa,  ga gajiya,  gashi ma ko sallar la’asar banyi ba gashi har angama magriba isha na shrin  gabatowa

Can jimawa naganta ta shigo d’akin nawa da leda a hannunta, ga dukkan alamu ni ta kawowa 

Mik’o  mani tayi tare da cewa Ya Wasila Kud akal (karb’i abinci) tare da yin murmushi,  kar6a nayi ina dubawa ita kuma ta koma Saala taci gaba da kallon Tamsiliyarta
Gurasa na gani da laban acikin ledar ,  a zuciyata nace tab’ aiko za ayita anan,  domin nidai gaba d’aya nan banga abincin da mai jin yinwa irina zai ci ba………… 

*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*
EDITED BY *Sady Jegal*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             12

Ga mamakina nima baccin ne ya kwasheni , inaga hakan yasamo asali ne saboda gajiyar tafiya ”
Sai azahar duka ‘yan  gidan suka tashi aka gabatar da sallah , da cin abinci kana kowa kuma ya tafi har kokinsa,  wasu aikin wuni,  wasu kuma tallar gumama, wasu tallar dawa.
“Wasila zo ga mamar ki ku gaisa ki sanar mata kin sauka lafiya ko?” Cewar Mama Uwani kenan yayinda take mik’o mani waya”
“Alo Haja kina jina ?”
Eh” ina jinki Wasila kun sauka lafiya?”
“Lafiya k’alau wallahi, ya Affa da su Yaya suna lafiya ko”
“Duk lafiyansu k’alau, kinsan su su yayan suna makaranta basu dawo ba har yanzu, amma babanki ma gashi nan kusa dani” amma kafin na baki shi ki tsaya ki saurareni Wasila da kyau” 
“Ina jinki Mamata ta kaina” 
“Dan Allah Wasila ki kama kanki, ki kuma rik’e mutuncinki,  karkiga cewa bamu ganinki kidinga yin abinda kikaga dama, to ki sani idan mu bama ganinki wanda ya halicceki yana kallonki, dan Allah karki bamu kunya, ki natsu kiyi abinda ya kaiki, tun tafiyar ki mutanen garin nan suke cewa mun turaki karuwanci saboda talauci yayi mana yawa,  wasu kuma cewa sukeyi mun turaki bauta gidan larabawa,  wasu ma har cewa sukeyi mun sayar dake dan muyi kud’i, dan Allah ki kula kinji Wasilata?” 

“Na amsa da to ” muryata a sanyaye tamkar zanyi kuka da jin wannan nasiha ta mahaifiyata” Haja ina Affana yake mu gaisa na fad’a murya a sanyaye?” 
“Gashi bara na basa wayar” 
“Ya amsa gamida yin sallama” 
“Affa ina wuni?” 
“Lafiya lau Wasila, ya bak’unta Da kuma abokan zaman?”
“Duk Lafiya k’alau Affa” 
“Wasila ayita hak’uri dai, musamman zama da jama’a sai anyi hak’uri, kuma arik’e amana,  wannan saurin fushin naki shima sai kin ragesa tunda ance zo mu zauna zo mu sab’a” 
“Insha Allahu Affa duk zan kiyaye, nagode sosai” 
A haka suka  gama waya kowa na kewar  kowa, nace Allah sarki,  inba talauci ba mi zai raba d’a da iyayensa,  musamman ma mace wadda akasan aure ne kad’ai zai iya rabata da iyayenta.
“Wasila tunda kun kimtsa ga Suwaiba nan saita kaiki harami ki sauke umra tunda itace malama malama acikin su ” ta fad’a gami da harararsu  Sakina tana k’umshe dariya”
“Suwaiba ce  naga tasaka wata doguwar riga bak’a har k’asa , kana ta nad’e kanta da kallabin rigar, sai kuma naga ta d’auko wani bak’in abu ta rufe idanuwanta” ina dariya nace wannan shigar fa saikace wata aljana?”
“Yarinya mu nan wannan shigar itace hijabinmu kema ga irinsu nan nad’auko maki ki saka mutafi” 
“Nidai da kun barni nasaka hijabina wallahi,  dan ba ganin hanya zanyi ba idan na rufe idanuwana”  
“Ke” bama son sakarci dalla saka kutafi , idan kuma bazaki saka ba sai dai kiyi zamanki” 
Mama Uwani ke fa’dar haka cikin fushi , yayinda ta shige d’akinsu. 
Hakanan dai Wasila tayi  irin shigarda Suwaiba tayi suka kama hanya sai Harami. Sai a yanzu ne Wasila take k’arewa makkar kallo,  iya had’uwa kam makka ta had’u dan tsayawa  fasalta maku had’uwarta zai d’au lokaci,  amma wad’anda sukazo su sun san da hakan.
“Haramin ma saida naga wad’an nan sojojin, suna kai komo,  nace Suwaiba su kuma wa’dan nan me sukeyi anan?” 
“Marar gaskiya suke dubawa,  kamar b’arawo,  ko namijin da ya fiye shiga cikin mata, ko kuma idan an cunkushe hanya su gyaggyra,  ko masu fad’a da dai sauransu”
” Hmm wallahi Suwaiba nan k’asar suna burgeni yanda suke kare hakk’in jama’a sosai” 
“Gaskiya sunada kula kam sosai gurin hakan, ammafa duk da haka sunfi kare hakk’in d’an ‘kasarsu akan mu ba’ki,  bazaki san hakan ba sai fad’a ya had’aku da d’an k’asa,  to a sannan fa ko kinada gaskiya ko baki da ita wannan d’an k’asar shi zasu goyawa baya” 
“Ta’b, to muma Allah yasa wata rana ‘kasarmu najeria ta zama haka” 
“Amen Wasila” 

Bayan sun gama D’awafi da Safa da marwa suka kama hanya sai gida 
“Sannunku da dawowa,  Suwaiba sannu da k’o’kari” Mama Uwani ce ke fad’ar haka yayinda taga shigowarmu tana bakin kicin” 
” Yauwa Khala Uwani ai munma yi sauri saboda yau babu  zahama sosai a haramin (cunkoso)” 
“Wasila ga abinci nan na dafa maku kuci,  kafin anjima Sakina ta dawo tayi maki kitso kinsan gobe ne za a kaiki gidan aiki, d’azun nan nayiwa mai gawalin waya (wacce ke kai mutane gidan aiki) tace mani akwai wata balarabiya da tace mata takawo mata mai aiki, kinga gara ki tafi goben dan kada ayi sanya su samo wata,  kunsan yanzu aiki wahala yakeyi saboda anata kawo mata daga najeria kuma farashinsu yafi namu sau’ki shiyasa yanzu  gara idan kasamu gidan aiki ka ri’kesa hannu biyu-biyu” 
“Wai dama Khala Uwani jita-jitan da nakeji da gaske ne kenan  ‘yan kasuwa suna kawo mata daga najeria?” Cewar Suwaiba kenan yayinda ta ri’ke ha’ba.
“Ai kuwa da gaske ne , kinsan wasu har sun fara sharri suna cewa da hannu Baba Buhari aciki, ashe bawan Allahn babu ruwansa, shi abindama ya damesa ya damesa”
“To Allah ya zaba mana mafi alkhairi” 
“Ameen kedai d’iyar nan” 
Da dare  Sakina tana yiwa Wasila kitso yayinda suke kallon wani film mai suna (Zinaru) suna kallo suna dariya domin film d’in na dariya ne,  Wasila ta dubi Aisha dake zaune kusa da ita tace 
“Allah yasa dai kar ‘yan nefa su d’auke wutar nan har sai angama yi mani kitso kuma mun gama kallon wannan kasait d’in,  kusan a garinmu idan mukaje kallo gidan D’ahara sai sun bari anzo daidai gurin dad’in sai su d’auke wutarsu ” 
Gani tayi su duka sunatayi mata dariya , Sakina ce ta tsayar da tata dariyar gami da ce mata
“Aike Wasila nan k’asar ba’a d’auke wuta,  ko kinga and’auke wuta tunda kikazo?” 
“Na gyada kai gami da cewa a’a,  amma ina mamaki acikin raina” 
“To mu nan inkinga an d’auke wuta to wani gyara ne za’ayi shima gyaran baya wuce awa daya” cewar Suwaiba kenan wacce ke zaune bakin ‘ kofar d’aki 
Bayan Sakina ta gama yiwa Wasila kitso sun gama kallo suna fira, anan ne Wasila take tambayar  su
“Waini ku bazakuje gidan aikin bane , ko ku ba kwa aikin ne?”
“Munayi mana ijaza mukazo (hutu)  gobe kamar yanzu duk mun kama gabanmu” cewar Aisha kenan 
“Dan Allah yaya akeyin aikin ne da wahala kuwa?”
“Wahala kai , amma a hankali zaki saba harma ki kai bakayjin wahalarsa” cewar Suwaiba kenan 
“To Allah ya kaimu gobe lafiya nima na ta’ba naji yanda kikeji” 
“Ameen , yarinya saura kuma kije ki fara yi masu kuka idan kikaji wuya” Sakina ce ke fad’ar haka tana dariya 
Yau ma dai sai safe mutanen gidan suka kwanta bacci, abin mamaki itama Wasila har safe idonta 2 

Ku biyo ni domin jin yanda rayuwar Wasila zata kasance a gidan aiki 

*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

+966592551785
Editing by *Sadiya Jegal*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ
                *16*
    

Ina gama sallar asuba nadawo d’akina na kwanta,  wai da niyar inyi bacci kamar yanda naga anayi agidansu Khala Uwani
 Dawowa Hanan tayi, ta nuna mani alamar cewa naje nayi wanka kana na shiga kicin domin fara aiki na 
Gahawa tabani tace na dafa, nace mata ban iya dafa kalar wannan shayin ba, bayan ta koya mani ne, nagama  dafawa na juya kuma domin yin wanke-wanke,  yanzun ma lodi na tarar da wanke-wanken,  a zuciyata nace ikon Allah!  Kome sukeyi da kwanuka haka suke yawan taruwa? Bayan nagama wanke-wanken kuma na hau gyaran d’akunan gidan duka,  da kuma band’akunan suma 3 harda na tsakar gida 4 kenan,  yauma dai saida na zuba wannan abin mai zafi a gurin wanke band’akunan (Kulurus)  
Hmmmm yau kam nasha aiki domin kusan gaba d’aya bangon gidan saida nasa soso mai laushi na goggogesa 
Aikin kam aiki ne,  amma nasawa raina zanyi hak’uri na jure har zuwa lokacinda zan biya bashinda aka kawoni,  inyaso dana biya bashin sai nayi haramar tafiya k’asarmu. 
Nayi zurfi acikin tunanin da nakeyi, kawai sai ganin Isah nayi ya d’auko asir (lemu) yana zuzzubawa a kwanukan da na wanke,  raina ne ya b’aci matuk’a,  bansan lokacin da na kama kunnensa nace ba “Kai wane irin wawan yaro ne mara hankali?” 
Wasila bata ankara ba sai ji tayi Hanan na cewa 
“La, la, Ya Wasila,  haram alaiki,  wallah dahin ana tassil shurta inti safar fi najeria”        ( kai! Kai! Wasila,  wannan bai kamata ba,  wallahi zankira maki yan sanda yanzun nan su kai ki najeria)
A birkice Hanan take fad’in wannan maganar kai kace tarar dani tayi nasawa yaron wuk’a a wuya,  sai a sannan ne na tuna da nasihar da Khala Altine tayi mani,  nacewar su ba’a dakar masu yara kome ka tarar su nayi,  iyakar ka dasu ido,  a firgice na juyo ina karkarwa na durk’usa har k’asa duk da bansan mitake cewa ba, amma ga dukkan alamu tana cikin 6acin rai ,  “ma’alish,  ya ummi”  bansan ya akayi na had’o wannan larabcin lokaci guda ba,  Suwaiba na ta6a jin ta fad’i haka sadda mukaje harami ta taka wata balarabiya naji tace mata haka,  ashe na hardace ban sani ba
Fad’anta taci gaba dayi,  ta kama hannun yaronta sukayi gaba.
Ashe fad’an bai k’are ba,  domin baban yaron shima naga ya fito yana maimaita nasa fad’an shima
Nidai yau na shiga uku na fad’a a cikin raina,  ashe haka suke masifar son ‘ya’yansu,  insha Allahu ko harara bazata k’ara had’ani da yaransu ba.

************
A kwana atashi ba wuya,  yau Wasila ta samu wata d’aya kenan a gidan aiki, kuma a hankali har ta fara sabawa da dukkan ayyukan gidan,  domin yanzu har ‘yar fira suke ta6awa da ita da uwar aikin nata

Yau wata ya k’are don haka aka Wasila kud’inta jaka d’aya da rabi cib-cib (A yanzu da dala ta tashi kusan dubu d’ari da hamsin kenan) 

Har ta gama shiryawa Khala Altine kawai take jira domin tazo ta d’auketa ta kaita gida domin yin hutun kwana 2 kamar yanda su Sakina suke zuwa gida  suma suyi hutun kwana 2.
Murna fala acikin raina da fuskata na shiga gidan 

“Sannunku da zuwa ‘yan gidan aiki,  sannunku sannunku” cewar Kha Uwani kenan data dad’e tana jiranmu
“Yauwa Khala Uwani, nasameku lafiya? ” ina fad’a ina kutsa kai cikin d’akinmu domin bakina cike yake da labarinda zan fesawa su Suwaiba 
“To mazari,  ai kya tsaya  ki ci abinci ki huta kana ku fara shiriritar taku ko” cewar Khala Asabe kenan wacce take abakin Kassala tana yin wanki (injin wanki)
Ko juyowa banyi ba na shige d’akin, saidai banji dad’i dana samu Aisha ita kad’ai ba
“Aisha ina Sakina da Suwaiba suke?”  Na fad’a ina dube dube ko zan gansu
Dariya tayi tace “Wasila ko sallama babu bare kuma gaisuwa kike tambayar su Sakina?” To wannan watan basuzo ijaza ba (hutun k’arshen wata) k’ilan sai wani watan zasuzo,  wannan watan ni kad’ai nazo,  zauna mana ki bani labarin kukan da kika sha, ko bazaki bani labarin nikad’ai ba?” Tana k’yak’yata harda k’walla take fad’ar wannan maganar 
Zama nayi tare da cewa “hmmm,  kedai bari,  kuka kam nasha kuka,  nayi dana sanin zuwana nan k’asar yafi a k’irga,  ke harfa zaginta nayi” 
Rik’e baki tayi da mamaki tace “da gaske?” 
Dariya tayo sosai kana tace “Wallahi kuwa,  inda Allah ya taimakeni ba hausa takeji ba, da tana jin hausa wallahi da taci ubana” 
Itama Aishar dariya takeyi tace ” aiko da ta had’aki da ‘yan sanda sunyi gaba dake, kinsan su larabawa da kayi masu laifi sai suce zasu had’aka da ‘yan sanda su aunaka najeria 

“Aiko nima ta fad’a mani haka (ta kwashe yanda sukayi da Hanan game da d’anta ta fad’a mata)
Uwani ce ta shigo d’akin tare da cewa “to malama baki bani kud’in ba kin tsaya sai zuba surutu kikeyi……..

    *DAGA TAKU*
*MAMAN JA’AFAR*

 Kyakkyawar gaisuwa ga ‘yan group d’ina wato *MUSHA KARATU*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

      
            *18*
      

“Albishirin ki Aisha” na fad’a a daidai lokacinda nazauna kusa da ita,  na dafa kafad’arta tamkar wata k’awata
“Goro” yaya? Ta amince ne?” Ta fad’a yayinda ta tattaro hankalinta gaba d’aya gun Wasilar 
“Wallahi kuwa ta amince,  ko gardama ma batayi mani ba dataji nace zan dad’e gidan aikin” 
Murmushi tayi irin na su na wayayyun ‘yan’mata tace”to goben idan ta siyo maki sai kuma kice mata ta saka maki Shabaka (DATA ) saboda ki ringa yin kallo ko kuma wasanni , kinga zuwa dare sai na sauke maki WhatsApp d”in,  amma bazan sakaki a groups d”in ba sai kin tafi gidan aiki, saboda  kar su Khala su fahimci munyi wata magana dake, kuma a goben zan  kokkoya maki komai kafin ki tafin insha Allahu
Cikin murna ta amsa mata da “Allah ya kaimu goben lafiya”

A zuciyata nace Allah sarki, da kinsan abinda waya zata ja maki….hmmm da bakiyi marmarin rik’eta ba,  ko dayake idan na duba wani abin kuma sai inga kamar Wasila yarinta na damunta,  ga dukkan alamu batasan inda duniyar ta dosa ba har yanzu.
 ***************
Wasila ce kwance a kan katifarta ta gidan aiki,  hutawa takeyi bayan ta gama tik’ar aiki ta gaji,  wayarta ta d’auko ta kunna Shabaka,  ta zurama wayar ido tana jiran taga ta inda sak’o zai shigo 
Bata dad’e da bud’e shabakar ba aiko sak’wanni sukaita shigowa ba tsaitsayawa,  nidai dana lek’a kusan sak’wanni 500 nagani kuma duk voice ne, group d’in da ta sakatan bashi da yawa domin inaga baifi 3 ba kuma duk mata da maza 
D’aya bayan d’aya tabi rikodin d’in tana saurara,  fira ce sukeyi a tsakaninsu,  wani lokaci ayi firar arzik’i, wani lokaci kuma ayi wasa da dariya, wani lokacin kuma a d’an taba magang-anun  batsa 
Ita dai abin burgeta yakeyi saboda ana samun nishad’i a ciki,  bata gama saurara ba ta tuno da lambar Farida da aka bata,  da kuma ta Yusuf,  dayake tanada Kidma ta Zain (Free call na wata d’aya amma sai ka saka 20 riyal, Zain to zain, dayake Zain d’in yafi sauk’i shiyasa mafi yawancin mu Zain mukafi  amfani dashi) 
Bugu d’aya kuwa  Farida ta d’aga tare da sallama cikin natsuwa “Farida mutanen gidan aiki” Wasila ta fad’a tana k’yak’yata dariya 
“Laaaa” Wasila kece?” Allah sarki,  inata cewa Khala Harira ta bani lambarki amma bata bani ba, ina kika samu lambata dan Allah?” 
“Khala Uwani ce ta bani sadda ta siya mani wannan wayar” ta k’ara da cewa “Farida nima ansiya mani waya ablims (ta ta6awa da hannu) ke wace kala aka siya maki?” 
“Minene kuma ablims Wasila?” Masha Allah kice kin fara iya larabci” ta fad’a tana dariya cikin murnar jin muryar k’awarta 
” Ai natsuwa nakeyi ina sauraronsu ina k’ok’arin fahimtar abinda suke nufi” wayatafa har WhatsApp takeyi Farida,  kefa taki,  tanayi?” 
“A’a wayata batayin komai,  sai dai nakira a kirani, Wai Harira cewa tayi wai zanfi dagewa nayi aiki”. 
Sun dad’e suna fira a cikin nishad’i,  kana daga bisani kuma sukayi sallama, ta kashe ta kira Yusuf 
Shima sunyi kusan minti 30 suna gaisawa,  yanata tsokanarta akan irin k’auyancin da sukaitayi farkon zuwansu Saudia.

*****************

Yau satin Wasila 3 kenan da dawowa a gidan aiki,  kuma a sannu a hankali tun bata tsoma bakinta a cikin group d’in *kuyi komai ba komai* har daga bisani kuma tafara  tsoma bakinta a ciki,  musamman da yake akwai wad’anda suke gidan aiki da yawa ciki,  to takan tsoma bakinta ne idan taji anta6o labarin gidan aiki,  kowa yana bada labarin gidan aikinsa, to a sannan ne itama sai ta tsoma albarkacin bakinta.
A ire iren wannan firar ne har Allah ya had’ata da  wani mai suna Adams

A kullum idan tana bada labarin gidan aikinta, yakan nuna tausayawarsa agareta, musamman data fad’a masu shekarunta,  har takai yana ta6ota ta privet suna d’an taba fira jefi jefi
A gefe guda kuma indai zata fara aiki to kuwa zata mak’ala samma’a a kunnenta (abin kunne na waya) tana aiki tana fira da Farida ko kuma da d’aya daga cikin ‘yan groups d’insu.
A hankali har ta fara jin dad’in gidan aikin nata saboda abubuwan d’ebe kewa da tasamu.

Wata rana suna fira da Adams ta voice yace mata” Niko Wasila na tambayeki mana” 
“Ina jinka”  ta amsa masa 
“Wai kin ta6a aikawa iyayenki wani abu kuwa tunda kikazo nan k’asar?” 
Shuru tayi alamar tunani,  kana tace masa…………..

   *DAGA TAKU*
*MAMAN JA’AFAR*
   +966592551785

             👆
Kyakkyawar gaisuwa ta musamman ga ‘yan group d’inmu wato *Musha karatu*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

                     20

Bata bani kud’in wata guda ba domin ban cika mata aikin wata guda d’in ba.
Khala Altine da fushinta ta rufe ni da fad’a tamkar zata dokeni, ni kuma hak’uri kawai nake bata, saida tayi fad’an mai isarta ta gaji kana tace “wai mema kikayi mata har tace nazo na d’aukeki?” 
Nan na tak’ark’are na dingi zayyano mata k’arya kamar yanda Aisha ta koya mani 
Ga mamakina sai naga ba wuya har ta gamsu da maganata, a zuciyata nace, lallai wad’an nan mutanen suna fifita kud’i fiye da komai,  indai magana ta kud’i ce,  to ananfa basa wasa.
*************
Ban wani dad’e sosai a gida ba aka samar mani wani gidan aikin, masha Allah gidan babu aiki sosai kamar wancen dana baro, sai dai matsalar sa d’aya,  wato yaron gidan Hammudi da baisan komai ba sai wulak’anta mutane, dan ranann ma ina zaune a Saala ina kallo ya jefeni da kofin tangaran saida goshin nawa ya tsage, bayan sun kaini Mustashfa aka bani magani da allurai, bada dad’ewa ba kuma ina guga wata rana, na ajiye dutsin gugar ina catin , ban ankara ba kawai sai ji nayi ya nana mani dutsin a cinyata
Wannan karon da kud’in aikina suka kaini assibiti,  ga matar gidan RANA bata da kirki ko kad’an , aiki duk girmansa nizata bawa,  ko k’ank’anta ta ma bata gani
Abin haushin hatta fant d’inta da bireziya ni nake wanke mata, ba anan kad’ai abin ya tsaya ba dan ko al’ada takeyi ni take bawa kayan jinin na wanke

Ko kwanciya tayi da mijinta,  yanda suka kwanta haka zasu tashi su bar gadon hakanan, ni zan gyara gadon,  na share d’akin,  na d’auke mundil d’inda suka b’ata nakai shara, ina k’yank’yami ina komai amma hakanan zan daure nayi,  tunda biyana sukeyi
Babban abin takaicin ma shine,  ko wanka sukayo ita da mijinta tare zasu jero su shigo d’aki,  ko kunyata basaji bare kuma ta d’ansu mai kimanin shekaru 5.
Ban dad’e sosai a gidan aikin ba,  nanma na kassaroshi (na karya shi) na dawo gida nace masu shara take bani ina zubarwa a waje, kuma hanyar ‘yan sanda na yawan bi,  idan tsatsayi ya gibta sai kuga tuni ankama mutum an tullasa najeria
Wata mata na kusa lokacinda nakeyin wannan bayanin bud’ar bakinta sai cewa tayi “Niko Uwani da zaki yadda aida kin bani ita mun tafi Jidda,  tunda gidan aikin ya gagara ko Dawwari basai ta ringa yi ba duk sati d’aya ko biyu ana aiko maki kud’in?” (BARA)
“Aini Salamatu ba Dawwarin ne banaso ba saboda naji ance ana samu , domin najima ance yafi gidan aikin riba,  amma matsalar Jidda yawan kame akeyi indai baka da igama (Takardar izinin zaman k’asa) ke ko kanada igamar ma indai suka kamaka a gurin bara Najeria Mastigo” 
Dariya suka saka gaba d’aya kana wacce aka kira da suna Salamatu tace” Inda ana kamawa aida mu tuni an kama mu,  domin shekara nawa ina Dawwari kuma har yau ba’a ta6a kamani ba? Kawai ki wakkala ki bani ita mu tafi kawai” 
“To” ku tafi  agwada dawwae kuma a gani koza a dace”………….

   *DAGA TAKU*
*MAMAN JA’AFAR*
  +966592551785

             👆
Kyakkyawar gaisuwa ga ‘yan group d’inmu wato                               *Musha karatu*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             26

Ashe kujera ce agurin,  kuma wani namiji nagani a kishingid’e akan kujerar tamkar mai bacci

Atunanina catin yakeyi domin mafi yawan mu masu yin catin naga haka muke tattara hankalinmu gaba d’aya akan waya

Da gudu na dawo Saala cikin tsoro ina cewa Sakina”wallahi wani k’ato nagani a d’akin kwance inaga bacci yakeyi”
Dariya naga sunayi gaba d’ayansu,  kana Sakina ta kalli Sahar”waye ne a d’akin namu?  ko Ahamad d’inki ne yazo?”
“Eh wallahi shine yazo,  kinsan tun ina gidan aiki yace mani idan nazo ijaza wai nazo nayi masa kwana d’aya a gidansa, to ni kuma gaskiya tsoron zuwa nakeji tun randa yan kamen nan suka kusan rutsamu a tare Allah ya taimaka muka haura ta katanga,  tun a sannan nace wallahi bazan k’ara je masa ba” 
Daga gefe guda wata wadda naji suna kira da Ikilima ta  tuntsire da dariya kana tace

 “Ai naso su rutsa dake wallahi,  kinsanko idan suka rutsa dake aradu ba nageria zasu kai tsaye zasu kai ki ba,  sai kinyi Sijin (gidan yari) na shekaru kana kuma su watsaki gida bayan sunyi maki Basmar (Shedar bazaka k’ara dawowa k’asar saudia ba)
Wata muguwar harara Sahar ta daka mata kana tace ” aini garamani ina zuwa gidan aikin,  ijaza kawai nake zuwa yi nan gidan na kwana 2 keko inaga kusan watan ki guda kenan kina nan gidan zaune saidai wannan shegen d’an mak’on ya dinga kai da komowa” ta k’ara da cewa”gashi kuma ‘yan kud’in aikin dama zai baki jaka d’aya da rabi ki kaiwa iyayenki amatsayin kud’in aiki ya gagara”taci gaba da cewa” ni kema nake tausayawa ranar da Askarawan nan zasu rutsa dake acikin gidan nan tare da namiji”
“Fad’a baizo ba gori yazo” cewar Hafsa kenan yayinda takeyi masu dariya
“Keko  ba dole ayi fad’a ba tunda ansako maganar kame? Kinsan ‘Yar Hajja (mata wad’anda basu da takardar izinin zaman k’asa) ta tsani taji ana maganar kame,  bare kuma a dangantata dashi, ai anan ne zakiga tashin hankali” Cewar Sakina kenan tana murmushi
Nidai ban tsaya na ida jin k’arshen firar tasu ba, tunda dai na fahimci abinda ya bani tsoro su basu d’aukesa abakin komai ba,  nad’auki soson wankana na shige Hammam.
*K’alubale*  ga iyayenda suke turo yaransu ‘yan mata da zummar suyi neman kud’i a Saudia, wasu iyayen ma suna tare da yaran nasu a Saudian,  amma son zuciya da kuma son abin duniya ya hana su tsayawa tsayin daka wajen kula da tarbiyar yaran nasu, basu da wani gurinda ya wuce su tura yaran gidan aiki ko kuma su turasu gurin bara su tara  kud’i su kawo masu.
Babu ma masu babbar matsala irin wa’yanda daga Nageria ne ko Niger zasu bada yaransu akawosu a bashi da zummar  idan zukazo sunema su biya bashin kana su samu wani abun nasu

To kusani ita wadda kika bawa ‘yar taki badamuwa zatayi gurin tarbiyantar da ita ba,  domin badan tayi mata tarbiya ta d’aukota ba
Data kula da kanta da karta kula da kanta duk wannan bai shafeta ba indai zata kawo kud’i akan k’a’ida
Karfaku manta tarbiyar d’iya mace nada matuk’ar mahimmanci,  shiyasama Annabi (S.A.W) yace duk wanda ya tarbiyanci ‘ya’ya mata guda 3 har ya aurar dasu,  bashida sakamakon da ya wuce gidan Aljannah.
A wani hadisin kuma cewa yayi: dukkan ku masu kiwo ne,  kuma dukkan ku sai antambayeku a ranara lahira akan kiwon da aka baku,  acikin hadisin ya ci gaba da cewa…..mace ma mai kiwo ce a gidan mijinta,  kuma lallai za a tambayeta akan kiwon da aka bata
Kai kuma mai gida!  da uwar da ‘yar dukkansu amanace agareka,  kuma kaima za’a tambayeka akan amanar da  aka baka
Iyaye *K’alubale*agareku, ku kula ku k’ara kula,  renon d’iya mace,  tamkar renon al’umma ce duka,  domin sai ta samu tarbiya kana zata bayar da ita
Talauci ba wata hujja bace da zamu mayar da yaranmu tamkar hajar siyarwa, duk dad’i, duk wuya, ki kasance tare da ‘yarki, ku rayu a tare.
 Duk inda rabonka yake a sannu a hankali zaizo har gida ya sameka.
Ammafa ku sani ba duka aka taru aka zama d’aya ba,  domin a ko ina ana samun lalatacce da kuma na kirki.
A kwai dayawa wa’yanda tsakaninsu da Allah sukeyin aikin domin su rufawa kansu asiri da kuma ‘yan’uwansu
Amma gur6atattun cikinsu sun saka anayi masu kud’in goro, wanda abin duk ya samo asali ne daga gun l iyayen wad’ancan d’in
 Bayan fitowata daga Hammam ina zaune a Saala ina shafa mai a jikina  wayata tayi k’ara alamar kira ne ya shigo, lambar Adams na gani akai domin ban iya saka suna ba bare nasaka,  saidai nagane lambar mutane da farkonta ko kuma k’arshenta
D’agawa nayi muka gaisa kamar yanda muka saba,  kana daga bisani yace mani “Wannan watan kinzo ijaza gida kuwa……..

   *DAGA TAKU*
*MAMAN JA’AFAR*
  +966592551785
Kyakkyawar gaisuwa ta musamman ga ‘yan group d’inmu wato *Musha karatu*

 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             27

“La-la wallahi banzo gida ijaza  ba sai dai….”
“Saidai me? Kin fara magana kuma kin tsaya kame-kame” ya k’ara da cewa”kodai kina nufin anan Madina kikaje ijazar?”
“Ehwa”acan naje” dama kai ma kasan ana zuwa ijaza wani gurin ne ba gida ba?” 
Maganarta dariya ta bashi kana yace “kema da baki dad’e a k’asar ba kinsan ana zuwa bare kuma ni? Ai dan dai kawai ina jin tsoron matsalar Tabtish (binciken ‘yan sanda)a hanya amma da kafin ki koma gidan aiki saidai ki ganni kwatsam”
Murmushi nayi kana nace”ashe har ku maza kuna jin tsoro?”
“Badole mutum yaji tsoro ba indai yanason zamansa lafiya a k’asar nan?” Nidai yanzu dan Allah ki daure,  ki taimakeni kamar yanda Allah ya taimakeki,  wata na gaba kizo mani hutu gidana a makka”
Gabana ne ya fad’i kana nayi k’arfin halin sake tambayarsa nace” gidanka kuma? Me zanyi a gidanka? Kuma wace amsa kakeso nabawa su Khala Uwani idan suka tambayeni inda naje?” Lokaci guda duk na jero masa wad’an nan tambayoyin,  kana na d’ora da cewa “nidai ka rufa mani asiri babu ruwana wallahi”
“Duk wannan ba wata matsala bace indai kika amince” haba Wasilata kodai baki so  ki ganni ne kamar yanda nakeso na ganki? kar dai haukana kawai nakeyi bakisan abinda nake nufi ba? Kodai so kikeyi sai na fito k’iri-kiri nace maki tun da dad’ewa sonki da k’aunarki yake ta d’awainiya da zuciyata? Haba Wasila wasilele ataimaki Adams mana da ganin wannan kyakkyawar fuskar taki”
Kalamansa dariya suka bani, amma dukda haka sunyi mani dad’i  matuk’a,  sai dai duk da hakan zuciyata bata amince mani akan naje gidansa ba.

***************
Kwanci tashi babu wuya yau Wasila shekararta guda kenan a Saudia harma da wasu ‘yan watanni, amma abin mamaki har yau ba’a taba ce mata ga lambar iyayenki kwa dinga gaisawa ba, dukda kuwa Uwanin tace ta aika masu da kud’i sun sayi wayar, tayi nacin duniyar nan har ta gaji,  amma fafur ta hanata lambar nan, ,  sai dai duk sadda Wasilar ta buk’aci da ta had’ata da iyayen nata su  gaisa sai ta kirasu da wayarta kuma bata matsawa ko nan da can har sai Wasilar tagama magana da iyayen nata, kana ta kar6i wayarta ta goge lambar dan kar Wasilar ta d’auka a 6oye.
A 6angare guda kuma soyayya na nan naci gaba da wanzuwa tsakanin Wasila da kuma Adams,  amma duk da hakan har yanzu bata samu damar ziyartarsa ba duk kuwa da k’wa-k’war  hakan da yaketa famanyi,  amma dukda hakan baiyi fushi ba, saima k’ara k’aimi da yayi wajen mik’a k’ok’on bararsa.
A 6angaren *Farida*  kuwa ta mayar da hankalinta kacokam gurin aikinta,  Harira bata barta ta rik’e ma babbar waya ba bare kuma a samu matsala

Gashi kuma tayi dace da iyayen aiki na gari,  domin sun d’auketa kusan tamkar d’iya agaresu, yanda zasu koyawa yaransu karatu bayan sun dawo makaranta, haka itama zasu koya mata duk da ba makarantar take zuwa ba

Dan yanzu babu abinda zakace ta rubuta da arabic batare data rubuta ba

Kuma acikin wannan shekarar ne ta ida biyan bashinda ake binta gaba d’aya yanzu cikin neman nata na kanta take
Yusuf kuwa ya zame masu d’an’uwa domin kullum idan suna waya bashida aikinda ya wuce yi masu nasiha akan su kare mutuncin su.
 **************
Yau ce ta kama ranar zakki-zakki,  wato ranar daren k’aramar salla(ranar da ake rabon zakkatul-fid’ir) ranar da mazauna makka da madina mafi yawansu suke haramar tafiya jidda domin acewar su a jidda anfi samun zakki-zakkin kud’i da kuma shinkafa mai yawa.
A gidansu Wasilama ba’a barsu a baya ba,  domin suma naga kusan gaba d’ayansu sai har had’a kaya suke a jakakunansu  zasu tafi neman zakki-zakki  a jidda.
Gaskiya Jidda ma ba a baya  gurin had’uwa ba,  domin zan iya cewama tafi makka kyau da kuma tsaruwa,  saboda makka mafi yawancin garin duk duwatsu ne,  dan duwatsunma su suke hana su tsarata yanda sukeso a wajen gine-ginensu,  ammafa duk had’uwar Jidda bata kamo ko k’afar Madina ba.
Gida mai kyau aka sauke mu ba kamar namu na makka ba,  domin wannan bama zakace na hausawanmu bane,  gashi akayi sa’a suma  ‘yan gidan masu tsabta ne sosai.
Mune zazzaune a bakin titin shara 80,  shara tamanin wata unguwa ce ko nace kasuwa da mutane suke yawan hada-hada a cikinta.
Kowannenmu ya saka abayarsa tsohuwa da silifas da kuma yagaggiyar qatwa,  wai a cewar su idan mukayi shiga mai kyau za’a zaci mu masu kud’i ne a hanamu sadakar yanda ya kamata.
Zaune muke a bakin titii, ko wannenmu leda ce a hannunsa ya bud’ata kuma ya rik’e,  amma sauk’in abin duk fuskokinmu a rufe suke

Dukda fuskata a rufe take amma hakan bai hanani jin kunyar wannan abin kunyar ba
Saboda nidai naga babu wata alama atare damu wacce ta nuna mu mabuk’ata ne,  lafiyar mu garas domin babu inda muka rasa a jikinmu.
A gefe guda kuma a kusa damu guragu ne da masu hannaye d’aya, da masu tafiya a kaikaice, wasu kuma a rarrafe, wasu kuma a dudduk’e,   dana gasken da kuma na k’arya,  saboda a gabana naga an d’aurewa wata yariya k’afarta waidan aga gurguwa ce a dinga bata sadaka mai yawa,  sai kuka takeyi yarinyar nan amma uwar ko alamar tausayi babu a tare da ita, itadai gurinta asamu kud’i da yawa kawai.
Duk wanda yayi niyar bamu sadaka  sai ya jifa mana a cikin ledar hannunmu, a hankali-ahankali naga ledata ta fara cika da manyan kud’ad’e,  Aisha dake gefena tsugunne itama ga dukkan alamu ta samu da yawa tunda naga sai zare manyan takeyi tana turawa a cikin zani,  

Bare kuma Sakina da tayi cikin k’arya,  tana zama da k’yar tana tashi da k’yar, sai kace wacce zata haifi ‘yan 2 aiko sai ruwan kud’i aketa yi mata
Niko duk sadda nakalleta sai na tuntsire da dariya
“Waike Wasila bazaki zazza6i manya manya  ki boye ba kin tsaya kina  kallon mutane kinata yi masu dariya sai kace wata ta6a66a?” Aisha take fad’a mun haka cikin rad’a’rada don kada wasu sujiyo mu
“Ban gane na 6oye ba? Kina nufin wai dama dake da Sakina duk na 6oyo ne kuke turawa a zani?…….

    *DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

  +966592551785
Kyakkyawar gaisuwa ta musamman ga ‘yan group d’inmu wato *Musha karatu*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

        

              *19*
       
Numfasawa tayi kana tace”to kai Adams in bayaga abinka, nida aka kawo bashi ina ni ina tura wasu kud’i gida?” 
Reply ya k’ara maido mata”ni kam ina ganin idan kina d’an tura masu wani abu zasuji dad’i, ace kusan watanki 2 anan amma shuru, gaskiya baki kyauta ba” 
Itam voice d’in ta tura masa kamar haka”to Adams idan nace zan basu wani abu,  ta ina zan basu,  kumama ina zan sami abin basun? Kudin aikina jaka da rabi ne kuma Khala Uwani tasan haka suke,  kawai mubar wannan maganar” ta fad’a tare da k’osawa da zancen nasa 
Domin a tunaninta yanaso ne ya d’orata akan hanyar sata, ita kuma bazata tab’a yada nasihar da Haja tayi mata ba.
Yau da gobe bata bar komai ba,  domin Wasila ta fara wayewa da taimakon Aisha da kuma k’awayenta na group,  saboda yanzu har tambayar Adams Kati takeyi ko kuma Shabakar ta idan ta k’are,  shi kuma a b’angarensa har jin dad’i ma yakeyi ta tambayesa wani abun,  shiyasama wani lokacin ko bata tambayesa ba zai turo mata katin 20 riyal ko kuma 50 riyal.
Yauma dai kamar kullum tana band’aki tana catin d’inta, (domin bata gama aikin nata ba bare ta kwanta a d’akinta tayi)
Adams ne ya turo mata voice akan yanaso idan ta dawo daga gidan aiki su samu had’uwa,  domin ko ba komai yanaso yaganta itama ta gansa, dukda sunga junansu a hoto amma shi a ganinsa hakan bai wadatar ba 
K’asa-k’asa takeyin magana domin kada uwar aikinta ta jita”insha Allahu zamu had’u amma ka k’ara hak’uri tukun,  kaga ni bak’uwa ce har yanzu”
Hanan ce take ta k’wala mata kira taji shuru”Ya Wasila! Ya Wasila! Shuru, Ya Shaqqala wen inti?” (Ke! ‘Yar aiki,  kina ina)
A hammam (ban d’aki) ta tarar da ita tana surutai k’asa-k’asa
Banga loakcinda ta shigo ba,  saidai ganinta nayi akaina tana ta faman yimun fad’a”Hada yakfiy, dahin Ana ma tubga shugul haggik Ya Wasila,  Dahin inti mu zayyannas,  inti tibga kaman zey sharmuta?” Wannan kad’ai na fahimta a cikin fad’an nata(Yanzu dai nagaji haka,  banason aikin ki, ya isa haka,  yanzu kin canza ba kamar da ba,  ko kinaso ki zama kamar karuwa ne?)
Hannayena na had’a guri guda alamar neman yafiya ina cewa”Billah ya Ummi,  ma’alish , haada aakar billahil-azim, ma sauyi kida abadan” (Dan Allah kiyi hak’uri uwata, wannan shine na k’arshe, na rantse da Allah bazan sake yin hakan ba , har a bada)
Juyawa tayi cikin fushi, ga dukkan alamu takai k’arshe gurin gajiya da halayen Wasila na yawan yin waya da kuma catin “Khalas maatubga shugul haggik,  Dahin ana tassil ATINE,  al yau mafi bukra inti ruhu bait haggukum (Ya wuce amma bana son aikin ki,  yanzuma zan bugawa Atine, yau ba sai gobe ba, ki tafi gidanku)
Na tsorata sosai da jin kalamanta, amma dukda haka saida sunanda ta fad’a ya bani dariya, wai Altine ce take kira Atine saboda gwaranci, saidai ban yadda dariyar ta fito fili ba na k’umsheta da hausa nace ” To dan kin koreni daga gidanki kuma sai me? Ai gari da yawa maye baya cin kansa, banza jan k’osai kawai” 
Dawowa tayi tace mani “ishgul?” (Me kika ce)
“Ana gul maa tubga ruhu bait” cewa nayi banaso na je gida” 
Tsuka tayi ta wucewarta d’aki.
Dakina na shiga domin rashin takamaimen amsar da zan bawa su Altine da Khala Uwani idan sun tambayeni,  Aisha na dokawa waya (bugawa)  domin jin tata shawarar
Bata dad’e tana ringing ba ta d’auka cikin fara’arta, ko gaisawa bantsaya munyi ba na rattabo mata matsalar da nake ciki
“Kinsan me zakiyi yanzu?”idan sun tambayeki me ya had’aku kawai ce masu zakiyi  kud’in aikinki ta rage maki, ke kuma kika nuna mata baki yarda ba,  shine ta k’ala maki wannan sharrin”
Ajiyar zuciya nayi domin gamsuwa da shawararda yayata kuma aminiyata ta bani,  saboda yanzu nad’an ja baya da Suwaiba,  munfi jonewa da Aisha kuma yanzu………..

   *DAGA TAKU*
*MAMAN JA’AFAR*
   +966592551785
Kyakkyawar gaisuwa ta musamman ga yan group d’inmu wato *Musha karatu*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             25

A zuciyata nace, idan ko haka ake sakin yara sagaga alakefinsu (Sunada damar yin komai) zuwa Saudia ga d’iya mace kuma budurwa zai iya zamowa da wata gagarumar matsala a 6oye

Ban k’arsa tunanina ba naji tana cemin
 “Ke malama ki had’a kayan da zaki tafi dasu kala 2 ko 3 kin tsaya kinata wani tunane tunane”
Nima jakata na d’auko na zari kayana kala 2 da kuma ‘yan kayan shafata da turare na had’a a wata jakar k’arama na zugeta na ajiyeta  gefe guda.
**********
Gida ne d’an  madaidaici, yanada d’akuna 2 a cikinsa,  sai d’an falo a tsakiya, da Mat’bak (kicin) da kuma hammam (band’aki) 
A falon kafet ne na gani shinfid’e a ko ina, sai kujeru da kuma tibin bango, inda a samanta aka d’ora mata risiba da kuma DVD sai kuma d’ima-d’iman  sifiku a gefe guda, wak’ar Adam A Zango naji  tana tashi ta ringin acikin sifikun.
A akan kujerun wasu ‘yan mata ne na gani kusan su 7 2daga cikinsu inaga zamuyi sa’anni , yayinda sauran suka girme mani kamar yanda Sakina ta girmeni

Dukkan su babu wasu masu kayan kirki a jikinsu,  wasu riga da d’an guntun wando suka saka, yayinda wasu kuma suka saka ‘yar mitsitsiyar riga da kuma dogon wando kowacce tanata harkokin gabanta
Da murnarsu suka tarbi Sakina suka rungumeta sunayi mata sannu da zuwa,  inaga hakan ya samo asali ne saboda shak’uwa da sukayi da juna, d’aya daga cikinsu ne naji tana cewa”  ni wallahi da najiki shuru-shuru nazacima bazakizo ba,  dan Aliyu ma saida yazo neman ki nace masa ina ganin kin fasa zuwa yin hutun ne wannan karon” 
Da alamun damuwa a fuskarta naji tace” Allah sarki Aliyu na, ashe da ya nemi wayata yajita a kashe saida yazo har gida nemana? Kinsan munyi da shi zamu had’u  yau,  to kuma sai wayar tawa tad’an samu matsala ta mutu, shine kawai na ajiyeta nace idan nazo nan na d’auki d’ayar tawa d’in”
Nidai mamaki ne ya kasheni jin firar da sukeyi a tsakaninsu,  ga dukkan alamu dai Sakina tana nufin wannan dai gidansu ne nasu na kansu wanda suka kama domin zuwa ijaza idan basu da niyar zuwa gida,  wato kenan tana nufin sai su cewa iyayensu suna gidan aiki alhalin suna nan gidan
Sakina ina kika samu Kyakkyawar yarinya ne na ganku a tare?”
“Afwan” wallahi na sha’afa ban gabatar da ita a gurinku ba, Wasila ga wad’annan duk k’awayena ne kamar yanda kika gani, kuma gidanmu d’aya amma ga aminiyata nan kusa dani” ta fad’a yayin da tadafa kafad’ar wacce naji suna kira da suna Sahar”
Nace” masu sannunku” 

Suka amsa cikin sakin fuska

Taci gaba da cewa”wannan ita kuma sunanta Wasila,  gidan mu d’aya da ita a makka, kuma sannan gidan aikin mu d’aya anan Madina”
Nanma dai muka k’ara gaisawa cikin wasa da dariya, daga nan kuma nasamu gefen kujera na zauna naja bakina nayi shuru,  inata kallonsu d’aya bayan d’aya.
“Wasila tashi ki shiga wanka mana ko kya d’anji sanyi,  nima yanzu zan shiga Hammam d’in, kin wani tsaya kina yiwa mutane raku6e-raku6e sai kace wata wadda bata magana….
Sahar ce ta tari numfashinta da cewa” Wai dama tana magane k’anwar taki?”
“Magana kai, dan idan kikaji ta bud’a wannan d’an k’aramin bakin nata tana yiwa mutane zuba da jero tambayoyi,  ke kyace wata ‘yar shekara 25 ce”
Tambayarta nayi inda zan ajiye kayana,  ta amsa mani da” ki ajiye duk d’akin da yayi maki mu nan APC mukeyi babu wani banbanci ko wariya a tsakaninmu” 
Dakin kusa dani nazaba domin ajiye kayana, d’akin ba laifi,  domin baza’a kirasa da  k’arami ba, gado uku ne a ciki,  irin gadon k’arfen nan amma k’araminsa irin na ‘yan mkarantar kwana, anan d’inma naga tibin bango.
Shima d’akin ashare yake tsaf kuma a goge tamkar na matar aure.
Bayan k’yaure na nema domin ajiye ‘yan kayana nasamu na shiga wanka kona d’an ji sanyi sanyi a jikina

Abinda ya firgitani, ya bani tsoro, kuma ya bani mamaki nagani a bayan k’yauren………….

   *DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

  +966592551785

Kyakkyawar gaisuwa ta musamman ga ‘yan group d’inmu wato *Musha karatu*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид

 

МДМДИ JдFдЯ

 

             21
“Wai wa za akai Jidda Dawwari ne? Ina Hammam naji kuna magana sama-sama bai amma banji sosai ba” Khala Asabe ce ta ida shigowa d’akin ta samu guri ta zauna
Khala Uwani ta numfasa kana tace” wai Wasila ce nakeso Salamatu ta tafi da ita idan ta tashi tafiya, saboda sau 2 kenan ana kaita gidan aiki tana karyosa tana dawowa,  tun bata saba da garin kenan sosai ba inaga kuma ta k’ara wayewa?” Ta k’ara da cewa wallahi gani nakeyi kamar nan gaba yarinyar nan fin k’arfina zatayi,  duka2 watan ta nawa a nan k’asar? Amma dubi yanda idanuwanta suka fara bud’ewa,  wannan d’iyar gani nakeyi anan gabama idan ta k’ara k’wari zata iya dukana” ta fad’a tana nuno ni da yatsa 
Dariya sukasa su duka.
 Nidai tagumi nayi na zuba masu ido ina ganin yanda aketa watanda dani sai kace wata hajar siyarwa.
Kana Asabe tace” nikam inda zaku bi ta tawa,  da kun bani ita nakaita gidan aikin Sakina,  tunda naji sunce suna neman k’arin mai aiki,  kinsan gidan da take aikin hawa 2 ne sama da k’asa”
Salamatu ce tace” ammafa ni ina ganin da wani gidan kuka nemo mata da zaifi,  saboda na lura tun lokacinda aka kama Mamar Sakina,  gaba d’aya yarinyar ta canza hali kamar ba itaba, Dan samarinta sunfi a k’irga wallahi,  kullum kunnenta nanik’e da waya tana fira da samari ko gajiyama batayi” 

Khala Uwani ce ta nuna Asabe da yatsa kana tace”ga mai laifin nan a gabanki kina kallo,  ai ita aka barwa amanar Sakinar amma tana kallo takeyin wani abin batayi mata magana”
Da fad’a Asabe tace” A’a kijiki da wata magana Uwani,  so kike nayi mata magana tayi mani rashin kunya? Ko kin manta rannan da nayi mata magana abinda tace mani a gabanku?  Ina ce mani tayi ba cewa akayi na saka mata ido ba,  cewa akayi kawai taje gidan aiki idan ta dawo ta kawo mani kud’in na turawa mamarta?” Ta kara da cewa” to saboda haka na tsaya matsayina, duk uwarda zatayi taje tayi,  nidai kawai abinda nasani idan wata yayi ta bani kud’i na turawa uwarta,  idan ta harhad’a ta tara kinga sai ta dawo ta rik’e ‘yarta” .
Dariya Uwani tayi kana tace”haba k’awata minene abin fad’a?  Maida wuk’ak’en mana,  abar maganar haka muci gaba da maganar da mukeyi” ta k’ara da cewa

 “yanzu ki k’ok’arta  kiyiwa ‘yan gidan aikin Sakinar magana,  inyaso naji yanda kukayi daga baya
Bayan na gama sauraren firar tasu ne , na mik’e nace

” Khala Uwani bara na lek’a nan mak’wabta gidan Matar Yakubu mud’anyi fira tunda ‘yan uwan nawa duk suna gidan aiki” ta kara da cewa”wallahi da basa nan gidan shuru babu dad’i ”
“To saikin dawo” amma ki dawo da wuri dan Allah, ki samu kiyi mana Nahas, (Wanki) nawa da naki, ga kayan can sun taru a Kassala (injin wanki) ta k’ra da cewa ki gaida mani ita”
Suma ‘yan d’akin suka bini da adawo lafiya ki gaida mana ita.
Raliya mak’wabciyar mu ce,  daga gidanmu zuwa nata babu wani nisa,  suna mutunci sosai da ‘yan gidanmu,  saboda ta iya zama da jama’a domin tana karrama kowa,  kuma abin hannunta bai dameta ba saboda batada rowa ko kad’an

Mijinta ba a nan makka yake aiki ba,  a Riyad yake aiki a Maqsala (gun wankin mota) yakanzo ijaza (hutu) ne duk bayan wata 2 zuwa 3

D’ansu d’aya mai suna Walid, dayake basu wani dad’e sosai anan k’asar ba,  kuma ita zuwan gata tayi,  domin tare da mijinta sukazo bayan d’aurin aurensu, ba irin zuwan mu ba zuwan bashi da za’a dannaka gidan aiki sai ka biya,  bayan uwar ribar da kuma za’a d’ora maka. 
Ban dad’e ina k’wank’wasa k’ofar ba ta bud’e, dayake anan Saudia babu gidanda zaka tarar a bud’e,  duk kuwa lalacewar sa,  kowanne gida ruf ruf zaka gansa.
Da murnarta ta tarbeni , dayake dama ita mai fara’a ce da kuma son mutane 
Sai dai kuma ga mamakina,  ganinta nayi ta d’au wani kalar wankanda ban saba ganin tayi ba,  domin a baya duk sadda muka zo gidanta mukan sameta ne da d’an guntun wando da kuma ‘yar k’aramar riga,  wani lokacin kuma da riga da wando masu d’an mutunci,  amma yau ga mamakina atamfa naga ta saka riga da zani,  kuma ga hijab ta d’auko ta ajiye kusa da ita,  da mamakina nace”Maman Walid yau kuma nageria aka tuna naga kin saka irin kayansu?” 
“Kai su Wasila sarkin surutu,  to nid’in ba ‘yar nageria bace da har zan saka atamfa kiyi mani tsegumi? ” ta fad’a yayinda take ajiye mani danbun naman kaza da kuma asir a gabana
“Dan Allah Maman Walid kodai kinyi bak’i ne daga nageria zakije ganinsu?” 
“Kai Wasila,  sai kace wata ‘yar jarida ? to tsaya da tambayar hakanan,  gidan Azuma zan tafi (Gidan biki ko suna ko makamancin haka)
“Kuma shine zaki saka wannan zundumemen hijabin?” Na fad’a ina d’aga hijabin ina dariya
Murmushi tayi kana tace” to inbansaka hijabi ba me kikeso insaka? Idan na saka abaya da qatwa (niqab)ace nayi k’auyanci to ba gara nasaka wannan d’in ba?” ta k’ara da cewa………

*DAGA TAKU*
*MAMAN JA’AFAR*
💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ
             22
    

Shifa suturta jiki ba k’aramin kariya bane ga ‘ya mace kuma musulma, da saka hijabi bashi da amfani, ai da Allah baiyi umarnin asakashi ba acikin ayoyi dayawa acikin alqur’ani mai girma

Idan banmanta ba akwai wata aya da take cewa Ya ayyuhan nabiyu qulli azwajika,  wa banatika,  wa nisa’il muminin, yudnina alaihinna min jalabiy bi hinnn.  (Wato yakai Annabi ka gayawa  matan,  da ‘ya’yanka,  da kuma matan muninai, su saka hijabinsu har ya kusanci k’asa )taci gaba da cewa
Kuma saboda mahimmmancin hijabin ne akayi umarni a sakashi acikin hadisa bila’adadin,  misali: Hadisin Aisha Allah ya k’ara mata yarda, bayan wafatin Annabi (S.A.W) da wasu shekaru tace,  da ace Annabi zaiga mata a yanzu da ya ce su rage fita, ko kuma ma ya haramta masu fitar gaba d’aya……
“To yayar Suwaiba idan kin gama wa’azin nima bara na gyara kwalliyata na rakaki gidan azumar,  domin ban ta6a zuwa ba,  su Aisha dai suna bani labarinta, yakamata nima yau naje na kashe k’wark’watar idona”
Gyad’a kai tayi kana tace “au yanzu Wasila dan ina fad’a maki gaskiya shine zakice mani yayar Suwaiba,  kenan bakwaso nida Suwaiba muna yi maku nasiha? ” to Allah ya shiryaku, ga kayan kwalliyar nan kiyi mu tafi,  amma kafin mu tafin yakamata kije ki sanarwa Khala Uwani ko kuma ki kirata a waya ko?”
“Bara dai na kiratan” na fad’a ina mai fiddo waya faga jakata irin mai dogon maratayin nan
Bata wani 6ata lokaci ba ta amimce, dama kuma abinda na tsammata kenan tunda dai tasan tare da Maman Walid muke.
*************
Wani k’aton hoshe ne mukaje (faffad’an guri) anjera kujeru gwanin sha’awa, kowacce taci kwalliyarta bakin gwargwado,  wasu sun saka irim kayan hausa (atamfa) wasu kuma shiga ce sukayi tamkar zasuje turakar mijinsu, ma’ana gasu sun saka kayan amma kuma kamar basu saka ba,  saboda dai kayan baza a kirasu da suturar arzi’i ba,  masu abaya da qatwa da kuma irin shigar Maman Waleed gaskiya kad’an ne aciki

Nikam dama riga da wando ne ajkina irin na fakistanai d’in nan,  yayinda na nad’e kaina da mayafin kayan,  bana mantawa a hoshen bukur Khala Uwani ta siyo mani ire irensu da yawa, dayake ba wani tsada ne dasu ba tunda na gumam ne,  amma kuma idan ka gansu sunsha Kawwi (guga) sai kad’auka sabi ne.
Bayan na gama k’arewa mutanen gurin kallo,  sai kuma na juya inda kid’a ke tashi domin naga me aka kunna tunda nidai banga ganguna ba,  ga mamakina sai naga mace ce Dj d’in , tasha riga da wandonta ta tsuke tana ta sakin sauti acikin kwafuta da kuma manya manyan sifiku,  a zuciyata nace ikon Allah,  yau fa ga mace da aikin maza,  matsawa nayi daidai setin kunnen Maman Waleed nace mata ” dama nan k’asar mace keyin Dj?” 
Dariya tayi k’asa-k’asa kana tace” ni Wasila bansan ko sai yaushe k’auyancin nan zai fita a kanki ba,  a ina kika ga taba ganin namiji yazo a gurin taron mata nan k’asar?  Ko kin ga cikinmu nan akwai namiji ko k’waya d’aya? To haka  tsarin k’asarsu yake,  bikin mata na mata ne,  haka bikin maza na maza ne zalla bazakiga macce ko d’aya a gurin ba. Kinga dai mata ne mu zalla ko? Amma tsabar tsaro kinga dai saida aka k’wace wayoyinmu kafin mu shigo nan saboda kar mu d’au hoto ko kuma video tun kowa dai gashi ga kalar shigar da yayi” 
Jinjina kaina nayi nuna alamar gamsuwa,  kana nace” ammafa wannan tsarin nasu ya burgeni matuk’a,  kinga ko ba komai an rage 6arna, tunda dama had’uwa mata da maza kusan duk shike haddasa komai” 
“Wallahi kuwa dai,  nima danaga wannan tsarin nasu abin ya bani sha’awa matuk’a,  amma kinga dukda haka su mutanenmu na Jidda (Hausawa) babu ruwansu kwamacalarsu kawai sukeyi mata da maza,  dansu har Dj d’inma inaga namiji ne suke d’aukowa”
Zaro ido nayi,  alamun mamaki fal a fuskata nace” kuma basa jin tsoron hukuma? ” 
“Kinsan ba lallai ne hukuma tasan ana shagali a wani gurin ba , tunda ko nan ai kinga a rurrufe yake ko? Amma dai bansan abinda suka taka ba”
Bayanta na shafa,  da mamakina nace a’a Aunty Raliya,  ina kika baro Waleed d’in ne bangansa a bayanki ba?  Tun a gida banji motsinsa ba, naso na tambayeki kuma shaf na manta wallahi”
“Gidansu Maryam na kaisa daya dameni da kuka,  kuma kawai sai naita yawo da goyo abayana sai kace Ke”
Dariya nayi kana nace”kai maman Waled,  kina nufin dai har yanzu ban waye ba ko?……
Ban k’arasa maganata ba naga mata sun fara shiga tsakar filin da d’ai-d’ai suna takawa cikin isa da tak’ama, tamkar dai duk d’inmu ba daga nageria muke ba ko kuma Niger
Lik’i naga anfara yi masu, kuma duk a cikin lik’in babu ‘yan riyal-riyal,  daga 10 riyal sai 50 riyar sai abinda yayi sama, kuma wuyan kowace idan ka kalla dam6are take da sark’ar zinari,  a zuciyata nace lallai nan ansha bauta gidan larabawa kana aka had’a wad’annan sark’ok’in……
*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*
Ina mik’a gaisuwa ta musamman ga ‘yan group d’inmu wato *Musha karatu*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             23

Anyi nisa sosai a gurin casu,  bamu ankara ba saidai mukaji alamar shigowar ‘yan garin (‘Yan kame kenan)

Da hanzari naga kowa yana raruwamar ‘yan tarkacensa, yana neman hanyar guduwa
 (Nima dai Maman Jafar ba’a barni a baya ba,  domin kamo hannun  Rahinatu Dikko ktn nayi,  nace mata k’awata!  mumafa yakamata mu nemi hanyar guduwa, domin ‘yan kamen nan wani lokaci ba mutunci ne dasu ba, idan idan suka tashi kamensu na tsiya babu ruwansu da kanada takardar izinin zaman k’asa, ko baka da ita, duk kwasheku zasuyi gaba d’aya, sai anje can kana a tantance)

K’ofar cika tayi sosai kowa yana neman hanyar guduwa, nida Aunty Raliya da muka rasa hanyar guduwa saboda cinkoson mutane  k’ark’ashin kujeru muka samu muka shige muka lafe,  tamkar babu kowa agurin
Mun d’an jima a gurin,  tunda a tunanina zamuyi kusan awa 2 a gurin,  saida mukaji k’ugin tashin motoci, kana muka tabbatar sun kwashi na kwasa,  sun bar na bari sunyi gaba.
Duk jikinmu k’ura muka fito, kayan kid’a kuwa,  da kayan ciye-ciye,  duk nan akayi wancakali dasu,  sai a sannan ma na tuna ashe ko amaryar bata kai ga fitowa ba wannan mugun al’amarin ya faru.
“Aunty Raliya  Kinga kuwa yanda hijabinjiki duk ya cukui-kuye yayi k’ura?” Na fad’a ina rik’e hijabin nata gami da k’yak’yata mata  dariya harda rik’e ciki
Sai a sannan ta lura da yanda hijabin yayi tamkar ank’wato ta daga bakin kura

Itama dariyar takeyi kana tace”Ai yarinya badan wannan 6oyon da nayi ba,  saidai kiji sunce Dammana jaka 8 (kud’in beli dubu d’ari8) kinga ko ina Yakubu zai iya biya mani Jaka 8? Ai saidai yace su turani kawai gida, kinga ko idan natafi najeria shi kuma yaushe zan ganshi? Ba saidai naji mugun labari ba cewa yayi aure?” Ta k’ara da cewa niko da hakan ta faru ai ko kwata na samu shiga zanyi na 6uya, ke ko cikin kashi ma na samu shiga zanyi…
Dariya nakeyi sosai harda k’walla nace”kice dai duk dan kishi kikayi wannan mugun 6oyon?”
Dariya itama tayi kana tace” to nidai Alhamdulillahi ban yada komai  nawa ba,  keko dubarki ki gani,  d’an gyalen ma da aka ratayo ana k’wanbo kin yar” ta k’ara da cewa “Laaaaa” wallahi Wasila har takalminki kin yar” tana fad’a tana dariya
Dube’dube na fara domin na tabbatar,  aiko maganar Aunty Raliya gaskiya ne,  domin har ‘yar jakar tawa dana ratayo ta gayu itama na yar,  sauk’inta ma wayata na hannuna
Faskewa nayi kana nace mata “ai ni koma me zanyi inada hujja,  tunda kinsan dai akwai uban bashi akaina, bayan kuma na biya bashin inaso nima nasamu nayi wani abin kaina, to akace ankamani a jaka 8 ai na mutu na gama,  tunda kinsan idan ta biya jaka 8 d’in nan cemani zatayi a jaka 20 ta kar6oni….
Dariya Raliya tayi kana cikin dariyar tace”kiji ‘yan  hajjojin nan suna fad’in jaka kaza da kaza,  sai kace wata jakar ratayawa” kana taci gaba da cewa nidai kam da ire-irena wad’anda aka kawo domin zaman aure ba neman kud’i ba  muna huta, kuma duk cikin gata mukazo, babu wani bashi da ake jiran mu  mu biya bare kuma musan hanyar gidan aiki ko wani abu mai suna Dawwari (Bara)……
“Inma ana biya aikun biya tunda gashi nan kunata haifa masu yara 
Muka saka dariya mu duka.

“Yanzu dai Wasila ba surutu ba,  jeki ki lek’o mana wajen ko sun bar ‘yan lek’en asiri” 

Baki na rik’e gami da zaro ido cikin alamun tsoro nace”ai wallahi Aunty sai dai mu kwana a nan,  dan bazanje garin lek’e  suyi awon gaba dani ba,  ni yunwa ma nakeji bara kiga naje  na zubo abincin can da suka haramtawa kowa cinsa”
Abinci ta zubo masu mai rai da lafiya suka kwasa sukayi nak’, kana ta suri wanu mafa’i  da wata ta yar yayin gudu, ta yafa suka nemi hanyar gida.

Khala Uwani ce ta tarbeni da masifa tana cewa”Hab Wasila wannan wane irin abu ne da zaki kama hanya ki fice a gidan nan tun kafin duhun dare yayi,  ki duba kiga k’arfe nawa yanzu,  kusan 2 fa na dare, duk kin bi kin tada mana hankali, kuma ankira wayar taki data matar Yakubun duk a kashe…
K’arasawa nayi bakin fanfo nad’an wawwanke jikina,  kana nadawo d’aki na sameta tana cin abinci, na zauna ina yamutsa fuska alamun gajiya nace” wallahi Khala Uwani yau Allah ne kawai ya taimakemu da saidai kuji mummunan labari (Nan ta kwashe labarin abinda ya faru ta fad’a masu)
Sallallami suka saka su duka,  harda Khala Asabe da take kwance ta mik’e ta zauna
“To Allah ya tsare kuma ya kiyaye gaba,  yasa muyi tafiyar kanmu”  kusan a tare suke fad’ar wannan maganar
Uwani ce ta juyo gami da fuskanta ta kana tace” to daga yau maganar yawo ta k’are,  gara ki tafi gidan aiki  ko kud’in babu yawa, da ki tsaya tan6ele a gida ki jawo mani a sara” 
A zuciyata nace,  wai na janyo mata asara sai kace jarinta ta zuba a gurin kasuwanci,  wata zuciyar tace mani jarinta ta zuba mana kuma riba mai d’inbin yawa take jira, kinga ko ai bazataso tayi asara 2 ba,  wato babu uwar kud’in kuma babu jarin…………

     *DAGA TAKU*
*MAMAN JA’AFAR*

Kyakkyawar gaisuwa ta musamman ga ‘yan group d’inmu wato *Musha karatu*

💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             24

Kamar dai yanda akayi magana tun farko,  cewa za’a samar mani aiki inda Sakina takeyi,  to kuwa hakance ta faru,  domin ‘yan gidan aikin nata basu wani 

6ata lokaci gun amincewa dani a matsayin mai aikinsu ba
Sai dai abin yazo mani ba yanda nayi tsammani ba,  domin wannan karon renon yaro aka bani d’an kimanin wata 6,  saboda dama sun riga sun k’aro wata mai aikin bayan Sakina, sai ya kasance ita aikinta gaba d’aya a saman benen ne,  wato gun matar d’an gidan,  yayinda waccen Habashiyar mai aikin kuma takeyi a k’asan benen gurin Sirikar wacce muke yiwa aiki kenan,  can kuma hawan k’arshe ‘yan’uwansu  suma suke zaune da iyalansu.

Sai yanzu nasan nayi dacen gidan aiki,  domin babu wata wahala da zanyi,  illa naci na k’oshi,  nayi wanka na ci gaba da renon d’a na wanda naji suna kira da Yuba
Shak’uwa ce mai k’arfi ta k’ara shiga tsakanina da Sakina kasancewar d’akinmu d’aya, sai dai bas kawai kowa da shinfid’arsa.

Wata rana muna zaune muna fira,  bayan ta kammala aikinta,  yayinda ni kuma nabawa Yuba madara na goyasa yayi bacci na kwantar dashi,  ta dubeni tace “Wasila gobe ne fa za’a bamu kud’in aikin mu ko?” 
Murmushi nayi wanda baikai zuci ba,  nace” ko anbamu kud’in aikinmu ai a banza tunda ba gida zamuje ijaza ba (hutu) shiyasa ni bana wata murna da k’arewar watan”
Murmushi Sakina tayi,  yayinda take had’a ‘yan kayanta acikin wata k’aramar jaka,   kana ta kalleni tace”nidai kam zan tafi ijaza amma ba gida zani ba” 
Da mamakina na kalleta nace”to idan ba gida zaki tafi ba,  ina zaki tafi? Nidai nasan ba kowa ne dake anan Madina ba,  da dai ma ace  makka ne to wannan ne zance bansani ba ko kinada ‘yan’uwa” 
Kallona tayi,  irin kallon nan na ke baki waye ba,  kana tace mani” banida kowa anan Madina,  amma munada gidan da muke biyan hayarsa anan Madina din…..
Da mamakina na tari numfashinta”ban gane kuke biyan hayarsa ba,  kedawa kenan?”
“Nida ire-irena ‘yan gidan aiki mana, anan muke yin ijazar mu,  dan sai munga dama muke zuwa gida yin ijaza”
A zuciyata nace ikon Allah, ashe dama maganar da su Khala Asabe sukeyi akanta gaskiya ne? A fili kuma sai nace”kenan goben can zaki tafi?” 
“Eh can zan tafi,  ke kuma sai ki zauna kiyita bauta babu hutu,  in kuma zaki bini ne mu tafi to”
Shawar-wari nayita yi acikin raina, saboda firar da naji su Uwani sunayi a kanta, shiyasa zuciyata bata gamsu d’ari bisa d’ari akan wannan  bin nataba

Amma kuma wani 6angaren na zuciyata yana shawartata akan na bita nad’an samu na huta da kukan yaron nan kona kwan biyun ne,  saboda Yuba shegen kuka ne dashi na masifa, bansan lokacinda zuciyata ta amince da bin natan d’ari bisa d’ari ba
“Ehwa Sakina” Nima zan biki muyi ijazar tare” 
“Yauwa ko kefa, zamuje kiga gidan namu,  babu abinda muka rasa acikinsa, wasun mu ma har wata 1 sukeyi a cikinsa suna hutawarsu”
Nace” to idan kuma sukayi wata d’aya basa gidan aikin to mezasu cewa marik’an nasu kan maganar kud’in aikin?” 
A jiyar zuciya tayi kana tace” Ai su marik’a babu ruwansu da bibiyar halinda kake ciki,  su indai zaka dinga bada kud’in aiki duk wata,  ai basu da matsala da ko kaje gidan aikin ko baka je ba……. 

  *DAGA TAKU*
*MAMAN JA’AFAR*

Ina mik’a gaisuwata ta musamman ga ‘yan group d’inmu wato *Musha karatu*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             31
Abinda Aisha tafada kuwa gaskiya ne, domin matar da mukaje gidan nata akwai natsuwa da kamala,  dukda bamu zauna wuri daya da ita na wani lokaci ba,  amma naga alamun zatayi addini, har tambayar zuciyata nakeyi ko ta ina wannan kamilar ta had’u  da Aisha har suka k’ulla k’awance?
Itama dai batafi sa’ar su Aishan ba domin amarya ma ce ga dukkan alamu
Cikin murna da farin ciki ta kar6emu, batare da 6ata lokaci ba Aisha ta gabatar mata da buk’atarmu ta neman abinci, ai kuwa ga mamakina k’atuwar kula ta ciko mana da dafa dukan shinkafa wacce taji kayan had’i.
Muna tafe a hanyarmu ta dawowa gida,  inata sak’e-sak’e a zuciyata game da gidan wannan matar da mukaje wacce naji Aisha ta kirata da suna Fatima, hardai na kasa hak’uri na fito fili nace “Wai niko Aisha ita wannan k’awar taki anan mijin nata ya aureta koko daga Najeria ya auro ta yakawo ta nan kamar Maman Walid? Saboda naga natsuwarta ta da iliminta da kuma hankalinta bakamar namu ba”
Murmushi tayi wanda baikai zuci ba,  wanda naji hausawa nacewa yak’e kafi kuka ciwo, kana tace “Hmm Wasila kenan,  Ai yafiya yawan samarinmu na hausawa bansan miyasa ba basa son auren irinmu ‘yan dawwari ko ‘yan gidan aiki ba,  sun k’wammace idan suka tashi aure su zuba ko nawa ne a Najeria ko Niger a auro masu mata masu hankali da natsuwa su kawosu nan,  ke babban abin takaici ma zakiga wasu mazan ko k’arin aure suka tashi yi saidai suyo daga k’asarsu,  mu kuma ‘yan matan nan tsakaninmu dasu sai yaudara, d’ai-d’aiku ne ake samu suna auren namu,  kuma suma idan sun aura basa d’aukar d’awainiyar duka,  daga angama amarci zakiji sun fara baki shawara akan ki fara fita neman kud’i saboda ku dinga d’aukar nauyin gidan tare,  a hankali zai dinga k’wace abinda kike nemowa cikin hikima,  idan kuma ya had’aki da yaro 1 ko 2 sai ya sakar maki komai, idan kinyi musu kuma ya mayar dake k’aramar bazawara, amma zo kiga tarairaya da rarrashi idan daga k’asarsu ya aurota, sai dai kuma ba duka aka taru aka zama d’aya ba domin na Allah basa k’arewa”  ta k’arashe maganar tata cikin nuna alamun damuwa
Nima dai magan-ganun nata sun sakani jimami gami da zullumin halinda rayuwata take a ciki,  domin  har yanzu bansan inda rayuwata ta dosa ba bare kuma nasan makomarta, saboda tunda nazo k’asar nan ko cikin fira ban ta6a jin ance idan aka mayar dani gida kaza da kaza ba,  kullum saidai inji  ance Allah ya kawo mani wani na gari nayi aurena anan, wai auren Nigeria aurn wahala ne, to indai haka shima auren nan d’in yake to wallahi gara na Nageria d’in sau dubu
A haka muka k’arso gida muna fira jefi-jefi akan rayuwarmu ta nan gaba
Kowa yaci ya k’oshi yayi nak da abincinda muka kawo, sai kuma muka fara har-had’a  kayanmu domin haramar komawa gida makka gobe da safe idan Allah ya kaimu.

 ************
Yusuf ne kwance akan katifarsa yana tunanin hanyar da zaibi domin ya bayyanawa Wasila irin sonta da kuma k’aunarta da suka dad’e suna kai komo acikin zuciyarsa
Yayi tunani iya tunani,  kuma yayi nazari iya nazari amma har yanzu yagaza gano dalilinda yasa son Wasila yak’i fita a ckin ransa, domin indai kyawu ne ko natsuwa ilimi ko kuma addini da nasaba duk Wasila bata cancanci asota dansu ba, hasalima Farida yake ganin kamar zata fita natsuwa,  domin kuwa aganinsa batada ko d’aya acikin lissafinda ya jero
To miyasa nakeson wannan yarinyar? inaga yawan barkwancinta da kuma surutunta yasa tayi kwance acikin raina ta kasa fita 

Anya kuwa zata amince ta kar6i soyayyata? 
Wata zuciyar tace masa da guduma kuwa,  domin ka cancanci duk wata wacce kace kanaso ta amsa maka cikin gaugawa batare ba 6ata lokaci ba,  saboda duk wata suffa ta had’add’en namiji ka had’a, Yusuf kana da kyau da kuma matsakaitan shekaru,  ga ilimin addini dana zamani…

Ke zuciya shifa so duk ba a wannan yake ba, amma duk da haka zan jaraba nagani ko zata amince 
Wayarsa ya d’auko ya lalumo lambar ta ya danna domin kiranta
Can k’asan jaka naji k’arar wayar tawa domin kuwa dawowarmu kenan daga jidda ko zama ma bamuyi ba

Da k’yar na lallumota nakara a kunnena tare dayin sallama
Amsawa yayi cikin muryarsa mai dad’in sauraro kana ya k’ara da cewa “K’anwata barka da salla da fatan anyi salla lafiya”

Lafiya k’alau na fad’a cikin murya mai had’e da girmamawa domin ina ganin girmansa da kuma mutuncinsa  matuk’a

Bayan mun gama gaisawa naji shuru,  shi baiyi min sallama ba kuma banji ya kashe wayar ba,  da dai naji shurun yayi yawa ne nace “Yayana kodai ka shirya mana Haflar salla ne?” (Fatin salla)
“Haba K’anwata Haflar salla kuma sai kace wani gaye? Ni wata muhimmiyar magana ce tasa nakiraki gashi kuma narasa ta inda zan fara, amma kafin na fad’a maki yakamata naji lafiyar saurayinki,  da fatan shima yayi salla lafiya?”
Murmushi nayi kana nace “Au Adams lafiyarsa k’alau wallahi yanzunma da nazo d’aga wayarka naga kiransa da yawa,  wai so nakeyi sai na samu natsuws kana na kirasa, kasan dawowarmu kenan daga Jidda cin Zahama……

*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*
Ina mik’a kyakkyawar gaisuwata kuma ta musamman ga duk masu karanta wannan littafin

💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             32
Gabansa ne ya fad’i lokaci guda,  saboda tunanin abinda kaje ya dawo,  amma dukda haka sai ya daure yayita maza yace “To idan kunyi wayar kice masa yayanki yana gaidashi”
Cikin fara’a na amsa da “Insha Allahu kuwa zan fad’a masa,  kasan kuwa kusan kullum shima sai yace na gaidaka domin ina yawan basa labarinka da kuma irin kulawarda kake bamu nida Farida….”
Shi dai bai tsaya ya ida jin k’arashen maganar tata  ba ya kashewa wayarsa
Jefar da wayar yayi saboda wani  matsananci kishi da yaji ya taso masa.
Bayan nayi wanka na rama duk sallolinda ake bina na samu wuri na ware kaina gefe guda domin yin waya da Sahibina
Bugu d’aya ya d’aga murya a sanyaye ” Haba Wasilata kinsan kuwa ko tun yaushe zuciyata takeyi mani k’una dalilin d’aga wayata da bakiyi ba? Wallahi nakasa sukuni,  hankalina ya kasa kwanciya, kawai tunanin babban dalilinda yasa kika k’i d’aga wayata nakeyi…..?
“Allah sarki Adams d’ina na tuba kayi mani afuwa,  nima wallahi bada son raina nak’i d’aga wayarka ba, kasan muntafi zakki-zakki ne Jidda,  to sadda kaketa kiran wayarma muna kan hanyar dawowa nan makka, kuskurena d’aya danace bazan kiraka ba sai nayi wanka nayi salla na natsu tukun,  amma a gafarceni Habibina kaina bisa wuya”
Kalamanta sunyi matuk’ar tasiri a gurinsa domin lokaci guda ya saki ransa, murmushi yayi gami da ayyanawa a ransa hak’arsa ta kusan cimma ruwa
“Zan hak’ura amma bisa sharad’i d’aya”
“To na amince fad’i sharad’in ina sauraronka Na Wasila”
Dariya yayi sosai har ina jiyo sautinsa kana yace “Sharad’in ba wani mai wahala bane kawai zuwa gidana zakiyi ki kar6i Mala’idin d’inki” (barka da salla)
Ajiyar zuciya nayi gami da tunano magan-ganunda mukayi da Aisha a Jidda 
“Adams dan Allah kayi hak’uri kadaina wannan maganar ta zuwa gidanka domin ni a ganina kamar bai dace ba,  kuma yanzu idan wani ya ganni na shiga gidan maza me kake tunanin za’a d’aukeni?”

 “Kawai malama fitowa fili zakiyi kice mani zargina kikeyi bawai ki tsaya wani kame-kame ba, idan har wani abu nakeso a gurinki ai akwaishi a gurin dubban matanda suke bina,  kuma sun fiki wayewa sun fiki komai , amma dukda haka ni batasu nakeyi ba,  ke d’in dai nagani kuma ke nakeso amma ke kullum baki da burinda ya wuce ki wulak’anta ni kuma ki kunyatani,  to Wasila nagaji,  nagaji nace, insha Allahu daga rana mai kama data yau ni Adam bazan k’ara ce maki ki ziyarceni…..
Bai tsaya ya saurari me zance ba kawai ya kashe wayar
Jikina yayi sanyi matuk’a da jin zafafan kalamansa agareni, saboda har ga Allah yanzu kam na kamu da son Adams matuk’a, jinsa nakeyi tamkar wani 6angare na Jikina,  bana jin zan iya rayuwa batare da shi ba
Ina nan zaune sororo in sak’a wannan in kwance wannan naji andafani,  d’ago kaina nayi muka had’a ido da ita,  Suwaiba ce kuma ina tsammanin taji tattaunawarda mukeyi nida Adams
“Wasila lafiya kuwa naganki cikin yanayin damuwa daga gama waya? Ko dai wani ne ya 6ata maki rai?”
A zuciyata nace hmm Malamar nan kona fad’a mata damuwata ba wata mafita zata kawo mani ba saidai taita jawo mani ayoyi tana fassarawa da hadisai
“Babu komai wallahi, dama Farida ce mukayi waya da ita take sanar mani wai bata jin dad’in jikinta shine duk na shiga damuwa”
Murmushi tayi irin mai nuni da cewa na rigaki zuwa duniya d’in nan ” Wasila kenan,  wato dan karna fad’a maki gaskiya kike 6oye mani damuwarki ko? To ai ko na fad’a sai kinga dama zakiyi amfani da abinda nace maki d’in domin ko Allah (S.W.A) cema Annabi (S.A.W) yayi Innaka lan ta hadiy man ahbabta wala kinnallahu yahadiy man yasha..wato kai Annabi bazaka iya shiyar da wanda kaso ba domin Allah shiyake shiryar da wanda yaga dama, kinga kenan ji ne yazama dole ba yarda ba”
A zuciyata nace tofa, anyi gudun gara an fad’a gidan zago, abinda na guda d’in dai saida ya faru
“Na fahimci laifina d’aya ne a gurin mutanen gidan nan, wato bin umarnin Annabi (S.A.W) da nakeyi,  saboda yace idan kaga abin k’i,  ka kaudasa da hannunka koda bakinka ko kuma da zuciyarka,  to saboda yace mafi raunin imani shine wanda ya kauda da zuciyarsa d’in shiyasa nake k’ok’arin naga na kauda da bakina, amma ina ganin nan gabama sai na fara kaudawa da hannun nawa tunda na lura bakwa fahimta da baki mutanen gidan nan” ta k’arashe maganar tata cikin zaulaya kana taci gaba da ayyukanta
Nima dai dariyar nayi dukda kuwa damuwa ce fal a cikin zuciyata, domin mafita kawai nake nema ido rufe, wa zan nema? Aisha ko Sakina?….
*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

            28

“Hmmm zauna nan sakarya ana harka ke kin tsaya wani k’auyanci, ni wallahi na rasa gane kalarki,  ace kusan shekararki 2 anan k’asar amma har yanzu baki waye ba,  to wai idan kika tara kud’in wace tsiya zasu tsinana maki? Naga dai ba komai za a siya maki ba,  kuma ba sisin da za a turawa wani naki, iyakarki neman kud’in fa, ke da shan wahala wata k’atuwar banza da kwasar garar, kura da shan bugu gardi da kwasar kud’i”  

Ta d’an tsaya da maganar tata kad’an tana waige-waige domin ta tabbatar babu wanda yake jinta
Dariya abin nata yabani, kana cikin dariyar na daure nace”ai yanda kika zak’al-k’ale kina koro wa’yan-nan bayanan bai kamata kuma ace kina tsoron wani yaji ba,  haba jarumata ci gaba mana…..
Tamke fuska tayi gam alamar babu wasa kana ta d’ora da cewa”banza babu abinda kika iya sai dariyar wofi da kuma shegen surutu,  amma kin kasa yiwa kanki wani tanadi saboda gaba,  to wallahi ina mai tabbatar maki idan kika daka  ta wa’yan-nan  Hajjojin da sannu zakiyi kuka da idanuwanki

Kinga nidai bama wata ce ta kawoni nan k’asar ba,  k’anwar uwata ce mahaifiya,  amma saboda wannan banzan neman kud’in ke kya rantse bamu had’a wata dangantaka da itaba

to Wasila kiyi tunani mana,  ina tun kafin zuwanki nan k’asar aka kama k’anwar mahaifiyar tawa,  amma ko sau 1 bata tab’a tambayata halinda nake ciki ba,  idan kinga ta tambayeni to akan kud’i ne zancen nata zai tuk’e,  shiyasa nima indai dama ta samu,  to kuwa damawa nakeyi bana sanya bare kuma wasa, dan hausawa ma sunce wai abari ya huce shiyake kawo rabon wani”
Lallai kam gaskiya ne abinda Aisha take fad’a domin ni har yanzu ban ta6a jin ance anbawa wani nawa abinda yakai darajar 20k ba,  alhalin duk watan duniya nakan d’auki albashin 150k koma sama da haka,  kai ko irin d’an d’aurin nan da kowa yakeyi (tura kaya k’asar ku, na sayarwa ko na amfani) ni banga tayi mani ba,  babban ma abinda yake bani haushi da ita shine ko katin wayar da take d’an siya mani idan nazo ijaza ta daina,  kai har ifada ma wadda zan saka idan ina jini nike siyawa kaina da ‘yan kud’in kyautar da muke samu a gidan aiki idan sunyi bak’i

Wato kenan idan ban bi shawarar Aisha ba haka zan k’are kenan a wahale? Dolena na d’au mataki kuwa tun kafin wankin hula yakaini dare.
Duk baifi cikin ‘yan sakwanni nagama wannan tunanin ba kana na kalleta,  nima wannan karon babu wasa acikin maganar tawa nace

“Maganarki gaskiya ce Y’ar’uwa kuma insha Allahu nima zanyi k’ok’ari na dinga tara d’an wani abin nawa” na k’ara da cewa”to amma wani hanzari ba gudu ba,  idan na 6oye kud’in ina zan ajiye inda bazata gani ba? Kinsanfa kusan kullum cikin binciken kayana take sai kace wata 6arauniya”
Da yake cikin qatwa muke (niqabi) babu wanda zai fahimci fira mukeyi a tsakaninmu,  kuma bama d’aga sauti sosai tunda maganar tamu ta sirri ce,  amma duk da hakan da larabawa da Fakistanai da bungalai sai ruwan kud’i sukeyi mana acikin ledejinmu
“Hm ai ba akayanki zaki ajiye ba malama,  nima idan na tara ba ajikina nake ajiyewa ba,  saboda Khala Tabawa nima binciken takeyi mani,  shiyasa nake kaiwa Maryama mak’wabciyarmu tana ajiye mani,  kuma matar batada matsala yanda kika bata ajiya haka zakizo ki kar6i abinki sai d’an abinda kikayi niya kika bata”
Jinjina kai nayi alamar gamsuwa “aiko indai hakane bara nima kiga na fara zare mayan-manyan kafin ta ankara”
Dariya tayi k’asa-k’asa kana tace “yauwa y’ar gari,  haka nakeso, wato fad’a da cikawa lokaci guda”
A tsorace gami da rashin sabo nad’auki  abinda na d’auka yanda bazata ganeba nima na soke acikin wandona, ammafa dukda hakan gabana bai daina fad’uwa ba,  saboda dama can ni matsoraciya ce,  kawai mutane ne basa ganewa saboda inada yawan surutu.
Anan mukayi sallar magariba dab da sallar isha k’afa ta fara d’aukewa samun kud’in yaja baya,  kowa ya fara haramar komawa gida, muma dai ba a barmu a baya ba domin Khala Asabe ce tazo ta umarcemu da mu tashi hakanan mutafi gida.
A d’akinda aka bamu masauki kowa ya baje kud’insa yana k’irgawa,  daga wanda ya samu fan 50 (50k) sai wanda ya samu fan 70 (70k) wasuma har jaka 1 (100k)naga sun samu,  nidai nawa  Khala Uwani ba a gabana ta k’irgasu ba,  shiyasa ma bazance ga abinda nasamu ba
Bayan munyi wanka munyi salla munci abinci, kana kuma muka nemi shinfid’unmu muka d’an mik’e hak’ar-k’arinmu saboda musamu muyi bacci ko yaya ne domin gobe idi ko masamu mu tashi da wuri  mu nufi masallacin idi muga abinda zamu samo kuma…….

 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             29
Duk d’akin kowa ya gama shiryawa, ko ince duka gidan,  domin masu gidanma jiya tare dasu muka fita zakki-zakki,  Suwaiba ce na gani zaune abinta tana sauraren qira’a tana bin karatun cikin nishad’i,  ga dukkan alamu bata da niyar shiryawa

 “Waike Suwaiba so nawa zance maki kitashi mutafi? Nifa nafara gajiya da wannan rashin kunyar taki, wallahi idan kika kaini k’arshi bazakiji dad’in matakin da zan d’auka a kanki ba” Khala Amina ce ke fad’ar haka tana tsaye akan Suwaiba da ‘yar ledarta a hannunta, ga dukkan alamu ta dad’e da shiryawa
“Nifa Khala na fad’a maku babu inda zani, yanda k’afata bata taka wajen kar6ar haramun ba jiya,  to haka yauma babu inda zanje wallahi” 
Baki suka saki su duka alamar mamaki,  yayinda Khala Amina tace” Eh lallai d’iyar nan, wuyanki yayi kauri har ya isa yanka, wato mu zaki kalli tsabar idonmu kice muna cin haramun ko?”
“Nidai bance kuna cin haramun ba,  amma dai nasan bakwa daga cikin wad’an da ya halatta suci sadaka, saboda Allah (S.W.A) cewa yayi ita sadaka tana kasancewa ne ga talakawa,  ko kuma miskinai,  wani gurin kuma Allah yace ko matafiyi.. da dai sauran mabuk’ata wad’anda daka gansu kasan a buk’ace suke, kinga ko idan har baka cikinsu kuma kaci sadaka ai kaci haramun ko? Annabi  (S.A.W) ma cewa yayi duk jikinda aka gina da haramun bashida wani sakamako face wutar jahannama, To ni kuma  tsoro nakeji nakasance abincin wutar jahannama shiyasa kukaga ina k’yamatar barar, ni wallahi gidan aiki duk wahalarsa zanjesa amma bara kam sam, badani ba wai gad’a a mak’abarta”
A zuciyata nace lallai Suwaiba tanada k’arfin hali, nikam ina zan iya tsayawa ina gayawa Khala Uwani wa’yan nan magan-ganu haka, amma kodayake bansan abinda ta taka ba,  tunda idan kaji makaho yace azo ayi wasan jifa ai ina ganin dutse ya taka
Gyara tsayuwata nayi domin ci gaba da kallon yanda wanna rigima tasu Suwaiba zata kasance
Amma a fili hak’uri muke bawa Khalan saboda gani da mukayi ta harzuk’a
“Ku k’yaleni na koyawa shegiyar yarinyar  nan hankali, har mu zata kalla tace mana muna cin haramun? To haramun d’inda kike fad’a ita ake aikawa mai dattin hula yana washe baki yana alashi albarka” Khala Amina ce take fad’ar haka cikin fushi mai tsanani
Bamu tsaya mukaji yanda wannan chakwakiyar zata k’are ba,  su Khala suka tasamu gaba sai masallacin idi, bawai sallar idin muka nufa kai tsaye ba,  a’a da sallar da kuma had’awa da d’an dawwari……..

    *DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐f💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             30
Sauri-sauri gudu-gudu muka samu muka iso masallacin saboda munso mud’an makaro.
Iya kallonka kowa ka gani a gurin yaci kwalliyarsa yana k’amshin turare, manya da yara da kuma maza da mata, sa6anin mu da mukazo yin bara da muka saka kaya duk’un-duk’un, saboda ko wankan idinma inaga babu wanda yayi acikinmu.
Gaskiya abin ya bani sha’awa domin nidai tunda nake a k’asarmu ban ta6a ganin Hajar taje masallacin idi ba bare kuma azo kanmu mu yara,  saidai nasan ran idi mukanyi wankanmu muyi kwalliya gami da saka sabbin tufafi,  bayan mun gama rabon abincin salla kuma sai mutafi ziyara da sauran shagul-gulan salla kamar yanda al’ada ta tanadar.
Dukda bansan abinda nasamu jiya ba amma na tabbatar kud’in yau basu kai na jiya yawa ba,  bamu samu wasu kud’in kirki ba sai uwar shinkafa da suka tara mana tuli,  dukda idan sun bamu muna sayarwa wasu maza wad’anda suke siya a kusa damu amma dukda haka saida muka rasa yanda zamuyi da sauran

Arabiyar wani namiji muka ara (baro)muka lollodata muna ja a hankali muna tafiya saboda rinjayarmu da takeyi
Yauma dai banyi sanya ba na zari na zara acikin kud’in nawa na bar na bari dukda ba wani yawa ne dasu ba
Ga mamakina suma Jiddah banga suna wani shagul-gulan salla ba kamar yanda naga makka suma basu damu dayi ba

Domin muna dawowa daga cin wannan zahama (lokacin samun kud’i) muka samu abinda mukad’an rubta acikinmu kowa ya sheme sai bacci, bacci kuwa mai nauyi mukeyi domin rabonmu da samun wani gamsasshen bacci tun kafin muzo nan
Tun safe bamu muka farka ba sai kusan magariba,  kowa ya gabatar da sallolinda ake binsa kana kuma aka fara shawar-warinda inda za’a samu abin sakawa a bakin salati
 “To y’an mata ku tashi ku d’an d’ora mana wani abu mana,  kun tsaya sai hamma kukeyi muma muna hamma sai kace babu kayan abinci a gidan” 

cewar Khala Amina kenan yayinda take gyara kwanciyarta, ga dukkan alamu inaga baccin bai wani wadatar da ita ba
“Nidai kam a k’oshe nake shiyasa bazan wani sha wahalar d’ora girki ba tunda baci zanyi ba” Aisha ce mai fad’ar haka tan danne-danne a wayarta
“Toke Sakina tashi ki d’ora mana tunda ita Aisha k’iuya ta hanata tashi,  wai hadda wani cewa a k’oshe take ko ubanmi taci?”
“Nimafa su Khala kusan hakan take, dan wallahi a gajiye nake,  k’ilanma nafi Aisha gajiya saboda wannan uban ciki na k’arya da nayi, duk yabi yayi mani wani hak’e-hake sai kace na gaske…”
Dariya mukayi mu duka kana nace”Ai wallahi naso a ce da kikazo cire cikin nan yak’i ciruwa yazama na gaske muga k’aryar izgili”
Harara ta tayi cikin wasa kana tace “aiko  dana shiga uku,  yanda dama su o’i ke zargina kuma aga haka,  aidai sai suji dad’in kaini gaba”
Tana maganar tana kallon Khala Asabe ta gefen ido, anan na tabbar ita take yiwa habaici.
Daga can gefe mukaji Suwaiba tace “ni wallahi harma kun tuna mani da kissar Annabi Isah, kunsan shima Annabi Isah da d’aukar cikinsa da kuma haihuwarsa duk a lokaci guda suka wakana, kuma sannan haka Allah yaga dama ya haliccesa ba tare da mahaifi ba…….
Bata k’arasa zancenta ba Aisha ta katseta tace “dalla malama yiwa mutane shuru, ke sai mutane suna zaman-zamansu lafiya,  babu wanda ta tambayeki ki fara jawowa mutane aya da hadisi, ki bari mana sai anbuk’ata kana kiyi, ni wallahi banason iyayi da nuna kai kafi kowa ilimi” ta k’arashe maganar tata da yin tsaki
“Wasila taso ki rakani can baya gidan wata k’awata na nemo mana abinda zamuci”  Aisha ce ke fad’ar haka yayinda ta mik’e tsaye tana saka abayarta
Da sauri nima na zira tawa abayar domin inason yawo da Aisha ko Sakina sabida koba komai zamu samu sakewa muyi firarmu harma nasamu k’arin wani ilimin da kuma y’an dabarun da ban sani ba
“Ku kuwa ina zaku samo abinci da daren nan bayan kunsan kowa yafita yadawo a gajiye yana hutawa?”
Khala Uwani ce mai fad’ar haka bayan ta cika bakinta da burodi tana korawa da ruwa
“Ai Khala ita wannan k’awar tawa mijinta baya barinta taje ko ina,  babu abinda mijinta ya rageta dashi, kuma itama inda take burgeni bata sa6a umarninsa, ai Wasila zaki ganta idan mukaje, wallahi rayuwarta tana matukar burgeni” 
Nidai murmushi kawai nayi nace mata “mutafi muntsaya sai 6ata lokaci mukeyi…………

   *DAGA TAKU*

*MAMAN JA’FAR*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

                33
D’akinmu na shiga kai tsaye domin nasan acan zan samesu, sai dai kash nayi rashin sa’a domin Suwaiba da Hadiza ‘yar can mak’wabtanmu kawai na tarar a d’akin, waya na bugawa Sakina domin jin inda suke
Cemun tayi suna kasuwa wai sun tafi sayen kayan Idi domin gobe zasu tafi Bahar Maliya da kuma Malahi (gurin shak’atawa)
“Amma Sakina meyasa baku gayyaceni zuwa kasuwar ba ko dan bakwaso ku tafi dani Malahin ne” nafad’a cikin yanayi na 6acin rai domin banji dad’in abinda sukayi mani ba
“To Wasila yaza’ayi na gayyaceki zuwa kasuwa bayan nasan ba kud’i ne dake ba”
Dariya nayi kana nace “Nimafa na fara wayewa domin yanzu haka inada kusan fan 70 nawa na kaina” Na k’arashe maganar tawa cikin nuna isa ina wani hura hanci
Dariyar tayi harda k’yak’yatawa “Kice kin fara zama ‘yar gari? To bakida matsala, yanzu fad’a mani duk abinda kikeso na siyo maki a kasuwar sai na taho maki dashi inyaso idan muka dawo sai ki bani kud’in”
“Duk abinda kuka siyo nima ki siyo mani madamar bai haura kud’ina ba”
“Kice mudai siyo maki iya kud’inki kawai amma maganar duk abinda muka siyo ai bazaki iya ba,  domin ko abaya ta fan 40 muka siya,  banda waya da muka sake da kuma kayan shafa, yanzu haka Mala’idin muke siya zamu kaiwa samarinmu Hadiya (Gift) 
“Aiko har kin sosa mani inda yakeyi mani k’aik’ayi domin yanzun nan muka gama waya da Adams yake ce mani wai nazo na kar6i mala’idin d’ina, dana nuna masa bazanzo ba bakiga irin fushin da yayi ba,  shiyasama nace bara na kiraki naji shawarar da zaki bani”
“To keko miye dan kinje kin kar6i mala’idin? Gaskiya Adams yana k’aunarki ma sosai mu bakiga mu muke had’a mala’idin d’in zamu kai masu ba? Nidai shawarata kawai kije ki kar6o yanzu hakama wata k’atuwar kyauta zaiyi maki tsautsayi na neman hanaki zuwa”
Ajiyar zuciya nayi “to Sakina kuma kina ganin wace dabara zanyiwa Khala Uwani ta barni naje gun nasa?”
“Indai dantasu Khala ne karki dami kanki dan ko ce mata kikayi zakije ki kar6o mala’idin gurin saurayinki ba hanawa zatayi ba, dansu kud’i sun fiye masu komai a rayuwa,  amma saboda ad’an saya,  sai kice mata kin tafi gidan Maman Walid kawai” 
“To kuma yaushe kike ganin zan fati gun nasa d’in?” 
“Ko yanzuma sai ki tafi,  ko kina wani abun ne a gidan? Saura kuma idan kinje ki nuna masa ke k’atuwar bak’auya ce”
Gama wayarmu keda wuya dama na riga nayi wanka k’ara shiryawa kawai nayi na fesa turare na zari jakata nacewa Khala zan shiga nan gidan Maman Walid yanzu ta kirani wai zan d’an kama mata wasu ayyuka”
Bata musa mani ba saima cemani datayi adawo lafiya.
Fitowata k’ofar gida keda wuya nad’auko wayata acikin jaka na kira Adams, saida ta dad’e tana ringin kana ya d’aga “Me akayi kuma?” abinda naji ya fad’a kenan cikin fushi
“Allah sarki Habibina maida wuk’ak’en,  dama tambayarka zanyi hanyar gidan naku….
Cikin matsanancin farin ciki naji yace “Kai haba? Dan Allah da gaske kikeyi koda wasa?”
“Wallahi da gaske nakeyi,  yanzu hakama ina k’ofar gidanmu kai kawai nake sauraro kayi mani kwatance nanda ‘yan mintina kadan ka ganni a gabanka”
“To tsaya daidai nan inda kike, yanzun nan zan aiko a d’auko mani ke saboda banason kisha wahala.”
D’an k’aramin gida ne matsakaici mai d’auke da d’aki 1 sai Matbak da kuma hammam, an gyara ko ina yayi tsab tamkar da mata a ciki,  domin harda gado da dolaf da kujeru a d’akin,  matbak d’in kuwa babu abinda babu na kayan girki,  dan har wani d’an k’ullin attarugu nagani a saman tallaja
“To Malama kin tsaya sai faman kalle-kalle kikeyi mana a gidan namu, shigo daga ciki mana,  kinga gidan gwarayen duk a yamutse shiyasa kika tsaya kallo ko”
“A’a wallahi ni had’uwar gidan cema ta burgeni domin nagansa a tsare tamkar bana maxa ba,  shiyasa kaga natsaya kallo” na fad’a tare da zama akan kujera mai cin mutum 2 lokaci guda
Tasowa yayi daga inda yake zaune akan gado ya dawo dab dani ya zauna akan kujerarda nake zaune harma ina jiyo numfashinsa

Hannuwana ya kamo ya rik’e kana yace mani “Yau itace rana mafi soyuwa a cikin raina, domin itace ranarda na zauna gani ga masoyiyata muna fuskantar juna ba tare da wani shamaki a tsakaninmu ba” yana magana ne a hankali  yana wani lumshe idanuwa kamar wani mai jin bacci 
Nidai kam ta 6angarena abubuwa 2 ne suka taru suka yi mani tsaye, 1 tunda nake a duniya banta ke6ewa da wani d’a namiji ba bare kuma har ta kaisa ga rik’e mani hannu, shiyasa nakejina duk wani iri,  dan a takure kawai nake

2 Ina tare da farin ciki mai tsanani na ganin masoyina wanda na dad’e ban ganiba sai yau,  amma dukda haka farin cikin nawa  ya kasa bayyanuwa kasancewar wasu canje canje danakeji ajikina….
*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*
Ina mika gaisuwata ta musamman ga masu bin littafin Kalubale

 Musamman 

Wamsy (Maman Aneesa)

Asiya (Maman Ihsan)

Khadija Katuru

Ummi Adamu

Badiya Darma (My Aunty)

Suhairat Bawadi (Mai kunya)

Umma Salma

Ummin Usman 

Maman Momy

Maman Ma’aruf
Da dai sauransu…
Jinjinarku ta daban ce Malamaina👍

 Sadiya Jegal

Aunty Mai jidda

Maman Aneesa

Maman Haneep

Allah ya k’ara daukaka

Kyakkyawar gaisuwata ta musamman bazata taba karewa ba ga yan group dinmu wato *Musha karatu*

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             35

Jiki a sanyaye na dawo gida,  domin tsoro ne fal acikin zuciyata na rashin sanin takamaimen abinda kaje ya dawo idan mutanen gidanmu suka fahimci halinda nake ciki.
“Sai yanzu kikaga damar dawowa?” Cewar Khala Uwai kenan yayinda take wurgo mani wata uwar harara
Inda inda nakamayi kana dai nayi k’arfin halin cewa “wallahi Maman Walid d’ince ta aikeni Dukkanin gado shiyasa kikaga na na dad’e ban dawo da wuri ba”
“Wace Maman Walid d’in ta aikeki? indai wadda nasani ce yanzun nan ta aiko akira mata ke, ko watace ta daban?”
Na firgita k’warai da jin kalamanta domin banda wata amsa da zan bata kuma,  saidai tsuru-tsuru da nayi ina wurgama kowa ido
Aisha ce naga taja hannun Khalar sun shiga d’aki,  bansan me ta fad’a mata ba naga Aishar ta sake dawowa ta kirani dama ina nana inda nake tsaye ban matsa ko ina ba sai kace wata soja,  sudai ‘yan gidan namu ido ne kawai nasu
“Wasila bata Mala’idin d’in naki ta gani mana kin tsaya sai faman muzurai kikeyi sai kace wadda tayiwa sarki k’arya”  cewar Aisha kenan yayinda take bud’e jakata
Sai a sannan ma na tuna da wayar da ya saka mani a cikin jakata,  k’irar I phone 7  kuma sabuwa dal acikin kwalinta,  sai kud’i sababbin ‘yan fan goma goma har na jaka d’aya (120k kenan) da kuma wani turare mai dad’in k’amshi shima mai tsada ne dukda ban duba kud’insa ba
Ga mamakina washe baki naga Uwani tanayi “Yo inbaya ga abinki Wasila ai sai ki fad’a mani kar6ar mala’idin kikaje ba wani guri ba,  da nasan haka nema ai da bazan tsaya inayi maki wani fad’a ba, ni wallahi nazacima gidan Maryam kikaje kinsan ba shiri mukeyi da ita ba sosai ba”
 Nidai baki nasaki ina kallon ikon Allah, a zuciyata nace na tabbatar inda d’iyarta ce wadda ta haifa babu yanda za’ayi takai kusan k’arfe 2 na dare batare da tayi mata k’wakk’warar tuhuma akan inda taje ba, amma dayake babu wata dangantaka a tsakaninmu ko canjin yanayin nawama bata lura dashi ba,  gaba d’aya hankalinta yana kan kud’in da nakawo da kuma wayar.
“Yanzu kinga wannan wayar kamata yayi nasaka maki ita acikin d’aurin da zanyi maki,  kinga idan kikaje gida zakifi jin dad’inta tunda mai tsada ce, su kuma kud’in kinga sai na turawa su Affanki saboda kwana biyuma ban samu na aika masu komai ba” hankalinta kwance take fad’ar wannan maganar yayinda take k’ok’arin tura kud’in a cikin ‘yar jakarta ta d’aurawa a k’ugu
Kud’i kenan masu rud’a mutum lokaci d’aya,  domin tsawon zamana a k’asar nan ban ta6a jin ance mani idan naje gida ba

Karab Aisha tayi tace “aiko Khala da kinyi hak’uri ko wayar kin bar mata koba komai shida ya batan zaiji dad’i idan ya ganta a hannunta”
“To ‘yar Iya” tsara mani yanda yadace nayi uwata”
“Ai ba maganar wata uwa bace maganar kayan yarinya akeyi ba wani abu ba” ta fad’a yayinda take zun6ura baki ta fice daga d’akin
“To ai sai kizo ki zageni,  rasa kunya 6eran masallaci” 
juyowa tayi 6angarena tad’ora da cewa
“ammafa Wasila wannan saurayin naki d’an albarka ne, yaushe rabon da naga wani saurayi yayiwa budurwarsa irin wannan kyautar? Allah dai ya saka masa da alkhairi, dan Allah idan kunyi waya kice masa muna godiyafa”
Hawaye ne naji yana k’ok’arin zubowa daga idanuwana,  amma ban bari sun zubo ba dan banaso ta fahimci komai a tattare dani, saima k’arfin halin cewa danayi
“Dan Allah Khala ki taimaka ki bani lambar su Hajar mana saboda idan ina gidan aiki kewarsu tana damuna, ranbon da muyi waya dasufa za’ayi wata kusan 5 tun wannan had’a mun da kikayi har yanzu fa….
“Inkinaso ku gaisa ne yanzu hakama da akwai kud’i acikin wayata nakira makisu ku gaisa amma maganar baki lamba ma ki barta domin ba baki zanyi ba,  salon ki k’ulla mani sharri a gunsu ki fad’a masu k’arya da gaskiya su kuma su zugaki ki gudu daga gurina ko? To kima canza shawara,  ni dan Allah fita ki bani guri insamu ko nad’an kishingid’a” ta fad’a yayinda take gyara kwanciya cikin nishad’i abinta
 Bansan lokacinda kuka mai k’arfi yazo mani ba,  da wanne akeso naji ne? Da bak’in cikinda Adams ya saka mani koda nisantani da akeyi da iyayena? Amma babu komai akwai Allah,  nasan dai Allah ba azzalumin kowa bane

D’akinmu na shiga na hau kan katifata na kwanta amma badon nayi bacci ba….
*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

+966592551785
Ina mik’a gaisuwata ta musamman ga dukkan masu bin littafin nan, Allah ya bar k’auna😘

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: [07/01/2017]

💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             34

Shisshige manin da yakeyi ne yake k’ara tsoratani,  banyi nauyin baki wajen dakatar dashi ba “haba Adams miye haka sai wani matse mani kakeyi sai kace wata matarka”
“Me kike ci na baka na zuba malama? Indai aure ne ai kin kusan zama matar tawa,  dama tun farko abinda yasa bakiji nayi maki maganar auren ba so nakeyi mugama fahimtar juna tukun, kumama in baya ga abinki miye acikin auren inba yadda da aminci ba? Kuma ni a zatona ai kin dad’e da gama yadda dani da kuma amincewa dani koba haka ba?” Ya k’arashe maganar tasa cikin langa6ar da kai sai kace wani d’an k’aramin yaro a gurin mamansa
“Amma dai ai sai kayi hak’uri a shafa fatiha tukun ko?” Na fad’a cikin shagwa6a
“Indai fatiha ce toko yanzu ashafa domin a shirye nake” ya fad’a yana murmushi tare da d’aga hannuwana ya shafa a fuskarsa
“Aini ba kalar wannan fatihar nake nufi ba,  ina nufin ta malamai”
“Yanzu dai ba wannan ba,  bara nakawo maki d’an abin ta6awa kana muci gaba daga inda muka tsaya,  inma baniba waye zaiyi muhimmiyar bak’uwa kamarki ya tsareta da surutu batare da ya bata ko ruwa ba? Ko dayake nima d’oki da zumud’i ne duk suka kawo hakan” ya mik’e ya nufi kicin
“Kai dai ke kid’anka kuma kai ke rawarka” na fad’a ina murmushi
Danbun nama ne ya kawo mani cike da tire,  sai ruwa da asir ya d’oro a k’aton tire ya ajiye a teburinda ke gabana

“To malama bisimilla ga abincin gwauraye nan”
“Nidai kam alhamdulillahi domin saida naci abinci nak’oshi kana nataho nan”
Tashi yayi daga inda yake zaune a kan gado ya dawo inda ya zauna d’azu a kusa dani ya zauna “yarinya wasa kikeyi domin wallahi baki isa ba,  dan wallahi tsab zanyi maki d’ura irin na yara idan bakici ba”
K’ara matsawa nayi kad’an domin yanzu jikinmu kusan a had’e yake,  ni kuma hakan wani iri yake saka mani acikin jikina “Allah da gaske nake na k’oshi”
Ga mamaki na danbun ya d’ebo ya rik’e mani hannaye wai shi d’urar zaiyi mani da gaske 
Nanfa kokawa ta 6arke a tsakaninmu, bansan ya akayi ba kawai na ganni akan gado, cikin hikima Adams ya cire mani abayata yazama riga da wando ne kawai a jikina

Da hannuna naci gaba da rurrufe jikina,  shiko bai daina k’ok’arin yi mani d’urar ba
Can dabara ta fad’o mani nace “to tsaya yi hak’uri bani zanci da kaina” 
Ci kawai nakeyi amma badan inaso ba sai dan kawai ya daina ta6a mani jiki

Bayan nagama na d’auki sauran nakai kicin nadawo ina neman abayata nasaka  domin tafiya gida dannaga dare yafarayi sosai
“Idan kin gama neme-nemen naki gata nan a hannuna sai kizo ki kar6a” 
“Dan Allah Adams ka bani darefa yayi” ina fad’a ina dire dire cikin shagwa6a
Bansan lokacinda naji ya rungumeni ba yana bubbuga bayana, waishi a zuwan rarrashina yakeyi

Luf nayi ajikinsa domin yanzu dad’in hakan nakeji, shi kuma yaci gaba da shasshafani,  bamu ankara ba sai gamu akan gado
Nanfa mai afkuwa ta afku,  domin dama Annabi (S.A.W) yace indai mace da namiji suka ke6e to kuwa babu wani na uku a tsakaninsu face Shaid’an.
Kuka nakeyi wi wi tamkar raina zai fita,  domin ko ba komai nasan nayi rashinda har abada bazan ta6a mayarwa ba,  barema kuma da komai d’in,  domin nasan Adams ko giyar wake yasha bazai ta6a aurena ba,  to shi kuma wanda ya aurenin wace amsa zan bashi a lokacin da ya tambayeni game da hakan?

Nan take tunanin iyayena ya fad’o mani,  a kullum Hajar bata da abin fad’a a gareni face na kare mutuncina,  indai wannan ne mutuncin to yau kuwa ya zube
Danasani kawai ke kai komo acikin zuciyata, domin da ace ba’a kawoni nan k’asar  ba nasan dukda hakan bata faru ba,  domin inda agaban iyayena nake da zuwa yanzu na dad’e da yin aure harma inada yaro 1 ko 2, yanzu gashinan bani ga tsuntsu kuma bani ga tarko, domin neman kudin da aka kawoni nan domin nayi,  har yanzu ban amfana da komai aciki ba bare kuma su iyayen nawa su amfana
Tsanar abubuwa da damace ta bijiro mani a cikin zuciyata 1 tsanar iyayena tunda kusan sune silar shigata wannan halin 2 tsanar Khala Uwani domin itace ta bada gudunmuwa mafi girma a ciki 3 tsanar talauci domin duk wani mai wadata baya tunanin tura d’ansa neman kud’i 4 tsanar ni kaina da kaina, domin ni nafi bada gudunmuwa mafi girma aciki

Koma dai mine ne ta fari ta k’are wai anyiwa mai zani d’aya sata.
Jiki a sanyaye na d’auki abayata na saka ina neman takalmana, yayinda hawaye ke bin fuskata
“Wasila wai ina zaki tafi ne acikin wannan halin da kike ciki? Ko baki lura da halinda kike ciki bane? Kin kuwa lura da irin tafiyarda kikeyi?”
Lokaci d’aya duk ya jero mani wad’annan tambayoyin, sai asannan na fahimci abinda yakeso na fahimta, kallonsa nayi alamar tambaya a fuskata
“Ok oya  akwai ruwan zafi a hammam kije ki gasa jikinki sosai,  idan kin fito kuma kizo ki kar6i magani kisha, ko so kikeyi wani ya fahimci abinda ya faru?”
Batare da 6abata lokaci ba na aiwatar da duk abinda yace,  kuma naji dad’in hakan sosai domin yanzu kusan tafiyata tad’an dawo daidai……
*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

+966592551785
Ina mika gaisuwata ta musamman ga masu bin littafin Kalubale,  Allah ya kara maku hakuri dani na yawan jinkiri da nakeyi maku👏

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             38

“Hmm keko ana maganar mutanen arzik’i kina maganar wani Adams, dalla manta dashi d’auko wata firar ta daban” na fad’a tare da yin wani mugun tsaki
Zaro ido tayi gami da ta6e baki lokaci guda alamar mamaki k’arara  tattare a fuskarta kana tace “Ikon Allah, yau kuma kece mai cewa abar maganar Adams bayan ni a sanina bakida magana mafi soyuwa a cikin ranki wadda ta wuce tasa? To da walaki, wai goro a cikin miya, dan Allah fad’a mani abinda ya had’a ku dashi?” Ta k’arashe maganar tata yayinda take dafa kafad’ata
“Babu abinda ya had’amu kawai dai hakanan naji ya fita a raina, ki tayani da addu’a kawai Allah ya bani wani nagari a Nigeria domin na tsorata k’warai da damarin nan k’asar ainun” 
Murmushi naga Sakina nayi ga dukkan alamu ta fuskanci inda maganata ta dosa
“Ni ina ganin dama hak’ura kikayi kukaci gaba da soyayyarku kedashi ki manta da komai,  k’ilanma idan kika lalla6asa kiga ya daure ya aureki, domin idan bashi d’in ya aureki ba ina mai tabbatar maki duk namijin da ya aureki babu wata k’ima ko daraja da zai gani taki, domin yasan tun kafin ki auresa duk kin zubar dasu a waje”
Jinjina maganar Sakina nakeyi a cikin raina, domin tabbas maganarta akwai k’amshin gaskiya, saboda bana manta wata al’ada ta k’auyenmu,  wato idan aka kai amarya d’akin mijinta, iyayenta kan shimfid’a wani farin k’yalle akan gadon nata,  yayinda gari ya waye danginta zasuzo da sauran abokan arzik’i a duba farin k’yallen nan agani ko takai budurcinta, idan aka samu jini akai to ta tsira, iyaye da ‘yan’uwa sai farin ciki domin sun isa ta barka,  idanko aka samu akasin hakan tofa ta shiga uku, iyayentama sun shiga uku da gori da kuma habaici, watama har acikin gad’a zakiji ana sakata a wak’a ana habaici,  matan aure kuwa sun samu abinyi yayinda suke yin daka,  domin wannan wak’ar itace zata zama abin nishad’insu har su gama dakanda sukeyi koda kuwa dakan yakai na kwano goma ne
Ajiyar zuciya nayi yayinda nadawo daga dogon tunaninda na tafi “Hmm wallahi Sakina magan-ganunki har sunsa jikina yayi sanyi, to yanzu ya kike ganin zamuyi”
“Ai ba wannan tambayar yakamata ki fara yi mani ba,  kamata yayi ki fara tambayata ya akayi nagano abinda ya had’aku fad’a da wuri wuri haka?”
“Bakiji hausawa sunce mugu shi yasan makwantar mugu ba?  Kinga kenan ai ba abin mamaki bane ba dan kin sani, kumama in baya ga abinki ai abokin cin mushe ba’a 6oye masa wuk’a ko? yanzu dai bani amsata ya kike ganin zamuyi wajen basa hak’urin?”
 Shuru tayi tana kallon sama nad’an lokaci ga dukkan alamu nazari takeyi kana tace “Ni a ganin mizai hana tunda mun kusan sauka Ijaza mu bari kawai sai munje gidan mu na nan Madina inyaso sai kiyi masa waya ki lalla6asa yazo yasameki acan kwafi fahimtar juna koya kika gani?” Ta fad’a tana mai kallon fuskata
“Ai inaga saura kwana 3 ko 4 ne mu sauka ijazar,  Allah ya kaimu lokacin lafiya” Na fad’a yainda nake ci gaba da gugata.

**********
Adams ne kwance akan gadonmu yayinda yayi filo da cinyoyina yana bani labarin yanda akayi ya iso Madina batare da ko takardar tsire ba
“Wato Wasila ina baki labari, kinsan kuwa dak’yar nasamu na iso nan gareki? Domin  gate gate d’inda na samu na Tabtish (bincike) yakai kusan 10, dayake kinsan lokacin aikin hajji ne shiyasa tsananta binciken nasu ya yawaita, danma Allah ya taimakeni manyan kaya nasaka kinga da sun ganni sai su zaci wani babban bak’o ne sukayi daga Nigeria basu san zindik’in d’an Alhaji  bane (mazaunin nan) baki ganni harda hula ba?” Ya k’arashe maganar tasa cikin dariya
Nima dai abin dariya ya bani sosai, domin inaga tunda nake dashi ban ta6a ganinsa da manyan kaya ba sai yau,  saiko wani lokaci idan yayi ra’ayi yasaka jallabiya

Da k’yar na gimtse dariyar tawa nace

“Su Adams akwai tsoron zuwa Nageria, to duk guje gujenka dai wata rana sai katafi, masu takardar zaman k’asarma ana binsu ana kamawa inaga kai da k’ilan ko takardar haihuwa bakada ita” Na fad’a yayinda nake ci gaba da dariyata

D’aure fuska naga yayi alamun dariyar tawa tafara bashi haushi, shiyasama na d’aure na gintse dariyar tawa na bayyanar da alamun tausayi a fuskata kana nace ” Allah sarki, wallahi da nasan zaka wahala sosai da ban d’ora maka wahalar zuwa nan ba”
Murmushi  yayi irin wanda ke k’ara tafiyar mani da hankali d’in nan “Haba? Wace wahala kuma ko dad’in ji babu? Yoni Allah  na tuba indai kika kirani ai duk inda kike ni mai iya zuwa ne na sameki koda kuwa a Riyadh kike ko Ta’ib, kina tantama akan sonda nakeyi maki kenan?”
“To yanzu dai ya maganar da nayi maka ta aure? har yanzu banji kace komai ba, kodai baka amince da auren nawa bane” Na fad’a muryata a raunane tamkar zanyi kuka, domin gani nakeyi fad’ar hakan tamkar k’ask’amci ne agareni
Cikin dakewa da gasgata abinda zai fad’a ya kalleni da yaudararrun idanuwan nan nasa masu kama da mai jin bacci yace “Ni a tunanina ai basai natsaya ina 6ata bakina wajen ce maki na amince da maganar aurenki ba, tun ba yau ba ke kanki kinsan ni masoyinki ne na hak’ik’a, kuma tun ba yauba nake da gurin aurenki,  karkiyi tsammanin wai faruwar wani abu a tsakaninmu zaisa na canza ra’ayina a kanki a’a wallahi,  ni Adamu ba haka nake ba,  idan na juya maki baya ai hakan ya zama yaudarama kenan? Saboda haka ki kwantar da hankalinki faruwar wani abu a tsakaninmu tamkar k’ara ruruta wutar k’aunarki yayi acikin zuciyata,  domin sai a sannan nema na tabbatar da baki ta6a amincewa da wani D’a namiji ba kafin ni, ki kwantar da hankalinki kinji Wasilata?” Ya fad’a tare da k’ara rungumeni
Nima rungumesa nayi cikin farin ciki marar misaltuwa
Tuni nayi watsi da shawar-warin Suwaiba na d’auki na Sakina domin ni a ganina da Sakina da Aisha sunfi Suwaiba k’aunata nesa ba kusa ba
“Amma Wasilata anan mu zamuyi Idin namu ko? Inyaso bayan sallah da kwana 5 ko sati d’aya basai ki koma gidan aikin ba? Tunda kinga mu kad’ai ne a gidan  sauran ‘yan gidan naku kince duk gida suka tafi Ijaza ko?”
Batare da 6ata lokaci ba na amince masa  domin gani nakeyi yanzu duk fad’in duniyar nan babu wanda yake k’aunata sama da Adams……
*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

+966592551785
Ina mika godiyata ta musamman ga dukkan masu bin littafin Kalubale musamman masu bani k’warin guiwa irinsu

Asiya (Maman Ihsan Kt)

Ummi Adamu

Khadija Katuru Kt

Badiyyah Darma Kt

Suhairat Bawadi

Ummu Sadiq

Zainab Ibrahim

Salamatu Ali

Huwa’u Abdullahi

Maman Ma’aruf

Ubaida Ellela

Khadija Dahiru
Allah ya bar kauna:)😘😘

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             36

Dafa kafad’ata naji anyi, cikin razani na juyo domin na dad’e da yin nisa a cikin tunanina
“Wasila miyake damunki ne naga yanayinki na d’azu dana yanzu ya banbanta kodai jikin Faridar ne yayi tsanani?” Suwaiba ce mai fad’ar hakan yayinda takeyi mani wani kallo irin na tuhuma d’in nan
Rasa me zance mata nayi domin ina k’ok’onton kodai taji maganata a waya d’azu, saima had’a kaina da guiwa da nayi yayinda zuciyata take ci gaba da yi mani k’una
“Wasila inma ki fad’a mani,  inma karki fad’a mani nidai nasan kina cikin damuwa, dukda wasu lokuttan ina ganinki cikin damuwa amma ta yau kam gani nakeyi tamkar tafi ta kullum,  Wasila nifa tamkar k’anwata wadda muka fito ciki d’aya na d’aukeki danmi zaki tsaya 6oye mani damuwarki?” Cikin sigar lallashi takeyin maganar tata
“Babu abinda yake damuna Suwaiba, kawai dai yanayin rayuwa ne,  kinsan bakoda yaushe mutum yake samun kansa cikin farin ciki ba”
Jijjiga kai tayi alamar gamsuwa, amma a fuskar tata naga kamar bata gamsun ba
“Dukda kink’i fad’a mani damuwarki,  hakan bazai hanani yi maki nasiha ba, da farko dai kiji tsoron Allah, kuma ki k’addara a ranki duk inda kike kuma duk abinda kikeyi Allah yana kallonki yayinda kuma mala’iku 2 suke  rubuta ayyukan ki na lada da kuma na  zunubi, idan har kika sa hakan acikin zuciyarki to kuwa ina mai tabbatar maki wasu ayyukanda kikeyi na zunubi ko kuma kike tunanin zakiyi zasu ragu”
D’ago fuskata nayi na kalleta alamar tuhuma,  domin a tunanina kamar ta gama harbo jirgina
“Niba zarginki nakeyi da komai ba,  saboda haka kada kiyi tunanin komai,  nidai shawara kawai nake baki”
Hmm a zuciyata nace ta faru ta k’are
“Abu na gaba da nakeso nasanar dake tunda dad’ewa shine ki kiyayi Sakina da kuma Aisha, domin sun fiki wayo fiye da yanda kike tunani,  saboda koba komai sun rigaki zuwa duniya, domin da kike ganinsu nan shed’anu ne na bugawa a jarida, saboda farkon zuwana nan babu yanda basuyi dani ba akan mu jone na nuna masu  halina da nasu ya banbanta,  wallahi Wasila ina mai tabbatar maki indai kika biye ta tasu sai sun kai ki sun baro

Annabi (S.A.W) ce mana yayi dukkan d’ayanku ana tadasa ne akan addinin abokinsa, Annabi yaci gaba da cewa,  saboda haka d’ayanku ya duba yagani waye abokinsa?

Acikin wani hadisin kuma Annabi (S.A.W) cewa yayi misalin aboki na gari da kuma misalin aboki na banza, tamkar mak’eri ne da kuma mai sayar da turare, shi dai mai sayar da turare ko baka siya ba indai ka zauna dashi sai ka shafi k’amshinda ke tattare dashi, shima haka mak’eri, indai ka zauna dashi sai ka d’auki k’aurinda yake tattare dashi,  inma bakayi sa’a ba ya k’ona maka kayanka

Kinga kenan duk yanda ka kai ga kama kanka indai zakaci gaba da zama da marar kamun kan akwana a tashi wata rana saika d’auki wani abu daga halayyarsa.”
Yau kam banji haushin nasiharta agareni ba,  hasalima jin dad’inta nayi, domin gaskiya ta fad’a saboda Sakina ma da Aisha sun taka muhimmiyar rawa wajen wannan abin da ya faru agareni yanzu
 Ban gama tunanina ba ta katseni “Idan kika lura dani sosai duk cikin mutanen gidan nan banida wani amini wanda zan zaua nafad’awa matsalata, hasalima kowa haushina yakeji saboda bana gani nayi shuru,  nifa farkon zuwanki nan gidan yanda nafara jawoki a jiki nazaci nasamu ‘yar’uwa,  amma ga  mamakina sai kika fifita mu’amala dasu Sakina a kaina,  yin hakan ba damuwa ta bane amma dai ina jiye maki tsoron kema ki fara kwaikwayon halayensu”
“Naji nasiharki kuma insha Allahu zanyi amfani da duk abinda kika fad’a mani” amma dan Allah idan bazaki damu ba,  zanso nasan ainahin dalilinda yasa kikazo nan k’asar domin yanayinki yana nuni ne da irin kamar an tilasta maki d’in nan ne kikazo”
“Eh to” zan iya cewa kusan hakan ne maganarki, domin banbancin da tilasti d’an kad’an ne

Dayake tun ina k’arama mahaifiyata ta rasu shiyasa na taso hannun matar babana, dayake Allah yayoni da bala’in son ilimin addini shiyasa matar baban nawa tayi amfani da wannan damar suka had’a baki da wannan Khalar tawa azuwan za’a kawoni nan k’asar ne badan nayi neman kud’i ba sai domin naci gaba da karatuna a Jami’atul madina, tofa shine suka kawoni suka danna ni gidan aiki,  dayake bason zama k’asar nakeyi ba shiyasa kikaga babu wanda nake shakka acikinsu, kuma babu wanda ya isa ya sakani abinda banyi niya ba

Yanzuma abu d’aya ne kawai ya tsayar dani nan k’asar,  so nake naje gidan aiki nasamu kamar wata 6 acan kinga kenan a lokacin inada kusan miliyan d’aya na Najeria kuma na tabbata miliyan d’aya zata isheni komai na kayan d’akina idan natashi yin aure harma da d’an jari, to asannan daga can gid’an aikin  kawai sai na tunkari ‘yan kame sukamani su kaini k’asarmu”
“Kenan ke ba a bashi aka kawoki ba” na fad’a tare da yin tagumi
“Wasila bashi kona jini ne ba na ruwa ba ai ya isa ace na biyasa cikin shekaru 4”
Bamu ankara ba saidai tsinkayar maganar Khala Amina mukayi a k’ofar d’aki, domin dama babu kowa a d’akin dagani sai Suwaibar
“Uwani taso kiji hud’ubar da Suwaiba takeyiwa Wasilarki, dayake ita ta fitsare k’afafuwanta bata jin tsoron ko shakkar uban kowa shine kuma yanzu takeso ta dinga bin ‘ya’yan mutane tana kangarar masu dasu”…..
*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

+966592551785
Kyakkyawar gaisuwa ta musamman ga dukkan masu bin littafin Kalubale, Allah ya bar kauna😘

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             37

“Nidama tunda naga yarinyar nan Suwaiba tana shisshigewa Wasila nasan za’a rina wai ansaci zanen mahaukaciya” Khalata ce take fad’ar wannan maganar yayinda take k’ok’arin gyara zaninta da yake shirin fad’uwa k’asa, ta k’ara da cewa ” To duk bak’in cikinki baki isa ki rabani da Wasila ba bare ta zame mani k’adangaren bakin  tulu kamar yanda kika zamewa wadda ta kawoki, saboda hakama gobe goben nan zata koma gidan aiki,  hutun sallar ya isa haka nan kuma muga ta k’aryar zuga”
“Oho dai koma me zakuce saidai kuce, amma gaskiya kam saina fad’a indai naga gurin fad’in nata” Suwaiba ce mai fad’ar haka cikin k’unk’uni
“Nidai Khala dan Allah kiyi hak’uri sai zuwa jibi mu koma tare da Sakina gaba d’aya saboda gobe Bahar da Malahi mukeso muje yawon sallah…
“Kiyi hak’uri idan Allah ya kaimu babbar sai kije, amma madamar kina gidan nan kuma Suwaiba na gidan nan hankalina bazai taba kwanciya ba”
“Aiko fafur k’in amincewa tayi da zaman nawa har zuwa jibi duk magiyar da nayi mata, ina ji ina gani ta had’a mani ‘yan kayana na tafiya gidan aiki , irinsu maggi, yaji, kuka, indomi, garin tuwo, yau har da su kati da ifada aka had’a mani koda zan buk’ata agaba
Inaji ina gani ta ingiza k’eyata gidan aiki, dukda munyi alk’awari da Yusuf yace mani zai biyata gidan su Farida ya d’aukota suzo mani tare yawon sallah, saida hak’ura nayi na buga masu waya nace masu suyi hak’uri domin ni har na koma gidan aiki.

 ***********
A kwana a tashi babu wuya, domin yau gashi kusan watana 3 kenan a gidan aiki batare da naje ijaza ba, saboda gidanda Sakina ke zuwa ijaza nima yanzu can nake zuwa, domin matsi da takurar gidan namu yanzu ya fara isata,  tsakanina da Khala kuwa saidai duk wata ta aiko a k’ar6a mata kud’in hannuna.
Yauma kamar kullum bayan mun gama ayyukanmu nida Sakina muna zaune muna fira take cemani “Kiga Wasila a kwana atashi babu wuya asarar mai rai,  wai har mun kusan wata 3 rabonmu da jidda”
“Wata rana kuma mu ganmu a kabari ba” na fad’a ina murmushi yayinda nake tayata gugar kayanda aka bata
“Bana zaki aikin hajji kuwa naga na bara kamar ya baki wahala sosai?” Ta fad’a da alamun zaulaya a tattare da ita
“Wa? Ni? Rufa mani asiri, ai aikin hajji ina ganin kamar nayi na k’arshe saboda wallahi baara nasha wahala ba ‘yar kad’an ba, gashi na d’au harami amma wallahi Khala bata barni ba saida ta sakani yin barar wajen jifa, ga alhazanmu na hausawa sai faman tofin ala tsine sukeyi mana, kunyarsu duk tabi ta isheni, ga yunwa ga k’ishirwa, ga kuma uwar rana a wajen,  shiyasama ko ijaza bazani ba ga Idin barema har ta ganni tace mani mu tafi aikin hajjin”
Dariya Sakina takeyi sosai kana dai ta daure tace “Yo angaya maki zama Hajiyar abu ne mai sauk’i? Ai sai ansha wuya ake samun sunan Hajiya, bakiji akace rago baya suna ba?”
“Hakane kam, ammafa karki manta babu wanda yasakamu muyi zaman Kuburi mu mukasaka kanmu,  haka babu wanda ya aikemu yin bara a gurin jifa shima mu mukasa kanmu,  kinga ko zama Hajiya nada sauk’i mune dai kawai muke maidasa mai wahala kuma sai yazo mana da wahala d’in”
“Yanzu dai  ba wannan ba,  waini ya labarin Adams ne naji shuru kwana 2 kin daina bani labarinsa?”…..
*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

+966592551785
Ina mik’a gaisuwata ta musamman ga dukkan masu bin littafin K’alubale musamman

Asiya (Maman Ihsan Kt)

Ummi Adamu

Badiyyah Darma Kt

Zainab Ibrahim

Farida Umar 

Salamatu Ali

Ummu Sadiq

Suhairat Bawadi
Da dai sauransu

Allah ya bar k’auna👍😘😘

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             39

Yau dai mun wayi gari ne cikin wani yanayi na matsanancin tashin hankali, domin labarin da naketa ji ban gasgata ba tun tuni shine abinda yake faruwa a yanzu, wato Kamen gida-gida wanda Askarawa keyi yayinda mu bak’i marasa takardar izinin zaman k’asa muka kwakkwanta da niyar yin bacci

Tun Askarawan suna nesa da gidanmu muke jiyo labarin suna tahowa,  har zuwa lokacinda suka iso dab damu suka fara farfasa gidajen mak’wabtanmu, Kuma a yanda muka samu labarin motocin da sukazo dasu ba ‘yan kad’an bane, domin acewar masu bugo mana waya wai hadda irin manyan motocin nan masu d’aukar kusan mutum 50 ko kuma sama da haka, bayan Kuma ‘yan k’anana motocin irin masu d’aukar mutum 5 zuwa 10 d’in nan, abin ba anan ya tsaya ba domin harda motocin assibitinsu sukazo suma manya-manya tare da likitocinsu saboda koda wani zai samu matsala a lokcinda suke kamasa.
Unguwar tamu ko ina ka duba Askarawa ne yanda kasan wani d’an k’ramin yak’i akeyi.
Cikinmu duk ya d’uri ruwa domin gaba d’ayanmu yau munsan badai mu kwana a gidajenmu ba sai dai mu kwana a Tarhin (Inda ake ajiye mutane idan an kamasu kafin a turasu k’asarsu) saboda yanda Askarawan nan suka fito k’wansu da kwarkwatarsu kuma babu alamun tausayi ko rangwame a tattare dasu ni nasan mutum yau ko cikin cikin uwarsa ya shiga sai sun fiddo shi.
Gidan namu gaba d’aya ya birkice domin babu mai rarrashin wani kowa ta kansa yakeyi

Khala Amina ce na hango daga nan inda nake b’oye cikin tummokara tana k’okarin 6uya acikin Tallaja (Firiza) bayan ta zare soket d’in da yake jikinta

a zuciyata nace hmm naga yanda za ayi ki shiga cikin wannan tallajar  da wannan uwar k’ibar taki, dariya ce taso su6uce mani Amma nayi k’rfin hali na mayar da ita kasancewar yau ba ranar dariya bace

Ita ko Khala Uwani Fitsari nagani yana bin zaninta saboda tsananin firgita da tayi

Khala Tabawa Kuwa addu’oi kawai naji tana zubowa  tare da wasu sabbatunta na shirme wanda a zatona su d’in dai ba addu’a bace kawai dai tsabar firgici ne
Suko ‘yan matan gidan sun rasa inda zasu 6uya sun had’a kai su duka sai faman koke-koke sukeyi
A zuciyata nace da ace yanda ‘yan hajjoji ke tsoron yan kame haka suke tsoron Allah, toda babu mamaki idan sun mutu aljanna tazama makomarsu
Suwaiba ce dai nagani cikin farin ciki domin nagama har wata ‘yar k’aramar jakar hannu ta d’auka bayan tasaka wayoyinta da sark’arta ta zinari a ciki ta rataya yayinda naji tana cewa Allah ya za6a mana mafi alkhairi.

Ban kai ga gama gulmace gulmace na ba naji baburetin d’in wayata, dayake dama a baburetin nasakata saboda koda ‘yan kamen sunzo karsuji k’arar wayar

Muryar Adams naji cikin tashin hankali yayinda yake shaida mani cewa wai gashi nan yanzu haka a motor ‘yan sanda shima kamen ya had’a dashi, kafin na dawo cikin d’imuwarda na shiga naji anayiwa gidanmu wani wawan duka na fitar hankali a zatonama k’ofar ta kusan 6allewa..
Kukanmu ne ya k’ara tsananta domin nima yanzu kukan nakeyi daga can lokonda nake 6oye, baram mukaji an 6alla k’ofar gidan ‘yan sandan suka farfad’o suka fara bincike-bincike.
 Suwaiba suka fara kamawa domin dama ba wani 6oyon Kirki tayi ba saboda tanason tafiya gida dama, kana daga bisani suka k’wamuso Khala Amina saboda k’afafun nata basu ida shiga cikin tallajar ba, kukanda Sakina keyi ne  ya tona mata asiri har suka kamata, kana kuma suka shiga dube-dube babu ji babu gani….
*DAGA TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

00966592551785
Kyakkyawar gaisuwata ta musamman bazata ta6a gushewa ba ga dukkan masu bin littafin Kalubale musamman

_Asiya Maman Ihsan kt_

_Ummi Adamu_

_Khadija Katuru_

_Ummu Sadiq_

_Maman Ma’aruf_

_Badiyyah Darma kt_

_Suhairat Bawadi_

_Zainab Ibrahim_

_Maryam Lawal_

_Maman Waleeda_

Da sauran wad’anda ban ambata ba👏

Allah yabar k’auna😘👏

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             41 
Da jin wannan maganar dukkanmu muka fara koke-koke, domin sanin kanmu ne Iyayen Waleed basu cika wad’annan sharudd’an da ake buk’akata ba, hannun Aisha naja muka ke6e gefe guda 

“Niko Aisha mizai hana ki kira mana baban Waleed d’in muji koda inda zai aro Igamar asamu a duba yaron nan?” 
Jin jin a kai tayi alamar gamsuwa “Aiko kin kawo shawara, bara na kirasan na fad’a masa halinda ake ciki muji ta bakisa, yanzu hakama Matar tasa bata sanar masa abinda ya faru ba saboda baiwar Allah gaba d’aya a rud’e take domin duk ta fita hayyacinta abin tausayi”
Waya ta zaro acikin zaninta tana lalumo lambar baban Waleed d’in,  domin bamu tsaya d’aukar ko ‘yar jakar hannun ba mukayo nan
Yayinda ni kuma na koma wajensu Maman Waleed d’in muka zauna muna jiran gawon shanu. 
Bayan Aisha ta gama wayar ne ta samemu a inda muke zaune, munyi jigum-jigum sai kace wasu masu zaman makoki 
“Yanzu nakira Baban Waleed nasanar masa abinda ke faruwa harma yace na sanar maku yanzun nan zai turo wani abokinsa mai igama yazo ya samemu, kuma shima yanzu haka yana Mogab (Tasha) zai hawo mota yazo, sai daifa ina ganin zai d’au lokaci kafin ya iso saboda kunsan nisanda dai ke tsananin Makka da Kuma Riyadh, dan ba mamaki ma sai safe zai iso”
“Allah ya kawo abokin nasa lafiya” abinda kawai Khala ta fad’a kenan, yayinda ita kuma Maman Waleed ko magana ta kasayi, bare kumani da hawaye yakasa barin fuskata na tausayin yaron.
Ba’a wani dad’e sosai ba abokin nasa ya k’araso, sai dai fafur k’in amincewa likitocin sukayi wai ala dole sai sunga igamar Maman Waleed d’in koda takardar auren nasu bata samu ba.
Nidai kam na jinjina wannan rashin imani nasu a cikin raina, domin ni aganina kamata yayi su fara duba lafiyar yaron kana inyaso duk wani abu da zai biyo baya sai ya biyo, wallahi da kafin nazo nan k’asar ne na samu labarin wai larabawa zasu iya yiwa dabba haka bama mutum ba, wallahi dana k’aryata duk wanda ya kawo mani labarin, saboda  ni a zatona ko ince a zatonmu mu ‘yan Nigeria da Kuma Niger da sauranma wasu k’asashen na daban, larabawa sunfi kowa jin k’ai da Kuma tausayi, saidai ashe gaskiyar hausawa da suke cewa wai D’an Adam 9 yake bai cika 10 ba.
Haka muka rankaya muka nufi wata assibin kuma,

Su assibitin ma da mukaje d’in cemana sukayi da gangan ne aka d’ikoshi da k’asa har yaji wannan mummunan ciwon, saboda hakama bara su kira ‘yan sanda su fara bincike a kansa
Nanma muna ji muna gani muka bar assibitin muka nufi wata 
Acan nema muka samu wani balarabe mai tausayi dayake dama ance na Allah basa k’arewa, ya taimaka mana da duk abinda zai iya har suka karb’emu.
Sai dai kash! ashe bamu sani ba duk yawonda mukeyi Waleed ya rigamu gidan gaskiya, domin likitocin cemana sukayi gurin awarsa 3 da mutuwa, kenan idan zan iya tunawa tun a assibitin farko da mukaje ya rigamu gidan gaskiya.
Allah sarki! Allah baya barin wani domin wani yaji dad’i, ko kad’an bazan iya kwatanta tashin hankalin da Iyayen Waleed suka shiga ciki ba.
Sai dai kuma ba’a nan gizo yake sak’arsa ba, domin fafur assibitin nan hanamu gawar Waleed sukayi wai sai sun gama binciken dalilin mutuwar tasa tukun.
Khala Uwani ce tazo daidai kunnaina ta rad’a mani ” Kinsan me za’ayi Wasila? Wallahi gara mu samu musan duk irin dabarar da zamuyi mubar wajen nan, domin wallahi idan har muka tsaya har ‘yan sandan nan sukazo kashinmu ya bushe, saboda abinda dai muka guda a gidan har nan zaizo ya samemu a zaune” (Kame)
Zaro ido nayi cikin mamaki, domin a tunanina kamar itama Khala imanin nata ragagge ne, koda yake ai dama bawani imanin ta cika ba “Khala ana maganar mutuwa wa kuma yake maganar kame? aini wallahi yanda nakeji d’in nan bank’i su kamani d’in ba, kifa duba kiga halinda baiwar Allan nan take ciki, batada uwa batada uba, batada kowa anan, mu kad’ai ta d’auka gatanta, shiyasama da abin ya faru mu ta fara fad’awa, idan mukayi mata haka kina ganin munyi mata adalci Kuwa?” 
Murmushi tayi wanda baikai ciki ba kana tace “wanda dai ya mutu ya riga ya mutu ba dawowa zaiyi ba, saboda haka babu yanda za’ayi nashiga matsala inaji ina gani, bara na fad’awa Aisha domin na fita hakk’inta, idan zata zauna nan d’in ne to, idan kuma zata tafin ne to yanda dai taga dama” a k’asa-k’asa takeyin maganar tata dan kada wani ya jiyota, ta mik’e ta nufi gun Aisha 
Bansan ya sukayi ba amma naga Aishan ta mik’e ta  biyota sun dawo inda nake sun zauna, ga dukkan alamu dai ta aminta da maganar Khala
K’us-k’us d’inda baban Waleed yaga munayi ne yasa yazo inda muke ya zauna, shima k’asa-k’asan yake cemana “Khala ina ganin da kun tashi kun tafi hakanan mun gode sosai Allah ya bar zumunci, saboda kunga ‘yan sanda suna hanyar zuwa, Case d’in nan  zasu iya maidasa babba tunda kunsan halinsu ‘yan jan sharri ne na bugawa a jarida, ba mamaki ma dalilin hakan su kaimu k’asarmu inma munyi sa’a kenan bamuyi Sijin ba (gidan yari) to kunga gara ku tafi kada abin ya had’a daku, mun gode sosai” Yana maganar amma ina lura hawaye bai daina bin fuskarsa ba dukda yana namiji
“To kai D’an nan mizai hana ku bar masu gawar anan ku samu ku sulale kamar yanda mukayi masu lokacin da K’anwar Tabawa ta rasu, tunda ba igama ne daku ba kaga babu wata sheda daza aganeku da ita ko ya kagani?” 
Cikin matsanancin 6acin rai ya kallemu kana yace ” Haba Uwani!  nabar gawar d’an nawa  na cikina natafi ina? gawar mutum sai kace gawar wani d’an tsako ?  ku dai kwa iya tafiya, amma mukam muna nan insha Allahu sai naga kabarin Waleed inyaso daga nan su ratayeni idan sunga dama ” a fusace yabar gun namu ya koma gun matarsa da Kuma Amininsa.
Sumui-sumui muka bar assibitin sai kace wasu munafukai
A zuciyata nace gaskiya garin nan ba garin zama bane, domin sadda bakada matsala kowa sonka yakeyi, Amma da zarar matsala ta sameka sai kaga makusantanka wad’anda kake ganin su zasu fara jibintar lamurran ka sai kaga sune wad’anda zasu fara gudunka.
Muna mota kan hanyar mu ta dawowa gida ne Khala ke shaida mani wai gobe ne ko jibi Salamatu ta Jiddah zatazo nan Makka idan tazo zata had’ani da ita mu koma jiddan tare nafara d’an ta6a Dawwari, acewarta wai tunda mun tabka asara a gidanmu asamu a mayar da wuri tunda a dawwarin anfi gidan aiki samun kud’i nesa ba kusa ba……
_Ina godiya ga dukkan masu bin littafin Kalubale, masu bugo mani waya da masu turo mani sako ta private, dama wad’anda suka karanta sukayi shuru. idan danbu yayi yawa baya jin mai. Sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa ba, sai dai kawai ince ina godiya Allah ya bar kauna_😘👏
*MAMAN JA’AFAR*

00966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: [24/01, 7:15 a.m

💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             44
Tun azahar muketa faman yin abu d’aya har zuwa bayan isha, saidai idan munji ankira salla mu ra6a masallaci mafi kusa muyi salla, dukda dai basamu muke muyi wata natsatstsiyar salla ba, saboda muna yin sallar amma hankalinmu ba akan sallar yake ba, Allah Allah mukeyi mu gama muzo bakin masallacin mu kasa hajarmu (Bara) yayinda masu fitowa daga masallacin zasu dinga jefa mana abinda ya sauwak’a a cikin ledejinmu, sai munga kowa yagama fitowa kana zamu tashi kuma mu nufi dawwarin ishara wato inda muka baro.
A gajiye nake saboda wata matsananciyar yunwa da take addabata, ga kuma k’afafuwana sai faman yi mani zugi sukeyi saboda  rashin sabo da banyi ba da irin wannan tsayuwar.
 Dawwarin nakeyi amma sai yamutsa fuska naketa faman yi gami da ‘yan guna-guni na
Can na hango Zulai ta tsallako inda nake (dayake yanzu ta koma can tsallake, acewarta wai nan samun kud’insa yayi sanyi) dafa kafad’ata naji tayi cikin nuna alamu na  kulawa naji tace
“Wasila lafiya naganki sukuku haka? ko wani abu ne ke damunki?  tun d’azun nake lura dake gaki nan dai duk kin wani canza lafiya?” 
Ajiyar zuciya nayi gami da murmushin k’arfin hali, akasalance nace mata
 “Wallahi lafiya lau Zulai, kawai dai yunwa ce ke damuna da Kuma gajiya, kodai zamu tafi gida ne hakanan?”
Zaro ido naga tayi gami da dafe k’irji sai kace na fad’a mata wani mugun abu 
“Mutafi gida yanzufa kikace? kice kinaso yau Antitiya tayi mani rashin mutuncinda ta saba kenan? saboda ni nasan kwata kwata kud’in da nasamu basufi fan 10 ba, itako indai kud’i basu harari fan 20 ba duk daren da kayo saita mayar da kai ishara ka ida cikosu.
Aiko abinda muka guda shi ya faru domin daga dawowarmu  ko hutawa bamuyi ba tace mu k’irga abinda muka samo
Nidai fan 18 da rabi nasamo, yayinda ita kuma Zulai ta samo 19 da riyal 7, kenan a a dadin da ake buk’ata anawa kud’in saura fan 2 ita kuma Zulai riyal 3 ne kad’ai suka rage mata bata ida cikawa ba (duk fan 1 yana d’aukar riyal 10 ne, kimanin nera dubu d’aya da wani abu kenan a yanzu)
Ko hutawa bamuyi ba matar nan ta hurgad’omu muka dawo ishara da nufin sai mun ida cikato abinda bamu ida ba d’azun ko sama da haka idan ya samu
Da k’yar muka samu muka ida ciko kud’in nan kana kuma muka dunfaro hanyar gida a lokacin inaga kusan k’arfe 12 na dare.
Bako sannu bare nagode ta k’ar6e ledejin hannun namu a wulakance ta shigewarta d’akinta ta barmu anan tsaye tamkarma batasan Allah yayi ruwanmu ba, muma Sumui-sumui muka wuce d’akin mu.
Bayan munyi wanka munci abinci mun huta ne Zulai take ce mani nazo na rakata can baya gidansu wata K’awarta Mariya, aiko banyi wani musu ba domin dama jina nakeyi duk atakure sai kace ansani acikin akurki,  kuma bayan hakama  inaso in zagaya in k’ara ganin garin jiddan yanda yake tunda a wancen lokacin da mukazo cikin sauri mukazo kuma cikin sauri muka koma.
Babu wani nisa tsakanin gidanmu da nasu, domin bamuyi ko cikakkiyar tafiyar minti 5 ba muka iso gidan.
Gidan nasu d’an matsakaici ne mai d’aki 2 kamar dai namu na Makka da Kuma na Antitiya, domin dama a yanda na fahimta mafiya yawancin gidajen Saudiya indai irin namu ne na bak’i d’akunansu baya wuce 1 ko 2, sai an tsananta ake samun mai d’aki 3 ko 4 dan tunda tunda nake ban ta6a ganin gidan bak’i mai d’aki 5 ba.
Da shigarmu gidan na fara jiyo sautin wak’ar Ado Gwanja na tashi a cikin d’ika-d’ikan sifiku
 D’akin farko muka fara shiga muka gaggaisa da manyan matan da ke cikin d’akin, wanda ga dukkan alamu harda mahaifiyar yarinyar da mukazo gunta a cikinsu wato Mariya, kana muka zarce d’akin k’arshe muka kutsa kai a ciki inda su Mariya suke
Yan mata ne nagani ak’alla zasu kai kusan su 5 kowacce tasha matsattsun kaya sunata tik’ar rawa abinsu, kai idan ka gansu ka rantse  basuda wata matsala a duniya
Wata bak’ar cikinsu kuma doguwa naga ta rugo da gudu ta rungume Zulai, ga dukkan alamu itace Mariya d’in
“Oyoyo Oyoyo! K’awata sai yau ake ganinki? aini wallahi fushi nakeyi dake, ke kullum saidai mutum yaita zuwa gidanku amma ke bakya son ziyartarmu, ai shiyasa nima na d’auke k’afata daga gidanku kwana biyu” 
“Hmm kema inbaya ga abinki harma kya tsaya kina yi mani wani k’orafi bayan kinsan sarai halin wannan Tunkiyar ta gidan namu da shegiyar takura”
Zulai ce ke fad’ar haka bayan mun zauna akan kujeru biyun dake cikin d’akin
Dariya muka tuntsire da ita gaba d’ayanmu harda k’yak’yatawa, a zuciyata nace ashe itama wannan Zulai d’in ba kanwar lasa bace nake ganinta Sumui-sumui sai kace wata ustaziya….

Shin wai Wasila tana farkawa daga dogon baccin da takeyi ta gane rayuwarta tana cikin garari ko kuwa sabon shafi take 6ud’ewa na holewa tunda ta samu sabbin K’awaye kuma ‘yan hannu?
Ku dai kuci gaba da biyoni domin jin yanda rayuwar Wasila zata  ci gaba da kasancewa a Jiddah

_Ina godiya ga dukkan masu bin littafin Kalubale, masu bugo mani waya da masu turo mani sako ta private, dama wad’anda suka karanta sukayi shuru. idan danbu yayi yawa baya jin mai. Sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa ba, sai dai kawai ince ina godiya Allah ya bar kauna_😘👏
*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             40

Sun kwashe kowa, dan gaba d’aya gidan babu wanda suka bari, dagani sai Aisha da Khala Uwani

bayan fitarsu bada dad’ewa ba muka sake jin motsin wasu mutane, a zatonmu ma sune suka dawo muka sake neman gurin 6uya, saidai ga mamakin mu wasu Shababan larabawa ne muka gani (Matasa) sunata shigowa cikn gidan namu yayinda suke d’aukar duk wani abinda yayi masu, irinsu kayan kallo,  mukayyif, kayan sawarmu da dai sauransu wasu abubuwan masu mahimmanci, atta k’ananan jakakunanmu basu bari ba domin duk kud’aden dake ciki saida sukabi suka kwashe
Munaji Muna gani sai dai babu halin muyi masu ihu ko kuma muyi wani yunk’urin hanasu, saboda da munce zamuyi wani yunk’uri ‘yan sandan basu yi nisa ba zasu iya tona mana asiri a gunsu
Saida muka tabbatar suma sun gama yin abinda zasuyi kana muka fito Muna dudduba kayan namu, saidai kash! duk wasu kayan namu masu amfani duk sun kwashe sai abinda ba’a rasa ba.
“Wai Khala dama haka zaman Saudiyar yake? atakaka, a wulak’antaka, ayi maka duk cin kashinda akaga dama kawai dan kai bad’an k’asa bane ko kuma dan bakada takardar izinin zaman k’asa? anya wannan zaman wulak’ancin munyiwa kanmu adalci kenan” ina fad’ar wa’yan nan mgan-ganun hawaye na bin  fuskata babu kakkautawa
“Wasila kiyi hak’uri ki daina kukan nan, inda sabo ai yaci ace mun saba da irin wa’yan nan abubuwan, bakiji sunan da muka sakawa kanmu anan k’asar ba? ‘Yan zaman Shahada, to wannan ai shine shahadar, danma bakisan sadda akayi korar NAYIB ba, inaga sannanma ko haihuwarki ba’ayi ba” ta k’ara da cewa

Ai da ace kina nan k’asar a lokacin da Kinga tashin hankalin da baki ta6a ganin irinsa ba, domin babu wanda aka bari da aka tashi kamen,  mutanenmu na nan Makka dana Madina ga na Jiddah da Ta’ib Saida duk aka kamo kowa k’wanmu da kwarkwatarmu, wasuma ko kayan Kirki ba’a barsu sun saka a jikinsu ba, Kuma k’arin abin takaicin ma babu wani gida da aka gina mana domin sakamu, sai wani wargajejen fili da aka zubemu sai kace tumakai, ga yunwa ga k’ishirwa, Wallahi Wasila ina mai tabbatar maki saida akayi rashin rayukka bila’adadin a gurin nan kafin su turamu k’asarmu, rashin imani k’arara babu wanda basu nuna mana ba a wannan lokacin” 
” Nifa sai inga duk abubuwanda sukeyi mana laifinmu yafi yawa a ciki, domin da ace munyi hak’uri mun zauna k’asarmu da dad’i babu dad’i dukda hakan bata faruwa ba, yo Khala a K’asarka ubanwa ya isa yazo har gida yayi maka wannan cin kashin? duk inda katafi ana binka a guje sai kace wani 6arawao, bakada halin zuwa inda kaga dama kuma a lokacinda kaga dama, haba dan Allah wallahi wulak’ancin ya isa haka” Aisha ce ke fad’ar haka yayinda take fitowa daga hammam bayan ta gama wanke jikinta daga dattin da yayi, inaga hakan ya samo asali ne saboda 6uya da tayi a cikin kayan wanki.
Muna nan muna tattaunawa akan abubuwan da suka faru mukaji shigowar Maman Waleed cikin matsanancin kuka na fitar hankali, Khala ce tayi k’okarin tambayarta abinda yake faruwa, bata tsaya da kukan ba saima k’aruwa da yayi, cikin kukan take cewa

” Wallahi Khala lokacinda Askarawan nan sukazo ne narasa inda zan 6uya shine na goya Waleed muka hau can saman gini, wallahi ban ankara ba dayake a rud’e nake bansan sadda Waleed d’in ya fad’o daga bayana ba, yanzu haka gashi can a gida kanshi ya fashe ko numfashima bayayi ina tsammanin ma mutuwa yayi” tana fad’a yayinda kukanta yake tsananta……
 Bamuma tsaya mun ida jin bayanin nata ba muka rankaya gaba d’aya zuwa gidan nata

Gaskiya halinda muka samu yaron abun babu kyan gani, domin gadon kansa data d’orasa akai yayi faca-faca da jini, saboda kan nasa indai ba gizo yakeyi mani ba a yanda na lura ya kusan rabewa gida biyu

batare da 6ata lokaci ba Khala ta nad’esa a cikin zani mu kuma muka rufa mata baya, bamu zame ko ina ba sai assibiti mafi kusa
Sai dai abin yazo mana a baibai, domin fafur assibitin nan k’in kara6armu sukayi wai har sai ankawo masu Igamar yaron, (takardar izinin zaman k’asa) data mamansa da babansa, da Kuma Takardarsu ta aure…..
Hmmm tirk’ashi! ashe duk dad’inka da zaman k’asar wasu wata rana zaka tuna da taka k’asar?😭
Kardai ku manta zaren labarin namu yana tafiya ne akan Wasila, bada jimawa ba zamu dawo kanta insha Allahu, kudai kuci gaba da biyoni domin jin Kalubalen da ke gaba
_Ina mika gaisuwata da Kuma godiya ta musamman ga dukkan masu bin littafin Kalubale_

_Allah ya bar kauna😘_

00966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             45 
Tun k’arfe d’aya da wani abu muke gidansu Mariya bamu muka bar gidan ba saida mukayi sallar asuba, kafin sannan nasaba da duk yan matan da muka tarar a gidan, domin munci fira mun k’oshi harma mukayi musayar lambobin juna.
*******************
Haka rayuwar Wasila taci gaba da kasancewa a garin Jiddah tana dawwari babu ji babu gani, yayinda duk bayan sati 2 ko wata 1 Antitiya takan turawa Uwani abinda Wasilar ta tara bayan itama ta gama d’ibar nata rabon, har zuwa lokacin da wani bak’on al’amari ya faru agareta wanda shima ya taka muhimmiyar rawa wajen k’ara ta6ar6arewa rayuwarta.
Wasila ce da Hauwa abakin ishara suna dawwari suna d’an ta6a hira abinsu cikin nishad’i.
Hauwa d’aya ce daga cikin yan matan da muka had’u dasu a gidan su Mariya, tafi sakar mani fuska duk cikinsu shiyasa tamu tazo d’aya da ita, hakan nema yasa wata ran na bita inda take dawwari wani lokaci kuma nabi Zulai
Itama sa’a ta ce saboda inma zamu girmi juna inaga baifi da yan watanni ba.
“Niko Hauwa badan kar na sakaki cikin matsala ba da nace ki taimaka mani da wani abu” na fad’a ina mai karantar fuskarta
Murmushi tayi kamar yanda tasaba kullum 
“Karki damuwa fad’a mun damuwar taki indai inada halin taimaka maki ni kuma nayi maki alk’awarin zan taimaka maki ‘yar K’awalliya” Ta fad’a tare da dafa kafad’ata 
Shuru nayi ina nazari na yan sakwanni kana nace 
“So nake yau idan mun koma gida zan saka Antitiya ta kira mani lambar iyayena mu gaisa, bayan mun gama gaisawa dasu idan ta kar6i wayar nakeso kisan duk dabarar da zakiyi ki sato mani lambar su, wallahi idan kikayi mani haka kin gama mani komai a duniya K’awata”
Ajiyar zuciya tayi gami da ciza yatsa nad’an wani lokaci kana tace
“Aikin naki fa Wasila ba k’arami bane saboda haka yana buk’atar sallama kafin a fara sa, indai kika sallameni ni kuma wallahi tsab zan gama maki aiki batare da wata matsala ba” ta fad’a yayinda take mik’o mani hannu alamar na biyata kud’in aikinta tukun
Cikin farinci na rik’e hannayen nata duka biyun
“Indai dan wannan ne bakida matsala tawan zan sallameki ma abinda yafi k’arfin kud’in aikin naki.
Canza akalar labarin namu tayi, cikin d’aure fuska tace
“Amma wallahi Wasila ina mamakin ace duk tsawon zaman nan naki a nan k’asar wai bakida lambar Iyayenki, kodai ada kinada ita daga baya ne kika rasata?”
Girgiza kaina nayi tare da ta6e baki duk a lokaci d’aya 
“Wallahi ba haka bane ba Hauwa, dama can banida ita  kuma banida hanyar samunta sai yanzu ne wannan tunanin yazo mani” 
Wata uwar ashar ta jawo ta sauke, da hanzarinta ta juyo ta dubeni
“Ammafa wallahi mutanen nan basuda mutunci ko ince basu da imani, haka kawai zasu mayar dake baiwar k’arfi da yaji? to wallahi bazata sa6u ba wai bindiga a ruwa 

ina mai baki shawara indai kika samu lambar Iyayen naki kawai ki gudu kisan inda dare yayi maki, Inma kinada k’arfin zuciya kamar ni basai kinma wani gudu ba, kawai tsayawa zakiyi ki zage uwarsu da ubansu tsab ki sa6i jakarki ki bar masu gidan….
Ban tsaya ta k’arasa abinda tayi niyar fad’a ba na tari numfashinta
“Nayi me ki kace  Hauwa? nabar masu gidansu natafi ina bayan duk k’asar nan kinsan banida wasu magabatan da suka wuce su, gaskiya nikam tsoro nakeji dan karma kiyi tunanin zan iya” 
“Wasila! Wasila! ina jiye maki shiga bak’in cikin da yafi wannan nan gaba, domin irin mugayen matan nan nasan su farin sani bama sanin shanu ba, saboda farkon zuwana nan k’asar a hannun ire iren su na fad’a , babu irin wahalar da bansha ba a gunsu, ke in tak’aice maki labari a lokacin da na haifi yarona Haidar ko wanka basu bari nagama ba suka kar6e yaron suka ajesa a gunsu suka danna ni gidan aiki, ko wayama basu barni na tafi da ita ba saboda a cewarsu wai sai nagama biyan bashin da aka kawoni kana zasu barni da waya, saidafa na shekara guda cir kana sukaje suka d’aukoni a gidan aikinda nake a can Riyadh” 
Da mamaki fal a fuskata na kalleta 
“Wai dama kina nufin kice mani kin ta6a aure harma kin haihu?” 
Ajiyar zuciya tayi gami da yin wani murmushi, ko ince yak’e kafi kuka ciwo 
“Wasila na ta6a yin aure amma auren bai wani dad’e ba muka rabu a lokacin inada cikin Haidar, dalilin bak’in cikinda nake ciki ne na rabuwata da baban Haidar har wad’annan mugayen kuma azzalumai sukayi nasarar kawoni nan”
Ta k’ara da cewa “Wasila nasha wahala iya wahala a gurinsu , nayi kuka nayi bak’in ciki da dana sani yafi sau shurin masak’i, amma da suka kaini k’arshe ingaya maki zagesu nayi tatas, ke in tak’aice maki labarima wallahi har kusan doke-doke mukayi kana muka raba jaha, yanzu haka ba’a k’ark’ashin ikon kowa nake ba, gidansu Mariya ma da kika ganni kud’in haya nake biya
“Lallai Hauwa kema Kinga rayuwa kuma kin cancanci a tausaya maki, amma kinata maganar Haidar kuma ban ganki da Haidar d’in ba ko kin turasa gida ne yayi karatu kafin ki koma?”
Saida ta goge k’wallan da taketa faman 6oyo tun d’azu dan karsu fito amma ina saida suka fito, cikin muryar kuka tace mani 
“Wasila Haidar ya rasu a gurin Mugayen matan nan, shiyasa bazan ta6a manta dasu a rayuwata ba

Ban dad’e da tafiya gidan aikin ba ya rasu, kuma babu wanda yayi tunanin ya sanar dani har saida na shekara guda nadawo kana nasamu labari, wallahi Wasila ko gawar Haidar ban samu na gani ba, ai tsakanina da wa’yanan matan na Riyadh Allah kad’ai zai iya saka mani, shiyasa ko mak’iyina bana fatan akaisa gidan aiki Riyadh, koda yake na Allah basa k’arewa domin ance a ko ina akwai nagari da Kuma lalatacce”
Labarin Hauwa ba k’aramin girgiza ni yayi ba, domin ta bani tausayi matuk’a, shiyasa nima na k’uduri aniyar yiwa kaina gata tun kafin wankin hula ya kaini dare 
Dafa kafad’arta nayi nace
“Ki daina kuka Hauwa insha Allahu komin daren dad’ewa sai sunga sakayyarki, shi kuma Haidar Allah ya jik’ansa yasa mai cetonki ne ranar gobe k’iyama” 
Goge hawayenta tayi kana tace “Ameen Wasilata” ta k’ara da cewa lokacin tashin mufa daga ofis yayi, (gurin bara) yakamata mu hanzarta fa mu tafi gida hakanan ko ma samu mu sato lambar wayar  taki ko?”
 *Ku fahimceni*

_Banyi wannan littafin da nufin cin zarafin wani ko wata ba, a’a nayisa ne kawai domin Jan hankali ga iyayenda ke turo yaransu ‘yan mata k’asar Saudiya da nufin neman kud’i batare da wani tsayayyen mai kula da tarbiyarsu ba_
_Idan labarin nan yayi kama da naki ko naka to arashi ne amma ni ba nufina kenan ba_
_Kuma ku sani labarin littafin bawai yana nufin duk wata budurwa wacce ke gidan aiki anan k’asar Saudiya lalataacciya bace, a’a akwai na kirki domin a zatona ma na kirkin sunfi yawa, saidai kawai labarina ya ta’allak’a ne ga masu gur6atacciyar tarbiya, domin akansu nakeso nayi Jan hankalin ko ince akan iyayensu, mai yiyuwa idan munada rai da lafiya nan gaba idan zanyi wani littafin na karkata akalar rubutun nawa akan kimtsattsun cikinsu_

_Karku manta a kowane gari kuma a kowace k’asa ana samun mutane na gari da Kuma lalatattu, dan ko Allah (S.W.A) cewa yayi *YUKRUJIL KABISA MINAD’AYYIB, WA YUKRUJIL D’AYYIB MINAL KHABIS* wato yakan fitar da marar kyau daga jikin mai kyau, ko kuma ya fitar da mai kyau daga jikin marar kyau._

_Kenan kuwa idan hakane a ko ina ana iya samun mai kyau da Kuma marar kyau_

_Ina fatan zaku *Fahimceni*nagode_
*NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

+966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             42 
Suko a 6angaren su Sakina dasu Khala wa’yanda aka kama, Khala Uwani tayi iya k’okarin dan ganin ta dammanosu konawa ne (Belin )kamar yanda suka buk’ata amma amma abin yaci tura, domin wannan karon abin yayi tsanani sosai, dole saidai suyi hak’uri su dangana da gida Nigeria, mai yiyuwa mai son dawowa ciknsu agaba  sai ya dawo.
Shara muke tayi babuji babu gani domin gaba d’ayan gidan namu a harmutse yake duk sunbi sun watsasa, yau mune har kusan 10 na safe bamu kwanta bacci ba saboda harmutsin da ya faru jiya da dare
A cikin tarin tsummokaran da nake gyarawa naci karo da wayata, wani dad’i ne ya ziyarci zuciyata kasancewar bata salwanta ba
Miss call kusan 50 nagani, amma na Yusuf da Adams da Kuma Farida sunfi yawa
Wayar Farida na fara kira, a kid’ime take tambayata abinda ya faru jiya ko ya rutsa damu
“Kedai bari Farida ai jiya munga tashin hankali, tashin hankalin da tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin irinsa ba , dukafa ‘yan gidanmu ankwashe , babu wanda aka bari dagani sai Aisha da Khala,” (anan na labarta mata rashin lafiyar Waleed da Kuma mutuwarsa)
Abin ya bata tausayi matuk’a domin har ji nayi muryar tata tad’an canza kamar zatayi kuka, kana dai ta daure ta canza akalar labarin

“Waini ko Wasila kinko san kamen jiya harda yayanmu ya rutsa?”
Gabana ne ya yanke ya fad’i lokaci guda, tare da wata zazzafar zufa ta babu gaira babu dalili “Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un kawai nake ambata, wai kina nufin yanzu haka Yusuf yana hannunsu? to ina igamar tasa ko kina nufin hakanan babu igama wannan k’aton hotel d’in suka d’aukesa aiki?” lokaci guda duk na jero mata wa’yan nan tambayoyin
“Kwantar da hankalinki dama jaddadi ne baiyiwa igamar da wuri ba (sabuntawa) kuma kinsan halinsu sarai nema kawai suke su kamaka da laifi tunda koda igamar taka bawani son zamanka sukeyi ba dan dai basu da yanda zasuyi da mai igamar ne kawai, amma koda yaushe cikin neman laifinsa suke, koda yake Yusuf d’inma yace mani zasu sakesa nan bada jimawa ba bayan sun saka masa karama” (Tara)
Ta k’ara da cewa” Yo ke inbaya ga abinki ina zai tafi yana niyar zama ango”
Wani bak’in ciki naji wanda bansan dalilinsa ba yazo ya tokare mani zuciya, dukda haka dai saida na jeho mata tambayata
” Wai dama kina nufinYusuf aure zaiyi amma bai gaya mani ba shine ya zagaye kuna shawar-warinku tare ko? To wannan kuwa wace mai sa’a ce wadda zata rabamu da yayanmu?”
 hakanan na daure nake saka raha a ciki zancen nawa amma zuciyata dam take kamar ta fashe dukda bansan dalilin hakan da nakeji ba
Maganarta ce ta dawo dani cikin hayyacina tamkar saukar aradu 
“Babu wacce ta isa ta rabamu da yayanmu domin yayanmu na nan tare damu, saboda nice matar tasa Kinga ko ai muna tare har abada koba haka ba Aminiyar?”
Bansan lokacinda wayar ta su6uce a hannuna ba ta fad’i k’asa tsabar firgici..
Da sauri na duk’a na d’auki wayar na karata a kunnaina dan gudun kada ta fahimci halinda na shiga ciki lokaci guda…
“Hmm kina bani labari K’awata wayar ta fad’i. kice har komai ya daidaita kenan d’aurawa kawai ya rage?”
“la! la! da d’an saura tukun  domin har yanzu maganar sadakin ba’ayi matsaya guda a kansa ba, ita Khala Harira tace sai ya bada jaka 5 (dubu d’ari 6) yayinda shi kuma jaka 4 ne dashi (dubu d’ari 5) saboda a yanda yace mani duk ya kashe kud’aden nasa a gurin gyaran gidan da zamu zauna da Kuma kayan d’akin da yasaka da kayan Matbak (Kicin) da sauransu, yanzu ga kuma wannan tsautsayi daya afka masa”
“Haba dan Allah! itako Khalar taki ta tausaya masa mana, ai yama k’ok’arta sosai, ga wannan uban sadaki gashi shine zaiyi komai na gidan harma da kicin, aiko abin a tausayawa ne, inda a garinku ne Katsina ba dubu 20 ne zai bada sadakin ba? sannan gidansa kawai zai gama ya shafa masa fenti, iyayenki sune zasu cikasa da komai, saboda tsananin gatama harda abinci za’a had’oki dashi, ai ya kamata muna godewa Allah tunda har yakawo mu k’asar wadata inda in za’a kai amarya ba’a buk’akatar tazo da komai face kayan sawarta, dukda dai ba al’adarmu bace mu hausawa ara mukayi gun larabawan amma wannan koyin da mukeyi dasu yana matuk’ar burgeni wallahi…
“To chakwai-kwaiwa ya isa hakanan ni duk kinbi kin cikani da surutu hardama wasu ‘yan k’ananan gore-gorenki, ina Adams d’inki? yakamata shima ya yunk’uro domin musha biki” ta k’arashe maganar tata cikin zaulaya”
“Hmm Adams ai shima yana can inda Yusuf yake, banbancinsu kad’an ne domin shi Yusuf zai fito shiko Adams saidai idan yaje gida ya sake dawowa”
Nandai ta jajanta mani muka cigaba da firarmu cikin nishad’i muna tsara yanda hidimomin bikin nata zasu kasance.
Amma a bad’ini Kuwa zuciyata sak’a kawai takeyi tana war-warewa, yayinda narasa abinda nakeji gameda ita, shin farin ciki ne ko kuwa akasin hakan? 
hakan na nufin nayi kamun gafiyar Kuido kenan, Ma’ana nasaki kuma ban kama ba? saboda babu shakka Yusuf yayi k’okarin fahimtar dani irin son da yakeyi mani akai-kaice, kuma ina sane, amma da yake lokacin babu kowa agabana sai Adams sai na ringa nuna masa tamkar banma fahimci abinda yake nufi ba, yanzu gashi nan bani ga tsuntsun kuma bani ga tarko, na saki reshe na kama ganye,  to yanzu ga ganyen  nan ya tsinke ya tik’oni da k’asa, yayinda reshen kuma yayi mani nisa nisanda bana tunanin zan iya kaiwa garesa..😫😭

_Ina godiya ga dukkan masu bin littafin Kalubale, masu bugo mani waya da masu turo mani sako ta private, dama wad’anda suka karanta sukayi shuru. idan danbu yayi yawa baya jin mai. Sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa ba, sai dai kawai ince ina godiya Allah yasa mu amfana da dunbin darussan da suke ciki kuma ya  bar kauna_😘👏
*MAMAN JA’AFAR*

00966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             47
Da shigar Zulai gidan ta sami Antitiya tana waya da Khala Uwani, tana labarta mata dukkan abinda ya faru a tsakaninmu sai kace a almara  
Uwanin ta dage sai surfama Antitiya masifa takeyi, tun Antitiya na bata hak’uri har takai itama tana ramawa, k’arshen dai zancen nasu ya tuk’e ne a inda Uwanin take sahidama Antitiya gata nan tafe Jiddan gobe goben nan
bayan ta gama wayar ne taga Zulai ta k’ura mata ido tayi mata zuru sai kace mai karantar wani abu a Fuskarta, bulalar gabanta ta d’auko a fusace ta zuba mata guda d’aya, ta k’ara da cewa 

“Shegiya kin tsaya kin wani kafeni da ido kema kina kissima yanda zakiyi ki gudu daga hannuna ko?” 
Ita dai kam Zulai zundumawa tayi a guje tana sosa baya, a cikin k’una-k’unin take  cewa
“Tunda dai na koya a gurinsu Wasila kuma na iya ai anyi mai wuyar, nima nan bada dad’ewa ba zan aiwatar insha Allahu, macuciya kawai, da yardar Allah hawan jini da ciwon zuciya ne ajalin ki da Kuma ire-irenki…
“Zo nan dan ubanki, inbaga tsoro ba ki fito fili ki fad’i abinda kikeson fada mana kiga idan banyi k’uli-k’ulin kubra dake ba”
****************
Gidansu Hauwa muka wuce kai tsaye d’akin su Mariya, dayake dama daga ita sai Mariya ne a cikin d’akin, shiyasa Uwar Mariya d’in take biyan kaso uku cikin hudun gidan, yayinda ita kuma Hauwa take biyan kaso d’aya.
Bayan mun ci abinci mun k’oshi munyi wanka muka zauna domin ida tattauna abinda ke gabanmu 
“Wasila ba mamaki fa kiga Uwani tazo garin nan yau ko gobe,  dan kinsan ba k’yalemu zatayi ba hakanan sakaka sai anyi gumurzu bama d’an kad’an ba, saboda haka duk bala’inda za ayi Karki yadda ki watsa mana aikinmu, ina fatan kin fahimceni? dan karkiga abin yayi tsanani kice zaki canza shawara dan nasan halinki da shegen tsoro zaki iya”
Kamar kuwa ta sani domin da jin wannan maganar tata sai tsoron ya k’ara ziyartar zuciyata
Amma a zahiri sai nace

“Karki samu damuwa insha Allahu zanyi k’okarin 6oye tsorona, dan yanzu haka bakiji yanda nakeji ba, kawai dai gani nan-gani nan dai”
Murmushi tayi kana tace

“Dama dole kid’an shiga damuwa kad’an, amma ki manta kawai a hankali komai zai wuce”
Ko kallonmu Mariya batayi ba (da yake dama d’akin sun saba basa rabuwa da bak’i, Inma K’awayen ita Mariya d’in ko kuma na Hauwa) Samma’a ne ta dad’e kunnenta da ita tanata faman yin ‘yan danne-dannenta a waya.
Haka muka zauna munata tattauna abinda ya faru da kuma wanda zai faru har asuba, bayan munyi salla ne munsha shayi muka nemi wurin kwanciya.
Sai sannan nema tunanin Maman Waleed ya fad’o mani a rai, Allah sarki! koya rigimar tasu ta kasance a assibiti? nasan dai yanzu Maryama mak’wabciyarmu ta Makka bata kai ga yin bacci ba, barama na kirata kawai naji yanda aka k’are.
Aiko wayar bata dad’e tana ringin ba ta d’auka
bayan mun gama gaisawa ne nake tambayarta rigimar su Maman Waleed yanda ta kasance
Ajiyar zuciya tayi  cikin murya mai alamun tausayi tace “Ke dai bari Wasila, wallahi saida sukabi diddigi ta hanyar kyamarorin da ke eriyarsu Maman Waleed d’in har suka gano musabbabin fad’owar tasa, amma dai Allah ya tak’aita abin, da addu’a da komai har aka samu suka safara su (kaisu)Nigeria batare da sun jima a cikin Sijin ba (gidan yari)
Allah ya k’ara kiyaye gaba nac, mukayi sallama na kashe wayata a lokacin 7 dai dai na safe.
Gyara kwanciyar nan da zanyi da niyar yin bacci, kawai mukaji dukan gida na masifa tamkar za’a 6alle k’ofar
Da sauri Mariya ta ruga domin ta tafi ta bud’e gidan, baiwar Allah tana tafiya tana layi, ga dukkan alamu tafara yin nisa a cikin baccin nata 
Tana bud’ewa tun kamin ta matsa daga jikin k’ofar Khala Uwani ta banko da k’arfinta har saida Mariya ta kusan  fad’uwa
Mu kuma muna bakin k’ofarmu a tsaitsaye muna jiran muga mahaukacin da ke yin irin wannan wawan dukan 
Buzum-buzum ta shigo tana raba ido tsakanin Mariya da Kuma Hauwa
“Ina Hauwa take a cikin ku? Kallon kallo muka fara yi a tsakaninmu babu wanda yace mata uffan 
Shak’e mani wuya tayi tun k’arfinta har numfashina na fita sama-sama 
“Zaki nuna mani Hauwar a cikinsu ko kuwa sai na hallaka ki?”  
Da k’yar su Hauwa da Maman Mariya suka samu suka k’waceni daga hannunta 
“Wai zaku nuna mani Hauwar ne koko sai na zazzagar maku da kalar rashin mutuncinda na iya?” 
Hauwa ce ta tattako ta iso inda take cikin isa da takama, nikam ina gefe ina maida numfashi da k’yar saboda wuyar da nasha
“Hee Uwani gani nan, nice Hauwa wani abu zaki bani ne koko wani abu zakiyi mani ?” 
Shak’o wuyan Hauwa tayi tamkar dai yanda tayi mani d’azu sai kace wata mahaukaciya 
“Ubanwa ya aikeki gidan Antitiya har kika iya k’arfin halin tafiya da Wasila? Shine kawai amsar da nakeso ki bani” 
Dukda tana hannun Uwani a shak’e amma bakin bai mutu ba, dan k’arfin hali saida tace
“Ubanki ne ya aikeni naje na d’aukota, banza tsohuwar kila…. 
Kafin ta k’arasa kwab Khala Uwani ta kwabd’e mata baki, nan take kokawa ta 6arke a tsakaninsu, muko sai k’okarin 6alle Hauwa mukeyi daga hannun Uwani amma ta rik’eta gam sai kace ranta da rayuwarta ta k’wace mata 
Keko Wasila kusan hakane mana ai hanyar samun kud’in ta ne akeso a  toshe mata Kinga ko ai sai inda k’arfinta ya k’are ko? Danma dai baki san irin mak’udan kud’ad’enda ta tara a dalilinki bane shiyasa kike cewa haka. Inji ni *Maman Ja’afar*
Bamu ankara ba sai ganin Hauwa mukayi ta zube k’asa a sume, aiko hankullanmu  gaba d’aya sun tashi, bamu kad’ai ba harda mai fad’an ita kanta

Kafin kace kwabo gidanmu ya cika dam da mutane mata da maza, niko inbaya ga kuka babu abinda nakeyi 

Da k’yar aka samu Hauwa ta farfad’o aka ci gaba da maida yanda akayi 
Yayinda Khala Uwani ta kafe ala dole sai na bita, ni kuma na buga kaina da k’asa nace allanbaram bansan da wannan zancen ba, mutane kuwa ire irenta macuta sai ganin rashin kyautawarmu sukeyi, yayinda wasu kuma suke ganin abinda mukayi munyi dai dai.
Da dai fad’an yak’i ci yak’i cinyewa sai wani mutum acikin masu rabon fad’an ya bamu shawara akan Mutafi Saffara kawai (Wajen hukuma amma wacce ta shafi K’asarku) inyaso can ne zasu raba mana gardama kuma zasuyi mana hukunci na adalci a tunaninsa……. 
Jama’a ku biyoni saffara domin ci gaba da jin labarin Kalubalen da Wasila ke fuskanta a nan gaba
_Ina godiya ga dukkan masu bin littafin Kalubale, masu bugo mani waya da masu turo mani sako ta private, dama wad’anda suka karanta sukayi shuru. idan danbu yayi yawa baya jin mai. Sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa ba, sai dai kawai ince ina godiya Allah ya bar kauna_😘👏
*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             46 
Da sauri-sauri nayi wankana naci abinci gami da yin sallah, yayinda ita kuma Hauwa na barota can d’akin Antitiya tana jirana nagama nazo muyi  duk wacce zamui.
Sallama nayi nashiga d’akin fuskata babu yabo kuma babu fallasa nasamu gefen Antitiya na zauna 
Ko kallon azzikima ban isheta ba domin k’anta a k’asa yake tanata faman kasabta kud’i abinta
“Antitiya! bani kud’i dan Allah nasiyo kati ki d’an kira mani su Hajar kinsan kwana 2 bamu gaisa dasu ba” 
Har yanzu dai bata d’ago kai ta kalleni ba saima wurgo mani 20 riyal datayi alamun naje na siyo katin 
Murmushi nayi kawai nad’auki kud’in domin ni nasan komai yazo k’arshe yau d’in nan basai gobe ba insha Allahu 
Tare da Hauwa mukaje muka siyo katin, muna tafiya muna k’ara tattauna abubuwanda zasu wakana har muka iso gida.
Sai yanzu ta d’ago kai ta dubemu a lalace  ta kar6i katin ta saka a wayar tata
 sai wani faman muzurai takeyi tana hura anci sai kace k’watar kud’in gabanta mukace zamuyi
Ina cikin wayar ne na k’yabtawa Hauwa ido, alamar muyi abinda ya kawomu kawai 
“Niko Antitiya d’azu da zan  wuce ta gidansu Ladidi naji kamar suna maganarki, amma ban sani ba ko kunnena ne yake jiyo mani k’arya” 

Hauwa ce mai fad’ar haka bayan ta tashi daga kan kujerar da take zaune ta dawo dai dai k’ugun Antitiya ta zauna 
Cikn fusata Antitiya tace “Ai dama nasan badaina gulmar tawa zasuyi ba dukda saffara tayi mana tsakani (hukumar da ke kula da mazauna k’asar Saudiya na najeriya ko Nijar) “Amma ke Hauwa me kikaji tana cewa a kaina? Dan insan da wacce zanje mata dan ba k’yaleta zanyi ba” kana taci gaba da fad’ace-fad’acenta tana kumfar baki

Gyara zama Hauwa tayi saboda ga dukkan alamu  hak’arta ta fara cimma ruwa, kana tace
“Ji nayi suna cewa wai kin samo yara kin ajiye sai wayo kikeyi masu kina k’wace masu kud’i, wai dama can ke macuciya ce azzaluma…”
Bata bari Hauwa ta ida dire zancen nata ba ta figi abaya tayi waje tanata faman fad’ace-fad’acenta, a tsammanina dai gidansu Ladidin ta nufa 
Tafawa mukayi gami da tuntsirewa dariya harda k’yak’yatawa, da k’yar nasamu natakawa dariyar tawa burki na kalli Hauwa nace
“Shegiya Hauwa! Ammafa kin iya tsula tsiya wallahi, to yanzu mi kike tsammani idan taje ta samu Ladidi kuma labari yasha banban?” 
Ta6e baki tayi gamida zakud’a kafad’a 
“Ohon masu, su suka sani, can suje su kashe kansu. da ita da Ladidin ai duk kanwar ja ce, k’waryar sama ce ke dukan ta k’asa” 

Ta k’ara da cewa “Malama bani wayar nan mu d’auki lambar kar mu tsaya garin surutu har ta dawo ta samemu bamu aiwatar da komai ba”
Cikin sauri muka d’auki lambar, kana kuma na nufi d’akinmu domin harhad’a kayana duka  kamar dai yanda muka tsara nida Hauwa
Ban kai ga kammala had’a kayan nawa ba na jiyo muryar Antitiya tun daga waje tanata surfa mana zagi nida Hauwa, take naji gabana ya fad’i tsoro ya mamaye zuciyata lokaci guda, d’akin Antitiya nadawo da gudu nasami Hauwa tanata sauraren wak’arta a cikn Samma’a hankalinta a kwance  tamkar bazata aiwatar da abinda ta tsara ba

 

“Hauwa anya kuwa zan iya guduwa nabar Antitiya kamar yanda muka tsara? Wallahi tsoro nakeji kuma king…..
“Naga me? Wasila wannan itace damarki ta k’arshe idan kikayi wasa da ita ke kika sani, nidai Allah na gani naso na taimaka maki saidai idan kece kika k’i”
 Bamu ankara ba mukaji ta banko k’ofa da k’arfi “kuna ina dan ubanku? munafukan banza munafukan wofi, ashe dama babu abinda Ladidi tayi mani kune kawai kuka tsara zancenku don ku kunyatani? To wallahi kunyi na k’arshe daga kaina bazaku sake yin wasa da hankalin wata ‘yar hajja ba (tsohuwar zama Saudiya) K’ana nan ‘yan iska kawai”
Rufe gidan mukaga taje tayi harda saka sakata, nidai kam bama fad’uwar gaba ba yanzu jikina har wata kyarma kyarma yakeyi saboda tunda nake da ita ban ta6a ganin ta harzuk’a sosai irin haka ba, shiyasa na tsammaci komai ma zata iya aikatawa akanmu. 
Wata zundumemiyar bulala naga ta d’auko tana tunkaro mu da ita, yayinda bakinta bai daina suburbud’a mana ashar ba 
Da sauri na ruga bayan Hauwa na rik’e ta gam ina runtuma ihu
“Au wai kina nufin da kika la6e a bayanta kin tsira ko kuwa? to bakiyi dabara ba domin gaba d’ayanku yau mai rabani daku sai dai Allah, jina jina zanyi maku inga ubanda ya d’aure maku gindi a fad’i k’asar nan” 
Ga mamakina Hauwa ko alamun tsorata batayi ba, domin sauraren wak’arta kawai takeyi hankali kwance
Saida taga Antitiya ta nufomu gadan-gadan kana ta mik’e tsaye  cikin siga ta rashin kunya ta nunata da yatsa 

“Kinga Malama tsaya! baki sanni ba ban sanki ba, dalilin Zulai kawai nake zuwa gidanki, idan kika rik’e girmanki zan girmamaki, idan kuma kikayi wasa dashi hmm zaki sha mamaki, kuma da kike ik’rarin zaki daki Wasila me tayi maki ? Ni na tsara maki zancen nan ba ita ba, saboda haka ni ya kamata ki daka ba itaba, kodan ita kin rainata kina ganin bata magana kuma batada mai yi mata? to kwantar da hankalinki Antitiya daga yau Wasila tabar hannun ku har abada, sai dai aje anemo wadda kuma za’a cuta nan gaba amma ba ita ba”
Wani wawan duka naga ta kaiwa Hauwa, ta d’aga bulalar domin ta k’ra Hauwa ta rik’e bulalar gam
 “Karki k’ara dukana Antitiya, idan kika sake bulalar nan ta sake ta6a jikina zakiyi dana sani…
“Dana sanin uwarki da ubanki, bara na k’ara dukan naki naga irin dana sanin da zanyi”
“Wallahi da kin k’ara sai nayi maki ihu na tara maki mutane ince kullemu kikayi acikin gida kikace ala dole sai kinyi lalata damu, da muka k’i amincewa shine kiketa dukanmu, kuma ki k’ara dukana kiga aiki da cikawa yanzun nan”
Nidai kam yanzu ‘yar kallo na zama, domin tsoron nawa ya fara fita ganin yanda bakin Hauwa yak’i rufuwa sai faman zazzaga masifa takeyi
Da jin wannan kalamin na Hauwa ina lura sai jikin Antitiya yayi sanyi, ajiye bulalar tayi ta buga uban tagumi sai kace gwaggon Biri na jin yunwa 
Da ganin haka saita bani tausayi harma nake ganin tamkar bamuyi mata adalci ba hakan da mukayi mata
“Wasila jeki ida had’o kayan naki kizo mu tafi, yau ai har fati yakamata mu had’a saboda murnar Allah ya k’watoki daga hannun mugayen zakuna” Hauwa ce mai fad’ar haka bayan ta mik’e tsaye ta rataya jakarta
Dibi-dibi na fara yi na rashin sanin madafa, idan na bita hakan na nufin yanzu nazama ‘yar kaina babu mai sakani ko ya hanani kenan? idan na zauna kuma hakan na nufin babu ranar yankewar wahalata haka zan k’are ina yi masu bauta har illa masha Allahu kenan?

Kai! ina? da babu gara ba dad’i gara nabi Hauwa kawai
Da hanzarina na koma d’akinmu na ida had’a kayana a k’atuwar jakata na d’orata aka muka fita daga gidan, yayinda muka bar Antitiya zaune a tsakar d’aki da ‘yar bulalar ta a hannunta sai kace wacce aka dasa, ko motsin kirki ta kasayi
A bakin k’ofar gidan ne mukaci karo da Zulai tana k’okarin shigowa ga dukkan alamu dawowarta kenan, da mamakinta ta kalleni, ta juya kuma ta kalli Hauwa 
“Wasila lafiya naga kun fito rai a 6ace kuma naganki da jakarki sai kace wata mai niyar barin gari?”
Murmushi Hauwa tayi kana ta mayar mata da amsa domin ni har yanzu a birkice nake babu wata natsuwa a tare dani 
“Wasila dai yau Allah ya tarfawa garinta nono ta rabu da Antitiya, saura kuma ke idan kinada rabo nan gaba, in kuma bakida rabo ki tsufa kina yi mata bauta” 
Baki ta saki galala tana kallonmu har mukayi nisa kana ta kutsa kai a cikin gidan…….

 _Ina godiya ga dukkan masu bin littafin Kalubale, masu bugo mani waya da masu turo mani sako ta private, dama wad’anda suka karanta sukayi shuru. idan danbu yayi yawa baya jin mai. Sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa ba, sai dai kawai ince ina godiya Allah ya bar kauna_😘👏
*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             43 
Durk’ushe nake a gaban Khala ina rok’onta ina had’ata da Allah da Annabi akan ta bani lambar iyayena nasamu mu ringa gaisawa bayan na tafi jiddan, amma fafur matar nan ta’ki bani, saima k’ara gyara kwanciya da tayi, da yake dama ita kullum sarkin kwanciya ce sai kace wata kasa.
Gyara zamana nayi na fuskanceta saboda nima yanzu na d’an fara bad’awa idanuwana kwallin Audi kad’an (rashin kunya) saboda abin nata ya kusan kaini k’arshe
“Khala dan Allah ki tashi muyi magana, ya muna magana kuma kin koma kin kwanta bayan kinsan Salamatu nacan gidan Maryama tana jirana mu tafi” na fad’a yayinda nake wani gatsina fuska sai kace zan iya yin wani abin Kirki
Firgigit naga ta tashi ta zauna sai kace wacce aka tsikarawa allura ” Waini Wasila waya kikeyi ne ko kuwa dani kike maganar taki ?”
Cikin dakewar zuciya nace “Niba wata waya da nakeyi hasalima ga wayar can bayanki tana caji, na fad’a tare da nuna mata inda wayar take, Aisha kuwa tun jiya ta koma gidan aiki barema kice ko da ita nake…
“To rasa kunya 6eran masallaci, basai kin tsaya kina wani kwane-kwane ba fitowa zakiyi gaba gad’i kanki tsaye kice mani dani kike, idan bakiyi haka ba ai bazan tabbatar Laban da shinkafa kaza da sanyin mukayyif sun ratsa ki ba (nonon roba da shinkafa kaza da Kuma A.C) 

ta fad’a tana wani zare ido da murgud’a baki sai kace mayunwacin zaki
Danaga tsiwar tawa babu inda zata kaini sai na k’as-k’antar da kaina cikin murya mai nuna ladabi agareta nace “Khala dan Allah ki taimaka mani ki bani lambar badan halina ba sai dan mu ringa gaisawa dasu, tunda Kinga yanzu zani  d’anyi nisa dake, ba mamaki mu d’au tsawon lokutta bamu had’u ba, Kinga ko idan hakane ta ina zan samu magana dasu?” na k’arasa maganar tawa da muryar kuka
Lank’washe k’afa tayi gami da gyara zamanta
“To kokefa! ai ni aganina Wasila abinda azziki baiyi ba ina zaton tsiya bayinsa zatayi ba, iyayen nan naki ina bakin k’ok’arina a kansu, lokaci zuwa lokaci ‘yar dubu biyar d’in nan zuwa goma ina aika masu, ni aganina ai  banga wani abin damuwa a ciki ba, tunda indai baki yaba mani ba, a zatona kuwa bakya zageni ba”
Da naga dai bata da niyar bani lambar saima nema da takeyi ta 6ata mani rai sai na share da maganar 
“To Khala babu komai ni zan tafi” Na fad’a yayinda nake sa6a jakata abaya 
Saida na kai bakin k’ofa na tsinkayi muryarta mai kama da antada Jannareto tana cewa
“Karki damu Y’ata, ki kwantar da hankalinki nabawa Salamatu lambar Iyayen naki ta kaiwa Antitiya wacce zaki zauna a gunta, duk sadda kika buk’aci da Ku gaisa zata had’aki dasu kinji? nidai babban fatana bai wuce ki dage ki nemo mana kud’i ba”
Sai sannan ne naji d’an sanyi-sanyi a cikin raina duk da kalaman nata na k’arshe basuyi mani dad’i ba, dukda haka ina laifin wanda zaya sama ya taka leda?

******************
Allah sarki! yau gani a Jiddah bayan na shafe shekara d’aya da wasu  ‘yan watanni rabona da ita, saboda k’aramar sallar da ta wuce bamu samu munzo zakki-zakkin ba saboda labari da ya samemu wai an tsananta kame a Jiddan,  dama haka lamarin  kamen na su yake, wata ran su tsananta a Jiddah, wata rana  kuma Su tsananta a Makka da sauran garuruwanda bak’i sukafi yawa a ciki. 
Isharar  dank’am take da motoci ta ko ina (titi) gabas da yamma kudu da arewa, ko ina ka  duba motoci ne, suke k’okarin wucewa, wasu gida zasu tafi, wasu gurin aiki, wasu gurin shakatawa da iyalansu, da dai sauran hidimomi irin na yau da kullum. 
Da yake titin mai 4 ne kuma ko ina motoci suna wucewa, shiyasa mu masu bara muma muka kasa kanmu gida 4, wasu gefe da gefe, yayinda wasu kuma suke can tsallake.
Kamar dai sadda muka tab’a zuwa, yauma abaya ce muka saka wata kod’add’iya da d’an hijabi a samanta, sai kuma silifas da muka saka da ‘yan ledejinmu a hannu (Shiga dai irinta mabuk’ata) wanda muke mik’awa duk wanda yayi niyar bamu sadaka sai yasaka mana acikin ledar,  kamar dai yanda Zulai ta koya mani wato wacce Anyitiya take rik’o, dayake dama ba a hannun Salamatu Khala tace zan zauna ba, dama cemata tayi ta kawoni gurin wata K’awarta Antitiya
Antitiya itama babbar mace ce kamar Khalata, domin dukkansu idan basuyi shekaru hamsin hamsin ba inaga kad’an ne babu aciki, saidai a gurin halaye ne bansan wanda yafi wani rashin mutunci a cikinsu ba.
Zulai kuwa ‘yar da take rik’o ce, inaga zamuyi sa’a da ita, sai dai bas (kawai) ita bak’a ce kuma mai k’iba, yayinda ni kuma na kasance fara siririya da d’an matsakaicin tsawo

itama dai bansan halin nataba tukun saboda jiya jiyan nan muka fara had’uwa.
Motoci muke bi wa’yanda aka dakatar kafin a basu hannu su wuce 1 bayan 1 muna d’aga masu yatsa alamar Sabilillah.
 Can naga Zulai ta runtuma a guje har wata mota tana neman ta kad’eta, amma ina hankalinta ba anan yake ba, nima da hanzarina na bita saboda tsammanina y’an kame ne ta gani ta ruga, saida na cimmata ne nake tambayarta ta inda ta hango yan kamen
Dariya naga tanayi kana tace
 ” Waike kin zaci ‘yan gari nagani shiyasa kema kika biyoni a guje? to babu wanda nagani sai waccen motar (ta fad’a yayinda take nuna mani wata mota da mata kusan 5 ciki, namijin ne kad’ai direba) ai matanda ke ciki, babbar sadaka suke badawa shiyasama dana hangota kikaga na runtumo a guje, ai indai kinaso kinaso ki zauna lafiya da Antitiya sai kin dage da neman kud’i babu ji babu gani, domin inba haka ba, hmmm wallahi  abinda zatayi maki sai kin gwammace dama bakizo duniya ba”

Ajiyar zuciya nayi araina nace wata sabuwa kuma kenan inji y’an  caca, amma a zahiri sai nace 
“A magan-ganun naki dai kina nufin kice mani itama Antitiyar babu sauk’i kenan kamar……..?

Shin wai haka rayuwar Wasila zata k’are ne a tan6ele da garari ko kuwa dai ana samun canji ne a gaba?
Don jin wannan amsar kudai kuci gaba da biyo ‘yar mutan Katsinawa dan jin chakwakiyar da ke gaba
_Fatana, da rok’ona, gami da addu’ata, bazasu ta6a gushewa ba ga dukkan masu bin littafin *Kalubale* Zano sunayensu ba karamin aiki bane, domin hausawa suna cewa wai idan danbu yayi yawa baya jin mai, sai dai kawai nace nagode Allah ya bar kauna_ 😘👏
*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             49
Ana sallar La’asar muka dawo, muna idar da salla ko abinci bamu tsaya ci ba na azalzali Hauwa ta taso mu tafi dawwari ko nasamu na kati na kira su Hajar yau musha fira.
Ana gama sallar isha na kuma matsa mata akan mu dawo gida tunda nasamu abinda na fito nema, wato kud’in kati da Kuma na abinci 
“Kinga Malama saurara mani dan Allah Karki takura mani, kawai dan kin samu kin rabu da alak’ak’ai shine kuma zaki saka wasa a wajen neman kud’in naki har nima ki hanani nawa? to nidai ban tashi tafiya ba, jeki saina iso” 
“Inma gatse kikeyi mani ni Kinga tafiyata, kin manta saura sati 2 nazama mai kud’i zan tsaya inata wahala a bakin titi?” Na fad’a yayinda nake tafiya ina dariya 
“Indai Saffara ne ki bari sai kud’in sun shigo hannunki tukun ki fara hura hancin” 
Nidai ban fahimci abinda take nufi ba nayi gaba abuna. 
Yau Albaik na siya filet biyar (Wata soyayiyar kaza ce mai shegen dad’i wadda larabawa ke ci) dani da yan gidanmu kowa yaci albarkaci tunda ba zaman wani nakeyi ba yanzu bare ace mani na kawo abinda na samo
Daga nan kuma na biya na siyo wadataccen kati na zubama wayata

Aini yau sharaf nake jina, dan jin yau nakeyi tamkar ran salla.
Da isowata gida nabawa Mariya da Mamanta nasu nabaro d’akin nasu sunata faman yi mani godiya,  naci nawa na ajewa Hauwa nata, na haye kan kujera na dannawa su Hajar kira
Aiko wayar bata dad’e tana ringin ba suka d’auka, muryar Hajar naji can k’asa-k’asa tana tambayar Wanda ke magana 
“Hajar nice fa Wasila baki gane ni ba?” Na fad’a cikin d’oki da farin ciki
 Sakin muryarta naji tayi itama cikin farin ciki take cewa “Allah sarki ‘yar halak kin k’i ambato yanzun nan kuwa Gwaggonki tabar gidan nan, munsha firarki da ita ashema kina nan kina shirin bugawa?” 
“Wallahi Kuwa, da badan ta tafi ba aida mun gaisa, ya su Affa da sauran ‘Yan’uwana? amma Hajar ai yanzu sun gama karatun allon sun dawo gida ko?”
Shuru naji tayi na tsawon lokaci, inata alo alo, shuru dai babu magana, har zan kashe wayar na sake bugawa naji tace
“Kullum idan mukayi waya dake sai kin tambayeni su Tanimu, wai mantawa kikeyi ne da sun rasu ne koko?”
Wani jiri-jiri naji, nan take na fara gani dishi-dishi, “wai Hajar da gaske kikeyi ko dai wasa kikeyi mani” Na fad’a cikin kuka 
“Haba Wasila! ko inayi maki wasa ai bazanyi maki wasa da mutuwa ba? Wallahi da gaske nakeyi, kuma ai tun ranar da had’arin ya faru na bugowa Uwani nace ta sanar maki, kaddai bata fad’a maki ba?”
Kukana bai tsaya ba nace “Wallahi Hajar bata fad’a mani ba, hasalima ko alamar hakan ban gani a fuskarta ba, saboda tasan idan ta fad’a mani ai hankalina zai tashi nakasa nemar mata kud’i shiyasa ta shareni”

Sallallami Hajar tafarayi, da alamun mamaki tace “Amma kam Uwani ta bani mamaki, saboda kwata kwata ban tsammaci haka daga gareta b…” Bata kai ga k’arasa zancen nataba kuka ya kubce mata 
Nima dai kukan naketayi, ya zamana dani da ita babu mai rarrashin wani 
Da k’yar Hajar ta samu kukan nata ya tsaya ta dawo tana rarrashi na
Saida nayi shuru ne nake labarta mata irin rik’on da Uwani tayi mani, gaba d’aya labarina ban 6oye mata komai ba, tun daga farkon zuwana Saudiya abubuwanda sukaita faruwa akaina babu abinda ban fad’a mata ba, har zuwa abinda ya faru yau da safe da kuma rabuwa da su Uwani da mukayi duk ban 6oye mata komai ba sai abu d’aya wato rayuwata ta bayan fage (Mu’amalata da Adams) 
Ta tausaya mani matuk’a kuma tayi dana sani sosai na turoni da tayi k’asa mai nisa alhalin babu dangin iya babu na baba 
“Wai Niko Hajar ina Affa banji kince mani gashi ba?”
“Wallahi Wasila babanki nacan d’akinsa kinsan ba wani jin dad’in jikinsa yakeyi ba tun mutuwar yan uwanki”
Nanma saida kukan nawa ya dawo sabo
“Kuma Hajar ankaisa assibiti kuwa?” 
“Wallahi munje Wasila kud’in assibitin ne da yawa shiyasa muka dawo gida munayin na hausa, kusanfa dubu ashirin sukace akawo, Kinga ko ina zamu samu dubu ashirin inba kanmu zamu saida ba” 
Wasu hawaye ne masu k’una suka zubo mani, ina nan ina tarawa wasu k’attin banza miliyoyi amma ga iyayena can dubu ashirin shegiya ta gagaresu.
Ajiyar zuciya nayi kana nace “Hajar kai masa wayar mu gaisa nayi masa ya jiki gami da ta’aziyya” 
Mun jima muna gaisawa dashi kana mukayi sallama ya bawa Hajar wayar.
Nan mukaci gaba da tattaunawa akan rasuwar su yaya gami da yiwa junanmu ta aziya, bamuyi sallama ba har saida ta k’ara jadda da mani nasiharta ta kullum agareni, wato na kama kaina kuma na rik’e mutuncina a duk inda nake 
A zuciyata nace daga baya kenan Hajar wai anyi sadaka da karuwa, tun yaushe aikin gama ya riga ya gama
A zahiri kuma cemata nayi Karku damu iyayena insha Allahu zan kiyaye da dukkan abinda zai 6ata maku rai kunji?
_Ina godiya ga dukkan masu bin littafin Kalubale, masu bugo mani waya da masu turo mani sako ta private, dama wad’anda suka karanta sukayi shuru. idan danbu yayi yawa baya jin mai. Sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa ba, sai dai kawai ince ina godiya Allah ya bar kauna_😘👏
*MAMAN JA’AFAR*

  +966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             48 
Mota biyu muka cika zuwa saffara, da Uwani da Antitiya da Zulai motarsu guda, yayinda mu kuma muka cika mota guda dani da  Hauwa da Mariya da kuma Mamanta.
******

Saffarar k’aton guri ne domin zai kusan girman gari guda, kuma iya ganinka duk inda ka waiga yan sanda ne ke kai komo a ciki
Da naga yan sanda ta ko ina har nafara tsorata ina yan ra6e ra6e, sai Mariya ke kwantar mani da hankali akan kar nadamu ba komai zasu yi mani ba , kuma hasalima basu sani ba munada takardar izinin zaman k’asa ko bamu da ita. 
Wani babban ofis aka kaimu mai girman gaske, da kujeru ko ina a cikinsa domin zaman mutane, sai wata kijera mai juyawa irin ta Yan gayun a nan tsakiya da Kuma teburi a gabanta, ga dukkan alamu mai saura rar k’arar ne ke zama akanta. 
Saurayi ne mai jini ajika ko kuma nace Dattijo, domin a tsammanina zai kai shekaru 40 ko kuma ya haura haka, sai dai yanada kyaun jiki da Kuma hutu daya zauna masa, shiyasa farat d’aya bazata iya k’iyasta shekarunsa ba.
Bak’i ne kuma dogo yanada yar matsakaiciyar k’iba. 
Bayan mun zazzauna ne ya k’are mana kallo d’aya bayan d’aya, kana ya tambayi sunayen mu  muka fad’a masa mu duka
Gyaran murya yayi gami da tatttaro natsuwarsa guri guda “Wace ce Wasilar a cikin ku?” 
D’aga hannuna nayi gami da cewa Yalla6ai nice ”
“Me yake tafe daku ne” Ya fad’a yana mai kallona cikin nuna isa da tak’ama 
In ina nafara yi saida ya daka mani tsawa kana na natsu nace 

“Dama na kawo k’arar wannan ne” na fad’a ina mai nuna Uwani da yatsa 
“Ok! Akan me kike k’arar tata? 
Nanma dai kame kame nashiga yi saida Hauwa ta Harareni kana na tuno da maganar da tace na fad’a koda rigimar ta kaimu saffara 
“Ina k’ararta ne kan wahala da naitayi yi mata ta tsawon shekaru amma har yanzu batace na biya bashin da ta kawoni ba” 
“Tsawon shekara nawa kenan kina yi mata wahalar kamar yanda kikace ?”
 “Zanyi shekara hud’u a hannunta ina cikin ta biyar” 
“Kuma a gidan aikin nawa nawa ake biyanki a wata?” 
“Duk wata ana biyana jaka d’aya da rabi ne, shekarata 3 da wani abu  ina gidan aikin daga baya kuma ta turoni nan Jiddah yin dawwari, yanzu haka shekarata d’aya kenan anan Jiddan da wani abu” 
Gyad’a kai yayi alamar gamsuwa, kana daga bisani kuma ya juya indasu Antitiya take 
“Wace ce Uwanin acikin ku?”
Saida ya k’ara maimaita tambayarsa kana ya ta d’aga hannu “Nice ranka ya dad’e” 
“Da kyau! Mice ce alak’ar da ke tsakaninki da Wasila? Ina nufin yar’ki ce ko yar wani naki?”
Muzurai ta fara yi tana rarraba idanuwa a tsakaninmu 
“Ban had’a komai da ita ba, kawai dai na kawota a bashi ne a zuwan idan tazo ta nema sai ta biyani” 
Gyad’a kai ya Kuma yi alamar gamsuwa 
“A nawa kika kawota kuma ribar nawa kika d’ora mata?” Ya fad’a yayinda ya kafeta da idanuwana
Um um “duka dai harda ribar miliyan d’aya ne da dubu d’ari biyu” 
“Da kyau! A lissafin da Wasila tayi mani duk wata tana d’aukar albashi kimanin dubu d’ari da hamsin, idanko hakane Kinga ko miliyan d’aya da rabi kika kawota a shekara d’aya ta biyaki ko ba haka ba ?” 
Kyarma naga ta farayi da k’yar ta samu tace “haka ne Ranka ya dad’e” 
“To Kinga kenan mu barsa a shekara 1 ta biyaki, ina kud’in shekara 3 suka shiga kenan?” 
Nanma dai batace komai ba 
Juyowa yayi 6angaren da muke “Wasila a dawwarin da kikeyi a kullum kina samo nawa?” 
“Eh to! Bama samo dai k’asa da fan goma, saboda Antitiya horo takeyi mana mai tsanani idan basu kai ko suka haura hakan ba ” 
“Kin yadda da abinda ta fad’a” 
Gyad’a kai tayi alamar amincewa batare datace komai ba 
“Yanzu dai Atak’aice  kuma a adalcin da zamuyi maki Wasila  tana binki bashin miliyan 5 saboda haka na baki sati 2 kije ki nemo mata kud’in ta duk inda suke ki kawo mata nan” 

Kana ya juyo inda nake “Ke kuma Wasila nanda sati 2 kizo nan ki kar6i kud’inki kina jina ko ?” 
Na amsa da “Eh ranka ya dad’e” 
“Ke kuma Uwani Karki kawo kud’in nanda sati 2 kiga abinda zai faru, Inma guduwa zakiyi ki gudu duk inda kikaje sati biyun bazata ida cikaba sai mun gano ki duk inda kika shiga, kuma idan mun ganokin kinsan dai hukuncin Safarar Ya’ya’n mutane ne akan ki ko? hukuncin kuwa d’auri ne har sai an manta dake a ajiye, mai yiyuwa ma sadda zaki fito ko d’and’anon suga dana gishiri bazaki iya banbancewa ba, Ku tashi ku bani wuri” Ya fad’a tare da Mik’ewa tsaye  
Wani matsanancin farin ciki ne naji ya ziyarci zuciyata lokaci guda 

Allah mai yadda yaso, shekara da shekaru ina faman wahala, yau gashi cikin lokaci k’ank’ani na zama Muloniya, Allah nagode maka kuma na godewa Hauwa, saboda badan ita ba bansan iya lokacin da zan d’auka ina yi masu bata ba. 
Cikin farin ciki da annashuwa muka bar gurin, yayinda Khala Uwani ta bar gurin tana runtuma ihu tana kuka sai kace wacce aka yiwa mutuwa….
_Ina godiya ga dukkan masu bin littafin Kalubale, masu bugo mani waya da masu turo mani sako ta private, dama wad’anda suka karanta sukayi shuru. idan danbu yayi yawa baya jin mai. Sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa ba, sai dai kawai ince ina godiya Allah ya bar kauna_😘👏
*MAMAN JA’AFAR*

00966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             50 
*BAYAN SATI BIYU*
‘Yan gidanmu basu samu damar rakani saffara ba domin bayan sallar La’asar akace na koma a lokacin kuwa duk basa nan sun fita dawwari, ran nanma dan dai ana cikin tashin hankali ne kawai suka samu damar yi mana rakiya.
****
Dayake dama nasan ofis d’in ban sha  wuya wajen ganesa ba
Zaune yake yana yan rubuce-rubucensa cikin nishad’i 
Sallama nayi masa gami da samun kujera guda nayiwa kaina matsugunni 
Da fara’arsa ya tarbeni ba kamar wancen zuwan ba da yake yi mana wani gani-gani 
Cikin ladabi na duk’a na gaidashi 
Amsawa yayi tare da tambayata cikin zaulaya 
“Kinzo kar6ar miliyoyinki ko Wasila?” 
Murmushi nayi kawai bance masa komai ba, tunda in baya ga rainin hankali ai yasan kud’i na nazo kar6a ba kallonsa nazoyi ba 
Can daga sama naji yace “Uwani ta kawo kud’in ki tun safe, saidai ni kuma dana karb6o maki miye nawa tukuicin?” Yana magana yana wani kashe ido yana lasar harshe sai kace wani tsohon maye 
Duk’ar da kaina k’asa nayi “Ranka ya dad’e ai basai ka tambayeni ba kawai ka d’iba konawa kakeso kabani sauran”
Tashi yayi daga inda yake yadawo kusa dani ya zauna dayake ofis d’in babu kowa aciki dagani sai shi
“Nifa Yan mata ba tukuicin kud’i nake so ba, abinda yafi kud’in mahimmanci nakeso kuma nasan ai baza kiyi mani rowarsa ba ko?” Ya k’arasa maganar tasa tare da dafa kafad’ata  
Tun ina k’okarin zullewa har dai na bada kai bori ya hau, domin dama can a matse nake dama ce kawai ban samu ba, daurewa kawai nakeyi, da Kuma tsammanin nadaina wannan harkar tunda abokin yin baya nan, amma yanzu dana samu dama kawai sai nabada kai bori ya hau. 
Sai dai fa hakanan nadawo batare da biyan buk’atar da ta kaini ba ta kar6o kud’i, saidai na biya buk’ata ta daban wacce badan ita naje ba
Hana rantsuwa ya bani fan hamsin (Kimanin dubu 60 kenan a yanzu) wai nayi kud’in mota kafin jibi nadawo
*****
Haka naita zarya tsakanin unguwarmu da Kuma saffara, amma kullum Hashim ce mani yakeyi naje nadawo ran kaza, bana samun komai daga garesa sai shima dayake samu a guna, Hauwa tayi tayi dani akan nabar masa kud’in tunda so yake yacinye amma nak’i ji, kullum gani nakeyi kamar idan naje zai bani kud’i na.
A haka a haka har muka saba dashi soyayya mai k’arfi ta shiga tsakaninmu, inda na maida saffarar gurin zuwana badan komai ba sai dan mu aikata abinda muka saba aikatawa  da Hashim.
Muna nan muna nan a haka har ya kawo mani shawarar akan yanaso ya kama mani gida kuma a cewarsa zai saka mani dukkan abinda nake buk’ata a gidan, batare da 6ata lokaci ba na amince domin bai rageni da komai ba, yana yi mun dukkan abinda nakeso .
Ranar da naje wa Hauwa da wannan maganar tsabar takaici har kuka tayi, domin bata tsammaci irin wannan rayuwar daga gareni ba 
“Haba Wasila wannan wace irin hanya ce kika d’aukowa kanki wanda kin sani sarai ba hanyar 6ullewa bace, irin wannan abin da kikeyi da Kuma wanda kike shirin yi babu inda zai kaiki sai a dana sani, Wasila bin maza ba wata hanya bace mai 6ullewa inda kinyi tunani, naso ace kin zama kamar ni, wato ki manta da maza ki nemi abinda zaki rufawa kanki asiri ki had’a kayanki ki koma k’asarku, ni sai dai ace mani inada rashin kunya kuma bana ganin girman kowa amma baza’a shedeni da yin zina ba” 
Haka Hauwa ta k’ara ci surutunta amma babu wanda ya shiga kunnena, saima baram-baram da mukayi k’arshe na had’a kayana na tafiyata sunaji suna gani na tafi  tunda babu wanda yake iko dani a cikinsu.
*******

A cikn wannan yanayin ne Farida ta bugo mani waya domin tunatar dani lokacin aurenta ya matso, ban 6oye mata komai ba na fito fili na nuna mata  gaskiya bazan samu damar zuwa ba, saboda a lokacin rayuwar mu muke ci da tsinke ni da Hashim .
*****

Suko a 6angaren iyayena lokaci zuwa lokaci ina tura masu kud’i kuma wadatattu, kuma duk matsalar da ta taso masu ta kud’i sukan fad’a mani na tura masu, bama su kad’ai ba harda sauran yan uwa, sai dai  basu ta6a tambayata a ina nake ko hannun wa nake ba , a’a saima faman shi albarka da sukeyi mani, wani lokacin harma inji Hajar nacewa ai sai yanzu mukasan mun haihu, haihuwa tayi mana rana….
_Ina godiya ga dukkan masu bin littafin Kalubale, masu bugo mani waya da masu turo mani sako ta private, dama wad’anda suka karanta sukayi shuru. idan danbu yayi yawa baya jin mai. Sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa ba, sai dai kawai ince ina godiya Allah ya bar kauna_😘👏
*MAMAN JA’AFAR*

 +966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

              51

Haka rayuwar mu taci gaba da kasancewa cikin farin ciki da annashuwa nida Hashim, har kawo lokacin da na had’u da wani KB d’an group dinmu dayake shima anan jiddah yake
Tun muna lamurranmu a 6oye nida KB har dai nagaji na fara nunawa Hashim cewar yanzufa na gaji dashi don haka sabon jini nake da buk’ata 
Bai wani damu akan lallai sai mun dawo kamar da nida shi ba, saima k’ara nisan tata da yayi, hakan da yayi kuwa ba k’aramin dad’i yayi mun ba, domin yanzu ne zanci karena babu babbaka.
******
Mun d’au tsawon lokaci muna tare, yayinda ya d’auke mani komai tamkar dai yanda Hashim yakeyi mani, dan tunda nake a gidan nan ban ta6a sanin wani abu wai shi kud’in haya ba, kai dawwarin ma yanzu ba kullum nake fita ba, dan ko aike na tashi yi gidanmu KB ne ke tura mani.
Kafin kace kwabo samarin Jiddah sunyo mani ca, inaga hakan ya samo asali ne da yanda suke ganin ina tafiyar da lamurrana. 
Ban fara biye masu ba saida naga hidimar da KB yakeyi mani ta fara ja baya.
Sai a sannan ne nasan na shigo bariki, domin ba k’aramin alheri nake samu ba, K’awaye na kuwa duk na watsar dasu domin nafison tafiyar da lamurrana ni kad’ai.
 *BAYAN SHEKARA 2*
Abubuwa da dama sun faru aciki kuwa harda haihuwarda Farida tayi da Kuma kama Uwani da akayi. 
****
Wasila ce kwance a cikin d’akin ta sai juyi takeyi tarasa abinda yakeyi mata dad’i acikin duniyar nan ta Maliki yaumiddini, zazza6i ciwon kai da yawan kasala duk su suka taru suka kwantar da ita lokaci guda, acikin watanni kad’an duk ta fige ta lalace ta fita hayyacinta tamkar ta dad’e tana yin jinyar.
Maman Mariya ce ta shigo d’akin tare da yin sallama 
Da k’yar nasamu na amsa mata saboda ciwonda ke muk’ur-k’usata 
“Wasila anya kina shan magan-ganun da nake kawo maki kuwa? ” 
Cikin nishi irin na mai jin jiki nace mata “Wallahi Khala inasha dai dai kamar yanda kikace” 
Zama tayi abakin gado kana ta kalleni cikin tausayawa tace 

“Nikam Wasila badan kin kafe cewa bazaki assibitin nan ba ni ina ganin da zuwan naki assibitin zaifi, Kinga koba komai za’a gano ainahin inda matsalar taki take” 
“Babu komai Khala maganin Sedaliya d’in ma idan nasha ina samun sauk’i (Kyamis) 
Mik’ewa tayi gamida saka abayar ta alamun tafiya
“To ai shikenan Wasila tunda dai anyi anyi dake kin k’i zuwa ke kika sani” Ni Kinga tafiyata.
Banji dad’in yanda ta tafi cikin 6acin rai ba, kasancewar tunda larurar nan ta sameni kowa ya juya mani baya, har samarin da nake tak’ama dasu, matar nan ita kad’ai ce bata k’yamace ni ba domin kullum saita kawo mani abincin nan sau uku tare da magani 
Ni kuma bawai assibitin ne banason zuwa ba a’a abinda zai biyo baya a assibitin shi nake tsoro.
*****

 Wasa wasa kullum rashin lafiya sai k’ara yin gaba take ba baya ba, har takaima tashi daga inda nake kwance wahala yakeyi mani, danko Hammam zani sai dai na rarrafa naje.
Yauma kamar kullum Maman Mariya tazo dubani kamar yanda ta saba taga irin halinda nake ciki, dan ko magana wahalar yinta nakeji.
Da gudu ta koma ta nemo mai Lomazin (tasi) sukazo suka cicci6eni ita da Mariya sai assibiti 
Suko yan unguwarmu duk sun fito sai kallonmu sukeyi ana sakani a mota, a cikin yan kallon harda Antitiya itama a gefe.
Duk k’ana nan assibitin k’in kara6armu saboda a cewarsu wai ciwon yayi tsanani sosai, saida Maman Mariya taje tasamo wata mata mai takardar izinin zaman k’asa tazo ta shige mana gaba kana aka k’ar6e mu a wani babban assibiti wato assibitin  hukuma.
Da gudu likitocin sukayo kaina domin bani agajin gaugawa, sai dai suna auna jinina zancen yasha banban, domin banga wata walwala a fuskokinsu ba ko kad’an, saima tambayata da sukayi Wai ina wa’yanda suka kawoki? 
Dana fahimci abinda suke nufi nan take sai dabara ta fad’o mani nace masu wa’yanda suka kawoni a bakin assibitin nan suka ajeni sukai tafiyarsu
Bayan fitarsu ne na lalumo waya acikin zanina da sauri na bugawa su Mariya nace masu suyi sauri su gudu daga assibitin nan domin ina tsammanin sun sameni da H I V ne saboda haka su gudu kawai nidai nasan tawa ta riga ta k’are domin babu makawa allurar guba zasuyi mani kana su turani k’asarmu idan naje bada dad’ewa ba na mutu (su haka tsarinsu yake)
Ina jinsu sunata faman koke koke a waya, nima dana kashe wayar kukan na rushe dashi, ba kukan komai nakeyi ba sai kukan nadamar abubuwanda naita aikatawa a rayuwata, yanzu gashi nan zanyi mummunan k’arshe inaji ina gani….

_Ina godiya ga dukkan masu bin littafin Kalubale, masu bugo mani waya da masu turo mani sako ta private, dama wad’anda suka karanta sukayi shuru. idan danbu yayi yawa baya jin mai. Sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa ba, sai dai kawai ince ina godiya Allah ya bar kauna_😘👏
*MAMAN JA’AFAR*

  +966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: :💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

             52
Kamar kuwa yadda na tsammata, allurar mutuwar sukayi mani kuma inaji ina gani Amman banida ikon hanasu, sai wani maganin boge da suka bani kwaya 2 nasha. 
****

Kwana na d’aya a assibitin suka kwashe ni, basu zame ko ina dani ba sai filin jirgi
Allah sarki! Wannan filin jirgin ne farkon zuwanmu nida Farida muka sauka muna murna gami da zuba k’auyancinmu cikin nishad’i, amma yau gashi nadawo masa ina tare da d’unbin bak’in ciki da Kuma tarin nadama, abaya nazo cikinsa ina dariya, yau kuma gani a cikinsa ina kuka

Allah sarki Farida! Yanzu haka tana can tare da mijinta da Kuma yaronta cikin farin ciki da kwanciyar hankali, niko dana biyewa rud’in K’awaye da Kuma samari yau ga yanda na zama.
****

Tun a filin jirgin nakirasu Hajar na fad’a masu halinda nake ciki, harma da allurar da akayi mani duk ban 6oye masu komai ba, kuma nace masu kome sukeyi su bari suzo filin jirgin su tarbeni, domin ina tsammanin a Kano zamu sauka gashi jikin nawa bashida wani k’arfin da zan iya d’awainiya da kaina har zuwa gida, kumama bayan haka babu ko sisi a jikina dagani sai kayan jikina sai kuma wayata, saida suka tabbatar mani yanzu zasu taho kana na kashe wayar saboda koke kokenda naji suma sun fara, dan ni nariga nayi kukan nawa har nagaji na sadaqar hawayenma sun daina fita.
******

Awarmu 5 a cikin jirgi kana muka dira k’asata najeriya, na barta ina dariya yau gashi na dawo mata ina kuka. 
Ba tare da 6ata lokaci ba na kirasu, ban wani dad’e ina jiransu ba suka bayyana domin dama suna kusa
Allah sarki Affa girma ya fara kamashi, itako Hajar duk ta wani yamutse ta bushe, ko suturar kirkima babu ajikinta.
Tun anan filin jirgi na bugar da wayata muka kar6i kud’inta dubu hamsin domin yin shatar mota daga nan Kano zuwa garinmu.
Har k’ofar gida mai motar ya kaimu saboda jin dad’in kud’in da yasamu
Nan Hajar da Affa suka kakkamani suka shiga cikn gida dani

Koda na cire abayar da ke jikina Hajar kuka ta kamayi Wiwi saboda ganin yanda na rame duk awazu na sun firfito, shima Affa hawaye kawai yake sharewa yana cewa 

“Wasila kiyi hak’uri ki yafe mana, duk mu muka jefaki cikin wannan halin da kike ciki, da munyi hak’uri mun jure talaucin da muke ciki da bamu kaiki wata k’asa neman kud’i ba har hakan ta sameki” 
Nidai kam kasama magana nayi sai binsu da nakeyi da kallo d’aya bayan d’aya  
Hajar ce ta rungumeni “Wasila kome ya faru agareki duk ni naja, ba irin k’okarin nusar dani illar hakan da Affanki baiyi ba amma na kafe nace sai kin tafi, yau gashi tafiyar babu abinda ta amfanemu dashi sai tarin nadama da Kuma dana sani” 
Durk’usawa tayi gabana guiwa a k’asa “Wasila na tuba Wasila ki yafe mani, insha Allahu na d’auki darasi daga kanki, ko mak’iyina naji yana niyar kai D’ansa wata k’asa da niyar yin neman kud’i zan hana sa bare kuma ni nayi k’okarin aikata hakan da kaina” 
Ban iya furta mata komai ba sai rungumeta da nayi na fashe da wani matsanancin kuka, babu abinda nake furtawa sai 
“Na yafe maku iyayena, na yafe maku, Allah yasa hakan ya zama izina gareku da Kuma sauran iyaye masu irin halinku” 
Shiko Affa yana gefe sai sharar k’walla yakeyi domin ya kasa magana
*********
Madadin a dinga zuwa gidanmu barka ko ince murna da Kuma sannu da zuwa ana rarraba tsaraba ga kowa, sai ya zamana saidai azo mana jaje gami da d’aukar rahoto 
*****

Mutane da dama tofin ala tsine sukeyiwa iyayena, wasu ko cewa sukeyi ai dama munsan a rina wai ansaci zanin mahaukaciya, yainda wasu kuma lamarin nawa tausayi yake basu.
*******
Allahu Akbar! ana shirye-shiryen kai Wasila assibiti ne tace ga garinku nan 
Wayyo duniya Allah baya barin wani dan wani yaji dad’i
Affan Wasila yasha kuka tamkar ransa zai fita, ba kuma kukan komai yakeyi ba sai kukan nadamar halinda suka jefa tilon D’iyarsu, mai yi masu biyayya da Kuma son faranta masu a koda yaushe
Itako Hajar tsabar kid’ima har kusan zarewa tayi, da k’yar aka samu ta dawo dai dai da addu’a da komai, abu d’aya ne yakeyi mata dad’i acikin cikin ranta idan ta tuna, wato cikawa da Wasila tayi da kalmar *LA’ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADUR RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM* 
Tammat bi hamdullah
_Anan na kawo k’arshen wannan d’an takaitaccen littafin nawa mai suna_ *Kalubale*

_Abinda nayi na dai dai ina rokon Allah ya bani ladarsa, wanda kuma nayi kuskure ina neman yafiye a gurin Ubangiji_
_Allah yasa mu amfana da dunbin darussan da suke ciki, ya kuma bamu ikon kiyaye Kalubalen da yake ciki_
_Zanyi amfani da wannan damar na k’ara jawo hankalin iyaye akan su rik’e amanar da Allah ya basu, domin y’ay’anku amana ce agareku, sannan kiwo ne aka baku kuma ranar gobe k’iyama Allah sai ya tambayeku akan yanda kuka tafiyar da wannan kiwo da ya baku, saboda haka mu kiyaye domin mu tunkari Ubangiji da Kyakkyawar hujja a gobe k’iyama_

*Ina mika godiyata da yabo da kuma jinjina gareki Malamata*
_SADY JEGAL_
_Saboda da taimakonki da shawarwarinki na fara wannan littafin har gashi Allah yasa na kammalasa lafiya_

_Nagode sosai Allah ya kara maki basira da Kuma daukaka sannan ya dawwamar da farin ciki mai dorewa cikin Familynki gaba d’aya_

*Dole na gode maku* 
_Domin ku kuka dage wajen bani kwarin guiwa har na kammala wannan littafin_
_Asiya (Maman Ihsan kt )_

_Ummi Adamu Bauchi_

_Khadija Katuru KT_

_Nagode Allah ya bar kauna a tsakaninmu_

*K’awayena*
_Zainab Ibrahim KT_

_Zainab Basiru KT_

_Zainab (Yaya) KT_

_Jamila Abba Imam KT_

_Hauwa’u Abdulqadir KT_

_Hamida & Lubabatu Isah KT_

_Asma’u Abdurrahman KT_

_Aishatu Isah KT_

_Badiyyah Aduwa KT_ 

_Maryam Lawal KT_
_Da sauran wadanda ban ambata ba, sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa duka ba amma duk kuna raina_
_Alkhairin Allah ya kai maku a duk inda kuke_
_Zulaihat Abubakar bata manta daku ba_

*Mak’wabtana*
_Ummin Usman_

_Umma Salma_

_Matar Sudani_

_Aishan Ali_ 

_Salamatu Gatafa_

_Suhairat Bawadi_

_Khaltum Riyadh_
_Zumuncinmu mai d’orewa ne tun daga nan Saudia har zuwa gida Nigeria insha Allahu_
*Sadaukarwar takice*
_Rahinatu Dikko Kankia Local government Ktn_

_Munyi nisa amma zuciyoyinmu suna tare_

_Allah ya tsare mani ke ya Kuma kare mani ke sana ya dauwamar da farin ciki a rayuwarki, ya Kuma raya mana Ameera da Haidar kana ya kara dankon so da kauna a tsakaninki da Momcy_

_Ina godiya ga dukkan masu bin littafin Kalubale tun daga farko har zuwa k’arshe, masu bugo mani waya da masu turo mani sako ta private, dama wad’anda suka karanta sukayi shuru. idan danbu yayi yawa baya jin mai. Sunayen sunada yawa bazasu iya ambatuwa ba, sai dai kawai ince ina godiya Allah ya bar kauna a tsakaninmu sai kuma mun had’u a littafi na na gaba wato IDAN KUNNE YAJI_..
*NICE TAKU*

*MAMAN JA’AFAR*

+966592551785

*D’AND’ANO*
🌻IDAN KUNNE YAJI🌻
Cire hannunsa yayi daga cikin kwanon tuwon, ransa a 6ace da Kuma nuna k’osawa akan magan-ganun Murjanatu yace
“Waini Murjanatu ke wane irin kunne ne Allah yayi maki wanda baya jin magana ko kad’an? Haba! kunne sai kace kunnen k’ashi, tun yaushe nake fad’a maki bazaki tafi SUDAN d’in nan ba,  bazaki tafi SUDAN d’in nan ba amma kin k’i ji, kullum sai kinzo mani da zancen, haba dan Allah ya isheni haka ki sakar mani mara nayi fitsari” 
Cike da tsiwa da rashin kunya Murjanatu take fice a d’akin, tana tafiya tana mayarwa da Haro amsa 
“Ai dama ni nasan bak’in ciki akeyi mani akan zan tafi nema nayi azziki, kullum akayi magana sai kace me na rageki dashi? miye ba nayi maki? to me kakeyi mani d’in iye? tafiya SUDAN dai tamkar nayita nagama ne sai dai idan mutuwa zakayi ka mutu…
Daga cikin d’akin Haro yace “to kuwa indai kika sake kika tafi bada yawuna ba wallahi, kuma ki tabbatar da kin ajiye min D’ana kafin ki tafi gantalinki, marar godiyar Allah kawai” Yana ida fad’ar haka yayi ficewarsa daga gidan gaba d’aya, abincin da Haro bai k’arasa ci ba kenan
Wata muguwar harara ta bisa da ita “Tafiya SUDAN kam Haruna sai nayita, da ka yarda da karka yarda duk uwarsu d’aya ubansu d’aya ni a gurina, inkaga damama in natafi ka biyoni da takardar saki uku matsalara kace kuma kai ta shafa, Kalleni sama da k’asa, tsaye da kyau zaune da kyau miji  goma ba uba goma bane, inma ka sakeni nasan dai miji d’aya tal na aure Allah ba zai hanani ba……
*IDAN KUNNE YAJI…* 

       Jiki ya tsira 

*Coming soon*

+966592551785

[3/4, 7:16 PM] ‪+966 59 255 1785‬: 💐💐💐💐💐

   💐💐💐💐

      💐💐💐

          💐💐

              💐

     К’дlц. ВдlЕ

            

             Ид
МДМДИ JдFдЯ

 

                8

***Nidai kamar yanda kasani sunana Farida , inada kanne 2 mace 1 namiji 1 wato Hasiya da ‘Dan Ladi 

Asalinmu mu yan garin BUDUWA ne,  buduwa wani dan ‘karamin ‘kauye ne dake ‘karkashin  NANGERE LOCAL GOVERNMENT  

Nangere shima ‘kauye ne amma ba sosai ba domin FOTISKUM tafisa zama birni sosai 

Duk dai acikin jahar YOBE 
Nataso ne a hannun mamata kasancewar sun rabu da babana tun ina ‘karama sai tayi wani auren ta tafi dani can gidan sabon mijin nata 

Saidai mijin nata yanada wata matar bayan mamar tawa hardama yaransu 5 

Itama mamar tawa ta haifi yara 2 a gidan wato Hassan da Husaina 

Gidansu gidan yawa ne domin yayun mijin nata da ‘kannensa duk anan ciki suke tare da iyalansu iyalansu,  saidai kowa da ‘bangarensa 

Itama mahaifiyarsu anan take zaune da nata ‘bangaren kasancewar  babansu ya dade da rasuwa 

Anan na taso babu yabo kuma babu fallasa domin mijin mamata ya rikeni tamkar yar da ya haifa 
Saidai shima talaka ne tamkar mahaifina bama samun abubuwan bu’katun yau da kullum  
Mamata surfe takeyi da kuma wankau 
To ke kuma ya akayi kikazo nan ‘kasar ?” ya katse Farida gami da jefo mata yambaya
Rakiya kawar mamana ce ita tabawa mamana shawarar kawoni nan domin neman kudi harma tace mata idan ta amince zata hadata da wata ‘kawarta Harira wacce take zaune anan Saudia 
Bata wani ‘bata lokaci ba gurin amincewa domin muna cikin wani hali na rashin abubuwan more rayuwa , wanda kusan halin rashin nema ya raba mamana da babana nake tsammani 
Saboda mamana bata da tawakkali na rashi a yanda na fahimta  

Da wannan shawarar Rakiya tayi mana hanyar Harira mai kawo mutane nan ‘kasar tana kaisu gurin aiki , nima har aka kawo ni nan gami da bani lambarta na taho da ita 

Itacema lambar da na baka ka kira mani ‘dazu 
To amma an nemi izinin babanki kuwa kafin kizo?” Ya katseta gami da jeho mata wannan tambayar” 

A’a gaskiya bai san natafi ba saboda mamata cewa tayi idan aka fa’da masa bazai amince ba ” 
“Ke kuma shekarunki nawa?”
Shekaruna 15  
Wasila kina zuwa makarantar boko ko ta arabi?” Ya tambaya gami da kallo guna ”

A’a bana zuwa makarantar boko amma ina zuwa ta allo ta gidan malam Habu ”
Ke kumafa Farida?” 
Nima dai bana zuwa bokon sai ta allo da nake zuwa bayan nadawo daga tallar kayan miya wanda DUDU yake dora mani, matar ‘kanin mijin mamata 
Rufe bakinta keda wuya mukaji ana ‘kwan’kwasa ‘kofa 

Yusuf ne ya bu’de ‘kofar gami da matsawa gefe guda ta shigo 

Tsalle nayi ina murna naje na rungumeta  ”  

itama murnar ce fal a fuskarta  ta ri’ke hannuna muka ida shugowa dakin muka zauna 
A sannan ne ta lura da Yusuf da Kuma Farida….

DAGA TAKU 

MAMAN JA’FAR

UBAN NE KO Y’AR? 11-20

​[2/27, 6:09 PM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{11}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

          Da tambaya da komai ta samu aka kaita har fad’ar mai martaba sarki anan garin Sokoto d’in har aka yi mata iso gurinshi, bayan taje sun gaisa ne ta kwashe komai akan matsalarta da Mahaifinta ta gaya mai, nan fadar aka yita jinjina wannan abin.
Mai martaba ya bud’e bakinshi yace’ “kin tabbatar duk maganar da kika kawo gabanmu babu k’arya ko k’ari a cikinta?”.
“Wallahi ranka ya dad’e babu abinda na yi k’ari a cikin wannan labarin sai ma abinda na rage daga ciki, saboda Uba kowanne iri ne Uba ne, amma bazan iya auran mutumen da yake son had’ani auratayya dashi ba, akan kalamanshi masu muni zuwa gareni”.
“To shikenan yanzu ki bada address na unguwar da kuka sauka, zan bada fadawana da sak’on takarda aje da ita da kuma ke da Mahaifiyarki zuwa ga Sarkin Jega”.
Da hakan ta bada address d’in gidan Kakanta sannan ta shiga napep ta wuce gida, har ta shiga gidan bata gayawa kowa cewa ga inda taje ba har Mamarta, inda ta baje ta yita sha’aninta tamkar babu wata damuwa tattare da ita.
****
6angaren Malam Nura kuwa kullum Nera na Sonka ya tunkareshi da maganar aure zai ce mai kawai yaje zuwa shirye-shiryen aure, duk da tsorace yake da rashin sanin takamemen ina Fateeha ta shiga, kuma gashi yayi alk’awari ga rayuwarshi cewa ko nan da k’ofar gida bazai neme taba.
Wasu irin mak’udan kud’i kawai yake zube mai domin k’ara tunzurashi domin ya bashi Fateeha, saboda hango cewa kud’in da yake badawa na k’ara ingiza Mahaifin nata.
****
Gidan ya shigo ga alama jikinshi a sanyaye yake sai dai kuma ya kasa cewa komai sai dai d’inbin tunani dake damunshi na in har Fateeha bata dawo ba ya zai k’arasawa da matsalar Nera na Sonka, shi ba ma wannan yafi damunshi ba irin gidan da yace zai canja mai da kuma kujerarshi ta Hajji da yake ganin duk zai tashi a tutar babu ne in har wannan auren bai tabbata ba.
“Malam duk fa wani dogon tunani bai ganka ba, mafita d’aya kasa hannu a neman Yarinyar nan, yau ace kusan kwana goma kenan Yarinya bata hannunka amma ka kasa bincikawa ko za ka gano inda take, ga kud’in wannan Alhajin da kake kar6a a madadin za ka aura mai Y’arka”, maganarta ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula.
“Don Allah rufa min baki kinzo kin dame ni da wani dogon sharhi naki, kinsan da za ta fice daga gidan nan neman izni ta yi ko kuma aikenta nayi ballantana inga ta jima bata dawo ba inje nemanta, in har kinga naje nemanta to ba d’an halak nake ga iyayena ba, kuma ki 6acemin dagani kinzo kin tsayamin a ka”.
Ganin in har ta matsa zai iya jibgarta yasa taja jiki tabar gurin had’e da damuwar tsattsauran ra’ayi irin na Malam.
****
“Gaskiya kar muyi sanya ya kamata mu tarar da Baba k’arami mu gaya mai ko akwai wani abu da zai yi akai, saboda ni fa ina jin tsoro kar Mahaifin Yarinyar nan ya gano inda take ya yi mata aure da wancan mutumen”.
“Sadeek nima kaina ina tsoron hakan, sai dai na fiso in jira har Baba yadawo in shawarceshi kan hakan, duk da Innarmu ma ta goyi baya na da hakan, insha Allah ba wani abu da zai faru, kuma kar ka manta da cewa rabon kwad’o bayya hawa sama”.
Hakan dai suka ta tsara abubuwa tamkar way’anda akace an basu Fateehar jibi ne aure.
****
Misalin k’arfe 11:00 suna zaune filin gida suna tsintar shinkafar da za’a yi girkin rana da ita sai ga Yaro ya yi sallama yace ana yiwa maigida sallama, dai-dai Malam Hamisu ya fito daga kewaye da buta rik’e a hannunshi.
Butar ce ya ajiye ya mara wa Yaron baya suka fita tare daga gidan. Ganin dogarawan Sarki a k’ofar gidanshi ba k’aramar razanashi ya yi ba, tunani ya shiga yi na wanne laifi ya yi da zai ga fadawa k’ofar gidanshi.
Bai k’arasa tunanin ba har ya iso gab dasu, durk’usawa ya yi ya kwashi gaisuwa tamkar mai gayar da Sarkin gaba d’aya, nan suka gaisa had’e da Isar da sak’on mai Martaba, cikin mamaki ya koma gidan yana salallami yana fad’awa su Mama Hajara abinda Fateeha ta aikata.
Nan suma mamaki ya lullu6esu kowa ya yi zurum yana kallonta itako ko a jikinta. “Yanzu dai ku tashi ku kimtsa in biku muje can d’in inga ya abin zai kasance, kuma don Allah kuyi sauri kunga suna daga waje suna jiranmu”.
Cikin mintunan da basu haura 7 zuwa 10 ba suka gama shirin nasu jiki na rawa suka fice daga gidan. Motar da fadawan suka zo da ita suka shiga kowa na nashi sak’e-sak’en a zuciya da tunanin ya wannan lamarin zai kasance.
****
Kamar yanda suka tattauna hakan suka tunkari Baba da maganar saboda ya dawo da tafiyar da yayi, wanda shima ya yi na’am da wannan shawara tasu.
“Yanzu ku bari zuwa gobe zan tunkari Malam Isa da Malam Sani sai mu tattauna yanda abin zai kasance na Kakan Yarinyar zamu tunkara da maganar ko kuma Y’an uwan Mahaifinta”. Da hakan suka yi godiya suka fice.

© *SDY JEGAL*💝

[2/28, 6:20 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{12}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

         Da shigowarsu garin Jega basu zarce ko ina ba sai gidan Sarkin Jega, bayan an gaisa ne fadawan Sarkin Sokoto suka gabatar da takardar da aka aikosu da ita, nan ya bud’e ya karanta ya ga sak’on wanda mamaki ne ya mamaye ranshi na wannan abin, nan ya rubuta nashi sak’on ya sallame su.
Bayan ficewarsu ne ya mayar da dubanshi ga Malam Hamisu had’e da neman k’arin bayani akan wannan abin. Fateeha ya nuna had’e da ba ta umurnin ta yima mai Martaba Sarkin Jega bayanin abinda ke faruwa, nan take ta zayyano mai komai na abinda ke faruwa.
Bud’ar bakinshi yace’ “to ke me yasa ba zaki hak’ura kibi za6in Mahaifinki ba?”.
“Ranka ya dad’e akwai kalamai masu muni da yake furtawa zuwa gare ni way’anda suka sa bazan iya aurenshi ba gaskiya, saboda duk mutumen da ke sonka da zuciya d’aya kuma so na hak’ik’a ba zai furta sai ya wulak’anta kaba, akan hakan nake ganin babu alkhairi a zamantakewata dashi, shiyasa na za6i na kawo maganar gurinku ko in kuka saka baki ya amince ya janye maganar”.
Bayan ya gama saurarenta ne ya tambayi address na gidansu suka gaya mai, nan ya kira d’aya daga cikin Fadawanshi ya tura shi domin ya kira Mahaifinta wato Malam Nura. Cikin mintunanda basu haura goma ba sai gasu sun zo tare.
Da isowarshi ya ci karo da Fateeha nan take ya tamke fuskarshi tamkar bai ta6a murmushi ba, kaf annurinta ya gushe.
Zama ya yi suka gaisa da Sarki sannan ya juya ya gaida Sirikinshi wato Mahaifin Hajara sama-sama tamkar mai ciwon hak’ori.
Nan dai Sarki ya yi gyaran murya ya furta’ “miye matsala tsakaninka da Y’arka akan neman aurenta?”.
Sai da ya watsawa Uwar da Y’ar harara alamun zamu had’u daku ne sannan ya furta’ “ranka ya dad’e Miji na yi mata tak’i aminta dashi, kuma na ga ko shari’ar musulunci ta bamu dama da mu za6ama yaranmu Mazaje nagari a farkon aurensu, shiyasa ta kawo wani da bai yimin ba niko nace bazan aura mata shi ba”.
Fateeha aka nema da tayi na ta bayanin, bayan tayi ta gama Sarki ya Kai dubanshi zuwa gare shi, “abu d’aya nake so ka fahimta a halinda ake ciki yanzu an daina auran dole, ko ba hakan ba ya dace ka za6awa Y’arka Miji nagari wanda zata samu kwanciyar hankali a gidan aurenta kuma naku ya kwanta”.
“Saboda haka ga sak’o daga Sarkin musulmi tun daga Sokoto ya aiko kan cewa ayi bincike in an tabbatar da abinda Yarinya ta furta gaskiya ne to a zauna dakai a gaya ma in har wanda take so baida wani abin k’i to ka aura mata shi”.
“Saboda haka ka janye maganar aurenta da za6inka ka bata nata za6i, don kai kanka baka kawo illar wanda take so ba”.
Zurum ya yi tamkar ruwa ya ci shi yana nazari a ranshi, daga hakan ya bashi amsar komai ya wuce za’ayi yanda suke so d’in, nan ya cika babbar rigarshi da iska ya fice daga gurin.
“Gaskiya ranka ya dad’e akwai matsala, ba fa lallai ne ace ya aminta da maganar da kuka fad’a ba in har kayi la’akari da yanda yabar gurin nan, yanzu zamu iya komawa gida wata matsalar ta taso ta daban”, Mama ce take furta hakan ganin yanda yabar gurin ko kallo basu isheshi ba.
“Yanzu ku tashi kuje gidan duk abinda ya biyo baya ku dawo nan ku gayamin”. Hakan yasa suka tashi da d’an k’warin gwuiwarsu suka nufi gida shi ko Malam Hamisu ya tari mota ya koma garinsu.
*****
Kamar yanda Mahaifin Mukhtasheem ya yi alk’awari hakan ya shirya mutanenshi aka je gun Kakan Fateeha neman aure, kuma ya yi na’am da cewa Yaro ya had’o sadakinshi ya kawo za’a aura mashi Yarinya.
Bayan sun dawo ne suka fad’i sak’on Mahaifinshi bai yi garaje ba ya kira su ya yi musu bayani kan abinda ake ciki, nan take ya cire dubu hamsin ya basuwa a matsayin sadaki sauran abubuwa zai yi su daga baya.
Hakan suka koma suka damk’a ma Kakanta kud’in, bayan ya kar6a ne ya basu tabbacin zai zauna da sauran Yaranshi duk yanda suka tsaida ranar aure za’a nemesu a sanarda su, da hakan suka fice farin ciki fal a ransu.
****
Har suka kai k’ofar gidan cikin fargaba suke, saboda sanin yanayinshi ya nuna ba abinda yayi k’asa na k’udirinshi akan aura wa Fateeha Nera na Sonka, hakan dai suka shiga gidan jiki a sanyaye.
Da murnar Mummy tazo ta tarye su Suka gaisa, nan aka baje ana hira suna mayarda zance. Tamkar guguwa hakan ya shigo gidan da wani sabon (Ankwa) a hannunshi, idon Fateeha na kai gare shi ta 6alla aguje tamkar walk’iya tabar gidan, da saurinshi ya bita amma ina ta riga tabar gidan, nan ta d’ale mashin sai gidan Sarki.
Bayan ta kora mai abinda ke faruwa ya kira Sarki da kanshi ya gaya mai, nombar alk’ali Farouk ya buk’aci ya turo mai, nan take ya kira shi ya gaya mai case d’in kuma ya buk’aci da yayi duk abinda ya dace, hakan sarki ya bata umurnin ta koma gida duk yanda ake ciki za’a neme su.
Tana fita daga gidan ta ji zuciyarta bata aminta da taje gida ba, sanin gidan alk’ali Farouk sananne ne a garin ya sa ta zarce sai gidanshi har sai an nemi mafita.

© *SDY JEGAL*💝

[2/28, 2:47 PM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{13}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

             Gidan ya dawo yana haki saboda rashin kamo Fateeha da bai samu yi ba, da harara ya bi su Mama sannan ya tarkata (Ankwa) da ya shigo dashi ya zarce d’akinshi, bayan ya ajiye sannan ya fice ya bar gidan.
“Ni dama nasan da ganin yanda Sarki ya yi mai magana ya amsa sannan ya fice tamkar guguwa nasan cewa wallahi akwai matsala, kuma ba wai ya sauko bane ya dai amsa ne kawai ya fice”.
“Wannan bak’in cikin dame ya yi kama, abu yak’i ci yak’i cinyewa, indai ba so yake Yarinyar nan ta shiga Uwa duniya ba ya dace ace ya barta haka nan tunda har manyan gari suka saka baki ya aura mata za6inta d’in kowa ya huta”, tana kai k’arshen maganar sai hawaye sha a idonta. Mummy ce ta rik’a lallashinta da bata baki har tana had’awa da cewa.
“Abu mafi sauk’i Yaya mu mik’a wannan lamarin gurin ubangiji, muyi ta addu’a Allah ya kawo sassauci a cikin wannan abin, domin shine kad’ai zai kawo muna mafita”.
“Habiba addu’a kinsan gwargwado ina yi, kema kuma nasan kina tayani, ballantana ita wannan Yarinyar da abin ya fad’a kanta, lokacinda muna Sokoto har sallar dare take tashi kullum daren Allah”.
“Na dai yarda da wannan kan k’addarar Fateeha ce, hakan kuma zan k’ara dagewa da addu’a daya kawo mata mafita ta alkhairi”.
****
Da zuwanta gidan ta tarar da alk’ali Farouk baya nan, amma tsoron sanin in ta koma gida komai na iya faruwa ya sa ta yi zamanta gidan kan cewa sai ya shigo ta ji wanne mataki zai d’auka akai.
Bayan ya shigo ne yayi duk wasu al’adunshi daya saba sannan ya nemi da ashigo da ita d’akin nashi, bayan ta gaida shine ta shiga labarta mai abinda ya faru tun daga farkonshi har zuwa yanzun da take gabanshi a zaune.
Bayan ta gama bashi labarin ne ya jinjina faruwar abin sosai, kuma ya yi mamaki da samun mutum mai kafiya irin hakan.
“Yanzu abinda za’ayi tunda munyi magana da Sarkin Sokoto kanshi to za’a shigar da k’ara kotu, kuma insha Allah za mu tsaya maki”.
Nan take ta razana, ta yi nazari a ranta kan duk yanda abin ya yi tsamari ba za ta aminta a gurfanar da Ubanta kotu a kanta ba, nan ta furta “ni dai Baba in son samu ne ka kirashi ku zauna dashi kuyi magana ko Allah zai sa ya fahimci inda ka dosa, amma bazan so ace an shiga kotu da Babana ba, saboda wannan wata fallasa ce ta daban”.
“Da zai amince da zaman sulhu da basu yi magana da Sarki ba kuma yasa k’afa ya shure batunshi har wannan abin ya biyo baya ba”.
Kuka ta rik’a yi da neman alfarma kan don Allah kar a shiga kotu da maganar, hakan ya sa matarshi dake zaune gurin ta lallasheta sannan ta bata umurnin ta koma d’aki gurin Yara ta zauna kamin tazo.
Bayan ta fice ne matar ta mayarda hankali ga maigidanta had’e da bashi shawarar kan ya dubi alfarmar da Yarinyar ta nema ya yi mata hakan, nan dai ta rik’a nuna mai irin illar hakan da Fateeha ke gudu, da hakan ya amince kan zai nemi Mahaifin nata domin zaman sulhu.
****
6angaren Nera na Sonka kuwa da yaji duk abubuwanda ke faruwa na dangane da auren kuma har magana ta kai manyan k’asa da manyan gari ana neman kai maganar kotu, hakan yasa ya nemi gaban Mahaifinta ya nuna mai cewa shi fa in don ta shine to gaskiya ya hak’ura ya janye maganar, kuma duk wani abu daya bada to ya yafe baya buk’atar ko sisi a dawo mai dasu.
Hakan ba k’aramin bak’in ciki ya saka shi ba, saboda Fateeha ta yi mai silar rasa duk wani buri nashi akan aurenta da Nera na Sonka, da hakan ya k’ara d’amarar ganin abinda ya turewa buzu nad’i.
****
Kamar yanda Fateeha ta nema hakan Alk’ali ya yi ya nemi Mahaifinta har gidanshi suka shiga tattaunawa akai, sai dai ga alama har yanzu ba alamun nasara akai.
“Ka saurare ni muyi magana ta fahimta tsakaninmu, saboda ma kaci darajar Yarinyarka da ta buk’aci alfarmar bata son mu shiga kotu dakai sai dai a kiraka ayi sulhu, hakan yasa na neme ka”.
“Abu na farko da nake so na tambayeka shine, Yaronda ke son Yarinyar ka na da wata illah ne, yana shaye-shaye, yana sata, yana neman Mata ne, bai da Sana’a?”, hakan ya jero mai duk wad’annan tambayoyin.
Amsa ya bashi da cewa’ “ko d’aya, sai dai banda ra’ayin bashi Y’ata ne saboda na yi mata miji, kuma shi nake da ra’ayin ta aura”.
“Na ji ka yi mata miji, amma kana sane da cewa akwai wasu kalmomi masu aibu da in yazo zance gurinta yake furta mata su ko?”.
“Wannan duk k’aryarta ce saboda bata son aurenshi ya sa ta yi mai k’azafi, amma tsakaninta dashi sai alkhairi”.
“Ba kada tabbacin k’arya ne tunda ba tare dakai ake zuwa zancen ba, amma yanzu abinda nake so da kai ka saka min ranar da za’a yi auren Yarinyar nan da Mukhtasheem”.
Zurum ya yi tamkar badashi yake magana ba, sai da ya maimaita maganar sannan ya furta mai cewa ya saka sati uku masu zuwa, daga hakan ya fice daga gidan.
Nan Alk’ali Farouk ya kira matarshi yana gaya mata yanda suka yi da Baban Fateeha, sannan yace ta gaya mata ankai k’arshe da ikon Allah ta tashi tabi Mahaifinta gida.

© *SDY JEGAL*💝

[2/28, 8:37 PM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{14}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

         D’akin ta koma ta zaunar da ita had’e da gaya mata yanda aka yi tsakanin Babanta da Alk’ali, “sanadiyyar hakan ne ya sa yace ki shirya ki koma gida sai ayi shirye-shiryen aure”.
Fuska ta had’e tamkar za tayi kuka wanda alamu sun nuna tana jin tsoro ko fargabar komawa gidan ne, “Mama ni dai in son samu ne kuma ban takura kuba don Allah ku barni nan har zuwa lokacin auren, saboda ina tsoron had’uwata da Baba yanzu”.
“Ahhh karki damu, in har kina da ra’ayin zama nan d’in me zai hana, sai ki samu lokaci Hafsat ta rakaki ki d’ebo kayanki”. Nan suka kai k’arshen magana Mama ta wuce kitchen.
*****
Duk labarin abinda ya faru ya je kunnen Mukhtasheem har zaman Fateeha gidan Alk’ali Farouk, sai dai yanzu ba wai ita yake son gani ba, shi dai babban burinshi yaji cewa komai yakai k’arshe to anan hankalinshi zai kwanta.
 Gashi anyi magana da Kakanta har sadaki sun bada amma ba wani motsi har yanzu.
Sak’on kiran Alk’ali ne ya risk’eshi kan cewa yazo yana nemanshi, hakan suka kwashi jiki shi da Sadeek suka tarar dashi. Bayan sun gaisa ne ya koro musu cewa yanzu maganar aurensu ta dawo hannunshi, saboda haka suje zuwa shiri kuma su kawo sadaki.
“Ranka ya dad’e sadaki dama mun bada yana hannun Kakanta yanzu kusan kwana biyar kenan, dama lokacin munga komai ya ca6e ne shiyasa iyaye suka yanke shawarar tunkarar Kakan Yarinyar, kuma cikin yardar Ubangiji ya amince da buk’atarmu har ya furta za’a nememu, to sai dai shiru muke ji har yanzu”.
“Ah to abu yazo da sauk’i tunda har sadaki kun bada, yanzu to kuje zuwa shiri nan da sati uku d’aurin aure saboda uzirin da Mahaifin Yarinyar ya kawo na shirye-shirye”.
Nan suka yi mai godiya sosai sannan suka fice, kowannensu ka kalla lokacin zaka san cewa yana cikin farin ciki marar misaltuwa.
****
Innarmu ce suka saka gaba suna bata labarin yanda suka yi da dattijo mai kamala wato Alk’ali Farouk.
Innarmu tace’ “to kagani yanzu duk irin ta6argazar da akayi gashi komai yazo k’arshe, da tun farko ka janye maganar da baka cimma dad’i ba, saboda haka ku hau shiri akai, Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alkhairi, Allah yasa k’arshen fitintinun kenan”.
“Sannan kaima ina mai baka shawara da ka rik’e yarinyar mutane amana, kaga dai irin jajircewa da kuma sadaukarwa da tayi akanka, don haka don Allah kar ka bamu kunya, ka zamo d’an halak a gareta”.
“Haba innarmu karki damu, Yarinyar da ban Sonta da ina mai tabbatar maki da cewa da yanzu na barta, ko a tarihin aure ban ta6a cin karo da irin wannan ba sai a kaina, bayan wahalhalunda aka sha kuma in 6ullo da wani abu na daban ai da ban cika d’an halak ba”.
Sadeek ne ya kar6e da cewa’ “Innarmu baki Sani ba fa kusan kullum muka kwanta bacci sai ya yi mafalkin wannan auren, ai ko yanzu kinga na huta yau zanyi baccin dad’in babu takura babu sambatu”, ya k’arasa maganar yana dariya had’e da kallon Mukhtasheem k’asa-k’asa.
Baba ne ya shigo da sallamarshi, bayan sun gaidashi yakai dubanshi zuwa garesu yace’ “to su rasa kunya sai a tashi a wuce, ke ko kin saki baki kina sauraren shirmensu”.
Hakan yasa suka fahimci Baba yaji abinda suke fad’a sum-sum suka shuri takalmansu suna dariya suka fice.
Abincinshi ta kawo mai da ruwa sannan ta zauna gefen tabarmar da ta shimfid’a mai ta kai dubanta zuwa gareshi sannan tace’ “Maigida fa da ikon Ubangiji komai ya wuce na matsalar auren Yaron nan, saboda yanzu haka daga gurin alk’ali suke”. Nan dai ta kwashe yanda su Sadeek suka gaya mata ta gaya mai.
Walwalar fuskarshi ta nuna nashi farin cikin shima, saboda kai k’arshen matsalar shima nashi hankali zai kwanta.
****
Yanda kasan guguwa ta taso daga gabas haka ya shigo gidan, sai hauri yake da duk kayanda yaci karo dasu a filin gidan. Su Mama ne suka fito suna kallon ikon Allah amma babu mai bakin magana cikinsu. “Sai ku shirya maganar aure nan da sati uku k’ila tunda Alk’ali ya matsamin, amma ina mai tabbatar muku ku gaya ma Fateeha kar ta kuskura k’afarta ta tako gidan nan, in ba hakan ba ko a hanya muka had’u da ita na lahira sai ya fita jin dad’i”. Daga hakan ya ajiye cefanen da yazo dasu yabar gidan.
Mama ce ta zabga uban tagumi ta rasa bakin magana sai zuciyarta dake yi mata zafi, ji take yi tamkar ta nemi Fateeha ta lallasheta kan ta hak’ura da wannan auren, sai dai babban abinda ke damunta bai wuce muggan kalamun Nera na Sonka ba akan Y’arta, ita ba don hakan ba da tuni tasaka Fateeha ta hak’ura ta aureshi, amma hakan yasa take bin duk abinda ake yi da ido saboda gudun gur6ata rayuwar Y’arta.
“Yaya ai ina ga wannan abin farin ciki ne a gare mu, saboda kawowar k’arshen wannan matsalar, gaskiya na yiwa Fateeha murna, Allah ya sanya alkhairi”.
“Ba wai banyi murna da hakan bane, tsoro d’aya kalamin Malam a kanta, kin sanshi kin san halinshi da kafiya irin tashi, zai iya rik’on Fateeha da wannan abin har k’arshen rayuwarshi, shiyasa kika ga jikina yayi sanyi wallahi”.
“Yaya insha Allah zai sauko nan gaba da ikon Ubangiji, kuma ni gaskiya k’ara hakan da a aura mata mutumen da ke fatar ganin bayan farin cikinta”. Hakan dai suka kasance masu sak’a da warwara a tsakaninsu.

© *SDY JEGAL*💝

[3/1, 8:37 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{15}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ _Wannan page nakune Batul Mamman Fan’s, nagode da k’aunarku da kuma kulawarku a gareni, Allah yabar zumunci, luv y’all_}

          Yaro ne ya shigo yana rafka sallama had’e da cewa ana sallama da Fateeha a waje, mamakine ya bayyana a fuskokin su Mama saboda sun San da wuya Mukhtasheem yazo nemanta gidan tunda yasan bata nan, kuma Nera na sonka sun san ya janye maganar ya hak’ura.
Nan dai suka cewa yaron yaje ya tambayo wake nemanta, bayan yaje ya dawo ne yace masu wai Kabiru ne daga k’auyen Raha. Razana ce ta bayyana a fuskokinsu had’e da kallon juna kowanne da abinda yake sak’awa a ranshi.
“Me zan cewa Mutumen?, saboda Inna ce ta aikeni siyen magi bakin titi”. Maganar Yaron ce ta dawo dasu hayyacinsu. Mummy ce tace mai don Allah ya shiga gidan Mal Issuhu ya kira masu Hamza yaje ya kira Malam.
“Ba matsala bara na biya ta gurinshi na gaya mai sannan na wuce siyen magin”. Daga hakan ya fice ya barsu nan sake da baki.
“To wai ni Yaya miye Mafita akan zuwan Kabiru ne?, ana murnar matsala tazo k’arshe ashe akwai wani abin tafe”.
“Ni fa gurin nan da kike ganina duk jikina yayi sanyi, sai dai mu jira zuwan Mal mugani wane hukunci zai d’auka akai”.
****
Zaune suke ita da Hafsat d’iyar Alk’ali suna hira tana bata labarin irin soyayyarsu da kuma wahalhalunda tasha a game da maganar matsalar aurenta.
“Duk cikin rigimar da ake yi babu abinda yafi bak’antamin rai tamkar maganganun Nera na Sonka a gareni, a tunanina in har Namiji ya gano Mace bata sonshi to k’ok’arin kyautatamata da kuma lallashinta ya dace yayi, amma shi kullum da kalar maganar 6acin ran da yake zomin, har yana ik’irarin sai ya wulak’antani in na shiga gidanshi”.
“Da hakan yake tunanin zan amincewa aurenshi?, ko babu Mukhtasheem a zuciyata bazan ta6a lamunta da auren 6acin suna ba, kana zaman zamanka a mayarda kai bazawari cikin k’ank’anin lokaci”.
Hafsat ce ta k’ara tausarta had’e da nuna mata muhimmancin k’ara dagewa da addu’a, domin addu’a ce kad’ai zata kawo mata d’auki.
****
Da fara’arshi ya shigo gidan ya d’auki shimfid’a ya fita, bayan ya zauna sun gaisa ne sannan yace bara ya shiga daga ciki a kawo mai ruwa. Ba yanda Kabiru bai yi ba kan nunawa Baba ba sai an kawomai komai ba, amma duk da hakan sai da ya shiga gidan ya d’auko mai ruwa da zo6o da yake itace sana’ar su Mama.
****
“Wai Habiba kin lura da rawar kan da Malam ke yi tamkar ya take kan jinjiri?”.
“Na gani Yaya, ai mu ido ne namu yanzu har muji wane mataki kuma zai koma d’auka yanzu”, hakan suka yi ta tattauna matsalolin had’e da jiran tsammanin me Malam zai ce.
****
Bayan Baba ya matsa wa Kabiru yasha ruwa da zo6o kad’an ne sannan yakai dubanshi ga Malam yace’ “Baba nazo maganar ajiyata ne daga gurinku in har wani bai rigani ba”.
Ba k’aramin dad’i Baba ya jiba, saboda a tunaninshi mafita ce ta zo mai wacce zai samu watsi da maganar Alk’ali cikin ruwan sanyi ba tare da sun d’ora mai laifi ba.
Sai da ya yi gyaran murya sannan ya furta’ “a halin yanzu haka ana cikin rigingimun maganar auren ta da wani ne, saboda Yarinyar nan ta bad’a min k’asa a ido sai da na kawo mata wanda zata aura tayi tsaye ita bata sonshi, ga mutumen dattijo wanda yasan mutunci da kuma darajar rik’on aure”.
“In dai tak’aicema magana Yarinyar nan har gurin sarki ta kai k’arana wai na hanata auren wanda take so”.
“Amma yanzu ga mafita tunda kazo ka shirya muje in gabatarda kai gurin Alk’ali, zan nuna mai cewa tun wancan lokacin ka bada kud’inka na nagani inaso, hakan zai Sa dole su janye maganar wancan su baka”.
Zurum ya yi yana nazari akan maganar ta Baba, sai murmushi ke bayyana akan bafulatanar fuskarshi.

( _Plxxxx kuyi manage da wannan bamu da nepa ne in mun samu zaku jini anjima_}.

© *SDY JEGAL*💝

[3/2, 6:27 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{16}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ _Wannan shafin naku ne Zauren karatu, Adda Benaxir, Allah yabar k’auna_}.

           Kallon Baba kawai yake yi, sai da ya tabbatar ya samu matsaya alamar ya kai k’arshen maganarshi sannan Kabiru ya furta’ “gaskiya ni dai Baba indan ta nine to na yafe Fateeha, dama tun fil azal ita ba rabona bace, dama yawon garuruwa Sana’a ne ya d’aukemin hankali”.
“Sannan yanzu ko da nazo ga abinda na tarar, to gaskiya ni na hak’ura Baba. Baya ga hakan ina rok’onka alfarmar da ka barta ta auri wanda take so in har Yaron yanada mutunci kuma ya fito daga gidan mutunci”. Da hakan ya yi shiru domin sauraren me Baba zai fad’a.
“Kawai kace min dama ba son Fateeha kake yi ba shiyasa, amma in ba hakan ba ai ga dama ta samu da zaka same ta”.
“Ba haka bane Baba, tabbas ina son Fateeha, amma naga cewa har manya sun shigo cikin maganar ne shiyasa zan janye, amma Baba kayi hak’uri Allah yasa hakan yafi zama alkhairi a garemu duka, daga hakan ya tashi ya yi mai sallama ya k’ara gaba.
Baba ji yake yi tamkar ya janyoshi yayita jibga kan haushinda ya bashi, yaso yayi amfani da damar nan yakai Kabiru matsayin mafita a gareshi, amma ko yanzu ba komai zanga k’arshen abin wai karuwa ta zagi shegiya.
*****
RANA BATA K’ARYA

    Kamar yanda Baba ya rok’i alfarmar a bashi sati uku masu zuwa to gashi yau sun cika. Tun safe ya shirya yaje gidan Alk’ali, bayan sun gaisa ne Alk’ali yace mai, “gashi har ka iso dangin Ango basu k’araso ba, koda naga har yanzu ma da sauran lokaci”.
“Ranka ya dad’e ko yanzu alfarma nazo nema saboda fasowar wasu abubuwa, nayi iya k’ok’arina domin ganin na kammala komai amma abin ya gagara, kasantuwar yanayinda ake ciki yanzu na halin yau da gobe”.
Shiru Alk’ali ya yi yana mai nazarin maganganunshi, tabbas yasan yanayin yanzu ya ta6a kowa, in can farko Mutum zai iya lalurar dubu ashirin to yanzu mawuyacin abu ne zai yi ta dubu goma, “to yanzu wane lokaci kake ganin zaka bada wanda kana da tabbacin zuwa lokacin komai zai zo dai-dai?”.
“Abani nan zuwa sati biyu, insha Allah komai zai kammalu kamin lokacin”.
“Kanada tabbaci akan hakan?, karfa sai lokacin yazo kace kuma baka shirya ba”.
“Ahhh ba matsala, zuwa lokacin komai yazo k’arshe da yardar Ubangiji”. Daga hakan suka yi sallama ya fice daga gidan.
****
Matarshi ya kira yana mai gaya mata uzurinda Baban Fateeha ya kawo, had’e da nuna mata yayi duba da yanayi ya kar6i uzirinshi, saboda haka ta shiga ciki ta yiwa Fateeha bayani, shi zai kira Baban Yaron ya gaya mai.
Tun Matar Alk’ali bata kai k’arshe a maganarta ba Fateeha ta d’auki kuka, saboda ita tun ba yau ba jikinta ke bata mawuyacin abu ne auren nan ya tabbata lokacinda Baba ya d’iba. Nan dai Hajiya ta lallasheta kuma ta had’ata da Hafsat don ta k’ara kwantar mata da hankali, ita ko ta wuce zuwa kitchen.
*****
Sadeek ne ya shigo gidan da sallamarshi ya d’auki wanka iya wanka, bayan sun gaisa da Innarmu ne ya kai dubanshi ga Mukhtasheem da yake ciro kayanshi da zai saka ya furta, “ai ni na zata koda zan zo har shirin naka ya fara biyar iska, ashe kai kana nan zaune ko shirin baka yiba”.
“Kaima dai ka fad’a, tun d’azu nake yi mai magana ya kimtsa tun kan lokaci ya gabato sai washemin baki yake yi tamkar mai tallar maclean”.
Murmushi ya yi sannan ya ciro babbar farar galilarshi ya saka, hula ce a hannunshi yana gyara karin nata sai ga sallamar Malam.
“Ya haka Maigida ban ganka da goron ba, ko ka bawa abokinka Malam Tanimu ya siyo ne?”.
Murmushi ya yi mai kama da yak’e sannan ya nemi guri ya zauna ya tattara hankalinshi gurinsu’ “kamar yanda kasan cewa mutuwa da lokacinta haka shima aure da nashi lokacin, duk iya yanda ka mato a son abu in har lokacin ka rik’a abin nan bai yi ba tofa ba yanda zakayi, da hakan nake son ka fauwalawa Allah lamurranka”.
“Yanzu dai na fita da sunan muje siyen goro sai ga kiran Alk’ali yana nemana, hakan muka wuce ni da Malam Tanimu sai gidan nashi. Bayan mun gaisa ne yake gaya mana cewa Baban Yarinya ya rok’i alfarmar a d’aga mai k’afa saboda fasowar wasu abubuwa. Aure dai yanzu kam sai nan da sati biyu, saboda haka karka sakama ranka damuwa”.
Baya yayi tagal-tagal tamkar zai fad’i, Sadeek ne ya yi saurin taroshi saboda shine kusa dashi, nan take idonshi suka rine suka yi jajir dasu.
“Bansanka da karaya ba Mukhtasheem, na sanka da juriya da kuma jajircewa, ka tuna da fad’ar bahaushe cewa Rana bata k’arya, kuma duk abinda aka sakama rana muddin akwai rayuwa to zai zo, ka natsu ka saka ma rayuwarka salama”. 

( _™ of Mukhtasheem kun bashi shawara ya hak’ura?, lolx_)

© *SDY JEGAL*💝

[3/2, 12:25 PM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{17}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

( *Wannan naku ne Yan Gidanmu Nagarta writers Association ku da Musha karatu*)

        Ido kawai yake bin Innarmu dasu tamkar wani ta6a66e, saboda yana jin zafin abin a ranshi sosai, “Innarmu ba wai nak’i tawakkali bane, abu d’aya nake tunawa na mutanen da na gayyato domin halartar wannan d’aurin auren ya zanyi dasu yanzu”.
“Ba ma wannan ba yanzu fisabilillah Baban Fateeha yasan da cewa bai gama shirinshi ba kuma yak’i yiwa kowa bayani sai yau da yasan itace aka saka domin d’aura aure. Nasan ya yi wannan abin ne domin tozarci a garemu gabaki d’aya”.
Innarmu ce ta rik’a lallashinshi had’e da kwantar mai da hankali, hakan yasa ya cire kayan jikinshi ya ajiye su ma’adanarsu sannan ya shiga kiran mutanenshi Sadeek na tayashi suna gaya masu an d’aga d’aurin auren.
*****
Gidan ya shigo da guntuwar fara’a kwance akan fuskarshi, wanda hakan ba k’aramin kayarma Mama da gaba ya yi ba, haka kawai ta ji ta tsalgu har cikin ranta.
“Ya haka Malam banga ka zo mana da goron d’aurin aure ba?”, fad’ar Mummy kenan data bishi da kallo yana Neman shiga d’akinshi.
“Da zan fita sak’on siyen goro kika bani hala?”. Ganin cewa ya maidata wata sha ka wuce yasa ta k’yaleshi, daga baya kuma ta yi nazari kan sanin cewa in har za’a shekara a hakan ba zai koma d’auko zancen ba yasa dole ta ajiye fushinta a gefe sannan ta furta’ “goron auren Fateeha nake nufi fa”.
“Saboda naga yaune dai-dai da sati uku d’inda ka d’iba na auren”.
“Wai aikin banza harara a duhu, inaga dai yarinyar nan kamar ni na haifi abata, sannan dai-dai da rana d’aya ban ta6a rok’on wani daya taimakamin da abinda zan ciyar da ita ba tun daga tashinta har karatunta kawo yanzu, saboda hakan ko wannan ya isa a sakamin ido da abata”. Yana furta hakan ya janyo shimfid’a ya sanya a tsakar gidan ya yi kwanciyarshi.
Mama ce ta tashi ta fad’a d’akinta da zuciyarta dake mata suya tamkar zata 6allo ta fad’i sanadiyyar fuskantar inda zancenshi ya saka ma gaba.
Mummy ce tabi bayanta domin kwantarmata da hankali, guri ta nema ta zauna sannan ta fara magana kamar haka’ “don Allah yaya ki cirewa kanki damuwa game da halayya irin ta Malam, kin riga da kinsan halinshi tun ba yau ba, sannan kinsan komai muk’addari ne daga ubangiji, in fa bai k’addarto auren Fateeha da Mukhtasheem ba to babu mahaluk’inda ya isa ya auramasu juna”.
“Kina tunanin damuwarki za ta sa Malam ya sauko daga dokin nak’in da ya hau ko kuma yaya?, abu mafi sauk’i a kullum shine addu’a”. Hakan dai ta yita kwantar mata da hankali har ta samu nutsuwa a ranta sannan suka fito filin gidan domin cigaba da aikinsu.
****
Sadeek ne zaune shida Mukhtasheem suna hirar yau da kullum, Sadeek yace’ “wai kanada labarin ashe akwai wani da ke son Fateeha itama tana son shi can baya kamin shigowarmu?”.
“Ban fahimci maganarka ba fa”.
Murmushi yayi sannan yaci gaba da maganarshi kamar haka, “wallahi wai wani Kabiru ne da suka had’u can k’auyen Raha da d’an jimawa, to daga baya ya daina zuwa gurinta kwata-kwata wanda iyayenta suka yi zaton ko ya janye ne, sai gashi shekaranjiya ya dawo”.
Wata irin zabura ce Mukhtasheem ya yi had’e da furta “no wonder, biri yayi kama da mutum, kuma ruwa basa tsami banza, tun farko na yi zargin ba banza ba Baba ya d’age wannan auren, ashe da wata a k’asa”.
“Sadeek me nayiwa Baba ne da baya sona?, ina da wani aibi ne wanda ni bansan dashi ba?, ko kuma na ta6a yi mai wani rashin mutunci ne wanda ni na manta da nayi?”. Yana kai k’arshen maganar sai hawaye sha a idonshi tamkar famfo.
“Ko d’aya Mukhtasheem, in dai kaji ana fad’ar rashin had’uwar jini to wannan itace, za kaga baka ta6a aikata wani mummunan laifi ga Mutum ba amma sai kaga gaba d’aya shi baka yimai ba, to jininku ne Allah bai had’a ba”.
“In har za kayi la’akari ai tun kan shigowar Nera na sonka Baba ya nuna bamu yimai ba, wanda kuma hakan ce ta samo asali har abin ya ta6a Y’arshi sanadiyyarmu, shiyasa ma nayi tunanin ko hak’ura zamu yi mu janye saboda dawowar wancan”.
“To abinda ya hanani magana jin cewa Kabiru d’in ya nunawa Baba ya hak’ura a bata wanda take so wanda hakan bai yiwa Baba dad’i ba ko kad’an. Saboda haka ka daina 6ata hawayenka ba wani abin tashin hankali bane, mudai k’ara dagewa da addu’a”. Da hakan ya samu ya shawo kanshi har ya aro dangana ya yafa.

© *SDY JEGAL*💝

[3/2, 12:36 PM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{18}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ *Wannan page naki ne Sis Feedoh Deedoh, saboda kinfi kowa son wannan littafin*}

                Kwanaki sunja wanda Mukhtasheem ya had’a nashi da nashi yayi gurin sana’arshi saboda yaga cewa zaman ba zai yi mai ba.
Tun kan ya wuce Innarmu ta saka shi gaba da k’arin nasihohi masu kwantar mai da zuciya da kuma k’warin gwuiwa na babu gudu babu ja baya sai abinda ya turewa Buzu nad’i.
Ba k’aramin dad’i yake ji ba na yanda Innarmu ke yi mai ba, yasan ba kowace Uwa ce zata lamunci wannan gararinba, amma ita ta jajirce ga abinda tasan shine za6inshi.
****
Duk wanda yasan Fateeha a wancan lokacin ya ganta yanzu tabbas ba zai gane taba, abu d’aya zai Sa ka gano itace manyan idon da take dasu, duk ta zabge ta kod’e ta jeme tamkar wata y’ar gudun hijira.
Damuwa goma da ashirin ne suka yi mata yawa, saboda ganin cewa mawuyacin abune Babanta ya sauko a wannan lamarin ganin cewa ya fara saka rana yana d’agewa.
Hukunci ta yanke na tunkarar k’anen Mahaifinta da maganar ko Allah zai Sa adace su d’aura auren kowa ya huta. Da wannan shawarar ta fita ta tunkari k’anen Babanta da maganar, nan take ya bata tabbacin ta gayawa Mukhtasheem nan da kwana hud’u su yi shirin d’aurin aure.
Da murnarta ta koma gidan Alk’ali Farouk tana gayawa Hafsat yanda tayi da k’anen Mahaifin nata, itama ta taya ta murna na ganin komai zai zo k’arshe.
Nan dai ta samu wayar Hafsat ta kira Mukhtasheem ta gaya mai yanda sukayi da k’anen Babanta, shima ya yi murnar hakan har da alk’awalin zai dawo gobe.
******
Kamar yanda k’anen Babanta ya yi alk’awali hakan ta kasance yau don kowane 6angare sun shirya domin halartar d’aurin auren k’ofar gidan kakan Fateeha.
Magana ce ta kai kunnen Baban Fateeha inda ya kira waya yana mai gargad’inshi da cewa kar ya kuskura ya d’aurawa Y’arshi aure inba hakan ba komai ya biyo baya shi ya jawa kanshi.
Wayar kawai ya kashe bai koma ta kanshi ba, saboda ya k’udurtama ranshi komai ta fanjama fanjam, saboda yawo da hankalin yayi yawa, ba zasu aminta da ana nunasu a gari ana k’ananun maganganu ba.
Saboda haka yau ya shirya d’aukar kowane hukunci daga yayan nashi, amma yasha alwashin sai ya d’aura wannan auren.
****
6angaren su Mukhtasheem ma ya shiryarda komai na d’aurin aure saboda yanzu har wani k’warin gwuiwa yake ji a ranshi, hakan ya siyi goro da sauran kayan buk’ata suka d’unguma sai k’ofar gidansu kakan Fateeha saboda a can aka yanke hukuncin d’aurin auren.
Kowa ya hallara ana gab da d’aura aure Baban Fateeha ya kira again yana mai k’ara jaddadawa k’anenshi kar ya kuskura ya d’aura auren nan, bai ma tsaya k’arasa jin zancen shiba ya tsinke wayar.
Cikin mintunanda basu haura hud’u zuwa biyar ba sai ga Baban Fateeha ya k’araso gurin da Adda a hannunshi zindir tana walk’iya.
“Tunda na gargad’eka kar ka d’aurawa Y’ata aure kak’i wallahi kana d’aurashi ina fillema kai har lahira”. Masu taron d’aurin auren na ganin hakan kowa ya ari ta kare domin ya samu mafaka, wasu mutane har cikin gidan kakan suka shige domin neman mafaka.
K’anenshi na hangoshi ya falla aguje, domin sanin muddin ya tsaya zai iya aikata abinda ya furta babu tsoro babu wani shamaki sai dai nashi hukuncin ya biyo baya.
****
Tashin hankali, 6acin rai da damuwa sune suka yiwa Mukhtasheem yawa a zuciyarshi, shi yasan yanzu ikon Allah ne kawai ke d’auke dashi, ba don hakan ba da tuni zuciyarshi ta dad’e da bugawa.
Wannan tashin hankalin dame ya yi kama, shi dai yasan cewa tabbas Baban Fateeha baya shaye-shaye lafiyarshi k’alau, to me zai kawo wannan abin cikin jama’a, hawaye ne gaba d’aya suka wanke fuskarshi.
Sadeek ne ke girgizashi shima hawaye sun wanke fuskarshi, “ka ga irin abinda nake guje mana tun wancan lokacin, shiyasa banso ka dulmiya a son Fateeha ba, saboda sanin fiye da hakan ma zai biyo baya wallahi”.
“Amma duk da hakan kayi hak’uri in zaka iya kabar wannan yarinyar   ka huta ma zuciyarka 6acin rai da damuwa, wannan abin yayi yawa gaskiya”, maganar yake yi cikin fad’a da 6acin rai kwance a fuskarshi, saboda ba Mukhtasheem ba ko shi dake abokinshi abin ya fara isarshi, duk abinda aka sakawa gaba so ake aga k’arshenshi amma k’arshen wannan abin yak’i zuwa, “meyasa?”. Ya furta a bayyane.
Cikin razana Mukhtasheem ya tayarda kanshi ya zubawa Sadeek rinannun idanunshi da suka kad’a su kayi jawur ya ce’ “banzaci Kalmar rabuwa ko hak’ura da Fateeha za ta fito daga bakin ka ba, saboda kasan ni kasan waye ni ban ta6a ja baya da duk abinda na saka ma gaba, addua kawai zaka tayani da ita, hakan ba zai Sa inja baya ba”.
Kallon tausayawa Sadeek ke yi mai da mamakinshi a ranshi, cikin ranshi ya furta lallai tabbas Mukhtasheem ka zurma dayawa, a fili ya furta’ “Allah ga bawanka kayo mai agaji acikin lamurranshi”.

( _Team of Mukhtasheem ku taya shi addua kar ya zauce, lolx_)

© *SDY JEGAL*💝

[3/3, 8:29 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{19}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ _Kune da wannan, Taskar Lubiee (Umma ta), Jegal Fan’s, Aneelurv novels, Mata masu aji & Melody novels_}.

           Bayan gayawa Fateeha abinda ya faru ne ta shiga tashin hankali sosai, saboda ita a tunaninta har da laifin way’anda ke tsoron Mahaifinta, me zai sa suja baya akan lamarinta, ita yanzu to waye gatanta a duniya, k’unci ne ya yi mata yawa wanda take ganin da ace zata ziyarci asibiti yanzu mai hana a bata gado tare da mugun labarin cewa tana d’auke da hawan jini Allah.
****
Haj Safiya ce taje ta fad’awa Alk’ali halinda ake ciki, shiru ya yi yana nazarin wannan lamarin na Malam Nura wanda ko a tarihi bai ta6a samun mutum irinshi ba.
Sai da ya tattara hankalinshi zuwa ga matarshi sannan ya furta’ “wannan abin bai cikin tsarin kwanakin da ya d’ibar min cewa sati biyu masu zuwa zai cika alk’awali, saboda haka ni yanzu a maganata dashi saura kwana biyar kenan kuma suna cika insha Allah zan d’aurawa yarinya aure ko da amincewarshi ko bada amincewarshi ba, saboda ba zai mayar damu k’ananan mutane ba”. Da hakan Haj Safiya ta fita domin zuwa ta lallashi Fateeha had’e da bata k’warin gwuiwa.
****
6angaren Mukhtasheem kuwa sak’o ne ya tarar dashi cewa d’aya daga cikin k’annen Baban Fateeha Mata tana nemanshi, bai yi k’asa a gwuiwa ba ya shirya ya ja Sadeek suka je.
Bayan sun gaisa ne ta k’ara bashi hak’uri akan irin abubuwanda ke faruwa sannan ta d’ora da cewa’ “dama na kiraka ne domin in yima wata magana inji ko za’a dace daga gurinka, saboda hakan shine k’arshen kawowar kowace irin matsala”.
Jin hakan ba k’aramin dad’i ya saka Mukhtasheem ba, saboda a tunaninshi wata mafita ce ta daban ta samo mashi. Nan ya bud’a baki yace’ “gayamin koma miye in har shine k’arshen wannan matsalar to zan amince dashi”.
“To masha Allah, dama abinda yasa na nemeka naga matsalarka da Fateeha ko ince da yaya tak’i ci tak’i cinyewa, shiyasa na nemeka domin in wanke ma wannan bak’in cikin, sanadiyyar hakan na baka Y’ata Zainab ka aura halak malak”.
Wata irin zabura Mukhtasheem ya yi saboda har ga Allah bai zaci haka zata furta ba, nan ya bud’e baki yace’ “nagode k’warai da tayinki a gareni, amma inason in gaya maki cewa Fateeha ce zuciyata ke so ba wai danginta ba da za’a musanyamin da Zainab in d’aukesu d’aya ba”. Da hakan ya kama hannun Sadeek suka fice daga gidan.
****
Mama ce ta kira Babanta can Sokoto ta labarta mai duk abinda ke faruwa, hakan ce tasa ya shigo mota yazo Jega d’in wanda suka d’unguma suka nufi gidan Alk’ali ita dashi.
Bayan sun je ne aka gaisa suka k’ara Neman alfarmar ganin k’arshen wannan ta6argazar, bayan sun yi mai bayani ne ya k’ara neman Baban Fateeha domin a zauna asamu tabbacin duk wata matsala ta kau a gareshi.
Lokacinda yazo aka tattauna akai nan ya furta’ “to gaskiya ko za’a kai k’arshen abin sai Mukhtasheem ya biya kud’inda Fateeha taci na Nera na sonka, in ba hakan ba ko a fasa aure asamu wanda zai biya ayi aure dashi”.
Ba k’aramar razana Fateeha da Mama suka shiga ba, musamman Mama da tasan cewa da jimawa Nera na sonka yace ya yafe duk abinda yabada ba.
Gyaran muryar Alk’ali ta dawo dasu hayyacinsu inda ya tambayi ko nawa ne kud’in. Nan Baban Fateeha yace dubu d’ari biyu da hamsin ne.
Wayar Mukhtasheem Alk’ali ya kira ya gaya mai abinda ake ciki, nan take yace zai kawo kud’in zuwa gobe insha Allah.
Bayan ya kashe wayar ne ya dawo da hankalinshi zuwa gurinsu sannan ya gaya masu cewa Yaro ya amince zai kawo kud’in gobe.
Tausayin Mukhtasheem Mama taji a ranta, hakan yasa ta kasa hak’uri ta furta’ “Malam kaifa ka furta da bakinka cewa Nera na Sonka yace ya yafe duk wani abu daya bada, saboda bazai iya ja da hukuma ba ko don gudun 6acin suna”.
Zuciyarshi ce ke wani tuk’uk’i tamkar zata hudo k’irjinshi ta fito, nan take ya rarumo wani katako ya bugawa Mama a kunkuru, sannan ya koma buga mata shi a goshi saida fatar goshinta ta d’aye tana fitarda jini.
Nan take Alk’ali da Babanta suka tashi domin kawo mata agaji, ya zabura zai fice daga gidan Baban Mama ya rik’oshi inda ya wankeshi da mari ya fice daga gidan.
Fateeha ce ke kuka tamkar ranta zai fita, saboda ganin yanda Babanta ya yiwa Mamarta kuma ya mari kakanta wato sirikinshi.
Nan take Alk’ali ya kira D.P.O na y’ansanda tare da bada umurni kan cewa ya yanka mai file za’a shigarda k’ara gobe. Bayan ya gama kora mai bayani suka kwashi Mama sai asibiti aka yi mata d’inki a goshinta.
Suna can ne D.P.O ya kira Alk’ali kan cewa ga wanda ya saka a yanki file a kanshi ya kawo k’ara cewa sirikinshi ya mareshi, nan Alk’ali yace su tsaida shi gasunan zuwa yanzu.
Nan suka d’unguma daga asibitin suka wuce office d’in y’ansanda, koda suka je ko ga Baba wai ya kawo k’arar Baban Mama akan aja mashi hakk’inshi wai ya mareshi.
Abin dariya, abin haushi, abin al’ajabi. Nan Alk’ali ya yi mai bayanin duk abinda ya faru had’e da nuna mai shaidar abinda Baban Fateeha d’in ya aikata.
Bayan haka ya kalli D.P.O yace’ “ku saka min shi a cell na tsawon wata uku”. Daga hakan ya juya domin ficewa daga gurin.

© *SDY JEGAL*💝

[3/3, 12:21 PM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

*Last page*

{20}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ *Wannan shafin Tukuicine, yabawa ne, jinjina ce ga d’aukacin masoyan Jegal, na nesa dana kusa, sanannu da 6oyayyu, Ngd da irin soyayyarku da kulawarku a gareni, Allah yabar k’auna*}

( _A Rayuwa ya kamata Mutum ya natsu yasan mai sonshi tsakani da Allah, Allah ka bamu masoya na k’warai_.

_Akwai shirunda ke nufin amsa a magana, kamar yanda wani kallo ma maganace_
_Sau da dama Soyayyar Nesa ke fin ta kusa tasiri muddin akwai kulawa, D’an hakinda ka raina hhhhh_}

           Ganin cewa da gaske Alk’ali ficewa zai yi daga gurin a saka Ubanta cell yasa da gudu tabi bayanshi tana kuka tana rok’onshi kan cewa don Allah yayi hak’uri kar a rufe mata Mahaifi, kuka ko take yi tsakaninta da Allah.
Juyowa yayi ya kalleta ya girgiza kai, tabbas Uba Ubane ko yaya yake, amma baya ga hakan ta yaya za’ayi tak’i son a kulleshi ko don ta huta. Kakantane  shima ya tako har gaban Alk’ali had’e da furta’ “ranka ya dad’e ayi hak’uri kar a rufeshi in har marinda yayi min ne har ga Allah ni na yafe”.
Hakan tasa Alk’ali yace a sakeshi, daga gurin Malam Hamisu Mahaifin Mama ya shiga mota ya wuce Sokoto, Mama kuma zata bi Baba gida ya watsa mata wani irin mugun kallo wanda tasan inta kuskura ta bishi k’arasata zai yi, da hakan suka d’unguma sai gidan Alk’ali.
**** 
*Washe gari*
Kamar yanda Mukhtasheem ya yi alk’awari zai kawo kud’in Nera na Sonka to haka ta kasance don yazo ya kawo an kira Baba an damk’a mashi kud’in, wanda daka dubeshi lokacin kasan yana cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa, dubu d’ari biyu da hamsin cikin wannan lokacin gaskiya ya more, hakan ya kar6i kud’in ko takan Mama da Fateeha bai bi ba ya fice daga gidan.
*****
Yau ne cikon kwanakin Sati biyu da Baba yace a bashi, saboda haka hakk’inshi ne a nemeshi domin jin ko ya shirya. Bayan yazo gurin ne suka shiga tattaunawa har aka kira Mukhtasheem.
Alk’ali yayi gyaran murya yace’ “kamar yanda mukayi dakai kan in baka sati biyu to gasu yau sun cika, sai ka saka muna lokaci kamar k’arfe nawa za’a d’aura auren”.
“Ranka ya dad’e ka ta6a ganin d’aurin aure babu sadaki babu wasu sauran al’adu haka siddin?”.
Sadeek ne ya tayarda kanshi cikin rud’ani ya kai dubanshi ga Mukhtasheem saboda mamakin wannan furuci na Baban Fateeha, a ranshi yake raya gaskiya abin ya yi yawa.
Alk’ali ya cewa Mukhtasheem “to kaji abinda Mahaifinta ya furta, dama baka biya sadaki ba?”.
Ohhh inda ranka kasha kallo, hakan Mukhtasheem ke rayawa a ranshi, nan dai ya gaya mai cewa tabbas sun bawa kakan Fateeha kudin sadaki dubun hamsin, nan take dai rigima ta k’aure gurin.
Ganin cewa abin bana wasa bane yasa Alk’ali ya k’ara bawa Mukhtasheem hak’uri kan cewa d’aurin aure sai nan da wata assabar saboda za’a bincika aji ina kud’in suke.
Cikin mintunanda basu haura biyar ba Mukhtasheem ya sauya daka kalleshi Kasan zuciyarshi gab take da bugawa, wannan wane irin bala’i ne, haka dai Sadeek ya lalla6a ya rik’ashi suka fice daga gidan tamkar zuciyoyinsu zasu buga kan tsananin tashin hankali da damuwa.
****
6angaren Alk’ali ya yi iya bincikenshi kud’in sadaki sunk’i fita, kowa aka tambaya zai ce shi fa ba’a bashi kud’in sadaki ba, hakan ba k’aramin tayarda hankalin Mama da Fateeha yayi ba su kansu.
Saboda iya tausayi sun tausayawa Mukhtasheem, gashi ya biya kud’in sadaki kuma ya biya na Nera na Sonka wanda suke da tabbacin Baban zai ci abinshi ba kowa ba.
***
Sadeek ne da Mukhtasheem zaune gaban Innarmu suna hira sun tasa abinci a gaba kowannensu da abinda yake sak’awa a ranshi, maganar Innarmu ce ta dawo dasu hayyacinsu inda take furta’ “ni dai shawara d’aya nake baku da ku cirema ranku damuwa, kar lokacin auren yazo ayi k’armusasshen Ango”.
“In har tak’amar Mahaifinta kafiya mu kuma mune naci, tunda ya nuna baison wannan auren kuma Y’arshi na sonka ina mai tabbatar ma in har ba ayi auren nan ba to dama can ba’a rubuta ba a (LAUHUL MAHFUZ).
“Saboda haka in kasan kanada wasu dubu hamsin d’in kacire ka sake badawa a matsayin wani sadaki, wancan kuma da suka ci ba komai”.
Sadeek ya kallo Innarmu cikin razana, ya bud’e baki zai yi magana ta d’aga mai hannu had’e da furta’ “inda arzik’i ai ba’a tsiya, kuma amfanin kud’i biyan buk’ata”. Daga hakan ta koma gurin ayukkanta na gida.
****
Kamar yanda Innarmu ta bashi shawara haka yayi, ya ciro wasu dubu hamsin ya bada matsayin sadaki, nan Alk’ali ya jinjina mai kuma ya k’ara bashi hak’uri da kuma tabbacin ranar assabar mutuwa ce kawai zata hana d’aura auren nan, yaje zuwa shiri kawai, nan ya yi godiya ya wuce.
****
Assabar *12:00pm* dubban mutane suka shaida auren Mukhtasheem da Fateeha, wanda Alk”‘ali Farouk ya jagoranci komai cikin yarda ta ubangiji, inda aka nemi Baban Fateeha har aka shafa fatiha babushi babu alamarshi.
Su kam masoyan biyu je kaga murna gurinsu ranar tamkar zasu zuba ruwa k’asa susha suke ji.
Bayan d’aurin aure kowa ya kama gabanshi, saboda Alk’ali yace sai talata za’a kai Amarya in an kammala sauran shirye-shirya.
****
Ranar litinin aka saka Fateeha a Lalle duk nan gidan Alk’ali akayi komai aka gama.
Washe gari yasa akaje aka duba d’akin Amarya, abin mamaki Mukhtasheem ya yi mata set d’inta na kayan d’aki an saka komai na buk’ata, har kuloli da sauransu duk ya siya mata.
Koda akazo aka gayawa Alk’ali shi kanshi ya jinjinawa yaron, don har garar aure duk ya yi mata saboda gudun fad’e nan gaba.
Tsintsiya, murhu, tukane, electric, risho da sauran kayan buk’atu ne k’ananu da bai siya ba Alk’ali ya bada kud’i aka siyo komi na buk’ata aka saka mata.
Je kaga murna gurin Mama da Fateeha da kukansu suka yita yiwa Alk’ali godiya da irin d’awainiyar da ya yi dasu, nan ya nuna masu ba komai yiwa kaine.
*10:00pm* aka kai Fateeha d’akinta, alk’awalin Allah ya cika, sai dai yi masu fatan d’orewar zaman lafiya, da kuma k’arin dank’on soyayya.
***
Ranar larba ne maganganu suka shigo kunnen Alk’ali cewa Baban Fateeha yace sai ya iskota har gidanta ya fille mata kai, hakan yasa Alk’ali ya nemeshi aka shiga kotu aka rubuta takarda kan cewa ko matsanancin ciwon kai Fateeha tayi zai gamu da mummunar hukunci.
Yanzu haka tana gidanta wata biyu kenan da aure. Inda daga baya aka bawa Baban hak’uri sannan Mama ta koma d’akinta.

TAMMAT BI HAMDILLAH, NA GODEWA ALLAH DAYA NUNA MIN NA KAI K’ARSHEN WANNAN LABARIN.
NA GAISHEKU MASOYANA A DUK INDA KUKE, ALLAH YABAR K’AUNA.
SAI MUN HAD’U A LITTAFINA NA GABA WATO *KOWA DA TASA K’ADDARAR* IDAN MAI KOWA DA KOMAI YA NUFEMU DA KAIWA LOKACIN, *LUV Y’ALL*

© *SDY JEGAL*💝

UBAN NE KO Y’AR? 1-10

​[2/24, 6:46 AM] Sdy Jegal: UBAN  NE KO Y’AR?

{1}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA.

®NWA 

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

GODIYA

Dukkan godiya sun tabbata ga Allah mad’aukakin sarki, mai jin k’an bayin shi, mai badawa da hanawa a duk lokacin da yaso, mai mayar da talaka mai kud’i ya mayarda mai kud’i talaka, mai  kar6ar rayuwar mai lafiya yabar marar lafiya in lokacin shi bai yi ba.
Ya Allah ka bamu ikon biyar abinda yake dai-dai ka kauda idon mu akan abinda yake ba dai-dai ba.
GORO

Ga dukkan masoyan Jegal, Ku saka ma ranku ta ta soyayyar tafi taku, sai dai fatan alkhairi a tsakanin juna.

TUKUYCI

Tukuyci ne gare ku Mamana Faty (Y’ar Mama)
&
Aisha Bala Hali (Aysha-Majid, Mrs Qane).

LITTATTAFAN MARUBUCIYAR:-

Fateema

Bahijja

Sanadin K’unci

Adalilin Gata

Dawa Zanyi Kuka?
MASU FITOWA GABA KAD’AN

Kowa da Tasa K’addarar
Mai Baya….

KU NA DABAN NE A GARE NI
Anty Jidda Musa

             &

Sanah Ismail Sulemain Matazu.
KUNA IYA K’OK’ARIN KU A KAINA
Aunty Sis (Mmn Sulty)

Mommah Mariya Jika

Mommah Snowhite

Shema’u Bello Bari

Maryam Idris Katsina.

DANGINA

Kuna raina, ina alfahari ta yanda Allah ya had’a kanmu, ina mai k’ara addu’a ya kara dank’on zumunci tsakaninmu, ina alfahari daku.

K’AWAYENA
Saratu Abubakar Abdussalam

Ayna Y Ango

Zulaikha’u

Zali Abdullahi

Aminiya Shafa

Mmn Haneef

Mum Faty.

TRUE LIFE SORY

Wannan labarin tabbas ya faru ne da gaske, sai d’an abinda aka k’ara kad’an domin gyara labarin.

        Garin Jega gari ne mai tarin dukiya ta 6angaren manoma, da Ma’aikata had’e da Malamai, masu kud’i, Talakawa, Alhazai da sauran su. Gari ne da suka san mutunci, karamci, had’e da taimakon juna.
 

    Tafiya take yi cikin nutsuwa kan ta nok’e a k’asa wanda ke nuna daga makaranta ta fito wato Comprehensive, na fahimci hakan ne ta uniform d’in da ke saye a jikin ta.
Wani saurayi ke tafe saman mashin a bayan ta yana tafiya kad’an-kad’an wanda ga alamu yarinyar ce yake bibiya, cikin hakan har ta iso unguwar su wato Filin tsakuwa, sai da ta sadu da gidan su sannan saurayin ya wuce daga unguwar.
****
“Sadik yau fa na yi farin gani wanda nake kyautata zaton na samu matar aure insha Allah”. Daga hakan ya gaya mai inda yaga yarinyar da kuma gidan su.
“Duk da bansan halayyar ita yarinyar ba ina mai kyauta ta zaton tamkar ba zaka iya da Families d’in su ba, da hakan nake son ka hak’ura ka nemi wata yarinyar tun maganar bata yi nisa ba”.
“A karon farko dana ganta naji cewa yarinyar ta kwantamin a rai, saboda haka duk matsalar families d’inta ba zai dame ni ba muddin tana So na”.
“To Mukhtasheem ubangiji Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakanin ku, kuma yasa yarinyar rabon ka ce”.
“Haba ko kai fa! Ameen Ameen nagode”, da hakan suka rabu ya shige gidan su.
****
Sadeek da Mukhtasheem abokanen juna ne kuma mak’wabta wanda suka kasance tare tun lokacin k’urciyar su, duk wani abu da suke yi kusan a tare suke yin shi babu 6oyo ko wani k’yashi a tsakanin su.
****
Zaune take saman kujera y’ar tsugune tana wanke-wanke suna hira sama-sama da abokiyar zaman Mamar ta wacce suke kira da Mummy. Yaro ne ya yi sallama yace ana sallama da Fateeha, daga ita har Mummy kallo suka bi yaron dashi kasantuwar hakan bata ta6a kasancewa a gare ta ba, nan dai Mummy tace yaron yace tana zuwa.
Yaron na fitowa ya gaya masu, nan Sadeek ya fitar da d’ari ya bashi, saboda ko sunan Fateeha shi ne ya gaya masu. Tattaunawa suka rik’a yi had’e da fargabar wace irin tarba za su samu gurin ta.
Sallamar da ta yi ce ta mayar da hankalinsu gare ta, nan suka gaisa a mutunce had’e da gaya mata abinda ya kawo su gidan na su.
Fara’ar da ta rik’a yi ce ita ta basu tabbacin kar6uwar da suka samu daga gurin ta, nan dai suka yita hira tsawon minti talatin sannan suka fice ita ko ta shige gidan.
“To yanzu kaga anyi mai wuyar kuma hankali na ya kwanta tunda har ta yi na’am dani, sauran abubuwa sai iyaye su biyo baya”.
“Hakane gaskiya, amma Allah yasa ba ta da wasu manema kar su zo su rik’a takara damu, don na ga budurwar taka kyakkyawa ce”.
“In ma akwai su ba zasu tayar min da hankali ba tunda wacce za’a yi domin ta ta amince da soyayya ta”.
“To Allah yasa ba irin soyayyar y’an matan zamani bace da zasu tara samari sama da bakwai su ce duk soyayya suke yi dasu kamin azo aure an wahala, kuma ma wannan kad’an daga cikin zuri’ar su kenan”.
“Insha Allah hakan ba za ta kasance tsakanina da Fateeha ba, indai har yanda nake jinta a raina haka take ji na to za ka same mu masu rik’e alk’awarin juna”, hakan suka rik’a jayayya har suka kai gida.
***
Da fara’a ta shiga gidan inda ta tarar da har Mummy ta k’arasa wanke-wanken, “ah lallai yau anyi farin kamu, wannan fara’ar tamkar gonar auduga”, tana zolayar ta.
Nan ta zauna tana labarta mata yanda suka yi da Mukhtashim, “lallai ko an taki sa’a, Allah ya tabbatar da mafi alkhairi, amma ina so in har zaki so yaron to ki so shi saboda Allah kuma da zuciya d’aya ba don wani abu nashi ba kuma ba don fatar wani ya shigo ki ka6e yaron ki koma wani gurin ba”, Mamarta ce ke furta hakan lokacin da take ninke kayan shanya daga saman igiya.
“Gaskiya Mama ya yimin kuma da zuciya d’aya, sai dai a taya mu da addu’a”.
“Oh ni Habiba! Yanzu a gaban mu kike furta hakan don rashin ta ido Fateeha”?, fad’ar Mummy.
Da saurin ta ta fad’a d’akin Mama tana mai rufe ido alamar jin kunya. “Ai ke ce kika cire mata kunyar saboda kowace hira yi kike yi da ita”, fad’ar Mama da fara’a d’auke a fuskar ta.

© *SDY JEGAL*💝

[2/24, 6:46 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{2}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ _wannan shafin naku ne, Hindatu Shehu, Fati Salihu, Munirat,  Autar Hjy, Feedoh Y’ar ficika, Fa’iza Tureta, Bizzy, Shatoo, Yaha Saddik, Ashnur, Chuchu, Chuchu2, Faty B-B, Futha, Aneelurv, Zainab Abdullahi_}.

        Mummy ce rik’e da ha6a tana kallon Mama had’e da fad’ar’ “kinsan me Yaya?”. “A’ah sai kin fad’a”, ta furta tana mai dakatar da ninke kayan da take yi.
“Kabiru natuna dashi, duk da cewa kusan shekara biyu yanzu babu d’uriyar shi, amma ina gudun sai maganar ta yi nisa tsakanin ta da wannan yaron shi ko ya dawo”.
“Ina ganin tunda ya kai hakan bai dawo ba da wuya in zai waiwayo ta, takan ma iya yuyuwa cewa ya yi auren shi tunda kika ji shiru”.
“To Yaya Allah dai ya za6a mata mafi alkhairi”, fad’ar Mummy da take zuba ruwa tana wanke gurin da ta yi wanke-wanke, “Ameen”, ta furta a gajarce.
*****
Cikin sati d’aya duk wani mahaluk’i dake zama tare da Mukhtasheem yasan irin son da yake yiwa Fateeha, saboda maganar shi d’aya biyu ta uku Fateeha ce, don kaf gidansu ba wanda bai san ta a baki ba. Koyaushe burin shi bai wuce yaga lokacin auren shi da ita ba.
****
Tsaye suke k’ofar gidansu suna zance ita da Mukhtasheem sai ga mahaifinta yazo shiga gidan, har k’asa Mukhtasheem ya durk’usa ya gaida shi.
Wani kallo ya bishi dashi shek’ek’e tamkar mai kallon kashi a tafin hannu, nan take ya ji tsanar Yaron saboda bai kwanta mashi ba.
Kallon shi ya maida gun Fateeha had’e da furta’ “shige daga nan ja’irar banza da wofi, zanji uban wa ya baki izinin tsayawa da wani a k’ofar gida kuna zance”. Sum-sum ta shige gidan, sannan ya kai duban shi zuwa ga Mukhtasheem had’e da furta’ “uban wa ya baka damar tahowa k’ofar gidana har ka tsayu da y’ata da sunan zance?”.
“Kayi hak’uri Baba, nazo ne domin mu fahimci juna sannan in turo magabatana ayi magana”, cikin ladabi da biyayya yake furta mai maganar.
Kan tsabar haushin da ya bashi ko sauraren shi bai yi ba ya fad’a gidan tamkar guguwa, “Hajara! Hajara!! Hajara!!!”, a na ukun ne ta fito gigice da zane a hannu daya kusa fad’uwa, “Malam meke faruwa hala?, wannan kiran ai sai kasa k’aramin ciki zubewa”.
“Ko mai ma zaki ce yanzu ai tunda kinsan baki kyauta ba, dawa naga Fateeha waje tana zance?”.
“Haba Malam akan hakan ne kake ta k’walamin wannan kiran haka, wallahi duk kasa hankalina ya tashi”.
“Kenan gurin ki ba komai bane, don an mayar dani shashasha d’iyata zata fita zance ba a gayamin ba”.
“Kayi hak’uri Malam ganin nayi kusan mutum hud’u ke zuwa gurin yarinyar nan amma banta6a jin ka yi zancen cewa da iznin wa take fita ba sai yanzu”.
“Duk mai zuwa yazo amma wannan Yaron banson in sake ganin shi a k’ofar gidana, in ba hakan ba daga ke har ita zanyi mugun sa6a muku wallahi”, daga hakan fuuuu ya wuce tamkar guguwa ya fad’a d’akin shi.
Mamaki ne fal a ranta na birkicewar Malam, saboda ta ga sau da dama Samari ke zuwa gurin Fateeha bai ta6a magana ba, asali ma wataran ita ke fad’a kan hakan yace a k’yale ta har ta za6i wanda take so.
“Yaya wai meke faruwa ne naji hayaniya haka?”.
“Ke dai tayani saurare, wai Malam ne ke fad’an kar ya kuma ganin Fateeha da wannan yaron tsaye a k’ofar gida, inba hakan ba zai yi mugun sa6amin”.
“To Yaya abi abin  a hankali saboda kesan zuciya irin ta Malam, kuma yarinya ai ba za a yi mata auren dole ba da ikon Allah, mudai taya ta addu’a itace mafita”, da hakan kowannen su ya shige d’akin shi.
****
Zaune take zurum d’akin su na Yara, duk wani abu da ake tattaunawa tun shigowar Malam har maganar su Mama duk tana jin su. Mamaki take yi kan fad’an Baba akan Mukhtasheem kuma gashi ita ya kwanta mata a rai, shi take so ta aura.
****
“Kayi hak’uri Mukhtasheem ka cire yarinyar nan a ranka tun da kaga Mahaifinta ya koro ka, kabari sai an tura manya sunyi magana sannan aji ta bakin shi”, Sadeek ne ke lallashin Mukhtasheem lokacin da yake gaya mai abinda mahaifinta ya yimai.
****
*Washe Gari*
Tafiya take yi a nitse za ta je makaranta wanda Mukhtasheem ke biye da ita bata ma sani ba, sai da suka kai filin ball na Comprehensive sannan ya sha gaban ta.
Wani sanyi ne ya ratsa ta na ganin shi wanda har ta cire tsammanin ba zai dawo ba, cikin nok’e kai suka gaisa yana mai nuna mata irin damuwar da ya shiga jiya tun komawar shi gida.
Nan dai suka d’an ta6a hira sannan ya wuce ita ko ta shige makarantar hankalin ta kwance da farin ciki fal a ranta.
Ko ba komai yanzu tana da yak’inin korar da Baba ya yi mai bashi zai sa yayi fushi har ya guje ta ba, da hakan ta shiga class duk da ta ma kusa makara.
Bayan sun fito break ne take ta bawa k’awayenta labarin Mukhtasheem, har wata daga cikin su ta furta’ “matsa ki tsaya hirar saurayi har abincin siyarwa ya k’are sai kici Mukhtasheem d’in”, nan sauran k’awayen na ta suka dinga dariya sannan ta wuce domin neman abinda za ta ci.

© *SDY JEGAL*💝

[2/24, 6:46 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{3}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ _Na gaida ku da babbar murya, Benaxir Omar, Umma ta Lubiee maitafsir, Jabo, Meenah D/Musa, Jameela Barrister, Feenat Ja’afar, Mamu, Mrs Saif, Fateema, Wamsyl, Ummietta Wabi, Maryam Yusuf, Biebee Isa, Mumyn Zahra_}.

       Duk inda dangin Fateeha dana Mukhtasheem suke sun san da maganar Fateeha a bakin Mukhtasheem da kuma tashi maganar a bakinta, sai dai har yanzu bai zuwa k’ofar gidansu tun korar karen da Babanta ya yi mai.
Tsakanin Mamar ta da Mummy su ma sun goyi bayan soyayyar da suke wa junan su had’e da alk’awarin aure wa juna duk rintsi duk wuya.
****
Da sallamar shi ya shigo gidan washe da baki tamkar an yimai albishir da gidan aljannah. Mummy ce ta yimai shimfid’a tsakar gidan ta kawo mai abinci kasantuwar lokacin zafi ne, bayan yaci ya yi nak sannan ya k’walawa Mama kira.
“Yau me aka samo ne Malam wannan fara’ar?”.
“Bari ke dai ina cikin farin ciki yau saboda kasancewar maganar Fateeha za ta tabbata, zuwa nan da y’an watanni sai maganar aure”, ya k’arashe maganar d’auke da yalwataccen murmushi a fuskarshi.
Kusan lokaci d’aya su ma farin ciki ya bayyana a fuskokin su had’e da furta, “dama Malam kaine baka fahimci yaron nan ba, gaskiya akwai shi da nutsuwa da kamala, gashi yaro mai mutunci”.
Lokaci d’aya annurin fuskar shi ta d’auke tamkar bai san ya ake murmushi ba, “shin dakata! Wai ke maganar waye kike yi hakan, saboda na kasa fahimtar inda kika dosa”.
“Ga alama ina biyar gabas kina janyo ni kina nuna min yamma, ya kamata ki nutsu ki yimin magana da yaren da zanfi saurin d’auka nan take”.
“Haba Malam waye kuwa banda Mukhtasheem”.
“Wai aikin banza k’iba a kunne, ce maki aka yi wannan tsinannen yaron nake magana?, in nan kika kwana to ki tashi, Akuya ba ta yi wasa da kura ba, ina fatar kinsan Alh Surajo Nera na son ka?”.
“Malam ai duk garin nan kowa yasan Nera na sonka, meke faruwa halan?”.
“Eh to shi nake fatar aurawa Fateeha nan da wata d’aya insha Allah, kinga za ta huta muma mu huta”.
Wannan karon Mummy ce ta kasa hak’uri ta bishi da kallon mamaki, “haba Malam ya za ka d’auki kamar Fateeha ka had’a ta aure da Nera na sonka, ko banza dai kasan ba sa’an auren ta bane, kuma kana sane da wannan yaron da take so shi ma yana son ta”.

“Bayan haka ma ya zaka yi da karatun yarinya da take aji hud’u yanzu?, ya kamata ka d’aga mata k’afa ta gama kuma ta fitar da za6inta”.
“To naji Uwa ta, kin jimin kicifi shege da Gwaggo to gayamin abinda ya dace, ni dai nine da Y’a kuma ni Allah ya d’orama nauyin za6a mata miji, saboda haka na za6a mata Nera na Sonka, ba gudu ba ja da baya, saboda ni na haifi abata”, da hakan ya tashi fuuu ya cika riga da iska  ya shuri takalma yabar gidan.
Jimami suka rik’a yi a tsakaninsu had’e da fatar Allah yasa maganar shi ba gaskiya bace, ko kuma ya sauko ya bawa Yarinya damar auren wanda take so.
“Yo aini Yaya tunda naga ya shigo yana fara’a nasan ba maganar yaron nan ce a bakinshi ba, saboda fahimtar yanda ya nuna tsanar yaron ba gaira ba dalili, kuma gashi way’anda suka sanshi sunce Yaro ne mai mutunci da yasan darajar manya”.
“To ni ko gaskiya bazan goyi bayan wannan ta6argazar ba, kawai yabar Yarinya ta fitarda za6inta, yanzu ai ko k’auye an daina wannan aikin ballantana birni”, ta k’arashe maganar da 6acin rai da damuwa d’auke a fuskarta.
“To Yaya mu dai bi abin a hankali da kuma addu’a wacce itace tafarkin mumini, saboda kin fini sani waye Malam don wani abin sai dai ki gayan shi”. Da hakan suka rufe maganar kowa ya shiga sabgar gabanshi.
****
Dawowarta Makaranta kenan tana tu6e uniform d’inta sai ga Babanta ya shigo gidan da sallamarshi, su Mama ne suka yimai sannu da zuwa, ya amsa yana fara’a ya furta’
“Habiba gaya ma Fateeha ta shirya tana da bak’o a waje yana jiranta”. D’akin ta shiga tana gaya mata sak’on Mahaifinta.
“Mummy ko Baba ya sauko ne?, na ga yau shi da kanshi yake gayamin Mukhtasheem ya zo”. Fahimtar cewa bata gano kan zancen ba ya sa ta bita kallo tana mai girgiza kai.
“Banfa tunanin Mukhtasheem ne, jikina ya fi bani Nera na sonka ne”.
Bakinta ne ke rawa wanda ke nuna alamar magana take son furtawa amma ta kasa, wanda sai ido take bin Mummy dashi.
“Wannan wane irin sakarci ne za kubar mutum a waje tun d’azu, kuma na gaya maki tana da bak’o har yanzu ke da ita ba wanda ya fito”. Bambamin fad’anshi ne ya sa ta saka hijab saman rigarta ta Makaranta sai zane data d’aura ta fito fuska tur6une.
“Saura in kinje kiyimai rashin kunya kizo gidannan kiga me zan yi maki”.
Hakan ta ja k’afa a salu6e ta fita k’ofar gida tamkar ta fasa ihu. Ja ta yi tayi turus tana yimai wani duba mai had’e da tsana k’arara a fuskarta.

© *SDY JEGAL*💝

[2/24, 6:46 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{4}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ _Ban manta ku ba, Mmn Muhsin, Ummy Dr, Shafa Aminu, Zee Zee, Khairat, Jidda Aliyu, Husna, Husna Y’ar Baiwa, Sady Marafa, Mrs Ambursa, Kwaiseh, Aisha Abubakar, Miss Hafcy, Mmn Ansar, Mrs Zannah, Deeja Saudiya, Mmn Jamila_}

{ *Y’ar Uwa rabin jiki, had’i daga Allah, zumunci mai d’orewa insha Allah, nagode da soyayyarki a gareni, wato Hauwer Jidder A.K.A, Allah yabar k’auna*}.

    Murmushin da yake yi mata ne yafi komi 6ata mata rai, saboda yanzu a duniya babu mahaluk’inda take so da kuma muradin gani kamar Mukhtasheem d’inta.
La66anta ne da yaga suna motsi ya bashi tabbacin fahimtar sallama ce ta yimai, wacce ta furta ta tsaya iya fatar bakinta saboda sanin muhimmancin sallamar.
Amsawa ya yi da fara’a d’auke a fuskar shi wanda take ganin yak’e ne yake yi tamkar sabon Alh ya saka hak’orin Makkah. Hakan ya yita janta da surutu wanda daga eh sai a’ah take kar6a mai dashi wanda ya fahimci hakan ya yimata sallama had’e da bata 20k wanda dak’yar ta kar6a ta koma gidan.
***
Durk’ushe take gaban Babanta bayan ta mik’a mai kud’in da aka bata tana mai gaya mai ita gaskiya bata son wannan mutumen, ya yi mata alfarma ya bata wanda take so.
“6acemin da gani ko na 6a66alaki yanzun nan, ke ba abin alfaharinki bane ace Nera na sonka yazo har k’ofar gidanku da sunan aurenki ba?”.
“Bayan hakan ma ki duba kiga zuwan farko ya sallameki da dubu ashirin, wanda ni ubanki rabon dana rik’a  irinsu har na manta. To bud’e kussuwar kunnenki kiji da kyau, ba zaki k’ullan tsiya ba arzik’i na bibiyarmu kisa mu guje shi ba, don haka aure babu fashi ke da shi”.
Kukan da yaci k’arfinta ne ya sa ta fad’a d’akin Mama wacce duk wainar da ake toyawa tana saurarensu ta gaza ta6uka komai akai, dama abinda take tunani kenan auren kud’i yake so ya yiwa Fateeha shiyasa yake tada jiyojin wuya in anyi maganar Mukhtasheem.
Lallashinta ta shiga yi tana mai bata hak’uri kan ta dage da addu’a, ita ma zata tayata domin neman za6in ubangiji.
****
Daka gansu kasan cewa hira ce suke yi irin tasu ta samari, sai dai duba d’aya zaka yiwa Mukhtasheem ka tabbatar da cewa kaf hankalinshi baya gurinsu, saboda yau kwana biyu kenan yana zarya a unguwarsu ko mai kama da ita bai gani ba.
Firgigit ya motsa saboda ta6oshin da Sadeek ya yi wanda koda ya duba duka sauran abokanen nasu sun watse saura su biyu kacal, “wai mi yake damunka ne tun d’azu ana maganar auren Aminu baka ko san muna yi ba?”.
“Yau fa kwana biyu bansaka Fateeha a idonaba, inda jikina ke bani tamkar akwai matsala daga gidansu, wata zuciya na bani shawarar inje gidansu wata na gargad’ina saboda gudun wulakancin Mahaifinta”.
Zurum Sadeek ya yi yana yi masu nazarin mafita wacce za su iya bi cikin sauk’i, sauke numfashi ya yi sannan ya kai dubanshi ga Mukhtasheem ya furta’ “mai nema yana tare da samu, saboda haka kar ka damu mu shirya kawai zuwa yamma muje k’ofar gidansu muga yanda abin zai kasance”.
“Kana nufin wannan ce mafita a gare mu?”.
“Tabbas inada yak’inin hakan, bisa da la’akari da cewa Fateeha bata da waya a hannunta ballantana ka kira ta, sannan ita maganar  aure tana son k’arfafa gwuiwa ba sanyin jiki ba ta hakan ne zaka iya samun nasara akan jajircewarka tunda Yarinya na sonka”.
Cikin second d’inda basu wuce uku ba doguwar fuskarshi ta bayyanar da farin ciki mara misaltuwa, hannun abokin nashi ya rik’a yana jinjinawa had’e da furta’ “samun aboki irinka sai antona, saboda hakan nake alfahari dakai”.
“Kakka damu da wannan domin damuwarka dama tawa ce, fatar nasara kawai nake yima a kullum tunda Fateeha ta rikitamin kai ta hana ma zama shak’at”.
Murmushi ne ya bayyana a fuskarsu dukansu, da hakan kowannensu ya shige gidansu.
*****
*08:30pm*
A bakin k’ofar gidansu Fateeha ta buga musu inda suka samu Yaro suka tura domin yi masu magana da Fateeha d’in, kusan tare suka fito ita da Yaron akan zumud’i.
Gaisawa suka fara yi tamkar sun yi wata d’aya basu had’u ba, nan ya jefo mata maganar meke damunta ya ga har ta d’an fad’a. “Tambayar da nake shirin yima kenan sai gashi ka riga ni”.
“Amsar itace rashin ganinki na kwana biyu, na yi zarya Makarantarku ko alamarki babu inda har ciki na shiga tambayar Malamanku suka bani tabbacin baki zo ba”.
“Wallahi damuwa ce tayi min yawa har zazza6i ya ta6a ni, ai dai za kasan Nera na sonka ko?”.
“Ni ko nasan Nera na sonka, meke faruwa hala?”.
Sai da ta wani 6ata rai tamkar ta rusa ihu sannan ta bud’e baki ta furta’ “shi ke Sona kuma shi Baba keso ya bawa ni, ta yaya ko hankalina zai kwanta ma hakan?”, ta k’arashe maganar hawaye na zarya saman fuskarta.
Tabbas yasan da ace tsaye yake da ba abinda zai hana mai fad’uwa k’asa warwas saboda jin maganar yayi tamkar saukar aradu a ka, wata irin zufa ce ta dinga sauko mai tamkar wanda ya had’iyi kunama.
Sadeek ne ya sassauta murya yanda ko Fateeha ba za ta ji me zai furta ba, k’arfafamai gwuiwa ya rik’a yi har ya samu nutsuwa a ranshi.
“To yanzu a tunaninki miye mafita a gare mu?, saboda kinga tun kamin 6ullowar Nera na sonka Babanki ya nuna bazai bani ke ba ina ga yanzun daya shigo gida”.
“Gaskiya zuciyata bata aminta dashi ba, kuma ba za ta ta6a aminta dashi ba, don haka a wuri na kakka ji haufin komai ni taka ce”.
“Saboda ke kike iko da kanki ba, shegiyar Yarinya ja’irar banza mai kan kwakwa”, mahaifinta kenan daya cire takalmen k’afarshi yana kai mata duka ta ko ina har ta shige gidan.
“Kai ko in tambaye ka tare da ubanka na had’a kud’i nasai wannan gidan ko kuma gadonmu d’aya dashi?”.
Duk wani tsoro ko shakku ya fice a ranshi saboda ganin yanda ya rik’a dukan Fateeha a gaban idonshi, kai ya ta da yana kallonshi had’e da furta’ “ko d’aya Baba, amma don Allah ka taimaka Baba ka bari in turo magabatana a tsaida magana tunda tana So na nima ina Sonta”.
“To sarkin iya tsara zance, naga dai ba Y’ata kad’ai ce Mace a garin nan ba, saboda haka kar na k’ara ganinka a k’ofar gidana saboda na yiwa d’iyata Miji, in kuma ka k’i ji to duk abinda ya biyo baya kai ka jawa kanka”, da hakan ya shige gida ya barsu nan sandare tamkar way’anda aka dasa.

© *SDY JEGAL*💝

[2/24, 6:46 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{5}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ _Wannan page naku ne, Mmn Nuceey, Ummu H², Maryam Atiku, Munirat Ayuba, Aysha Girbo, Miemi Bee, Queen Miemi, Xarah Bukar, Ummul Fadeela, Munayshat, Deeja Abdul, Aysha One, Fareeda Gulo_}.

       Kofin koko ne a gabanshi yana ta juya ludayi a ciki, shi bai sha ba kuma bai ajiye ba, kallo d’aya za ka yimai ka hango tarin damuwa a tattare dashi wacce ta sa ya zabge tamkar wanda ya yi jinya.
“Mukhtasheem! Mukhtasheem!! Mukhtasheem!!!”, na uku ne data had’a da jijjiga kafad’arshi sannan ya zabura da k’arfi wanda ya nuna cewa duk sunanshi data kira har sau biyu ko d’aya bai ji ba.
“Wai ni meke damunka ne kwana biyun nan ka koma min tamkar mai shafar aljanu?, ina fa hankalce da kai yanda ka susuce duk wasu abubuwa na ka sun ja baya, kana da wanda zaka gaya ma damuwarka da ya wuceni ne?”.
Zurum ya yi mata yana saurarenta, saboda ko ya yi yunk’urin gaya mata sai yaga tamkar za ta ce dole sai ya rabuda Fateeha ne, saboda ba kowace Uwa za ta ji ana wulak’anta mata Yaro ba ta yi hak’urin hakan. Baki ya bud’e zai gaya mata kuma ya fasa.
Salis k’anenshi ta kira tace yaje ya kira mata Sadeek. Cikin mintunanda basu haura bakwai ba sai gashi ya shigo gidan, bayan ya gaishe tane sannan ya nemi guri ya zauna.
Kallon karka furta komai Mukhtasheem ya yi mai sannan ya duk’arda kanshi k’asa ganin duk abinda yake yi ashe Innarmu na hankalce dashi.
“Sadeeku ina son na tambaye ka ne akan meke damun abokinka kwana biyu?, kakka manta daga kai har shi duk wanda ya yimin k’arya to zan fahimta saboda hanjinku ne kawai bazan gani ba, amma kaf halayyarku na a tafin hannuna”.
Murmushi Sadeek ya yi sannan ya duk’ar da kanshi k’asa, sanin tabbas abinda ta fad’a haka ne ya sa bai 6oye mata komai ba a game da maganar Mukhtasheem da Fateeha ba.
Gyaran murya ta yi sannan ta furta’ “kana da tabbacin Yarinyar na Sonka?”.
“Eh wallahi Innarmu, asali ma shekaranjia da Babanta ya kore mu daga k’ofar gidansu muna hira da ita tana gaya min irin yanda take So na”, ya furta hakan cikin zumud’i.
“To ina mai k’arfafama gwuiwa da kuma fatar alkhairi, Allah yasa rabonka ce kuma ya nuna muna lokacin”.
Wani irin dad’i suka ji dukansu, saboda basu zaci hakan daga Innarmu ba, asali ma sun zata fad’a za ta yi musu tace kar su koma gidansu Fateeha, nan suka baje suka sha kokonsu cikin walwala da sakin fuska.
****
Takunkumi ya saka mata na bata ba fita nan da k’ofar gida har sai in Nera na sonka ne yazo, shi ma tana zauren gidan, Babanta na k’ofar gida zaune gadinsu saboda kar ma ta fice zuwa wani gurin. 
Babban abinda ya k’ara zautar da Mahaifinta shine furtawarda Nera na sonka yayi kan cewa muddin ya aura mashi Fateeha to tabbas zai kai shi Makkah ya kuma canja mai gida da kuma jari mai tsoka, hakan ya sanya bai ji bai gani duk ya wani haukace tamkar wanda aka kunce daga turu.
Kamar kullum yau ma da kukanta ta shigo gidan bayan ficewar Nera na sonka, saman jikin Mummy ta fad’a tana kuka tamkar ranta zai fita.
“Wallahi Mummy komai za ayi bazan ta6a yarda da auren Nera na sonka ba, yau fa har bud’e baki ya yi yace min tunda na nuna banson shi to wallahi duk ya aure ni sai ya lalatamin rayuwa, sai ya k’ask’antani sai ya wulak’antani, Mummy miye ribar auren irin wad’annan mutanen”?, ta k’arashe maganar cikin k’unar zuciya da damuwa.
“Ai ko in har hakane gaskiya bazata sa6u ba bindiga a ruwa, ta yaya mu ma kanmu za mu zuba ido muna kallon wannan ta6argazar, gaskiya da sake an bawa mai kaza kai”.
“Ba kai aka bashi ba hanji aka bashi, yo wai ma ina ruwanki da duk wanda zan bawa Y’a ta, ke kika haife ta ne?, ke koma ke kika haife ta ba zaki hanamin aiwatar da duk abinda naso ba, irin kune munafukai masu hure ma Y’ay’a kunne su bijirewa iyayensu”, ya k’arashe maganar yana kumfar baki tamkar wanda aka ceto daga halakar shan guba.
“Ni fa Malam duk abinda za ka fad’a sai dai ka fad’a amma wannan abin bazai yuyu ba, kana fa ji yanda yake tutiya da in ya aure ta zai wulak’anta ta sannan kana ik’irarin shi za ka bawa y’arka”.
“Ko namanta zai rik’a yanka ana miya gidanshi bazai hana inbashi yarinyar nan ba muddin ina numfashi a doron k’asa, saboda haka Habiba ki fita idona in rufe in har baki son in sassa6amiki”.
“Yo ai kaima kanada na sama da kai don haka dole a sanarda su abinda kake shirin aikatawa”.
Rufe bakinta dai-dai yake da saukar mari biyu a fuskarta, kan kace kwabo ya hauta yana ta jibga tamkar an aikoshi gurinta, kasancewar Hajara mahaifiyar Fateeha ta fita unguwa.
Kururuwar Fateeha ce ta janyo hankalin mutanen da ke zaune k’ofar gidan tasu, ko da suka shigo ya yi mata lilis baki jini fuska duk shatin hannuwanshi ne.
Dak’yar suka ceceta hannunshi wanda sai haki yake yi tamkar namijin zaki. D’aki Mummy ta fad’a ita kuka Fateeha kuka don ma abin yazo da sauk’i sauran Yara suna Islamiya.
Sai yamma Mama ta dawo daga unguwa tana ta kwad’a sallama shiru ba amsa, k’ofar d’akin Habiba ta tunkara had’e da d’age labulen k’ofa tana furta’ “ba dai baccin yamm…., sauran maganar ce ta mak’ale sanadiyyar abinda taci karo dashi, da saurin ta ta k’arasa d’akin had’e da binsu da kallon mamaki.
“Me ke faruwa haka Habiba, me ya same ki?”, cikin rud’anin da rashin fahimtar abinda ke faruwa take ta jero mata tambayoyin. Kallonta ta maida gun Fateeha da ido suka yi mata sulu-sulu tamkar an dafa gyad’a.
“Tambaya nake meke faruwa daku kunyi min shiru, ina Malam hala?”.
Cikin kuka Fateeha ta zayyane mata abinda ya faru wanda ta k’arashe maganar tamkar ta shid’e kan kuka.
Hawaye ne na hango ke zarya a saman dattijuwar fuskarta, matsawa ta yi kusa da Habiba had’e da dafa kafad’arta sannan ta furta’ “Habiba ki daina saka bakinki a wannan maganar, saboda na fahimci Malam akan wannan maganar zai iya illata kowa don kinsan kafiya da zuciya irin tashi, sannan ko an kai maganar gurin Alhajin Yara ba lallai ne yaji maganar tashi ba, ina mai baki hak’uri da dukanki da Malam yayi a sanadiyyar Fateeha”, nan ta k’arashe maganar tana kuka mai cin rai.
Shigowa ya yi gidan har ya kawo k’ofar d’akin basu san da zuwan shi ba, “haka kawai zaku mayar min da gida tamkar gidan zaman makoki, duk ku 6acemin da gani, d’iya dai ni ke da iko da ita saboda haka na yanke shawarar wanda zan bawa ita, don haka aure nan da wata d’aya da yardar ubangiji”, daga hakan ya cika rigar shi da iska ya bar gurin.

© *SDY JEGAL*💝

[2/24, 6:46 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{6}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ _In har da halacci ya dace na gaidaku, Namcy stylish Bch, Sahaf, Hauwa Nayaya, Mrs Umar, Fiddausi Sodangi, Ummu Abdullahi, Melody, Ummu Ahmad, Fatima Sidi, Mmn Khayree, Mardiyya Khadir_}.

       Cikin sand’a ta fice daga gidan har ta kai unguwar su Mukhtasheem, tsaye tayi gefen wani shago tana lek’en ta ina za ta hango Mukhtasheem saboda a yita ta k’are, Sadeek ta hango zai shiga gidansu ta k’wala mai kira cikin muryarta data koma dusasshiya akan kuka koda yaushe, waige ya rik’a yi domin ganin inda yaji an kirashi, can ya hango ta raku6e bayan shago, da sassarfa ya k’araso gurinta suka gaisa yana mata kallon tausayawa saboda yanda ta koma.
“Sadeek ina Mukhtasheem kwana biyu ban ji shiba?”.
“Mukhtasheem ya yi Kano d’auko wasu kaya, amma ina tunanin yau ko gobe zai dawo insha Allah”. Nan ta kwashe maganar tsananin da Babanta ya saka ta had’e da maganar aurenta da Nera na Sonka nan da wata d’aya mai zuwa.
Cikin rud’ani ya lalabo waya ya kira Mukhtasheem ya bata suka yi magana had’e da tabbatar mata gobe zai dawo, da hakan suka yi sallama ta bawa Sadeek wayarshi had’e da yi mai godiya, nan ya rik’a kwantar mata da hankali sannan ta wuce zuwa gida.
****
Wani irin abu ta ji ya k’ulle mata ciki tamkar fitsari zai fito mata, sanadiyyar Babanta data gani tsaye k’ofar gida tamkar namijin zaki, sai huci yake yi kace kasa ce ta biyo mutum bata samu sararshi ba.

“Inkin dawo daga yawon iskancin naki sai ki wuce ki shiga, zamu had’u dake ne”. Ganin cewa tabbas in taje wucewa ta gurinshi zai iya dukanta ne yasa taja gefe tayi tsaye tana yarfe hannu tamkar mai jin fitsari, sai da ta ga ya hau mashin d’inshi ya buga ya wuce tukuna ta shige gidan da sauri tamkar walk’iya.
Mama ce ta tarye ta had’e da tambayarta ina ta shiga har Mahaifinta ya zo yana nemanta? Nan ta kwashe komai ta gaya mata wanda hakan baisa ta goyi bayanta ba, “wannan ya zamo na farko kuma na k’arshe da zaki d’auki k’afa kije gun saurayi domin neman ya turo gidanku don maganar aure, wannan ba tarbiyya bace kuma ba mutunci bane, ki daina ganin ina goyon bayan aurenku ki wuce makad’i da rawa”, hakan dai ta dage tana mata fad’an so kanka.
Suna hakan ne Mahaifinta ya shigo gidan da wata leda d’auke da wasu k’arafa yakai duban shi ga Mummy had’e da furta’ “ina Fateeha d’in?”.
Jin hakan kawai yasa saida ta saki fitsari tana daga d’akin, “don Allah Malam karka dake ta kayi hak’uri, na yi mata fad’a insha Allah hakan ba zata kuma faruwa ba daga yau”.
Ko ta kanta bai bi ba ya fad’a d’akin Yaran yana kicin-kicin bud’e ledar da ya shigo da ita, abinda ta gani ne yasa fitsarinda take matsewa ya k’arasa fitowa had’e da kurma wani uban ihu da ta yi wanda Mama da Mummy ke rige-rigen shigowa d’akin.
Abinda suka gani ne su ma yasa suka ja dogon birki a k’ofar d’akin had’e da rok’onshi Allah Annabi yayi hak’uri. Yanda kasan wani dasasshen ice haka ya maida su ya fitar da handcuff (ankwa) da yazo dashi ya sanyawa Fateeha a k’afa.
Ba abinda kake ji a d’akin sai kukan iyayen da yaransu, wanda hakan bai sa ya risina ba sai ma wani kallo daya bisu dashi na rainin hankali, “ku bud’e kunnenku da kyau kuji wallahi duk wanda ya kuskura ya yi gigin yanke kwad’on da na d’aure ta dashi daga cikinku sai na kusa aikashi barzahu, saboda haka ku kiyaye”, daga hakan ya fice daga d’akin tamkar wata guguwa har yana had’awa da bankad’e Mama wacce tayi taga-taga tamkar za ta fad’i.
Bak’in ciki ne ya hana mata magana ta juya ta koma d’akinta tana hawaye tamkar ta had’iyi zuciya ta mutu. Mummy ce ta k’arasa gurin Fateeha tana mai lallashinta kan cewa tayi hak’uri, za ta aika a fad’awa Mahaifin Babanta don yasan meke faruwa.
Wani murmushin bak’in ciki ta yi sannan ta furta’ “Mummy kar ki aikawa kowa, ki bar ni a hakan zan so ki fitarda kanki daga matsalata da Baba saboda gudun kar ya kuma huce haushinshi akanki, amma wallahi wallahi bazan ta6a amincewa da auren Nera na Sonka ba sai dai in gawata Baba zai kai gidanshi”.
“In har bai aminta da aurena da Mukhtasheem ba to ya canjamin wani Mijin amma banda wannan mutumen da kalmar wulak’anta ni ta fito daga bakinshi”.
“Gashi magana har ta bi gari cewa Mahaifina ya ga kud’i duk ya rud’e yana takuramin, to wallahi ba na Sonshi kuma bazan aureshi ba”. Jikin Mummy ne ya yi sanyi da maganganun Fateeha, tasan cewa tabbas duk abinda ta furta hakane, sai dai matsalar tasan halin Malam da kafiya hakan Allah ya bashi Fateeha mai irin halayyarshi wanda tasan tabbas duk abinda ta furta hakane har a zuciyarta.
Ajiyar zuciya ta sauke ta ci gaba da lallashinta sannan ta fice daga d’akin rai 6ace.
****
Yau kwanan Mukhtasheem biyu da dawowa amma bai ji d’uriyar ta ba, duk wata hanya da zai bi domin ya ganta abu ya faskara, iya shawara da nazari sunyi shi da Sadeek sun ka sa samun mafita.
Zaune yake zurum yana dogon nazarin miye mafita a gare shi, wanda wani lokaci sai ya ji tamkar ya hak’ura da Fateeha amma zuciyarshi ta k’i aminta da hakan, zungurarshi Sadeek ya yi wanda ya yi dai-dai da dawowa hayyacinshi ya zuba mai rinannun idonshi masu kama da an watsa mai ruwan barkono.
“Kayi hak’uri ka rage ma kanka damuwa, ina ganin ka shirya muje unguwarsu mu bincika muji ko zamu ji meke faruwa da ita”.
Jin hakan ya Sa ya saki murmushi tamkar ita ce a gabanshi, da hakan suka ajiye kan cewa za su je unguwar ta su zuwa bayan la’asar.
****
*5:15pm*
Dai-dai wannan lokacin suka iso unguwar ta su, ganin Mahaifinta zaune k’ofar gidan ya sa suka wuce gaban gidan kad’an suka faka mashin d’insu saboda gudun kar ya gansu. Wani Yaro ne ya zo gilmawa ta gabansu suka tsaida shi had’e da tambayar shi ko yana da labarin Fateeha.
“Tabbbb ai yau kwanan Fateeha biyu kenan da Ankwa a k’afa, ba ta fita ko ina, akan Babanta yace zai aura mata Nera na Sonka tace bata sonshi, kuma…..
“Ya isa je ka mungode!”, fad’ar Mukhtasheem da k’arfi wanda ya sa yaron ya tsora ta ya 6ace tamkar walk’iya.

© *SDY JEGAL*💝

[2/24, 7:11 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{7}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ _Na gaida ku kyauta, Amiyner, Mas’udat Ahmad, Ummu Abdurrahman, Ameera Maisikeli, Mmn Walida, Meesha Lurv, Khadeeja Candy, Sadiyer Fulani cediya, Shukrah_}.

( *Ina mai baku hak’uri na rashin jina kwana biyu, wannan ya faru ne sanadiyyar y’ar matsala data faru komai na wayata ya goge, way’anda kuma nabar group d’insu suyi hak’uri, hakan ba yana nufin na guje su bane groups suka min yawa shiyasa, luv y’all*)

       “Mukhtasheem kayi hak’uri ka natsu in har Fateeha matarka ce babu mahaluk’inda zai hana ma aurenta, in kuma ba matarka bace dole kayi hak’uri”, da hakan ya samu ya lallashe shi sannan ya kar6i mashin ya ja su suka wuce gida.
****
Duk wani d’anuwa ko mak’wabci da ya kamata yaba Malam hak’uri ya yi iya bakin k’ok’arinshi domin ya cirewa Fateeha (Ankwa) da ya saka mata amma abin ya faskara, dai-dai da Mahaifinshi ya yi magana har ya gaji sai dai yace mashi zai cire.
A kullum in za tayi lalura wanka da sauransu sai dai a rik’a ta akaita toilet in ta yi a dawo da ita, tun tana jin damuwa a ranta har zuciyarta ta bushe ta daina jin komai akai, sai dai iyayen da sauran k’annenta dake tausaya mata.
****
Ganin wata irin muguwar rama da yayi ce ya sa Sadeek ke ta bashi shawara kan cewa ya hak’ura da Fateeha haka nan, saboda wannan bala’in ya yi yawa da mahaifinta ke yi da nuna k’iyayyarshi a gare shi.
“Sadeek in har ka ga na bar Fateeha to tabbata cikin d’ayan biyu, an yimata aure ko kuma mai rabawa ta raba tsakanina da ita wato mutuwa, amma in har ba hakan ba bazan ta6a janye maganar aure na da ita ba”.
“Ni kaina farko ina goyon bayanka da hakan Mukhtasheem, amma ka duba kaga yanda abu ya yi tsanani yanzu har (Ankwa) an saka mata saboda gudun had’uwarka da ita”.
Shiru ne ya biyo baya na y’an dak’ik’ok’i sanadiyyar dogon nazari da tunani da kowannensu ya shiga, in har akwai abinda yafi damunsu bai wuce rashin saurararsu da Mahaifinta bai yi ba, ballantana suga fuskar tura manyansu aje ayi magana ba.
Mukhtasheem ne ya dafa kafad’ar Sadeek had’e da furta’ “mafita d’aya itace zan tunkari Baba don ya tura a nema min izni saboda inji wace amsa ce Mahaifinta zai bada, takan iya yuyuwa don bai ga manyana bane yake tunanin kamar lalatamai Y’a zanyi”.
“Eh gaskiya ko ka zo da shawara hakan shine mafita saboda sanin miye matsalar”, da hakan suka shiga gida domin gaya ma Babanshi shawarar da suka yanke.
*****
Kamar yanda suka yanke shawara hakan suka tunkari Baba da maganar, shi ko bai yi k’asa a gwuywa ba ya tura mutanenshi domin nema ma d’anshi izni.
Sai dai ko da suka dawo ba nasara, saboda cewa ya yi ya yiwa d’iyarshi miji. Ba k’aramar razana Mukhtasheem ya shiga ba saboda tabbas ya san cewa yanzu ya rasa Fateeha har abada.
“Ina ganin abu mafi sauk’i ka rabuda yarinyar nan tunda har mahaifinta yace ya yi mata miji, ka nutsu ka mayar da hankalinka gurin sana’arka, sannan kayi ta addu’a Allah ya za6a ma Mace ta gari”, da hakan ya d’an lallashe shi ya samu nutsuwa.
****
Kud’i ne ya shigo dasu mak’udai a hannunshi sai washe baki yake yi tamkar wani gaula, da kanshi ya shiga d’aki ya cirewa Fateeha (Ankwa) da ya saka mata suka fito tsakar gida, su Mama ya k’walawa kira.
Nan tsakar gidan suka had’u kowa ya tsurawa Baba ido saboda hango farin ciki fal a fuskarshi, ga kuma jin dad’in ya kunce Fateeha, bud’ar bakinshi ya furta’ “kud’in na gani ina so ne aka kawo na Fateeha dubu d’ari”.
Cikin sakin fuska Mummy ta furta’ “ko kai fa Malam, Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu”.
“Ai kad’an kenan daga aikin Nera na Sonka, fiye da hakan ma zaiyi, don ina ganin sadakinta ma sai miliyan guda, ku dai rik’a lurar da ita da kuma kwantar mata da hankali zamu ci arzik’i sosai”.
Nan take annurin fuskar kowa daga cikinsu ya gushe sai ido da suke binshi dasu. Mama kam ta kasa hak’uri tace’ “lallai yau na tabbatar Malam kud’i ke rud’arka, wane irin son zuciya ne ya yima yawa? ace sam baka dubin farin cikin y’arka da kuma kwanciyar hankalinta kud’i kawai ka sanya ma gaba”.
“Yarinyar nan in za ka yi la’akari da irin maganganunda Alh ke furta mata bai dace ka nace sai shi za ka bawa ita ba, wannan kawai ya isheka ishara ka san cewa bada zuciya d’aya yake son ta ba, sannan……
Saukar marinda ta ji ne yasa sauran maganar ta mak’ale a bakinta, bugu yake kai mata ta ko ina yana haurinta tamkar mai haurin ball, cikin kuka Fateeha ta fad’a saman jikin Mamarta, Mummy kuwa na rirrik’e Malam inda ya zubar da ita k’asa yaci gaba da dukan Mama da Fateeha sai da ya yi musu lilis sannan ya kwashe kud’inshi ya bar gidan.
Kuka suke yi duka ukunsu tsakaninsu da Allah, “wannan abin bak’in cikin dame ya yi kama, mutum ya koma cikin gida tamkar namijin zaki, babu wata maganar arzik’i tsakaninka dashi kud’i sun rufe mai ido, ni kam ba zan iya lamuntar wannan bak’ar wahalar ba don haka had’a kaya na zanyi in wuce garinmu, in ya aurar da y’arshi inda yake so zan dawo”, hakan Mama ta k’arashe maganar cikin matsanancin kukan bak’in ciki.
D’aki ta shiga ta had’o kaf kayanta da tasan za ta buk’aci amfani dasu ta fito, ba irin hak’urin da Mummy bata bata ba amma tak’i hak’ura, har ta kai k’ofar gida taji Mutum a bayanta koda ta juyo taga cewa Fateeha ce, “koma gidan ubanki ba inda za ki bini, in yaso duk yanda zai yi dake ya yi”, da hakan ta fice daga gidan.
Keke napep ta shiga sai tashar motoci, a can ta samu mota ta shiga sai sokoto birnin Shehu.
****
Mummy ce ta ja Fateeha tsakar gida tana mai bata hak’uri had’e da lurar da ita ko zata sauko ta bi za6in Babanta, “wallahi mummy sai dai Baba ya kashe ni bazan ta6a aminta da auren Nera na sonka ba”.
Lallai tabbas ta yarda da ake cewa da yawa kake haifar d’a ya biyo wasu halaye na ka bai zarce ka ba, to gashi Fateeha ta biyo kafiya irin ta Mahaifinta har ta soma wuce shi, “Allah ka shirya mana yaranmu baki d’aya, Allah ka iya mana kar ka barmu da iyawarmu”.

© *SDY JEGAL*💝

[2/25, 8:37 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{8}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

( _kuna cikin raina, Sumeeluv, Fati Jajimaji, Umm Hydar, Ummuaseem, Xee Ahmad, Mrs-Gee, Mmn Sadiq_).

      Ko da Malam ya shigo gidan ko ta kan d’akin Hajara bai bi ba ballantana ya duba ya lafiyar jikinta na dukan da ya yi mata, hakan ya yi sabgarshi ya fice daga gidan takan kowa bai bi ba.

****
Yau kam Mukhtasheem ya yi shirinshi domin zuwa gurin kasuwancinshi, saboda ganin cewa in har ya zauna zai yi asara biyu ce, ba sana’arshi kuma ba Fateeha. Bayan ya shirya ne zai wuce sai da ya je unguwar su Fateeha ya ga ko alamarta babu sannan ya wuce tasha ya shiga mota sai Kano.
***
WAYE MUKHTASHEEM?

Mukhtasheem d’a ne gun Malam Haruna da Mama Hauwa’u, yana da yayye uku da kuma k’annai biyar, Yaro ne daya taso cikin gatan iyaye duk da kasancewarsu ba masu arzik’i ba sai dai ace dasu masu rufin asiri daga ubangiji, saboda kasantuwarsu masu wadatar zuci.
Tun tashinshi ya taso da son neman na kanshi, saboda yana y’an sana’o’i na yara warinshi, wanda har ta kai ya san ciwon kanshi inda yanzu yake zuwa kano domin d’auko kaya yana saidawa har Allah ya yi mai rufin asiri dai-dai gwargwado.
****
Da ido ya bi Mummy had’e da mamakin jiya ko da ya zo an ajiye mai abincinshi, hakan ya ci ba tare da ya tambaya ina Mama ba har aka kwana yau safiya ta waye.
Yanzu ne da yaga Mummy ta dama koko ta kawo mai kuma sanin ba girkinta bane ya sa yake mamaki har ya bud’a baki ya tambaye ta ina Hajara hala, cikin halin ko in kula ta bashi amsa da cewa, “tana gidan ubanta tun jiya”, da hakan ta shige d’akinta.
Fateeha ya k’wallawa kira d’aya biyu sai a na ukun sannan ta kar6a ta fito cikin kumburarrar fuska da ido tamkar gauta ta durk’usa ta gaida shi, bayan ya amsa ne ya jefo mata tambayar kamar haka, “ina Mahaifiyarki ta tafi?”.
Kamar kar ta ansa shi, saboda jin Mummy ta gaya mai sai kuma ta jure ta ce mai, “ta yi Sokoto tun jiya bayan ficewarka?”.
“Ban gane ta yi Sokoto ba, to da iznin wa ta fice daga gidan nan?”. Shiru ta yimai wanda take ji tamkar ta tsinka mai mari sai dai babu damar hakan.
Ganin ta yi shiru tak’i amsa shi ya buga mata tsawa da cewa ta 6ace mai da gani. Nan ta fice zuwa d’akinsu zuciyarta na yi mata k’una tamkar garwashi.
Bambamin fad’anshi ta jiyo a tsakar gidan, “ni za a kawo ma rainin wayo don na za6arwa Y’ata mijin da nake tunanin shi ne dai-dai ita, ai kowa na so ya samu inda zai je ya huta, kuma ni Nera na Sonka shine za6ina ko da kuwa bak’in ciki zai kashe mutum, Hajara in kin iya kifi ruwa gudu aure ne dai ba fashi sai in mutuwa Fateeha ta yi”.
Tun tana jiyo bambamin fad’anshi har ta ji shiru alamar ya fice daga gidan ko kuma ya shige d’akinshi, hakan tasa ta rego filin gidan ta ga wayam sai ta fice sad’af-sad’af daga gidan. Har ta bi hanyar unguwar su Mukhtasheem kuma ta tuna da fad’an Mama na wancan zuwa da tayi sai kawai ta fasa ta nufi hanyar tasha, a can ta samu motar Sokoto ta bi bayan Mahaifiyarta.
****
“Fateeha ki raba kanki da zaman cikin d’aki hakanan, in ba hakan ba zaki janyo ma kanki wani ciwon na daban, lamarin Malam kawai sai dai a bishi da addu’a”, tana maganar ne tare da yaye labulen d’akin taga wayam ba Fateeha ba alamarta.
Filin gidan ta dawo tana had’a kayan wanke-wanke wanda take nufin Fateeha ta fito ta yi a zatonta tana toilet, daga hakan ta kama sharar filin gidan wanda har ta gama bata ga alamar fitowarta ba.
K’ofar toilet d’in ta zo tana fad’in da mutum har sau uku ta ji shiru, hakan ya sa ta tura k’yauren toilet d’in ta ga wayam, gabanta ne ya yi mugun fad’uwa saboda tabbacin cewa Fateeha bata gidan. Tsakar gidan ta koma ta zauna saman kujera y’ar tsugune ta tasa wanke-wanke a gabanta tana nazarin ina ta shiga to.
Sallamar Malam ce ta zaburar da ita inda ta bishi da kallo har ya k’arasa shigowa, “ke lafiyarki kika zo kika tasa wanke-wanke a gaba kika zabga wannan uban tagumin?”.
“Malam burinka ya cika Yaya ta barma gida, kuma Fateeha ta gudu, yanzu sai inga wanda zaka aurawa Nera na Sonka, tun abu bai yi nisa ba muke ta baka shawara kan cewa ka janye maganar nan kak’i to yanzu wa gari ya waya?”, ta k’arasa maganar da hawaye taf a fuskarta.
Wani irin k’ugi ya ji cikinshi ya shiga yi, ba k’aramar razana ce ta shige shi ba jin cewa Fateeha ta gudu, to ina ta dosa?, ko dai gurin Mahaifiyarta ta je?, hakan ya jera ma kansa tambayoyinda yasan ba amsar ko d’aya a gare shi.
Mazgewa ya yi ya nufi hanyar d’akinshi had’e da nuna bai damu ba, “haba Malam yanzu ko kare ka ajiye gidanka na tsawon shekara goma sha bakwai yana tare da kai a kace ya 6ata kana sharewa baka je nemanshi ba ballantana d’an da ka haifa da cikinka”.
Wani kallo ya bita dashi shek’ek’e duk da tsorace yake ya furta, “tabbas in kare ne zan je nemanshi banje neman wannan Yarinyar ba, kuma wallahi wallahi wallahi kinji rantsuwa uku ko nan da k’ofar gida bazanje neman ta ba, saboda ban haifi d’an da zai wulak’anta ni a gari ba ko waye shi, yanda tasa k’afa ta fice  gidan nan da kanta hakan za ta dawo komai dad’ewa, in ma yawon bariki za ta je Allah ya bata sa’a”, da hakan ya k’arasa shigewa d’akinshi.
Mummy baki ta saki tana mamakin wannan ikon Allah, tabbas tasan halin Malam da zuciya da kuma kafiya, amma bata zaci abin nashi ya kai haka ba, lallai hankalinshi ya karkata ga dukiya, hannunta ta tada sama had’e da fad’ar’ “ya Allah duk inda wannan baiwa ta ka a fad’in duniyar nan ka tsare mana ita, ka kare mana ita da kariyarka Allah”, da hakan ta shafa sannan ta koma bakin aikinta.

© *SDY JEGAL*💝

[2/26, 7:33 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{9}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

{ _Fahimta fuska, kowa ya iya allonshi ya wanke, lolx_}

      Da sallama ta shiga gidan tana raku6e-raku6en batasan wace irin tarba zata samu a gidan ba, musamman data tuna da furucin Mama cewa kar ta biyota ta zauna gidan ubanta. Shahada ta yi kawai ta fad’a gidan saboda taga hakan ba zai yi mata ba.
Salallamin Inna Rakiya ne ya ankarar da Mama jin tana furta’ “wa nake gani hakan kamar Fateeha, ke da wa kika zo?”.
Nan Mama ta fito ta bita da kallon mamaki, saboda ba tayi zaton cewa za ta biyota ba ko a mafalki, duk da rabin hankalinta na gurinta sai dai tarin addu’a da take binta dashi.
Kakarta ta rungume had’e da ratsa kuka tamkar wacce aka yiwa mutuwa, “wallahi Kaka bazan koma gidanmu Baba ya lalatamin rayuwa ba, ku duba yanda wanda yake son auramin ke fad’a da bakinshi sai ya wulak’anta min rayuwa in har ya aureni amma zaku saka mai ido ya auraminshi”.
“Yo ke Fateeha wannan kafaffen uba naki wake iyawa da halinshi?, mu fa bamu da iko dashi sai abinda ya zartar a kanki, abinda zakiyi duba akai da yana da isassu to hakan ba zata ta6a faruwa ba, kiyi hak’uri kibi za6inshi kinji Y’ar nan”, tana maganar ne had’e da lallashin ta.
“Wallahi Kaka bazan ta6a lamunta da wannan k’addararren auren ba sai in gawata za’a kai gidan wannan mutumen, kuma in har ya fi k’arfin iyayenshi to bai fi k’arfin hukuma ba ai”.
Kusan lokaci d’aya Mama da Inna Rakiya suka had’a ido da mamaki fal a ransu, Mama ce ta yi mata magana da cewa ta tashi ta shiga d’aki. Bayan ta shige ne Mama takai dubanta ga Inna tace’ “kinga irin abinda nake gaya maki Inna, na rasa wace irin kafiya ce ke da wannan yarinyar, akan hakan naso lurar da Malam kan ya bata za6inta amma abin ya faskara, shi ya kafe kan sai wannan Alhajin ita ko Mukhtasheem take so”.
“Kuma shi Yaron da take so bai da wani mugun hali ko wata illah da za’a guji had’a zuri’a dashi, sai dai kwata-kwata Malam baya k’aunar Yaron bansan abinda yasa ba”.
Inna ce ta girgiza kanta cikin jimamin wannan lamarin, tun tahowar Mama take gaya mata abinda ke faruwa, sai dai bata zaci abin ya kai haka ba sai tahowar Fateeha yanzu, “yanzu mu jira har Babanki ya dawo muji me zai ce a kai”.
****
Yau ne Mukhtasheem ya dawo daga Kano, bayan ya huta ne yaja Sadeek sai unguwar su Fateeha, nan ko suka ci sa’a Babanta ba ya k’ofar gidan, da shahada suka shiga har zauren gidan suna kwad’a sallama. Daga cikin gidan Mummy ta turo Suleiman domin ya duba wake sallama, nan suka tambaye shi Fateeha yake basu amsa da cewa ai Fateeha ta 6ata tun shekaranjia, amsar da Mummy ta ji yana basu yasa ta saka hijab d’inta ta lek’o zauren gidan.
Nan suka gaisa had’e da yi mata bayanin ko su waye, nan ta kwashe komai ta gaya musu had’e da furta’ “amma nasan da wuya Fateeha ta wuce Sokoto  gidansu Yaya”, da hakan ta basu address d’in gidansu Mama Hajara, nan suka yi mata godiya suka fice daga gidan.
****
Bayan Baba ya dawo ne Mama Rakiya ta kwashe komai ta gaya mai, nan ma ya rasa me zai ce akai, sai dai ya furta Fateeha ta yi zamanta har aga iya gudun Mahaifinta, shin zai neme ta ne ko yaya, da hakan aka bar maganar domin jiran tsammani duk da Mama Hajara bata tunanin Mahaifin Fateeha zai binciki inda ta shiga akan kafiya irin tashi.
****
Yau ta kama kwanan Fateeha biyar kenan a Sokoto amma babu alamar aiken Baba na cewa yana bincike ko da tazo Sokoto d’in, abu d’aya ke damun Mama har cikin ranta shine yanda Malam yake kan bakanshi ta wannan auren, wanda babu abu d’aya daya ta6a girgizashi har yayi tunanin fasa wannan auren, kuma tasan hakan ya faru ne sanadiyyar kud’in da Nera na Sonka yake bashi had’e da alk’awarin Makkah da kuma canjin gida.
Ita a tunaninta a duniya wane farin ciki ne ya wuce farin cikin d’anka da kuma kwanciyar hankalinshi, saboda duk yanda ka aurar da yaro bai samu zaman lafiya a gidanshi ba to tana ganin kaima baka ba kwanciyar hankali, amma kam yanzu tunaninta ya ta’allak’a ne akan iyaye Mata ke da wannan damuwar Maza ko oho, nidai Jegal nace wasu Mazan ba.
Tana cikin wannan tunanin ne Fateeha ta zo ta zauna gefenta had’e da d’an girgizata saboda fahimtar bata ma san ta iso gurin ba. “Haba Mama ki rage ma kanki wannan tunanin mana, in dai maganar aure ce an zo k’arshe saboda wallahi bazan ta6a auren wannan mutume ba sai dai Baba ya biyashi kud’inshi dayaci”.
“Fateeha ina nazarin halayya ce irin ta Mahaifinki, kuma kinsan dai duk daren dad’ewa dole ki koma gabanshi ko gaban danginshi, saboda bazai yuyu ace kinzo gidanmu kin tare anan za’a yi maki aure ba, duk gatanki na 6angaren aure yana gurin Mahaifinki ko danginshi”, Mama ta kai k’arshen maganar da damuwa kwance fal a dattijuwar fuskarta.
Zurum sukayi su dukansu kowa da abinda yake sak’awa a ranshi domin neman mafita cikin sauk’i, cikin hakane yaro ya yi sallama had’e da furta ana sallama da Fateeha, cikin mamaki suka koma kallon kallo tsakaninsu saboda sanin babu wani mahaluk’i da yasan cewa tana Sokoto d’in.
Mama ce ta kai dubanta ga Fateeha d’in ta ce’ “to ko dai Babanki ne ya biyo sawunki?”.
“Mama ina Baba yasan cewa nan nazo, ko fa Mummy bata san da fitowa ta ba, sai dai in wasu ne cikin garin nan”.
“Tun shigowarki garin nan ina tunanin ko nan da k’ofar gida baki fita ba ballantana ace wani ya ganki har yasan sunanki, yanzu dai ki tashi kije kiga wake nemanki”.
“Wallahi Mama tsoro nake ji in ba Baba ne yazo ba, kar inje ya wuce dani gida”. Dariya ta so ba Mama amma ta basar ta matsa mata taje dai ta gani.
Da hakan ta saka hijab d’inta ta nufi zauren gidan duk da a tsorace take da fitar don Mama ta matsa ne yasa ma ta fita d’in, abinda taci karo dashi ne ya sa taja tayi turus daga zauren ta ma kasa fita.

© *SDY JEGAL*💝

[2/27, 7:43 AM] Sdy Jegal: UBAN NE KO Y’AR?

{10}

DAGA TASKAR Y’AR MUTAN JEGA

®NWA

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

      Sadeek ne ya ji tafiyar mutum ya juya suka had’a ido da ita dai-dai tana tsayawa a zauren da mamaki kwance a fuskarta, “to ki k’araso mana tunda kin tada mana da hankali kin hana mana shak’at mun zata Nera na Sonka ya gudu dake”, hakan Sadeek ya k’arasa maganar cikin zolaya da murmushi d’auke a fuskarsa.
Hakan ta k’arasa gurinsu farin ciki fal a ranta, wani irin kwarin gwiywa ne take ji na jajircewa kan auren Mukhtasheem, saboda ganin yanda shi ma yake biye da ita akan duk wani runtsi da take ciki. “Sannunku da zuwa, ya hanya, ya mutan gida?”.
“Komi da kowa kalau, sai dai tarin fargabar rashinki, amma yanzu hankali ya kwanta tunda gamu gaki”, fad’ar Sadeek.
“Ina ko hankali ya kwanta tunda har yanzu banda tabbacin za ta iya zamowa Mata a gare ni, Fateeha don Allah ina so na tambaye ki akwai wani aibi ne da Baba ya hango ni dashi wanda ni bansaniba har yasa yake gudu na akanshi?”, hakan ya k’arasa tambayar tamkar zai yi kuka.
Ba k’aramin tausayin Kansu take yi ba akan wannan matsalar, amma insha Allah zata nemi mafita kamar yanda ranta ke raya mata a kullum, saboda hakan ce kawai zai kawo musu kwanciyar hankali. Da hakan ta kwantar mai da hankali  suka shiga hira har suna gaya mata Mummy ce ta gaya masu su zo nan.
 

Daga baya ne ta tuna da Mama bata ma san dawa take magana ba ya sa ta shiga gidan ta gaya mata cewa Mukhtasheem ne ya zo, je kaga murna da farin ciki gurin Mama na jin dad’in yanda ya biyo Y’arta sokoto.
“Yo shiyasa kika baro Mijin nawa k’ofar gida saboda kishin kar ya shigo ya ganni yace ya fasa aurenki”.
“Kai Kaka har kinban dariya, in ba lalurar majina zai rik’a yimaki ba miye abin so a gurinki?, ke dai ki lalla6a da naki tsohon ya fi maki”, ta k’arashe maganar tana mai murmushin zolaya.
Nan aka yi masu shimfid’a ta fita ta shigo dasu, inda aka taryesu da ruwa sai kuma fura da nono. “Ni inda nasan da zuwanku ai da na rangad’a maku girkin da in kuka ci sai kunce ba Fateeha kuka zo gani ba ni ce kuka zo gani”. Ba su Mukhtasheem ba dai-dai da Mama sai da ta yi dariya sosai.
Bayan sun natsu ne Malam ya dawo daga kasuwa ne an gaisa suka shiga zantawa kan mafitar da ya dace abi. “To ni dai kunga banda hurumin da zan aura maku da Fateeha saboda dangin Mamarta muke, in har Babanta ya k’iya maku to ku tuntu6i wani cikin k’annen Babanta ko Mahaifin Mahaifinta tunda yana nan da ranshi, takan iya yuyuwa cikinsu a samu  wanda zai iya tank’warashi”.
“Gaskiya ko munji dad’in wannan shawarar, saboda tun fara wannan rigimar bamu ta6a tunanin hakan ba gaskiya, mun gode sosai sai kun jimu”. Da hakan suka tashi domin wuce wa, nan Fateeha ta raka su suka k’ara tattaunawa sannan suka wuce.
****
WAYE MALAM NURA?

    Asalinsu y’an garin Kimba ne zama ya kawosu a garin Jega, kuma y’an babban gida daya had’a Matan aure hud’u da Yara kusan ashirin Maza da Mata. Sun taso cikin gatan iyaye musamman ubansu, saboda yana daga cikin mutanen da za’a lissafa su a masu kud’in Jega, wanda daka ce Alh Inuwa kaf Jega an sanshi lokacin yana tashe a garin ba abinda yaranshi suka nema suka rasa muddin baifi k’arfinshi ba, hakan tasa yaran suka tashi a sangarce ba kwa6a ba kyara kowa abinda yake so shi yake aikatawa.
A cikin zuri’arshi ne Malam Nura ya fito wato Mahaifin Fateeha wanda ya kasance mai zuciya da kuma kafiya tun tashinshi, ya kasance yana da Matan aure biyu da kuma Yara tara wanda cikinsu ya aurar da biyu Fateeha ce ta uku da zai aurar yanzu.
Mama Hajara kuwa Y’ar asalin garin Sokoto ce kuma marainiya kasantuwar bata da Uwa bata da Uba yasa ta taso hannun Inna Rakiya da Malam Hamisu da suka zame mata iyaye, saboda Malam Hamisu ne kacal ya rage a cikin K’annen ubanta yasaka da matsalar auren Fateeha ta saka ta gaba ta kwaso kayanta ta koma can har taga iya gudun Mahaifin na Fateeha.
Amma tana tunanin daga Mahaifinshi har y’anuwanshi mawuyacin abu ne asamu wanda zai iya tank’wara zuciyarshi, kasantuwar tashin da suka yi cikin sangarta yasa tun suna Yara ba’a cika nuna musu kuskure ba ballantana fad’a ya biyo baya da har zasu fahimci wannan kuskure ne bari mu gyara saboda gaba.
Ita dai addu’arta a kullum bata wuce ko da ba zai aurawa Fateeha Mukhtasheem ba to ya za6a mata wani mijin na daban da yasan mutunci had’e da sanin karamcin zamantakewa, amma har ta yaya Mutum yasan cewa Yarinya bata sonshi don yaga Ubanta na tilasta mata akan kud’i zai rik’a tsorata ta da bak’ak’en maganganu na rashin kwanciyar hankali, tabbas itama kanta ba zata goyi wannan k’adararren auren ba da za’a ce ga dukiya amma cinta ba zai yi rana ba tunda babu kwanciyar hankali, gara talauci da kwanciyar hankali duk da Mukhtasheem kanshi ba za’a ce dashi talaka ba saboda yasan zafin nema.
{ _Don Allah iyaye mu natsu mu gane cewa su waye Mazan da ya dace mu bawa yaranmu da aure, a kullum kwanciyar hankali shine abin nema a Yaronka, muddin ya rasashi kaima naka ba zai ta6a kwanciya ba, Allah ya datar da Yaranmu Mata da mazaje nagari, suma Mazan ya had’asu da Mataye nagari_}

© *SDY JEGAL*💝